Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ummee,shi yai qasa da kai kunya na lullubeshi,ita kuma ta dauke kai tana sakin murmushin tsantsar farinciki,waskewa yayi da cewa
"Ummee ya adam bai qaraso bane?"
"Ka fadi haka mana tunda wannan karon ka rigashi zuwa,ina zaton sai wajen laraba zai qaraso,amma dai ni'ima ya hadato da yaran sunyo gaba,dazun da safe suka sauka,shi da fahariyya sai ran laraban"kai ya gyada cikin gamsuwa
"Kunje kun gaida maamaan ne?"
"A'ah"
"To bari ta fito sai kuje ku gaisa,da alama itama batasan da zuwan naka ba,babanku kam baya gari,ya tafi jigawa ta'aziyyar wani abokinsu da ya rasu,amma gobe ma zaya dawo" ta fadi tana daga wayarta dake ringing wanda amira ce ke kiranta,bayan sun gaisa take shaida mata zuwansu sumayyan,ihu ta saki har almustapha dake zaune yana jiyota,hararar wayar yake kaman amiran ma wajen,magiya ta dinga kan ummee ta bata sumayyan ta kira wayanta a kashe,dai dai sanda sumayyan ke fitowa daga kitchen din,ummi ta miqa mata wayar,a ladabce ta amsa ta koma gefe tana fidda murmushi,addu'a kawai take kada amiran ta baro zance ta bata kunya,ai kuwa zuba ta hau yi
"Amma namecy kinci amanar qauna da baki gayan har kin iso abuja ba,halan soyayya ta fara zaqi har kin soma mancewa da kowa sai wannan miskilin mijin naki,ina fatan kina bada wuta wajen sukurkuta masa shi muga ta tsiya,tab ai wallahi jibi nima zan taho Allah,ina fata kin samo mana tsaraban baby,wallahi har so nake naga babynku,kyau tako ina,wazai dauko uwa ko uba?,wa yaga ya man ya baby" gaba daya kunya ta cika sumayyan,yadda almustapha kadai ya kafeta da ido tasan yanajin komai amiran ke fada,ta sanshi sarai da kaifin ji,yunqurin datse kiran take sai ya miqa mata hannu,a hankali ta tako ta miqa masa wayar,ya kara akunnensa sanda amiran ke cewa
"Wayyo soyayyya zamu sha kallo......"
"Gidanku mara kunya fitsararra,idan naga qafarki gidan nan jibi sai na karyata na zubar,idan kin musa kuma bismillah" ya datse kiran,daga bangaren amira sai ta kwabe fuska zata sanya kuka,saifullah dake zqune gefanta ya dunga tiqa dariya har da qwarewa da lemon da yake sh,haushi ya sanyata daukan filo ta dinga maka mishi shi kuwa yana fadin
"Maganin aku kuturu mai shegen zance kenan,tun dazun nake kwabarki kiyi a hankali may be suna tare amma kika qi ji,tunda kuwa ya man ya fadi haka ke da zuwa gida sai ana gobe daurin aure"kuka kuwa ta sanya taba buga qafa
"wallahi wallahi ban yarda ba,don kawai kaji ya almustapha ya fada ko?"sai ta saki filon ta wuce bedroom alamaun taji haushi ya miqe da sauri ya bita domin yayi lallashi.

        Boye dariya ummin ta shiga yi tana basarwa,don itama taji wani abun,sauka yayi daga bangaren kira ya shiga wajen adana lambobi,da dai dai ya dinga bi har ya iso wajen lambar da ya tabbata tata ce saboda ga hotonta nan saman lambar,ya dauki wayar shi ya kwashe lambobin ya adana a tashi wayar,ganin yadda kunya ta rufe sumayyan yasa tace
"kuje ku gaida maamaa,daga nan ku wuce sashenku sai da safe ma hadu"
"To" ya fada yana sauke qafarshi wanda ya dora daya kan daya ya miqe ya isa gefan ummin ya ajjiye mata wayarta
"Sai da safe ummee" suka hada baki wajen fada sai da ya waiwayo ya dubeta,dauke kanta tayi ummen ta amsa
"Sai da safe,Allah ya bamu alkhairi".

