Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saqonni ya bude kana ya tura mata dukkan wayoyin gabanta
"Su'af bata yi arba'in ba baban yarinyar da na yiwa aiki ambassadorn nijer yake min tallan 'yarshi,duba qasa bayan shi ga saura nan,mutane iri daban daban,ba wadda idan nace ina so za'a hanani,so kike na dauko wata cikinsu dolen dole na kawo rayuwarmu?" Kuka ta fashe da shi qwarai fiye dana dazu,tausayinsa da tausayin kanta ya kamata,tabbas gashinan har da hotunan wasunsu
"Kayi haquri don Allah man kayi haquri,wallahi na daina,ina son cikina ina son abuna,kuskure ne" sai tausayinta ya kamashi ganin yadda yake take kuka haiqan,hade hannayensa yayi waje guda yana dubanta
"Yanzu ya kike so ayi,a cire miki cikin?" Wata harara da batasan da ita ba ta watsa masa
"Wallahi banaso ina son abuna ba wanda zai cire min" a zahiri da ranshi ba'a bace yake ba tabbas dariya ce zata zo mishi,amma da yake yana cikin bacin rai sai harar tata ta saukar masa da sanyi cikin zuciyarsa,ya lumshe idanu sannan ya ware mata hannayenshi,tamkar jira take sai kuwa ta taso da hanzari ta fada ya rufeta ruf ta sake narkewa da wani salon kukam
"Relax baby...relax" ya fada yana shafan sumar kanta dake fake waje guda,a hankali kukan ya ragu ta soma sauke ajiyar zuciya
"Kace musu kana so?" Ra furta a hankali
"Suwa?" Ya tambayeta yana dan tunani
"Au" ya fadi bayan ya tuna,sai ya sanya dariya har sautinta na fitowa,wato wani kishi da da can bata da shi a yanzu zata koya
"Bance musu ba,amma indai kika sake cewa bakison baby na dake jikinki to ki tabbatar zan auro saliha tayi ta haifo min yara iya yadda nakeso..." Bai qarasa ba ta cika masa kunne da kukan shagwaba
"Sorry sorry....bazan sake fadi ba indai kema baki sake ba" ya fada yana dariya tare da sake gayyatota zuwa cikin jikinsa tayi lamo tana dariya ciki ciki,kusan tare suka sauke ajiyar zuciya kowa najin wani nauyi na sauka daga qirjinsa,saboda ba qaramin kewar juna sukayi ba,ba wanda bai jigata ba cikinsu dauriya kawai sukayi,a ranan an biya bashin soyayya qwarai,dama ance fushin masoya hutu ne.


Rayuwa mai cike da tsafta da ingantacciyar soyayya ke gudana cikin gidan,gida ne da suka ginashi cikin so qauna da aminci,kowanne farincikin dan uwansa shine nasa,dukkansu kowa ya qoqarin ganin ya kyautatawa dan uwanshi,sai da cikinta yayi wata biyu cif sannan suka daga dubai da kyawawan 'yan biyunsu,sun tafi sun bar mutane da kewarsu,a can dinma gida ya saiya musu mai dauke da falo daya kitchen mai girma da corridor biyu,daya dakunan baccinsu shi da sumayyan,daya kuma na yaran da spare din wani guda,a nan dinma ingantacciyar rayuwa suka shimfida,duk abinda yakeso shi take masa,kaman yadda duk abinda takeso shi yake mata matuqar bai saba dokar shari'a ba.



