Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai lokacin da almustapha ya qaraso,wani kallo ya watsawa su'ad,tunda ya shigo ya cimmata tsaye ko kusa da wajen bata dosa ba,ya san halinta sarai sai ya dauke kanshi,cikin hanzari ya iso gabanta ya durqushe yana riqe da ita saboda yadda take yunquri mai wahalarwa,sai data amayar da dukkan naman data ci,sannu kawai yake jera mata,ya miqe da kanshi ya ciro ruwa ya bata ta kuskure bakinta tana maida numfashi,kamata yayi ya zaunar da ita saman kujera ya amshi maqullan dakinta da niyyar bude mata tukunna kafin ta tashi ta isa ga dakin.


Duk da yadda take a galabaice amma sai data daga kai ta dubi su'ad sanda ta sheqe da wata shaqiyyar dariya
"Su ciki manya,oh Allah ya rufamin asiri,wallahi yarinya kin tashi a aiki,sai yanzu zaki san baki da wayau" dariya ta sake saki
"Allah ta inganta" ta fada farinciki fal ranta,hango yadda komai zaizo qarshe tsakanin sumayyan da almustapha cikin sauqi,mutum ne shi mai bala'in tsantsami,ta tabbatar bazai iya daurewa qazantar laulayi ba sam,itakam wanne tsautsayi ne zai aiketa daukan ciki?,ai gwara da tayi mai dungurun gum haihuwa da damuna,ta raba kanta da haihuwar rabuwa ta har abada,yanzun irin wadan nan wahalhalun ina zata iya da su tana tsaka da morewa duniyarta,rangaji taci gaba da yi murmushi na fita a fuskarta
"Hahaha.....zamu ga ya zata kaya kuma,sannunki da kayan nauyi" lumshe idanunta tayi tana sauke numfashi a hankali,bata da lokacin sauraren shirmenta sam,don ra fuskanci akwai wani abu da take son gaya mata wanda ta tabbatar ba zayayi amfani gareta ba,koma ace baki day bai shafeta ba,dawowa ya sake yi cikin falon,gabanta ya qaraso,ya sunkuyo inda take jingine da kujerar yana duban qwayar idanunta,cikin taushi yace
"Sannu babe......" Kai ta gyada tana lumshe idanu sannan ta bude
"Zaki iya tashi?" Langabe kai tayi
"Saidai ka dagani"kusan da biyu ta fadi hakan saboda su'ad dake tsaye ta zuba musu idanu,zuciyarta kamar ta tsinke
"Daukarki ma zanyi cancankat" ya fada yana gyara hannun suit dinshi murmushi na fita a fuskarshi
"Meye hakan almustapha?"waiwayowa yayi yana barin gyara hanunshi da yake ya zuba mata ido
"amman dai kasan cewa ranar girki na ce ko?,bai kamata ace kana tabata ba"hannunshi duka biyu ya riqe qugunshi
"Zoki taimaka mata ta tashi" ya fada a dake,ranshi a bace yake yana qoqarin dannewa ke kawai,tunda ya tafi tsakamin jiua da yau babu wanda ta shiga ta gaisar a cikin mutanen gidan,sannan yana jin sautin dariyarta bayan shigarsa daki,saidai bai ji me take fadi ba,fuska ta bata
"Gaskiya bazan iya ba,ta gama aman yanzun sannan na tabata?....a'ah gaskiya" ta fada tana kada kai,juyawa yayi ba tare da ya sake dubarta ba ya daga sumayyan cak ya wuce da ita,binsa tayi a zabure ranta a bace,cikin tsantsar mamakin yadda ya taba jikinta babu wannan qyamar bare qyanqyamin,me yake nufi kenan?ya shirya ci mata fuska ne?,sai kuma ta dakata a bakin qofar dakin saboda tuna wani abu da tayi.


Gyara mata kwanciya yayi ya rage mata kayan jikinta sannan ya sumbaceta a goshi
"Ki kwanta ki huta,banson ko qwaqwqwarar magana ki sake yi,zan kawo miki maganin tsaida amai.....zanje nayi wanka yanzun"
"Na gode" ta furta a tausashe,murmushi ya saki yana shafa saman kanta,ji yake tamkar ya maidata jikinsa su koma abu daya
"Shshshshsh......nine da godiya,kin manta cewa babban gift kika bani wanda ba wanda ya taba bani kwatankwacinshi?"murmushi ta sake masa,ya sake sumbatar labbanta masu taushi dake burgeshi sannan ya soma takawa da baya da baya ya fice,ido ta rufe bayan fitarshin,tabbas so shike iya juya mutum ya sauya masa halayya komai girma isa da qasaitarsa.


