Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

RAYUWA*
A kullum ta kebe kanta ita daya tunani take yi yaya
rayuwa zata kaya mata?,meyw kuma kundin qaddararta na
gaba?,wanne shafi kundin zai bude mata kuma?,amma a
zahiri ta saki jikinta ko don yadda 'yan uwa da iyayenta suka
damu da ita,burin kowannansu ya faranta mata ya sanyata
dariya,kowa tausayinta yake,tana ganin bai kyautu ba taci
gaba da zama cikin damuwa har ta sanya wasu,mukhtar dai
ya riga ya tafi ba kuma zai taba dawowa ba har abada duk
kuwa yadda take qaunarsa,qauna daya ce tsakaninsu kada ta
manta da yi masa addu'a,hakan yasa ta rungumi rayuwarta
ta kuma rungumi danta,a lokacin cikin kudinta na tumunin
takaba ya abbakar ya ware mata wani abu yace ta fara
sana'a,dama can sumayya ta iya sana'arta,saboda haka babu
bata lokaci ta shiga kasuwar kurmi ta saro kayan humta
turaren wuta na daki kaya dana tsugunno sai kwalakca ta
koma tsohuwar sana'arta,mutum ce ita mai nasibin
sana'a,duk abinda ta sanya kanta ta fara saidawa sai Allah ya
kama mata,cikin ikon Allah kuwa sai wannan karon abun
nata ya sake bunqasa,cikin abokan ya abbakar akwai mutum
uku da iyayen gidansh ke da supermarket,suka buqaci ta
kawo su gwada cikin shagon,ta samu kwalabe masu kyau da
tsari ta zuba,ba'ayi sati ba suka qare suka kawo mata
kudinta suja sake nemam wasu,cikin lokaci qanqani abun ya
habaka,sai ta sanya halima da zainab ciki sukeyi tare,tunda
ta aikama anty dije itama take karba ta amfanin gida,wani
lokaci ta saida ko tayi kyauta.
Sana'ar da take yi ta dauke hankalinta sosai,ta rage mata
zaman tunani da kuka,saidai duk da haka babu wani abu da
ya ragu na tunanin mukhtar cikin ranta,hakanan duk dare
kafin bacci ya dauketa sai tayi kuka mai isarta.
****** ***** ********
*_Bayan shekara daya_*
Koda kwana daya ne ya ratsa cikin rayuwar bawa ta iya
yiwuwa kaga sauyi tattare da rayuwar nan tasa,walau a sarari
ko a boye,hakan ce ta kasance ga rayuwar gidan su
sumayya,wanda a wannan shekara guda din an sauya fasalin
gidansu san sake musu gini mai kyau da tsari cikin ribar
kudin abdallah sumayya tasa aka yi wannan aiki,sun sake
samun rufin asiri sosai,babu abinda ta nema a rayuwarta ta
rasa,ci da sha da sutura baki daya,don har taimako takanyi
cikin ribar sana'arta wanda bai gaza dubu hudu zuwa qasa
ba,an kawo kudin auren zainab wanda ba'a sanya rana ba
ana jira zuwa wani lokaci kafin na halima ya gama shiryawa
kamar yadda yace a bashi lokaci.
***** ********** ******
Sanye take da dogon hijabi mai hannu wanda har jan
qasa yake,qafarta na sanye da safa sai niqabi daure a
fuskarta,wannan itace shigar data koma yi tun randa ta taba
fita wani ya biyota ta yiwa kanta alqawarin canza shiga,duk
da dama can ma'abociyar sanya hijabi ce,daga ranar ta bada
kudi aka dinka mata su kaloli masu kyau har kala biyar,ko
ina zata su take sanyawa duk tsadar suturar dake jikinta,ko
yaushe kar suke a goge cikin tsafta da qamshi,shigar na
matuqar yi mata kyau qara mata kwarjini da kuma boye
kyawun sufarta baki daya,dawowarsu kenan daga gidan anty
salma ita da halima ta kai mata humra da turaren wutar da
