Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

min gashi kuma ni bansan daga zan fara neman matar da zan aura ba, Kuma kai Ali dakake cewa mata masu cewa suna sona tun kamin ni na furta mata masu kalamar so ai har abada ta kayar da darajar ta gareni haba yo ina ajin na mata duka ta zubar to ni mizanyi da mace marar aji da kamun kai kuma wanibi irin matan da suke Nuna ma namiji suna sonsa tun kamin shiyace yanason su to fa'aksarin su ba son gaskiya suke masa ba kawai dai dan wani abu ne da Allah ya yi maka to ka ga irin matanan ba irin matan da yadace ya zauna dasu bane indai yana son samin mata ta gari dan haka babu wace zan zab'a a cikin su." AFREED ya fad'a


Ali yace "Hakane to taya wai zaka sami matar kaida ba kulla su kake ba kasan idan har lokacin da dady ya ibar mana ya k'are bamu fitar da matan aure ba wallahi zamuga b'acin ransa sabida zai iya aikata abinda yace zai aikata a kanmu sabida dai kasan shekara guda ba kwana guda bace bai kamata ace shekara guda da ya d'ibar mana har ta k'are baka fitar da matar aure ba don gaskiya dady ba zaiji dady ba ni wallahi kai nafi tausayi ma sabida baka iya kallon mace bare har kace kana sonta nidai kaga inada wada nakeso ko yanzu dady yace na gabatar da ita to zan gabatar masa da ita kai fah da ko secrétariat ta baka sani ba da kai kawo daga office inka zuwa nata har yanzu baka tantance ta ba to Inama zaka samu damar sanin wata."


"Nima fah shine nike tunani Ali amma Allah zai shige man gaba insha Allah zan samu wada tayi daidai dani kamin dady ya fitar min da mata ina neman zab'in Allah, ina fatan Allah bani mata ta gari ni wallahi inba dan dady ya matsa ba ni babu aure a gabana yanzu duk nawa nake da za'a matsa sai nayi aure."

"Kam wallahi AFREED baka jin kunya kai ne zakace a nawa kake shekara 30 da kakeda itace a nawa kake wanda gashinan har ma kazama tuzuru Ali ya fad'a tare da tuntsirewa sa dariya."


Dariyar shima AFREED yayi sannan yace wallahi Ali kayi mugun rainani ma yanzu shekara 30 kince zaka wani cewa na zama tuzuru to wallahi ka kiyaye ni idan na zama tuzuru to wallahi kaima tuzuru ne tunda dai ba girme maka nayi ba."


Koma dai minene to kaji dashi wajan wata biyar ka bani da haihu ko da kuwa second guda ne ai dai ka girme min don haka yanzu dai nasan kana da ayuka da yawa a gaban ka ka d'auka ka fara ni kaga tafiya ta zanje na dawo."


Murmushi AFREED yayi sannan yace sai ka dawo to ai kasan yau da wuri zamu tashi."

D'aga masa kai Ali yayi sannan ya juya ya fice daga office d'in."



Sai mun had'u a next page💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃


Alhamdulilah...



🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


ÉCRIT


PAR



*QUEEN ZEEFAT*


Ƴar
Mutan
Niger

_Wanan page taki ce my kawa my Aminiya ta_ *Rida* *Chou* _que le bon dieu te protège kawar arziki ina yinki irin sosai ɗin nan_


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan
-niger-111773560677003/




_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_




*Page* : 19 & 20


Ƙarfe 12:00am Ali ya shigo office ɗin AFREED tare da ƙaraso kusa da table ɗin AFREED yace "Ranka ya daɗe kataso mu wuce gida lokacin tashi daga aiki yayi, kuma naga kamar da aiki a gaban ka baka kamala ba, kaga kuma ni yinwa nakeji inason naje gida naci abincin don nasan yanzu momy tagama mana spécial, amma dai zan zauna har ka ƙarasa sai mu wuce."


AFREED dai bai tanka masa ba, kujera Ali yaja ya zauna, yana zaunawa AFREED ya fara tatara takadun dake gabansa yana kammala hada su guri guda ya tashi daga saman kujeran dayake Ali na ganin haka shima ya mike ya nufi ƙofa ya buɗe masa don yasan tashin da yayi fita zaiyi duk da bai fad'a masa haka ba, AFREED na kawowa bakin ƙofar Ali ya ida buɗe ƙofar AFREED ya fice sannan Ali ya bi banyan sa tare da rufo ƙofar garde-corps ɗin dake bakin ƙofar suna jiran fitowarsa suka ƙame guri guda suna sara masa batare da ya kalle suba yayi gaba abinsa sukuwa suka mara masa baya.


