Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kusa dashi.

Juyawa yayi da k'arfi gefan da yake jin kukan, wata matashiyar budurwa ya gani duk'e ta had'a kai da gwiwa tana kuka kamar ranta zai fita............



Na Queen Zeefat


Kuyi comments masoyan zanba cikin aminci hakan zai sa nayi wani pageπŸ’“πŸ’–β€οΈ


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZANBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


ECRITE:


_PAR_


*QUEEN ZEEFAT*


Yar
Mutan
Niger


Wattpad@nazhabibou


_BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM_



Page 9


Juyawa yayi da k'arfi gefan da yake jiyo kukan, wata matashiyar budurwa ya gani duk'e ta had'e kai da gwiwa tana kuka kamar ran ta zai fita, d'auke kan shi yayi daga kallon ta da niyar ya bar gun, kawai sai ya tsintsi kansa da kasa barin wurin sake juyowa yayi ya kalle ta take ya ji wani matsanacin tausayin ta ya shige sa.

D'aga k'afafun sa yayi ya k'arasa kusa da ita ya tsuguna yace "Asalama aleikum baiwar Allah lafiya mi yasa meki kike zaune bakin hanya kina kuka."

Firgigite tayi ta d'ago da sauri lokaci d'aya ta mike tsaye yarinyar buzuwa ce mai massifar kyau duk da hawaye da suka cika fuskar ta da idanun ta duk sunyi ja haka duk illahirin fuskar yayi ja abinka ka farin mutum, hakan bazai hana ka hango tsananin kyau da Allah ya mata ba sabida ko a cikin buzaye samun mai kyau irin nata sai an tona kuma sai ansha wuya gun neman koda za'asamu mai kyau irin nata sabida kyakyawa ce ta gasken gaske.

Zuba mashi manyan idanun ta tayi cikin na shi.

Take yaji wani abu ya tsirga mashi cikin zuciya da sauri ya k'auda idon sa yana kallon wani gefe yace "Baiwar Allah magana nake maki ko kurma ce ke ban sani ba."

Har yanzu idon ta na kanshi amma ta kasa magana, kusan minti biyu da yaji shiru ya juwo dan yaga ko ta tafi ne, sai yaga tana tsaye, har lokacin shi take kallon hawaye na k'ara bulbulowa ga fuskar, kuma tak'i magana, ganin haka yasa ya k'auda idonsa sabida bai jurar kallon cikin k'wayar idanun ta don da sun had'a ido wani abu yake ji yana masa zirrrrrrrrr tun daga saman kanshi har cikin tafin k'afar sa.

Da yaga bata da niyar yin magana sai ya juya da niyar barin gun da sauri ta rik'o hannu shi ta k'ara fashewa da wani matsanancin kuka mai tab'a zuciya.

Juyowa yayi da k'arfi yana fuskantar ta yace "Dan Allah baiwar Allah ki daina kukan nan wallahi har cikin rai nake jin wanan kukan naki."

Har yanzu dai kallon sa take hannuta rike da na shi kuma tak'i cewa komai, amma ta bar kukan sai hawaye dake anbaliya a fuskar ta kamar ruwan teku.

K'ara kallon fuskar yayi da tagama yin ja yace "Ki daina kukan nan kada kisama kanki ciwon kai, kuma ni ki sakeni na tafiya ta tunda baza kiyi magana sabida na lura ke ba kurma bace kina jin duk abinda nake fad'a." ya fad'i haka tare da fizge hannu sa daga nata.

K'ara sauri riko hannu tayi cikin wata siririyar muyar ta bud'e baki da kyar cikin kuka tace "Dan Allah ka taimaka min aike na akayi da 2000f shine yanzu ina shirin tsaleke titi wasu maza biyu suka zo suka sabce suka gudu gashi yanzu idan naje gida nace an sabce min wallahi dukan mutuwa za'a man ka taimaka min dan kashe ni zatayi, tun d'azu nake nan ba wanda ya min magana bar inyi tunanin za'a taimaka min se kai duk wanda na tsayar nace dan Allah ya taimaka min sai ya fara min wata maganar banza ni kam ba halina bane."

