Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsaye,shiru tayi masa kamar bata jiba,don bata ga dalilin da zai sanyata cire hijabinta ba,ransa ya soma baci da shariyarta,abinda bai qauna tsawon rayuwarsa,uhmmm wanzami dama hausawa suka ce baya son jarfa,sake matsawa baya yayi hannayensa zube cikin aljihunsa yana dubanta
"Ko kaxa baaba ya bani da hannunshi yace na kula da ita daga ranar tafi qarfin wulaqanci ko tozarci a wajena,kina neman ki hasalani nayi miki abinda banyi niyya ba ko?,kada ki yarda raina ya baci,idan kuwa ba haka ba bazakiji da dadiba,kina iya tashi ki tafi idan har ba zaki bari baaban yasan asibitina kuma gurina kika zo ba,kiyita zama da cutarki wannan ba damuwata bace" ya qarashe maganar yana daga kadunshi,hakan ya bata qwarin gwiwa ta muqe da hanzari duk da ciwon da takeji na tsikarinta,ta isa ga jakarta ta tattare kayanta ta maida ciki cikin hanzari,wanda hakan ya sabba ba mata manta hotunan mukhtar guda biyu qananu wanda suka zube ta doshi qofa abinta.

       Wata zuciya ta taso masa,tana jin bata da kunya kenan?,ita din wace?,bai manta rashin kunyar data yi masa ba randa ta bigeshi duk don yace ta dinga kula,me take da shi da take wani qunshe qunshe,taku daya biyu ya isa inda take,hannunshi ya sanya ya finciko hijabin baki daya ya fiddashi daga jikinta wanda hakan ya sanya gashin kanta warwarewa baki daya,dama daureshi kawai tayi ba tare data sanya komai ba,hakan ya tilas ta mata tsayawa cak,waiwayowa tayi da niyyar sauke masa magana kwarjininsa ya cika idanuwanta
"Mijinki ne",kalaman malam suka dawo mata,ita din ba mai tsiwa ko rashin kunya bace tun da can baya,tun daga aurenta daga mukhtar zuwa lukman,bata iya kallon tsabar idon wanda ya girme mata tayi masa rashin kunya ba,sai yanzu zata fara?,a kan dan mutumin dake qaunarta,uba a gareta babban masoyi amini ga mahaifinta,sai ta runtse idanuwa,yayin da juyawar tata ya tilastawa mustapha kau da idamuwansa daga kanta,skert ne a jikinta da riga 'yan kanti,irin masu robar nan wadanda suke bin jikin mutum,gajeran hannu gareta,wuyanta kuma v.hape ne wanda ya fidda kyawun wuyanta zuwa qirjinta
"Idan ka wulqanta sumayya ka tabbatar wa kanka ni ka wulaqanta" maganar baabaa ta dawo mishi shima kwanyarsa,dukkaninsu lokaci guda umarnin iyayensu ya yi musu linzami,lokaci guda ya sauke dukkan wani abu da kowannansu keji game da dan uwansa a zuciyarsa,hijabinta ya wurga mata ba tare da ya dubeta ba,da yatsa yayi mata nuni da gadon dake bakin na'urar scanning,bata ce komai ba ta maida hijabinta jikinta,ta taka a hankali zuwa bakin gadon ta hau,sai da ya bada wasu mintuna sannan ya soma takawa zuwa kan gadon
"Kwanta" yace mata,idanu ta fiddo har sai da ya sake dubanta,da baya ta koma ta kwanta saman gadon
"Janye hijabin da rigarki" ya sake fada yana duban wani gurin,hijabin ta janye amma sai ta kasa janye rigar,sake waiwayowa yayi yaga abinda tayi,bai ce mata komai ba ya sanya hannunshi ya dage rigar,idanunta ta runtse zuciyarta na bugawa,da sauri ya sake rigar ya koma da baya,bai iya tuna mata nawa yayi wa scanning tun daga farawarsa aikin likita kama yau,mata daga nau'in yare jinsi da qasashe daban daban,amma haka kawai yake jin wannan bazai iyaba.

