Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da tafiya a hakan,idanunshi ne biye da ita duk inda ta taka qafarta tamkar mai qididdige adadin takun nata,a jikinta takejin akwai idanuwa a kanta baya ga idanun jama'ar dake kai kawo wajen,hakan shi ya sanyata ta fara jin rudewa,tun baya can mutum ce da aka raineta cikin tsaftataccen yanayin da bata iya cudanya da ajnabiyyanta ba,bata sakewa da kowa a lokacin idan ba malam ko yaya abubakar ba,koda wani taro ne na dangin mama matuqar ya hada da maza kamar daurin aure da sauransu bata sakewa,hakan na daya daga cikin dalilan da suka ja ko bikin amira da qyar ra iya sakewa(gareku iyaye mata,wannan dabi'a ce mai kyau,ana son a dasawa diya mace dabi'a ta rashin yarda da sakewa,dari dari da takatsantsan da duk wani jinsin d'aa namiji,wannan dabi'ar na taimakawa qwarai da gaske wajen dakusar da sharrin mai sharri cikin jinsin maza,misali masu baata yara da sauransu,ko da yayye gareta ko qanne maza ki nuna mata yadda zata dinga kamewa a cikinsu,to balle wani d'aa namijin a wajen,idan yayanta ne namiji ki nuna mata girmama shi zata dinga yi,bawai su dinga wasu wasa don tana qanwarshi ba,ko zama a jikinsa kada ki yarda ta yawaita yi don yana wanta,wannan dalili ne yasa ma'aiki yace mu rabawa yaranmu maza da mata wajen kwanciya da zarar sun fara wayo,idan qannenta ne kuma ki koya mata kama girmanta,bata shiga suyita wasu wasanni ba,koya mata sanya hijabi kallabi,saka sutura mai rufe jiki,kada kiyi tunanin ai yarinya ce babu komai,a'ah,ita rai dabi'antar da ita ake akan abu,ta yadda komai tsahon zamani zata dawwama a kan wannan dabi'ar).


Ba tare data ankara ba taji ta harde tana yunqurin kaiwa qasa,cikin matsanancin zafi ya tarota ta fada a qirjinsa idanunsu suka harde cikin na juna
"Sannu,da fata dai bakiji ciwo ba ko?" Cewar wata dattijuwa cikin mutanen dake kai kawo a wajen ita samarin yaranta su uku
"Eh banji ba mama"
"To Allah ya taqaita"
"Amin na gode" ta fada cikin siririyar muryarta data ratsa kunnenshi,idanunshi ya daga yaga yadda idanuwa sukayi caaa a kansu,hakan yasan baya rasa nasaba da kasancewarshi sananne cikin fadin nijeria,wani abu yaji ya taba ranshi na yadda dukka idanuwa ke kanta,haushin ta jawo musu kallo ne kokuwa meye ne oho,sai ya fasa sakinta,ya jata sosai cikin qirjinsa ya rungumeta baki daya tamkar mai duba qafartata
"Ki nutsu kada ki sake jawo mana idanuwan jama'a" ya fada cikin kunnenta yana sabule jakar dake hannunta,jikinta taso janyewa,ya fuskanci hakan sai ya daga lumsassun idanuwansa ya watsa mata su cikin salo na harara a fakaice,baki daya ta qarasa gigicewa kamar yadda yakejin sauyin yanayi tattare da shi yana qoqarin kokawa da feelings din,da da hali sakinta zaiyi saidai idan yayi hakan kan idanun jama'a kamar ya tona sirrinsu ne,jikinta ya saki qirjinta na wata iriyar bugawa sanda ya kewaye hannunshi a bayanta zuwa daya kafadar tata yaci gaba da tafiya da ita jakarta na hannunshi,tsoro da firgici duka suka kamata,zuciyarta ta dinga bugawa,yayin da gefe guda qamshinta ke neman buwayar hancinsa,nan da nan suka sake zama abun kallo ba tare da sun ankara ba,abinka da irin yanayin tamu qasar kenan,kanta na jingine a kafadarsa cikin kasala idanubta a qasa saboda kunya da nauyin jama'a data dinga ji,dai dai sanda zasu wuce eesha ta fito,baki ta saki tana dubansu,ya man ne wata?,tamkar taso kuma tasan fuskar,sam ba su'ad bace,kodai gaske ne labarin da humaida ta gaya mata ta zaci tsabar hassada ce?,abinda ya barota daga gida kano kenan ta taho abuja da safiyar nan tazo ta tabbatar,ko gida bata je ba daga hostel direct sai airphort,don bata son taje gida ma a bata labari gwara ta tabbatarwa idanuwanta,tunda ta samu labarin yana abujan,tuni ta zare sun glasses din idanuwanta ta maidashi saman goshinta,sun riga sun wuce shingin bincike tilas ta juya ta fice a sukwane jikinta na rawa,tana fatar samun mota da wuri don isa gidan baba prof,bata jin zata iya yiwa ummee waya har ta jira driver yazo daukanta,wace ce haka take tunanin ta mata shigar sauri?,wace take son sake sanya nisa mai tsaho tsakaninta da muradin ranta?,ta tabbatar da cewa koma wace ba qaramin kamu tarkonta yayi ba,tunda har cikin dumbin jama'a ya man da ko matarsa yake dake mawa amma ya iya rungumarta cikin jikinsa hannunshi dauke da jakarta.


