Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yau ba sumayya na dawo gobe,tunda yau kun zama 'yan qwadago yinin fenti kukayi" ta fada tana miqa mata ledar data shigo da ita,tana dariya ta amsa tana dubawa,ko bata ce mata komai ba ta fahimci meta kawo mata,magunguna ne masu kyau ingantattu na 'ya'yan itatuwa data saba bata.

     Sanda mukhtar ya dawo yaga aikin da sukayi cak ya tsaya,sai kuma yayi gaba ba tare da yace komai ba,qaunarta ke saka ratshi,uwa uba kuma tausayi don yasan har yau da zallar quruciya tattare da ita,inda yasan zata yi da tun sanda yace ba zaiyi ba da tuni ya hada da yimata hannunka mai sanda don kada ma tace zata yi din.

    Kamar yadda abba malam ya alqawarta mata,sati biyu da yin maganarsu kuwa saiga motar kaya,irin kayan da sam sumayya bata zata ba,kaya ne 'yan italy masu kyau da tsada har kujerun wanda ko a aurenta ba'a yi mata irinsu ba,har da qarin labulaye masu kyau da door mat,mamam naana da maman ummi ne tare da uaran gidanta suka tayata jerawa,saiga dakinta ya fito fes tamkar ma ita ce amaryar,mukhtar baiyi qasa a gwiwa ba yace har gida yiwa abba godiya,hakanan shima ba'a barshi a baya ba,kayan kitchen baki daya ya sauya mata,kasancewar yanzun an maida kitchen din bangare biyu,hannun hagu da hannun dama,kowacce anyi mata kantarta da drowers dinta,hakanan ya sauya maya plasma wadda tafi waccar girma harda qarin home thierther,sai ta dinga mamaki da yace bashi da kudi da bazaiyi lefe da fenti ba,bata ce masa komai ba tunda ta fuskanci dama ce bai gani ba,godiya ta dinga zuba masa sosai kamar yadda yake al'adarta.

     Mamanta ita ta sauya mata showglass da kayan cikinta baki daya,farinciki duk ya cika sumayyan,ta fuskanci ita 'yar gata ce sosai,batasan duk sunyi haka bane don kwantar mata da hankali da sake sa mata nutsuwa,ba qaramin kyau dakinta ya sake yi ba sai ka rantse amarya ce.





*mrs muhammad ce*



📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

__________________________

_bismilla hir rahmanir rahim_

_iza qada amran fa innama yaqulu lahu kun fa yakun_
________________________


0⃣4⃣




      Sati guda da kammala gyara gidan ranar wata litinin mukhtar ke gaya mata ran laraba masu kafin amarya zasu zo,sai da taji wata faduwar gaba da bata san ta mece ba
"Allah ya kawo su" ta fada kawai kana tayi shiru tana dubansa yana rubuta lissafin kasuwa cikin wani qaramin excercise book.

       Jin shirun yayi yawa ya sanyashi dago kansa ya dubeta,sai yaga littafin take kallo,ya sanya tsinin biron ya dan mintsini cinyarta,sai ga dago tana dubansa fuskarta dauke da murmushi tana sosa gurin
"Yadai 'yammata?" Kai ta girgiza tana murmushi
"Babu komai.....cewa nayi ai za'a yi musu girki ko,tunda naga ana yi",rai ya bata,don yasan yanzu zata fara soko masa zantukan da baiso,ya tabbatar sumayya danya ce shakaf,domin da wata macen ce aka yi mata zancan kishiya da tuni yanzu gidan ya dade da zama dan qaramin sansanin yaqi,ya tabbatar ba qaramin dauki ba dadi za'a yi ba,duk da quruciyarta ma ya tabbatar da gudun mawar qarin tarbiyya da ta samo daga gida,tunda ko a gidansu bata taso taga mamanta da kishiya ba,da wata ce wannan kadai ya isheta mafaka.

" ba da kayan abinci na ba,kuma kema ban lamunce kiyi ba,idan kunne yaji....."sai ta ja bakinta ta tsuke,don bata son yayi fushi da ita irin na baya kan zancan fenti da lefe.