        Bakin teburinsa ya isa ya soma qoqarin kiran reception ta wayar landline yana tambayarta
"Duk wata kina period dinki?"
"Eh" ta bashi masa murya can qasa cikin jin haushi da kunya
"When last kika ga period din" shiru tayi tana tunani,a qalla kusan watanni biyu kenan baizo mata ba
"Wata biyu"tabe baki yayi yana mamakin rashin damuwa da kai da har zakayi wannan watannin baka ga al'adarka ba kana zaune.

       Wata nurse ce ta shigo wadda a qalla ta kusa shekara arba'in,cikin harshen nasara da tataccen engishinsa yake gaya mata abinda zata yi duka sumayyan na jinsu sai,a ladabce ta amsa ta qarasa inda sumayyan ke kwance,yayin da shi kuma yayi lamo cikin kujerarsa idanunshi a lumshe,yanajin yadda wata gajiya da kasala ke saukar masa,bai sake motsawa ba har nurse din ta kammala ta masa bayani idanunshi na arufe yana gyada kai,idanuwa sumayyan ta fiddo jin tana zancan scanning din da ake ta qasa za'a yi mata wanda nurse din bata iya ba,qirjinta ya dinga bugawa,ta soma ayyanawa a ranta yadda hakan zata kasance,sai data bayyana bayaninta tsaf sannan ya bude idanunshi wanda suka sauya launi kadan,ya jawo wata paper yayi rubutu da baifi layi hudu ba ya miqa mata yace ta karbo masa yanzu yana jira,karba tayi a ladabce ta fice.

       Shiru ya ratsa office din sai qarar a.c dake buso sanyi tare da wani ni'imtaccen qamshi dake gauraye da office din,tana kwance wajen zuciyarta na bugawa
"sauko"ya fadi yana miqewa tsaye ya shige toilet,da hanzari ta sauko ta sanya takalmanta sannan ta dauki hijabinta ta nufi qofar,sau uku tana murzawa taqi buduwa,dole ta dawo ta zauna,wanda tana zama nurse din ta sake turo qofar ta shigo,saman teburin kawai ta dora maganin ta fice.


       Fitowa yayi daga toilet din fuskarsa da hannayenaa wanda ya nannade hannun 'yar cikin suit dinsa jiqe da lema,da alamu alwala ya daura duk da ba lokacin yin sallah bane,bai dubeta ba ya isa gaban teburin ya fidda magungunan ya dudduba sannan ya koma gaban freezer din ya ciro ruwan roba,ya balli magungunan ya zube gabanta tare da ruwan sannan ya juya ya bude daya qofar wanda ke kusa data toilet ya shige bayan ya sanyawa qofar office din baki daya key,ba musu ta kwashi magungunan ta zuba a bakinta baki daya ta kora da ruwa ta hadiye,duk yadda taje qin magani haka ta hadasu baki daya ta hadiye,wannan karon ma ta sake jarraba bude qofar don bata ga mai zai zaunar kuma da ita na saidai taqi buduwa,a gaban idanunta ya rufe ba kuma tasan yanda zata bude din ba.

       Fitowa yayi sanye da kayan da likitoci ke sanyawa duk sanda zasu shiga yin c.s,saidai nashi sun dan banbanta,saboda ash ne nasa,wanda suke a wanke fes da karin guga muraran a jikinsu,riga ce iya cinya mai qaramin hannu,sai dogon wando da hula,kamar ba kayan aiki ba sun masa kyau,qafanshi sanye takalmi plate sabanin dazu da yake sanye da ciki,qwanqwasa qofar aka soma yi baki dayansu suka dubi qofar,yana qoqarin sanya abun hanci yace
"Waye"
"Ranka ya dade Dr maqarfi ne" aka fada daga waje,takawa yake zuwa bakin qofar yana fadin
"Ki koma wancan dakin,ki dauki jakarki"
"Gida zan wuce,me zanyi a ciki?" Ta fada cikin zafi zafi,bai gasa nufar qofar ba bai kuma juyo ba yace
"Ba shi na tambayeki ba,kada ki yarda ya shigo ua ganki a nan"cikin qunan rai ta miqe ta dauki jakar tata,tana gunguni cikin zuciyarta ta tura qofar ta shige.

