Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sha'awa,kamar yadda garin yayi dadi,iska mai dadi mai cakude da qamshin qasa na kadawa,sai ta dinga jin wani mishadi na shigarta,tana shaqar iskar tana mata dadi har cikin qirjinta,ta dinga takawa a hankali har zuwa tsakiyar harabar gidan,su biyu ta fara hangowa tsaye da alama magana suke kamar rannan,mahmoud din kawai ta iya ganewa saboda shike fuskantar qofar shigowar,kamar wancan karon dai dayan na fuskantar mahmoud sai bayansa kawai ta iya hangowa,yana sanye da jallabiya ta maza fara sol da silifas farare a qafarsa,hannunshi riqe da dadduma,tana gab da isa garesu ya juya ya shige ta wata qofa da zata iya sadashi da waje,yayin da mahmoud har ya juya sai ya hangeta,tsayawa yayi yana murmushi har ta qaraso,hanmunsa ya miqa zai amshi flask din hannunta yana fadin
"Bisa alamu abincin baabaa ne" murmushin itama tayi tana miqa masa
"Eh shine"
"Masha Allah,a gaida umman khalipha" sai ya dubi drivan yana miqa masa hannunshi alamar ya bashi ,rusunawa yayi cikin girmamawa ya miqa masan sannan ya juya zuwa qofar fitan,dubanta yayi
"Muje nayi sauri na rakaki kada liman ya tada salla na rasa wata raka'ar,don na tabbata ya isa masallaci saura minti biyar a tayar" dan baya ta ja kadan
"Ai ba sai na shiga ba ma,ina cewa ma duka masu gidan basa nan,ka kaima baaban kawai kace ina gaidashi" murmushi yayi
"Kamar ya sanki,na tabbata baki taba zuwa kin gaidashi ba,sannan ko ba kowa a gidan su anty farida da sauran yara na nan" murmushi ta sake yi
"Zanzo na gida baabaa in sha Allah,su anty farida kuwa ka gaishesu na tabbata suma basu sanni ba,amma kace ina gaishesu,nima sallah zanje nayi"
"Is ok,ki yiwa umman khaliphan sannu"
"Zata ji" ta fada tana juyawa a hankali ta fice daga gidan.

      Tana shiga ta isarwa anty dije saqon,sannan ta shige dakinta,da hanzari ta tada isha jin an fara kiran sallar tarawih don sun gama isharsu,cak ta tsaya lokacin da limamin ya fara karanta fatiha,daina aiki qwaqwalwarta tayi na wucin gadi,babu abinda kunnuwanta ke ji sai karatun dake fitowa daga lasifiqar yana karade unguwar kasancewar masallacin na daura sa su ne,muryar da bazata iya mancewa da ita ba komai tsawon zamani,komai sauyawar yanayi,komai dadi komai wuya,muryar MUKHTAR dinta take ji tana karade kunnuwanta,wani irin faduwa gabanta ya dinga yi har ya haifarwa da gabban jikinta yin sanyi,tana so ta zauna amma ta kasa,jin kunnuwanta take kamar zasu zaunce,hannunta ta sanya ta toshe kunnen nata ko zata daina jin amsa kuwwar karatun amma hakan ya gagara,kanta ta shiga girgizawa
"A'ah,ba mukhtar bane,wanda ya mutu baya dawowa" ta fada tana ci gaba da girgiza kanta hawaye na shirin soma sauko mata,a sukwane ta juya ta fito zuwa falon gidan ba tare da tasan me zata aiwatar ba.