       Kusan bangaren anty maamaa wannan karon yafi jama'a,hakan baya rasa nasaba da kasancewar ita keda bikin wannan karon,auren yara biyu tak duka maza da Allah ya bata,baki ta kama itama
"almustapha?,tun yanzu?"murmushi kawai ya saki yana fatan kada ta sake cewa wani abu saboda 'yammatan dake falon,bai ko zauna ba hannunshi zube a aljihun wandonshi ya soma gaidata,ta amsa cikin farinciki itama,don ta tabbata lallai hasashen baban ya soma zama gaskiya,tunda ga mustpha ya waiwayi gida ana daurin auren qannenshi saura kwana shida,sumayya kam tuni tana wajen humaida,wadda sukayi farinciki ganin juna,ya waiwaya bayan sun gaisa,ganinta wajensu ya sanya ya basar ya juya ya fice,cikin sakewa suka gaisa da anty maman tana dan tsokanar sumayyan kafin ta miqe ta fice ta basu wuri,ta sake sosai cikinsu humaidan aka dinga hira,abinka da mata gwanayen gulma,kusan kowa kallon sumayyan yake,kowa da irin gulmar dake cinsa arai,yayin da dama daga cikinsu ke jin dama sune sumayyar,a qalla sai gashi sun kwashe wajen awa daya suna shan hirarsu,don humaida har kiran amira tayi ta saka handsfree aka dan taba da ita,hakan ya sake tsokalota taji kamar tayi tsuntsuwa ta taho.

       Tun da ya shigo yaje duba agogo yana kasa kunne amma yaji shiru,har ya kammala shirin kwanciya cikin wasu hadaddun pyjamas masu shegen kyau da suka haska shi,yana son ya daure ya basar amma sai zuciyarsa ta gaza,a hankali ya sauko ya soma takawa ya sauka qasan benen,ya bude dakunan baccinta bai ga alamun ta shigo ba,ya koma sama ya bude dakin baccinta dake sama nan ma babu alamun an shiga,dakinshi ya koma ya zauna gefan gado yana son samin meke sanyashi damuwa haka da lamuranta?,laluba lambarta fake cikin wayrsa wadda yayi servinn dazu yayi sannan ya shiga bangaren aikawa da saqonni ya tura mata gajeran tex
"Come back", suna tsaka da hiransu saqon ya shigo,sai abun ya daure mata kai kasancewar bata da lambarsa,daga bisani ta ajjiye wayar tana zaton batan kai saqon yayi ba wayarta zai shigo ba,mintina goma suka shude shiru,ya sake lalubo lambar ya kira,bugu kusan uku sannan ta daga ta kara kunnenta,yana iya jiyo hayaniyar su ta cikin wayar,haka kawai tasha jinin jikinta duk da batasaj number din ba
"Assalamu alaikum" ta furta a nutse,har cikin zuciyarsa sallamar ta ratsashi,cikin zuciyarshi ya amsa a fili kuma yace
"Bance ki dawo gida ba?" Ta fahimci muryar sarai amma sai tace
"Waye ke magana?"
"Ok,baki gane ba kenan?"
"Eh" ta fada tana sani
"Well" ya ambata shima yana katse wayar,sai ta ajjiye wayar yana qoqarin saukowa daga saman gadon.

       Anty maamaa ce ta sauko daga sama tana duban sumayya
"Lalala amiran umman khalipha?,me kike har yanzu baki wuce gida ba?,ya zaki baroshi shi kadai waya gaya miki ana wannan sakacin,tashi ki wuce tun bai biyo sawunki ba wallahi" ta fadi don tasan halin mustaphan sarai,murmushi ta saki yayim da su humaida suka sanya dariya,humaida tace
"Allah sarki mu da yake warin takalmi muke mu kwana muna hira ma ko anty"
"Yo wa ya damu da ku?", ta fada tana juyawa sama tare da yiwa sumayya sallama,dif dariyansu ta katse baki daya,kowa ya kama kanshi,hakan ya sanyata dagowa,sai ta ganshi tsaye cikin kayan bacci,takowa ya dinga yi a nutse har inda take sandare a atsaye,yasa hannu ya zare wayarta dake hannunta ya dauke cak,baki daya 'yammatan sukayi mutuwar zaune na wucin gadi har ita sumayyan,ko a jikinsa ya juya dauke da ita ya fice daga falon.