     Baya yi zaton ganin dakin ba haka,daki ne sosai mai dauke da madaidaicin gado wanda ya wadatu da shimfidar bedsheet fara qal bayan lallausar katifar dake kai,shimfide dakin yake da carfet maroon sai fararen labulaye,daga daya bangon kwaba ce ta glass wadda aka tsarata cike da littattafai da suka shafi aikin likitanci,saj wata iriyar hanger kai kyau ta silver ta rataye kaya,qamshi dakin yake kamar ba cikin asibiti yake ba,gefan gadon ta qarasa a hankali ta yiwa kanta mazauni gefan gadon tana kalle kalle tana jiyo maganan mutumin da ya kira kanshi da dr maqarfi a cikin office din,magana suke kan tiyatar da zasu shiga yanzu.

       Sauka idanuwanta sukayi kan wani dan qaramin frem dake zaune kan wata 'yar bedside,idanu ta saka sosai sai ta gane su'ad ce,sanye take cikin qananun kaya masu fidda sura,tayi makeup sosai tana dariya cikin hoton,kanta ta dauke tana wassafa yaya zama zai kasance tsakaninsu,tun tana karanta wasiqar jaki har bacci ya fara rinjayar idanuwanta,batasan sanda ta jingina da fuskan gadon ba yayi awon gaba da ita.

       A qalla kusan awanni biyu suka share dakin c.s din saboda mutum biyu suka yiwa,kowanne anyishi successfull,a gajiye yake saukowa daga sama inda sukeyi aikin zuwa qasa,ya sanya maqulli ya bude,ya sanya qafafunshi masinjanshi na biye da shi,da sauri ya dakata sabida tunowa da yayi tana ciki,ya karbi kayansa dake hannunshi ya sallameshi sannan ya shiga ya rufe office din,sai da ya sanya wani sabulu ya wanke hannunshi cikin wani dan sink kana ya doshi qofar dakin,yana tura qofar ta farka,idanunta ta bude baki daya wadanda suka qara girma sakamakon baccin da tayi ta zubesu fes cikin nashi,sai ya janye nashi idanun yana fadi cikin zuciyarsa
"Kaman mayya" bai taba ganin idanun da yake jin nauyin sanya nashi ciki ba ko na waye irin wadan nan idanun,hakan ya sanya yake jin haushinsu,da hanzari ta gayara zamanta daga kashingidar da tayi saboda ganinsa da ya tuna mata inda take,wuceta yayi ya nufi inda kayanshi suke da alama zai canza ne hakan ya sanyata miqewa ganin lokacin azahar yayi,da sauri ta koma ta zauna inda ta miqe din zuciyarta ba bugawa,jini ne digo digo a inda ta tashin
"Yaya akai haka?,yaushe al'adan har tazo mata bata sani ba,bayan dazun nan ta lissafa wata biyu bata ganta ba" kamar wadda aka daure haka take jinta,bayansa tabi da kallo sanda ya kwashi kayansa yana yunqurin ficewa,tamkar ta tsaidashi haka take ji,ya zatayi  da jikinta?,ya zata yi da wajen?,abinda ta dinga fada kenan har ya fice,tana jiyo sanda aka ja waccan qofar ta office dim,wanda hakan ke nuna mata ya sake ficewa ne baki daya,hakan ya bata damar miqewa da hanzari,yaye zanin gadon tayi cikin sanda ta shige toilet din dake cikin dakin da shi,bandaki ne madaidaici wanda aka qawatashi,akwai komai a ciki na amfani harda soson wanka da nau'in sabulai ma ruwa da daskararre,wata roba dake manne da tambarin klien ta bude ta zazzaga ta soma wanke wajen,sai data tabbatar ya fita sannan itama ta gyara jikinta,fitowa tayi da zanin gadon ta baje shi saman katifar don ya matsu sosai,tana qoqarin maida hijabinta ta juyo sallama cikin office din,a hankali cikin sanda ta fito,nurse din dazu ce,cikin fara'a ta miqa mata wata leda wadda ke dauke da tambarin sunan gidan abincin seven thirty tana cewa
"Gashi inji yallabai" murmushi itama tayi mata da alama matar na da kirki ta amsa tana fadin
"Na gode" har ta juya zata fita ta dawo
"Ammm,ranki ya dade ba don kada nayi shishshigi ba da na tambayeki,don Allah matarshi ce ke?" Girma tambayar tayi mata,amma saita waske tana murmushi
"Qanwarshi ce" cikin murmushi ta sake miqa nata hannu
"Naji dadin haduwa da ke,suna na nurse barira" miqa mata yi itama tana murmushin
"Ameera" sakin hannun nata tayi sannan ta fice tana murnar ganin jinin gidansu doctor almustapha.

