Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi tana zama tare da amsar ledar humrorin,budewa tayi tana shanshanawa tare da yaba yadda sukayi bala'in qamshi,godiya tayi mata sosai tamkar ba biyanta tayi ba,miqewa tayi tana shirin tafiya
"Umhmmm,za'a gudun ne?" Amira take baro kitchen ta fada tana dan murmushi,waiwayawa tayi tana dubanta itama fuskarta qunshe da murmimushin,sam batayi zaton zata yi sauqin kai haka ba
"Na baro aiki ne a gida shi ya sa"
"Ayyah to sai yaushe?,ko sai na shigo?"
"Allah ya kawoki lafiya"
"Amin,ni sunana sumayya na gaskiya,sunan mamar babanmu ce ake kirana amira,kefa?" Murmushi ta saki
"Nima suna na kenan?" Idanu amiran ta zaro gami da rufe baki
"Kai kai,dama baabaa na kusa ya ganki,yaga mai sunan mamarshi,yana son mai sunan mamarsa wallahi,me ake ce miki to?"
"Shi ake gayan" kai ta kada sannan tace
"Gaskiya ni bazan fadi haka ba,zan dinga kiranki kema da amira,amiran umman khalipha" dariya sosai sumayya tayi
"Shikenan to" ta amsa mata sannan sukayi sallama ta juya da niyyar fita tana dariya amiran,kusan zasuyi shekaru daya da ita,saidai yanayin inda ta taso da gata sai take ganin kanta kamar qaramar yarinya,duk da aqalla zasuyi shekaru ashirin da daya.

A bakin qofar shigowa falon taji tayi karo da abu har yana bangazar kafadarta,da sauri ta ja baya tana fadin
"Subhanallah"
"Mtsweeeeww" taji an tsaki,baya ta sake ja tare da daga kanta tana kallonta wanda ita dinma kallonta take,saidai nata kallon yasha bamban da wanda sumayyan ke mata,kallon farko ta fahimci macace mai izza da jin kanta,haka yake don sumayya bata yi qarya ba,matashiya ce dake jin duniyarta dai dai,wadda a qalla ta doshi shekara ashirin da takwas a duniya,doguwa ce sosai hakanan siririya ce,fara ce itama sosai kamar yadda sauran suke,sanye take da wani baqin hight rise slim leg jeans da v neck t.shirt mai gajeran hannu,hakan shi ya fiddo surar ta da shape dinta baki daya,kanta yane da wani dan kwali mai santsi don ba za'a kirashi mayafi ba,idanunta saye da sun glases da ya kusa cinye rabin fuskarta,wani kallo take wa sumayyan na sama da qasa cikin izgilanci kafin ta zare gilashin nata,tsaki ta ja kafin ta wuce tana taku dai dai tana duban amira
"Maamaa fa?" Ta tambayi amira kamar bata son yin magana
"Ta haura sama" ta fada tana nufo sumayya dake gab da ficewa daga falon,da sauri ta daga murya
"Kiyi haquri sumayya" amiran ta fada cikin damuwa,sai ta waiwayo tana sake mata murmushi tare da fadin
"Kada ki damu", sai da sumayyan ta fice sannan ta dawo da kallonta cikin falon ta saukesu kan wadda ta shigo din,sai ta kada kai kawai ta shige kitchen ganin ta zauna saman kujera tana jiran saukowar maamaan,ta sani sarai ba zata iya haurawa saman ba dama idan ba da wani qwaqqwaran dalili ba,shi ya sanya tayi saurin komawa kitchen don kada ma tace zata aikata.

Tana hanya tana tuna irin kallon da ta yi mata,a qa'ida ita ta bigeta,ranta yaao baci amma sai ta dorama kanta laifin,ko ba komai ita tazo musu gida,tana isa gidan ta bawa anty dije labarin amiran,
"Amira kam akwai son mutane ai haka take ita da mahmoud ai mutane na ne"
"Eh kam na ganshi shine ma ya rakani wajen anty maamaa,yana da kirki sosai"
"Shine d'a na uku a wajen ummee"
"To ita amiran 'yar waye ne anty,yau tana can gobe tana nan"
"Itama d'iyar ummee din ce"
"Ita ummin bata da yara ne?" Hararta tayi tana cewa
"Yau kin zama 'yar jarida,to ban sani ba,ai baki son jama'a ne,banda haka watanki nawa a gidan nan yaci ace kin gama saninsu,tunda alhamdulillah mutane ne masu kirki karamci da son jama'a" dariya sumayyan tayi tana kame bakinta da yatsunta
"Ni dama amiran nake son na san 'yar ina ce kuma an gayan" sai suka yi dariya anty dije na qorafin qib sakin jiki na sumayyan.