***** ***** ****** *****
******* ****** *******



       Qatuwar harabar gidan dattijon tsohon professor muhammad mukhtar wanda aka sake sauyawa ginin gidan fasali qawace yake da nau'o'in ado kama daga yadiddika balan balan da launin qwayaye iri iri,kujerun zama da tebura ma alfarma,carfet carfet da ka qawata wajen,iya ganinka yara ne ke sha'aninsu wadanda ba zasu gaza shekara biyar zuwa qasa ba,sai kuma manya jifa jifa wadanda 'yan uwa ne na jimi,daga qofar iya wajen da aka tanada saboda sha'anin makeken hotone na amataullah da amatur rahman,yan biyu kyautar Allah,'ya'ya ga doctor muhammad mukhtar,hamshaqin attajirin nan wanda ya mallaki kamfanoni na sarrafa abaya da mayafai a qasashen duniya daban daban,babban mai noma auduga afadin nijeria,mutum da ya mallaki manya manyan gidan marayu da gajiyayyu wanda babu irinsa a fadin africa dake taimkao ga wadan nan mutane,mijin macen data zama haske wa al'ummar nigeria bama yankinta arewa kawai ba,matar data mallami centers na koyawa mata sana'o'i,centers na horar da yara 'yammata matasa,macen data shahara wajem gina makarantu da masallatai,matar data yi fice wajen samar da maqabartu,tallafawa tsofaffi da masu rangwamen gata wato hajiya sumayya sulaiman abdu,sannan jikoki wajen dattijo mai cike da dattako da karamci,tsohon ambassador muhammad mukhtar gwambe,yau rana ce ta musamman wanda ilajirin jikoki da 'ya'ya wanda suka fito daga barin familyn mukhtar na uwa da uba,da kuma na abokai,da duk wanda ya hada alaqa da sumayya dukkansu suna gidan,rana ce ta murnar zagayowar ranar haihuwar amatullah da amatur rahman,wanda suke cika shekara uku da haihuwa,duk yara matan dake wajen suna sanye cikin dogayen riguna fara qal da aka yiwa don baqi wanda kyauta doctor almustapha ya bada a rabawa suk wanda ya halacci wajen,mazan ma jallabiya ce ta maza fara qal da baqin hirami a kansu,wajen yayi kyau matuqa da irin adon da aka masa na fari da baqi,shewa yaran suka sanya sanda aka iso da qaton cake din 'yan biyun cikin kwali aka sanyashi a muhallinsa aka budeshi jiran fitowarasu kawai ake.

        Daga daya bangaren yaran suka fito,sanye da gown golden mai adon baqi,ta cikin tsahonta ya kai gwiwa mai gajeran hannu,sai ta saman mai dogon hannu,kallo daya zaka muau idan bakasan au wayw iyayensu ba kace daga jinsin karabawa aka dauko su,sun kwashi kyau ta kowanne bangare,sunyi kyau matuqa da gaske,takalmin qafarau kawai abun kallo ne,kana dubansu kasan sunji gata iya gata,daga bayansu kuma hajiya sumayyace dauke sa wani yaro wanda saika rantse usainin sumayya ne saboda kama,sanye yake cikin wando na yara three quater da baqin takalmi hightop na yara,sai farar shirt a jikinsa mai gajeran hannu,kan yaron na kwance saman kafadarta,kar kaso kaga sumayyan a lokacin tayi kyau na qin qarawa,sanye take da wani lafiyayyen lace wanda kyawunsa da tsarywarsa kadai ya isa ya gaya maka shi din mai tsada ne,peach ne mai dan turuwa,wanda aka yiwa ado d'ai d'ai da mint green,komai nata ya dace da shigarta,ita dinma kana dubanta kasan cewa Allah yayi halittar mace a wajen,wadda kyau da nutsuwa suka hadu suka nuna hutu da tsantsar nin dadin da take ciki,murmushi kawai take sakewa sanda taga yawan yaran da wajen ya tara,ciki kuwa harda yaran yaya abbakar,yaran halima da kuma yaran zainab,yaran farida huda da uwar gayya amira wadda ke cikinsu tana ta qoqarin saita wajen,sai yaran mahmoud da mus'ab mace da namiji,ga kuma yaran lamin da usman,musaddiq da huzaifa ne basa qasar banda nasu yaran saidai ayi hotuna a tura musu,baki daya wajen ya rude da hargowar yara badon komai ba sai hango boss dinsu amatur rahman,yarinyace mai tsokana rawar kai da surutu,itace usaina saidai tafi 'yar uwarta iya komai,saika rantse itace babba,kusan duk yaran dake wajen dan team dinta ne,dai dai ne suke sabga da amatullah,itakam zamu iya cewa tayo gado ne,gadon miskilanci rashin son magana da shiru shiru,hakan ya sanya amatur rahman ta rainata qwarai,don ma maibi musu ,a hakan ma sumayya tayi tsaiwar daka a kansu,wani lokaci MUKHTAR wanda shike bi musu wanda yaci sunayen mutane biyu shike shigarwa amatullah din,suna kiranshi da qarami yayin da almustapha ke kiransa da aboki,amatullah da amatur rahman kuma daughters,idan daya zai kira zaya ce daughter,qaramin dake hannun sumayya kuma shine MUHAMMAD mai sunan baban professor suna kiranshi amir.