      Ledar ta bude qamshin da ya daki hancinta shi ya tabbatar mata abinci ne,sau wata ledar wadda tana budewa taga always ce a ciki,idanu ta zaro tana mamakin yadda akayi yasan tana buqatarta,bata wani tsawaita tunani ba ta dire abincin ta ciri pad din ta shiga bandaki ta saka ta jefa saurar a jakarta,gyara zaman hijabinta tayi sannan ta rataya jakarta ta fice a office din.

       Rufe laptop din yayi cikin dakin hutawarshi dake asibitin bayan ya gama kallon duk abinda tayi din,yana iya ganin kowane sashi na asibitin a dakin hutawar tashi ta na'urar cctv camera dake asibitin,ya dire cup din coffen da ya gama sha sannan ya tattare kayanshi ya sauko zuwa qasan.

       Idanu ta shiga rabawa ganin babu motar data kawota babu alamarta,da alama ya gaji da jiranta kenan ya tafi,babu mamaki,tun qarfe tara na safe suke gashi yanzun har uku tan gab da yi,bata ga laifin drivan ba ba,haka kawai ya wani tsareta bayan bata ga alfanun tsaretan da yayi ba,hakan ya sanya ta soma takawa a hankali don taje titi ta samu abun hawa gangar jikinya da zuciyarta duka a gajiye.


Tana yunqurin fita mai tsaron qofar wanda yake dattijo ne ya qaraso cikin girmamawa fuskarsa qunshe da fara'a
"Ranki ya dade,ai ya tafine wanda ya kawoki,yallabai yace ya tafi zaku tafi tare,yace ki tsimayeshi idan kin fito" murmushi tayi cikin gajiyawa
"Babu komai zan samu abun hawa,ina sauri ne kuma bai kammala abinda yake ba" ta sake sanya kanta zata fice sai ta kuma jiyoshi yana cewa
"Ranki ya dade gashinan ya fito ma ai" ya tunkaro get din yana qoqarin bude masa,tilas ta ja birki ta koma da baya ta soma takawa zuwa wajen get din saboda yadda idanuwa suka yi mata yawa,batasan me mutanen ke kallo tattare da ita ba haka.


Gidan baya ta sanya hannu ta bude ta shige ba tare da tayi tsammanin a bayan yake zaune ba,sai data rufe qofar sannan ta ankara da shi,yana zaune hakimce abinsa,maimakon suit dake jikinsa dazun yanzun shadda ce jikinsa mai gajeran hannu,iyakarta gwiwa da dogon wando
"Zaki ci wuyar zama da ni matuqar zaki kasance mai taurin kai da rashin jin magana" ya fada cikin muryarsa qasa qasa,ta gefan idanu ta kalleshi wayarshi yaje dannawa kafin ta maida idanunta kan titi,wayar ya ajjiye gefansa ba tare da ya sake cewa komai ba.


A tunaninta zasu maidata gida ne sai taga sun canza hanya,dubanshi tayi tana sake kallon titin
"Ba nan bace hanyar" ta yi magana tana kallon titin,sai da ya shaqi isaka sannan ya amsata
"Wacce hanya kenan?"
"Gidanmu mana"
"Baki da abinda zaki koma gidanku kuyi,so kin taho kenan" idanuwa ta zaro tana kallonshi cikin mamaki,wannan wacce iriyar magana ce haka?,me hakan ke nufi?,kallon mamaki taci gaba da yi masa kafin tace
"Ban gane ba,kawai daga zuwa asibiti sai ka zarce wani gun da ni haka akeyi?"
"Haka baba yace nayi,idan kuma ni din kwartonki ne sai ki gayan" ya fadi yana balle kwalin lemo ya kai bakinsa,ci gaba tayi da kallonsa baqinciki fal zuciyarta,so yake ayi abunda ba'a taba yinshi ba cikin tarihi kenan,idan wani ya fahimta wani bazai fahimta ai,wani zai iya dauka ita ta kai kanta
"Amma ba haka al'ada ta tanadar ba ai"
"Addini fa?,me ya tanadar?" Ya maida mata amsa cikin yanayin ko in kula,bata haqura ba dai duk a qoqarinta na fahimtar da shi,duk da yadda ranta ke baci
"Ko 'yar tsana ce ai tayi sallama da mu......"
"Shut up,idan kika sake magana zaki fitarmin a mota!" Ya fada cikin hargagi wanda ya tsoratata ya sanyata yin shiru,kanta ta kwantar jikin kujerar motar,bata ankara ba hawaye suka fara bin kuncinta tana daukesu,wai me yasa ba tun fari bata zabi abdur rahman ba?,ta tabbatar da cewa koba komai da tuni tana can cikin farinciki,itakam gaskiya bata jin zata iya da wannan mutumin mai shegen girman kai izza da taqama.