Ali daya tsaya rufe ƙofa suka barshi abaya, yana ƙarasa kule ƙofar tare dayin saurin tardo yace "Haba AFREED sai ku tafi ku barni don kawai kasa sai nayi gudu idan inason cimmar maku kuma fa kaji nace yinwa nakeji gashinan yiwar ta ƙaru sabida ɗan gudun da nayi."


AFREED dai bai tanka masa ba hasali ma ko kallon sa beyi sai ma damun sa da surutu yayi don ji yake kamar ya makesa ma ya futa ko zai yi shiru da bakin sa.


Ali da yaji shirun yayi yawa ya gane da surutun da yake masa ya damesa kawai sai yayi shiru bai sake cewa komi ba har sukakai ida suka parking motocin su duka garde-corps ɗinn saida suka nufi motar da AFREED zai shiga suka kewaye ta sannan Ali ya buɗe masa ma zauni sa ya shiga kamin kowa ya nufi motar da zai shige, daga bisani aka tayar da motocin sai gida.


Suna isa gida direct ɓangaren mahaifiyar su suka nufa kamar yanda suka duk in sun dawo daga gun aiki sai sun biya gun mahaifiyar su sun gaida ta kamin su wuce ɓangaren su, suna kawowa bakin ƙofar ɓangaren mahaifiyar tasu Ali ya juya yayiwa garde-corps ɗin signe da suka ma gaban su a take suka juya suka bar gun, kamin Ali ya juyo AFREED har ya buɗe ƙofar kawai sai suka shige lokaci guda tare da yin sallama.


Hajiya Falmata na zaune saman ɗaya daga cikin haɗaɗun kujerun dake falon ta hakimce tana kallon télé (TV), tanajin sallama su farin ciki ya luluɓe ta juyowa tayi ta sakar masu murmushi tareda amsa sallamar sannan tace "Oyoyo da ɗiyan albarka na ku ƙaraso kuzo ku zauna," tana nuna masu kusa da ita, ƙarasawa sukayi sedai basu zauna saman kujerar da take a zaune ba sai suka zauna ƙasa kowanan su ya za'a kansa saman ciyar ta ita kuwa ta shiga shafa masu kai a tatare sukace "Momy ya gida?"


Ta amsa da "Alhamdulilah ya aikin ku ya gajiya?"


A tare suka kuma cewa "Da godiya."


Mom tace "To madala Allah ya taimaka, Allah tsareku ya kareku daga duk wani sharin mai sharin da kuma sharin ƙarfe."


Suka amsa da "Ameen momy."


Ali sai ya zarce da cewa "Wallahi ni fah momy yinwa nakeji dama da safe wanan fitinanan ɗan uwan nawa bai bari nayi Kari mai kwari ba ya fitineni da na tashi muje wajan aiki duk gashinan yanzu yinwa duka tabi ta dameni anyi mutum sai fitina," ya watsawa AFREED tare da murguɗa baki kamar wata mace.


Dariya sosai momy tayi sannan tace "Kaga kuwa harna gama dafa maku abinci kuma abinda kafiso na girka maku."


"Yawa momy dan haka nake ƙara sonki Allah dai ya biya ki da gidan aljanna."


Da ita da AFREED suka amsa da "Ameen."


Momy tace "Bari naje na kira ƙanan ku sun ce bazasu ci abinci ba har sai kun dawo ku ci tare."


"Ah momy bari naje nawo masu magana su fito muci to."


A'a Abbana yi zaman ka, ka huta zanje na kira su kuyi hutawar duk kun gaji kaga daga aiki kuke nikuwa ina gida zamana ina hutawa ba abinda nayi sai girki nan shima dan AFREED ne bai girkin masu aiki shi yasa na girka maku da kai dan nasan kai babu ruwa da wannan iwayin nasa Allah maku albarka," faɗar mom tana ƙoƙarin hawa escalier don kiran su Fariya.


AFREED dai najin su bai tankasu ba gani momy tayi saman yasa shi tashi ya nufi hanyar barin falon da niyar sa ta komawa ɓangaren su, Ali na ganin ya mike yace "Ina kuma zaka??? nagani zamuci abincin."


Cigaba da tafiyar sa yayi baiko tsaya ba bare yayi tunani zai amsa masa.