Tunda ta fara maganar ya k'urawa d'an k'aramin bakin ta ido yana kallon yanda take magana sannu sannu cikin nutsuwa da kuma yanda bakin ke motsawa. Jin shiru baice komai ba yasa ta d'ago da kanta ta ga ita yake kallo ko k'yabtawa baiyi da sauri ta saki hannu nasa tana ja da baya d'aga mata hannu yayi alamar ta tsaya sabida bakinsa ya masa nauhi, ja tayi ta tsaya d'an nesa dashi jikin ta na rawa sabida gani take shima d'aya yake da sauran mutanen da tayi ta tsayar wa, wanda a farin ganin shi da tayi bata mishi wannan kallon ba amma yanzu da taga ya tsura mata ido yana kallon ta kawai sai take ganin shima d'aya yake da sauran.

Cikin sark'ewar murya yace "Baiwar Allah dakata ba cutar dake zanyi ba tambayar ki kawai zanyi."

"To.... i...na jin...ka," ta fad'a cikin in ina hawaye na koma zubowa a fukar ta.

Shiru yayi na kusan sakan 5 sannan yace "Miyasa za'a yi miki fad'a idan kince sabce kud'in akayi? Su a gidan basu san.........." Bai k'arasa maganar ba sakamakon katse sa datayi.

Tace "Oh mon dieu (oh my god) idan fad'a ne kawai za'a min da sauki da bazan zauna anan ina asarar hawaye na ba kuma ina neman taimakon jama'a ba, kawai idan zaka taimaka min toh inko ba zaka taimaka min ba? na kama gabana tare da k'ara matso k'walla a idanun ta.

Wata irin ajiyar zuciya ya sauke tare da saka hannun sa cikin aljihun wanda sa ya ciro da kud'in sannan ya k'arasa kusa da ita yace karb'i kije ki siyo abinda aka aike ki siyowa sai ki koma gida, amma dan Allah ki daina tsayawa a hanya kina kuka kina min asarar tsadadin hawayen ki wanan ba girman ki bane kin ga ke ba wata karamar yarinya ba kuma ki daina fitowa ba hijab gaskiya kina barin kowa na kallon surarar jikin ki bazan lamun ta da hakan ban kuma shine yasa duk wanda kika tsayar yake gayami ki magana banza.

Sororo tayi tana kalonshi kamar taga wata sabuwar halita, sake waro ido tayi lokacin da idonta ya sauka kan kud'in dake hanun sa tace "Dan Allah ka rufa man asiri ni fa 2000 nace maka an sabce min ba wai 5000 ba taya zaka d'auki har 5000 ka bani ya zanyi da ita, kuma dakake cewa kan na daina maka asarar hawaye na na za'a kaima cewa kayi hawaye na to taya zan maka asarar su? da kace kada na sake fita ba hijab sabida ba zaka yarda ba to ni shine ban gane ba bawan Allah? Amma zan daina.

Wani irin had'ad'en murmushi ya saki yace "Nima bansan na fad'i hakan ba, amma tunda kince zaki daina ai shikenan kuma yanzu bazaki gane da cewa wanan kukan da kike nine kikewa asarar hawayen ki ba sai nan gaba insha Allah zaki gane, karb'i kud'in ni na wuce.

Saida ta nisa kamin tace "Dan Allah ka rufaman asiri ya zanyi da'ita sedai ka tafi mu tafi na sami canji sai na baka cikon."
D'aga k'afafun sa yayi ya fara tafiya tare da cewa "To mu tafi."

Jerawa sukayi suna tafiya kamar saurayi da budurwa masha Allah couple in su yayi suyi matuk'ar kyau duk idan suka gifta sai an kallesu shi kuwa da ya ga haka sai yai tunanin kowa itace ya ke kallo, tsayawa yayi cak ya daina tafiyar, juyowa tayi tana kollon sa da alama tambaya a bakinta amma kamin tace wani abun shi ya rigata.

Fido da rigar sanyin sa yayi tare da cewa "Karb'i wanan kisa naga kamar kina jin sanyi kuma mutane sai kallon ki suke" dayake lokacin sanyi ne.

Ba musu ta karb'i rigar ta saka ta soma tafiya bin bayan ta yayi da kalo tareda sauke wata kyakyawa ajiyar zuciya sannan ya fara tafiya.