     Washe gari ranar talata gefin magariba lokacin dawowarsa,ta gama komai kamar yadda yake al'adarta,gidan nata qamshin turaren tsinke,tana tsakiyar yaranta ta siyo madarar ruwa ta musu iloka ta rarraba musu suna sha,wani yaro dake bayan gidansu yayi sallama dauke da akwati wasu yaran na bayansa.

"Wai gashi inji yaya mukhtar" ya fada kamar yadda yaji matar gidan na gaya masa,sai mamaki ya kamata don bata ji alamar  shigowarsa ko qarar babur dinsa ba,tashi tayi ta bude masa labulen falonta suka shiga da su,akwatunane guda shida masu kyau duka iri daya uku set daya uku set daya.

    Suna fita ya shigo yana dauke da baqar leda,duka yaran suka masa sannu da zuwa suna qoqarin tafiya gida,ya bibbisu da alawa kamar yadda al'adaraa take sannan suka bi sumayya da
"Anty sai da safe.....anty sai gobe"
"To Allah ya bamu alheri" ta amsa musu suka fice ta rufe gidan sannan tabi bayan mukhtar da tuni ya shige falon.

    Murmushi ta sakar masa kamar yadda ya sakar mata
"Kinyi kyau sumayya ta" kanta ta sunkuyar cikin kunya tana murmushi
"Na gode yaya na,sannu da zuwa" ta fada tana cire masa hular kansa da bai samu cirewa ba
"Ya kasuwar" ta sake fadi tana qoqarin ajjiye masa ruwa mai sanyi
"Kasuwa alhamdulillah......kinga ai my sumy abinci zaki kawomin don yunwa nake ji",ta dan zaro ido tana dubansa
" da wuri haka yau?,na zaci sai ka dawo daga sallar magariba",shafa cikinsa yayi yana murmushi
"Salla bazata yiwu cikin nutsuwa ba ina fama da yunwa,taimakeni ki bani sumayya magaribar da sauran lokaci,idan na kammala ko masallacin sun idar mayi jam'in da ke"
"To" ta fada tana miqewa zuwa kitchen.

     Bayan ta gabatar masa da komai tuwon semo ne miyar kuka sai qamshin daddawa take duk da babu nama amma tayi dadi qwarai,taasa bismillah sannan ta koma gefansa ta zauna.

     Sai da ya kai loma biyu sannan yace
"Ga kayanku nan ki duba kiga" ya fada yana mata nuni da akwatunan dake jere gefe,da to ta amsa masa sannan sannan ta sauka qasa ta janyo akwatunan ta soma dubawa.

    Tana dubawa yana zuba mata santin tuwo,yayin da itama ke santin kayan,komai yayi kyau,sai data kammala tas,lokacin har ya gama cin twon ya jngina da kujera yana kallonta tana ta daga kayan tana yabawa,ta rurrufesu yadda ta gansu sannan ta dubeshi.
"Nayi zaton ma har an kai kayan ne naga lokaci ya qurato"

"Um um" ya fada a taqaice

"Sunyi kyau sosai ya mukhtar,Allah ya qara budi,saidai komai naga bibbiyu ka saka kala daya,nufina kayan dake cikin akwatin kayan sawa sune a daya akwatin,under wears da mayafai ma"

"Eh,akwatin uku naki ne uku nata", idanu ta zaro a firgice tana dubansa
" aini yaya ka manta ka yimin lefe na tun sanda zaka aure ni?"
"Na fiki sani,kayan fadar kishiya na miki".

    Tsoro ne sosai ya kamata,tsoron su yaya yahanasu,ina zata sa kanta idan suka ga wadan nan kayan,komai iri daya ita da amaryarsu,hatta da man lebe iri daya ne?,tabdi lallai ya mukhtar so yake ya janyo mata bayan lallabawa takeyi.

" gaskiya ya mukhtar ba'a haka,itafa amarya ce ya zaka hadamu kayi mana abu iri daya?bayan kayan kitchen da kayimin,ka sauya min kayan kallo,kasan su yaya yahanasu sai sunce wani abu idan ma basu ga laifina ba lo sun zargeni ba"

"Eh,saboda kin fiye min ita,ke din zabi na ce,kuma raino na ce,tun kan kisan ciwon kanki kike zaune da ni,tun ana ciyar da mu bana daukar nauyinki,ita din ban santa ba,bansan halinta ba bansan ko zata iya irin zaman da kika yi da ni ba,sannan idan su yaya yaha da kike zance ai basu suka yimin ba,da kudina nayi balle a ce don me?,kufi na ne kuma iyali na ne,saboda haka bana buqatar ki sake cewa komai".