      Cikin lokaci qanqani aka soma gabatar da bikin birthday din,wanda yayi masifar qayatarwa,yara sun wala sunyi farinciki qwarai da gaske,a qalla sai magariba sannan suka soma haramar tashi,masu tafiya aka fara zuwa daukansu,masu kwana cikin gidan kuma kowa ya shiga ciki.

       Bayan amira wadda kwana zatayi ra saka duka yaran mata sunyi wanka sai ta fice zata wajen ummi ta bawa qaramin yaronta nono,wanda yaranta biyu,babbar itace farha sai qaramin hadim,sumayya ta bari da su tana tsakiyarsu tana fama da su kan kowanne ya nutsu,mai cin abinci yaci mai kwanciya ya kwanta,wahalar da ita suke sosai don amatur rahman ta hada gang sunata tayi,miqewa tsaye tayi kawai tana kallonsu
"Wannan yarinya halan fitinar amira ta dauko ne?" Ta raya haka cikin zuciyarta,qaramar dariya taji an saki a bayanta,hakan ya sanyata waiwayowa a hankali,almustapha ne tsaye ya jingina da qofa,hannayenshi harde a qirjinsa yana murmushi da alama ita yakewa dariya,sauke hannyen nashi yayi ya fitota da hannu,don tabbas idan ya sake ya shigo cikin dakin yaran ba zasu barshi ya fita da wuri ba,ta gane sarai me yake nufi,sau ta dubi jikinta,don tunda aka tashi daga wajen batayi wanka ba,abinda take ta sauri tayi kenan kada yazo ya sameta a hakan,sai gashi bata cimma nasara ba,kafadarshi ya dage hadi da girarahi ya watsa hannayenshi yana murmushi alamun babu ruwanshi,ta nuna kanta da yatsa alamar niko?,ya kada mata kai yana nufin eh din,sai kawai ta juya ta dubi su amatallah tace
"Amatu.....ga abul_aulad" take kowa hankalinsa yayo kan qofar,kafin kace meye sun moqe aun dunguma kanshi,wayyo sumayyan ta gama masa tsiya,yau yasan ciwon kai babu fashi,idan ba'ayi da gaske ba ma duk yadda ya ciwa yau din buri bazai iya aikata komai ba,tana masa dariyan mugunta ta zame ta barshi da su,hakan ya bata damar yin wanka ta shirya tsaf,sannan a gurguje ta shirya masa abinda zaici sannan ta dawo wajensu.