       Kallon kallo aka soma yi tsakaninsu,humaida ce ta soma tuntsirewa da dariya,abun ya matuqar burgeta,kamar a fina finan india
" to wallahi tunda guy din nan ya soma haka mu rufawa kanmu a siri mu dinga kora masa matarsa da wuri,idan ba haka ba wataran sai munga abinda idanuwanmu ba zasu iya dauka ba"
"Wai shi dan air ba" inji wata daga cikinsu,wadda a zahirin gaskiya hassada take ji cikin zuciyarta,don itama taso ace ta zama daya daga cikin matanshi
"Ba wani dan air wallahi,har ga Allah abinda ya sanya nakesom auran irin mazan nan,nuna so babu limit ko a gaban waye wallahi,wani miskilin namijin bai iya nuna miki qauna ba,idanunshi basa gani balle suji kunyar kowa" dariya suka sanya suka ci gaba da tattaunawa kowa na fadar albarkacin bakinshi.

         Bai direta ba sai da ya saita mata hanyar matattakala,ya harde hannunshi yana mata nuni da idanu kan ta hau,babu musu ta haura saman kunyar abinda ya mata cikin jama'a na kama ta har cikin dakinshi,qofa ya maida ya kulle ya waiwayo cikin shammata ya turata saman gadon,baki daya ya danneta,ya dora mata nauyinshi,fuskarsa kawai ya dago yana dubanta,idanunshi cikin nata suna musayar numfashi,sosai ta gane kuranta,numfashinta ya soma mata nauyi
"Qirjina ka daga ni"
"Eh ai so nake na nuna miki banbancin,don na lura kin soma rainani saboda kinga makwancina.....me kike gayawa amira take rawan qafan zuwa ta sameki?,sannan me kike gayawa wadan can shashashan suke babbaka dariya kaman hauka sabon kamu?" Narai narai tayi da idanuwa,yatsansa ya dora saman lebansa yana fadin
"Shshshshsh,banson wani kuka,idan kuwa kika sake kikayi yau tilldown zanyi sai an miki ruwan zafi"cikin taushin murya a shagwabe da son qwatar kanta tace
"Allah babu komai ka yarda dani"sosai ta masa kyau,shagabarta ta taba zuciyarsa qwarai,murmushi na son qwace masa amma ya dake,bai son ta gwada abinda su'ad taso dauka dabi'ar yi,wato kwarzantashi da yabonshi da fadan qwarewarshi a kan shimfidarsu gurin qawayenta,randa kunnensa ya ji masa Allah ya sanya ranar ta soma,mutum biyu ta gayawa,ranar taga tashin hankalin da bata taba gani ba,don cewa yayi tunda ta gaya musu to ta sa a ranta sai ya auresu babu fashi,har ciwo sai da yaso kamata,babu shiri ta fatattakesu sukayi baran baran bata sake ganinsu ba,da qyar ta sha kanshi
"ta yaya zan yarda da ke?"
"Saboda da gaske nake,ba aninda zan gaya musu,nasan fa haramunne mace ta dinga fadin sirrin mijinta,Allah ya la'anci mai aikata hakan"murmushin da baiso dole ya kubce masa,sai ya samu kansa da sanya hannunshi kan hancinta yana jan hancin
"au Allah,ashe ni din mijinki ne" kunya ta kamata,ta rasa inda zata tsomala ranta,sai kawai ya rintse idanuwanta
"Kada fa ki tsammaci na haqura,dole ki bani wani abu da zai sanyani na haquran,idan ba haka ba,Allah yau sai jikinki ya gaya miki" ya fada yana shan qamshi,da sauri ta bude idanunta,kamar zata saka kuka
"To ni mai zan baka?,banda abinda zan baka"
"Akwai" ya fada yana jifanta da wani kallo wanda shi kansa baisan yana mata shi ba,sosai take amsar saqon da yake aikata mata,sai ta kasa janyewa daga kallonshi tamkar masu kallon quda,nuni yayi mata da bakinshi yana cewa
"Kiss me,shine kadai zai sanya na haqura" da sauri ta dago kanta da niyyar yi masa din don ya barta,nauyinsa da kunyarsa take ji amma shi baya gani ne wai,tana dora bakin nata ya hade su waje guda ya shiga sarrafa shi yadda yake so,bashi ya barta ba sai da ya tsotsi lips dinta son ranshi,da gudu ta fada toilet,tana iya jiyoshi cikin rarraunan murya mai taushi yana cewa
"Be carefull,ke da su yanzu akwai banbanci"mamakinsa take,wai almustapha ne haka?,dama haka yake?,tayi maganar a zuciyarta tana tsaye gaban mudubi tana duban kanta murmushi ya qwace mata,wanka ta sake yi saboda kwanciya sannan ta daura alwala ta fito.

