Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abinda ya dace din" duk da bai gane da wa yake nufin ba amma ya miqe kasancewar ya riga ya bashi umarni,cikin girmamawa ya rusuna yana cewa
"A huta lafiya" baban bai amsa shi ba har ya miqe ya juy,har ya taka daya biyu sai kuma ya juyo ya dawo ya sake rusunawa aladabce
"Dambun naman naka ya qare?" Ya fahimci me yake nufi,dambun naman da sumayya tayi masa ne,ya ganshi yana ci ya tsokaneshi da cewa gun saidawa aka siyo masa don yasan baison cimar siyarwa,yace idan ya qare zai masa magana ya sake siyo masa a inda aka siyo
"Bai qare ba" baban ya bashi amsa idonsa akanshi har ya miqe,baiyi qarya ba,mustaphan daban yake cikin yaranshi,kamar yadda yake da wasu baqin halaye haka dabi'unsa na kula da iyayensa suke,daban ya daukesu,martaba da darajarsu bai hada ta daya data wani halitta ba,cikin kowanne yanayi ko motsi nashi yakan sanya shi gaba,fatarshi da addu'arshi daya Allah ya azurta shi da zuriyya dayyiba saliha,wadda zata ji qansa yadda yake jin qan nashi iyayen.


***** ****** ****** *****


Daren da zasu tafi kanon kasa bacci tayi baki daya,tsaf ta gama hada komai,hatta da kayan da zata sanya goben ta waresu gefe,cikin irin wannan zaman taji kuwwar wayarta,ta janyota tana dubawa,baquwar lamba cr,maidata tayi ta aje don a yanzun tsoron daga baquwar lamba take,sai data fuskanci wayar na neman hanata sakewa ya sanya ta dagawa,muryar alqasim ce ta bayyana,yasan kadan daga aikinta ta datse wayar wanda baya fatan haka,saboda yaci wahala kafin ya kai ga samun lambarta,hakan ya saka ya cikata da magiyar ta tsaya ta saurareshi,bai kyautu ta watsa masa qasa a ido bo saboda qimar mahmoud,hakan ya sanya ta tsaya tana sauraronsa zuciyarta fal da mamakin inda ya samu ainihin lambarsa,gaisuwa sukayi ta mutunci ya sake mata sannu da jiki ta amsa masa,shiru yayi kamar ba zaice komai ba hakan ya sanya ta buqaci kashe wayarta,wanda shi ya zaburar da shi ya soma magana,tatsuniyar gizo dai bata wuce ta qoqi,
"Alqasim,ni bazawara ce na taba aure,ko da ina da ra'ayin aure banda ra'ayim auren saurayi,ballantana ma mi ban hango shekarun da na tsara ba kafin na sake aure,babu lokaci,saboda haka ina mai godiya bisa qaunar daka nunan,kuma ina mai baka haquri tare da addu'ar ubangiji ya baka wadda ta fini" ta kaiwa qarshe ta kashe wayar ta cillar gefe tare da mirginawa ta kwanta ta runtse ido tana son bacci ya dauketa ko zata samu damar tashi gobe da wuri ta shirya.


******** ******* *******


Qarfe sha daya na rana dukkan shirin tafiya ya kammala,wannan karon har da abban laila zasu tafi a mota daya,sun gama komai har motar ma drivern ta faka ta bakin get din gidan,duka suna ciki zaune,abban laila kawai da ya shiga yiwa baaba sallama suke jira,wanda sabonsa ne baiyin kowacce tafiya bai sanarwa baban ba,saboda ya daukeshi a mazaunin mahaifi.


Anty dije ce tayi mantuwa cikin gidan,botiki ne data zubawa mama sabulun salo mai yawa a ciki wanda su zainab zasu hada sabulun gyaran jiki,sau biyu tana aiken laila bata ganshi ba,ganin zata bata mata lokaci kada abbansu ya fito ba'a dauko ba ya sanyata tura sumayya.


