Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma hirarsu suka dinga yi da baban
"Almustapha....wai bakaji me ya samu 'yar uwarka aisha ba?" Baba ya tambayeshi
"Naji ummi ta gayan"
"Ta gaya maka ka sanya hannu wajen nemanta ko Allah zaisa a dace?" Kai ya kada
"Ta gayan,zan qoqarta" kallo daya hamza ya masa yasan cewa akwai qulalliya,yana iya gane yanayin almustaphan ta farat daya,suka hada ido da hamza sai mustaphan yasha mur,da ido hamzan ya tambayeshi ya akai,sai ya share kawai,a nan suka ci abincin dare tare da baban,su kuma suka koma wajen ummi anty maamaa bata nan tayi tafiya bare suje wajenta,ganin har sun gama basu fito ba yasa sumayya jan abida suka shiga wajen anty dije,nan gidan ya rude,duk yaran na nan,duka minti ashirin suka mata sumayya tace zata dawo idan sun dawo gida suka fito,ran anty dije fes,ba shakka tafi kowa murna da wannan aure.

      Suna fitowa daga bangaren baban hamza ya dubeshi
"Maan....nasan halinka baka da kirki idan baka ga dama ba,me yarinyar mutane tayi maka ka batar musu da ita?"
"Dakeni ubana sai in gaya maka" kai ya girgiza
"Seriouse almustapha...ka kama musu yarinya kuma kana wani cewa Allah ya bayyanata don iya shege?" Kanshi ya shafa,har yay yana jin haushin abun,haushin yarinyar yaje ji ainun,yanajin dama yana wajen tayi yunqurin turo sumayyan ba shakka ita zai wurgo
"Abinda tamin mutum biyu ne a duniya zasuyi shi na qyalesu,babe taso hankadowa daga bene bata ko lura da abinda ke jikinta ba" kai hamza ke kadawa,eh lallai almustapha zaiyi fiye da haka ma akan wannan
"Bata kyauta ba sam.....amma kayi haquri ka fito da ita ko don iyayenta" kai shima ya kada
"Na riga da na rantse sai tayi sati,saboda haka kada ma ka bata yawun bakinka,sai jibi zata fito" ya sani kaifi daya ne shi,tunda ya fada din bazai canza ba,tilas ya haqura ya qyaleshi.

  ******    *******  ********

     Da yammacin ranar ya isa policestation din,kaman waccan karon a office din DPO suka zauna,ta rame zuwa lokacin tayi baqi kaman ba ita ba,ba abinda jikinta yake sai buga tsami,baki daya taji ta muzanta gaban almustaphan,kallon da yake mata kadai ya sata jin nadama,ga kunyar yanayin da take ciki,bata san cewa haka zai faru ba da ko kallon banza bata yi mata ba
"Ya akai 'yammata?,kin tuna kece kika yi aikin ko har yau sharrin ne dai aka miki?" Kai ta kada hawaye na zubo mata,don bata fata ace ta sake komawa dakin nan koda na sakan daya ne
"Nice wallahi...." Fuska ya sake dinkewa
"To me tayi miki?"
"Wallahi sharrin zuciya ne da sharrin shaidan"
"Qarya kike.....saboda kina sona shine zaki kashemin mata?,na miki kama da sa'an aurenki?" Sai tayi shiru magana ta mata nauyi
"Nace na miki kama da wanda zai kwasheki?" Ya sake tambayarta a tsawace har yana buga teburin wajen,tsoro ya kamata da sauri ta hau girgiza kai
"A'ah....kayi haquri"
"Kinsan me?" Kai ta kuma girgizawa
"Yadda qasa ta haramta wajen jemage ya takata saidai qarar kwana,to haka aurenki ya haramta awajena....sumayya da kike gani...tabata dai dai yake da tashin hankalin rayuwarki"
"Kayi haquri don Allah ya almustapha" yatsanshi ya dora saman lebansa sannan yace
"Ai baki horu ba,zaki koma ne baban naki da kike taqama da shi har kike zagin na sama dake kike tutiyar zaki hanasu cin abincinsu ki ciresu daga bakin aikinsu ya nemoki yayi kuma belinki" ya fada yana miqewa alamun tafiya zaiyi,tuni ta saki kuka ta sauko qasa tana roqarshi tana bashi haquri,sai da ya gama shan qamshinsa sannan ya waiwayo,ya nuna mata kujerarta yace ta koma kai,tuni ta miqe ta koma
"Zaki tafu gida yau bisa wasu sharadai,sharadi na farko....sumayya....kada ki yarda ko kallon banza ya hadaku bare kiyi yunqurin taba jikinta,saboda indai ina raye ta gama shan wuyar mata irinku.....sharadi na biyu wallahi kiki dora da halinki na wulaqanta jama'a zaki dawo cell,ba kuma wannan cell din ba,inda sai kinyi sati bakiga hasken rana ba,and last...ruwanki ne kice ni na kamaki na kulle...ruwanki ne kiyi shiru duk daya" yana kaiwa nan ya miqe,cikin zumudi tace
"Na gode...baxan sake ba in sha Allahu"
"Damuwarki" ya fada yana ciro kudi a aljihunsa ya jefa mata ya fice,a can ya basu umarnin su bata jakarta da sauran kayanta,ya riga ya bata kudin mota,ya sallamesu suna masa godiya ya wuce.