       Gaban drawer ta ganshi tsaye ya zuge jakarshi,jikinta ta shafe da turaruka bayan ta shafa mai wanda ya qarawa fatarta laushi,ta taka a hankali ta isa inda abun sallah yake ta shinfida zata yi shafa'i da wutiri,har ta idar yana tsaye kaman mai nazari,qaramin tsaki ya saki ya koma gefan gadon ya zauna ta daga kai tana son dubanshi,wai meke sauyashi haka ne?,dazu da zata shiga toilet murmushi ne kwance saman fuskarshi amma yanzu ba haka bane,can qasa taji yace
"Gobe adam zaizo zamu wuce jigawa wajen baba,i think sai wajen alhamis zamu dawo tare da shi"
"Allah ya nuna mana" ta fada tana miqewa ta fahimci kayan sawarshi yake son hadawa ya kasa,hakan ya sanya ta qarasa bakin cupboard din ta soka zaqulo kayan daya bayan daya,sai ya bita da kallo,yana son yaga damuwar tafiyar da zaiyi ya barta ko qanqani ke saman fuskarta,mutum ne shi mai son a kula da shi,rashin hango hakan da baiyi ba sai ya sake dagula masa lissafi,sam baison zuwa jigawar nan,saidai umarnin baban babu abinda zai hanashi binsa matuqar hakan bai sabawa mahalicci ba.

         Wani tsakin ya sake ja,yanajin duka lissafinshi ya dagule,bai taba jin wata tafiya ta dameshi ba sai wannan 'yar qanqanuwar tafiya da bata kai matsayin komai ba a irin tafuye tafuyen da ya saba yi,ya bar gida tsawon wata da watanni ba'a ganshi ba shima baiga kowa nashi ba
"Bar kayan,zan samu wasu a can,zo nan" ya fada yana dubanta,ta waiwayo sannan ta tako a hankali zuwa inda yake,da idanu ya nuna mata hijabin jikinta,gabanta ya fadi,bata tsammaci zai ce ta fidda shi ba shi ya sanya ta gwada wata riga da amira ta bata,ta mance da ita baki daya sai yau cikin kaya ta ganota,idanunshi a kanta yana tabbatar mata da cika umarninsa,haka ta sanya hannu tana ji tana gani ta cire din
"Sunbahanallah" ya fada da wani irin amo,hannunshi ya bude mata yana jingine da gadon,sai taci gaba da takowa har inda yake ta shige jikinsa ya rufe hannayensa yana shinshinar qamshinta,ta jima ajikinsa yana abinda ranshi keso,zuwa sannan ya soma sakin layi,a kunnenta ya rada mata
"Naso na barki to have some rest,but i will miss you gobe,zan iya kasancewa dake?,kin amince?" Kanta ta daga masa cikin kasala
"Thank you,thank you soo much" ya fada cikin murya mai cike da shauqi,yanayin yadda ya tafi da ita ya tilasta mata bashi cikakken hadin kai wanda hakan ya yi masa dari bisa dari.

      Tana jikinsa amma tunaninta yake,wannan daren ya sake zamar masa na musamman,wani abu ya tsaye masa game da ita,ji yake kamar ya nemi alfarma wajen baba ya barshi a nan,ko kuma ya dauketa su tafi tare,saidai babu damar hakan,ya tabbata tunda baban ya nemi ganinsu wani muhimmin abu zasu yi a can.

        Yana tsaye yana shiryawa itama tana tsaye kusa da shi tana miqa masa duk abinda zaiyi amfani da shi,yau din ma dai surukuta suke taqi kallonshi,duk da yadda taso ta morewa kallon nashi,sakamakon shigar shadda da yau yayi,duk da cewa ba dinkin tazarce bace amma tayi masifar yi masa kyau,kwalliyar taso ta tafi da ita don dai kawai ta maze,ga kuma kunyar da jiya ya bata,har ya kammala shiryawa tsaf ta miqa masa kofin hadden coffe wanda ta daidaita masa zafinshi,kofin na riqe a hannunshi,tururinsa da qamshinsa na shiga masa hamci,yayin da dukkan idanunsa da tunaninsa suke kacokam a kanta,ya lura sarai shigar tayi mata,amma bai furta mata ko nuna mata ba
"Wai dama haka aure yake?,haka ake ji?" Yake qiyasatawa a ransa,a hakan yasan bata gama sakewa da shi ba,baisan wanne matsayi ta bashi cikin zuciyarta ba baya ga matsayin miji,sarari yake nema wanda zai zauna ya dasa mata zazzafar soyayyarsa cikin zuciyarta,don har yau baisan a wanne rank ta bashi ba,sai data gaji da shirun ta waiwayo ta dubeshi
"Yana sake hucewa,yaya kuma na jiranka"
"Eh jira dama nake ki gama yajin aikin kallona din sai na sha" ya fada yana kai kofin bakinsa,kai ta kautar tana murmushi a boye,a haka sai ka rantse bai iya magana ba sam,amma idan ya yankota a nutse sai ta tsaya maka.