*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

5⃣9⃣


*Bismillahir rahmanir rahim*

*KO KUNSAN RANAR QIYAMA ANA DAURE DAN WUTA DA SARQA MAI TSAHON ZIRA'I SAB'IN KAFIN A JASHI ZUWA JAHANNAMA*

*Astagfirullah wa'atubu ilaih*

___________________________________

     Birki ta ja a falon zuciyarta na wata iriyar bugawa,idanu ta shiga rarrabawa qwaqwalwarta ta daure tamau,muryar na ci gaba da ratsa kunnuwanta cikin daddadan sautin karatun mai qunshe da muryar mukhtar,me zata aikata?,abinda ta kasa baiwa kanta amsa kenan
"Ya mukhtar,ya mukhtar" ta soma fada hawaye na zubo mata,shigowar laila a guje wadda fitsari ya korota daga wajen sallar ya dawo da ita hayyacinta,bata jirayi qarasowar lailan ba ta isa gareta ta riqe kafadarta
"Laila,wake karatun sallah a masallaci?,mukhtar ne?"dariya ta saki tana kallonta tare da yin tsalle alamar fitsarin ya matseta
"A'ah,yaya ne fa,duk azumi shi yake jan sallah" ta fada tana zillewa ta ruga bandaki,sam bata fuskanci bayanin laila ban ta ji anty dije na cewa
"Shike limanci fa,nan da goman qarshe zai tafi a saudiyya yake sallah sai dai malam usman ya qarasa" firgigit tayi tana duban anty dije,sai ta kada kai kawai ta juya jiki a sanyaye zuwa cikin dakin nata ba tare da ta furta komai ba,zama tayi bakin gado tana jingina da jikin gadon,tamkar wadda aka zarewa laka,ta kasa kowanne irin tunani,muryar ce kawai ke ratsa dodon kunnenta tana mata shawagi,runtse idanunta tayi ta koma ta kwanta a gefan hannun damanta,wani abu take ji yana yana zagaya kanta kamar ana yamutsa qwaqwalwarta,haka hawaye yaci gaba da tsiyaya ta gefan idanuwanta.

        Sallar da bata iya yiba kenan har aka kammala sallar laila ta shigo kiranta tazo suci abinci,can qasa ta amsa mata data qoshi sai anjima zata ci,haka taci gaba da kwanciya,tana ganin tarin misscalled din abdur rahman amma ta kasa dagawa har ya gaji ya bar kiran ya turo mata texs,baccin dole ne ya dauketa,bata wani jima ba ta farka,har a lokacin tana jin wata iriyar damuwa na ratsata,sallar isha'in da bata yiba tayi,sannan tayi tarawih din raka'a bakwai har da wutiri.

  *******   ******   *******

       Daga ranar karatun shi ya zame mata abun sauraronta daga sallar isha'i har a kammala,sosai karatun da muryar ke debe mata kewa ya sanyata nutsuwa,wani lokaci tana ji tana hawaye don ba qaramin tuna mata mukhtar yake yi ba,babu wanda yasan halin da take ciki sai ita kadaj,kawai dai anty dije taga ta rage walwala,bata kawo komai ba ta dauka ibadar da ake ciki ne.

       A haka aka kammala azumi ashirin cif,ranar ashirin da daya sai taji ba waccan muryar bace,duk sai taji ta damu,ji take kamar ta fita ta gano me ya kawo wannan sauyin,daga bisani ta tuna anty dije ta gaya mata goman farko da na tsakiya kawai yake jan sallah,to wannan wane ne?,babu shakka ba don anty dije ta sanshi ba babu abinda zai hana tace mukhtar dinta ne,baki daya sai ta jita sukuku,ba qaramin dadin jin muryar take ba,a ranar uncle farouq ya shigo musu da kayan sallarsu,kowannensu kala shuda shida a dinke,sumayya laila da anty dije kam harda mayafai takalma da jakankuna,daga mayafin kawai sumayyan tayi ta ajjiye gefe,tun mutuwar mukhtar ta sake qanqame hijabi duk da cewa dama al'adarta ne sanyashi,sai dai a baya tana sanya mayafan lokaci lokaci,anty dije ta lura sai ta bada sautun yadin hijabai masu kyau aka yi mata irin wadanda take so,anty dijen ita ta sanya kudinsu ta saya musu dan kunnaye da awarwaro da sarqa fashion designers masu kyau kala uku uku.