Kunnenta maqale da waya suna waya da abdur rahman,yayin da daya hannun ke riqe da dan botikin,ta sanyo qafarta waje kenan kunnenta ya jiyo mata muryar tasa ginshira yana fadin
"Amma why not kubi jirgi,akwai jirgi daga nan zuwa kano 12"dariya uncle farouq yayi
"wannan kam ai su ku manya,ba damuwa,awa biyar ne ba dadewa zamuje" hannu ya bashi yana fadin
"Allah ya tsare"
"Amin amin,wataqil kafin mu dawo kun koma,sai gani na gaba" murmushi kawai yayi ya juya,har a lokacin tana labe bakin qofar,hakanan jikinta ke rawa har wayar hannunta ta subuce ta fadi bata sani ba
"Ah ah,ashe kin dauko me kuma kike a tsaye a nan?" Anty dije ta tambayeta wadda ta biyo sahunta jin shirun yayi yawa
"Ba komai...fitowa zanyi dama" ta fada muryarta na rawa tana durqusawa tare da soma tattare wayarta data watse a gun,bin wayar anty dije tayi da kallo cikin ranta tana tambayar kanta me ya faru har ta kammala tattarewar ta juya tabi bayanta bayan ta rufe gidan.


TOFA!


*Mrs muhammad ce👑*

📚📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

6⃣2⃣


*Bismillahir rahmanir rahim*

*KO KUNSAN SABODA BALA'I DA JAHANNAMA KE DA SHI HAR WANI SASHE NATA YANA NEMAN TSARI DA WANI SASHEN?*

*Allahumma ajirna minan nar*

_________________________________





        Luf tayi cikin motar idanuwanta a lumshe,duk da hayaniya da karadin da suke tayi cikin motar amma babu ita,bata san me ya haddasa mata mutuwar jiki ba,batasan me take tsoro ba,abu daya ta sani muryar na daga mata hankali,muryar na sanyata ta tuna da mukhtarinta,anty dije ma tayi tsammani bacci take saboda ta san jiya batayi wani isashshen bacci ba,yau kuma ta riga kowa sammakon tashi,tun tana jin hayaniyarsu sama sama har bacci barawo yayi awon gaba da ita.

      Kamar kullum yau ma sun tsayawa wannan restaurant din don cin abinci saidai banda ita,zaman ta tayi cikin mota sai takeaway sukayi mata sannan suka wuce.

      Yamma lis suka isa kano ta dabo tumbin giwa,ko da me kazo an fika,gari ba kani ba dajin Allah,wani farinciki ya dinga shigarta tun kafin su qarasa gida,iskar garin na kano take shaqa sosai,taje farinciki ya lullube zuciyarta,doki ya mamaye zuciyarta,kewar mama malam abdallah dama su zainab suka dawo mata sabuwa fil,kamar kuwa uncle farouq ya sani yace a fara biyawa gida a sauke sumayyan,anty dije zatayi qorafi kan ba haka ba su wuce gida idan sun huta baki daya sazo gobe yace a'a sam tana son taga mamanta,hakan ya mata dadi matuqa duk da ta boye dokinta,suna sauketa kuwa suka wuce kan sai gobe zasu shigo,tana fara'a ta daga musu hannu sannan ta sanya kanta cikin gidan yaran maqota na shiga mata da jakarta.

      A tsakar gidan ta ware muryarta tana kwada sallama,abdallah ne ya soma fitowa da gudu halima na biye da shi,da gudu ya qarasa wajenta yana kiran
"Mami na"
"Abdallah na" itama ta fada cike da kewa ta durqusa tare da ware hannayenta ya fada ciki ta miqe rungume da shi tana dubansa fuskarta fal murmushi,ya qara kyau wayo da girma kamar ba abdallahnta ba,kallo daya zakayi masa ka tabbatarwa kanka yana cikin kwanciyar hankali tare da samun cikakkiyar kulawa,yayi bul bul da shi,fes kamanninsa da babanshi kan fuskarsa.