Wani zama ne sukayi cikin jirgi,tunda suka shiga wani babban yaron abokin kasuwancinsa yayi masa magana taga ya sake tsare gida,mutum ne shi da baison shishshigi,mu kuma kusan tamu al'adar kenan,sau tari wasu basa tashi yiwa mutum magana ko kulashi sai sun ganshi tare da iyalinsa,to bare wannan yasan cewa su'ad kadai ya sani,mai yiwuwa wannan yana masa kallon ko ya soma hutawa da 'yammata kamar yadda su sukeyi,kujerunsu na jere da juna,hakanan ya sanya tafin hannunshi cikin nata yana sake matsowa kusa da ita yana magana qasa qasa,idan daga nesa ne zaka rantse shauqin soyayya ke yawo da su duka su biyun sararin samaniya,amma idan a tsakanin kujerun nasu kake idan ka qware wajen iya gulma zaka ji yana fadin
"Banson kiyi komai sai nace kiyi,idan nace kiyi din kuma kiyi babu musu ko tambaya,kibi a hankali" kai ta gyada zuciyarta na bugawa,laushi da taushin tafin hannunshi kadai ke ratsata,yayin da shima ya sauke boyayyar ajiyar zuciya yana jin wani dumi cikin tafin hannunta yana bin kowacce jijiya ta jikinsa.


Gulma ta hana mutumin da yaji ya ambata da bashir zama,ya taso daga tashi kujerar ya nufosu,ya ganshi hakan ya sanya da sauri yace mata
"Kwantar da kanki a kafadata,bance ki dago ba har sai na gaya miki" idanunta ta daga ta dubeshi,saidai ba itama yake kallo ba,yanq danne dannen waya ne da yake qoqarin kashewa yaga tasowar bashir,a hankali ta dora kan nata saman kafadarsa,dumin jikinsu ya soma gauraya,taja wani numfashi wanda ya zuqo dukkan tattausan qamshin jikinsa,kana ta sauke numfashin a hankali tana lumshe ido qamshin nayi mata dadi,gab da zai qaraso ya lura da yanayin almustaphan,ya sanshi sarai,hakan ya sanya ya koma da baya,haushi ya cikashi,baison me ya hanashi zaman VIP ba wannan karon,irin wannan shishshigin ne da takura baiso,shi yasa yake zama can.


Jin baice mata komai ba ya sanya bata bude ido ko daga kanta ba,tayi lamo tana sheqar daddadan qamshinsa,a hakan batasan sanda bacci yayi awon gaba da ita ba,shi dinma ya sha'a fa,sai da jirgin ya lula zuwa sama yana niyyar gyara zamanshi sannan ya tuna,juyawa yayi ya dubeta,yana iya jin yadda zuciyarta ke bugawa a nutse,wanda hakan ya tabbatar masa bacci take,zai janye kafadarsa me ya tuna sai kuma ya fasa,ya jingina da kujerarsa shima yana lumshe idanuwansa.