ta yiwa wata amarya da za'a yiwa aure 'yar maqotanta,daga
nan ta tsaya aka musu lalle ita da haliman bayan ta shiga
kasuwa ta sayi kayan humra,saboda anty dije tace sati na
sama tana nan zuwa kano,har tana tsokanarta da ita zata
koma abuja don ta fuskanci bata qaunar zuwa abujan ko
kadan,dariya sumayyan ta dinga yi tana tsokanar anty dijen
itama da cewa zaman garinku sai wanda ya saba,haka kawai
kaje a qunsheka cikin gidan ba motsin yara bana maqota
saidai idan kai ka shiga.
Sam bata damu da sabuwar motar da ta gani ajjiye
qofar gidansu ba suka wuce zuwa cikin gidan ita da halima
suna 'yan hurarrakinsu,tun daga soron gidan su qamshin
turare ke dukar hancinsu ba kuma irin turaren humrarta ba da
ya kama gidan,daga bakin qofar falonsu ta hangi takalma
sau ciki na maza bata kawo komai a ranta ba tadage niqaf
dinta tayi sallama cikin falon.
Abdur rahman ne zaune cikin daya daga cikin kujerun
falon sanye da shadda ruwan madara wadda ta haska
fatarsa,kansa hula ce zanna,hankalinsa na kan mama suna
taba hira da alama labari yake bata,sallamar su ce ta maido
hankalinsa bakim qofar,baki ya saki yana kallonta cikin
mamaki kamar yadda ta saki baki itama tana kallonsa cike
sa mamakin yaushe ya diro nijeria
"Kai kam baka da aiki sai zuwan bazata?"
"Kawai kice yaushe a gari inji maqi baqo" ya fada yana
murmushi,sai data samu gu ta zauna sannan ta dubi mama
"Wai don Allah mama yaushe yazo?"
"Fitarku ba dadewa" sai tayi murmushi tana gaida
shi,amsawa yake shima cikin sakin fusakar suka fara dan
tsokanar juna yadda suka saba,halima ce ta shigo wadda sai
da ta tsaya ta daura alwala,a ladabce ta gaidashi ya amsa
yana dubanta
"Wai shekara daya tal naga duk kum qara girma,halima ke
kam ashe ke kika debo kamar sumayya"dariya tayi ta shige
daki don tada sallah,mama ta miqe jin zainab na kiranta tazo
taga ruwan miyar tuwon daren data tsayar ya isa.
Maida dubansa yayi ga sumayya
"sumayya ya kuma bayan saduwa,bayan tafiyata lamura
masu yawa sun wakana,Allah ya jiqan yaya mukhtar,ya
gafarta masa ya masa kyakkyawan masauki a aljanna yasa
ya huta"
"Amin ya Allah" ta fada wani miki na neman motsuwa a
zuciyarta,zuciyar na son karyewa hawaye na neman
zuba,shuru ya ratsa dakin yana nazarinta,ya fuskanci ya taba
mata mikin dake zuciyarta
"Tunda nazo nake tambaya ina mutumina ashe yana gidan
gwaggwo yahanasu,da yake ban leqa gidan ba,jiya na shigo
qasar" sai ta murmusa tana cewa
"Ayyah,ai da ya samu hutu sai tazo ta daukeshi da kanta"
idanu ya zaro
"Kice abdallah an fara makaranta,lallai an girma"murmushi ta
kuma tana bashi amsa sanda mama ke dawowa cikin falon
"eh,ai yana cika shekara ya abbakar ya sanyashi"
"Wacce makaranta ce?"
"New egypt international" kai ya kada
"Masha Allah" hirar sai ta koma gun mama sai ta miqe itama
tayi sallar la'asar,bashi ya bar gidan ba sai da yayi magariba
suka gaisa da malam sannan ya ajjiye musu tsaraba dangin
alawoyi da jallabiya ta maza data mata tasu sumayya zainab
da halima,sai tarin qananan kaya na abdallahnsa.
Mrs muhammad ce✍
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

