Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zura da gudu,dariya ta taso masa amma ya danneta,ta maidashi kamar wani dodo tun daga ranar da suka hada shimfida,baki daya bata iya masa wani cikakken kallo
"Yau zanga qarshen kunya" ya fada a ransa
"Zo nan" yace da ita
"Ni?" Ta tambaya tana raba idanu,kicin kicin yayi
"Da wa?" Miqewa tayi tana takawa a hankali har ta iso bayanshi ta tsaya,towel ya miqa mata cikin halin ko in kula
"Jikina zaki tsanemin" sakato tayi kamar zatayi kuka,baice uffan ba ya kafeta da ido,a sanyaye ta karbi towel din,cikin sanyin jiki,sai ta gaza motsawa tayi tsaye riqe da towel din
"Uhm,bismillah ina so na shafa mai ne fa"qwal qwal tayi da idanu sannan ta matso tana dauke idonta daga kallon jikinsa saboda yadda yayi mata kwarjini,bugu da qari sai tq zama wata 'yar cukul a gabanshi,sai da ya wanata,dariya a cikinsa kuwa kamar zata fito amma yana maidata,wanda a zahiri fuskarsa ba haka take ba sannan ya amshi towel din yana fadin
"ba abinda kika iya ma"baki ta tura cikin ranta tana qunquni
"Haka kawai dama mugunta ce tasa kace sai nayi,kai ko kunyar abinda ka aikata ma baka ji" bude jakarshi yayi ya fito da abayar ya miqa mata sannan ya zuba mata shanyayyun idanunshi.


Kuyi manage da wannan,ina da uziri,koda gobe baku jini ba kuyi haquri,idan kuma ya samu falillahil hamdi,na gode.








*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



8⃣4⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah madaukaki yana cewa*

*HAQIQA ABINDA AKE YI MUKU ALQAWARI/ALWASHI(NA ALQIYAMA)MAI ZUWA NE,KU BA MASU TSEREWA ALLAH NE BA*

Allah ka sanya farinciki a zukatanmu a wannan rana,ka sanyamu qarqashin inuwarka.
_____________________________________


*WANNAN SHAFI SADAUKARWA NE GAREKU,HAQIQA ALKHAIRINKU GARENI BAZAN MANTA BA*

*SISTER AINA'U(HUGUMA CONVERSATION)*

*TASH (INSPIRING STORIES GROUP)*








       Hannu biyu ta sanya ta karbi rigar tana kauda kai daga kallon da yake mata wanda sam bata sonshi,yana sanyata jin wani irin abu da nauyi cikin jikinta
"Inji hamza" ya fadi yana juyawa gaban madubi yana ci gaba da taje sumarshi hankali ta furta
"Na gode,Allah ya saka da alkhairi" bai amsa ba saici gaba da kallonta da yake ta cikin mudubi,bai tsammaci jin wata addu'a ko godiya daga bakinta ba,don hamzan yasha yiwa su'ad kyauta wanda ta ninninka haka saidai ta karba ayatsine,wani lokaci idan ta duba ma takance
"Shikam baisan me yasa bai iya kyauta ba,yana qarqashun mijina yana aiki yana cin arziqinsa ya rasa mai zai bani sai wannan?" Harara yake jifarta da ita almustaphan sannan yace
"Ki shiga hankalinki su'ad,hamza ba aiki yaje qarqashina ba kafada da kafada muke aiki,ba tilas sai ya miki kyauta ba don ba qasanki yake ba,ki gyara bakinki" hakan na mata ciwl,don ita a duniya ba abijda ta tsana irin a daidaita matsayinta dana wani,wanin ma dake gain kamar bai isa komai ba.