        Kwanansu goma yace ta shirya wannan karon ba inda zashi sai da ita,da kanshi ya murje idanunshi ya tunkari baabaa kai tsaye da maganar,murmushi kawai baban yake yana kallon yadda mustapha ya zama mara kunya yanzu,duk da hakan ya masa dadi,alamune dake nuna zama na dadi tsakaninsu,sai yayi niyyar tsokanarsa,saboda haka ya hade fuska
"Sannu mara ta ido,umminnaka kenan kana nufin batayi dai dai ko bata iya riqo ba ko?,to ka tafi akwai sauran wasu watannin nan gaba ta biyoka tunda ba riqe ta zamuyi ba ai" anty maamaa dake boye dariya tace
"Haba prof,ka barshi mana ya dauki matarsa,ina cewa nan ganin gida naje kwana uku amma ka matsanta sai na dawo"
"Ba ruwanki bilkisu" baban ya dakatar da ita,cikin damuwa ya daga kai ya dubi baban,ji yake kaman ya rusa ihu,murya a shaqe yace
"Idan na tafi ba lallai na dawi nan kusa ba"
"Kada ma ka dawo sai ta haihu" wayyo kadan ya rage ya rusa ihu,sai kawai ya ware baki daya ya fito masa amutum
"Don Allah baba kayi haquri idan laifi nayi ka bani matata,wallahi zan......"
"Allah ya tsare hanya sai kun dawo" ya fada dariyar daya qunshe tana fitowa,kunya ta kama almustapha,lallai yaro yarone komai shekarunshi kuwa wajen babba,sai ya fara shafa kai ya miqe zumbur yana musu sallama,suka amsa suna rakashi da dariya.

        Shima da yaje sai daya wana sumayyan yadda akayi masa,yace nan zata ci gaba da zama shi zai koma,ta amsa amma baki daya kamar wadda aka zarewa laka,sai da suka gama shirin kwanciya sannan ya cafkota yana mata dariya
"Iyeeee,ashe yarinyar ta sab ciwon miji ko?" Dariya ta kubce mata tana kai masa dukan wasa tare da fadin sai ta rama.

  ******    ******    ********

       Sama sama cikin barcinta ta dinga jiyo tamkar muryarsu shi da su'ad,tunda suka iso qasar ta lura akwai abinda ke faruwa tsakaninsu,saidai ta dauke kanta tunda bai shafeta ba kuma basu sanyata ciki ba.

        Randa su'ad ta iso da baturiyar kukunta ranar daga sumayyan har su'ad ding sunga tashin hankali da ainihin almustaphan,su'ad na daga kai suka iso gidan tare da ita,ta kuma bata umarnin shiga kitchen ta dafa musu ita da almustapha nau'in abinci kala kala tunda girkinta ne,da yake sun riga su'ad din isowa da kwana biyu,hakan ya sanya sumayyan bata bi ta kanta ba ta miqa mata kwananta.

