Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsanake ta kwatanta mata yadda tayi din sannan ta dauke farantan tayi kitchen da su ta dawo suka ci gaba da hirarsu.

         Tare suka sauko tana biye da shi a baya,ji take tamkar ta dawo da kwanakin baya,bata so ta tuna cewa yau zata sallamawa waccar 'yar qauyen mijinta da tafi so fiye da komai a duniya,sam fuskarta babu walwala haka suka ci gaba da takowa,muryar ni'ima ya jiyo,ya waiwayo ya dubesu,cikin girmama juna suka gaisa,sannan sumayya ta gaidashi tana dan dauke kai,kishinsa itama take ji har cikin zuciyarta,saidai bata son ta nuna,dining din da masu aiki suka shirya da kayan kari suka nufa,yayin da ni'imah ta miqe
"Bari na wuce,ko wajensu ummee ban shiga ba" sam bata son ni'iman ta tafi,taji dadin zuwanta,sai ta miqe tana fadin
"Bari na dauko mayafi mu shiga tare,nima ban je ba" tana nan tsaye sumayyan ta shiga daki ta dauko mayafinta,hankalinshi na kansu duk da yadda su'ad ta tare gaba da baya,da biyu take yin komai,a nutse ta qaraso bakin dining din a ladabce tace
"Zanje mu gaisa da su umme ni da anty ni'imah" ba tare da ya dago ba yace
"Ni din ma banje ba,ta wuce ma taho" sam bataji dadi ba,sai ta dawo a sanyaye
"Anty ni'imah tare zamu fito" murmushi ta sakar mata
"ba damuwa sai kun fito"daya daga cikin kujerun dake falon ta samu ta zauna tana jiranshi ya kammala,tana iya jiyo duka abinda su'ad ke fadi,hirar darensu na jiya take ta sako mishi yana basarwa,jin bacin rai na neman mamayarta ya sanyata miqewa tsam tayi shigewarta dakinta.

        Tana gaban mudubi tana gyara zaman kayan makeup dinta ya shigo cikin nutsuwa,har yanzu ranta a bace yake,sai taqi dagowa ta dubeshi duk da yadda take jin tsaretan da yayi da idanunshi
"muje na kammala"ya fada a a taqaice
"Kuje na taho" itana ta maida masa da yanayin da yayi mata maganar,sarai ya fuskanci ranta a bace yake
"Muje nace"
"Nace na taho" shiru ya ratsa na wasu muntuna
"Ummu abdallah" da hanzari ta daga kai ta dubeshi,ita yake kalla da shanyayyun idanunshi masu dauke da wani irin magadisu mai qarfi da tasiri,yana kallon yadda cikin kwana biyu fatarta ta skma sauyawa tana wani qyalli,ko idanunshi ke mashi gizo?,ya tambayi kansa,shidai yaga sauyi qwarai tattare da ita,kawar da kanta tayi,saidai sunan yayi mata dadi har cikin ranta,cikin qaramin lokaci ya soma saukar da sanyi a ranta,shima sai ya dauke nashi kan,ya taka zuwa inda mayafinta yake ya dauko,ya iso gabanta,sai ji tayi ya soma yafa mata yana fadin
"Idan baki shirya takawa da qafafunki ba,am ready to carry you,komai ta fanjama fanjam" dan qanqani daga cikin aikinsa kenan,hakan ya sanya yana gamawa ta motsa tayi gaba yabi bayanta.

        Kamar jiya haka suka rankaya su ukun baki daga,saidai ita bata dawo bangaren nata ba sai wajen qarfe biyu,bayan ta bada saqon abubuwa da take ganin tana da buqatar amfani da su,bayan ta kammala sallar azahar din dakinshi ta haura,dai dai sanda su'ad ta fito cikin heavy makeup,idanunta manne da sun glasses da cogen takalminta tana karkada muqullin mota tare da taunar chewing gum ta fice bayan ta watsawa sumayyan wani banzan kallo,kau da kanta tayi itama tana jan tsaki,ya ilahi batasan ma me yasa take kishin almustapha haka ba.

        A yamutse ta tadda dakin,ita ta gyara kowacce kusurwa ta dakin,ta dauko sabon zanin gado ta sauya,ta gyara toilet,ta hada dukkan under wears dinshi ta tsaftace da hannunta ba tare da taimakon washing machine ba ta shanya cikin toilet din,tana saukowa aka kawo mata saqon,ta amsa ta nufi kitchen kai tsaye.