    Tun asali ita ba mai musu bace da ya mukhtar din ba,girmansa take gani,kallon yaya take masa saboda haka cikin sanyin jiki tsoro da sanyin murya tace
" hidimar ce naga kamar taso tayi yawa,na gode Allah ya saka da alheri,Allah ya jiqan magabata ya basu aljanna madawwamiya"cike da jin dadin yadda ta yiwa mahaifansa addu'a yace
"Amin,Allah yayi miki albarka"
"Amin ya mukhtar na gode sosai".

     Tun qarfe takwas washegari ta kammala komai saboda da wuri mukhtar yace zai fita saboda masu jere,qarfe tara ta sallameshi,har ya fita ya dawo ya dubeta
" idan kinga babu dadi zaman gidan,na baki izini kina iya tafiya duk inda kike so,idan yaso idan sai kimin waya ki gayan inda kike,idan na taso daga kasuwa sai na biyo na daukeki"murmushin yaqe kawai tayi,don hakanan tunda ta tashi yau take jin fargaba da bacin rai
"Babu komai ya mukhtar zan iya zaman ma,me zai hana"
"Kada dai ki takura kanki idan ba hali kiyi ficewarki"
"To,a dawo lafiya",ya amsa mata da " Allah yasa"ya saka kai ya fice.

      Tayi wanka ta shirya tsaf cikin atamfarta da abbanta ya dinka mata ita kwanaki,dark brown ce da adon mint green ajiki,sosai ta mata kyau dinkin ya zauna mata das a jikinta,falo ta koma ta zauna,jikinta a sanyaye bata san dalili ba,gidan ya mata shiru kasancewar 'yan hirar tata duka ana makarantar boko sai sha biyu da rabi suke tashi.

     Ganin akwai wuta ya sanyata jona kayan kallo,tashar arewa 24 ta kama,cikin sa'a suna maimaicin shirin agent ragab,tana son film din sosai,kusan shi ya dauke mata hankali har sha daya da rabi.

    Gamawarsu yayi dai dai da bugun qofa da ta soma ji,ta miqe ta fito tana tambayar waye tare da nufat soron,tun kafin ta kai ga budewa taji cikin kakkausar murya
"Malama ki bude bana son salo kin wani kama qofar gida kin rufe,bayan kinsan akwai wadanda zasu zo,dadin abun saura 'yan kwanaki naga ta iyayi" da sauri ta qarasa bude qofar domin tuni ta dauki muryar wace,yaya bara'atu ce sai fadima tsaye a bayanta,dai sauran da bata san su waye ba,tasan dai ba zasu wuce dangin amaryar ba tunda ita daga amaryar har 'yan uwanta babu wanda ta sani,iyaka dai tasan cewa amaryar 'yar aminiyar yaya yahanasun ce.

      Saura kadan yaya bara'atun tayi gaba da ita badan tayi gaggawar matsawa gefe ba ta wuceta saura suka biyo bayanta suka bar mazan da zasu shigo da kayan katakon da kujerun.

     Bata qosa ba tabi bayansu zuwa dakin da aka bawa fa'izan wanda tuni yasha fentin farar qasar data siya tayi da kudinta,babu komai a dakin a share yake fes kasancewarta gwanar tsafta ce,tun kafin tace wani abun yaya bara'atun ta galla mata harara yayin da sauran suka mata caa da ido
"Uban me kuma kika biyo mu ki mana?" Ta tambayeta tana huci,qasa tayi da kanta saboda yaya bara'atun ta girme mata nesa ba kusa ba cikin ladabi tace
"Zuwa nayi mu gaisa ne"
"Riqe gaisuwarki bama so"
"Uhmm,wallahi kuwa" fatima tayi caraf ta karbi zancan
"Allah ya baku haquri" ta fada sannan ta juya ta fice kai tsaye falonta ta shige taci gaba da kallonta.