       Tunda aka jere abincin ya dinga binsu da kallo daya bayan daya,kallo daya ya musu yaji baki daya basuyi mishi ba,zuciyarshi ma sam ta kasa aminta cewa order tayi musu
"Wadan nan abincin fa daga ina?" Ya tambayeta yaba dubanta,murmushi tayi tana zaton ta burgeshi ne
"Kuku na taho mana da ita ta musamman,kuma mommy ce zata dinga biyanta" wani abu ne ya tsaya masa a wuya,baturiyar mai dafa abinci cikin gidanshi wadda baisan da zamanta ba?,babban abinda ya fara baqanta masa rai wai mommy ce zata biyata albashi,me suke nufi kenan?,ya gaza shi din,wani abu mai daci ya tsaya masa awuya,mutum ne shi da baisan raini,irin mazan nan ne da basa buqatar tsinke ki taimaka masa da shi cikin gidansa,Allah ya hore masa yafi qarfin duka buqatunshi,bai marmarin ko daga waje ayi ma iyalansa kyautar abin amfanin gida,yafiso komai suyi amfani da abinda ya fito daga aljihunsa,kallo yaci gaba da binta da shi wanda take jikinta yayi sanyi,ta rasa wanne irin kallo ne
"Ce miki akayi na gaza daukar nauyin kuku?,ke zaki bada labarin cewa babu irin kukun da bazan iya ajjiyewa cikin gidana ba ko daga ina yake daga fadin duniya,sai dai me?,banda ra'ayi,ke din ke nakeso ki shiga kitchen da kanki a matsayinki na matar aure ki dafa min" sai a sannan ta gane har yanzu yana kan bakansa,tun a can mummyn ta riga ta zigota kan kada ga yarda ya tauyeta tunda ba shi zai biyata ba,hakan ya sanya ta fara fadin maganganu,ransa ya baci ainun,ya sanya mata ido kawai,da yaga bata da niyyar saurarawa ya daka mata tsawa,wadda ta kada hantar sumayya dake cikin nata falon tana kallon film tare da shan fruit,tsoro ya kamata ra ture plate din gefe tana kiran sunayen Allah
"Na baki nan da minti goma ki tattarata ta bar gidan nan"
"Ba inda zata almustapha wallahi" ta bashi amsa daidai sanda kodaddiyar baturiyar ta fito,sanye da mini skert  wanda idan tayi kyakkyawan tsuguno ba abinda zai hanaka ganin mazaunanta da t shirt mai gajeran hannu,wani baqinciki ya sake shaqeshi ya dakawa baturiyar tsawa cikin yaren da zatafu fahinta yake sanar mata ta wuce ta tattara duk abinda tazo da shi ta fice masa daga gida,tuni ta soma rarraba ido don bata taba zatar haka ba,idan ta fita din ma ina zata?,sai su'ad din ta rushe da kuka iya qarfinta ko hakan zaisa almustapha ya sauya qudurinsa,ihun kukan su'ad din shi ya daga hankalin sumayya,ta tsammaci ba lafiya,sabida haka ta yafa mayafi saman doguwar rigar dake jikinta ta fito zuwa babban falo,dai dai sanda mujadala ta harqe tsakaninsu,tuni yace ta hada kayanta itama ta bita,wanda hakan ya sage nata gwiwa,maimakon hana mai girki tafiya sai ta koma qoqarin yadda ita din zata zauna,kallo daya zaka yi masa kaga zallar bacin rai shimfide a fuskarsa,ita kanta sumayyan sai da tsoro ya kamata ganin yadda ya birkice,da addu'a a bakinta ta nufi inda yake zaune saman dining yana fuskantarsu,gefanshi ta tsaya cikin kwantar da murya
"Haba yallabai,haba.....bai kamata ba,ba fa cikin qasarmu muke ba,yanzu ta yaya don kawai ta maka laifi zaka ce tabi baquwar fuska subar gidanka?,kasan kuma yanzun qarfe nawa,a karamcinka ko mai aikin bai kamata kace ta fita ba,koba komai macace mai rauni,balle kuma matarka ta sunna....kayi haquri don Allah ka sawa zuciyarka ruwan sanyi,yanzu kaga baki daya fushinka ya hautsina gidan ummm,ina kake so musaka ranmu?" Shiru yayi yana sauke numfashi sannan ta juya ga su'ad
"Anty....tunda baiso kiyi qoqari gobe ki saya mata ticket ta koma a zauna lafiya don Allah" harara ta wurgawa sumayyan amma bata ce komai ba,saboda ko banza taji dadin ganin almustaphan yayi shiru,miqewa yayi ya dauki muqullin motarshu dake ajjiye kan freezer ya fice,dukkansu suka bishi da kallo,sai da ya gama fita kowacce ta dauke idonta,suka hada ido sumayya da su'ad,sumayyan tace
"Don Allah anty kiyi qoqari ki karanceshi ku daina musayar yawu haka da shi,gaban baquwa fa ba don Allah yasa bata jin yaren ba,haramunne mace ta dinga daga murya sama data mijinta,miji sama yake da kai dole ka saukar da kanka qasa ka bishi,tana janyowa kanta tsinuwar mala'ikun Allah" ta fada a tausashe
"Ke da Allah sauraramin,a naku tsarin ba,ba wanda yafi wani tsakanin mata da miji kowa mai 'yancin yin yadda yaga dama ne,wai wa ya saka da ke ma?" Kada kai tayi babu alamun jin haushu a fuskarta
"Allah ya baki haquri idan kinji haushi"ta juya a nutse ta shige falonta ta zauna taci gaba da binda take,saidai lokaci lokaci hankalinta na kan agogo,har ta soma gajiya da zaman ta buqaci kwanciya bata ji motsin shigowar almustaphan ba,har dare ya soma shiga sha daya da kusan rabi,duk da su a can daren ba komai bane wajensu,hakan ya daga hankalinta,ta dauki wayarta ta dinga qoqarin nemansa saidai sam bata samunshi,sai data gwada a qalla wajen sau biyar ana shida ta dace ya shiga,a jiyar zuciya ta sauke
"haba yallabai,ka tashi hankalinmu fa" shima ajiuar zuciya ya sauke,muryarta ta soma rage masa bacin ranshi
"Me ya faru?"
"Ka fita cikin iyalanka cikin fushi,sannan kuma har war haka ace baka dawo ba ai dole hankalinmu ya tashi ko?"
"Lafiya nake,kawai yau bazan kwama gidan bane,sai gobe idan Allah ya kaimu,ki kwanta kiyi bacci sosai,good night" ya katse wayar yana jin dadin yadda ra kula da shi har ta nemeshi,ya tabbatar idan su'ad ce kota nemeshi qorafi ne abu na farko da zata fara ba tare da kwantar da murya ba,ranan haka ya kwana sai da safe sannan ya dawo cikin gidan,to sai gashi yanzu tana tsaka da bacci ta soma jiyo muryansu,wanda hakan ya sanyata farkawa ba shiri,uwa uba da kuma yunwa data fara tambayarta,har ta shiga toilet rayi brush ta fito tana jiyosu,ga yunwa tana sadakarta,bata so ta fita ta taddasu haka,amma dole ta sanya hijabinta ta fice sanoda yadda cikinta ya soma motsawa saboda yunwa.