Cikin tsari da nutsuwa fasinjojin ke sauka daya bayan daya daga jirgin,waiwayawa yayi yana kallonta,bata motsa ba bai kuma san ta yaya zai tayar da ita ba,a hankali kamar wadda aka bawa umarni ta bude idonta,fes suja sarqe cikin nashi,cikin hanzari ta daga kanta daga jikinshi tana jan mayafinta daya zame,baice komai ba ya miqe ya soma takawa,itama miqewa tayi tana biye da shi,gab da matattakalar ta lura babu jakarta
"Jakata" ta ambata qasa qasa,sai ya waiwayo yana dubanta da idanunshi,ya kafeta da su kafin ya furta
"Ohhh,u mean naci gaba da yi miki dako?" Bata ce komai ba ta koma ta baya ta dauko,zuwa lokacin har ya gama sauka yana farfajiyar a tsaye.


Motar dake mallakinsa ce tazo daga company daukarsu,lafiyayyar mota ce dake da sit daban daban kusan hudu,sarai yaga bashir din,haka ya sanya shi saka hannu ya bude mata motar,yana tsaye ta shiga dai dai sanda ya qaraso yana murmushin gulma
"Yallabai,ko zaku saukeni hanya?"
"Babu waje" ya fada cikin dakiya ya shige shima tare da rufe motan ya bawa drivan umarni yaja suka tafi.


Tun daga hanya take kallo har suka isa qawataccen hotel din,wanda hotel ne na isassu sai kaci ka tada kai kake iya zama cikinsa,hotel ne mai kyau da tsari,duk wani mazaunin cikinsa da ya kama daki yana jinsa ne kamar a gidansa,saboda babu ruwan wani da wani,hakanan babu abinda zaka buqata ka rasa,saidai tun a nan ta fahimci bisa dukkan alamu akwai na matan da mazan dake kai kawo ciki masu wata mu'amala ta daban,hakan baya rasa nasaba da yadda taga almustaphan na riqe da hannunta har suka cimma dakinsu.


Komai a gyare yake neat a dakin,kasancewar ya bada sanarwar dawowarshin,hannunta ya sake da sauri don dama Allah Allah yake su isa ya saki hannun,tsaye take a gefe,baquwa zam tana dan kalle kalle,yayin da yake tsaye gaban gado yana qoqarin sassauta tie dinsa,da alama daya daga cikin rigunan jikinsa yake son ragewa,wayarshi dake saman gadon ta dauki ruri,sai data katse bayan ya gama sassauta tie din sannan ya dauka yana dubawa,hannunshi daya riqe a qugunshi yana takawa zuwa bakin window din hotel din,ya bude yana kallon harabar shi,magana yayi wadda bata wuce ta minti daya ba taga ya dawo da hanzari ya maida safarshi da takalminsa,ya maida tie dinsa ya matse,wayarshi kawai ya dauka da maqullin dakin nasu ya fice da hanzari ya rufe qofar.


Ajiyar zuciya ta saki bayan ficewar tasa,wanne irin mutum ke shi da bai hutawa rayuwarshi?,baki daya ko minti goma cikakke basuyi da shigowa dakin ba amma har ya sake ficewa,ta yaya matarshi zata samu kulawar da take so?,Allah ma yaso ba soyayyarshi cikin ranta bare hakan ya baqanta mata,ta fada cikin zuciyarta tana daga kafadarta tare da yarfe hannaye.