       Dakin mama ta shige tare da su halima da maman,tana sanya kanta falon taga amina zaune matar abubakar ciki a gaba,baki sumayyan ta bude tana kallonta
"Antynmu kice kema kina gidan namu yau?"
"Gidanku ko gidanmu,aike kam yanzu baquwarmu ce" dariya sumayya tayi
"Allah sarki anty amina,kice kinyi nauyi shi yasa kika kasa tasowa ki tarbeni" dariya aminan tayi a dan kunyace saboda mama na gurin,gaban maman sumayya ta qarasa idonta a kanta tana jin wani dadi na gajin mahaifiyar tata,itama maman kallonta take,a gabanta ta durqusa ta gaidata,cikin farinciki maman ta amsa tana tambayarta ina dijen kuma,nan ta sanar mata sai gobe zasu shigo,hira ce ta barke babu qaqautawa tsakaninsu abdallah na kan cinyarta,yaqi yarda ko nan da can yaje,halima ke dungureshi tana cewa
"Zata tafi ta barmu da kai ne mai qaton kai da kaqi zuwa wajen kowa" amina ke kareshi
"Barshi malama,yaro da uwarsa,ai yayi qoqari ma,yaushe rabon da ya ganta?" Har magariba suna hira,sai da aka gama sallah magariba sannan sumayya ta cewa zainab ta hada mata ruwa zata yi wanka,dariya zainab tayi
"Wankan lafiya da daren nan?"
"Bazan iya bacci ba sai nayi wallahi" dariya ta kuma yi
"Kice ba banza ba yaya sumayya kika dad wannan dan banzan kyan,wallahi abuja ta karbeki,baki ga yadda kika koma 'yar gayu ba"
"Hada min ruwan sai kizo kici gaba da sharhin naki" sumayya ta fadi tana dariya,anty amina ce ta karbe
"Gaskiya ai ta fadi,wallahi garin ya amsheki sosai"
"Kin biye mata kenan antynmu" ta fada tana dariya anty aminan na tayata.

       Bayan tayi wanka ta sake shiryawa cikin doguwar riga ta wani cotting din yadi mau gajeran hannu,ta yane kanta da dan qaramin mayafi ta dawo falon mama,a nan suja zuba tuwon dare baki daya idan ka dauke maman,suna ci suna ci gaba da hira,har yanzun idanuwan maman ma kanta,ita kanta tasan diyar tata ta soma sauyawa kamar ba ita ba,ta tabbatar sauyin rayuwa ya fara samuwa a gareta,cikin zuciyarta ta dinga mata addu'ar Allah ya azurta ta da miji na gari,wanda zaici gaba da dawainiya da ita cikin ingantacciyar rayuwa.

      Suna gab da kammala cin tuwon malam da yaya abubakar sukayi sallama,amina tayi saurin janyo hijabinta ta sanya,yau malam da kanshi ya shigo falon maman,fuskanshi shina dauke da farincikin ganin diyar tasa,cikin girmamawa ta gaida malam din ya amsa yana tambayarta mutan abuja,tace kowa lpy suna gaida ka,amma gobe su antyn zasu shigo,madallah malam din yace sannan ya fice yana cewa bari ya barta ta huta da gajiyan hanya,murmushin jin dadi kawai tayo ganin yadda kowa cikin 'yan uwanta ke qoqarin nuna mata qauna da kulawa.

       "Hala nan gaba kadan zamu kasa ganeki sumayya,irin wannan kumatu haka" sosai ya bata dariya,bama ita kadai ba duk jama'ar falon,don babu wata qiba da tayi tsabar tsokana ce,saidai duk wanda ya kalleta zauga yadda fatarta ta murje tayi kyau,hutu da wayewa suka sake bayyana a jikinta,sai da ya gama tsokanar tasa sannan yace
"Dazun dama nake cewa ko baku zo ba cikin satin nam zaki ganni kafin ku wuce london,inaso muyi maganar kudin abdallah dake hannuna,sun fara yawa gaskiya ya kamata kuma ayi tunanin sake fadada wani kasuwancin da su" dubanshi tayi
"Haba ya abbakar,kaima fa kamar uba kake gunsa,duk abinda ka yanke dai dai ne,baya ga haka ga malam ga mama ga yaya yahanasu ko su sun isa kayi shawara da su ku zartar da duk hukuncin da ya dace ko?"
"Eh duk munyi magana da su kuma su suka ce aji ta bakinki,amma koma me ake ciki kan ki koma zamuyi magana,yaushe zaku koma?"
"Ba zamu wuce sati daya ba"
"To ba damuwa....ke taso mu tafi" ya fada yana miqewa,amina tasan da ita yake,sai ta shiga yunqurin miqewa
"Dakata mata mana,yanzu fa ta gama cin abinci ko fada mata baiyi ba,koma ki zauna ki shirya a nutse" cewar mama tana hade rau,dariya ta kama sumayya,ba shakka idan da duka haka surukai suke da ba'a dinga samun baraka tsakanin surukai ba.
"Idan kin gama ki kirani a waya,zan je ayimin aski" ya fada yana ficewa ta amsa da to.