       Daga bayansu ta tsaya tana kallonsu tana sakin murmushi a jejjere,babu shakka haihuwa rahama ce,yara ni'imah ce,koda shashancinsu kawai wani lokaci abun debewa zukata kewa ne,almustaphan da baison hayaniya ko kwaramniya ko qanqani yau sai gashi tsakiyar yara,ya bude musu kwalin chaculets wasu na cin gugguru(popcorn),wasu na fama da ice cream,baki daya sun bata mishi jiki,amma ba yadda ya iya haka yake biye musu,sai data gaji da kallonsu don kanta taga sun fara cakar da shi ya soma riqe kai sannan ta qarasa wajen tana masa dariya,ya daga kai suka hada ido,maimakon harar nuna ta masa laifi fa yayi niyya sai gashi ya buge da zuba mata idanu yana kallonta kaman zai cinyeta,sai data kada hannunta saitin fuskarshi,ta zauna gefan madina 'yar gidan abida ta biyu ta janyi guggurun ta soma ci,gardin madara dana zumar dake ciki na ratsata harda lumshe ido
"Madam,u r pregnant fa?kinsan yaushe nayi shi?,randa zamu baro dubai,unforgotable night din nan da kika bani"ya rada mata saitin kunnenta sanda yadda ba wanda zaiji sai su Cak ta tsaya da taunar ta waiwayo tana dubanshi,tasan tunda ya fada din mawuyacine idan ba hakan bane,saboda ba yau ya fara ba kamar wani mai gani har hanji,duk sanda yaui cikinsa shike gaya mata kuma daga qarshe ya tabbata hakanne,haka sukayi cikin qarami da cikin amir,tana son nuna alhinin dake cikin zuciyarta amma tasan sharadin yin hakan bata manta ba,yace duk sanda ta sake nuna bata son cikinsa ta tabbatar da cewa ta bashi license na qara aure ne,har yau diyar ambassador na nijer na nan,duk da an kusa bikinta idan yace yana so babu abinda zai hanasu bashi
"amma likita don Allah?"
"Na auro saliha?" Kada kai tayi da sauri
"Amir fa,shekararsa daya da rabi yanzu fa"
"Sanda kika haifi aboki shekarar su amatu daya da wata hudu,me ya sameki?" Kai ta kada
"Ba komai"
"Kada fa ki yiwa Allah butulci,kin manta sunan da ake kiranki a baya"
"Asragfurullah" ta ambata da sauri,har yau bata mance rigimar cikin qarami ba,anty ni'imah cewa tayi tana so a bata ita,tun a sannan jikinta ya sake sanyi,sai yanzu zata sake gwadawa abinka da dam adam kayan Allah
"Taimakeni ki sallami yarankin nan don Allah nima aji da ni" ya fada yana langabe kai gwanin tausayi kaman gaske,bushewa tayi da dariya don ya bata dariya,cikin wayo da dabara ta dinga kaisu daki suna kwanciya har da amir kuwa duk da dafarsa,amatur rahman kawai ta rage,ta kafe kai da fata sai an fara bude gifts da suka samu a daren,tun tana daurewa har ta bata haushi ta kai mata duka,tako sameta cinya da daku sosai,kuka ta saki ta soma sosa wajen yayin da sumayyan ta rufeta da hargowa kaman zata sake kai mata wani dukan,kallonta kawai almustaphan yayi sai ya dauke kai,ya janyo amatur rahman din ya yaye rigar jikinta,abinka da farar fata wajen kuwa yayi jazur sosai,shafa mata wajen ya aoma yi yana hura mata cikin salon nusarwa yace
"Ba'a yiwa mama musu da taurin kai,haba amatu...ke da kike babba....baku ganu su ikram da su affan duka kin girme musu kuma sun tagi sun kwanta,baki son mama ta huta ne itama?" Kai ta gyada alamar tana so a sanyaye
"tun jiya mama bata zauna ba uhm,ki bata haquri kuce ba zaki daina ba" a sanyaye ta dubi sumayya da tayi kicin kicin da rai,ranta na wanu irin baci,wanda abinda tayi mata baikai bacin ran da take ji ba,don idan da sabo da tasa ba da halin amatur rahman
"Ammi....kiyi haquri" da yake suna kiranta da sunan da abdallah ke kiranta ne,saboda duk hutu anan yake zuwa yayi,akwai sabo da shaquwa sosai tsakaninsu tamkar uwa daya uba daya,su kansun a yanzun sun dauka babansu shi ya haifeshi,an ce musu shine babbansu yana kano ne yana karatu sai ya gama zai dawo,qin amsa mata tayi sai data maimaita sannan tace
"Naji....tashi kije ki kwanta" miqewa tayi har ta soma takawa tace
"Ammi....amma yaya abdallah da yace zai kiramu bai kira ba fa"
"Ban gaya miki jarabawa yake ba baya waya sai ya gama?!" Ta fada mata a tsawace,sai ta juya sum sum ra fice zuwa dakin,yayin da almustapha ya zuba mata ido,sai da yarinyar ta fice sannan ta ja tsaki suka hada ido da shi,dauke kai yayi ya miqe ya wuce nashi bedroom din,sannan ta miqe ta bishi a baya.