Gefan tattausan gadon ta zauna tana duban dakin,falle daye ne dauke da makeken gado,sai kujera doguwa guda daya da qananu guda biyu ajiye daga can wani sashen daban,babbar ma'ajiyar zuba kayan sawa,madubi bedside da kuma qofar toilet,daki ne mai matuqar fadi da yalwa,ta dauki lokaci zaune har sai data duba taga lokacin sallar azahar yayi sannan ta miqe ta shiga toilet din kasancewar dazu da asuba ta samu tsarki,bandaki ne mai tsari,komai neat yake,ko ina qamshi ya kama,qamshin duka abinda yake mu'amala da shi,kama daga turare sabulu turaren gashi da sauransu,sai data kammala sallar sannan ta janyo kayanta ta fiddosu daya bayan daya ta fara jerawa ganin cewa babu abinda zata yi,akwai makekiyar t.v plasma dakin saidai batayi sha'awar kunnawa ba bare ta debe mata kewa,bayan ta gama jera nata ta janyo nashi,ta zuge a hankali,a jere kayan suke gwanin sha'awa suna fidda qamshi mai sanyi,haka ta dinga fitar da su tana jerawa daga daya side din a tsare,komai ta sanyashi a muhallinsa sannan ta sanya jakankunan nasu a wani bangare daban na sif din,zuwa lokacin sallar la'asar yayi,ta soma jin yunwa,saidai babu komai a dakin na ci,hatta freezer dake dakin babu komai ciki,idan zaiyi tafiya yakansa ma'aikatan su kwashe duk wani abu dake cikin freezer din,alwala ta sake daurawa ta dawo ta gabatar da sallar la'asar din,sai ta kwanta lamo saman abun sallah yunwa na nuqurqusarta,dama bata karya ba suka fito,haka cikin jirgi babu abinda taci saboda bacci da ya dauketa.



Wasa wasa a wanni suka shiga shudewa,duhu ya fara sako kai,lokacin magariba yayi,a daddafe ta tashi tayi sallar magariba ta dawo ta kwanta,a haka akayi isha'i,zuwa sannan ta fara raina kanta,tuni ta fara fidda ruwan hawaye,tunanin da gayya al mustapha yayi mata haka ya cika zuciyarta,tana daga kwancan amma jiri take ji saboda tsabagen yunwa,ta dinga share hawaye tana juyi saman abun sallah,tuni idanunta suka sauya launi saboda kuka da yunwa.


Tunda ya fita wunin baki daya bai zauna ba,gagarumar matsala ce ta taso cikin companyn tsakanin qananun ma'aikata ta qabilanci,wanda hakan har ya kai kunnen hukumar qasar,tun jiya abun ya faru amma ba'a sanar masa ba sai yau yana sauka qasar,kasancewar akwai jinsin daban daban kuma 'yan qasa kala kala dake aiki qarqashin company,tunda ya fita banda coffee cup biyu babu abinda ya sanyawa cikinsa,shaf har ga Allah ya manta da ita baki daya,har sai da aka idar da sallar magariba cikin masallacin dake cikin kamfanin,yana tsaka da azkar ya tuna,katsewa yayi cikin hanzari ya soma lalubar wayarshi,sai ya tadda ya barota a office,cikin hanzari da sassarfa ya miqe ya nufi office din,inda yake rataye keys yaga key din dakin,sai a sannan ya tuna da rufeta ma yayi,hakan ya sanya babu shiri ya kira P.A dinshi yace ya sallami kowa sai gobe zasu qarasa zaman,yayi kiran drivansa yace su hadu a parking space.


A gaggauce suka tsaya wani gun saida abinci da bashi da tazara da kamfaninsa inda anan yake order din abincinsa yayi musu takeaway,sunyi mamakin ganinsa saboda kiransu yake kawai su kai masa yau sai gashi da kanshi,bazai iya jira bane kawai shi yasa yayi hakan,abinda ya saba ci da dare tayi order,ita din baisan me take so ba sabida haka kawai ya saimata abinda yaga amira tafici idan tafiya irin wannan ta kama,tafiyar minti arba'in cif tsakanin companyn da hotel din suka isa,ficewa yayi daga motar dauke da kayan yana bashi umarni cikin harshen nasara kasancewar dan india ne ya gyara parking din motar ya bada key din a reception.