Ali yace "To wallahi baka isa mu jiraka ba idan kanaso ma kada kaci abincin ko kuma kaci kai kaɗai ah to."


AFREED ya juwo yace "Kaga Ali fita haraka ta ni nace ku tsaya jirana kokuwa dole ne sai naci abincin tare daku ko an gayama ka sai tare daku zan iya cin abinci?"


"Anji ɗin kuma anki a fita harakar taka kayi abinda zakayi ko an gaya maka ana tsoron kane wallahi ina tausayawa matar da dady zai haɗaka da ita don narantse ba ƙaramin aiki ne gabanta ba, haba anyi mutum sai baƙin miskilancin tsiya,"Ali ya faɗa tareda sakin murmushin mugun ta dan yasan da ya gama ɓatawa AFREED rai.


AFREED najin haka ya juya ya bar falon don ya tabatar cewa Ali so yake ya ɓata masa da rai.


AFREED na fita momy da su farissa suka sauko ta wanga nan ta wanga nan bataga AFREED ba tace "Abbana ina ɗan uwan naka kuma yayi alhalin yasan za'a ci abinci?"


"Wallahi momy yayi tafiyar sa ɓangaren mu babu wanda banyi dashi ba ya tsaya amma ya ƙi."


Ɗan ƙarmin murmushi momy tayi sannan tace "AFREED yau halin akeji tunda gaka yayi tafiyar sa ba zai cin abincin anan ba ƴan miskilancin su na busa kai yau."


"Barshi dai mom bari na kai Masa abincin acan sai ya ci."


"A'a abbana yi zaman ka har kaci abinci barshi daga baya a kai masa."


"Hum ai su AFREED manya ne mom, ba maiyin irin tasa ace mutum ko yana jin yinwa babu abinda ya damesa kamar cikin wani zai sakawa abincin to ai dan kansa mu dai Kam ba fasa cin zamuyi don AFREED ɗan gayu ne yinwar ma bai cinka jinta ba ai duk miskilanci na ba zan ƙi cin abinci ba gaskiya sabida bana iya jurar yinwa," Ali ya faɗa yana Mai miƙewa daga zaman dayake.


Dariya momy da su Farissa suka yi sannan Fariya tace "Kai yaya irin wanan surutu haka bama kajin yinwar da ka faɗa."


"Kai kai ƙanwata sosai nake jin yinwar nan kisan hausawa sunce baki abun magana, to shiyasa ba najin daɗi idan banyi ba cikin ko wane hali kuwa."


Koma yin dariya sukayi daidai lokacin da suka ƙaraso bakin table à manger (dinning table) kowa yaja kujerar da yasaba zama ya zauna banda Farissa dake servir ɗin su tana gamawa itama ta ja tata kujerar ta zauna, shiru kakeji gun cin abincn babu mai cewa komai sedai ƙarar cuillère (spoon) kawai kakeji har suka kammala, Ali ya fara tashi ya nufi cikin falon ya zauna kan ɗaya daga cikin kujerun dake falon, momy ma falon ta dawo ita kuwa Farissa ta zubawa AFREED abincin ta tafi kai masa, Fariya kuwa ta tare kayan da suka ɓata ta mayar cuisine (kitchen). Ali yakai kusan minti 30 suna fira da momy da ƴan biyu wato Fariya da Farisa, sai daga bisani ya miƙe yace "Momy zanje na duba frèro naga ko yaci abincin kuma na sauya kayan jikina duk sun takura man."


Momy tace "To jeka abinka sai ka fito idan kuma AFREED baici abincin ba ka yi min waya zanzo na same shi don bazan lamunci rishin cin abincin nan nasa ba gaskiya."


"A'a bama sai kinzo ba ai, zai ci insha Allah tana yiyuwa ma har ya kammala cin abincin."


"Hum AFREED ɗin ne zaka ce ya kammala kana dai son ƙulle masa gidine amma idan har bai ci ba ka ɓoyemin to wallahi idan na gano haka duka zakuga ɓaci raina ehe kadai ji abinda na faɗa maka, ban cin wannan naga kamar wani abu na damusa ko zan iya sanin miye? Dan nasan baƙin ɗaya ba ƙi faɗa maka zai yi ba.


"Babu abinda ke damun AFREED momy kawai dai yanayin sa ne ya nuna hakan, idan kuma akwai bai wuce akan magana da dady ne yayi mana juya dadare ba amma in bashi ba to ba wani abun."