       Miqewa tayi zata dauko wayarta dake uwar daki tana ringing ta hangosu suna kici kicin budw kwadon dake rufe da dakin ya mukhtar wanda da kansa yasa ya rufe ya tafi da abinsa,da taga a kulle yake sai ta saka tana fadin
"Lallai,kaddai yaya mukhtar daki daya ya bayar,tabdi lallai,yana nufin ita a falle daya zata zauna waccar tana da ciki da falo....haka ne....mu shirya mata kayan idan muka koma ma sanar da yaya yahan",bata ce uffan ba don ba mas'alarta bace,ko tata din ce ma basu sako da ita ba.

      Ya mukhtar ne ya kira yana tambayarta komai lafiya ko tace eh sannan sukayi sallama ya kashe wayar.

      Kafin wani lokaci gidan nasu ya cika da 'yan jeren,ko ina sai shewa ke tashi da qananun magan ganu,take tsoro ya cika sumayya,ta dinga kiran lambar maman naana kan ta shigo ta tayata zama amma wayar a kashe take,ta dinga leqe ta window dinta taga ko akwai hanyar da zata ratsasu ta fice.

      Bata samu sararin gurin ba sai da suka fara daura alwalar sallar azuhur,tayi hanzarin shiga uwar dakanta ta dauko hijabinta tare da padlock  ta sanyawa qofar dakin nata ta fice.

     A qofar gida ta tarad da su naana suna tsaye,suna ganinta suka nufota da sauri,ta dubesu tana cewa
" me kuma yau kuke tsaye a qofar gida?"bilkisu ce tace
"Hanamu shiga anty akayi?"
"Waye ya hana ku shiga?"
"Masu jeran amarya"inji nana,take taji ranta ya baci,sam bata son abinda zai taba mata yaran,ba zata juri haka ba sam,bata ce misi komai ba sai
" kuzo muje,qila fitina zaku shiga kuyi musu shi yasa suka hanaku shiga don kada ku bata masu kaya"
"Wallahi anty a'ah" inji aysha
"Shshshshah" sumayya tace da su,sun san me take nufi ko batayi magana ba,bata da son su kawo mata hirar wani dama.

      Gidan mamam naana ta shiga,ta taras da ita tana kwashe abinci cikin kula
"Ina zaku haka ke da gayyar yaran naki,ina kika baro baqin naki,ai yanzu nake shirin shiga kinga girki ya tsayar da ni ina so na kammala na turasu islamiya sannan na shigo" murmushin yaqe tayi ta ja kujera 'yar tsuguno ta zauna daga bakin qofar falon maman nanan,yaran nata suka zazzauna kusa da ita
"Eh wlh,na gaji da zama ni daya nace bari na leqo"
"Banda abinki sumayya aiko baki aiko na shigo miki ba kyayi waya a turo miki halima da zainab ko su tayaki zama"
"Wallahi maman naana bansan haka akeyi ba ai" murmushi tayi tana tausayawa sumayya da quruciyarta
"Ai shikenan,Allah ya bada zaman lafiya,ya kade fitina tsakaninku"
"Amin" sumayyan ta fada cikin faduwar gaba.

     Duka yaran ta zubawa abinci suka ci sannan ta tura kowa ya gida saboda ganin lokacin tafiya islamiya yayi,ta shirya su naana ma suka tafi sannan suka daura alwala sukayi sallar azahar ita da sumayyan.

     Shinkafa da miya har da salad da kifi abinda ta dafa ta zubo musi cikin plate
"Sauko sumayya maza muci" kai ta girgiza don a cunkushe take jin cikinta babu space din abinci
"Na qoshi maman nana" tausayinta ya kamata amma ta dake tayi murmushi
"Sauko muci akwai abinda nakeson gaya miki" bata da jan doguwar magana saboda haka ta sauko ta sanya hannu suka soma ci.

      Cikin hikima maman nanan ke kwatantawa sumayya dabarun zama da kishiya,qissa dabara da wayo kala kala,ta dora da yi mata nuni da haquri,kau da kai kara da alkunya,gaskiya da amana,zama na tsakani da Allah,sai gashi sun tashi da abincin tas,har sai da hannayensu ya fara bushewa da miya saboda sun kasa tashi a gun darussan maman naana sunqi su qare,saiga sumayya na kwasar dariya saboda wani abun idan maman nanan na gaya mata kunya ce ke kamata ko mamaki.