*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽


✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



1⃣0⃣2⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*


*ya zul jabarutu wal malakutu wal kibriya'i wal'azmati*
_____________________________________





       Tunda ta fito ta fuskanci maganar dai kusan kan shiga kitchen ne,ita kanta ta gaji da wannan jeka ka dawo magana daya tak mai sauqi amma ta rasa dalilin su'ad na qin yarda da maganar tashi,har zata rabe ta wuce sai kuma ta fasa sakamakon tuna fadar Allah da tayi
"Haqiqa muminai 'yan uwa ne kuyi sulhu tsakanin 'yan uwanku", a nutse ta qarasa wajen da suke tsaye,ta sanya hannunta ta riqe hannun almustapha ta gefe ta yadda su'ad din na zata gani ba ta soma matsawa a hankali idanunta cikin nashi,cikin 'yan kwanakin nan su'ad tasa ta ga halinshi da bata taba gani ba,ta fuskanci yana da fushi saidai yakan jima ba'a ga fushinsa ba,barshi dai da miskilanci wannan tambarinshi ne,sai data fuskanci hankalinshi ya soma dawowa gareta yayin da su'ad rayi carko atsaye tana jiran kota kwana
"maan" karon farko ta kirashi da sunan da mutane ke yawan kiranshi,saidai yaji sunan ya zama wani sabi na musamman daga bakinta,a tausashe hadi da karyar da wuya tace
"Bai kamata ba....." Dakatar da ita yayi da hanzari ra hanyar daga mata hannu sannan ya waiwaya ya dubi su'ad
"Option ne na baki,na kuna rantse yau ko zaki kwanta asibiti sai kin dafa tea din nan,naga wanda zaya sake min order din abinci cikin gida na" yana fadin haka ya zame hannunshi daga nata ya wuce zuwa sashensa,da kallo suka bishi,yayin da gaban su'ad ke faduwa,ta tabbatar da cewa yau din matuqar bata yi abinda yace ba babu abinda bazqi iya faruwa ba,saidai ta yaya zata ta ina zata soma tunkarar kitchen?,sai kawai ta wuce fuuu kaman guguwa ta shige kitchen dinta,sam abun baiwa sumayya dadi ba,hakan ya sanya batayi qasa a gwiwa ba ta bishi zuwa dakinsa.