Da daddare dukkansu suna zaune a qasa suna cin abincin dare har da mai gidan,sumayya ce kawai ke zaune can gefe tana cin nata,babu yadda anty dije da uncle farouq baiyi ta dinga cin abinci cikinsu ba amma ta kasa,kunya gareta,bata da sabo sosai idan ba wajen yara qananu ko mutanen gidansu da suka taso tare ba,tun suna qorafi har suka suka haqura suka zuba ido a haka suka saba saboda sun lura halittarta ce ba zata sauya ba.

Sai da suka kammala baki dayansu sannan hafiz yace cikin doki
"Abba,wanne albishir ne da kace sai mun gama cin abinci zaka yi mana?"idanu ya zaro yana murmushi yana duban hafiz din
" ummm,wannan zumudi haka?"
"Eh wallahi abba nima na qagu ya rigani fada ne kawai a baki" juyawa yayi yana kallon lailan,wannan karon dariya ce ta subuce masa
"Au kema?"
"Eh abba" ta fada itama tana dariyar,sai ya dubi anty dije
"Kefa madam?" Murmushi tayi tana gyara zama
"Ai yara sun gama magana,nima na zaqu inji wanne albishir ne?" Dariya ya sake yi
"Uhmmm,shine kenan to tunda bakinku yazo daya" ya fada yana gyara zamanshi,sumayya na gefe tana satar kallonsu,yanayin rayuwarsu tana burgeta,soyayya dake tsakanin uncle farouq da anty dije kullum kamar wasu sabbin aure,waiwayawa yayi ya fito sumayyan da hannu
"Taso kema ya shafeki" sai tayi qasa da kanta sannan ta miqe ta qaraso tana murmushi,gefan laila ta samu ta zauna,duk sukayi shiru suna sauraronsa.

"Alhamdulillah,Alhamdulillah" ya fara cewa
"Wato a yau labari ya iskemu gwamnatin tarayya ta aiko da takarda ma'aikatarmu,ta zabemu mu goma zamu tafi london bayan sallahn nan mai zuwa da sati daya,zamu qaro karatu don samun qwarewa kan aikinmu na tsawon shekara guda" ya fada yana sauke numfashi,duk sai fuskokinsu suka sauya,kowa da abinda ya fara yawo cikin zuciyarsa,suna wassafa yadda zai tafi ya barsu da yadda zasuyi kewarsa,dariyan da ya saki ita ta maido hankalinsu kanshi
"Jibi fuskansu,to gwamnati ta bamu daman tafiya da iyalanmu amma kada su wuce mutum hudu,shine babbar matsalar,gashi mu mun kai mu shida,tunani daya wa za'a bari da wa za'a tafi?" Shuru dakin ya dauka,murna ta soma komawa ciki,kowa na zulumin kada ace shi za'a cire,banda sumayya da farinciki ya mamayeta zata koma kano kenan har tsawon shekara daya,don dama ko a mafarki bata zaci ma zata bar state dinta ba balantana akai ga qasarta,ganin ba wanda yace komai sai sumayyan tayi gyaran murya don fidda abinda ke cikinta,dubanta uncle farouq yayi yace
"Ummm,me zaki ce?" A ladabce tace
"Dama uncle.....cewa nayi.....ni mai zai hana a cireni a lissafi sai na koma kano kafin dawowar taku?"
"Shawara bata karbu ba" anty dije ta fada kanta tsaye,sai ya saki dariya yana kallon sumayya
"To kinji abinda antynki tace" yana maganar tare da mai da hankalinsa kan anty dije
"To ke hajjaju mai zai hana cikin taskarki din nan da ake boyo ki dauki nauyinmu baki daya?" Ya fada cikin zolaya wanda hakan ya sanyasu dariya baki dayansu,sai da suka nutsa sannan yace
"Ni a binda nake gani,hafiz,kai zakayi haquri saboda karatunka a yanzu yake buqatar nutsuwa da dagewa,kai zamu bari a nan garin,sumayya kuma kema 'yar mu ce,kinga kuwa mai 'ya mace bazai dinga barinta wani gu ba,ni zan yi mata passport da visa a kudina,shikenan madam?"murmushi ta saki
" yayi yallabai,mun gode Allah ya saka da alkhairi ya qara arziqi"hafiz wanda sam baiji dadi ba har cikin ranshi,amma da yake yarone mai hankali da haquri,da wuya ka gane bacin ranshi sai yace
"A wanne gida abba Zan zauna?"
"Duk inda ka zaba,ko gidan inna(kakarsu da yake nan ya dawo da ita,ba wata tazara bace mai nisa tsakaninsu),ko gidan baabaa prof,kayi haquri kaji hafiz,girman kenan kaji?"
"Ba komai abba" ya fada,sai ya baiwa antu dije tausayi
"Ni har ka tunan ma abban laila,ina zuci zuci sukai sumayya ta gaidata,innan tace wai ba zata iya gane sumayyan yanzu ba"
Yana miqewa yace
"Kinsan tsufa sai a hankali,ai babu damuwa ko zuwa gobe ko jibi sai suje"
"Allah ya kaimu" injita,miqewa hafiz din yayi yabi bayan abban nasa da ya kirashi yace yazo ya karbi wani abu,take falon ya sarqe da murna,laila anata wassafa kai a jirgi,sumayya na dubanta tana dan murmushi duk da hankalinta ya kasu kashi biyu,ran qwashi anty dije ta zuba mata tace kota nutsu ko ta saka a cire sunanta a saka na hafiz take ta kame bakinta duk da bata fasa mutsu mutsun murna ba.