       Lafiyayyar sakwara ta shirya tare da water leaf soup,wadda taji ganyen water leap,ogun,ganda,tsokar na da stock fish,blander ta jawo ta niqa aya da kwakwa da dabino ta hada lemo ta sanya a fridge,nono mai kyau da aka siyo mata ta hada da fura ta dama bayan ta wats kwakwa a ciki ta saka shima cikin fridge,sai data tabbatar da kammaluwar komai sannan ta rufe kitchen dinta da key,don bata mance rayuwar da sukayi da fa'iza ba,wuyat data sha kasancewar kitchen dinsj daya,kalanzir gishiri,suger duka a girkinta,murmushi ta saki tana rayawa a ranta,duniya labari,ko ina fa'iza ta shiga yanzu ohi,Allahu A'alamu.

     Lokaci ta bata sosai a toilet tana murje jikinta,ita kanta mamakin yadda fatarta ke sheqi da laushi tayi,saidai tana ganin kayan gyaran jikin data yi amfani da su ne suka amsheta,kwalliya tayi maras yawa saidai ta dace da kyakkyawar madaidaiciyar fuskarta,ta sake kuma fito da armashin kyanta,ta jima tana saqe saqen wanne kaya zata saka,wando ta ciro belted high top wide leg trouser ash colour ta hadashi da long sleeve t.shirt fara qal wadda aka yiwa adon ash daga wuyan rigan zuwa qasanta,kisonta ta raba jelar gida biyu ta kama kowanne da qaramin ribbom ash,ba qaramin kyau tayi ba,duk wani tudu da kwari na jikinta ya fito turarukanta na musamman tayi amfani da shu,wadanda qamshinsu ke tashi a hankali har su gama cika hancin mutum,kwalabar turarenta babba ta dauka bayan ta kammala komai,ta zira wani irin plate din farin takalmi mai taushi ta soma bin duk inda burner take a gidan tana zuba turaren,a haka har ta qaraso falon.

        Tana durqushe kusa da burner din dake bakin matattakala tana zuba turare a ciki taji an bude qofar sashen,batayi tsammanin ganin kowa ba hakan ya sanya ta fito haka,a nutse ta juya,almustapha ne a gaba su'ad na biye da shi
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya ambata yana lunahe idain nasa sanda idanunshi sukayi tozali da nata,karon farko da ya soma ganinta cikin suturar da ta bayyana duk wani structure ta jikinta,su'ad dinma idanuwanta na kanta,mamaki da kishi suka cikata,take wani bacin rai ya lullubeta,dama yarinyar tasan sanya ire iren kayansu?,ba sai an gaya mata tahowarta din nan taga shigen kayan a shagon da take siyayya acan,taso siyosu saboda tasan zasu burge almustapha kuma sun burheta itama,bugu da qari kayan sabbin design ne da suka fito sati sati uku kacal da suka wuce,amma saboda kudin hannunta yayi qasa ta haqura,kishin yanayin halittar da Allah yayi mata ya cika mata zuciya,ba zata manta ba har mai ta saya na qara mazaunai da qirji amma almustapha ya hanata shafawa,ya zaunar da ita yana gaya mata irin illolin dake tattare da irin wadan nan mayukan da kuma na bleeching,duk da bata taba bleeching ba ita,natural farinta ne,to amma ko banza yau gashi ya dauko mai abun,ita tana zaune,kewayeshi tayi ta wuce corridor dinta da zaya kaita ga dakinta kai tsaye,zuciyarta na tafasa,kamar ta shaqe kanta,ta wurga jakarta saman gado tare da tuje mayafin kanta ta wurgar shima tana yamutsa gashin kanta
"No....no,it can't" ta dinga maimaitawa tana girgiza kai,sai ta sake takowa a hankali ta dawo corridor din nata,ta tsaya tsakanin labulayen da suka rabata da hango falon kai tsaye,ta sanya hannu ta yaye labulen ta yadda zata iya hangosu.