Hum AFREED kenan yo ai in a kan maganar da dadyn kune ya maku yasa damuwa a ran to garama ya daina dan babu guda babu ja da baya, amma ai ba sai na faɗa maku ba kun fiini sanin halin abban naku, kun sani sarai abinda ya faɗa sai ya aikata kawai abinda ya kama ce ku shine ku fitar da matan aure tun kafin lokacin da ya ɗibar maku ya ƙare gashi kuma ya baku isashen lokacin sabida shekara guda ai ba kwana guda bace hakan daya maku daidai kuma ya nason ya ga kun ɗoki maganarsa da muhimmanci ko kuwa, sabida haka kuyi ƙoƙari yurin ganin kun faranta masa ba, bawai ku ɓata masa ba wai dan baya don ku ne yace muku haka ba hasali ma sayayyar taku ce da yake maku yake ƙaunar ya kun zama cikakkun mutane sabida ku ƙara daraja a idon kuma ku raya sunnah manzon tsira Sallallahu alaihi Wasallam."


"Insha Allahu mom zamuyi abinda kukeso dan samun albarka kuma ran ku bazai taɓa ɓaci ba a kan wanan maganar zamu baku mamaki."


"To dako kun kyauta dan ni a cikin wanan maganar bani bayan ku gaskiya saboda nima inason ganin ƴan jikokina amma kunzo kuyi zama kunƙi yin aure ko so kuke sai mun mutu kuyi auren in hakanan kuma kukeso to ai shikenan."


"A'a insha Allahu haka bazata faru ba abinda kukeso zamuyi momy kun kwantar da hankalin."


Murmushi momy tayi mai matuƙar nuna farin cikin ta tare dacewa "To ai shikenan tashi kaje Allah maku albarka."


Da amin ya amsa sannan ya tashi ya fice daga falon ya nufi ɓangaren su, yana shiga direct ɗakin AFREED ya wuce, tardo sa yayi kwace idonsa a lumshe kamar mai bacci, juyawa yayi ya kalli abincin da aka kawo masa wanda ko kallon sa baiyi ba bare ma ace ya ci sa, da sannu sannu ya nufi bakin gadon ya zauna sannan yace "Ɗan uwana AFREED tashi kaci abincin mana ya za'a kawo maka abincin tun ɗazu kaƙi ci tashi dan Allah."


Shiru kakeji AFREED bai ko motsa ba bare ya nuna ya jisa har ayi maganar zai amsa masa, Ali ya koma cewa "AFREED ka tashi man kada abincin yayi sanhi kuma ka kasa ci," nan ma shiru AFREED bai motsa ba, "Haba ɗan uwana mi yayi zafi haka?" Har yanzu AFREED bai motsa ba bare ayi tunanin zai tashi daga kwanciyar dayake.


Shiru Ali yayi na tsawon minti biyu yana kallon AFREED sannan ya kuma cewa "Nifa nasan ba bacci kake ba, amma tunda kaƙi tashi bari na kira momy na faɗa mata baka ci komai ba dama tana can cikin damuwa sabida ka taso ka ta howarka baka tsaya kaci abincin ba shine ta aikoni nazo nagani idan baka ci ba naje na faɗa mata."


AFREED najin haka yayi sauri ya tashi zaune tare da ƙoƙarin saukowa daka saman gadon Ali yayi saurin riƙo sa yace "Ina kuma zakaje?"


Wani mugun kallo AFREED yayiwa Ali sannan yace "Kai dan Allah cikani ina fah zanje da ya wuce gun momy naga halin data ke ciki."


Mtsss Ali yaja wani ɗan ƙaramin tsaki sannan yace "Dan Allah dakata malam ka damu da halin da zata shiga ne ka kama hanya kayi tafiyar ka kamin taje ɗakin su Fariya ta dawo sannan kuma kaje gunta da alamu damuwa a fuskar idan baka don sata cikin damuwa miyasa ka aikata haka, abu guda ne zaka yi idan kana son kaga damuwar ta ta gushe shine ka karɓi abincin nan ka ciye shi sannan kasamu kayi sallah idan ka gama sai kaje gunta cikin sakin fuska a take za kaga farin cikin ta mara musultuwa amma ba ka wani tashi da sauri haka ba wai kai ga meson gani halin da take ciki, idan kaje haka ba sedai ka ƙara mata damuwar ba ɗan raini hankali kawai."