Saura kadan yaci karo da ita sanda yake fita don bai tsammaceta a wajen ba,dauke idonshi yayi yayi gaba tabiyoshi a baya tana sauri don ta cimmasa,daidai sanda daya daga cikin ma'aikatan dake shirya abincin dare a kitchen ta fiti,da hanzari ta koma da baya zata koma kitchen din ganin tahowar almustaphan
"ki qarasa bakin qofan can ki gyara wajen ya baci da amai"
"To yallabai" ta furta kanta. aqasa cikin ladabi
"Amma girki take mana,ya za'ayi ta je ta taba qazan......"harara ya watsa mata wadda ta hanata qarasa fadin abinda take da niyyar fada,yayi gaba ta sake bin bayansa.


Yana tsaye yana ragw kayan jikinsa yayin da take tsaye bayanshi tana lissafo qorafe qorafanta daya bayan daya,tie dinshi ya cire ya wurgar saman gadon,cikin zafin nama ya fincikota sandan take tsaye bayanshi ya zaunar da ita bakin gadon da yake tsaye,ba waramin tsorata tayi ba da ganin yanayinshi,cikin kakkausar murya ya soma magana
"Wace irin macace ke da bakisan komai ba sai qorafi da tashin hankali?,wace iriyar macace ke da komai na mijinki bai dameki ba,lalurarki da buqatar ki itace gaba akan ta kowa,a haka kike so na kyautata miki?, ahaka kike so naji dadin zama da ke,bakisan komai nawa ba,bakisan duk wani abu da ya shafeni ba,na dauka laifi nane da fari na zaunar dake na karanta miki komai da yadda nakeson komai ya zama amma a banza,shin wai sai yaushe zaki sauya ne?,sai yaushe?,dame na rageki da shi na dukka haqqinki da Allah ya dora min?me kike so nayi miki?"ya qarashe maganar yana jin zafi har cikin zuciyarshi,idanu ta zuba masa tana dubanshi,idanunsa ya lumshe yana komawa da baya ya zauna,qoqarin cooling temper dinsa yake,baiso wani abu ya bata zallar farincikin da yake ciki a yau.



Kuyi manage da wannan,ba lallai gobe wani ya samu banyi alqawari ba,naso yau na barshi sai gobe na hada na turo muku mai yawa amma nasan zaku fison a baku ko kadan ne.






*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



9⃣5⃣


*Bismillahir rahmanir rahim*


*LA HAULA WALA QUWWATA ILLA BILLAHIL ALIYYUL AZIM*
___________________________________





      Zuba masa ido kawai tayi tana jin wani zallar bacin rai na ratsata,hawaye na bin kuncinta,ji take a duniya ya gama tozar tata,ya gama wulaqantata,a dacan ba haka ai ta sanshi ba,ta ina zata fara debo irin rayuwar da yake da muradi,sam ko daya ita ba zata iya ba
"Yanzu na sake tabbatarwa cewa baka qaunata almustapha,kanka tsaye kake gayan wadan nan maganganun?" Ta furta tana nuna qirjinta da yatsa,a nutse ya daga idanunshi ya zuba mata su,wato wanda yayi nisa baijin kira,barin hali sai mutuwa?,duk yadda ya kai ga dorata a hanya kenan qaryarshi ta sha qarya,bazata taba fahimta ba,ya fuskanci duk abinda yake gaya mata ashe bata bakinsa yake,kwanaki biyun da yayi dakinta ya bata lokuta sosai yana nusasheshe da ita abubuwa da dama,ta kuma kwantar da kai ta nuna tana dauka,ashe duka busa yake mata cikin kunnuwanta ba magana ba.