      Halima ce ya shiga tsokanarta kan tafiyarsu london
"Yaya sumayya dama nice,ki barmim don Allah" haka ta dinga fada,murmushi kawai tayi tana kallonsu,abinda basu sani ba ita din ce ke jin dama ita ce su,basu taba fuskantar wata matsala ba,ko yaushe suna tare da mamarsu da babansu,suna cikin garinsu,basu da wata damuwa da ke hanasu bacci ko ta sanyasu a halin tunani,tana ganin quruciya ce kadai ke sasu sha'awar zamowa ita.

        Sai takwas na dare amina suka tafi da ya abubakar,zuwa lokacin itama bashin baci da gajiyar hanya sunyo mata kabbara,tilas ta musu sallama ta dauki abdallah da yayi bacci kan kafadarta suka nufi daki.

  *******   *******   *******

     Washe gari kusan tare sukayi aikin gidan ita da mama,kasancewar qarfe shida da rabi su halima na fita makaranta sai goma na safen suke dawowa a irin wadan nan ranakun,a yanzu haka ma shirin tafiya musabaqa suke wanda suna daya daga cikin wadanda aka zaba,sunayi suna hira irin ta tsakanin da da uwa,zuciyoyinsu fes,sumayya na jin gata ga mamanta kamar kar ta sake tafiya,yayin da maman ke farincikin sauyawar diyar tata,tara da rabi suka kammala har karin kumallo,wanka sumayyan ta shiga tayi sannan ta shirya cikin atamfarta super wadda tayi mata kyau ainun,ta dan taba kwalliya kadan sannan ta sanya hijabinta ta nufi dakin malam.

     Karyawa take sanda ya shiga,ta gaidashi ya amsa mata yana fara'a
"Mutanen abuja yau anyi kwanan kano" kanta tai sunkuyar tana dariya
"Ai malam,duk wanda ya bar gida gida ya barshi" tace tana wasa da yatsunta
"Wannan kuma gaskiya ne" labari take bashi kadan kadan game da abinda ta fahima kan rayuwar garin har mama ta cimmasu a haka
"Qarfe sha daya ne daurin auren fa malam" maman ta tuna masa,a gogo ya duba sannan ya miqe
"Au,au,ai kuwa na manta,gashi sha daya saura kwata,hira ta dauken hankali,idan na dawo ma qarasa ko?"dariya tayi." To,a dawo lafiya"
"Allah yasa".

      Falon mama ta koma don ta karya itama,tana tsaka da hada tea abdallah ya tashi,dole ta bar karyawar ta yi masa wanka ta karbi kayansa wajen mama ta sanya masa
"masha Allah"ta fada tana dubansa tana murmushi ganin yadda yayi kyau,shima sai ya maimaita abinda tace din,dariya ya bata dai dai sanda mama ta shigo bayan ta sallami malam
"gaskiya mama bakin yaron nan ya kuma budewa"
"Ba dole ba,yaron dake zuwa makaranta me zai hana bakinsa budewa", su halima ne suka shigo hakan ya sanya ya qyaleta yayi wajensu can yana buga musu rigima,gefe ta koma ta soma karyawa tana jinsu tana dariya cikin ranta.

        Sallamar abdur rahman data jiyo ita ta sanya ta kusa qwarewa,da sauri ta dauki ruwa ta sha,tare da janyo mayafi ta yafa kafin a amsa iso,yana sallama cikin falon ta soma tattare kayan breakfast din ba tare data kammala karyawa ba ta maida kitchen,tunda ya shigo idanuwansa na kanta,don bai tsammaci tazo garin ba,bayan sun gama gaisawa da mama ta miqe ta fice,su halima ma suka gaidashi sannan suka fice don sauya unifoarm da kama aikin abincin rana na gidan.