      Wayarshi ce ta fara tsuwwa,ga zatonshi ma umme ce zata ce ya hadata da sumayya,saboda haka bai ko dubaba ya daga yana karawa akunnensa,ya maqaleta a kafadarshi yana ci gaba da shafarshi,muryar su'ad ce cikin bacin rai da kwantar da murya cikin harashen nasara
"Ashe da gaske ne abinda akefadi idan namiji yayi aure wulaqantaki yake?,yanzu a haka kakeso na yarda na karbi kishiyar da ka yimin mu zauna tare?"shiru yayi tamkar bai kam layin har sai data kira sunanshi,kawai sai ta saki kuka harda sheshsheqa,cikin harshen hausa da son dawo da qauna cikin zuciyar wanda kuke magana tace
"almustapha kasan duk duniya babu wani abu da nake qauna sama da kai don me zaka yimin haka?"
"Look su'ad,wannan baki daya matsalarki ce ni ban da case da duka zantukanki,i think na gaya miki dukkan wani rules nawa ko?,so pls idan zaki iya bi bismillah,if not ki qyaleni na huta hakanan"
"Ni kake wulaqantawa haka maan?"cikin fushi yace
"if u dont like how things are,take control,decide how u ar going to change it,kada ki sake nema na daga yau,take me as iam,or leave me as iam"katse layin yayi ya jefa wayar gefanshi,cikin bacin rai yaci gaba da shiryawa sauri sauri,sumayya kam tunda taji ya ambaci su'ad ta miqe ta shige toilet,dama wanka take sonyi wanda yau bata samu tayi da wuri ba tun na safe da tayin.

         Cire wayar su'ad tayi daga kunnenta sanda ta fahimci ya katse kiran nata,duk da ba yau ne farau ba idan tazo masa da shirme amma wannan yayi matuqar baqanta mata,gani take kawai saboda ya sake aure ne ya sake qaro wulaqanci fiye da wanda ta sanshi da shi,hawaye na bin idanuwanta ta dubi mamanta,sannan ta dubi qanwar maman nata anty kubra dake zaune tana kallonta wadda ke zaune ita mijinta a south africa,ta zo ne american wajen yayarta ta tadda wannan cakwakiyar
"Ba sai kince komai ba naji komai,ai wallahi laifinki ne khaulat,ta yaya har zaki bari su'ad tayi wasa da damarta,kunfi kowa sanin samun damar auren irin su mustaphan sai wanda Allah ya zaba nan gidan duniya,tun tuni kallonku kawai nake,yarinya tana gantalinya da sunan karatu,karatun uwar me?,me zata ci da karatun?,me take nema da shi?,dame mijinta ya rageta?,bata taba tambayarsa abu komai yawansa yace mata babu ko bazai bayar ba saidai ma ya ninka mata,kuna zaton miji irin mustapha wanda Allah ya yuwa baiwar kyau da kudi zai zauna bai sake aureba bayan yana da mace irin su'ad?,to ta godewa Allah ma daba neman mata yake ba ya kwaso wata cutar ya laqaba mata,kinga idan zaki zubar da wannan gantalallen karatun naki kije ki kwashu makaman qwatar mijinki kije ku buga ke da ita mai rabo ka dauka to,ta taki qatuwar sa'ar samun auren elmustapha bayan gwagwarmayar da aka sha,duk da tasan cewa ba sonta yake ba amma tausayi da qaunar da take masa ya sanya ya amincewa aurenta" ta fada tana maida numfashin takaici
"To kuma kubra me ya kawo tonon silili haka?,abinda ya wuce ai ya riga ya wuce ko?,kawai shawara muke da buqata"
"Ki tattarata ta koma gidanta,ko a kango yace ta zauna ba nijeria ba ta zauba,bare ma meye marabar gidan nata da nan din?don kawai tana cikin family house,kowa ya sani qaryarka kace gidan mutum kamar almustapha an rasa jin dadi da walwala da dukka wata qawar duniya,idan zata koma taje kowa ta qwaci mijinta to,idan kuma zama zatayi bismillah saikici gaba da dorata akeken bera ki kuma share mata wajen zama,kinsan dai ko auren ta kaso wallahi duk yadda takejin kan nan nata a sama ba zata samu wanda ya koda kama qafar doctor mustapha ba"
"Ya isa kubra don Allah,ke dole sai kin zagi mutum zakiji dadi" waiwayawa haj khaulat tayi ta dubi su'ad dake zaune hawaye shabe shabe,har cikin qirjinta taje jin kishin mustapha,tamkar ta dauki ran wadda ta aure mata shi haka take ji,kullum kwanan duniya ji taje kamar ta yanki ticket ta koma masa,don tun kafin a kai ko ina ta soma raina kanta,ta tabbatar rabuwa da mustapha kamar yadda tayi iqirari ba mi yiwuwa bane a rayuwarta,ko sakinta yayi tana jin ba zata iya qara aure ba har ta mutu,don gani take nan duniya babu kamar yashi
"Zaki shirya ki koma wajen mijinki,daga yau so nake kada ki saurara kada ki daga qafa,duk inda ya sanya qafa ki bishi,sai kin tabbatar kin mamaye rayuwarshi,sannan cijin gidan bance ki saurarawa uban kowa ba,fin baki dayansu munafukai ne,suna da masaniyar qara auren nasa su suka hada,ki taka uban kowa koda kuwa hajiya zuwairiyya ce uwarsa kinji na gaya miki,ki fara shiri,naji labarin biki ya tasi a gidan,zaki isa ranar daurin aure don kiga idon uban kowa,uban kowa yaga naki idon ihee"kai su'ad ta gyada cike da gamsuwa da samun qwarin gwiwa,itadai kubra na gefe tana kallonsu tana tabe baki,ta tabbatar zamansu bazai taba daidaita da mustaoha ba matuqar tace zata taba iyayensa,kai ta dauke tana qissima yadda dramer zata kwashe.