Bata fahimci airphort suka zo ba sai da motar ta tsaya ya fice yana bata umarnin fitowa,binsa kawai take jiki a sanyaye baki bude,qarar wayarta ta dawi da ita hayyacinta,number malam ta gani cikin hanzari da daga
"Jirgin naku bai tashi bane sumayya?" Cewar malam din,mamaki ya cikata,me kenan?,malam ya sani ne dama,kamar yasan me yake kai kawo a ranta yace
"Drivan muntari da ya dawo ya sanar mana shi mustaphan yace abuja zaku wuce,Allah ya tsare hanya,ki riqe aurenki da kyau mamana,kiyi biyayya kiyi kuma haquri,ki kauda kai ki zama mai kara,ki ninka haqurinki,in sha Allah ba zaki tozarta ba,ni nasan ba zaki taba wulaqanta ba gidan muhtari,Allah ya tsare hanya ga mamanki"
"Daga zuwa ganin likita sai ki gudu abinki kuma?" Cewar mama cikin salon tsokana,a zaton sumayya da gaske maman take sai ta sanya kuka
"Wallahi mama ban san shine ba,bansan tafiya zaiyi da ni ba"
"Keee,a kul na sake jin kukanki,wanne irin shirme ne wannan daga tsokana?,to dama me zaki dawo kiyi?,dukka qannanki fa kowa ta tafi nata gidan"
"Amma mama ni kadaice ba'a rakani ba,banyi muku sallama ba babu"
"Sallamar me zaki mana,sannan abujan baquwarki ce da sai an rakaki,mu kuma ba gashi muna sallama ba,kibi mijinki sumayya kiyi biyayya,yi nayi bari na bari,ki girmamashi ki tuna waye shi a wajen mahaifinki,kada ki sake yayi kuka da ke" nasiha tayi mata qwarai mai ratsa jiki,duk sai ta tafiyar da wani zafi da take ji cikin zuciyarta,kafin suyi sallam ta wanke mata zuciyarta fes da kyawawan kalamai sukayi sallama,bata ajjiye wayar ba sai data kira nafisa ta gaya mata tahowarra,jin ta fara cikata da tsokanar amarya ya da biyo miji haka babu ko 'yan rakiya,sai tazo tsuma amarya wai,sai ta kashe tana kada kai,tsokana cikin nafisa ita da amira tana da yawa,anty dije ta sake laluba ta kirata ta gaya mata,bata damu ba itama da jin tahiwarta ita da shi,saima farinciki daya cikata ta musu addu'ar isowa lafiya tare da shirin tarbar sumayyan,tayi niyyar kiran amira amma ta fasa,sai kawai ta tura mata tex ta kashe wayar.


Bayan ya gama sallamar drivan ya tako a hankali zuwa inda take tsaye don batasan abunyi ba,wayarshi dake aljihu ta dauki tsuwwa,ya laluba ya cirota yana duba mai kiran,su'ad ce,shafa wajen ansawar yayi ya daga ya kara kunnenshi
"Mustapha ina tafe zuwa abuja a daren yau ba sai gobe ba,ina son kafin na qaraso ka tabbatar ka saki wannan kidahuma bagidajiyar yarinyar mai yawo a hijabi,idan ba haka ba wallahi sai na tashi abuja" tsawa ya daka mata cikin matsanancin bacin rai tamkar tana gabanshi
"Kin manta da waye kike magana?,kin manta waye almustapha?,ok.....naga alamun kin manta,amma ina jiranki idan kika iso zan tunasar dake waye muhammad almustapha" ya datse kiran cikij bacin rai,ya zuqi iska mai zafi yana fesarwa,ya kashe wayar baki daya ya jefa aljihu yayi gaba,yana jin lallai wannan karon idan su'ad batayi wasa ba zai juna mata qaramin hauka ta iya ga inda ake babban,zai koya mata darasi mai girma,binshi tayi cike da tsoro da taraddi,haka yake da fada?,haka yake da saurin hawa?,wace tayi kiransa ya dugunxuma haka?,baki ta tabe tana biye da shi koma meye ba sabgarta bace.