*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

5⃣8⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*KO KUNSAN ACIKIN 'YAN WUTA WAYE MAI QANQANUWAR AZABA MAFI SAUQI?,WANDA AKA FI SAUQAQAWA??*

*Shine wanda za'a sanya garwashin wuta a tafin qafafunsa guda biyu,kowanne tafi daya garwashi daya,sai qwaqwalwarsa ta dinga tafasa*

*ALLAHUMMA AJIRNA MINANNAR*

__________________________________


      Falon anty dije ta basu tana fita laila ta dora daga inda ta tsaya,har gwada irin shigar da zata dinga yi take idan suka tafi,sumayya na gefe tana kallonta tana dariya,can qasan ranta kuwa tana ta jujjuya maganar,wai itace zata wata qasa wata uwa duniya a jirgi har london?.

       Suna haka hafiz ya fito daga wajen uncle farouq,fuskarsa qunshe da murmushi hannunsa dauke da laptop sabuwar qar,idanun laila suka fara kaiwa kai
"Laaah,ya hafiz sabuwar laptop abba yayi ne?"
"Wannan ba ta abba bace,tawa ce wanda ba za'a london da shi ba" ya fada yana zama tare da budeta ya kunna,tuni laila aka fara raba ido,ta matso kusa da shi
"Da gaske kake ya hafiz" hararta yayi
"Da da wasa nake miki" shiru tayi sannan daga bisani tace
"Allah ko nima na fasa zuwan ne a siya min,kada muje mu dawo dadi ya qare kai kuma ga abarka nan kama mora?" Dariya ta qwacewa sumayya,tana niyyar cewa wani abu anty dije itama ta fito daga dakin hannunta dauke da wata laptop dim,gefansu sumayyan ta zauna tana kallon hafiz
"Tofa,an samu nayi ko?" Murmushi yayi kawai yana danne dannensa dadi ya cikashi,sumayya ta miqawa laptop din tana cewa
"Ungo wannan" amsa tayi tana duban antyn
"Daki zan kai miki?"
"A'ah taki ce,abba laila ya siya miki yace zai miki bayani,akwai abinda ya shirya miki kan bunqasar karatunki yana so kiyi karatu ne da ita,idan mun tafi ina tsammanin akwai makaranta da zai sama miki da zaki koyi karatu ma shekara gudan,nasan baki da matsala ta karatu da rubutu duka kin iya,hakanan turancinki ba laifi zaki iya karantawa ki fahimci wasu abubuwan,fahimtar sosai da maidawa yadda ya kamata ne kawai matsalarki" qamewa tai a gun tana mamaki,to ita ya zata iya da wannan aba da uncle din ya mallaka mata,kasa magana tayi har sai da laila ta saki dan ihu tana karbarta daga hannunta
"Wayyo!,muma munyi computer,ya hafiz ka daina mana kallon banza" cikin sanyin murya da sake gasgata qaunarta da anty dije tace
"Anty na rasa wacce iriyan godiya zan muku,na gode na gode Allah ya saka muku da alkhairi,ya biya muku dukkan buqata ya jiqan magabatanku,ya hada kan zuriyyarku baki daya"
"Amin" anty dijen ta amsa tana shigewa ciki.