        Tsam kawai ya miqe ya ci gaba da rage kayan jikinshin,ya daura towel ya shiga toilet,yana tsaye riqe da qugunshi yana tarawa kanshi ruwan wanka ta turo qofat,hankalinshi kaf bai wajen,ya kasu gida biyu,wani na wajen sumayya yana tunanin tayi bacci kuwa?,yayin da daya ke kai kawo kan halaye da dabi'un su'ad
"Kana nufin kai maisheni banza da baka da lokacinta kenan?,amma ita waccar ai kana da nata lokacin ko?,har kana iya kamata bayan qazantar data futar,wanda iyakar sanina da kai kana da qyanqyamin da bansan lokacin daka zama haka ba" shiru yayi mata baice mata kanzil ba,iya tsahin rayuwarshi mutum ne da baya son hayaniya,tubewa yayi ya shige bathtube abinshi ya barta tsaye,sai ta fashe da kukan baqinciki ta juya ta fice zuwa uwar dakin.

          A nutse yayi wankanshi,ranshi na sake fari da haske a duk sanda ya tuna cewa nan da wasu watanni shima zai zama baba,nan da wasu watanni zai dinga gajin gilmawar yaro ko yarinua cikin gidanshi,yaron da za'a kirashi da d'anshi,mallakinshi,jininshi,murmushin farinciki ne ya subuce masa sannan ya miqe ya fito.

        Kwance rub da ciki ya tadda ta tana rusgar kuka,ya bude ma'ajiyar kayanshi ya fitar da shirt da trouser ya sanya,ya shirya tsaf abinshi ya fice ya sauka qasa,dining ya wuce yayi serving kanshi yaci abinci ya qoshi sannan ya wuce zuwa sashen ummee.

         A kwance ya taddata tana kallon news a al-akhbar,sallamarshi ta sanyata miqewa ta zauna tana amsawa,suna ranta shi da sunayyan tun jiya da bataji motsim daya daga cikinsu ba,ya qaraso wajenta fuskarshi dauke da murmushi ya zauna gefanta suka soma gaisawa
"Ya sumayyan take?"ummin ta tambayeshi ba tare data tambayi su'ad ba,rabonta data shigo ta gaidasu tun shekaran jiya da suka shigo tare da shi,amma ita hakan ba damuwarta bace tunda dama ba zamansu take ba zaman mijinta take,indai kuma suna zaune lafiya lau to da sauqi
"Lafiya.....na barota tana bacci"
"To masha Allah" hira suka shiga yi irin ta da da uwa,cikin daqiqu kadan ta fuskanci yaron nata na cikin farinciki da annashuwa qwarai,sai ta danganta hakan da cewa tsantsar farinciki kulawa da walwalar da yake samu ne daga wajen abokiyar zamanshi,ya jima gurin ummeen sosai sunyi hirar da suka jima basuyi irinta ba,bai bar wajen har bayan sallar magariba,sai da aka kirashi a waya ya qarasa baqin get wajen masu gadi da kanshi ya amshi saqon da ya bayar ayi masa order.

          Sanda ta farka taji dadin jikinta sosai,hakan ya sanya ta shiga toileta ta hada ruwan wanka mai dumi ta wanke jikinta,ta dawo gaban madubi daure da towel ta janyo kujera ta zauna kai,don kasala take ji ba zata tsaiyawa ba,haka kawai take jin wani farinciki da annashuwa tana ratsata,ta dinga kallon kanta a madubi tana sakin murmushi,lokaci lokaci tana shafa cikin nata wanda yake a dame da hannunta,itakam ciki na zuwa mata a bazata,tun yanzun Allah ya dasa mata so da qaunar abinda take so tamkar yadda taso abdallah tun kafin ta haifeshi,gababta ya yanke ya fadi sanda ta tuna irin gwagwarmayar da tasha hannun zainab,tsantsar makirci zalla da kuma wuyar da tasha kafin abdallah ua kai labari,ambaton sunan Allah ta dinga yi tana nemawa kanta da abinda ke cikinta tsari tun daga lokacin,bata fatan makamancin abinda ya faru da ita wancan karon ya sake maimaituwa da ita, akasalance ta dinga shafa man gabanta na faduwa ta wani bangaren.

        A nutse ya turo qofan dakin wanda sam bata ji ba saboda yadda hankalinta yayi gaba,takowa yake amma idanunshi na kanta yaja qarewa halittar Allah kallo,saboda banda qirjinta zuwa mazaunanta ba inda yake a rufe,dogon wuyanta da santala santalan cinyoyinta a bayyane suke,fatarta data sake kyau sai sheqi take yi,wani qaunarta da shauqinta na fusgarshi,a haka ya qarasa ya sanya hannayenta ya rufe idanunta,taushi da sanyin hannunshi kadai sun isa gaya mata waye?,ballantana da zuwa yanzun koda bata ganshi ba matuqar yana muhallin da take sai jikinta ya bata,matuqar tasiri yayi cikin rayuwarta,ya mallaki duk wani tunaninta,shiga da fitar numfashinta na tattare da nashi,bata son ta fiya zaqewa ne da yawa kawai,tunda ta sani cewa ba ita daya bace ta mallakeshi.