     Hararta maman nana tayi dariya itama nason qwace mata itama amma ta dake saboda yadda taga sumayya na dariya wani abu da ta gaya mata
"Au dariya ma nake baki ko?,zaki ci gidanku wallahi idan baki dauke duk abinda nake gaya miki ba" cikin dariyar ta dafe baki
"Yi haquri maman nana,abunne wallahi" ta kuna saka dariya,kada kai maman nana tayi itama dariyar ta qwace mata,ba shakka sumayya danyace har yau,ta miqe ta dauke plate din da suka gama cin abincin ta fice da shi.

     Basu ankara ba sukaji ana qwala kiran sallar la'asar,nan suka tashi sukayi,maman nana ta dubeta tace
"Ba zaki koma gida kiyi girki wa mukhtar bane"
"Ina som in koma maman nana amma ina zaton har yau basu tafi ba,bari na kira ya mukhtar din naji mai zai ce".

     Koda ta kirashi cewa yayi tayi zamanta kawai idan ya dawo din ya kirata ta dawo,a nan tayi zamanta suka ci gaba da hirarsu har su nana suka dawo daga islamiya,sai qarfe shida kiran mukhtar ya shigo wayarta,ta yiwa maman nana sallama ta wuce gida.

      Kaca-kaca ta tarad da gidan tun daga qofar gidan tamkar bata taba shara ba,kwalaye da ledojin abubuwan da suka jera duja ko ina a gidan,ga kwanukan abinci nan nata har da sabbi da bata taba amfani da su ba,da alama ma girki sukayi saboda kitchen din na bude zasu jerawa amarya nata kayan a ciki,mukhtar na tsaye a tsakar gidan riqe da qugu cikin bacin rai,da alama ransa ya baci da irin abinda sukayi,ga abincin da suka dafa din ma basu iya cinyewa ba sun kuma lalata bare a bawa wani,zai soma sababi ta shige jikinsa ta soma lallabashi,sai da ta sauke masa temper dinsa sannan ya tayata suka fara kintsa gidan fes.

     Kafin su kammala anyi kiran sallar magariba,ruwan wanka ta dora musu sannan sukayi alwala sukayi sallah,bayan sun idar ta juye musu ruwan sukayi wankan tare,ta shirya tsaf tayi kwalliya cikin qananun kaya,zata dora musu girki yace ta barshi kawai ya zura jallabiyyarsa ya fita.

    Cikin minti a shirin ya dawo da ledoji a hannunsa,ya ajjiye kan kujerar yana cewa
"Dauko faranti ki juye mana wannan,ki hado da cups,hala ma yau duka bakici abinci ba" murmushi tayi sanda take fita daga falon tana cewa
"Naci mana ya mukhtar a gidan maman naana" ,ta dawo dauke da plates din ta juye abinda ke cikin ledar.

     Tsire ne da zafinsa sai zuba qamshi yake,sai rabin gasashshiyar kaza,ta bude dayar ledar,lemon roba ne na fanta sai maltina wanda tasan ta mukhtar din ce tunda ita bata dameta ba.

       A nutse suke ci suna hirarsu jifa jifa kamar babu wani abu dake damunsu.

      Suna tsaka da ci wayar sa ta dauki qara,sumayya ta miqe ta isa inda take chargy ta ciro masa kana tazo ta miqa masa,baquwar lambace,yayi kamar bazai daga ba amma yadda kiran keta nacin shigowa ya sanyashi dagawa ya kara a kunnensa.




*mrs muhammad ce*


📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

_________________________

_Bismillahir rahmanir rahim_

*_la yadillu rabbi wala yansa_*
_______________________


*_ina taya maman farida(dan maliki,baya tsami banza,hanyan ruwa)murna sauka lafiya tare sa samun zan kadeden baby boy,Allah ya raya mana shi cikin musulunci,ya albarkaceshi,ya qara musu lafiya ita da babyn,sannan kuma muna kamu tun yanzu,lol_*




0⃣5⃣





    Sallama yayi maimakon ya amsa hello da ake faman cewa,yayi jim yana jiran amsa sallamar tukun,fahimtar abinda yake nufi da akayi ya sanya aka sa sallamar
"Da wa nake magana?",cikin karyar da murya akace
" mukhtar baka ganeni ba,fa'iza ce fa"
"Fa'iza?,wacce fa'iza" wani murmushi akayi mai fidda da sauti cikin siga ta nufin jan hankali
"Fa'iza amaryarka mana".