        Minti talatin cif ta fiti daga bandakin,ba kowa cikin dakin alamar ya fita,hakan ya sanya cikin nutsuwa ta fara shiryawa bayan ta kulle qofar,sai data gama komai tsaf sannan ta bude ledar daya bata ta zari rigar ta wareta,sosai rigar tayi mata bata taba ganin irin desing dinta ba,bisa dukkan alamu sabuwar design ne dako kasuwa bata kai ga fita ba,sai taji tana sha'awar sanyawa,saboda haka kai tsaye ta zirata ta daidaita ta ajikinta,cif cif tayi mata har fadin tamkar an gwadata,ta fidsa shape din qirjinta sosai zuwa faffadan qugunta,qila hakan baya rasa nasaba da tsahonsu da ya kusa zuwa daya da abida,saidai abidan ta fita jiki,don sake qawata rigar a jikinta sai ta bude inda take ajiyar dankunnayenta,ta sanya dankunne da 'yar sarqar hannu wadda ta dace da kalar dutsen da aka qawata rigar da shi,yafa mayafin kawai tayi bayan ta daure gashinta,sai ta fito tamkar wata balariyar qasar,murmushi ta saki sanda ta kalli kanta a madubi,ba shakka tayi amsheta rigar,wayar dake gefanta ta jawo ta dauki hoto guda biyu,zata qara sai ta tuna ta almustapha ce,ajjiyeta tayi inda ta dauka ta wuce zuwa saman kujera kuma gadonta ta koma ta zauna ta janyo littafin wajen anty dije taci gaba da karantawa karo na biyu tunda ta bata shi.