      Yana tsaye gaban window,hannayenshi zube cikin aljihun wandonshi,qoqari yake yayi controlling kansa tare da hana zuciyarsa aikata abinda take raya masa,so yake yaga ta ina ya gazawa su'ad,ci?,sha?,sutura?,kudin kashewa?,walwala ko adalci,duka babu,babu ko daya daga ciki,hasalima ta wani bangaren tafi sumayyan samun wasu abubuwa,tunda suka fara tarayya da sumayya bazai iya tuna rana qwaya daya tak da ta tambayeshi wani abu ba,saidai shi don gashin kansa ya bata,ko idan su'ad din ta tambaya yayi adalci itama ya bata duk da bata tambaya ba,abinda ya lura ma shine tara su take,ba abinda take da su,shi kansa yasan babu wani anu qwaya daya da na kusa da shi bama iyalinshi ba da zasuyi kukan basu da shi ko yafi qarfinsu,shi a ganinsa babban abun kunya ne ma ace kai din wani je,ko Allah ya maka rufin asiri,ana maka kallon mai rufim asiri,a ganka cikin kama kai kyau amma iyalinka a wahale ko cikin mummunar kama,wannan shine babban abin kunyar da magidanci zai aikata wanda zai jawo masa tur da ala wadai a bakunan al'umma.