         Washe gari akayo aike daga gidan baabaa prof,duk da cewa a jiya ya daga saudiyya shima zasu dawo tare da iyalansa a ranar sallah,a qasarsa yake nashi bikin sallah saboda ziyara da ake kawo masa tako ina,abokai 'ya'ya jikoki 'yan uwa da abokan arziqi,daya daga cikin ma'aikatan gidan ne,sanye da unifoarm dinsu,a mutunce ta gaida anty dijen sannan ta miqa mata wata qatuwar baqar leda dake dauke da tambarin wani company dake dubai,company ne da yaje mallakin daya daga cikin iyalin baabaa prof din,shahara da daukakar company din ya sanya wasu suma saka jarinsu a ciki
"Kiyi haquri umman khalipha,tun jiya baabaa ya bada saqon,sai yau na samu sauqin aiki,munata ayyuka ne"
"Babu komai shema'u,baabaa dai kam bai gajiya,Allah yasa a gama lafiya" murmushi tayi
"Baabaa badai alkhairi ba,ko mu bai mana mu kadai har 'yan uwa na kusa alherinsa bai barsu ba,ina zaton wannan karon har baquwarki da nata kayan,naji kamar ita taiwa baabaan abincin kwana ashirin ko?" Dariya anty dije tayi
"Sumayya,eh itace"
"Ai baabaa na jin dadin abincin nan kam qwarai,rannan har yasa a kira ta su gaisa sai yayi baqi kuma ya sha'afa"
"Allah sarki,ai idan suka dawo da kaina zan tura ta ta gaidashi,Allah ya saka masa da alheri,yaci gaba da shirya masa zuria"
"Amin ya Allah"
Shema'u ta fada tana ficewa.

       Juya ledar anty dije tayi tana murushi,tambarin kamfanin kadai data gani tasan ba kaya bane masu qananun kudi,bude ledar tayi ta fara zarosu,diguwar riga ce irinta mata mai bala'in kyau da tsari wadda aka zauna aka yiwa aikin duwatsu daga sama har qasa,iya dutsen kadai idan ka kalla kasan ba qaramin kudi zaka sanya ba kafin ka mallakesu,yadin kansa abin kallo ne bare dutsen,guda daya baqa ce,sai dayar fara ce qal da aka yiwa aikin baqaqen duwatsu,dayar kuma ruwan jinin kare ja ba dau ba ya dan rusuna amma baikai duhun maroon ba,tana duba size din rigar ta gane sune na sumayya,kowacce akwai vail da ya dace da ita,murmushi tayi don tasan aikin amira ne wannan,wani shegen fashion mai zubin gwal guda daya da banguls dinsa,haka na lailaa suke saidai banbancin tsaho da kala,tasan laila kam za'a sha murna,duk shekara ya saba haka yake musu,duk cikin kayan sallarta tafi ji da kayan gidan baabaa prof,mazan ma baki dayansu jallabiua ce irinta maza mai tsada,sai gezna wadda kana mata kallon farko itama kasan ansha kudi kala bibbiyu duka kalolin iri daya,sanda aka kawo su sumayya basanan sun tafi wankin kai,da suka dawo baki sumayya ta saki,zata iya cewa banda lace din da aka bata taba kaya masu tsada haka ba,ko lace din ta tabbata baikai kudin wadan nan ba,yana ajjiye ma bata dinkashi ba,godiya tayi sosai kamar suna wajen tare da yaba dimbin karamcin ahalin gidan.

      Cikin ranakun goman qarashen so kadan bata yi sanya wajen zabga addu'a gareta da d'anta da sauran yaran musulmi ba da al'umma ba,musamman ranakun da suke mara,wato ranakun da ake tsammacin dare lailatul qadr,tayi addu'ar samun kyakkyawar rayuwa da kuma kyakkyawar QADDARA,sai ta dinga jin nutsuwa da kwanciyar hankali,tsoro da damuwarta suka dinga raguwa a hankali.

        Ran ashirin da tara ga wata aka tabbatar da ganin watan sallah waahegari idin qaramar sallah kenan,a gajiye ranar suke don wuni sukayi gidan qunshi,da cewa sumayyan tayi ma bata yi,anty dije ce ta matsanta mata tilas ta bisu,ga wainar shinkafa da ta tsara zata yi musu a ranar sallah,Allah ya taimaka kafin ta kwanta tayi miyarta,zumudin zuwan sallar take sosai wannan karon,saboda uncle farouq yace sallah da kwana biyar zasu tafi kano,a qalla zasuyi sati guda sannan su dawo su fara shirin tafiya london.

*******   ******    *********

        Qarfe goma na safe tuni an sakko daga sallah,zuwa lokacim sumayya ta kammala aikinta,wankanta tayi ta shirya cikin daya daga cikin dinkin da abban laila ya musu,ba wani makeup tayi ba amma kayan sun mata kyau,rabon abincin sallah anty dijen tayi kamar yadda ta saba.