Saƙe AFREED yayi na wajan second 3 yana kallon Ali daga bisani dai ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi ba tare da yace wani abu ba ya karɓi abincin daga hannun Ali ya fara ci har sai da yaci fiye da rabin assiette (plet) sannan ya ajiye, yana ƙoƙarin tashi daga bisa gadon Ali ya riƙo sa yace "Yo ina kuma zaka kaida baka ƙarasa cin abincin ba?"


Da sauri AFREED ya fizge hannun sa yana cewa wallahi Ali ka fita haraka kazo ka sakani cin abincin nan naci ba dan maso sannan kuma so kake sai na cinye wannan uban abincin to wane irin ciki ne dani da zan iya cinye sa? kuma wallahi baka isaba don na tabata ko kai dake cin abincin sosai ba iya cinye wannan abincin zaka yi ba amma ni kake son kaga na cinye shi a cikin wane cikin kake son gani na saka shi? to wallahi duk fitinar ka yau sai ka barni," mtsss yaja tsaki tare da shigewa douche da sauri ya banko ƙofar toilette ɗin da ƙarfi.


Murmushi Ali ya saki tare da cewa "Ɗan uwana, abokina, kuma uban gidan AFREED Allah tsare min kai ya baka mata ta gari wada zata iya jure wannan halin naka sannan kuma ta zama sillar gyara maka wannan bahagon halin naka amin tunda dai kaci abincin ai shikenan dama da gaganne nace sai ka cinye shi."


Daga na shi ma ya tashi ya fita daga ɗakin AFREED ya nufi nasa ɗakin.


Shikuwa AFREED dake cikin douche yana jin fitar Ali ya fito a cikin zuciyarsa yana cewa anyi mutum sai shegin surutu da fitina da son takurawa jama'a, mtsss yaja ɗan ƙaramin tsaki tare da shimfiɗa darduma ya tada sallah.




*WANENE AFREED*

AFREED Sumana Gissa shine cikakken sunan AFREED wato ɗan ga Alhaji Sumana Gissa wanda yake cikakken bazabarme ne ɗan asalin garin Dosso kuma ingénieur (injiniya) ne aiki ne ya maido sa Niamey da zama, sai mahaifiyar AFREED Hajiya Falmata Ita kuwa cikakkiyar babarbara ce gaba da baya ƴar asalin garin Diffa, su biyu iyayen su suka haifa ita ƙanwarta Kaltum sun haɗu da Alhaji Sumana ne wajan walimar taron buɗe wata ma'aikata gina-gine a garin diffa ita kuwa tatafi wucewa ta gaban ma'aikatar ta dawo Ga aikin da aka mata yana ganinta ya ruɗe sabida Allah yayi mata kyau ga wani uban kamshi dake tashi a jikin ta, kun san barebari game da kamshi babu kamar su sedai kuma ba fara ce sosai ba haka dai har ya samu ya tsayar da ita ta yi masa kwatancan gidan su ida yaje ya sami mahaifin ta da maganar, da mahaifin nata yayi bincike a kansa ya samu kyakyawa shaida a tatare da shi, ya bashi auren Falmata cikin ƙanƙanan lokacin akayi komi da komi haka a ɗaura auren Falmata da Alhaji Sumana Gissa cikin aminci, suka tare a babban gidansu dake cikin garin Niamey wata uku da auren Falmata akayi na ƙanwarta Kaltum wani bafilatani mai rufi asiri a garin Tillaberi amma ba ɗan asalin garin bane neman kuɗi ya kawo sa Niger shi ɗin ɗan asalin garin Senegal ne.


Bayan shekara guda da auren Falmata da Alhaji Sumana Allah ya basu ƙaruwar ɗan namiji murna wajan wannan famille (family) ba'a magana kowa ka gani cikin farin ciki yake yaro mulmulmul dashi kyakkyawan gaske sai farin jini kowa ya gansa sai yaji kamar a basa shi kuma duk wanda ya ɗauka ba yason ya ajiye har saida jikinsa yayi ciwo kamin suna, ranar suna yaro yaci sunan AFREED, bikin sunan ya ƙawatu dan anci ansha sai dai son barka.