Tana daga kwancen taji ana yunqurin bude qofar,sai ta sake tsurewa ta zaro ido tana duban bakin qofar,a nutse ya turo qofar ya shigo kana ya maidata ya rufe,a kanta idanunshi suka fara sauka,sai ya tako a hankali zuwa inda take kwance wanda tuni ta runtse idonta da hawaye ya jiqe zara zaran gashin idonta,durqusawa yayi ya gabanta yana sauke ledojin tare da cewa
"Na manta da ke ne,tashi ga abinci kici" haushi ya qumeta,ya manta da itama kenan tsahon awanni sabida rainin wayo,sai ya miqe bayan ya gama bude mata ledojin yana cire suit din sama
"Wannan amanar da kace zaka riqe ce?" Ta furta cikin subutar baki muryarta na rawa,batasan zai fito ba maganar,abinda ke zuciyarta ne kawai,cak ya tsaya da abinda yake,ya sake takowa a hankali bayan ya janyo wata kujera mai siffar zero wadda jikinta baki daya cushion ce katifa ce baga da nauyi ya ajjiye gabanta
"Am so sorry" ya furta yana janyo ledojin gabanshi,da mamaki ta daga idanunta ta dubeshi,batayi zaton jin kalmar daga bakinsa ba,bai dubeta ba ya fito da soyayyar shinkafa da gasashshiyar kaza,bayan ya ajiye robar fresh milk data tataccen ruwan inibi,kusan wadan nan sune abun shansa,cikin park din akwai wani dan plate na qarau mara qwari,a kai ya juye mata ya sanya cokali sannan ya daga kai ya dubeta
"Tashi kici" tazarar sakan uku kafin ta miqe cikin rashin cikakken kuzari tana goge qwalla,idonsa ya dauke daga kanta,ya tsani kuka,musamman wannan kukan da yake jin shi ya zalunceta,baison zalunci shi yasa yake jin kukan har ranshi,kaman fushin baba zai sauka a kansa haka yake ji,can qasa bayan ya kauda kansa wani sashe yace
"Stop crying" bata amsa ba illa jan plate din data yi ta soma tsakuran abincin,baifi loma biyar ta kai cikinta ba taji cikinta ya dunqule waje guda,take ta soma yunqurin amai,almustapha dake gaban t.v ya waiwayo yana dubanta,kafin yace wani abu tuni ta fara kelaya aman,a gaggauce ya qaraso ya tsaya kanta,baisan ya akeyi ba,baisan me ake cewa ba,sai data gama tsaf sannan ya miqa mata ruwa ta kuskure bakinta,ta rasa inda zata zuba yace
"Zuba anan" yana danna waya,jikinta ta janye gefe tana maida numfashin wahala,magana yayi a recption,cikin qanqanin lokaci saiga leburori,ya matsa musu yana tsaye harde da hannaunshi a qirji har suka kammala gayarawa,jifa jifa yana dora idanunshi a kanta,suna yunqurin ficewa wani ma'aikacin ya sake shigowa da butar shayi da qananun cups,sai da suka fice ya maida qofar ya rufe sannan ya nufi inda butar shayin take,ya tsiyaya cikin daya daga cikin kofunan ya qarasa inda take ya miqa mata
"Karbi" ya fada a taqaice,hannunta na rawa ta amsa sai ya bita da kallo,sai da yaga ta shanye baki daya sannan ya miqe ya shige toilet.


Tsahon awa guda sannan ya fito daure da rigar towel wanda da kadan ta zarta gwiwarsa,hakan ya sanya kwantacciyar gargasarsa data sha ruwa kwanciya luf,idanu suka hada sanda yake fitowa,ta dauke idanunta da sauri ta maida idonta ta rufe,tana jin yadda ruwan dumin ke warware hanjinta,gun jakar kayansa ya nufa sai yaji babu komai ciki,hakan ya sanya y nufi drower din ya bude,cikin mamakin yadda kayan ke jere a tsare yake kallonsu,kadan ya waiwaya yana son satar kallonta sanda ransa ya raya masa ita ta gyara,tunda dakin na rufe bare yace wani ne yayi,kayansa ya diba ya koma toilet ya saka sannan ya fito,pyjamas ne na maza me v.neck wanda igiya ce ke daure da su,wani sashi na gashin dake cike a qirjinsa kwance luf ya bayyana,dogon wando ne da ita sai takalmi slippers a qafarsa,gun ya sake dawowa ya janyo abincin ya miqa mata,da idanu ya mata nuni data ci,fuska ta soma yamutsewa tana tsoron kada ya sake dawowa,kafeta yayi da idanu wanda hakan ya tilastata yin yadda yake so din,baki daya cin abincin kawai take saboda yadda ya rutsata da idanunshi yana bibiyar motsinta,qarar wayarshi ce kawai ta ceceta,miqewa yayi daga gun ya koma gefan gado bayan ya dauki tashi ledar ya janyo center table ya dora,baki daya abincin daren nasa chips ne da hadin salad kamar ko yaushe da ruwan inibi,sai fresh milk wadda ya jima bai shata ba saboda wasu dalilai,baya kuma sha din sai ya tabbatar bai da matsala,sai da ya zauna sosai sannan ya fara amsa wayar.