       Sautin murmushin dat fitar kadai ya sanar da shi ta gane waye,shima yana murmushin ya cire tafukan hannunshi daga fuskarta yayi kissing wuyanta a tausashe,sannan ya zagaya gabanta ya dane saman mudubin yayi zamanshi hannayenshi harde a qirjinsa bayan ya ajjiye ledan takeaway din daya shigo mata da shi na abinci yana ci gaba da qare mata kallo,baki daya ta takura,kunya ta lullubeta
"Me yasa baki taba zama nayita kallon ki a haka ba bayan kinsan hakan ashe ba qaramin qayatarwa gareshi ba?" Murmushi ta saki cikin kunya,bai tsaya jin amsarta ba ya dora
"Tunanin me kike haka ummu abdallah?,kinsan hakan yana da illa ga lafiyarki?"kai ta gyada sannan ta maida masa amsa
"Babu komai abu abdallah" sosai sunan ya masa dadi har qoqon ranshi,sai da ya lumshe idanunshi sannan ya bude bisa kanta
"Kada ki cemin bakiyi bacci ba"
"Nayi,na farka ne naje nayi wanka da sallah" ta fada tana murmushi
"Ummee na gaisheshi" idanu ta dan zaro
"Shine kayi tafiyanka baka tsayani munje na gaisheta ba ita da baba,kwana nawa ban gansu ba" ta qarashe maganar a shagwabe,binta kawai yake da kallo,ko iya nan ta samu wata madaukakiyar daraja da baiga macen data sameshi ba,ta maida iyayenshi tamkar naga,tana sonsu so na bilhaqqi,ya samu kabarin tun kafin suyi aure take sonsu da ganin girmansu,abinda har yau su'ad ra kasa fahimta daga gareshi,mutum ne shi wanda da iyayensa kadai zaki iya cinsa da yaqi,saboda daraja da matsayi ya basu bana wasa ba,yace bazai taba yin wasa da aljannarsa ba,duk duniya idan suka take masa ita babu mai bashi,ki ubangijinsa bai isa ya tunkara ba bayan babu kyakkyawar alaqa tsakaninshi da su,saboda yardar Allah tana tattare da yardar iyaye,hakan fushinsa yana tare da nasu fushin,sirrin nasararsa da daukakarsa ba'a komai take ba face ga albarkar iyaye,koda bata mallaki komai wanda za'a sota ba yana da yaqinin ya samawa yaranshi uwa ta gari,ya tabbata yaransji zasu tsira da sanin girman na gaba
"Yanzun ma banje wajen baba ba,shirya idan na idar da isha'i zan shigo muje" ya fada yana duba agogonshi tare da sauka daga saman madubin
"Ina fata amma baka gayawa ummee komai ba ko?" Ta fada saboda tana jin nauyinta,bata son ummeen ta fuskanci akwai wani abu,murmushi yayi,ya gano sarai mai take nufi
"Don me zanqi gaya mata?" Tuni idanunta sukayi qwalqwal da hawaye,sai ya dawo da baya,ha dagata suna fuskantar juna,nauyi ya cikata,yadda yake sake qare mata kallo a kaikaice
"Banason naga wani abu mai kama da hawaye a fuskarki......kinsan me?" Kai ta girgiza tana dubanshi
"Nima kunya nakeji,bansan me zance musu ba,espicially baba,na masa ba dai dai ba sanda ya bani aurenki ya damqa min amanarki....yanzu idan nace kina da ciki kinsan me zaice?" Kai ta sake girgizawa,sai ya jawota ya rungumeta tsam,jikinsu na gogar na juna,ya dora bakinshi a kunnenta
"Zai iya rayawa a zuciyanshi....dan banza,yace baya so ashe har yayi aiki irin haka?" Dariya ta qwace mata cike da kunya,sai ta tura kanta a qirjinsa tana dariya qasa qasa,shi dinma dariyar yake ya dan janyeta yana dubanta
"Ki shirya muje,idan kin shirya jin wannan kunyar sai a sanar mai,amma nikam ban shirya ba gaskiya,ga abinci nan kici kafin na dawi,ba nama kawai zalla ba za kiyita ci" ya fada yana juyawa,dan rage dariyar tayi tana bin bayanshi da kallo
"Me kayi masa naba dai dai dinba sanda yace ya aura maka ni?....." A ba zata tambyar tazo masa,sai ya tsaya cak ba tare da yaci gaba da tafiyar ba,jin yayi dif ya sanyata tace
"Kace masa baka sona ko?" Ta baiwa kanta amsa tana ci gaba da duban bayanshi,a nutse ya waiwayo sannan ya sake takowa zuwa gabanta,hannunshi daya ya dora kan kafadarta ya riqe yana dubanta
"Sumayya......daga kanki ki dubeni" ya bata amsa cikin kakkaurar murya,a hankali ta daga kan ta dubeshi
"Ci gaba da kallon qwayar idanuna,ina son ki bawa kanki amsa ne,kada na fadi ki dauka wasa nakeyi" a hankali ta saka idanunta cikim nashi,tsahon mintuna aqalla hudu,kamar masu kallon quda,saiga tsaiwa na neman gagararta,tuni ta janye daga kallon nashi,ba zata iya jurewa ba,ya tareta suka fada gefan gado
"Uhmmmm,zaki iya explaining?"kai ta girgiza tana niyyar tureshi,murmushi ma subuce mata,sai yanzu ta karanci wayau yayi mata,yau ta sake yarda da maganar anty dije da tace vatasan sanda sumayya zata girma ba
"Ko ni kike so nayi miki?" Da sauri ta dora hannunta saman bakinshi yana girgiza kaj,sai yayi murmushi yana sauke hannunta daga kan bakinsa
"Okey......daga yau duk ranar da kika sake min tambaya makamanciyar wannan zan hukuntaki fiye da haka,mace nada dataja wajena.......macen ma matar aurena na......matar aurena wanda ta soma kawon cikakken farinciki cikin rayuwata......kinsan wani abu?.....uwar d'ana.....dole ta zama ta daban,dole na bata wani matsayi na musamman,koda kuwa kuturwa ce gurguwa ce makauniya ce....balle ke...ke din da kika zama wata ta musamman a dukka tarihin rayuwata,kika kafamin tarihin da ban taba cin karo da shi cikin rayuwata ba" tabbas ta gamsu,ta gamsu koda bai fada ba,miqewa yayi
"Ki shirya zan kiraki muje mu gaidashi"kai kawai ta iya gyadawa,har ya fice kowannensu na murmushi.