5⃣3⃣


*Bismillahir rahmanir rahim*

*innash shaidana lakum aduwwun fattakizuhu aduwa*

*HAQIQA SHAIDAN ABOKIN GAABARKU NE,KU RIQE SHI ABOKIN GAABA*
___________________________


*Afuwan nayi mistake na number,yau ne zamu tashi page na 53*

___________________________________

        Yanayin sanyi ya fara ja baya,yayin da zafi ya fara sako kai,wannan shike nuna alamu na tahowar damuna,mafi yawanci lokutan zafi bata iya bacci mai yawa,hakan shi yake sanya ta tashin wuri,qarfe goma tuni ta kammala ayyukan gidab,bata ma jirayi tashin zainab ko halima ba,wanka tayi ta sanya kaya sa'annan ta debi kayan kari daga kitchen ta shiga falon mama,a zaune ta sameta itama tana gyara mafitai tunda lokacin amfaninda su ya zo,kasancewar ba ko da yaushe ake samun wuta ba,nan ta zauna tana karyawa suna hira da mama,bayan ta kammala ta dauko kayan hadin humrarta tana fadin
"Mama bari kiga na fara hadawa anty dije tata,saura kwana biyar tazo kada lokaci ya quren"
"Ai kam don idan tazo baki matan ba ke da ita,ya taku kada ku sakani ciki" dariya sumayyan ta danyi tana bude robar ruwan turare
"Ai ba'a shiga fadan uwa da d'a mama,Allah mama tun ina mamakin irin qaunar da anty dije kemin har naxo na daina" murmushi mama tayi
"Ko sanda muna gida tamu tafi zuwa daya ai,dana haifi abubakar lokacin bata yi aure ba cewa tayi da sai ta karbeshi,sanda na haifeki kuma basa garin nan ita da farouqu da tuni gunta zaki tashi,kinga kuma kina da shekara sha uku aka aurar da ke" kai take jinjinawa tana hadin humrar tare da jin dadin labarin da mama ke bata.

      Halima wadda bata jima da tashi a bacci ba ta shigo dauke da wayar dake burari sumayya wadda gunta wayar ta kwana tana miqa mata
"Yaya ana kiranki" kanta ta daga ta dubeta
"Waye?"
"Baquwar lambace" ta daga mata kiran sannan ta miqa mata,karawa tayi a kunnenta tana mai sallama daga daya bangaren aka amsa mata sannan ta buqaci sanin waye,ajiyar zuciya ya saki yana lumshe idanuwansa
"Amma kam banji dadi ba da har cikin sauri haka kika manta da ni sumayyah" gabanta ne ya fadi,idan ba gixo kunnenta ke mata ba muryar lukman ce,dakewa tayi cikin qarfin hali tace
"Ba abun mamaki bane don na mance muryar wanda ban sani ba" dariya ya dan saki sannan yace
"Lukman ne sumayya,lukman tsohon mijinki wanda kuma yake fatan sake zamantowa mijinki a karo na biyu" jikinta ne ya dauki bari,sai kawai ta katse wayar tana duban halima da ta zuba mata ido tana kallonta,mamanta shiga uwar daki maida mafitan
"Halima lukman ne wai" ta fadi muryarta na rawa
"Mene?,me ya gaya miki?"
"Ba komai"
"Shine kuma duk kika bi kika rude yaya,har yau kamar mune yayun kece qanwar wlh,kinga,ki tsaya kiji me zai fadi bawai ki katse waya ba"
"Cewa yayi tsohon mijina mai kuma fatan sake zama mijina"
"Dole aka ce haka ce zata tabbata?" Ta tambayeta tana kallonta,shiru tayi bata amsa mata ba,ganin bata da alamar ansawa ya sanyata juyawa zata fice,sai sumayyan ta niqa mata wayar tace ta tafi da ita.

       Gabanta ne ya dinga faduwa,sai aikin nata ya koma sukuku sabanin dazu da take yinsa cikin karsashi,har mama ta ankara saidai bata tambayeta ba,tana zaton ko mukhtar ta tuna,da yake yawancin lokuta haka na faruwa da ita idan ta tuna shi,tana shirin miqewa ta adana kayan haliman ta sake shigowa riqe da wayar,idanuwa ta tsareta da shi
"Ya aka yi?"
"Ba lukman bane wannan karon ya abdur rahman ne" tsaki ta ja tana ci gaba da ayyukanta,ta gama lura da take takensa
"Duk kanwar ja ce,dauki kice bana kusa"
"To" haliman ta fada tana daga wayar gami da ficewa daga dakin.

      Sai bayan kusa awa daya sannan ta dawo dakin tana dariya ta dubi sumayy
"Wlh yaya kin ban kunya,kinga ya abdur rahman ya gane fa,cewa yayi har da ni a yi masa qarya ko,yace zaya zo anjima zamu hadu" shiru tayi ba tare da ta ce komai ba,bata fata ko buri abdur rahman ya dora daga inda ya tsaya wajen yada manufarsa,domin a yanzu bama abdur rahman ba,bata buri kowanne namiji ya sota,don kwata kwata bata ji a rayuwarta zata iya sake yin aure,idan tayi tana jin kamar taci amanar mukhtar ne,gwara taci gaba da rayuwarta a haka har itama tata tazo ta tadda ita ta hadu da mukhtar dinta a jannatul firdausi.