       Hade rai yayi kana cikin dakiya yace"ok,ya akayi?",sake marairaice murya tayi
"Haba mana mukhtar,ai ko gaisawa ka bari muyi tukunna ko?"
"Yayi kyau,ina gajiya?"
"Gata nan muna fama da ita mun fara shiga sabgogin biki,amma mukhtar ko marmarin sake zuwa guna bakayi,haba"
"Wannan ne dalilin da yasa kika kira ni?" Kai ta girgiza kamar tana gabansa,cikin ji haushin yadda yake amsa mata da qyar kamar wanda aka tilastawa
"A'ah ba shi bane"
"Fadi uzirinki kai tsaye".

      Gyara zama tayi sannan cikin salo da kisisina ta fara magana
"An ce daki falle daya ka bani,haba mukhtar,ya zaka bani daki falle daya sannan ka bawa uwar gidanka ciki da falo alhalin nice amarya ni nafi cancantar ciki da falo"tana direwa ya dora
"Ko?,a wanne hadisin?".

     Fara quluwa tayi amma ta dake"haka na ya dace ai"
"To ai babu damuwa,sai ki gayan nawa muka hada muka gina gidan sai na fidda miki haqqinki" ya fada cikin jin haushi da sigar gatse,da sauri tayi saurin cewa don kada kwabarta tayi ruwa
"Allah ya baka haquri ba nufina kenan ba" tayi saurin katse wayar,cilla wayar yayi gefe yana jan tsaki kana ya tsame hannunshi daga tsiren ya wuce daki.

      Itama kasa ci gaba da cin tayi,saboda haka ta tsame nata hannun ta fada wanka,ta gyara jikinta ta sanya kayan bacci sannan ta lullube farantin tsiren ta bishi da shi,cikin kwantar da murya da tausasa harshe ta sanya shi suka cinye tare.

      Ranar alhamis ta siyi relexer,nan saloon din dake bayan layinsu ta shiga aka wanke mata kanta aka busar mata cikin drayer,da yake tana da gashi babu laifi sai ya sake kyau ya kwanta sosai,daga nan bata shiga gida ba,gidan maman nana ta shiga wadda ta kwaba su madara ruwan kankana qwai su dilka da kurkur tana jiran dawowarta,ita ta gyare mata jikinta fes,zuwa la'asar ta fito shar,fatarta ta sake wani kyau da haske.

    Tsokanarta sosai mukhtar ya dinga yi,yana mata waqa
"Uwar gida na,amarya ta,amanata ki damqeta(waqar my habib(muhammad)" dariyar itama ta dinga yi.

     Ranar juma'a aka zo aka mata lalle ja da baqi,ta aika halima da zainab suka karbo mata dinkinta data bada kala takwas cikin kayanta,duka sai data gwada babu wanda bai mata kyau ba,a nan su halima suka kwanar mata da anty dije qanwar mamanta saboda washe gari asabar zata yi wuni saboda ranar sukace zasu kawo amarya.

       Wuni tayi babu laifi ta dan tara jama'a,sosai mutanen unguwar suka yi mata kara sun shishshigo,maqotanta na kusa da gidan ne suka zauna mata suna jira a kawo amarya su karbeta.

       Ana gab da sallar magariba ta shiga tayi wanka,ta sauya wasu kayan cikin kayanta,shadda ce ja wadda aka yiwa baqin stone work,kwalliya tayi mai kyau da tsari,sosai tayi kyau saidai komai da take yi cikin sanyin jiki take yinsa,haka nan take ta fama da fargaba da faduwar gaba,anty dije nata azalzalarta kan ta shirya kada 'yan kawo amarya su iso bata gama shiryawa ba,ta dauki turare ta feshe jikinta sannan ta nemi baqin mayafinta mai kyau da kwalliyar duwatsu ta yafa ta dawo falo.