Sun k'washi kusa da rabin awa a hanya suna neman canjin 5000 basu samu ba ja yayi ya tsaya yace kinga ni gaskiya nagaji dayawa kawai kije ni bar miki 5000 d'in juwo tayi ta kalleshi idonta ya shiga sosai cikin nasa wani irin fa'duwar kaba taji tayi sauri k'auda idonta ta tunanin miyasa gaban ta fad'uwa yanzu tayi alhalin tun dazu da take kallon cikin idonshi bata ji hakan ba sai yanzu.

Katse mata tunanin yayi yace "Lafiya kika yi shiru."

Ba tare da ta d'ago ba tace "To katsaya a nan dan Allah naje na kai kud'in adashan dama sune aka aike ni kaiwa tsausayi ya samesu idan matar ta bani cikon sai na kawo ma wallahi idan naje da cikon kud'in nan gida matsala za'a samu tunda kaga ga gidan da zan shiga can ba jimawa zanyi ba ina kai mata zan fito." ta fad'i haka tana nuna masa wani gidan.

Kollon gidan yayi sannan ya dubeta yace to jeki ina nan ina jiranki."

D'ago kanta tayi da niyar masa magana ta kasa sakamakon haduwa da idanun su su kayi sanadin jin wata irin bugawa da zuciyar ta tayi kawai sai tayi saurin juyawa ta fasa maganar ta nufi hanyar gidan.

A k'ala zata kai kusan minti goma da shiga gidan sannan ta fito, kanta na duk'e ta na kallon k'asa ta nufo idan yake tsaye yana jiranta.

Sallama tayi masa ya amsa sannan tace cikin sanyi jiki "Dan Allah kayi hakuri na b'ata ma lokaci daga taimako na, wallahi matar ta tsayar dani itama bata da canjin kuma har yaro ta aika ya nemo bai samu ba, shine tace na bar mata kud'in idan ta samu canji zata kaimin har gida, to shine na fito na tambaye idan har ka yarda sai ka gayamin ida zan sameka in ta maido da cikon sai na kai ma."

Murmushi yayi sannan yace wai miye kike ta wani sunne kai baki son kallo na tunda d'azu duk kin wani canza duk naga jikin ki yayi sanyi, kuma ni na ce maki na barmi ki sauran kud'in kawai ki rike idan ta dawo da cikon."

Waro idon tayi waje tana kallon wani gefe tace "So nawa zan gayama ka cewa da akwai matsala idan a gida a ka gani da kud'in nan dan Allah ka rufan asiri ka gayamin inda zan ganka? Don na mayar maka da kud'in ka, yanzu ma sedai nace ma mai a dashan idan ta sami canji kada ta kai min gida zan zo na karb'a wallahi."

Sak'e yayi yana kallon ta ita kuna ko da wasa bazata k'ara yarda ta sake had'a idon da shi ba.

Wani tunani yayi sannan ya saki murmushi yace "To gashi nikuwa bason na saka ki a matsala amma kinsan mi za'ayi? Gigiza masa kai tayi alamar a'a, sannan ya ci gaba "Yanzu muje ki nuna man gidan ku idan kin karb'o canjin sai naje da kaina har gidan ku na karb'a."

Ba tare da ta d'ago ba tace "Taya zaka gane cewa na karb'o."

"Bata yada zayi na gane kin karb'o gaskiya, amma ba gobe sai na dawo nazo na karb'a ba, sabida nasan bazaki fuce gobe da yamma ba baki karb'o kudin ba nikuwa sai nazo da dadare na karb'a."

Ba tare da tayi wani tunani ba tace "To muje na nuna maka."

Tafiya suke ba me cewa dan uwasa wani abu kowa da tunanin da yake suna shiga wata wahalaliyar anguwa wada kana ganin ta kasan ta irin wanan talakawa nan talak ne.

Ja tayi tatsaya dan nesa da wani gida batare da ta kalle shi ba tace "Kaga wacan gidan to shine gidan mu idan kazo nan zaka shiga ka tambaye dani sai na fito na baka kud'in ka."