       Da yammaci su laila da khalipha nata hada barka da sallah sabbin kudi baki yaqi rufuwa,sai shigowa suke suna bawa sumayya labari su wance sunzo gidan baabaa su wane sunzo,itakam kusan bata sansu ba saidai tace musu to,dariya anty dije tayi
"Abokansu ne jikokin baabaa prof, 'ya'yan babban dansa da me bi masa,kinsan duk wani da nashi da jika dake nesa a gida yake sallah". Abban lailan nata baqi,wasu na zuwa wasu na tafiya kusan haka suka wuni.

        Wajen biyar tana sama dakin anty dije tana gyara mata,saboda yau baki daya ta kasa zama saboda baqi,hayaniya ta dinga jiyowa da qarar motoci,sau ta miqe a hankali,ta yaye labule tare da bude qofar da zata sadaka da balcony din anty dije dake saman,bata fiya budeshi ba sai lokacin zafi ko kuma idan ta kama saboda idan ka fita kana iya hango jama'an waje suma suna iya ganinka musamman da yake yana center din tafkeken get din shiga gidan su amira,duk da cewa waccar babbar qofar da akafi shiga  wadda jami'an tsaro ke gadinta tana daya daya layin nasu,wannan a nan suka fi harkokinsu.

      Motocine na alfarma qirar zamani,wanda ke dauke da lamba mai tambarin sunan baabaa prof,wanda hakan ke alamta mallaki ne na ahalinsa,kimanin mota shida kowacce na qoqarin shiga gidan ba tare da wata ta gogi wata ba,sai da suka kammala shiga baki daya sannan wadanda suka wangame get din suka rufe shi,ajiyar zuciya ta saki sannan ta juya ta koma cikin dakin wanda hakan yayi dai dai da shigowar anty dije
"Kai,har kin gama?" Tana duba yadda ta gyara kayan
"Na gama anty" inji sumayya tana dan kashingidewa
"Kinga yanzun abban laila ke gayan su baabaa sun dawo,amma dai wannan karon zaki ki masa sannu da zuwa ko ku gaisa"dan murmushi ta saki yana yamutsa fuska
"Eh anty,amma dai ba yanzu ba ko?"
"Nima ai bance yanzu ba,kinji an ambaci maqiyinki shiga gidan baabaa ko?" Dariya ta tuntsire da ita har tana kwanciya ganin irin yadda antyn tayi maganar.

  *****  ********    ******

    Washe gari da yammaci hudu da ashirin bayan ta gama yima anty dijen komai,sai ta shirya cikin wasu kayan nata,swiss ne mai asalin tsadar wanda aka tsara mata dinki na riga da skert,babu kwalliya a fuskarta kamar ko yaushe tun bayan rashin mukhtar cikin rayuwarta illa hoda jagira da liptsic,sabon hijabinta mai hannu wannan karon iya gwiwarta ta zura wanda yayi marching da lace din jikinta,tayi kyau sosai kayan sun haska ta,tun dazun take laqai laqai na zuwa gaida baaban,hakan ne yasa ma ta tsiri yi masa dambun zallar tsokar kaza.

       Anty dijen ita ta sake turo qofar dakin karo na biyu tun bayan shigarta wanka
"Baki gama bane har yanzu?"
"Na gama anty" ta fada tana fesa turare
"To,saidai fa ki shiga ke daya kya tadda lailan acan,don duka suna can gidan,ta kasa jiranki,don naji tana kamar zasu park ne"
"To" ta fada badon ranta ya so ba,takalmi ta zura mara tsahon dunduniya sannan ta fito.

        Daga qofar gidan baka gane gidan na qunshe da baqi ba sai ka kai ga shiga harabar gidan,yara ne da 'yammata kala kala,wadanda kana duban yanayin shigarsu zaka tabbatar da cewa lallai boko ya ratsasu,wayewa da kuma sanin kam duniya,kamar yadda group group ya rabu haka kowacce da irin tata shigar,ta wannan tana wace wance,nan da can zaka ga mutum biyu uku har hudu ma a tsaitsaye,kowa na sabgar gabansa saboda wadatar guri da kujerun zama a ko ina,wanda suke nuna lokaci irin wannan ake fiddo su ayi amfani da su.