Ya jima yana wayar wanda har batasan sanda ya kammala ba sakamakon gyangyadi data soma a wajen data gama cin abincin saboda wata mutuwar jiki da kasala data rufeta,wutar dakin na akashe sai hasken wasu qwayayen bacci guda biyu masu duhu,jikinta ya bata yayi bacci saboda haka ta miqe ta kunna haske wayarta ta fidda doguwar rigar baccinta wadda keda santsi,silk ce sosai mai bin jiki ta wuce bandaki,cikin sanda take takawa don kada ya motsa har ta shiga,saidai abinda bata sani ba idanunshi biyu,hakanan yana iya ganintar tar sakamakon ya jima cikin duhun dakin shi yasa bai ganin duhun sosai,so yaje yayi bacci amma abun ya gagareshi,dalilin da yasa baya shan irin wadan nan abubuwa kenan,duk sonshi da fresh milk da yoghourt ya haqura da su don ya zauna lafiya,yana son kunun aya matuqa haka shima ya ajjiye shi gefe,koda yaje gida ya tadda ummee tayi saidai yace baisha,acan ta wanke hannunta,sannan tayi brush ta sauya kaya sannan ta fito.


A hankali ta ja qofar toilet din ta rufe,idanunshi suka sauka a kanta,haske pink din rigan baccin na yawo cikin dakin,binta yaci gaba da yi da idanu har ta qarasa bakin mudubi ta dauki turarenta ta mutsetsike jikinta duk idanunshi na biye da ita,take qamshin humrar ya karade dakin ya isa har inda yaje kwance,bai san mai yaje sake jansa ga kallonta ba har ta kai saman doguwar kujerar ta haye tana karanta addu'o'i tana shafe jikinta da su,bayan ta yane jikinta da mayafi ta kwanta tana rufe idonta,baki daya abincin data ci ya sanya mata mutuwar jiki,bacci kawai take da buqatar yi.


Sai a sannan ya dauke idanunshi yana sauke numfashi hadi da ambatar sunan Allah,wani irin juyi yayi ya sauya yanayin kwanciyarsa idanunsa a rufe yana son tilastawa kansa yayi bacci,saidai yasan yaci qarya,ba kasafai a irin wannan yanayin yake iya bacci ba,yayi juyi yafi sau arba'in,take ya soma ganin baiken kansa,mai ya kaishi shan abunda yasan zai zame masa damuwa,sannan ya bige da kallon abinda baiji cikin ranshi har yanzun nashi ne,a qalla ya kwashe kusan awanni biyu a haka kafin ya fara samun sassauci,gumin da yaji yana yi shi ya tabbatar masa da komai yazo qarshe,kimanin minti talatin sannan ya miqe ya kunna qwan dakin ya shige bandaki.


Fitsari ne ya farkar da ita,ganin saman gadon wayam ba kowa ya sannan ga motsin ruwa a bandaki ya sanyata zaman jiran fitowarsa,minti biyar tsakani ya turo qofar ya fito daure da towel jikinsa jiqe da ruwa,baiyi tsammanin farkawarta ba,dauke kai yayi cikin dakewa da daure fuska tamkar ita ta kar zomon ya bude ma'ajiyar kaya,yayin da ta miqe wuf ta fada bandaki saboda wani nauyi da kunya da suka lullubeta,ganinshi a haka yayi matuqar yi mata tsauri,bata fito ba sai data bada tazarar minti goma sannan,saman abun sallah ta ganshi yana salla,da sauri ta koma saman kujerar ta qudundune bayan ta duba agogo ta tabbatar tsakiyar dare ne,ya bata aqalla awa daya kafin ya koma saman gadon ya kwanta bakinsa dauke da tasbihi a haka bacci ya daukeshi.