Wayar ta sauke daga kunnenta tana duban mahaifiyarta dakezaune gefanta,wadda itace ta karanta mata dukkan abinda zatayi din
"Nifa mom gaskiya ina jin tsoro,ina son mijina kada naje nayi abinda zai zame mana dana sani,nasan halin almustapha sarai baya daukar raini" harara ta galla mata tana huci tamkar ita aka yiwa kishiyar
"Ai sai ki zauna dan ubanki,ke yanzu ba abun kunya bane gareki ace wai an miki kishiya?,uwarki ma har ta qaraci quruciyarta har zuwa tsufanta bata zauna da kishiya ba?,ki tashi ki masa hauka ki qwaci 'yancinki,rashin qwatar 'yancin naki shi zai haifar da abinda kike tsoron na rasa mijin naki,kishiya bala'ice masifa ce annoba ce,ke kishiya ta wuce duk inda kike zatonta,ki tabbatar ya zaba ko ke ko ita,ke yarinya ce baki sani bane,inda ina da ita 'yancin da kika samu a rayuwarki da baki same shi ba,ban taba sanin hajiya kilishi da gaske har yau bata qaunata ba sai yanzu,daboda ita ta zauna da kishiya shine suka hada baki suka yi miki,dama can ba jituwa muke ba,aurenki da danta ne ma ya sake sawa muke hulda ta dole,to wallahi zata ga tsantsar rashin arziquki,ki tashi tsaye kada ki raga mata har sai kin raba tsakaninsu,sannan duk wanda ke gidan kada ki raga masa ciki harda hajiya kilishin,ku juye rashin mutuncinki son ranki,har sai kowa yayi laushi ya nemi daidaito da ke,indai nonon khaulat kika sha rainon america ce ke" kalamai masu nauyi ta dinga amfani da su tare da nuna mata cewa ba zata taba mallakar almustapha ba matuqar yana da wata matar,kalaman sunyi tasiri matuqa a kunne zuciya da gangar jikin su'ad,hakan ya sanya ta soma hada kayanta haiqan don isowa nageria ta bashi zabin zama da ita ko zama da amaryarsa,wanda baki daya haushin jama'ar gidan takeji musamman data samu labarin diyar aminin baabaa prof ce,tana jin dama can suna adawa da ita,suna adawa da zamanta da mijinta,saboda ya dauke mata komai tana juyawa da takunta yadda taga dama,ba shakka ba zata raga ma kowa ba indai akan almustaphanta ne.

To masu karatu,ku biyoni muje.







*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



7⃣7⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

___________________________________

      Bayan sun shiga cikin jirgi bata sake ganinshi ba,batasan inda ya zauna ba sai da suka sauka,cikin motocin gidan aka zo daukarsu,tana tsaye har ya shiga sannan itama ta bude ta shiga,yana zaune daga daya bangaren itama haka,motar tsit,shi yana danne dannen wayarshi yayin da ita kuma ta bige da kallon titi tamkar yau ta soma ganin garin a haka har suka qarasa.