      Idanu ta dinga zubawa tana addu'a kada yazo,addu'arta kuwa taci don baizo ba din har suka kwanta,saidai washegari da yammaci ta gama wanka kenan tana shafa mai taji muryarsa a tsakar gida,yau duka a kasalance ta wuni cikin mutuwar jiki,saboda yadda lukman ya matsanta mata da kira da turo saqonnin ban haquri yafiya da kuma yunqurin dawowa gareta,baki daya ya birkita mata kwanya,baisan yadda ta tsani batun aure ba yanzun,sam ya fice mata a kai,ta yaya zatayi marmarin abunda tasha wuya cikinsa,baki daya tarihin rayuwarta wahalar aure ce wadda ta cimmata ta jigata ta cikin qananun shekaru.

      Ta kammala sanya kayanta tana shirin tada sallah wadda zata yita ne a makare don lokacin ya fita zainab ta shigo wadda ta gama shiryawa zasu yinin biki ita da mama
"Ya sumayya kizo inji yaya abdur rahman"
"Ina zuwa" tace tana yunqurin tada sallah
"To mu mun tafi inji mama,tace ki kula da yadfa halima zata sa sanwa kada tayi yawa tunda yau banda malam" kai ta gyada mata don ta riga ta tayar din.

       Falo zuwa tsakar gida ta duba duka baya nan,hakan ya sanya ta leqa soronsu a bakin sitting room ta hangi takalmansa,sai ta sanya silifas ta fita zuwa can,da sallama ta shiga ya daga kamsa daga wayar da yake daddannawa ya dubeta,gefe can ta samu ta gaidashi ya amsa idanuwansa na kanta,kallon ya fara mata yawa saboda haka ta kau da kai tana shirin magana sai kuma ya rigata
"Nima sai an ja min aji sannan za'a fito?" Idanu ta watsa masa wadanda suka sanyashi lumshe nashi idon,sau tayi murmushi ba tare da ta dubeshi ba tace
"Wanne irin jan aji kamar saurayin da yazo zance gurin budurwarsa"
"Ai hakanne,saurayin ne yazi zance gun budurwarsa ko kin manta?" Sai ta sake dubansa,Maganar ta taba ta duk da ta tsammaci haka,shima ita yake kallo,cikin son maida maganar wasa tace
"Ah ko?,to ai kayi kuskure,ka manta ni din ba budurwa bace,saboda haka saidai bazawari yazo guna ba saurayi ba,saurayi sai budurwa ai"
"A haka na gani nake kuma matuqar so" shi kuma ya fada ba tare da alamun wasa ba,ganin yanason maida zancen gaske sabanin yadda take son maidawa saita waske da cewa
"Yau kuma tsurfa ce ta tashi daga toge a sitting room maimakon ka shiga ciki yadda ka saba?"
"Neman aure nazo,kinga bai kamata naci gaba da shiga cikin falom surukai ina zama ba" sai ta danyi dariya duk ason bagarar da zancan
"Ah wai...auren halima ko?"ya fuskanci da gangan take watsi da manufofin da yake son yadawa,hakan ya sanya ya kira sunanta wanda ya tilasta mata dubansa
"kinsan ko a da idan na fadi magana irin wannan da gaske nake ko?,to har yau din ma hakan take,da gaske sumayya na dawo neman aurenki ke karo na biyu babu wasa,kuma ina fata wannan karon ni zan jefa qwallon"shuru tayi tana jin yadda zuciyarta ke bugawa,mukhtar dinta ta tuna,ta daga kai tana kallon abdur rahman idanuwanta fal qwalla
"yanzu kaima sai ka yarda naci amanar ya mukhtar?" Cikin rashin fahimta ya tsuke gira
"Cin amana kamar yaya,da aurensa ne a kanki?,ina cewa koda yana raye halas ne na aureki bare ya rasu?"
Kalmar ta mata ba dadi sai ta miqe
"A gunka mukhtar ya rasu amma ni a cikin zuciyata rayayye ne tamkar yadda kake a raye" sai ta juya ta fice kuka na qwace mata,sam bayi tunanin wannan maganar ta isa bata rai ba,amma da ya tuna cewa har yau tana cikin zafin mutuwar uban danta sai ya mata uziri,hakan ya sanya daga sitting room din ya wuce ba tare da ya dawo ciki ba,har dare ranta na a jagule,tana zaman zamanta yana neman jagula mata lissafi,tana ganin kiransa ta share shima da yaga bata daga ba sai ya tura mata tex ya qyaleta.