Sak'e wayi ya kollon gidan da ta nuna masa ya kuma juyo ya sake kallon ta yakai a kala sau biyar yana hakan, "Ko kad'an yarinya nan batayi kama da wada ke rayuwa cikin gidan nan ba duk da kayan jikin ta ka'dai ya isa ka gane cewa d'iyar talakawa ce amma bai tab'a tunanin har ya kai haka ba, ya fad'i haka a zuciyar sa sakamakon ganin ginin gidan da yayi na jar kasa duk yabi ya rarake sabida idan a kusan gidan kake ma zaka iya hagon mutanan gidan sabida k'ank'antar katangar take ya kara jin tausayin ta ya mamaye shi burin zuciyar sa ya k'ara k'arfi, a cikin zuciyar sa ya ce "Allah ka cika min burina."

Katse maya tunanin tayi tare da mika masa rigar sanyin sa tace "Ungo rigar ka nagode ni zan wuce gida.

Juyowa yayi ya kalle ta itama shi take kallo da sauri ta k'auda idonta, murmushi yayi sannan yace "Ki rike na bar maki."

Saida ta sauke numfashi sannan tace "So nawa zan gayama ka cewa idan nashiga gida da wani abu wanda ba a sanni da shi ba zan shiga matsala amma ka k'i yarda." haka ta fad'a tare da sake mika masa rigar.

Yana karb'a riga kamin yace wani abu ta bar gun ta nufi hanyar gidan su, bin bayanta yayi da kallo har ta shige cikin gidan, a sanan ne ya tuno da ko sunnan ta bai tambaya ba, murmushi yayi sannan yace "Bai komi idan na dawo zan san sunan." daga nan ya bar gun ya kama gaban shi.

Ita kuwa tana shiga gidan wata 'yar dattijuwa ta yo kanta da masifa tace "Oh ni duniya ina zaki damu yarinyar nan tun yaushe na aike ki, amma dan gantali sai yanzu kika dawo kina can kina yawon iskancin ki da kika saba to yau uban mi ya tsayar dake kuma? Yo tambaya mima zan maki nida na riga da nasan hali? maza ki wuce daga gaban tun kamin na b'ab'alaki wallahi, nidai wallahi an barmin fitina miyasa uwarku da zata mutu baku mutu tare kika je can ki bita ni kawai sai a barmin jaraba ni da ban haihu ba amma wata ta haifa tabar min bala'i."

Jikin yarinya na rawa ta gusa da ga gun matar tana sauke ajiyar zuciya ko kukan ma kasawa tayi sabida sabo da tariga tayi da halinta taje ta d'auki tsintsiya ta fara share tsakar gida.

Da marece wajan karfe biyar sai ga matar da taje kaiwa kud'in adashe ta shigo gidan da sallama, matar gidan na zaune saman tabarma tana sauraran radio ita kuma yarinya na cikin wata rub'ab'a cuisine (kitchen) ta na dafa masu abincin dare, wanda tunda taji sallamar matar gabanta ya yanke ya fad'i da k'arfi har saida ta saka hannu ta dafe gaban ta.

Mai adashan ta shigo ta zauna kussa da matar gidan tana washe baki, "Ah yar uwa kece tafe da marecan nan bari na koyo maki ruwa." matar gidan ta fad'a tare da k'ok'arin mikewa.

"A'a yi zamanki banida k'ishirwa."

Komawa tayi ta zauna tana me cewa "To kodai wacan 'yar iskar bata kai maki kud'in ba ne."

A'a ki kwantar da hankalin ba shine ya kawo ni ba wata magana ce na zo muyi."

"Ah to shikenan ina jinki." matar ta fad'a tana mai sake gyara zama.

Mai adashan ta saka hannu a cikin jakar ta tafido da kud'i ta mika ta sannan tace "Ga cikon kud'in da dazu yarinyar ta kai min 5000 to banda canji sai nace tayi tafiyar idan nayi canza sa nazo nakawo maki, amma sai cemin tayi a'a kadana kawo maki na bari taje ta k'arba , to ni kuwa sai nayi tunanin ko so take ta kashe maki kud'in shiyasa na taso da kaina na kawo maki sauran canjin ki."