        Ta baya taji ya ruqota,ya mannata da jikinsa kansa saitin kunnenta
"Me zan samu?" Ya fadi yana duban wani kwantaccen gashi dake wuyanta mai santsi,shiru tayi tana tunanin me yake nufi,ganin bata ce komai ba sai ya dora
"Zan wuce,kada ki fiya fita wajen gidan nan,coz nasan akwai baqi da yawa da za'a iya yi a kwanakin nan,ok?"kai ta gyada tana jin wani iri babu dadi,sakinta yayi sanda wayarshi ta soma ruri ya duba yaga yaya adam ne,wanda ya gama shirinsa shi kadai yake jira,ya tsammaci ma shi zai rigashi gama shiryawa kamar yadda aka saba,sai gashi wannan karon almustaphan yana son ya makarar da su,juyawa yayi a hankali zaya fice,sai ta biyo bayanshi cikin sanyin jiki tace
"adawo lafiya,Allah ya tsare hanya,a gaishemin da baba"saqon yayi masa dadi,sai yayi kamar zai juyo sai kuma ya fasa,ya amsa da
"ok" yana ficewa,bayanshi tabi da kallo,bata taba ganin mutumin da kayan hausawa suka masa kyau har haka irinsa ba.

       Haka kawai take jin ba dadi,wani yanayi na shigarta,qarfafa jikinta tayi ta gyare ko ina tsaf,sannan tayi wanka tare da yin madaidaiciyar kwalliya ta yafa wadataccen mayafi ta fice wajen su ummee,sai data shiga ta gaida,gidan babu laifi ya sake cika,ga jikoki nam sun soma halartar gidan,yaran huda anty farida da 'ya'yan adam yaran kishiyar ni'ima data taho da su,a wajen maamaa ta hadu da ni'iman,fuska sake suka gaisa,hira ta dan gudana tsakaninsj,haka nan ni'ima ta kwantawa sumayya kamar yadda sumayyan ta kwantawa ni'ima,daga bisani tace bari taje wajen ummee,a can ta tuqe wajen ummeen,cikin siyasa ummen ke janta da hira tana son taji ya zaman nasu yake,sosai tayi qoqarin nuna mata komai lafiya yake,hakan ya sake faranta ran ummeen matuqa,sai ga amira da azahar a gidan,ranar sunga tabara,tunda taji labarin yaa man din sun tafi jigawa tace sai ra taho,ya saif ya iya da tabara,haka ya barta amma da sharafin wuni kawai zata dinga ta dawo,wunin baki daya ya zowa sumayya cikin sakewa,hankalinta kwance,babu gilmawar eesha sam,bata san ina tayi ba,bata san meke faruwa ba don haka babu abinda yazo ranta gamenda eeshan,bata koma sashenta ba sai bayan isha'i,kasa zama tayi,baki daya sashen nata yayi mata babu dadi,hakan ya sanya ta koma neman 'yan kwana,da fari kowa qi yayi,sabida sashen ba wajen zuwan kowa bane,daga mai sashen har uwar gidansa ba masu jan jama'a bane,humaida da humaira suka ce sai sunje,hakan ya sanya nadiya da yusra binsu suma,a dakin gadonta na qasa ta saukesu,hakan ya debe mata kewa matuqa,don suna tsaka da hira bacci ya kwashesu.