       Sai taso ta rude baki daya,ta dinga takawa a hankali tana tunanin inda zata shiga
"Muje na rakaki,naga alamar ko yaushe tsoron shigowa gidan nan kike,ko wani ne zaya kamaki?" Taji an ambata daga gefanta,waiwayawa tayi a hankali,mahmoud ne,yayi adonshi cikin shadda ruwan sea blue,ta masa kyau sosai ta fidda ainihin surarsa,murmushi ya subuce mata,sai ta girgiza kai kawai tana gaidashi,ya amsa mata suka fara takawa zuwa ciki
"Naga kowa tun daga ranar sallah da muka dawo zuwa yau,amma ke kam ban ganki ba,su laila tun dazu suna gidan nan,zaman gida bai damunki ne?" Murmushi ta sake saki tana kada kai
"To ina zanje,ba wanda na sani"
"Nan fa,nan ma gidanku ne,ko bakiga yadda su laila suka maidashi gidansu ba?"
"Haka ne" ta amsa masa don batasan me zata ce ba,shima shirun yayi suka ci gaba da takawa,suna gab da shiga bangaren anty maamaa yace
"Dama dai wani abun dadi kika kawowa baba,yau a gunsa zan maqale,kinsan ni da yaa man bamu cin abinci idan akayi buda baki har sai an kawo na gidan umman khalipha,yace shikam bai gane mana wannan wayon namu ba da muke maqale masa a kwanon,har gwara ni gauro ne shifa yaayaa fa" dariya ya bata har sai data murmusa,ta fuskanci mahmoud irin mutanen nan me masu barkwanci faran faran da saurin sabo da mutane.

        A falon anty maamaan suka ci burki,wasu 'yammata ne zaune a falon biyu na saman kujera biyu na qasa,kowacce ta baje kayan kwalliya suna makeup,baki daya sun cika falon da hira da karadi,kayan sawarsu na aje gefe da alamu fita zasuyi wata unguwa,kana dubansu zakasan suna daga cikin baqin da gidan ke karba a irin wannan lokaci,sallamar mahmoud ita ta janyo hankalinsu
"Anty maamaa" kawai ya fadi,daya daga cikinsu wadda ke qoqarin daura dankwalinta tace
"Tana G-kitchen" juyawa yayi ya dubi sumayya
"Idan baki gaji ba muje bata cikin nan" bata ce komai ba tabi bayansa yayin da 'yammatan suka bishi da kallo,wadda ke daura dankwalince ta tabe baki,kishi ne fal bayya ne a fuskarta,ta kusa da ita ce ta zungurota ganin yadda take binsu da kallo
"Uhmmm,yadai?" Qaramin tsaki ta ja
"Nikam baisan me yasa Allah ya zubawa mazan gidan nan girman kai ba,suna jin kamar su kadai ne halittar maza da Allah ya qirqira a ban qasa,jibi,kamar baisan wace ni ba" dariya wadda ke shafa powder ta qyalqyale da ita sannan ta tsaya da abinda take yi
"Kema kinsan su isa sun kai suyi girmankan,karfa ki manta su su waye?,kina zaton samunsu a bagas ne,nikam banga laifi ba don sunyi girman kai sun kai suyi ne,kibi a sannu idan da rabonki zaki shiga familyn prof,nikam tuni na sallama" ta fadi tana ci gaba da murza hodarta,shiru tayi bata sake cewa komai ba sai taci gaba da gyara daurin dankwalin nata cikin sanyin jiki.