        Da sauri laila ta miqe ta jona mata chargy hadu da kunnata,tana da rawar kai hakan ya sanya ta iya laptop din kamar wadda ako koyawa,don suna game sosai a cikin ta muhsina daya daga cikin qawayenta jikokin gidan baabaa prof,nan ta fara duba games din ta ta tarar a ciki,ta zabi daya ta fara bugawa minal ta matso tana kallo.

        Daga bakin qofa akayi sallama,dukkansu hankalinsu na kan laptop din sai sumayua wadda ta amsa yana waiwayowa,amira ce ke shigowa fuskarta qunshe da murmushi,sanye take da black gown brided tube midi mai adon zane orange a jiki mai dogon hannu,kanta yane da mayafi medium orange haka plate shoes dinta,hannunta riqe da wayarta,fuskarta ba makeup saidai akwai alamun hoda da lipstic,bayanta wata matashiya ce,sanye da baqin skert da t.shirt ruwan omo dukkansu na yadi,sai dan madaidaicin hijab dake wuyanta,kallon farko zaka gane 'yar aiki ce,eh tana daya daga cikin ma'aikatan gidan baabaa prof,qarasowa tayi cikin falon wanda hakan ya ankarar da su laila
"Anty amira ina wuni" suka gaisheta baki dayansu ta amsa tana zama gefan sumayya
"Kin ganni da daddare ko?" Murmushi kawai tayi tana janyo lemo da ruwa nata wanda tun dazun bata sha ba da suka gama cin abinci ta ajjiye gaban amiran tana cewa
"Bismillah"
"Um_um,a qoshe nake,shopping naje nayo sai nace bari na shigo,ina so dama na baki haquri ne kan abunda ya faru dazu" kusan ta mance ma ma ya farun
"Mefa?" Sumayyan ta tambayeta
"Bigeki da antynmu tayi dazu,kiyi haquri don Allah,antynmu ce saidai bata da kirki sam,kiyi haquri" murmushi ta kuma yi har fararen haqoranta na bayyana
"Babu komai,ai karo mukayi"kai amira ta girgiza
" duk da haka,nasan halinta ai,kiyi haquri"
"Bafa komai" ta sake maimaitawa,maida dubanta tayi ga wadda suka shigo din tare,tana tsaye har yanzu
"Ki zauna mana" sumayya tace mata,murmushi tayi tace
"No madam,na gode". Kan ta sake cewa komai wayarsu ta tafi da gidanka dake  kitchen ta fara burari,laila ta subi khalipha
" jeka duba khalipha"kanta na ga laptop don bata son a mata game over,da sauri ya miqe ya shige kitchen din minti daya tsakani ya fito
"Anty sumayya ke ake nema" yana fada alqasim ya fado mata,fuska ta tsuke
"Kace bana nan"
"Yace don annabi ki daure ki daga" khaliphan dake tsaye bakin qofar kitchen din ya fada,goshinta ta dafe da tafin hannunta,bata so a hadata da ma'aiki taqi yin abu,amira ta miqe tana dubanta
"Kije ki amsa mana namecy,zan tafi sai da safe ki gaida umman khalipha" ta fadi tana murmushi
"Sai da safe ki gaida gida" sumayyan ta fadi itama tana miqewa,ita tayi kitchen su suka fice ita da mai aikinta.