         Washegari ummee ta danqa mata kayan fitar biki kamar yadda ta yiwa ni'ima fahariyya da su'ad,haka ummeen take,duk wani sha'ani idan ya taso sai ta yiwa jikokinta da 'ya'yanta kayan fitar biki,macace mai hannun kyauta,hakan ya sanya mutane da dama kejin dadin zama da ita,kowa takan masa dinkin ne daidai da ra'ayinsa ko abinda taga zaya dace da shi,godiya sosai ta yiwa ummeen har taso tafi wadda ni'imah ke mata,bangarenta ta koma ta dora girki,karo na farko,girki tayi musu mai shegen dadi wanda ya janyo wasu ma bangaren nata,ta diba wani da kanta ta kaiwa ummeen,ba qaramin burgeta abincin ya yiwa ummee ba,ba shakka almustapha ya dace,ya samu macen da suka jima suna masa addu'ar ya samu,godiya ta dinga mata har hakan ya bata kunya,har gidan wanda ke musu dinki yazo ya karbi dukkan dinkunansu wanda zai gama musu ne a kwana biyu kacal,abinka da kudi qare magana,shi dama haka dinkinshi yake,manya mutane yakewa dinki saidai fa babu saba alqawari,kaman qaramin kamfani ne,yana da ma'aikata,kowa da abinda yake hadawa,wani hannu,wani gaban riga,wani bayan riga,wani kalmasa haka dai da sauransu


Laila,khalipha,hafiz da minal duka sun shigo,ta rasa yaya zatayi da laila,ta addabeta,duk bayan mintina sai ta tanka ta
"Wai,wallahi ansha da mami da batazo taga yadda 'yarta ta koma ba,don Allah khalipha zaka ce anty summynmi ce wannan" da yake shima uban magana me sai ya biye mata sukayi tayi,dariya ta shata ta gode Allah,batasan sanda lailan zata daina shegen surutu ba haka,antyn dijen ce taqi shigowa,ta dinga kiran layinta tana qorafi amma saidai tayi dariya tace zata shigo,gashi ita babu damar fita tunda bata sanar masa zata fita ba,haka kuma kunya take ba zata iya kiranshi ba,


Ranar laraba mai qunshin dakewa su ummee tazo har gida,daki ne babba aka ware a can bayan gidan anan take zama idan tazo musu qunshin,ummeen da kanta tasa aka kira mata sumayya tace ta shirya za'a yi mata qunshi,qarfe hudu na yamma aka gama mata baki daya ja da baqi,kowa yasan yadda lalle ke yiwa farin mutum kyau walau ja ko baqi,kamar ka cire hannun saboda yadda ya zanu ya zauna sosai kamar dorashi aka yi,ita kanta ummen sai da tace masha Allah,ta dubi sumayyan tana cewa
"Kije kinyi baquwa,umman khalipha sai yau taga damar zuwa" farinciki ya cikata, bata iya tsayawa ta qarasa cire lallen na hannunta sai ta miqe ta nufi sashen nata,da gudu ya qarasa ta rungume anty dijem,sarkin kuka har ta soma tara qwallar
"Au ashe har yanzu baki girma ba sumayya?,inaga tare zaka daina kukan quruciya ke da abdallah da alama" sai ta saki antyn tana dariya,daki suka shige da anty dijen,farinciki fal zuciyarta,kallo daya zaka yiwa sumayyan kasan cewa kwanciyar hankali ya fara samuwa,kasa gayawa antyn komai tayi,sai take jin kunyarta,to ita din ma bata damu sai taji ba,ta dai sake jan hankalinta kawai,sun jima tare kafin antyn fa fidda wasu kayayyakin gyaran jiki ta bata
"Hajiya lami ta kawo min su,suna da tsada amma akwai kyau,wannan wata hadaddiyar dilka ce,kwana biyu kadai zakiyi amfani da ita zaki ga yadda zaki sauya,da kanki zaki nemesu nan gaba" sai wata gumbar aya ta kankana data dabino da madara,sabo dadinta da gardi tuni sumayyan ta kusan cin rabi a haka suna zaune suna hira,riqe antyn tayi sai da akayi sallar magariba sannan ta tafi,kasancewar bangaren nata babu kowa duka suna gidan amare sunje musu kamu.