      Tattausan murmushi ya soma sakin mata idanunshi cike taf da mayen qaunarta,ita dinma duban shi take fuskarta dauke da murmushi,duban cikin idanunshi kadai sun gamsaf da ita,wani irin qauna take ji na daban na ratsata,qwafin gwiwa game da shi take ji,ya bude dukka hannayenshi yana mata alama ta taho,sai ta noqe kai kamar qaramin yaro yaso quya cikin wani salo na daban,ya motsa bakinsa cikin muryarsa da har gobe take sake daukaka darajarshi cikin idanunta
"Don't kill me babe,taho please" a yangance ta soma takowa,sai ya kasa jiranta har ta qaraso inda yake,ya soma shima takawa a hankali suka hade tsakiyan falon,kyakkyawan masauki yayi mata a qirjinsa yana sakin wawuyar ajiyar zuciya,baisan ta taka wannan matsayin cikin zuciyarsa ba karo na biyu sai a yau ya sake tabbatarwa,qamshin dake tashi kawai jikinta ya isar masa samun nutsuwa da kwanciyar hankali,sumbarta ya soma yi a ajejjere tako ina cikin nuna zallar soyayya da shauqi.

       Cikin matsanancin tashin hankali ta saki labulen ta shiga dakinta a sukwane ta soma ball da jakarta data yar a bakin qofa
"No almustapha,no,why u r doing this" ta ambata tana dukan bango da hannunta,kana ta tafi saman madubinta ta soma watsar da dukkan abinda ta gani samanshi suna sauka qasa gami da tarwatsewa saman tiles,wannan bai isheta ba sai data dauki kwalbar turarenta ta doka jikin madubi,tunu ya tarwatse dai dai ya kuma yi silar yankarta.

        Qarar wannan fashewar kayayyaki ita ta dawo da almustapha hayyacinsa,idan dai dai kunnuwansa ke jiye masa daga dakin su'ad ne,cikin hanzari ya raba sumayya daga jikinsa ya juya zuwa dakin,hawaye shabe shabe ya sameta tanayi bayan tarwatsa gashin ta dake daure da tayi,bata damu ba tana ci gaba da jifa da dauk abinda hannunta ya kai kai ciki har da t.v plasma dake manne a bangon dakin ta kwada mata make up kit din data wawuro,riqota yayi yana ambatar
"Meye haka su'ad,hankalinki daya kuwa" yunqurin qwacewa take
"Leave me almustapha,leave me" ganin haukar tata da gasje take ya sanyashi daka mata tsawa wadda ta sanya sumayya dake tsaye falo hankalinta yayi matuqar tashi
"U r mad?!,baki ganin wai me kike yi ne?"
"I know almustapha,am going to kill my self ma gaba daya" tsatstsauran riqo yayi mata sanda yaga tana laluben kwalabar dake farfashe a wajen,ya damqeta baki daya ya hankadata saman yamutsatstsen gadonta,ranshi ya kai qololuwar baci,sai kace tabin jinnu?,yanzun nan fa suka shiga gidan tare lafiya lau,binta gadon yayi ya mata riqon tsauri tana gunjin kuka tare da yunqurin qwacewa.

         A qalla sun tasamma kashe mintuna goma a haka kafin ta soma sassauta haukan da take yi,sai kuma kuka da taci gaba da yi,cikin fargaba da nutsuwa sumayya tayi sallama bakin qofar dakin,a karon farko kenan,sanye da dogon hijabinta har qasa,waiwayowa yayi da jajayen idanunshi ya zubeta kanta,wadda ita kuma idanunta ke qarewa yadda dakin ya hargitse kallo,ko bai bata amsa ba ta soma hasashen abinda ke faruwa,ba zata manta ba,ba zata manya daren data yankeshi a hannu ba sanadin kishi
"Jeki am comming,everything will be okey" kai ta jinjina ta juya ta fice,idan da tasan ma abinda ke faruwa kenan ba zata bata lokaci ta shigo duba abinda ke faruwa ba,ranta ya dinga baci,me mata suka mayarda kishi ne?,tabbas babu halittar da bata da kishi,kishi halitta ce,kuma dole kayi kishin abinda kake so,hatta dabba tana da kishi,to amma meye amfanin hankali kenan?,meye amfanin ilimi?,meye amfanin girma da shekaru?,sai ta tsinci kanta ta mai jan tsaki data tuna zainab fa'iza karima ga kuma su'ad.