  *******    *******   ********

      Batasan cewa ana shirin jagula mata lissafi ba sai washegari da azahar data tsinkayi sallamar su nuwaira a tsakar gidansu,baki daya yaran ne cikin kyakkyawar kaka data bayyana mata har yau basu sauya kan turbar data dorasu ba,zuciyarta ta dinga bugawa tsoro ya cikata,duk da a bangare guda tayi farinciki da ziyarar tasu.

       Sosai taji dadin zuwan yaran,basma ta dubeta
"Anty abbanmu ne ya kawo mu,yace wai kema zaki dawo gidanmu ko?" Yarinyar ta tambayeta,murmushi tayi tana shafa kanta
"Basma,har yau surutu na nan kenan" ta fada da sigar son bagarar da maganar,tare suka wuni da ita,suna zagaye da ita suna bata labarun gidansu da yadda lamura suka sauya,inda sukayi dai dai ta yaba musu,inda suka kuskure ta gyara musu ta nuna musu yadda akeyi.

     Da yamma bayan sun gama sallar la'asar sun sake cin abinci nuwaira ta dubi sumayya
"Anty,don Allah ki daure ki dawo gidanmu,abba yace mu roqeki,muna sonki wallahi anty,baki ga yadda hajiya ma ke son ki dawo ba,naji tana cewa ne ba zata sanya baki ba tun yanzun,kada nauyinta ya sanya kiyi abinda bakiyi niyya ba ta shiga haqqinki,don Allah anty ki dawo" ta fada tana karkatar da kai,sai islam ma ta matso
"Eh wallahi anty tunda kika tafi baki daya gidan babu dadi,ko abba ma barin garin yayi,baifi wata daya da dawowa na,da ya dawo kuma kullum masifa suke da mama,gidan ba dadi muna gun hajiya ko yaushe,ki dawo anty don Allah kinji" kasa magana tayi baki daya,wato lukman kwaso mata yaransa yayi kenan su masa campaign ko su daure ta da jijiyar jikinta?
"Anty baki ce komai ba" cewar nuwaira wadda ta qagu taji sumayyan ta amsa,murmushi ta sanya ta kama hannayensu ta hade waje guda
"Kunsan komai nufin Allah ne,kuma ko wanne bawa da irin tasa qaddarar,to ku yita addu'a idan akwai alkhairi zan dawo in sha Allah kunji?"
"To anty" suka fada jikinsu a sanyaye,duka sai suka bata tausayi,babu shakka yaran abun tausayi ne,su masu uwa ma kenan bare mara uwa a gidan,ko da yake dace da uwa ta qwarai shine jigon farinciki da jin dadin rayuwar 'ya'ya duniya da lahira.

       Qarfe biyar saura yaro yayi sallama gidan yace su nuwaira su fito,tuni basma ta sheqa da gudu ta gano abban nasu sannan ta dawo
"Abba ne,yace ku fito",kyautar humra da kwalakca ta yiwa kowannansu,sannan ta zuba wata da yawa ta hada da turaren wuta tace su kaiwa hajiya.

       A bakin qofar soro ta ja tunga tana musu sallama,nuwaira ta dubeta tana narai narai da idanuwa
"anty iya nan ko qofar gida ma ba zaki rakamu ba?"dariya tayi,ta fuskanci wayo wai yarinyar keson yi mata
"shikenan muje"ta fada don faranta musu,yana tsaye bakin mota ya bubbude qofofin,da dai dai yaran suka dinga shiga tana musu sallama sannan ta rufe musu qofar motar,tana dagowa suka hada idanu
"Ku gaida gida ku gaidamin hajiya" ta fada tana juyawa da niyyar shigewa ciki,da sauri ya tari gabanta
"Haba mana sumayya,ko gaisuwa ai kya tsaya kuyi ko?" Ta tabbata idon yaran yana kanta hakan ya sanyata tsayawa tana dubansa
"Don girman Allah sumayya kimin alfarma ki koma gida na,kimin alfarma ko don rayuwar yara na"
"Ni kuma tawa rayuwar fa?" Ta masa tambaya kai tsaye
"Sumayya gida na ya sauya a yanzu,da qafafuna nake tsaye,hijabin dake lullube da idanuwa Allah ya yamin shi,ki taimaka ki koma gidana ki sa cikasa mana sauran haske da farincikin da muke da buqata,kowa a gida na na buqatarki sumayya,don Allah kada ki gujemu". Kai ta kada
" lukman,bani da buqatar nayi aure har na koma ga mahalicci na,domin ina fata naje na hadu da mijina uban 'ya'yana,ina mai baka shawara tun wuri kayi haquri da ni"ta qarashe zancan zuciyarta na raurawa ta kewayeshi ta wuce ciki,jiki babu qwari a sanyaye shima ya koma cikin motar ya tada ita ya bar layin.