Aiko ran matar a matuk'ar b'ace tace "Ni wallahi ban aikata da 5000 ba da 2000 na aiketa nace taje ta kai maki, amma bari na kirata na ji gidan ubanwa ta samu kud'in nan sabida nima da kyar na sami 2000 d'in na bata ta kai maki cikin d'aga murya tace ke uban miye ma sunan ki zonan yau sai naji ubanda ya baki kud'in nan.

Yarinyar da tunda mai adashan ta shigo gidan hankalin ta ke tashe, tana ji kiran da aka mata tasan ba lafiya ba take cikin ta ya murd'a ya bada sauti k'ululu, mikewa tayi da sauri har tana tuntub'e ta fito daga cikin cuisine (kitchen) ta k'arasa inda suke ta tsugun bakin ta na rawa tace "Gani Ufadi."

Bata tantance ba ta ji saukar mari biyu a tatare da sauri ta dafe kunci ta tana hawaye.

Ufadi tace "Ubanwa ya baki 5000 da kika kai ma mai adashe banyan 2000 na baki? Tsinanniya tambad'ad'iya mai yawon gantali wane mazinacin ne da yaje ya gama shanye ki ya d'auki 5000 ya baki, oh ni yau naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba dama ni nasan jimawar da kikeyi baki dawo gida ba idan an aikeki yawon iskanci ne kike zuwa shegiya mai biyan maza wallahi halinki sai ya k'are kanki, bari ubanki yazo sai na fad'a masa shi dake d'aure maki gindi idan ance mashi kinyi abu yace bahaka bane to yau zai zo yaga abinda nake fad'a masa ya tabata da kina bin maza gashi kud'ad'en da suke baki tun kina b'oyewa har sun fara fito wa sannan kuma abiya ni tawa 2000 d'in wly, karuwa kawai tsinanniya, k'ara uban naki yazo ya san abin yi tun kan ki d'auko mashi abin kunya.

Da sauri ta d'ago tana kuka tace " Wallahi Ufadi ba haka bane." Ta kwashe duk abin da ya faru ta gayama ta na mai k'ara fashewa da wani matsanancin kuka, ban abinda ya mata ciwo kuma ya sata kuka shine cewa wanda ya taimaka da ta kira mazinaci shine babban abinda ya ke kara sata kuka, idan itane ta riga da ta saba da wa'inan mugayan kalaman nan daga Ufadi har sun daina d'aga mata hankalin, amma gashi ta ja ma bawan Allah da baiji bai gani ba daga taimakon ta, bata k'arasa zancan zucin da take ba taji Ufadi nace wa.

"Kinji mak'aryaciya toh ko uban ki bai isa ya min k'arya ba na yarda ba bare ke banza wofi kawai, ni maza tashi daga gaba na tun kamin na buge ki daga ganin wanan banzan halin naki na uwarku kuka d'auko tunda gashi shima tambad'ad'en dan uwan naki yana can yawan neman mata har Canada wai da sunan karatu itama karama an kaita wai Arlit gun k'anwar uwar ku Allah kad'ai yasan abinda ake can ana koya mata dagin tambad'ad'u sai ni aka bar make dan jaraba, miyasa kema ba'a kaiki wani gun ba. irin asarar da kuka d'auko halin uwarku.

Tashi tayi daga gun Ufadi ta koma cuisine (kitchen) tana hawaye cikin zuciyar tace najawa uwata zagi baiwar Allah dake can cikin k'abari bata masan abinda ake ba, niko wace irin d'iya mai jama uwarta zagi, kara fashewa tayi da wani kukan mai tsanani abin tausayi.

Mahaifinta na dawo Ufadi ta nufe shi da maganar ta kara hada abinda bata ji ba kuma ba tagani ba ta k'ulla makircin ta.

Rai b'ace mahaifin nata yace " Jeki ki kikara min ita" fita tayi tana murmushi ta shiga d'akinta tace ubanki na kiranki ko jiran abinda zata cewa batayi ba ta fice daga d'akin.

Tashi tayi hankalin kwonce ta nufi d'akin mahaifin nata sabida tasan tana gaya masa yanda abin yake zai yarda, da sallama ta shiga sannan ta sami guri ta zauna kusa da mahaifin nata tace "Abbu sannun da gida."