Sai data yi sallar sannan ta janyo kayan dilkar ta soma hadawa tana fadin bari ta gwada,ta gama rsaf ta shafe jikinta bayan awa daya ta murje ya shiga wanka,ba shakka mai kyau ce haka ta dinga fadi a ranta yadda fatarta ta sake wani santsi bayan na da,su humaida basu shigo ba sai wajen tara da rabi,har ta shirya zata kwanta ma,yau bata jin qwarin jikinta sosai,tun safe tunaninsa ya dinga kawo mata caffa,tunda ya tafi bata ji muryarsa
"Akuyar daure ta samu sake yau mun wataya wallahi wannan miskilin mijin naki bai nan" humaida ta fada tana dariya tare da tsokanar sumayya,murmushi kawai ta saki cikin kara da yakana tace
"Ai kunfi kusa" baki humaira ta rufe
"Rufamu ki saya mu,wacce kusar?,ai shi bashi da kusa,matanshi kadai za'a cewa sunfi kusa,shekara nawa amma har yau kamar bai san mu su waye dinsa ba,ku dai ku dauki mijinku kuje ku qarata"
"A'ah fa,kada kuma a wuce gona da iri" inji sumayya cikin zolaya,dariya suka sanya baki daya,kusan wannan hirar ce ta sake dauke mata hankali.


Cikin dare baccin nata ya katse,ita kadai ta dinga juyi saman gadon,tana kallon yadda su humaida ke baccinsu hankali kwance,wayarta ta janyo tana dubawa,babu wani abu sabo tattare da ita,sai ta samu kanta da lissafin awannin da suka rage gare ya waye musu zuwa ranar alhamis.


Washegari tana wajen ummee amma baki daya hankalinta bai wajen,tana yi tana duba agogo,tun la'asar ta koma sashenta,awanni suka dinga shudewa amma babu labarin dawowarsu,a haka dare ya cimmata,cikin daren ta kasa bacci,ta miqe a hankali daga dakinta ta haura sama zuwa nashi dakin,ta tura qofar ta kunna fitilar wayarta ta haska makunni ta kunna qawayayen dakin,a hankali ta qarasa bakin gadon ta zauna,da kdanu take bin ko ina na dakin da kallo,wanda dazun ta gyarashi fes,komai a killace,wani irin yanayi take ji mai kama da kewa,sai ta qudundune cikin bargo tana sakin ajiyar zuciya,qamshinsa take shaqa har cikin qwaqwalwarta,juyi ta shiga yi daga farkon gadon zuwa qarshensa,haka kawai taji zuciyarta ta karye kuka take so tayi,hawaye ne masu dumi suka fara zirya saman fuskarta,cikin haka taji wayarta na fidda sauti mai dadi,da fari ta tsorata,amma daga bisani ta tattara hankalinta ta janyo wayar,babu suna akan lambar,amma sai taji zuciyarta ta tafi kan ta daga,karata tayi a kunnenta ba tare da tace komai ba
"Baki bacci ba ko?,dama jikina ya bani hakan"tsumammiyar muryarsa ta ratsa dodon kunnenta,bai damu data amsa ba ya dora da tambayoyinsa
" me ya hanaki bacci qarfe daya saura na dare?"zuciyarta ta kuma karyewa da jin muryarshi,hawayenta ya qaru,sam batasan kukan nata ya fara fidda sauti ba sai da taji amon muryarsa ya dan qaru sabanin dazu da take kama da ta maijin bacci yana fadin
"Subhanallah?,me ya sameki?," rasa me zata ce masa tayi,sai 'yar qaramar sheshsheqa da take fitarwa,to me zata ce masa?,tace masa ta kasa bacci?,ko tace masa gidan ba dadi?,duka saboda me?,sabida shi ko saboda wani dalili na daban,idanunsa na lumshe daga can bangaren yana sauraren sheshsheqarta,cikin sanyin murya yace
"Is ok,ya isa,ya isa.....tunda ba zaki gaya min ba ni bari na gaya miki,saboda ke na kasa bacci,saboda baki a kusa da ni,tunaninki da kewarki tunda nazo banji dadin garin nan ba,ta yaya kika yiwa zuciyata ta'addanci har haka ba tare da na farga ba?"shuru tayi kukan ya dauke duf tana saurarensa,ya qware wajen watso kalaman dake taba zuciya,wai da gaske ma ita yake gayawa haka?,kodai yaudararta yake son yi?
"kema haka ne a zuciyarki uhmmm?" Ya ambata cikin salon rada wanda ya sake hautsinata,baki ta turo kaman yana gabanta
"Umm ummm.nifa ba haka bane"
"To meye?" Ya fada dariya na qwace masa wadda baisan ta fito ba,jin shiru bata ce komai ba

Please Login or Register in order to submit comment