AFREED na da wata shida da haihuwa Kaltum ƙanwar Hajiya Falmata Ita ma ta haihi ɗan ta fari kal mai mugun kama da AFREED tunda yazo duniya mahaifinsa yayi masa huɗuba da Ali wato sunan mahaifinsa su Hajiya Falmata sedai tunda Kaltum ta haihu jini yaƙi tsayawa, likitoci suyi iya bakin ƙoƙarin su wajan ganin sun shawo kan matsalar amma abin ya ci tura, kwana biyu da haihuwar tace ga garinku aikuwa tashi hankali gun Hajiya Falmata ba'a magana taci kuka taci kuka har ta godewa Allah har yakai kukan baya fitowa saida ayita jin tana sauke ajiyar zuciya, sosai takasa hakura da rasuwar ƙanwarta ta kullum cikin kuka take ganin haka yasa Alhaji Sumana ya roƙi mahaifin Ali da ya taimaka ya bawa matarsa yaron sai taci gaba da shayar dashi tunda ita cikin jegon take, kuma ganin ɗan ƴar uwatata zaisa ya dinga ɗebe bata kewa haka kuwa akayi Mahaifin Ali yace ya bata shi halak malak tasa ma kanta cewa itace ta haifesa sannan ya ƙara da cewa shi yanzu ƙasar su zai komawa dama sabida Kaltum yake zaune a Niger amma yanzu komawa zai yi tunda ya gama abinda yake a Niger abinda ya samu Allah sa masa albarka, kuma yace su taimaka idan Ali ya girma su bashi labarin shin duk dacewa zai dinga zuwa ganisa lokacin zuwa lokaci amma daya ke bai san halin rayuwa ba ko yanada rai zai girma kokuwa Allah dai masani.


Ai kuwa kuka sai ya koma dariya gun Hajiya Falmata don ba ƙaramin farin ciki tayi ba daji an bata Ali har abada, ba ma ta iya musulta farin cikin da take cikin don ji take kamar ƴar uwata in ce gaba-ɗaya take raino, haka dai Hajiya Falmata ta haɗa ɗiyanta biyu gaba ɗaya ta na shayar dasu cikin tsantsan so da gata dan ba ƙaramin ji dasu take ba shima Alhaji Sumana ba'a barsa a baya ba sabida idai yana gari to a kowa ne lokacin suna tare dashi babu wani banbanci da iyayen AFREED ke nunawa ga Ali duk ɗaya suka ɗokesu, har ma sufi yiwa Ali Abu basu ma AFREED ba, Ali dai kam baida maraicin uwa da uba don Hajiya Falmata da Alhaji Sumana ba ƙaramin sonsa suke ba.


Shikuwa mahaifin Ali ya riga da da ya koma ƙasar su ya bar amanar Ali a hannun iyayen AFREED.


AFREED da Ali na da shekara uku uku aka saka su école coranique (islamiyya) da jardin d'enfants (nursery school) Mai tsadan gaske Masha Allah duk da yarinta su haka bai hana su rike abinda ake koyar dasu ba kuma idan sun zo gida Hajiya Falmata ta ƙara koyawar dasu su, AFREED sun tashi cikin gata sosai amma hakan bai hana iyayensu basu tarbiyya ba Hajiya Falmata da Alhaji Sumana suna iya ƙoƙarin su wajan ganin sun basu cikakkiyar tarbiyya, AFREED ya tashi miskili mara son magana bai ƙaunar zama inda ake hayaniya da yawan surutu sedai halinsa yasha banban da na Ali wanda shi kuwa ma'abucin surutu ne da barkwanci duk da wannan halin na surutu na Ali da AFREED bai so amma ba ƙaramin ƙaunar junansu suke ba ko kaɗan basa son ganin junansu cikin damuwa a tare suke komai nasu, ko Hajiya Falmata da Alhaji Sumana basu san tsakanin su ba.


Kwanci tashi babu wuya a wajan Ubangiji su AFREED har sunyi shekara bakwai bakwai sosai sukayi wayo masha Allah idan ka gansu zakayi tunanin sufi shekarun dake garesu sabida tsananin wayo da Allah ya masu. Ita kuwa Hajiya Falmata tunda ta haifi AFREED Ko ɓatan wata bata taɓa yi ba bare ayi batun samun cikin shiru shiru kakeji har saida su AFREED su kayi shekara goma sannan Allah ya ƙara bata haihuwa wanda har sun fida rai da samun ta idan ta haifi ƴan biyu duka mata ranar suna yara aka raɗa masu sunan Fariya da Farisa murna gun AFREED da Ali ba'a magana kullum suna tare dasu an samu ƙanai duk in sun taso daga makaranta suna tare da su bacci kaɗai ke rabasu da ƙannansu.


Su AFREED na ƙarasa primaire (primary) Alhaji Sumana ya mayar da su France a can sukayi secandary school da University sannan suka dawo Niger dan su riga da sun kammala karatun su nacan, watan su biyu a gida AFREED yace

Please Login or Register in order to submit comment