      Bayan suka zagaya sai gasu cikin wani qaton kitchen wanda idan ba wajajen kayi ba ba lallai kasan da zamansa,kitchen ne babba mai dauke da electrics kala daban daban da manyan tukwane,kayan girki nau'i daban daban,kitchen ne da ma'aikatan gidan ke haduwa suyi amfani da shi duk lokacin bikin sallah irin wannan,biki ko suna na gidan idan ya tashi,gaidasu sumayyan tayi tare da yi musu sannu da aiki,antyn na tsaye sanye da jar shadda wadda keta maiqo da qyalli dinkin bubu da aka yiwa adon baqin zare,duk da ta tasamma shekara arba'in da kusan biyar amma sai ka zaci 'yar talatin ce,anty mama kam badai ado ba,tana sabe da wata kyakkyawar yarinya wadda aqalla zatayi shekara daya,an mata kwalliya cikin riga da wando,gashin kanta kuwa adin ribbom ne kala kala,ma'aikatan take sanarwa mai za'a dafa a mazaunin abincin dare a gidan baki daya
"Ah mahmoud yadai?,kun fasa tafiyar ne?" Ta fada bayan sun gama gaisawa da sumayya,shi kuma yana jan yarinyar dake kafadarta din da wasa wadda da alama itama jikar gidan ce,sumayyan na tsaye gefanta antyn riqe da hannunta daya
"A'ah,wannan mai tsoron shigowa gidan nan din na rako zata gaida baabaa" murmushi tayi ta juya tana kallon sumayya,haka nan sumayyan take burgeta tun ganin farko,da alamu zatayi nutsuwa,bata da rawar kai da fi'ili irin na 'yammatan zamani,shigarta kadai ta tabbatar mata da cewa daga babban gida ta fito,koda ba gidan da suke da kudi da ababen more rayuwa ba,a'ah,babban gida na nufin gidan mutunci da karamci,gidan da aka san dattako,gidan da usuli ilimi tarbiyya da wadatar zuci,gidan dake cike da tarbiyya da daraja
"Ba tsoro bane,baqunta ce" inji antyn tana murmushi,kusa da antyn ya matso bayan ya ajjye mata kwanon
"Nidai anty gashi nan,a tuna da ni idan baabaa zaici abinda ke cikin kwanon nan" hararsa tayi
"Haka fa,anqi aure anbi an takura mana miji,kunqi barinsa yayi auki,komai zaici sai kun tayashi" dariya ya sanya yana ficewa tare da fadin
"Wannan tsohon mijin naki anty ana ji da shi" itama dariyar tayi sabida tasan halin zolayar mahmoud,qarasa lissafa musu abinda ya dace tayi sannan ta dubi sumayya tace
"Bismillah" ta soma qoqarin tafiya tare da daukar kwanon,ganin haka ya sanya sumayyan matsawa kusa da antyn ta miqawa yarinyar hannu,zubawa sumayyan ido tayi tana kallonta,dariya anty tayi
"Wannan uwar qyuyar,Allah yasa ta yarda,uwarta na can ta tafi yawon saloon din da ba'a yishi ba sai yau ta barni da rigimamma" kamar taji kuwa abinda antyn tace sai ta miqawa sumayyan hannu alamar ta dauketa,ba antyn ba har masu aikin ta basu dariya,saboda kowa yasan qyuyarta ba da kowa take yarda ba
"Lallai kin ciri tuta mai sunan umma" ta kira sumayyan da haka saboda tuna sunan wace garesu,murmushi ta danyi tabi bayan antyn tana duban yarinyar,sai ta tuna mata abdallahnta,ko yanzu me yake?,tana kewarsa sosai,ta qagu lahadi tayi ta ganshi,sai kuma ta tuna yaranta wadanda ke tayata zama tun suna tsohon gidansu da mukhtar,su naana kam tasan yanzu sun girma,tana saka ran in sha Allah da zarar ta koma zata ziyarcesu,itakam tasan cewa son yara a jininta yake haka halittarta take,duk inda taga yaro ya dinga burgeta tana kallonsa kenan.


A hankali suke ratsa gidan anty maamaan na janta hira kadan kadan,jefi jefi suna gaisawa da mutane a kan hanya wanda da alama basu hadu bane tun safe sai yanzu,ba mamaki saboda girman gidan wanda ya iya hadiye duka baqin dake ciki,tun daga farkon sashen ta tabbatar da cewa akwai banbanci da sauran sasannin gidan,antyn dai na gaba tana bin bayanta,yarinyar na ci gaba da kallon sumayya tare da yi mata shirmen surutu irin na yaran dake son koyon magana ita kuwa na biye mata anty na binsu da murmushi har suka isa qofar da zata sadasu da babban falon dake mallakin mai gidan ne.