      Murya a sanyaye ya mata sallama,a dake ta amsa
"Bakisan halin da zuciyata ta fada sanadinki ba sumayya,please don Allah ki daure ki dinga daga wayata ko ba zaki ce min komai ba"shiru ta danyi ta rasa me zata ce da shi,zuwa yanzu yaci ace yayi zuciya ya bar nemanta
"me kake so nace mai kake buqata?"
"Yauwa beauty,a qalla ko gaisuwa ma ta wadatar" kusan wannan ne abinda abdur rahman ya gaya mata,gashi yana neman jefata cikin tarkon sabo da jin muryarsa,wannan wanne irin wayo ne,ba zata yarda ba kam
"Sai anjima" tace masa tana kife kan wayar ta fito daga kitchen din tana sauke numfashi,inda ta tashi nan ta koma ya zauna ta janyo wayarta tana laluban lambar mamanta tana son jin muryar abdallah.

******    ********    ********

       Ramadan ya rage saura kwanaki uku,nan sumayya taga tsari,yadda anty dije ke tsara gidan nata tare da sauya abubuwa sabida shigar watan,baki ta sake tana mamaki don su duk basu irin wannan,dariya anty dije tayi
"Da kike mamakin nawa gyaran kice idan kika ga na gidan baaba prof saikin yada idonki?"ido ta qwalalo
"duk kyau da tsaruwar wannan gidan sai an sake masa wani tsarin?"
"Duk shekara iwar haka sai dukka gidan sun sake komai nasu,sai su rabar da tsofaffin ga 'yan aikinsu,wasunsu har kayan sawa da yayi shekarar nan ake canza wardrobe baki dayanta" baki sumayya ta sake tana duban anty dije kamar ita ce ke sanya su
"Gaskiya mutanen nan mabarnata ne,yanzu wannan gidan ba ya isheka har qarshen rayuwarka ba,wani ma idan yana wani gu baisan da wani ba,har meye ne zai tsufa a shekara a sauya shi?"dariya sosai anty dije tayi
" lallai har yau bakisan wannan familyn ba,kowa da irin matsayinsa fa,ita rayuwa kowa da inda Allah ya ajiyeahi,idan kaga rayuwar wasu kai a gunka barna ce da almubazzaranci,ko kaga tsabar warya ce ko bazata yiwu ba,amma kaima da Allah zai kaika irin wannan matsayin babu shakka sai kayi kamar ko fiye da abinda yakeyi,yanzu kamar ni din nan,da wasu zasu ga abinda nake cewa zasuyi nima almubazzaranci bane,amma ba haka bane,idan Allah ya wadataka kana da shi ka sauya to ka bawa na qasa da kai wancan su amfana suma,ba ka qanqame ba ka qanqame jama'a ba,amma.....zauna na gaya miki su waye wadan nan family din kinji"ba musu sumayyan ta zauna tana baza kunne,itama anty dijen zama tayi,kafin tace komai laila ta shigo tana sanar mata tayi baquwa tilas suka katse hirar ta fita wajensu,sumayya ta tashi ta kama mata aikin da ta tafi ta bari.

  *********  ******  ********

      Baki daya a yanzu rayuwar gidan bata yiwa karima dadi,bata da buri a yanzu da ya wuce taga yaranta da mijinta kusa da ita amma abu ya gagara,kowa tsoro da haushin zama kusa da ita yake,hatta da lukman din ma kwanciyar bacci kadai ke kawoshi bangaren,ya sauya mata irin sauyin da bata taba zata ba,bai shiga shirginta indai ba haqqinta na aure zai sauke mata ba,wanda shima yasan idan ya take mata sai Allah ya tuhumeshi,a nan takan so jan ra'ayinsa amma abu yaci tura,da ya gama yake wanka idan an kusa asuba ya zauna karatun qur'ani da addu'o'i har sai an kirayi asuba ya fita yayi sallah,idan ya dawo ya zarce wajen hajiya su hafu da yara suyi karatu sannan su shirya ya miqa su makaranta,idan ya dawo shine zai shigo mata yayi wanka ya fice ko sauraron abincinta baiyi gun hajiya shima yake ci,hakan shi ya sake taka muhimmiyar rawa wajen rugujewar duk wani aiki da zata masa,walau na abinci ko na jinnu,ya tsayawa addu'a abincinta kuwa baici bare ya dameshi,bata gane bata da wayo ba sai sanda taso ta gwada yi masa tawaye kan yadda yake maganar sumayya da daukar yaranta ya kaiwa mama su,ranar taga tijarar da tunda Allah ya hadata da shi bai taba yi mata ba,tayi kuka na fitar rai,a hankali kuma sai ta soma tunanin me yafi zaman lafiya dadi?,me zaisa ba zata haqura da komai ba ta kawo qarshen wannan zaman fagen yaqin da sukeyi,abinda bata sani ba tanqwara busashen itace abune mai wahala,ta riga da ra yiwa kanta mummunar lamba wajensa.