         Saman kujerar falon sama ya tadda ta wannan karon zaune,sai ua dauke kai kamar bai ganta ba yayi niyyar wucewa ciki,ganin haka ya sanyata cikin hanzari ta isa gareshi ta rungumeshi ta bayansa,cikin salon kwantar da murya ta soma fadin
"am sorry my dear,am sorry,ba nufina na bata ranka ba,u know i love you thats why,but am sorry"baisan ya zaiyi ta zama yadda yake so ba,har ga Allah bai nufin tozarci ko wulaqanci gareta,saboda bazai manta hadisin da annabi ke wasiyya ga maza su kyautatawa mata da alkhairi ba,but hakan baya nufin idan ta kauce kayi qoqafin nusashsheta taqi kabi dukka hanyoyin da zaka ladabtar da ita wadanda suka dace ba tare daka cutar da ita ba,hannunshi ya sanya ya zagayo da ita gabansa ya sanyata a jikinshi
"shikenan,ya wuce,amma kiyi qoqarin sauyawa,kiyi koyi....." Sai kuma ya katse bai qarasa din na,saboda bai kamata yayi mata misali da itan ba zata ga kaman cin fuska ne
"Ki gyara ki zaka yadda nake so,koda ba duka ba kiyi qoqarin kamantawa"
"Thank you,thank you verry much" ta fada cikin farinciki,don ba zata iya missing wannan daren ba,ta tabbatar ya juya mata baya ba komai bane wajenshi,ko a jikinsa tun sanda suke su biyu bare yanzu da yake da wata,alwala ya daura ya fice masallaci,sanda ya dawo zai sake fita ta tareshi kan ina zaya je yace zashi gaida baba
"Sau nawa kika je gaidasu bayan bana nan?" Ya tambayeta yana tsareta da ido,sai ta rausayar da kaibtana son basarwa,ranshi ya quntata,amma gyara yake son kawowa,dole yabi abuna hankali cikin hikima
"U know what?" Da sauri ta juya tana dubanshi gami da girgiza kai
"Duk yadda zaki soni....ko hadiyeni zaki kina fiddo ni,zan qaryata son da kike min matuqar baki bawa iyayena darajar data fi wadda kika bani ba" ya gaya mata da yaren da zata fi ganewa,sosai zancan ya shigeta,cikin zuciyarta ya soma mitan wanne irin sone wannan da zaya takurata da taso iyayenshi,itakam bata ga ana irin haka ba a al'ummar data taso,kuna iya kai iyayenku gidan gajiyayyu ma idan suka soma zama nauyi kanku,ko ka kai qararsu ga hukuma matuqar suna takura ka,kana iya komai gaban idanunsu ma ba kwaba ba hantara,suna yin nasu zasuyi,amma shi ko hugging dinta bai taba ba a gabansu,randa ma tayi gigin yin hakan sai da ya sabar mata,daga haka bata sake gwadawa ba,to kuma haka kawai ba zamansu take ba zai tilastata hulda da su,wannan qaddara da yawa take,ba yadda ta iya ta shiga daki ta sauya kayan jikinta zuwa gown,sakakkiya ce ba'a matse take ba,har ya soma sauka tabi bayansa,yaji dadi sosai har y fuskanshi ya nuna hakan,wanda itama hakan ya sanyata jin dadi cikin ranta.