       Tun magariba suke zuba idon ganin amarya har qarfe takwas na darw babu ita babu alamarta,hakan ya sanya maqotam suka fara tafiya da dai dai da dai dai saboda dawowar mazajensu,wasunsu kuma sun bar yara a gida,har tara shiru hakan ne yasa 'yan uwanta suka fara mata sallama suma saboda tafiya nasu gidajen,babu wanda za'a bar mata saboda anty dije tace hakan baiyi tsari ba,sai taji zuciyarta ta raurawa qwalla ta cika mata ido,bata san me zata yi ba batasan ya zata yi ba hakanan bata san yadda akeyi ba,anty dije da maman nana ne suka dinga kwantar mata da hankali tare da bata shawarwari wadanda suka sake sanya mata nutsuwa,sukayi mata sallama suka tafi,maman nana kawai ta rage.

       Qarfe goma na dare maman nanan na shirin tafiya itama ganin shirun yayi yawa sai ga hayaniyarsu da ta motocinsu,hakan ya sanyata ta koma ta zauna tana tsumayin isowarsu,saidai ga mamakinta yadda akeyi a al'adance a fara kai amarya ga uwargida su ba hakan bane,dakinta suka bude kai tsaye suka shige da ita suna faman yada kirari tamkar jinin maroqa
"Shiga da bismillah uwar 'ya'yan mukhtar".

       Da sauri maman nana ta soko ma sumayyan wata hirar don ta hana kunnuwanta jin abinda suke fadin,saidai ko kadan bata cimma nasara ba saboda wani tashin hankali da taji ya ziyarceta,gudun zuciyarta ya qaru,sai ta kalli maman nana
" maman naana,qirjina bugawa yake bansan me ya sameni ba"dan murmushin kwantar da hankali tayi mata
"Kada ki damu,wannan shi ake kira kishin,kiyita ambaton hasbunallahu wa ni'imal wakeel,ni'imal maula wa ni'iman nasir" kai ta kada hawaye na silalo mata,ta sanya hannunta ta share tana mai bawa kanta qwarin gwiwa tare da hana kanta da kanta kuka.

     Labule aka bankade aka shigo,fiddausi cs goye da 'yarta,ta dubi sumayyan sannan tace
"Kije dakin amarya,yaya bara'atu na son ganinki",cikin mamaki maman nana ta dubeta
" a'ah,ai ba'a haka,amaryar ai ya kamata tazo ko?"duban maman nanan tayi sai ta juya ta fice ba tare da tace komai ba.

     Ko minti daya ba'a qara ba saiga yaya bara'atun ta shigo
"Baiwar Allah ke a suwa kuma,wacece ke da har zaki hanata zuwa,to bari kiji,idan ma irin masu shige da fice ne gidan kishiyoyi suna hurewa kishiya kunne wahalar da sumayya kawai zakiyi,don zama fa'iza tazo yi ta kuma hayayyafa,ba mun kawota ne don ta tafi ba,saboda haka ke sumayya ina jiranki", wani abu yazo ya tokare maman nana a wuya,tamkar zata tanka sai taga hakan bashi da wani alfanu,tayi qoqarin kai zuciyarta nesa,saboda koda ta tanka din qila qarshe abun ya juye kan sumayyan wanda bazata so hakan ba,sai abun ya mata yawa ta rasa da wanne zata ji.

     Itama ta riqe hannun sumayyan cikin kalamai na qarfafa gwiwa ta mara mata baya har zuwa dakin marya,babu laifi dakin ya cinye komai nata kasancewar yana da yalwa,kuma ba wasu uban kaya suka mata ba,tunda gaba daya sun daga hankali ne anyi bikin cikin matsatstsen lokaci ba tare da sun gama shiryawa ba su kansu.

   
       Gefe daya suka samu suka zauna,sumayyan ta gaidasu daidaikum cikinsu suka amsa,maman nana kam babu wanda ta duba cikinsu don dama darajar sumayyan ya sanyata shigowa dakin,wata 'yar tsohuwa ce dake zaune gefan amarya wadda ta lullube fuskarta da mayafi tace
" to sumayyatu,ga 'yar uwa nan mun kawo miki,abokiyar zama,Allah ya baku zaman lafiya,muna fata zaku

Please Login or Register in order to submit comment