        Miqewa yayi cikin takatsantsan don ma qafanshi da sau ciki ya laluba inda suka ajiyan kayan akwatin taimakon gaggawa,ya qaraso inda take,har yau qwalla na bin idanunta,tsugunnawa yayi ya soma mata dressing inda ta yanke ba tare da yace komai ba,idonta na kanshi ta soma maganganu cikin dashewar murya,tsaf ya fahimci abinda ya jawo mata aikata hakan,baya ga kishi har labe kenan ta soma?,abinda ya tunzura shi kenan,yana jin kamar ya dauketa da mari zuciyarsa na tausarshi,har ya kammala wanke mata tsaf,yayi kama hannunta ba tare da ya dubeta ba yayi mata allurar rage radadin ciwo ya maida akwatin muhallinsa ya juya da niyyar ficewa,qam ta riqe hannunshi ciki marairaicewa
"Kada ka tafi ka barni na roqeka almustapha,kada kaje wajen yarinyar nan,duk abinda kake so zan maka" idanunsa da suka sauyi launi kadai da ya watsa mata ya sata laushi kaso hamsin cikin dari
"Sake ni!" Ya fada a tsawace,sakin nasa tayi yaja baya baki bude tana kallonshi har ya fice a dakin,a falo ya tsaya ya fiddo wayarsa ya kira ummee yace ta turo ma'aikatan nan dakin su'ad zasuyi dan wani aiki,ya gama ya maida wayar aljihunsa ya wuce bedroom dinshi.

       Har suka zauna cin abinci alamun bacin ran basu sakeshi ba,hakan ya matuqar taba ranra itama,yana zaune saman dining ya hade hannayenshi waje guda yana dubanta,qoqari yake ya saita kanshi don kada ya shiga haqqinta ko ya sanyata damuwa kamar yadda yaga kuzarinta ya soma raguwa,baki daya warmers din ta bude wanda take qamshi ya cika wajen,sai ta koma kujerar dake daura da shi ta zauna,idonta cikin nashi tana sakar masa murmushi,a hankali ta sanya hannunta saman hancinsa ta ja madaidaicin hancinsa da ya zauna das bisa fuskarshi ya qawata kyawunsa
"Me zaka iya ci ciki mu gani?,kai din cikakken bahaushe ne?ni duka ma fa nakeso ka cinye" ta qarashe maganar taba dage masa girarta,murmushi ya subuce masa lokaci guda,ya raba hannyenshi yana rarraba ido tsakanin kwanukan,abincin da ya jima baici ba kenan,kusan ya manta ma da ita a jerin abinciccika,ya maida kallonshi kanta
"Kina son miji lukuti me qiba kenan" qayataccen murmushi ta saki masa
"Idan na cinye wannan abincin duka yau anan gun zan kwana,bazan iya kai kaina daki ba" dariyar data riqe ce ta subuce mata,ganin yadda ya soma kwatanta yana shafa sumar kanshi
"Dariya kike?,ke zakiji a jikinki,don ba lallai ki iya daukan lukuti ba idan na qara qiba" kunyar maganar ta bata,sai ta soma gunqurin zuba masa abincin yana binta da kallo,komai nata burgeshi yake sake yi duk kwanan duniya,dabi'u da al'adun masu burgewa da kuma mabanbanta kullum yake sake gani wajenta,wasu ya manta da su tana tuna masa su daya bayan daya,wasu yana sane da su saidai baisan inda zaya gansu ba yau gasu cikin gidanshi a gabanshi,spoon ya amsa da niyyar fara ci,sau ta langabe kai tana dubanshu,yau wani irin abu take ji yana fusgarta zuwa gareshi
"I promise to feed you when we r together"
"Thanks" ya fada murmushin na fita a fuskarshi
"No" ta fada tana girgiza kai,ya gane mai take nufi,zuwa yanzu ya fara fahimtarta,tafi qaunar ya sanya mata albarka fiye da godiya,hakan baya rasa nasaba da muhimmancin albarkar wajenta fiye da godiyar,shima hancinta ya ja
"U r smart,barakallu fiki"
"Wa laka" itama ta maida masa,ta debi abinci ta kai bakinshi da cokali,sai yasa hannunshi ya amshe cokalin ya ajjiye
"Da hannunki nakeso ki bani" ba musu ta sanya hannun,ta miqa bakinsa yayi bismillah sannan ya soma amsa,kasa cewa komai yayi sai jinjina kai da yake a fakaice,wasa wasa sai gashi yaci leda hudu,ya dubeta suka hada idanu sai suka qyalqyale da dariya baki dayansu
"U r the best cooker apart from my mom da na sani" yabon yayi mata dadi qwarai,sai ta jangi jug na tana tsiyaya masa lemon da tunda ta fara zubashi ya zuba masa idanu,ta cika glasa cup ta kai bakinsa,ya kurba,sai ya cire yana duban cup din tare da hadiya na bkinshi
"Kunun aya?" Kai ta gyada masa,dariya ta subuce masa,yayi qas da murya
"Kinsan barnar da yake min ko?,halan kin shirya gyarota" ido ta zaro don har ga Allah batasan komai a kai ba,matsowa ya sake yi dab da ita,cikin kunnuwanta ya gaya mata komai,kunya ta sanyata sunne kai,sai yayi relax jikin kujera yana dubanta murmushi na fita a fuskarshi
"Can you remember our first night?,the day i start......." Sai ya kasa qarasawa yana dariya
"Hamza......shi ya hadani da shi,ashe gata yayimin,ya zama silar shigata wata sabuwar duniya mai qunshe da ababan mamaki da jin dadi masu tarin yawa,sai ta dire cup din tana dariya idanunta a qasa,riqe hannun nata yayi caraf yana fadin
"Saikin qarasa bani ai,kin dandana min zuma a baki kuma ki janye,u r at my side ai,nasan ba matsala ko?" Haka ta dinga zuba masa yana shanyewa,ya masa dadi qwarai da gaske,cup biyu yasha qwarara sannan ya haqura jin yadda ya qoshi,ya jima baiji qoshi a jikinsa irin hakan ba.