Tana shiga zainab na miqa mata waya,bata san ko waye ba haka bata tambaya ba,tama yi tsammanin anty dije ce don tace anjima zata kira ta,wayar ta maqala a kunne,muryar abdur rahman ta mamayi dodon kunnen nata
"Ba mukhtar kadai ba,ashe har lukman ma na raye a zuciyarki?" Tambayar da ya fara jefo mata kenan wadda ta sanyata saurin janye wayar daga dodon kunnenta,yaushe abdur rahman ya ganta da lukman?,tambayar data yiwa kanta kenan,kawai sai ta tsinci kanta da fashewa da kuka,saman katifarta ta fada tana kife kanta a saman filo,baki daya cikin kwanaki hudu zuwa biyar kacal suna son lalata zaman lafiyar zuciyarta ruhinta da ma gangar jikinta?,wa yace musu tana da buqatar aure a yanzu?,wa yace musu tana buqatar wani daga cikinsu?,akan me zasu yi mata kutse cikin rayuwar data lallabata ta fara samun nutsuwa da dangana?su suke suce ta mance da mukhtar ta fara sabuwar rayuwa da su?,ta mance da mutumin da shi ya fara gina tunani da zuciyarta?.


Qarar wayarta karo na biyu ya sake katse mata tunanin da ya karade ilahirin qwaqwalwarra,kamar ba zata daga ba sai taga lambar anty dije ke yawo bisa fuskar wayar,qara fashewa tayi da kuka da taga sunanta,zuciyarta ta sake karyewa,tasan a irin wannan yanayin babu wanda take budewa damuwarta irin anty dijen,taso ace a yanzu tana kusa da ita,sai ta daga kiran da sauri,saidai maimakon sallama da anty dijen ta tsammata sai taji sautin kukan sumayya ya karade kunnuwanta.








*mrs muhammad ce*👑

✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

5⃣4⃣


*Bismillahir rahmanir rahim*

*Rabbukum a'alamu bima fi nufusikum*

*(haqiqa)ubangijinku shine mafi sani ga abinda yake cikin zukutanku*
_________________________________



       A rude anty dije ta soma tambayarta
"Lafiya sumayya?,me yake faruwa?,ko wani ne ya mutu?" Ta jero mata tambayoyin baki daya,jin tayi shiru bata tanka ba ya sanyata itama shirun tana sauraren kukanta,ta tabbatar wata matsalarce ta taso mata haka jikinta ya bata,tausayin yarinyar take ji,sai yaushe ne zata fita daga matsala,sai data dauki a qalla minti goma sannan ta soma magana cikin karayar zuciya
"Anty,lukman da abdur rahman"
"Me ya samesu?"
"Anty......dukkaninsu sun dawo,kowanne so yake na aureshi,fisabilillahi anty ni bazan huta ba?,duka duka yaushe na soma samun nutsuwa?,anty bana buqatar sake wani auren yanzu,tsoro nake ji kada su nufi malam da maganar,idan malam ya umarceni anty bazan iya bijire masa ba" sai ta fashe da kuka,tsaki anty dijen tayi sannan tace
"Zancan banza,kema kin riga da kinsan cewa malam yasan haqqinki na hannunki yanzu,ke zaki zabawa kanki miji ko?,sannan tsakanin lukman da abdur rahman akwai wanda ya isa ya aureki ne bada amincewarki ba da zaki tadawa kanki hankali ki dinga zubda hawayenki?,duk wanda kika zubar a baya bai isheki bane sumayya?,ko so kike wani ciwon ya sokeki?,to nikam na gaji da ji da gani,kishirya da gaske idan nazi tare zamu koma,idan yaso naga wanda zai qara bata ranki" ta fada tana katse wayar.