       "Abu abdallah" ta furta a nutse,tunda yaji sunan yasan itace,amma hakan bai sanyashi ya waiwayo ba,sai ya nutsu yana jin yadda take takowa zuwa inda yake tsaye,bata dakata ba sai data sha gabanshi,ta tsaya tana dubanshi idanunta cikin nashi kaman yadda nashi yake,duk da cewa a cikin hijabi take,duk da cewa daga bacci ta tashi batai wanka ba,duk da cewa ba ko digon kwalli cikin idanunta amma bata fasa yin kyau ba cikin idanunshi,kyanta cikarta da kamalarta sun fito muraran,ta jima tana kallonshi wanda sannu a hankali dumin da zuciyarsa tayi ya soma sauka,da wannan damar tayi amfani ta soma cewa
"Ina ganin bata haka ya kamata ka bullowa anty ba....bazaiyiwu dare daya kace sai ta maka girki ba bayan can bata saba ba,a mata haquri a bata dama ta koya tukunna...."
"Wacce damar?,wacce dama za'a bata ne sumayya?" Ya furta cikin sanyi,saidai daga yanayin yadda yake maganar kawai kasan ranshi akwai sauran damuwa a ciki
"Akwai damar data wuce na sai mata rana guda cikin ranakun makaranta catering school?,ta koya ita kadai?,cikin gida ko a can duk wanda take so?......daga yau bana son ki sake sanya baki cikin wannan matsalar...ki barmu" ya fada cikin salon dakatarwa,yawu ta hadiye kafin ta sake lanqwasa murya
"Kayi haquri idan hakan ya bata maka,banyi ba da niyyar shishshige...rayuwarka rayuwata ce,haka nan rayuwarka rayuwar su'ad ce,hakan na nuni da cewa dukkaninmu abu guda ne...kwanciyar hankali nutsuwa da zaman lafiyar dayanmu yana da amfani a garemu baki daya,bazanso ace kullum kai da ita ba kwanciyar hankali ba....hakan zai iya shafata zai iya shafar iyalin da muke son samarwa nan gaba,tunda dai muna tare da ku"idanu ya zuba mata yana karantar tsantsar gaskiyar dake cikin zuciyarta da takeson fadi,hankali nutsuwa da karamci ne zallah cikin kalamanta,don me yasa ta samu dama irin wannan maimakon tayi qoqarin tarwatsa zamansu da su'ad ta mallakeshi ita daya saima take qoqarin gyarawa?,kyakkyawar zuciya ce itace amsa,wadda ba kowanne bawa Allah yake wa baiwarta ba,sai 'yan baiwa daga cikin bayin nasa,maimakon ya bata amsa kawai sai ji tayi ya janyota cikin jikinsa ya juyata da hanzari ya rungumeta ta baya yana shinshinarta,duk da cewa batayi wanka ba amma hakan bai hana wannan qamshin nata mai sanyi fita daga jikinta ba,dumin fatarta ya dinga ratsawa cikin tashi,hannunshi ya dora saman cikinta yana yawo da shi,wani farinciki na maye gurbin bacin ranshi,duk sanda ya farka da shi yaje farkawa cikin ranshi,kullum yana lissafe da ranar da zaya iso cikin duniya
"Wannan ne abu mafi muhimmanci da ya kamata ace kinyi zaki tsaya kina wani tsarani" dariya ce ta kubce mata ta soma qoqarin boyeta
"Au tsara ka ma nake yaya?"
"Waye yayan naki,yau kuma yaya na zama?" Girarta ta dage sanda yake leqo fuskarta
"Eh....ko nayi laifi?"
"A'ah....bakiyi ba" ya fada yana cikata tare da durqusawa gabanta,tasan me zayayi tunda ya fara kware mata hijabi,ba dama su tsaya inuwa daya sai ya fara lalubar cikinta,baya ta ja tana ware ido tare da kada masa yatsa alamar a'ah,sosai idanun nata suka fito sun sake wani fari tas da su,hakan yaso shagaltar da shi
"Sulhu nazo nema ba gaidaka muka zo yi ba" sai ya miqe daga durquson da yayi yana ci gaba da kallonta tare da nuna kanshi da yatsa
"Ni kuka yiwa haka?,zamu hadu,awa ashirin cif suka rage" dariya ta saki ganin yadda yake kwatantawa da hannunshi,ta juya taba niyyar ficewa,duk da yadda tayi kewar lafiyayyar fatarsa amma hakan bazaisa ta bashi dama suyi wani anu sq zai sosa ran su'a din ba,abinda ko ita aka yiwa ba zata taba jin dadi ba
"Amma kaman zazzabi naji jikinki ko?" Waiwayowa tayi tana dubanshi
"Ina jin hakan idan na tashi da safe,amma da nayi wanka shikenan bana sake ji"
"Ko nazo na dubaki?" Ta gane sarai wayo yake son yi mata sai ta saki qaramar dariya sannan ta juya ta fice tana cewa
"Mun yafe".

       Kacaniya sosai ke tashi a kitchen din kamar wadda zata dafa abincin baqi dari,ta rasa inda zata tsomala kanta,gefanta sumayyan ta nufa da niyyar dafa ko couse couse ne sharp sharp tunda tana da miyar hanta a fridge,har ta dauko tukunya taji su'ad ta fasa ihu,da sauri ta waiwayo kana ta nufeta,tukunya ta soma dorawa bayan ta kunna gas din,sai da tukunyar ta dauki zafi sannan ta taro ruwa ta soma zubawa,tururin da taga ya taso ya nufo hannunta shi ya sata sakin qara ta yarda cup din ruwan nan ua tarwatse a wajen har ya kashe wutar gas din gas ya soma fita,da hanzari sumayya ta qarasa tana ambatar subhanallah ta kashe gas din,sannan ta dubi su'ad data janye gefe
"Amma dai bakiji ciwo ba?" Harara ta watsa mata,dukkan komai itace ummul aba'isin data tsiri yi masa girki da ya sashi cewa itama sai tayi,da can ai basu san dora tukunya gidan ba idan ba kuku ne yake nan ba,ganin bata amsa mata ba ya sanyata nufar wajen ta sauke tukunyar daga saman gas din ta zubda ruwan ta zuba sabo sannan ta sake kunnawa ta dora,inda suke ajiyan kayan tea ta nufa ta hada ganyayyaki masu dandanon da tasan almustapha naso ta dinga gwadawa tana zubawa ta gama ta sanya ganyan shayin ahmad tea ciki sannan ta maida murfi ta rufe,su'ad na gefe haka kawai taji kishi ya rufeta yadda taga sumayyan nayi,itakam bata lura ba tace da ita ne kawai
"Idan ya dahu zakiji yana qamshi sai ki juye a flask" tsaki ta bita da shi
"Nima na iya ai basai an nunan iyawa ba" bata bi ta kanta ba tayi ne dama kawai saboda mijinsu,tunda ta sani tunda ya kafe tofa sai tayi kuma sai ya dandana ko baici ba,idan bai masa ba dandanon baci zaiyi ba haka zaya fita da yunwar cikinsa.