       Sanda ta shiga har ya shiga wankanshi,qwafa tayi ganin ya hada ruwan wankan da kanshi kenan,abinda ya kasance aikinta ne ita keyi,hakan ya sanya ta zauna tana hade rau ta janyo wayarta ta soma neman mamanta,ba jimawa ta daga,sunyi hira sosai ta tambayeta 'yan jikokin nata tace duka sunyi bacci,suna gamawa ta katse ta kira halima suka gaisa ta hadata da abdallah wanda keta karatun common intrance za'a shiga secondry,suka gama hirarsu ta masa addu'a sannan ta kira zainab itama suka gaisa,tace gata kwance shiru gidan ba dadi duk sabida ba hayaniyar yara,gashi sabon gida suka koma sabuwar unguwa,dariya tayi tace idan zaki kwanta ma kiyi baccinku gwara kiyi,donsu yanzu haka ma sun jima da yin bacci,dariya tayi suka dan taba hira sannan ta katse ta kira nafisa,itama yaran nafisan na wajenta su biyu,sunyi hira abinsu sosai irinta qawaye kafin suyi sallama,daga qarshe ta kira yaya yahansu wadda a yanzun ta bata jari take business ba saida atamfofi,ba qaramin ciniki take ba,sosai rayuwarta data yaranta dake gidan aure ta inganta sai son barka,dai dai sanda ta ajjiye wayar ya fito yana tsabe jikinsa da towel,suka sakw hada ido ta kauda kai,dariya yake qoqarin boyewa amma ya kasa,ya sani cewa ta koyi fushi cikin kwanakin tun kafin tasan cewa tana da cikin,wanda yasan baya rasa nasaba da cikin da take da shi,kowanne ciki akwai irin yanayin da yake zuwa ma mace da shi,yadda ta hade rai ya sanya dariyar fitowa a dole,sai ta juyo ta dubeshi take ta saka kuka kaman qaramar yarinya,dariya yake sosai ya ajjiye towel din ya tako zuwa inda take
"U r craying like a baby,ko qarami bazayayi irin wannan kukan ba,wai mema aka miki,you beat my daughter bance dake komai ba,shi ya bata miki rai ko kuwa?"
"Wallahi hancina kakewa dariya" ta fada taba shafa hancin wanda sai yanzu taji alamun ya bude kaman cikin 'yan biyu,wata dariyar ce ta sake hardeshi,yayin data qara volume na kukanta,ganin tana kukan bilhaqqi ya sanya ya fara damunsa,sai ya sassauta dariyan ya tako gabanta,kan gwiwoyinshi ya durqusa,yasa duka hannyenshi ya kama kunnuwansa yana cewa
"Is ok...am sorry...am really sorry babe,idan baki huce ba kimin duk hukuncin da kike so" sai ta fara sassauta kukan tana kallonshi,tsahon minti biyar kafin tace
"Labari zaka ta bani har na awa daya" dariya ta sake kamashi wannan karon ya maidata,yasani sarai mugunta ta shirya masa,ra ina zai iya surutu na awa daya ai da sai yasha magani,sai ya narke mata kalan tausayi ya sanya tafin hannunshi duka biyu a kumatunsa alaman tagumi
"Wayyo ummina....kina ina ana punishing dina"salon yadda yayi maganan dole ya baka dariya,sai data daara sannan ta maze
"ba ruwan ummi a nan,ita ta aikeka kayi tsokana?....so tunda karanta labarai ya maka tsauri sai kayi kamun kunne ko tsallen kwado wanne yafi maka?" Hannayenshi ya hade waje daya yana jujjuya kai
"Almustapha yau kaga ta kanka wallahi,ka tabo uwar biyun nan" idanu ta zaro
"Wa ya gaya maka 'yan biyu zan haifa?"
"In sha Allahu,kisa ido ki gani,zuwana umara na qarshe kafin ki samu cikin su na roqa,kuma nasan in sha Allah Allah ya amsa" harararshi tayi,sai ya saki dariya ya miqe yana dagata
"Kinga....naga labarin babba ne,muje kiyi wanka kizo kiji" shi ya rakata ya kuna tsayata ta gama wankan suka dawo dakin tare.