       A quntace yake takowa zuwa qofar dakin nasu cikin tafiyarshi ta qasaita,ranshi har yanzu a matuqar bace yake,hannunshi ya sanya ya murda handle din da niyyar turawa ya shiga sai yaji qofar a rufe tanke,ranshi ya dan baci,ya soma knocking a zafafe,littafin ta ajjiye cikin fargabar yadda ake qwamqwasa qofar,ta isa bakin qofar cikin siririyar muryarta tana fadin
"Ana zuwa" ta janyo qofar baya,idanunshi suka fada kanta ba tare da ya shirya ba,kallo ya shiga qare mata tun daga yatsun qafarta zuwa kanta,ya dawo ya dire a qirjinta,boyayyar ajiyar zuciya ya saki,bai taba tsammanin rigar da suke fitarwa ta kai kyawun haka ba duk da yasan yadda suke zuba fasaha wajen saqata ba sai yau,dalili kuwa bai taba tsayawa ya qare mata kallo jikin wata ba sai yau din,koda ya kawowa su'ad bai taba gani ta saka ba,hasalima saidai ta bayar ko tayi kyautar neman suna,ita dole ace mijinta ke da MM VAIL AND ABAYA INTERNATIONAL COMPANY,amma bata taba rabata a jikinta ba,a cewarta tayi mata nauyi ko zata bata mata tsarin shigarta duk kuwa da yadda abayar ta kai ga kyau da tsada,sosai shigar abaya ta sake burgeshi duk da dama can yana sonta,da sauri ya hade fuska sanda suka hada idanu ta kama shi yana kallonta,baya taja a hankali cikin tsoron irin kallon da yake kata,takowa ya soma yi zuwa ciki murya a dake yana fadin
"Idan da wani ne kuma kr bugawarfa,kawai saiki bude ba tare da kin tambayi waye ba?"
"Ai nasan kai kadaine zai shigo"
"Ba tabbas,hotel ne dont do this again"
"In sha Allah" ta fada kai tsaye kuma cikin sanyi,sai amsar tata tayi masa dadi,a hankali sai ya dinga lalubar bacin ran nashi yana rasawa har zuwa sanda ya dubeta sanda take nannade saman kujera tana ci gaba da duba littafin
"Ki shirya kayanki,nan da gata zaki je naijeria" a ba zata maganar tazo mata,sai ta dago kai tana ware fararen  idanuwanta a kansa tana bude baki cikin tsananin farinciki har batasan sanda tace
"Da gaske?,da gaske kake don Allah"
"Ni abokin wasanki ne" ya fada yana mai fatan ta janye fararen idanuwanta daka kanshi,wani feelings akanta ke son kamashi,idanuwa ya lumshe sanda ta girgiza kai alamun a'a ta janye idanuwan nata daga kanshi,saidai murmushin dake saman fuskarta yaqu boyuwa,sake bude idanuwan nashi yayi a hankali ya azasu kanta,wanda ita bata ma sani ba ta tattara hankalinta ga littafin duk da ba karantawa take ba,zai iya cewa bai taba ganinta cikin farinciki haka ba,sai ya sake maida su ya rufe again,baya son abinda yake ji a kanta yaci gaba da tasiri a kanshi,don matuqar yaci gaba da tasirin to zai jagoranceshi ya aikata koma mene,tun wancan daren zuwa yanzu bai taba samun sukuni ba duk sanda tunanin moment na daren ya fado masa,sai yaji kamar ana mintsini ko tsikarinshi,baiso ya karya alqawarin da ya daukarwa kanshi a kanta,hakan ya sanya tilas ya kwanta duk da baijin bacci,da qyar ya samu bacci ya daukeshi.

*******   ********    ********

      Baki daya ta kasa sukuni tunda ya shaida mata tafiyar,ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a gida,har ya fura lura da irin dokin da takeyi,ana ya jibi zata tafi kuwa ta kwashe kusan duk wani abu nata mai muhimmanci tayi parkinga nasa waje guda.

       Ana ya gobe kuwa zata tafi har ya kwanta tana ta zirga zirgan hada komai nata,ya jima kwance cikin bargo yana kallonta cikin kayan bacci,wanda ita har ga Allah ta tsammatar masa bacci,mamakin irin zumudin da take kawai yakeyi,sai tayita sakin murmushi ita kadai.

        Shi da kanshi yake tuqa motar zuwa filin sauka da tashin jirage na qasar,yayin da m'aikatansa biyu ke binsu a wata motar ta daban dake bayansu,har suka isa airphort din wani farinciki na ratsata,musamman data duba ticket dinta taga jirgin zai sauka kano ne,hakan na nuna cewa gida zata fara isa,waiwayowa tayi sanda aka fara kira matafiyan da zasu tashi zuwa nijeria ta dubeshi,sai ta sadda kai ta rasa me zata ce
"Allah ya tsare,ki gaida su"ya fada hannayensa zube cikin aljihunsa,wani yanayi ke ratsashi wanda baisan na meye ba,kamar wani abu na neman gushewa daga gareshi wanda ya jibanceshi,ranshi a bace yake haka kawai baijin duk wani karsashi da farinciki,dagowa tayi ta dubeshi suka hada idanu
"zasu ji,na gode"
"Ba case" ya fada yana ci gaba da dubanta ba tare da ya janye idanuwanshi ba,a hankali ta daga qafafunta tana takawa,tana jin idanuwanshi a kanta,ita dinma sai taji karsashinta da murnarta na dan raguwa,sabo ne take zato wanda hausawa ke cewa turken wawa,ko dabba ce kana tare da ita randa kuka rabu sai kaji wani iri,yana nan tsaye hakanan ya kasa tafiya har ta bacewa ganinshi sannan ya juya a hankali ya bar wajen,kwance yayi cikin salo na kashingida abayan motar drivan ka janshi wanda ya kama tashar gidan redion dake qasar,umarni mustapha ya bashi kan ya kashe,baison hayaniya,
"Sorry sir" ya fada yana kasheta.