       A bakin qofa ya tsaya yayi mata knocking,koda taji tasan cewa shine,sai ta zura dogon hijabinta kan riga da skert dake jikinta ta fito,sun sanyashi tsakiya saidai ba wadda ke cewa da 'yar uwarta kanzil,suna tsaka da tafiya hibba ta hangosu ita da hibban yaran fahariyya da adam yayan almustapha,gudu ta debo ta iso inda suke kai tsaye ta ruqunqune sumayya iya qarfinta tana kiran anty
"Sake antyn taku hakanan kada ta fadi hibbah,bata jin dadi" cewaf almustapha,tana dariya ta gaidashi hibban ma haka,suka gaida su'ad sannan suka gaida sumayya
"Anty...tun ran nan rananan din cannnn.....da kika je zaki bamu labari baki bamu ba har yanzu" murmushi ta saki tana shafa kanta,tana mamakin kaifin qwaqwalwa irin ma yarinyar da har yau ta kasa mancewa sa maganar
"Zan baku in sha Allah"
"Yaushe anty"
"Ba yanzu ba sai ta warke" almustapha ya fada
"Abbanku na gida?" Ya kuma tamyarsu,hibban ne ya amsa,yace suje suce yana sin ganinshi amma ya shiga wajen baba tukunna
"Yana wajen baba prof din ai muma daga can muka fito"
"Is ok,ku shiga gida to ba kyau yawo da dare" da gudu suka juya suja wuce shi,su kuma suka ci gaba da takawa
"Anya son yaranki baifi nawa ba" murmushi ta saki
"Yara ai rahama ne,ko wajen ubangiji sau tari albarkacinsu muke ci,ba don su ba da wataqila ko ruwan sama mun daina samu" ta fada tana murmushi tare da dan dubanshi,kusan da biyu ta fadi haka,raddi ne kan maganar da su'ad ta gaya mata dazu na ta gama aiki tunda ta dauki ciki
"Gaskiya ne" ya furta a fili,cikin zuciyarsa yana sake jinjinawa baiwa da fasahar zancanta,tsaki takeso tayi amma dole ta bame bakinta,don bata son abinda zai bata daren nasu.