     Tana jikinsa yana daddanna cumputer yana,bangaron hotunan dake cikin cumputer din hannunshi ya kai,hotunansu amatallah ne amatur rahman aboki da amir,hutuna ne kala kala,wasu cikin gidansu,wasu a makaranta,wasu bakin ruwa wasu sanda suke fita shan coffe,wasu kuma a wasu park park da ya saba kaisu duk qarshen sati idan bai samu dama ba kuma bayan sati biyu ko sumayya ta debesu su fice,da yake dubai gari ne da suke da yawan wajen shaqatawa sai wanda ka zaba,yana son yaranshi qwarai,yana son moment din,sanda zai kaisu wajen wasan yara,ya zauna daga gefe guda yana lura da duk motsin kowannensu,yana musu hoto ko vedios,yana kalla yana murmushi,bashi kadai ke ganin kyawun yaran nashi ba,kowa cikin dangi yana fadan haka,sun fita daban,haka tarbiyyarau abar kwatance ce da misali,duk da zamansu a baquwar qasa hakan baisa sunyi sakaci da tarbiyyarsu ba,hankalin su na tashi qwarai ko yaya suka ga wani canjin dabi'a a wajensu har sai sun tabbatar sun gusar da haka,sai da ya gama kallon tana tayashi suna tattaunawa ko halayen kowanne cikin yaran nasu sannan ya fita ya soma nuna mata wasu sabbin estate da ya gina cikin abuja,sai da ya kammala tsaf sannan yace
"Daya naki ne,akwai kudi da na saka miki cikin accnt ki duba" idanu ta zaro zatayi magana,sai ya dora hannunshi kan lebansa
"Kada kice komai,a duk sanda kika haihu nayi yunqurin yi miki kyauta sai kice a'ah,wannan karon kam kada ki hanani kuma kada kice komai" qwalla ce ta cika a idanunta,sai ya soma share mata yana murmushi tare da cewa
"Kin cancanta,kinfi qarfin komai a wajena" godiya tayi masa sosai da addu'a mai bala'in shiga zuciya da ratsa jiki,bayan ya gama amsawa ya sake cewa
"Akwai abinda nakeso a yuwa su'ad da mukhtar,abban abdallah"
"Sadaqatul jariya?" Ta tambaya da sauri,murmushi yayi yana dubanta
"Eh....dama nasan abun yana ranki,na sanya wani yaro sharu ya binciko min qananun hukumomi dake kano gwambe katsina da jigawa wadanda ke buqatar ruwan sha,masallatai da makarantu,zamu gina Allah ya sanya ladan a mizaninsu,muma zanyi mana,saboda halin rayuwa,duk da gidajen marayu dana gina,da qungiyoyin da tallafi da nake badawa hakan bai gamsheni ba,zamu qara sabida mu tadda kyakyawan guzuri a lahaira,ke ni ummi baba malam har da anty maamaa" kuka ya qwace mata,ta rasa da bakin da zata masa godiya,wanne irin taushin zuciya gareshi haka
"Allah yayi maka kyakkyawan qarshe,ya rabaka da iyayenka lafiya" addu'arta ta qarshe da shi kenan,idanu ya lumshe yana amsawa don ba qaramin dadi addu'ar tayi masa ba
"Na gama shirya komai,in sha Allah za'a bamu abdallah da zarar ya gama junior secondry a dubai zaiyi senior da jami'a baki daya har sanda zaice karatu ya isheshi" murmushi ta saki tana goge hawayen farinciki
"Danka ne noor,duk yadda kayi dai dai ne"
"Ina son abdallah baby...Allah ne baiyi zai fito daga tsatsona ba,ina jinsa kaman dana na ciki na" murmushi kawai take,ko yanzu babu abinda abdallah ya rasa banda mahaifi wanda ya haifeshi,amma a rayuwarshi saidai ya yiwa wani ma,kafin tace komai wayarta dake gefe ta dauki ruri,sunan zainab kano ke yawo,ta miqa hannu zata dauka ya rigata daukar ya kashe wayar tana kallo
"Time dina ne,na tsani abinda zai dinga shiga tsakanina da ke,banson abinda zai dinga hanani kallonki" murmushi kawai tayi,tasan da biyu yake fadin haka,ta rasa me yasa duk mutanen da suka munana mata yafi riqar zainab akan kowa,bai hanata tayi mata duk abinda tayi niyya na alkhairi ba amma baison tarayyarsu ko kadan,zainab ce ke kiranta wadda sun hadu da ita ne randa ta qaddamar da bude qungiyar ta ta taimakon nakasassu da masu buqata ta musamman dake cikin gidan yari wanda zainab na cikinsu,ranar tayi kuka tayi kuka wanda hakan ya sake bata ran almustapha kaman yadda zainab din itama tayi kuka kaman ta cire idanunta,zainab ce babu qafafu biyu,tana rayuwar tantal bataiti,bata da cikakken wajen zama,mamarta baqincikinta ya kasheta,babansu ya koma qauyensj bayan ya aurar da qannanta,danta nafi'u kuwa an saceshi an nemeshi sama da qasa an rasa,daga bisani bincike ya tabbatar masu yankan kan data so saida abdallah ne da basu sameshi ba suka ce ba zasu haqura ba tunda ta saka musu rai suka daukeshi suka salwantar
"Ba za'a sake ba yallabai in sha Allah" ta furta tana murmushi,sai ya saki murmushin shima,ya janyota jikinsa sosai yana shaqar qamshinta wanda ko tafiya yayi yana daya daga cikin abinda ke tsaya masa game da ita acikin ranshi.