     Cikin awannin da basu da yawa suka iso qasata nijeria,tuni mota daga gidan baba prof dake kano ta iso tana jiran ta,tamkar jira wayarta take ta soma ruri network ya dawo,ta laluba aljihun jakar na baya ta zaro wayar tana dubawa,amira ce,murmushi ya subuce mata tana mirgina kai
"Wohoho amira,i missed you wallahi so much" ta fada a fili sanda take shigewa bayan motar sannan ta daga wayar,wani ihu da amiran ta sakiwa kunnuwanta sai data rufe ido
"Kunne na amira kunne na"
"Wallahi kaman a mafarki namecy ashe kin iso,last week muka je umra na takurawa my saif sai munje wajenki wallahi yaqi wai nauyin ya musty yake ji,wayyo namecy kina ina?"
"Saukata kenan ko gida ban qarasa ba,ina mota a kani na sauka,next week insha Allah zan qaraso"
"Qarasa gida namecy ki huta akwai labarai wallahi" ta fada tana dariya,murmushi sumayya ta saki
"To ba damuwa"
"Ki gaidan mama,amma fa idan naga ba dama zan biyoki na zaqu wallahi naga matar yaya na" dariya suka sa baki daya sumayya ta kashe wayar,har yau amira halin dai bai sauya ba.

        Saboda murna bata iya tsayawa an shiga mata da kayanta ba,wanda itama batsan da kayan bama sai da suka sauka ta gansu,da sallama ta kutsa kai tsakar gidan,wata dake shirin shiga kitchen ta dakata ta juyo,halima ce,ta zama wata babbar mace,haliman da ake zaton ba zatayi qiba ba saiga kumatu a fuskarta,da gudu ta nufo sumayya suia rungume juna kowa na ambatar sunan dan uwansa,hayaniyar ita ta sanya mama dake falon ta daga labule ta leqo
"Kada dai kicemin gudu kike halima me yasa kike da kunnen qashine wai?" Sak maman tayi sanda sumayya ke dagowa,bakinta har kunne,da hanzari sumayya ta saki halima ta nufi mama tana kiran sunanta,hannayen mama ta kama ta riqe gam qwalla na taruwa a idonta
"Me kuma na kukan ne sumayya?" Maman ta fada cikin farinciki sanda sumayyan ta fada jikinta,dakin suka shige baki daya farinciki zuciyar kowannansu ba magana.

        Nan da can kowa ya kasa motsawa cikinsu,anata hirar yaushe rabo,mama nata kallon sumayyan,farinciki na zagayata,bata taba ganin diyar tata cikin kyakkyawan yanayi makamancin wannan ba tunda take aure,wani kyau haiba da cikar kamala,ta sake zama babbar mace qwarai,da alama hankali ya fara gameta,ita kuma sumayyan na duban halima sannan ta dubi mama
"Wai dama mama halima zatayi qiba?" Murmushi ya subucewa maman
"Gata nan kuwa sumayya"
"Masha Allah,lallai abdur rahman ya iya kiwo"
"Har ya kai yayanmu,wai baki kallon madubi ne yaya,wallahi sanda kika shigo na zaci baquwar balarabiya mukayi Allah kuwa kada ki dauka sharri ne ko mama baki gani ba?" Murmushin jin dadi maman ta saki
"Masha Allah kam" sai kunya ta kama sumayya tadan rausayar da kai,idanunta ya sauka kan abdallah dake kwance yana bacci,baki ta bude
"Kai dama mama yaron nan na gunki?" Dubanshi sukayi baki daya
"Sunzo dai tare da mamarshi halima,abdur rahman yayi uwa yayi makarbiya ya karbe abdallah daga gunmu baki daya,baki ga dambun tsiyar da aka dinga yi tsakaninsa da yahanasu ba amma yace saidai tayi haquri shida mu saidai ziyara" kai take gyadawa taba duban halima,dariya ta saki
"To ai koni bazan bada abdallah ba Allah yanzu ko kece saidai ki haqura" dariya ta saki
"Ni meye mawa,dama abdallah ai danku ne,kuyi duk yadda kuka ga dama da shi,Allah ya qara zumunci" miqewa mama tayi ta basu waje don sauke tukunyar abinci,wanda halima ba zata iya ba sabida an hanata duk wani motsi mai qarfi sabida juna biyun da take da shi wanda bai wuce wata daya da rabi ba,a nan haliman ke gayawa sumayya da kuma barin da zainab tayi wanda ita taje dubawa ma ta biyo ta gida,baki sumayya ta saki tana dariya tare da duban halima
"Kai halima ko kunyata bakiji,Allah ya inganta mana ya raba lafiya" cikin jin 'yar kunya ta amsa.