      Duk sanda yaje yakanyi yunqurin karbar adreas din sumayya wajen zainab ko halima,saidai duk sanda yaso yin hakan sai ya taras basa nan suna tahfiz,ita kuwa mama ba wani riqe adress din tayi ba,yaciji yatsa yaji ciwon abun da tun lokacin aurensu da tace zata gidan anty dijen lokacin da shima zaije abujan bai bita ba yaga gidan,da tuni yanzu bakinsa alekum sai ya kama hanya,wayarta kuwa idan ya kira sau biyar idan yaci sa'a zata daga sau daya su gaisa ta tambayi yara,daga haka zata katse kiran sai kuma wani lokacin.

******   ********   ********

       Ranar lahadi da daddare watan azumi ya bayyana,hakan ya sanya litinin daukacin al'umar musulmin duniya suka tashi da azumi a bakinsu,duk gidan kowa na azumi banda minal saboda shekarunta basu qarasa ba,ta fara gwadawa zuwa sha biyu anty dije ta bata abinci,kafin azahar su laila anyi laqwas saman kujera,khalipha an fara mutstsuka idanuwa,dariya sosai sumayya ta dinga sheqa musu yayin da anty dije tayi kicin kicin da fuska don kada ma wani yaga fuskar da zaice zai karya,hafiz ne kadai da qwarinsa da yake shine babba.

       Biyu da rabi bayan sumayya ta kammala sallar azahar tana tilawar qur'ani anty dije ta taddata da hijabi jikinta itama da alama bata jima da gama sallarta ba,gefe ta zauna hakan ya nunawa sumayya magana tazo yi da ita saboda haka tana kaiwa qarshen shafin ta rufe tayi addu'a ta shafa ta waiwayo ga anty dijen
"Ya ibada,ke kam azumi nasaj gwaninki ne,tunda kina na litinin da alhamis dama" murmushi tayi
"Wallahi kam anty"
"Allah ya kawo min sauqi wannan karon shi yasa nace bari nazo na sameki,kinsan duk watan azumi nike wa baabaa prof abinci har a kammala azumin,abban laila ne yasa a dinga yi saboda karamcin dattijon,yana son abinciccikan gargajiya duk da kasancewarsa dan boko,to su mutan gidan sun fishi boko,da azumi basa wani abincin azo a gani sai abinciccikan zamani,ummee ce ke masa lokaci lokaci don itama tana so,to wannan karon ummee sun tafi umra mazan ne kawai suka rage a gidan,duk da kowa na da mai aikinsa amma shima baabaan baison girkin ma'aikata shi danshi ya gado" ta fada tana dariya data tuno shi
"nasa gwanar girkin gargajiya ce ke,ni ki barni da girkin gida ki dinga na baabaa" murmushi tayi
"To ai zan iya ma anty duka,haba,sai kace ba mace ba"
"Nasan zaki iya,ai ranon mama ce,amma kya dai tayani na gidan"
"Tom anty" miqewa anty dijen tayi
"Naga yau garin kam masha Allah akwai hadari,ko yau zamu samu ruwan farko a ranar farko?"
"Allah yasa anty,dama tun muna kano naga irin garuruwan nan kunfi ko ina samun ruwa,ga damunarku itace qarshe wajen tafiya"
"Wallahi masha Allah,muna shan ruwa kam,saidai zafi"
"A hakan anty,duk wannan ac da kuke kwankwada"
"Saikin fita ai sumayya zakiji a jikinki"
"Saidai haka" ta miqe itama tana nannade abun sallahr ta don shiga kitchen saboda su kammala komai kan lokaci.