       Idanu ya zuba mata har sai da taji nauyinsa ta kau da kai
"kin kyauta qwarai,tunda har baki iya gayamin cewa zaki zo kano,matsayin yaya ma da nake tunani an bani ashe ba haka abun yake ba na bar murna" murmushi ta saki tana kada kai
"Ba haka bane,afuwa,suprise naso baka"
"Da shi dai kike so ki fake,amma inda hakanne ai da a yau da safe zaki kirani ki gayan,ko kuma tun a jiyan ki sanarmin kina zuwa kano ko?"
"To nayi laifi babban yaya ayi haquri" ta fadi cikin raha,numfashi ya dan dauke kadan,kwata kwata baison sunan,wannan sunan bai masa ba,so yake yaji ta kirashi da wani suna dake qunshe ko yake nuni da zallar qauna,kai ya gyada kawai yana murmushi,sabida ya lura idan baiyi wasa ba wankin hula na neman kaishi dare
"Ina abdallah?" Sai ta dan ware idonta kamar tana nemansa
"Yanzun na masa wanka na bashi abinci,ina zaton ya fita"nashi idanun shima ya waro
" kan me zaki dinga barmin yaro yana fita waje?"dariya ta danyi
"To duka ma yaushe na dawo garin ni?,abdallah ya riga ya saba da fita tunda ya tashi gidan yara" halima ya kira yasa ta dauko masa abdallahn,ba dadewa ko ga dawo da shi,yayi budu budu da qasa da alama ya sha wasan qasansa ya qoshi,kicin kicin da fuska abdur rahman din yayi ya hau fada,tilas ta tashi ta sake gyarashi.

       Sai da ya tabbatar ta gyarashin sannan ya miqe yana dubanta
"Har zaka tafi?" Ta rigashi fadi
"Eh,dama ai zuwan ba naki bane,tunda ba'a gayan zuwan ba,amma zan dawo ko zuwa gobe,idan ba gobe ba jibi,akwai muhimmiyar magana da nake so mu tattauna" shiru ta danyi
"Allah ya nuna mana,ka gaida bahijja da hajiya don Allah"hararar wasa yayi mata
"bazan gaya mata ba,maruqar ba zaki je ki gaidata ba,ko kara ma sumayya fa baki da ita"dariya tayi a kunyace,ita kanta tasan bata kyauta ba
"Kayi haquri in sha Allah bazan koma ba sai naje na gaida hajiya" kafada ya daga yana fadin
"Da dai yafi" sallama ya musu ya danqawa abdallah kayan qwalama kamar yadda ya saba sannan ya wuce.

       Kwanakin ta a kano jinta take kamar wata sabuwar duniya,wuni suke hira,hakama anty dije idan ba wani gu zata ba tana gun mama,ranar da abdur rahman yace zaizo har yammaci taji shiru,hakan ya sanya ta shirya don zuwa tsohuwar unguwarsu kamar yadda tayi alqawari,halima da zainab ne 'yan rakiya,sai laila wadda a gidan ta kwana,sumayyan tayi kyau cikin wani leshi wanda daya ne daga cikin kayan sallarta da uncle farouq ya siya mata,mayafi ta yafa bisa matsantawar halima,duk da babba ne amma tayi kyau matuqa,talkalmi da jaka komai da tayi amfani da shi ya dace da kalolin jikin lace din,sai oga abdallah shima da tayi masa kwalliya cikin qananun kaya,da rufaffen takalmi irin na maza.

      Tana tsakar gida suna sallama da mama suka ji sallamarsa a soro kamar yadda ya saba bai shigowa har sai an masa izini,maganar da suke da mama ta katse tana duban soron,sai da maman ta sanya hijabin sannan aka masa iso,tunda ya shigo idanuwansa na kanta,tayi masa kyau fiye da duk lokutan da ya saba ganinta,yai yayi kamar yayi sallama da mama ya fito saidai ita tasan ba tafiya yayi ba,suna fitowa suka ganshi hakimce jikin mota,shi din ma yayi kyau cikin wani yadi mai taushi ruwan qwaiduwar qwai,gaban motar kawai ya bude mata tare da cewa
"Bismillah" kai ta rausaya ganin yadda ya tsareta da idanu kawai ta shige,su laila suka shiga baya sannan ya shiga ya tada motar.