         Da sallama suka shiga wajen baba,yana tare da adam yayan almustapha suna hirarsu,kusan ranar sumayya zata ce ta soma ganinshi,akwai 'yar kama tsakaninsu,kana ganinshi zaka san jininsa ne,saidai almustaphan ya fishi kyau da quruciya,ran baban yayi qal ganinsu dukkansu su ukun a tare,murmushi yaqi yankewa daga fuskarshi ya tarbesu suka zauna suna gaidashi
"Sa'adatu(da yake wani lokaci hakan yake kiranta,abinda ta tsana kenan,ita aginta bata suna ne)yanzu muka gama waya da babanki"
"Allah sarki" kawai ta fadu,har ga Allah haushin tsohon take ji,gani take shine ummul Aba'isin komai ma da ya faru da ita,kanwa uwar gami,sai ya waiwaya ga sumayya wadda ta gama gaida yaya adam a mutunce
"Maman tun daga randa naci tuwo kuma sai kiyi batan dabo,inata nemanki na bada tukuici" qas tayi da kai tana wasa da yatsun hannunta kawai,ya tambayi lafiyarsu baki dayansu suka amsa mai,ganim almustapha sun soma hira da adam yasa almustapha yace suje wajen ummeen shi zaizo,su'ad ita ta fara yin gaba,sumayya na bayanta,ganin tayi wucewarta bata ko saurari bangaren anty maamaa ba ya sanyata ita shiga ta gaidata,taji dadi kuwa sosai,bangaren itama sai ita daya,dama can yaran mazan ba zama suka fiya yi ba,bare yanzu da kowa ya kama nashi gidan,don su a waje suke zaune,saidai kowanne yace idan yana sha'awa zasu zo suyi kwana biyu cikin gidan tunda suna fa wajensu,sosai taji dadi suka dan taba hira atsaitsaye ta wuce zuwa sashen ummee,tana gab da shiga su'ad ta fito tana hura hanci,ganin tana yunqurin bangazarta ya sanyata ja gefe,wani kallo su'ad din ta watsa mata sannan cikin harshen turanci tace
"Banza" murmushi ta jefeta da shi,cikin salon nuna qwarewa itama ta karya nata harshen da salon data koya a uk
"Banzayen ai suna da yawa ba daya bace,suna da yawa,bansan wacce daga ciki kike nufi ba"cewar sumayya sannan ta juya hankali kwance tayi shigewarta.

        Cikin kulawa suka gaisa ta samu gefan ummin ta zauna,bakin kowanme yayi nauyi,sumayya ya kunyar ummin ita kuma yau ummin surukuta ce ta motsa,saidai duk motsin sumayya tana lura da ita,sai take ganin ta soma sauyawa baki dayanta,jefi jefi suka dinga hira da ita har almustaphan ta shigo ya taddasu,baiyi zaton zai sameta har tsawon lokacin a nan ba,a sannan ummi ta shiga kitchen tana hanyar fitowa ta jiyoshi yace
"Baki gaji da zama ba?,akwai magungunan da zaki sha fa?"
"Me ya sameta?" Ta fada tana fitowa akitchen din tana fatan jin abinda zuciyarta keta faman raya mata,kanshi ya shafa yana jin nauyin ummin
"Ciwom ciki ne,kuma tana shan magani yanzu haka yana samun sauqi" ta san zurfin cikinshi qwarai,sai ta zauna tana cewa
"Allah ya sawwaqe,lallai kam ki kula da shan magani"ta miqawa sumayya wani dan bowl na plastic mai garai garai wanda akayi wrapping dinshi,maganar tata sai ya jita kamar a baibai,gaba yayi cikin jin nauyi yana cewa ta taso su tafi,ummi ta bita da kallo sanda ta miqe tayi mata sallama,sai taji tamkar ra tsaidata taji ainihin meke damunta,saidai kuma koma meye tasan indai da gasken ne abinda take zato to nan da wani dan lokaci qanqani zata fasu,suna ficewa ta samu kanta da yin sujuddushshukur,duk da bata tabbatar da cewa hakan bane,wani farinciki data jima bata ji irinsa ba yana ratsata,tamkar bata taba riqe jika ba.

*******     ******    *********

      Bai taba riskar kansa cikin farinciki ba irin na wadan nan kwanakin,bai taba tunanin haka samun d'a yake dadi ba sai wannan karon,ashe daa baki daya hasashene kawai yake yi,sumayya kam na fama da laulayi sosai,saidai Allah ya bata wata juriya da qwarin gwiwa,tana matuqar qoqari wajen boye ma almustapha,saboda kullum kwanan duniya tunaninshi na kanta ita da abinda ke jikinta,bai da sukuni yana gida koko baya gida,dawainiya yake da ita bilhaqqi,idan da yana da iko numfashi ma shi zaya yi mata,bata taba cin karo da soyayya kwatankwacin wannan ba,bata taba zaton ita din sumayya abar soce har haka ba,bangaren su'ad kuwa gani take Allah ya sita da bata taba gwada daukan ciki ba,musamman duk randa amai ciwon kai ko zazzabi ya make

Please Login or Register in order to submit comment