        Darene data kaishi wata duniya da bata taba kaishi ba,duk wani hanya data sani da wadda ya koya mata wadda ke tafi da mutum sai data masa,abinda ya sake sukurkutashi kenan,ya kuma sanyashi tafiya mai nisan gaske cikin kogin sonta.

        Suna idar da sallahr asuba ta dauke wayoyinshi baki daya ta kashe,taci alwashin maida shi mutum mai cikakken lokacin kansa,tayi alqawarin rage masa jibgin sabgogi da hidindimu da yake wuni yi,walau yana kano abuja america ko dubai,babu hutu cikin lokutansa baki daya,tamkar kuwa ta sani yau qarfe goma na safiyar zaiyi taro da dukka ma'aikatan asibitinsa dake abuja,sannan sunyi da hamza zasu je yaga gonakin da suka siya domin fara noman auduga,wanda hakan zai sake habaka kamfaninsu,tare da rage musu kudaden da suke kashewa wajen sayen zare da auduga wajen wasu kamfanoni na waje,hakan kuma zai kuma samar da ayyuka ga matasan qasarmu.

       Tana gaban mudubi tana qarasa daurin dankwalinta goma na safe sanda almustapha ke kwance saman gado yana bacci nannade cikin bargo,cikin cikakkiyar nutsuwa da kwanciyar hankali,knocking aka fara da qarfi tamkar an samu bangon dakin,barin abinda take yi tayi tana tunanin waye?,sai ta dauki turarukanta ta fesa sannan ta nufi qofar ta bude a hankali,su'ad ce a wani birkice,babu wannan kwalliyar kwata kwata tattare da ita,neman hanya take kawai zata sanya kanta cikin dakin,lura da haka ya sanya sumayya rage fadin qofar ta hanyar karo qofar ta riqeta a hannu,sauran wajen da yayi ragowa kuma ta tsaya tana dubanta
"Anty su'ad lafiya kuwa?"kallo ta watsa mata mai siffar harara
"bake nake nema ba matsa kiban waje" murmushi ta saki cikin kwanciyar hankali da nutsuwa
"Kin manta kin shardanta cewa kowa dan girkinsa ba ruwan miji da 'yar uwata?,ke kika fadi hakan,amma kasancewar nasan akwai haqqinki rataye bisa wuyanshi bazan hanashi ganinki ba,amma banda yanzun don Allah,don bacci yake,yana buqatar isashshen hutu,amma idan ya tashi na gaya masa"
"Ke baki isa ki hanani ganinsa ba wallahi" ta fada a zafafe,sai kawai sumayya taja baya ta kuma maida murfin qofar ta rufe.