        Sai da suka fice daga layin sannan yace
"Ina zuwa ranki ya dade?" Kanta ya sake rausayarwa tana murmushin sunan da ya laqaba mata
"Tsohuwar unguwar da muka zauna ni da ya mukhtar" wani kishi ne ya soki zuciyarsa,amma sai ya danne ba tare da ya nuna ba,kamar ta fahimci mekw tsinkulinshi sai tace
"Zanje mu gaisa da yara da iyayensu da muka zauna tare"
"Hakan nada kyau" ya bata amsa,da fari motar tayi shiru,sai daga bisani abdur rahman din ya sako hira,kadan kadan suke tabawa har suka isa unguwar.

      Unguwar na nan kamar yadda ta santa,saidai tsohon gidansu da suka zauna wanda mutanen da suka siyeshi suka masa kwaskwarima,gidan maman naana suka fara shiga,taso ta kasa gane sumayya sai da naana ta fito daga daki,da gudu ta nufi sumayyan tana ihun kiran sunanta,rungumeta tayi tana dariya itama tana kiran sunanta,daga nan maman naanan tayi mata iso zuwa falo
"Wallahi sam fuskarki taso bacemin sumayya saboda canzawar da kika yi,kin sake zama babbar mace?" Maman naanan ta sake fada cikin mamaki,murmushi kawai sumayya tayi sannan suka fara gaisawa,naana na gefe bakinta yaqi rufuwa,tashi tayi taje ta siyo wa sumayyan pure water mai sanyi da lemo,dubanta sumayyan tayi tana murmushi,ba zata manta ba wannan na daya daga cikin rainon da ta yiwa yaran na girmama baqo,ashe har yau basu manta ba,ita kanta nanan ta girma ta sauya,nan sumayyan ta dinga tsokanarta na ganin girman da tayi.

      Kafin ta bar gidan sai ga yaran na shigowa daya bayan daya,da alama nana ke shiga gida gida tana gaya musu zuwanta,dui wadda ta shigo rungume sumayyan take cikin jin dadi,itama mamakin girman yaran take,kusan awa daya da wani abu tayi a gidan sannan ta dinga shiga gida gida yaran na rakata,kowa mamakin sauyawarta yake inda ita kuma sam bata ganin sauyawar da tayi,duk gidan data shiga sai ta ajjiye musu dubu daya,cikin kudin da ya abbakar ya bata jiya a ribarta na kudinta da ake juya mata,sunyi murna kuwa sosai,sai magariba sannan suka bar unguwar duka abdur rahman na cikin mota yana jiransu.

        Sai wajen isha'i suka koma gida,don daga qofar gida da ya ajjiye motar masallaci ya tafi sallar isha'i,sai da ya dawo yayi kiranta a waya kan ta fito ya dawo,sanda ya kira din fitowarta kenan daga wanka,don ranar ta gaji da wuri take sonyin bacci.

        A sitting room dinsu ta sameshi wanda halima ta bude masa ta masa masauki a can,kamar kuwa tasan sumayyan bata son komawa cikin motar,kallonta yake sake yi,komai ta sanya kyau yake mata,rigar data sanya ba wata ta azo a gani bace amma ta mata kyau duk da hijabi ne a jikinta saidai qarami ne.