       "Ranar lahadi zamu wuce kano da duka yaran nan a maidasu gida,sabida birthday kin dauko musu yara haka kawai...tab..wallahi nikam bani iya barin yarana su motsa nan da can" duban idanunshi take tana dariya,Allah ya zuba masa qaunar yaranahi,inda Allah yayi taimako hakan bai sanya sun sangarce ba yana tsawata musu da nasiha idan sukayi ba dai dai ba,cikin salon tsokana tace
"Wai da zan barsu nan gidan wajen ummi ma idan zamu koma ko na kai wasu kano wajensu zainab"
"Allah ya baki sa'a" kawai ya fada yana kashe system din ba tare daya dubeta ba,hakan ya bata dariya sosai
"Ni na isa?,tuba nake yallabai,Allah ya taimakeka,da kai da kaya ai duka mallakar wuya ne,ko ni kaina banda iko da kaina sai abinda ka zaratar" wani juyi yayi cikin zafin nama ya juyeta qasa ya danneta yana duban qwayar idanunta,itama shi take kallo kowannensu na fidda murmushi,suka soma musayar numfashin juna
"Sai yaushe zaki daina kambamani ne haka,farinciki da umarni na ne ko yaushe gaba da komai naki koda baki so"cikin siga ta rada da muryarta mai tsananin laushi tace tana girgiza kai
"Babu wannan ranar,banganta ba noor....mijine kai na musamman daya tamkar da miliyan.....inaso naci gaba da kasancewa Mace ta gari a gareka,na shiga qabarina kana mai yarda da ni"
"Kin dade da amsa wannan sunan baby.....a mace ta garin ma keta musamman ce...,da mutum na bawa dan uwanahi mutum aljanna tun a duniya da tuni na baki sunayyah!,na godewa Allah da ya sanya kika zamo cikin KUNDIN QADDARATA"fari tayi da idamunta cikin tsantsar farinciki da jin dadin lambar yabo da cikakkiyar yardar data samu daga mijinta tace
" nice da wannan godiyar MY MAAN,NA GODEWA ALLAH DA YA CIKA KUNDIN QADDARATA DA ZALLAR FARINCIKI DA SAMUN MIJI NA GARI KAMAR KAI,YA SAUYA KUKA NA YA KOMA DARIYATA,FARGABATA DA RASHIN TABBAS YA ZUWA YAQINI DA CIKAKKEN TABBACI"dariyar zallar farinciki ya saki yana sake qanqameta
"indai haka ne saidai muci gaba da damqawa junanmu zallar qauna soyayya da yarda,mu kuma yi addu'ar haduwarmu a aljanna ki zame min jagorar mata na ta gidan aljanna" kai ta jinjina tana sake shigewa jikinsa tana jin wani aminci gewaye da da dukkan rayuwarta
"INDAI HAKA NE INA MANA FATAN HADUWA GIDAN ALJANNA"
"allahumma amin ummu aulady"ya furta cikin zafin nama yana hade bakinshi da nata ya shiga aika mata saqonni,nikam nace Allah ya bar qauna na fice na bar musu dakin,a bankali na fice daga gidan ina musu bankwana dasu,tare da musu kyakkyawan fata har zuwa qarshen rayuwarsu,da ci gaba samun dawwamammen farinciki.