        Baqinciki ya hanata aikata komai,sai kawai ta juya ta sauka tana laluben wayarta ta nemi almustaphan kawai,saidai kash ta buga rashin sa'a tunda sumayya ta jima da kashesu,batayi tsammanin ya farka fa,saidai tana waiwayowa suka hada ido da shi,yana zaune daram yana kallonta,hannunsa ya bude mata fuskarshi a dan tsuke cike da miskilanci,a nutse ta iso gareshi ta fada jikinsa a tausashe ya maida hannu ya rufe
"Hausa girl" ya rada mata a kunneta,shigar atamfa tana mata kyau tana kuma burgeshi,dalili da ya sanya take yawanyi itama kenan
"Meyw dalilin kashemin wayoyi,sannan aka qi tashina?,kina son na soma halin da ba nawa ba karya alqawari?" Ya fada har yanzu tana jikinsa,kai ta girgiza
"You need some rest"
"I know,kuma nima bansan fitan,ya kamata ace idan nazo qasata ina hutawa sa iyalaina kadai basai wani sabgar ya shigo cikin wadan nan lokutan ba,sai yanzu na gane muhimmancin hakan.....amma duk da haka zanje meeting da ma'aikata a asibiti,so ki shirya,zaki min rakiya?"kai ta gyada masa,sosai taji dadi,ko banza zata miqe qafa,tunda tazo banda gidan anty dije bata je ko ina ba
"Ok,shirya min ruwan wanka"
"Jiranka ma yake" ta furta itama cikin salon rada,sai ya matseta cikin jikinsa
"Kina son hanamu fitan ma kenan baki daya ko?" Da sauri ta girgiza kai tana dariya,don tasan me tayi masa
"Dagani to" ya fada yana dubanta,ta janye jikinta a hankali sannan ya miqe ya shige toilet din.

        Tare suke saukowa baki dayansu,cikin shigar cikakkiyar bahaushiya take,plain zani da riga fitted,tayi daurinta das biasa kanta,lullubinta har saman ka,yayin da ya kasance shi kuma cikin yadin kufta da aka yiwa aiki irin na gidan sarauta,cikin kayan da ya bayar ayi masa tun daga randa ya fahimcu ire iren shigar na burgeshi,
"Wait" ya fadi yana nufar wajen su'ad,gefan kujera ta samu ta zauna tana tsumayinsa.

       Fitowarta daga wanka kenan daure da towel,tana ta qamshin shower gel dinta mai matuqar tsada da take amfani da shi duk din saboda tattalin fatarta,ranta a quntace yayi sallama,ciki ciki ta amsa shima don tasan yadda suke qarewa da shi idan bata amsa ba,abu na farko data fara shine qorafin taje wajensa sumayyan ta mata rashin kunya,ta kira wayoyinshi kuma a kashe,bai ko tanka mata ba ya duba ciwukan nata
"Suna zafi har yanzu?"kai ta girgiza tana tabe baki,ya qarasa bakin mudubinta ya ajjiye mata kudi
"baka ce komai ba na maka magana but ka share" ita batasan bacin ran mutum bane?,a nutse hannayensa cikin aljihunsa ya dawo inda take tsaye
"Bakisan abinda kika aikata jiya ba dai dai bane?"kafada ta daga
"to sai me,kishinka nake kuma dole na nuna"idanunshi ya zuba mata wanda ya sanyata rusunar dole ta janye nata idanun,cikin bacin rai yace
"Wannan ba kishi bane hauka ne,kin dauki aqidar da ba taki ba kin yafawa kanki?,daga ranki ya baci saiki hau yanka kanki koki yanka wasu?,zubar jini wannan baki daukeshi a bakin komai ba?,zan miki warning na qarshe,kinyi na farko kinyi na biyu,kada ki yarda ki sake na uku,if not zan dauki mataki a kanki,take note" ya fadi yana juyawa ya fice a dakin,tabbas ba qaramin illa baqin al'adu ke mana ba da yaranmu,sai yaji baki daya zaman wata qasar bashi da fa'ida karon farko a rayuwarshi,ya tabbatar sanda suna zuwa islamiyya a america da su'ad bata yaye kanta ta daina zuwa ba wasu halayen nata ba zasu ta'azzara har haka ba.