       Tana tsaka da bare plaitain ta soma jiyo qamshin dahuwar shayin,cikin flask din tea na alfarma dake kitchen din su'ad ta zabi daya ta fiddoshi ta bude ta ajjiye cikin sink,tukunyar ta tsurawa ido,yadda take tururi kawai ya sanya ta tsorata,ta yaya ake juyewa kawai take tunani,haka tayi qundunbala ta janyo towel hand socks dake maqale a hanger da suke ajiye towels na kitchen ta zura a hannunta,murfin ta fara budewa tayi wancakali da shi nan ma tayi gefe tana haki,ta dauki a qalla minti biyar ta rasa ya zata sauke,murmushin mamaki ya qwacewa sumayya,ashe da gaske akwai irinsu su'ad a duniya?,wannan mece a cikin mata,sai kawai ta miqe ta isa bakin tukunyar ta ciri safa daya ta sauke tea din tana juyeshi a flsk din,tana tsaka da juyewa ta matso kuda da ita
"Waike wa ya sakaki,ce miki akayi bazab iya ba?" Sai data gama juyewa ta daga kai ta kalleta
"Na san zaki iya ai,kawai taimako ne kuma ba laifi hakan ko a musulunci" shiru tayi tana daure fuska tare dq zare idanu har ta gama ta kulle flask din bayan ta daurayeshi ta wuce gurin nata sabgar.

      Kusan dai har ta gama bata san me su'ad ke ciki ba,tana gamawa ta juye plaitain dinta ta dumama liver souce dinta ta fice ta bata kitchen din.

       Tun daga lokacin matuqar tana kitchen din zata mata iya gyaran da ya dace,bata damu da duk abinda zata fada ba,tana yine kawai saboda almustaphan,tun tana masifa har ta dawo saidai harara,sau tari dariya take baiwa sumayyan,saboda ta lura da cewa tsabar girman kai ne kawai ke dawainiya da su'ad din,wani lokaci qunshe dariyarta take kawai idan tana girki,abin sai wanda ya gani,taka hau yanar gizo ne ta dubo yadda ake yi,wani abun bai ciyuwa hatta gurin wanda ya takura din sai ta dinga yi,idan har ya ciyu to ranan sumayya na kusa ta sanya hannu,cikin qanqanin lokaci su'ad din ta fara gane shayi ruwa ne,tayi roqon tayi magiyar ya samo mata mai aiki yayi funfurus da ita,har kukan takaici da wuya duka sai da tayi ,ya share tamakar baisan tana yi ba,don wannan ce kadai hanyar da zai hora ta kan iskancin da take ji saman kanta,har sumayya a wani dare take roqarshi ua samo matan wadda zata kama mata,saboda tana ganin yadda ake gwagwagwa wajen dafa shayi ma kawai,har yau ta kasa dauke yadda ake,ita dinma shiru ya nata kaman baiji me tace ba,ganin hakan ya sanya taja bakinta ta tsuke,tasan tunda yayi hakan baison zancen ne,sai da ya tabbatar ta dahu sannan ya samo wadda zata dinga taimaka mata,da sharadin tare zasu dinga yi tana ganin yadda akeyi.

      Abu na gaba daya soma jan hankalinta shine yadda ta fuskanci maan din na nuna tsantsar kulawa da riritawa ga cikin dake jikin sumayyan,da fari ta dauki abun duka wasa,sannu sannu ta soma fahimtar soyayyar da bata taba gani yana yiwa wani abu ba ita yake gwadawa abinda ke cikin dako duniya bai iso ba,bata tabbatar da haka ba sai a wani yammaci wanda ranar sumayya zata karbi girki.

       Tun da yamma tana zaune babban falonsu,bata faye zama

Please Login or Register in order to submit comment