       Shiru tayi tana juya wayar a hannunta,ba haka taso anty dije tace ba shawarar yadda zata kubuce daga tsakanin da lukman da abdurrahman suka sanyata take so ta bata,amma da tayi tsai sai ta lura lallai babu hanyar da zata zille musun idan ba barin garin kanon zata yi ba kamar yadda anty dije tace,sai ta sauke ajiyat zuciya tana goge hawayenta,tana qiyasta idan ta bar kano koda na tsawon wata daya ne itama ta samu hutu,ta samu ta manta da wasu lamuran ta manta da damuwoyinta.

  *******  *******   *******

  Washegari ta shirya don zuwa gidan yaya yahanasu ta dauko abdallah tunda duka duka saura kwana biyu anty dije tazo,tana tsaye a falon mama tana sanya hijabinta tare da yiwa mama sallama suka ji sallamar abdur rahman,kamar ta juya ta shige daki amma tasan idan tayi hakan kamar ta nunawa mama akwai wani lamari tsakaninsu irin wanda ya faru a baya,abinda bata da buri ko fatan kowa ya fahimta kenan
"Ina yini" sumayyan ta gaisheshi tana shirin ficewa bayan sun gaisa da mama
"Lafiya......ina zuwa haka?" Ya tambayeta yana dan dubanta,cikin hanzari ta soma sanya takalmanta tana bashi amsa
"Zan dauko abdallah he gidan ya yahanasu"
"Yauwa,nafi jin dadin tafiya,dama jiya da naje na yiwa abdallah alqawarin yoghourt" ya fada yana miqewa tsaye,kamar ta zura da gudu haka taji,take yanayin fuskarta ya sauya wanda tashin farko ya fahimci bata ji dadin shishshigin da ya mata ba,saidai sam bashi da damuwa matuqar zai kasance da ita,inda zata iya zata ce masa bata so amma idanuwan mama ya sanya ta kasa cewa komai
"Sai mun dawo mama"
"Allah ya kiyaye hanya ku gaida min yahanasun"maman ta fada ba don son ranta ba,don ba kasafai take barinsu suna shiga motocin gida ba koda na 'yan uwa ne,tafi ganewa su hau ta haya
"Zataji" inji zainab wadda ita ce 'yar rakiyar.

      Gaban motar ya bude mata da kansa,sai da yaga ta shiga ta zauna sannan ya zagaya nashi mazaunin ya tashi motar suka tafu,shiru ya ratsa motar,babu mai magana tsakaninsu,sai ya sanya hannunshi ya dannan plate jikin redion motar,cikin sakanni lacture malamin dake cikin fefan ta fara tashi,ya daj qaro volume din sannan ya dauke hannayensa ya maida kan sitiyarin motar
"Nikam bansan wanne irin baqin jini ne da ni ba" ya fada qasa qasa yadda ita da shi ne kawai zasu iya jin me yake fadi,ta gefen ido ta kalleshi don ta tabbatar da ita yake ko kuwa,sai ta gane da ita din yake saboda yadda yake kallonta kadan kadan,shiru tayi bata da niyyar tankawa saboda bata fuskanci ma inda zaurancen nasa ya sa gaba ba
"Sumayya me nayi da jiya baki sona,yau ma kinqi karbata,ko na aikata miki wani laifi ne?,ko ina da wani aibu da ban cancanci a soni ba?" Ya tambayeta yana mai muradin jin amsarta
"Baka aikata komai ba,amma don son annabi mubar maganar nan,kada ka manta har yau jinyar zuciyata nake bata warke ba,ban kuma san ranar warkewarta ba" ta fadi tana duban gabanta ba tare da ta dubeshi ba.

     Shuru yayi yana jin yadda ransa ya quntata,karo na farko da ya soma jin kishin nukhtar har cikin ransa,mukhtar jininsa ne wanda har ya mutu babu wani abu mara dadi da ya taba hadasu,hakan ya sanya bai sake tofa komai ba har suka iso gidan yaya yahanasun,tayi zaton zai shigo ne da ya ajjiyesu,sai taga ya juya kan motar yayi gaba.

      A tsakar gida suka samu abdallan,yana ta wasa da dan qaramin

Please Login or Register in order to submit comment