       "Sumayya,zuwa yanzu na gaji da zaman kare a karofi da nakeyi,lokaci yayi da zamu fukancu gaskiya baki dayanmu,ni na sani cewa bazai yiwu naci gaba da biye miki a yadda kike so ba,kamar yadda kema kika sani cewa indai da rai da lafiya malam bazai taba barinki babu aure ba" abdur rahman yayi shiru yana maida numfashi tare da nazartar yanayin da sumayyan ta shiga sannan ya dora
"Ko baki so sumayya dole a ce mukhtar ya koma ga Allah,kin sani na sani haka ma duniya ta shaida,don wani wanda kake so ya rasu ba shine zaisa kace kai kuma ka bar yim taka rayuwar ba,yin hakan dai dai yake da gayawa Allah bai maka dai dai ba kenan,tunda ya dauke wanda yaga dama ne ya kuma bar wanda yaga dama babu wanda ya isa ya tilastashi,gata daya zaki masa shi da yaronshi ki killata kanki a gidan aure,ki bani dama sumayya na cike miki gurbin farincikin da kika rasa"
"Sumayya!" Ya kira sunanta cikin kaurara murya
"Inason yau ki gayamin matsayina,mu bar wannan zaman qaryar,zaki iya aure na ki zauna da ni?" Shiru tayi maganganun abdur rahman na ratsata,babu shakka gaskiya ya fada mata,wanda shine ya fara gaya mata karo na farko tun bayan rashin mukhtar idan ka dauke malam da mama
"Idan har kin yarda ki barni na yiwa malam magana,tunda a yanzu yana tunanin na janye tunda har kin sake wani auren,ya taba gayan hakan cikin wasa,saidai ni sam cikin zuciyata ba haka bane,har yau sumayya sumayya ce bata sauya ba a idanuwa na"
Shiru ya sake yi don ya bata damar fadin ra'ayinta da abinda ke zuciyarta.












*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



6⃣3⃣


*Bismillahir rahmanir rahim*

*MANZAN ALLAH S A W YANA CEWA,KUJI TSORON WUTA KODA DA TSAGIN DABINO NE*
_____________________________________






      "Ka yimin afuwa,a yanzu haka tafiya zanyi ta shekara daya,ka barni har na dawo don Allah,na sani cewa ka cika mutum,kuma ka nunan dukkan wata qauna da halacci,amma ina son ka barni har zuwa sanda zan dawo daga wannan tafiyar,wala'alla zuwa sannan zuciyata ta sake sanyaya daga rashin da nayi,ka sani abdur rahman yadda mutuwa ke da ciwo da wuyar barin zuciya,kayi haquri da ni don Allah" ta qarashe maganar muryarta na rawa idanuwanta na tara hawaye,tausayinta ya kamashi,ya sani cewa raba zuciyar sumayya da mukhtar ba qaramin abu bane,a kanshi ta fara sanin so da qauna,a kansa ta fara sabawa da wani namiji baare,ta soma iya magana da d'a namiji,tilas yaci gaba da haquri kafin ya cimma burinsa,zaici gaba da addu'ar samun zabi mafi alkhairi,kafin lokacin dawowarta ya tabbatar shima duk wasu burikansa sun gama cika,ya kammale hankalinsa guri guda,dubanta yayi cikin sigar lallashi
"Na sani cewa shekara daya ba kwana daya bace,amma gurin Allah ba komai bace,Allah ya nuna mana,amma kema sai kinyi yaqi da zuciyarki,sannan kada ki bawa wani dama bayan ni,kinyi alqawari?" Murmushi tayi saboda maganar ta bata dariya,to shi dinma tanqwara zuciyarta take qoqarin yi ina ga ace ta bawa wani dama,ko ya mance zuciyarta ba lafiyayya bace?
"Baka da wannan damuwar" ta fadi tana kada kai,maganar tayi masa dadi sai yayi murmushi ya soma janta da hira,bai tafi ba sai da ya rage mata damuwa sannan sukayi sallama.

       A daren kasa bacci tayi baki daya,juyi ta dinga yi daga farkon gado zuwa qarshensa,tunani fal zuciyarta,zuciyarta sam babu dadi,rayuwa kenan,yau zaqi gobe madaci,abinda ya dinga yi mata kai kawo kenan har bacci barawo ya dauketa.

       Kwanakinsu a kano sunyi mata dadi qwarai,ana ta gabatar da hawayan sallah irin na al'ada don ma saura suka tarar,garin cike yake da baqi cikin kowanne sassa na duniya masu zuwa kano daga qasashe daban daban,kama daga qasashen turawa har na larabawa don ganin hawan sallahr garin kano,wanda babu irinshi kaf arewa saidai a kwaikwayeshi,ta yadda tabbas kano nan ake morewa bikin sallah ba kamar sauran garuruwa ba da basusan ana yiba ma,tayi hira da mama

Please Login or Register in order to submit comment