Wajen ummee suka fara biya,cikin farinciki ta tarbesu suka gaidata,farinciki fal ranta,yau almustapha ne ya kusa dosar sati biyu a abuja bai nemi komawa inda ya fito ba,wanda ta tabbatar da da ne da tuni ya koma din,a qalla ma yayi kwanaki uku kacal,sallama suka yi mata ta rakasu da addu'a suka fice,suka gaida anty mama sannan suka wuce,don baba ranar baya nan,sun fita shi da su mahmoud angwaye.

         Kana ganin asibitin kasan nashi ne,baida maraba da na kano har tsarin ginin,tun a hanya yake karbar gaisuwar ma'aikata manya da qanana,yana riqe da hannunta har suka shiga babban office dinsa,ya mata mazauni kan daya daga cikin kyawawan kujeru masu siffar duniya dake office din,baki daya ma'aikatan asibitin ba wanda baisan da zuwanshi ba,hakan ya sanya kowa ke cikin taitayinsa,landline dake office din yayi amfani da ita,aka tabbatar masa da cewa duk wanda ya dace yana babban dakin taron dake asibitin suna jiranshi,ya ajjiye wayar yana dubanya,itama shi take kallo,yanayin jagorancinsa na burgeta,yasan abinda yakeyi,komai nashi kan doka da tsari yake
"Zanyi missing dinki na kusan two hours,ko zaki rakani muje muyi meeting din mu dawo?" Hakanan taji tana sha'awar binsa,murmushi ta saki tana gyada masa kai,hakan ya masa dadi,ba musu ya kama hannunta bayan ya dauki laptop dinshi da yake ajjiye record na komai suka wuce.

       Cikin girmamawa ma'aikatan suka miqe baki dayansu,bai tsaya ko ina ba sai kan babbar kujerar da take tashi ce shi daya,janyo mata ita baya yayi,ta dubeshi sannan a hankali cikin nutsuwa ta zauna,daga kai yayi ya baiwa kowanne damar zama kowa ya koma mazauninsa,laptop dinsa ya bude a gabanta ya kunnata,yana tsaye kan sumayyan har komai ya daidata,wani cikin ma'aikatan ya miqe yana daukan kujerarsa ya kai masa,hannu ya daga masa yayi qaramin murmushi yace ya barshi ya gode,tsaiwan ma is ok,a hankali suka soma tattauna abinda ya tarasu,tsahon wasu mintuna,ya waiwaya da niyyat soma shigar da abubuwan da yake buqata,a fakaice yake dubanta cikin mamaki,tuni tayi misa wajen shigar masa da muhimman batutuwan,cikin qwareea da nutsuwa,baisan ta iya sarrafa computer haka,saboda bai taba ganin ta taba masa tashi ko ya ganta da ita ba,kawai sai ya dora hannunshi saman nata hannun dake kan madannan computer din ya dan matsa a hankali alamun dariya,murmushi ta saki ba tare data dago ba taci gaba da abinda take.






*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



9⃣3⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*ya Allah ka sanya farinciki a zukatan musulmai,ya Allah ka wadatar da talakawan cikinsu,ya Allah ka qosar da duk wanda ke cikin halin yunwa,ya Allah ka dawo da matafiyanmu lafiya,ya Allah wanda bashi ya masa yawa ka biya masa,ya Allah ka tufatar da wanda ke cikin tsiraici,ya Allah duk wanda ke da mummunan hali cikin musulmi ka gyara mana halayyarsa,ya ubangiji dukka wanda yake cikin tsananin baqinciki ka yaye masa*

*ya Allah*

*ka fada cikin qur'aninka mai girma*

*idan bayina suka tambayeka game da ni kace musu lallai ni makusanci ne*

*ya Allah*

*kai kayi umarni da mu roqeka(zaka amsa mana),ka kallafawa kanka amsawa(addu'ar bayinka),ya ubangiji ka amsa mana,ka biya mana dukkanin buqatunmu,ka cika mana burikanmu ya ARHAMAR RAHIMIN*
_____________________________________

         Ya jima zaune saman table din office din yana duba yadda ta shigar da komai a tsare,wani abun ma da shi bai taba yunqurin dubashi ko shigar da shi ba,murmushi ne keta fita a fuskarshi,ya dauke idanunshi sanda ta fito daga bandaki bayan ta daura alwala

Please Login or Register in order to submit comment