       A hankali motar ke kutsawa cikin unguwar tasu,tana kallo suka wuce qofar gidan anty dije,kamar tayi tsalle ta fita haka take ji,saidai ba yadda zata yi,yanzun a qarqashin wani take dole,ajiyar zuciya ta saki tana sauke jumfashi,a yau a kuma wannan lokacin gata ta sake dawowa cikin gafin,saidai cikin wanu matsayi na daban,ta dawo cikin garin a matsayin matar wani kuma surukar gidan baabaa professor,ma'ajiyar motoci motar ta tsaya bayan mai gadin ya bude masu wakekiyar qofar gidan,a hankali ta sanya hannunta ta bude murfin motar bayan tsayawar motar,qafarta ta zura guda daya waje ihun amira ya karade kunnuwanta,kafin tace wanu abu tuni ta ruqunqumeta
"Wayyo amaryarmu oyoyo oyoyo" murmushi ya subucewa sumayya,da ido takewa amiran nuni da bayanta,sam bata ankara ba karadinta kawai take
"Ke matar nan kiji tsoron Allah,har an fara sanin dadin miji ko?,anty ta bani labari daga zuwa ganin doctor sai kawai ayi mai gaba daya,kodai......" Bata kai ga qarasawa ba ya fito daga cikin motar,wanda hakan ya tilasta mata sanyawa bakinta fulasta sabida kallon da ya jefeta da shi,magana ce fal cikinta amma tilas ta saita kanta,a ladabce tace
"Barka da isowa yaya"
"Sake mata hannu ko?" Ya fadi ba tare da ya damu da amsa gaisuwar tata ba,hannun ta saki tana baata fuska ta janye gefe,kafeta yayi da idanu yana mata alama data wuce yana yin gaba,binsa tayi a baya amira ta rufa musu baya,duk da haka bata haqura ba sai data tsaya saitin sumayyan murya qasa qasa
"Wannan hadi yayi kyau,Allah ka nunamin idanuwan su'ad naga ya zata yi" ta gefan idanu ta jefa mata harara amma hakan bai sanya ta fasa ba,waiwayowar musty din ne ya sanyata ja da baya tana raba idanu.

      Kai tsaye bangaren ummee suka soma shiga,a hankali suke takawa jere da junansu tamkar wasu shaqiqan masoya,su biyun ke zaune a falon ummee da maamaa,da alama suna tattauna wani abu ne,amsa sallamar sukayi kowacce fuskarta a sake,idanun umme bisa fuskarshi,shi ya soma yiwa kansa matsuguni kan daya daga cikin kujerun falon kafin ta qarasa takowa a ladabce zuwa cikin falon,kanta a qasa a kunyace ta qarasa amira na gefanta,wata kunya da nauyinsu take ji a yanzu wadda ta ninka ta da,musamman ummee wadda dama can ba wani sakewa ko sabo sosai tsakaninsu,gefe ta zauna qasan carfet kan ta a qasa
"Tashi ki koma saman kujera mana,wacce irin tafiya ce haka almustapha?" Ta tambayeshi tana dubansa,kanshi ya shafa yana yana yiwa ummeen magana da idanu zuwa sashen da su sumayya suke,ta fuskanci mai yake son fadi amma duk da haka bata fasa sake magana ba
"Babu sanarwa ba komai,halan ma baka barta ta kintsa ba ka tattago ta ko?" Inji ummeen tana bata rai,don tuni amira ta fesa mata yadda ya dauko sumayyan,cikin salon bada uziri yace
"Ummee,umarnin baba ne"dauke idanunta tayi ta maida kan sumayyan wadda suke gaisawa da anty maamaa,cikinnurmushi ta soma gaidata
"Ummee ina yini"
"Lafiya qalau ya gajiyan hanya"
"Alhmdlh" ta fadi cikin ranta tana fadin wacce gajiya gurin mutumin da yayi tafiya a jirgi
"Anty kun yini lpy?" Cewar almustapha yana miqewa tsaye
"Lafiya qalau almustapha,ashe kuna hanya babu sanarwa bare ayi abun tarbar baqi" qaramin murmushi kawai ya saki na gefan baki,bai amsa ba sai ya jefo tambaya
"Baabaa fa?"
"Ya fita,yana can suna lissafin gidajen gonar nan"
"Ok" ya fada a taqaice yana takawa zuwa hanyar barin falon,ko motsawa sumayyan batayi ba,wanda hakan ya burge ummee da anty maamaan baki daya,ta tabbatar da cewa da su'ad ce da tuni miqe ta rufa mishi baya
"Kada ka rufe sashen idan ka shiga,anjima zamu kawo amarya" inji anty mama
"Ok" kawai yace yana ficewa a sashen,kamar jira amira takeyi ta buga tsalle ta iso gaban sumayyan
"Tashi muje namecy" harara ummee ta buga mata
"Saura ki hanata sakewa kuma bare ta huta gajiyan data kwaso ko?" Dariya amira tayi yayin da sumayya ta miqe ta bita tana murmushi kanta a qasa.




Please Login or Register in order to submit comment