        Sosai sumayyan ta zage ta daki abincin,ba qaramin missing abincin gida tayi ba,wanda kullum suna fama dana hotel,wanda idan ba fried rice ba bata iya cin wani abu sosai saidai kawai ta taba sama sama,da qyar ta yakice ta kira nafisa ta shaida mata zuwan ta,kamar ta ballo itama tazo haka take ji,amma sumayyan ta gaya mata satin sama tana tafe,tace tana nan tana jiranta,daga nan anty dije ta kira,bakin antyn har kunne,itama ta zaqu taga sumayyan,sun dan jima kan layi kafin suyi sallama,sun sha hira qwarai,a nan mama ke bata labarin irin gidajen gonar da baba prof ya damqawa malam yace nashine,tun tsohuwar dukiyarsa da bai tsaya da juya masa ba,irin hayayyafar da tayi,kai kawai sumayyan ke kadawa,babu shakka samun abota irin wannan tana da wuya a wannan zamanin,wani qima da mutuncin baba ke sake hauhawa cikim zuciyar sumayya,qaunarsa na sake kamata,qauna ta fisabilillahi wanda tun kafin tasan matsayinsa wajen mahaifinsu take masa ita
"Allah ya saka da alkhairi ya cika masa burikansa duniya da lahira" amsawa itama maman tayi,tana sake gaya mata ci gaban da aka samu,kwanaki kadan ya rage subar wannan gidan zuwa wani sabin gidan da malam din ya saya,wanda da baba ne zai biya malam din yaqi,dawainiyar da karamcin tayi yawa inji malam.

       Farincikin da malam yaji sanda yaga diyar tashi ba mai misaltuwa bane,ido ba mudu ba yasan kima,yasan cewa bisa dukkan alamu addu'ar da yake binsu da ita dare da rana zatayi tasiri a kansu,sun jima sosai suna hira da malam har kusan sha daya na dare,shi da kansa ya sake warware mata abinda ya faru na danqa masa gidajen gonakinsa da baba yayi,wanda har yau basu ma je na wasu garuruwan ba,addu'a sosai ta yiwa baban malam na amsawa.

        Washegari tare suka karya ita da malam din da abdallah,wanda abdur rahman yace a barshi yaga mamanshi har sanda zata tafi,shi kansa abdur rahman din tsokanarta ya dinga yi yana cewa manyanmuyaya sumayya,raha suka yi sosai kamar babu wani abu da ya taba faruwa tsakaninsu,dariya ta dinga kawai,shi kansa ya sauya ya sake zama magidanci,alamun hutu da kwanciyar hankali baki daya sun bayyana tattare da shi,cikin zuciyarta tana gode ma Allah,tasan ko ba komai 'yar uwarta na cikin rayuwar jin dadi da walwala kamar yadda take fata.

       Kwalayen jiya ta bude ta duba,uwar tsaraba ce a ciki,akwai wasu dake nannade da sunayen malam da baba,bata taba ba ta miqa musu cikin mamaki,sai take jin wata qimarsa cikin ranta
(Gareku maza,abune mai kyau ka dinga kyautatawa iyaye da 'yan uwan matarka,don haka na qara qimarka a idanunsu da idanun matar taka gaba daya,ko yaya alkhairi yake dadi gareshi,Allah ya hore ya kuma bada iko amin),sai data gama sannan ta shirya zuwa gidan zainab,ranan can ta wuni baki daya,ta sameta cikin kyakkyawan yanayi itama kamar 'yar uwarya,jikin nata ma ya warware gaba daya,washegari kuma gidan yaya yahanasu ta wuni,kallonta yayan ta dinga tana qarawa,har sai data kasa shiru
"Allah qadiran ala may yasha'u,ashe sumayya ke din rabon wani ce da muntarinmu ba,kowanne bawa da kalar tashi qaddarar" ta fada tana matse hawaye,hakan ya sosa tabon dake zuciyar sumayyan,duk da haka sai ita ta lallashi yaya yahanasun,sai la'asar taje ta gaida hajiyan bahijja da abdur rahman,sosai taji dadin ganin sumayyan,ita ta tsaidata ma bata wuce gida ba sai magariba.