      Ana la'asar kuwa ruwan farko ya soma sauka zuwa qasa,tana kitchen din a lokacin,sai ta zuge glass tana kallon yadda ruwan ke juqa shukoki yana tayar da qamshin qasa,a rayuwarta tana son damina,murmushi ya subuce mata data tuna sanda suna tare da mukhtar,duk sanda baya gida takan fito ita da yaranta dake tayata zama susha wankansu a ruwan sama,kafin ya dawo ta share gidan ya sauya kayanta kamar bata shiga ruwa ba,amma kallon farko idan ya mata yake gane ta shiga ruwa,musamman gashinta dake saurin fallasata saboda cikarsa da tsahonsa bai bushewa da wuri,abinka da quruciya a lokacin yaron da bai saba qarya ba idan yayi ma sai an ganeshi,sai ta fitittike tace masa wankan tsarki tayi
"Wanne wankan tsarkin,me ya sameki bayan fitata da zakiyi wankan tsarki?" Narai narai take da ido tace itadai wankan tsarki tayi a tunaninta shi kadai ne mafitar da zai yadda ba wasan ruwa tayi ba tunda wankan tsarki ne kadai ake jiqa kai idan za'ayi,idan yaga ta dage sai kawai ya qyalqyale da dariya ita kuwa ta sake hade rai don kada ya gano,tilas yake sakin murmushi yace ya yadda,tana kawowa nan a tunaninta ta saki itama murmushin qwalla na bin kuncinta
"Allah ya gafarta maka ya mukhtar,ya kyauta makwancinka" tayi furucin tana goge hawayen da tafin hannunta,baki daya sai walwalarta ta tafi kamar yadda hakan ke faruwa yawancin lokuta idan ta tunashi,girkin take amma zuciyarta babu dadi,duk da haka hakan bai hanata hanzari ha,kafin kace me wannan ta gama girkin baabaa prof,dashishi ta masa da miyar ganye,wanda kallonta kadai ya isa ya tsinkar maka da yawu,tun ba yau ba tun tana qaramarta haka hannunta yake da iya sanwa,ballantana a shekaru takwas zuwa tara da tayi gidan aure ya sake maida ta gwana fagen iya girki.

      Ko da anty dije tazo tayi mamakin saurin girkinta,don tuni suma ta musu miya,miyar qwaice da alayyahu tayi shar tayi kyau sosao,gun any dijen ta koya amma sai take ganin kamar ta fita ma iyawa,kasancewar sumayya bai bala'in qwaqwalwa da saurin dauke abu,cewa tayi ta bar mata sauran ta qarasa tunda tayi kusan rabin aikin gidan bayan na baabaan.

      Daki ta shiga tayi wanka,saura kusan awa guda kafin a sha ruwa,ta fito ta shirya kanta cikin atamfa riga da zani,kanta ta daure da dan kwali ta dauki carbinta ta fito falo,dariya ta zo mata ganin yadda laila ta sake bajewa saman kujera,khalipha kuwa tuni bacci yayi awan gaba da shi,bata ce musu komai ba ta sauya tasha zuwa sunna t.v wanda suka sako tafsirij shehun malaminta sheik Ali ibrahim isah fantami,sosai take jin dadin tafsir din har zuwa wani lokaci data koma kitchen din ta tadda anty dije ta kammala komai,ita ta dinga kwaso kayan tana shiryawa saman dining anty dije kuma ta shiga wanka ganin saura mintuna akira sallah.

     Lokaci qalilan gidan ya kacame,kowa na kaiwa baki,daga nan uncle farouq ya kada kansu zuwa masallaci sukayi sallar magariba.

     Babu kowa gidan duka sun fita sallar asham tarawih,ta sanya hijabinta zata tada tata kenan cikin gidan anty dije ta shigo itama sanye da hijabi
"Sumayya,yanzu abban laila ya kirani,yace ki miqa abincin baabaa prof,ga driver nan yana waje zai amshi nashi abinci sai ya riqe miki wasu kwanukan" babu musu yau kam sai faduwar gaba jin an ambacin gidan tace to,dirvan nasu shi ya dauki kwandon ita kuma ta dauki flask daya da ya rage.

     Tana gaba yana binta a baya har suka isa bakin qofar,a mutunce suka gaisa da baba harunaya bude mata qaramar qofar suka shiga,harabar gidan tarwai take da haske da fararen qwai,ko ina a haskake tamkar rana,ma'aikatan gidan sanye da unifoarm nata kaikawo kowa na aikinsa,grass carfet da shukokin dake jere a tsare sun samu ruwan sama sunyi kyau gwanin

Please Login or Register in order to submit comment