     






*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

6⃣0⃣


*Bismillahir rahmanir rahim*

*SHIN KO KUNSAN DUK LOKACIN DA AZABA TA TSANANTA GA DAN WUTA,FATAR JIKINSA TA KWASHE TA QONE,ANA SAUYA MASA WATA FATAR NE SANNAN ACI GABA DA GANA MASA AZABA*

*Allahumma la tada a lana zanban illa gafartah*

____________________________________

        Dattijo ne mai kimanin shekaru sittin da biyar zaune kan daya daga cikin kujeru na alfarma dake zagaye da falon,haiba kwarjini da kamala sun bayyana qarara kan fuskarsa,Allah yayi masa baiwar furfura tun daga gemu zuwa kansa,farin gilashi ke saye a fuskarsa baya ga shaddar dake jikinsa fala sol,dogon wando da riga mai gajeran hannu iya gwiwa,da alamu akwai babbar rigarsu wadda bai sanya ta ba,gefensa daga hannun dama samari ne guda uku,wanda ke daura da shi yana fuskantarsa sosai,bisa alamu magana suke mai muhimmanci,kyakkyawan matashine mai cike da kyau kwarjini izza da haiba,sanye yake da irin kayan tsohon bisa dukkan alamu anko sukayi,shi dinma fuskarsa sanye take da gilashin,daya hannun nashi ma wasu matasanne su biyu sai mata guda biyu.

     Tunda suka shigo falon gabanta ke mugun faduwa,sosai ta dinga qoqarin baiwa kanta qwarin gwiwa saboda haka sai ta sadda kanta qasa har suka qaraso cikin falon suna sallama,dattijon ne ya amsa da wasu daga cikin mazauna falon,idonsa na kan antyn da sumayya har suka qaraso,gefe ta samu ta zauna daga qasan carfet din,da sauri baabaa yace
"A'ah,tashi ki koma saman kujera mana" murmushi tayi kanta na qasa,ta soma gaidashi tare da yi masa sannu da zuwa,fuska sake tamkar ya santa ya amsa mata,anty ta dubeshi
"Nasan baka santa ba" sake dubanta yayi yana gyada kai
"Gaskiya kam,koda na santa to ta kwanta min,kinsan shekarun sun fara turawa sai a hankali" sauran dake zaune sukayi danyi dariya banda mutum daya da tun shigowarsu ya dauke kansa ya maida hankalinsa kacokam kan wayarsa yana tura saqonni,hakanan ransa yake a bace.
"Itace wadda ka dinga bamu labari ka kwashi girki na kwana ashirin ka dinga zabga santi" baki daya dariya suka kuma saki wanda hakan ya dan ja hankalinsa,har ya sanyashi daga kai ya mata kallo daya tak ya sake maidawa kan wayarsa yaci gaba da abinda yake
"Masha Allah,Allah yayi albarka,naji dadin abinci kam qwarai da gaske,Allah yayi albarka"
"Amin baabaa,na gode" ta fada cikin jin dadi bisa dabi'arta ta son na gaba da ita wanda take saka ran addu'arsa zata iya binsa ya sa mata albarka,hannu ya miqawa husna wadda ke hannun sumayya,ta kuwa lafe a jikinta tamkar ta santa,qememe taqi zuwa,sai ya zura hannunshi cikin aljihun rigarsa ya zaro alewa,kasancewarsa mai yawan kyauta,musamman a irin wannan lokaci da jikokinsa ke kasancewa a gidan tare da shi,hakan ya sanya baya rabo da alewa da sabbin kudi,miqa mata yayi take kuwa ta tafi gurin nasa,hannu yasa ya dagata yana dariya jama'ar falon na tayashi,tsaki ya ja qasa qasa yana miqewa,shikam bai san me yasa abun dariya bai yiwa su mu'azzam wuya ba,shi baki daya ma baiga abun dariya ba,yarinyar ma tunda ta shigo baki daya ma yaji ransa ya baci,musamman katse musu hanzarin da tayi kan muhimmin batun da suke tattaunawa,tun dazun dama yake addu'ar kada wani ya shigo saboda baison abinda zai katse masa bayanin da ya daukowa baban,ya san mutum ne shi mai mutunta baqo,kome yakeyi yana iya katsewa ya saurari baqonsa,sarai baaban ya ganshi amma sai ya qyaleshi,yasan halin kayansa sarai,da idanu ya rakashi har ya fice,ganin ya fita ya sanya sauran miqewa
"Baabaa kada fa ya tafi ya barmu"
"Jeku,don tsaf zai iya aikatawa,musamman da kun zo da tsarin da baiyi masa ba"dariya

Please Login or Register in order to submit comment