*SABO TUREKEN WAWA,KOMAI YAYI FARKO YANA DA QARSHE BANDA IKON ALLAH*


Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki wanda ya banbamta tsakanin bata da shiriya,ya bambanta tsakanin haske da duhu,tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban talikai annabi muhammad S A W.


Ina godiya ga daukacin ilahirin fans dina,na kusa dana nesa,wadanda na sani da wanda ban sani ba,ina miqa matuqar godiyata,grouos din da nake ciki da wadanda bana ciki,jinjinata a gareku HUGUMA CONVERSATION ROOM DA HUGUMA NOVELA ROOM,haqiqa qaunar da kuke nunamin ba kadan bace,ina fatan Allah ya faranta muku fiye da tunaninku,sauran groups bazan manta da ku ba

ZAMA NA AMANA GROUP
HAUSA NOVELS NA UMAR DALHA
HAUSA NOVEL
ZAUREN BIEBIE ISAH DA NOVELS SHELF
INSPIRING STORIES
MAMAN HANEEF NOVELS
MAMAM AYSHA NOVELS
KUNDIN HASKE
HASKE FANS GROUP
DA KUMA QUNGIYATA TA

HASKE WRITERS ASSO

BAZAN WUCE BA BAN GAIDAKU BA

MAMAN KHADIJA
HAJJA
RANO
KDEEY
DA KUMA ME SUNAN SURUKATA

AYSHA DAN SABO
ALLAH YACI GABA DA HADA KAN MU

INA SAKE GODE MUKU
SIS SAHURA
SIS RUQAYYA
SIS TASH
MARIYA SB

JAZAKUMULLAH BI KHAIR

MASU SON A QARA TSHON KUNDIN QADDARATA

ina mai baku haquri,komai yayi farko dole

Please Login or Register in order to submit comment