         Again washegari kuma gidan yaya abubkar ta wuni,amina ta rasa inda zata sanyata saboda murna,itama dubanta take kamar yadda kowa kallonta,sosai sumayyan ta sauya mata cikin 'yan watanni
"Masha Allah sumayya masha Allah,dama haka almustaphan naki ya iya kiwo?"
"Kai anty kai" ta fada tana qyalqyala dariyar irin yadda meena tayi maganar.

   ******   *******   *******

        Qarfe sha daya na dare ya dawo daga office din,baki daya ranar ya maida kanshi busy,sosai ya tsaya da kanshi cikin kamfanin yana zagayawa waje waje yana ganin yadda ma'aikatan ke gudanar da aikinsu,abinda tunda suka taho tare da sumayyan baiyi ba,baisan me ya hanashi ba,daga qarshe ya tuqe a warehouse nasu,hamza ne ya dubeshi a gajiye
"Gaskiya maan na gaji gida zan wuce,magariba fa ta gota,na tabbata abida na can na zuba ido" cikin ko in kula yana duban bangaren da suke ajjiye kayan aikinsu yace
"Wani ya hanaka tafiya?"
"Ok,dama kai na tsaya,na lura kuma kai yau aikin naka ba mai qarewa bane,ko don yau gauro kake?" A nutse ya waiwayo ya maka masa harara
"Ba yau na fara ba bare ka gaya min ba dadi" dariya hamza ya saka
"Gaskiya ne wannan,ko zaka zo mu wuce tare kaci abinci wajena?"
"Bana buqata" ya fada yana ci gaba da takawa hannunsa zube a aljihu,haka kawai yake jin sam baida sha'awa ko karsashin komawa hotel din,a haka hamza ya juya ya fice ya barshi a wajen,yasan tunda yace bashi zuwa to bazashi din ba.

         A hankali ya tura qofar dakin,babu haske a dakin kasancewar babu kowa,ko ina dumdum yake da duhu,kunna qwai yayi yabi ko ina na dakin da kallo,sai yaga dakin tamkar bashi ba,komai ya canza,wani fili yaga dakin ya sakeyi kamar an dauke wani abu,wata gajiya ta musamman ta saukar masa,ya taka zuwa cikin dakin ya zauna gefan gadon idanuwanshi na kan doguwar kujerar data saba zama,yana fidda takalmin qafarshi da safa yana jefarwa,gadon ya fada baki daya yana fidda iska daga bakinsa,a qalla ya kai kusan minti goma a haka kafin ya miqe ya zauna dai dai,wayarsa ya fidda ya kira ya bada umarnin a kawo mishi dinner sannan ya miqe ya cire kayan jikinsa ya fada toilet,turus yayi yana duban bathtube wanda yake wayam babu komai a cikinsa,sabanin watannin baya da idan ya dawo yake tadda shi cike da ruwa mai qamshi da dumi,cikin kasala ya soma tara ruwan kafin ya shige cike,qaramin tsaki ya ja,baki daya ruwan bai masa ba,sabanin nata da yake jin baison fita a ciki,a gurguje yayi wankan ya fito yana tsane jikinsa da towel aka yi knocking,sai daya sanya doguwan riga sannan ya bude ya karba,shafa'i da wutiri yayi kafin ya dauko computer dinsa ya kunna bayan ya jonata chargy,sosai ya zauna a qasa ya bayan ya janyo abimcin ya bude ya soma kaiwa bakinsa,lokaci lokaci yakan daga kai ya kalli inda ta saba nadewa duk lokaci irin wannan da yake zama cin abinci ko yin wani aiki,lokaci lokaci yakan kamata tana satan kallonshi da fararen idanuwanta,ko ita wani lokacin ta kamashi ko su kama juna,kowa yakan dauke kai da sunan ba kallon dan uwanshi

Please Login or Register in order to submit comment