*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



8⃣1⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis,aslih li sha'any kullahu,wala takilni ila nafsy darfata aynin*
___________________________________




Qarfe takwas na safe ta farka bayan baccin data koma bayan ta kammala sallar asuba,babu kowa a dakin sai ita daya,alamu sun nuna ma ya fita,gefe daya ta tarar da kayan break fast,komai da komai irin wanda zata iya ci,toilet ta shiga tayi wanka ta dawo ta gyara dakin sannan ta sanya kayan taja kayan ta karya,kwanciya ta sake yi bayan ta gama,ba dadewa wani baccin yayi awon gaba da ita,bata farka ba sai data ji ana knocking qofar,ta miqe ta isa ga qofar,ga mamakinta a bude take muqullin ma na jiki yau bai rufe ba kenan.


Matashiya ce sanye da kayan ma'aikatan hotel din,cikin murmushi ta dubi sumayya ta gaidata da harshen larabci cikin kokwanto,don bata da tabbacin zata ji,murmushi ta saki tana mamakin jin larabci mai kyau a bakin matar,tasan yawanci larabcinsu ba irin wanda ake mana amakarantu bane ta maida mata,sai ta sake fadada murmushinta ganin cewa tana jin yaren,ta miqa mata wani abu a nade da wata leda mai qyalli tana shaida mata abincin ranarta ne,sannan ta nuna mata tarin lemuka da ruwa tace idan ba damuwa zata sanya mata a fridge,matsa mata tayi tana fadin
"La ba'as,tafaddal" ta koma ciki ta biyota,tana tsaye ta gama shirya komai sannan ta maida qofar ta rufe bayan tayi mata godiya,sai data fara sallar azahar sannan ta bude,gasashshiyar kaza ce da soyayyar taliya sai hadin coleslow,ba wani da gawa taci ba ta rufe kasancewar bata jin yunwa.


Kusan haka ta wuni ba cas ba as,har kwanciyar ma ta isheta,ita ba sanin kan hotel din tayi ba ballantana ta fita,sai daga bisani ne ma ta koma bakin window din dakin tayi zamanta kasancewar tana ganin mutanen dake kai komo ta nan.



Kusan haka zaman nasu ya kasance har kusan kwanaki goma,da safe zata tadda ya fita amma ga breakfast dinta,da rana wannan matar zata kawo mata lunch,da yammaci ta dawo ta tambayeta koda wani abun,sai kuma na dare zata sake kawo mata shima,sau tari kafin ya dawi tayi bacci,sai haduwa tayi wuya a tsakaninsu idan ba da asubahi ba,sai data ta farka taga an fidda abincin da bata cinye ba a ajjiye mata wani,abinda ta fuskanta shine shi din mutum ne wanda bai san dadin jikinsa ba,mutum ne da ya baiwa sana'a da business muhimmanci mai tsoka cikin rayuwarsa,bashi da wani lokaci sai na kasuwancinsa,bugu da qari kuma ta lura da yadda matsalan kamfanin ta sanyashi a gaba,sam ba haka rayuwarsa ya kamata ta kasance ba,ya qare qarfinsa wajen kasuwanci ba kawai,tana ganin hakan bai dace ba,ita kanta ta soma qosawa da zaman garin,don baki daya bata ga wani amfani da zamanta ke da shi ba,tunda bata ganin wanda take zaunen saboda shi,saidai kullum taci ta sha ta kwanta,hakanne ya sanya yau ta qudurce ba zata yi bacci ba har sai ya dawo,tanas son tayi waya da 'yan gida,mama,malam abdallanta,zainab da

Please Login or Register in order to submit comment