Kallon ta yayi sannan yace "Yawa Arahamat, Ufadi tazo man da wani zance da bangane inda ta dosa ba shine nace ta kirawo man ke naji gaskiyar maganar a bakin ki."

Saida ta sauke ajiyar zuciya sannan ta shiga labarta ma mahaifin nata abinda ya faru sannan tace "Wallahi abbu ni ban ma sansa ba a hanya na had'u dashi kuma na nemi ya taimaka min, gudun kar na dawo nace wa Ufadi an sabce kudin ta dokeni amma shine daga baya da ta sami labari tace zina nayi aka bani su kuma ma yace zai dawo ya k'arbi saura kud'in idan ba gaskiya na fad'a ba idan yazo a tambaye sa."

Lokacin da ta fad'i zina mahaifin nata ya runtse idon sa har saida ta yi shiru kan nan ya bud'e yace "Shikenan tashi kije idan yazo karb'a kud'in nasa ki ce yazo ina neman sa.

To tace sannan tashi ta bar d'akin a bakin k'ofa ta tarar da Ufadi rai b'ace sanadin jin duk abinda suka tatauna ita da mahaifin ta alhalin ba haka taso ba...

Gaisuwa mai tarin yawa ga duk wani mai kauna ta da kaunar litafin nan ina ma kowa fatan alkairi.........πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–πŸ’–
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZANBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


ECRITE:


_PAR_


*QUEEN ZEEFAT*


Yar
Mutan
Niger


Wattpad@nazhabibou




πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/




_BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM_




Page: 11 & 12


Sanadin gigitaciyar k'arar da Arahamat ta saki yasa 'yan cikin d'akin suka fitu da gudu har suna bangazar juna kowane na k'ok'arin k'arasa ida take a yashe babu alamun numfashi a tatare da ita, suna k'arasowa tashin hankalin da suke ciki ya k'ara nin kuwa, a tare suka durkusa gaban ta suna kiran sunan ta su girgiza ta, sabida tsanani tashin hankalin ko lura da namijin da ke rik'e da ita yana girgiza ta basuyi ba, wanda shine bak'on da yayi sanadiyar firgicin ta har ya kaita ga suma.

"S'il te plait ma soeur reveille toi dan Allah il ne faut pas partir me laissΓ©(Please my sister wake up dan Allah you must not leave left me)" Bak'on ya fad'a yana mai k'ara girgiza ta.

Duk da maganar da yayi hankalin su bai kai garesa sunata Arahamat, tanti Fatima ce tayi hausar tafiya ta d'ebo ruwa, tana zuwa ta zuba mata ruwan, wata atishawa tayi da k'arfi tare da sauke ajiyar zuciya mai k'arfin gaske, sannu a hankali tafara bud'e idonta har ta sauke su kan tanti Fatima da kiran sunanta tana mai jero mata sannu.

Tare da cewa "Lafiya Arahamat miya firgita dake haka har kika suma mu mun fito ba muga komi ba."

Da sauri ta mike zaune tana mai zubar da hawaye, tace "Tanti wallahi yaya Ibrahim nagani ya shigo ta k'ofar gidan nan dan Allah kada kuce man ba shine ba Kar kuce man mafarki ne nake."

Da sauri Tanti Fatima ta juya ta na kallon k'ofar shigowa gidan, shima da sauri ya matso kusa da Arahamat dake zubar da hawaye har yanzu yace "Nine k'anwata ba mafarki kike ba zahiri ne."

A tatare suka juyo daidai saitin da suka ji muryar shi ta fito suka tsura masa ido suna kallon shi baki sake, kowa ya kasa magana, da sauri Arahamat ta fad'a jikin sa tana kuka sosai tare da cewa "Ashe yaya zan kara ganin? kulum sai nayi kukan rashika a tare da mu ba kad'an mukayi kewarka ba, ashe dai yaya kana raye ka manta da mu? Mu kuwa babu ranar da ba zamuyi hirarka da Abbu ba, amma kai kana can kana jin dad'i ka manta da mu se mune muka damu dakai kasan cikin tashin hankalin da muka shiga kuwa sabida rashinka a tare da mu......." kasa k'arasa maganar tayi dalilin kuka da ya ci karfinta.

Sukuwa su Tanti Fatima kasa magana sukayi suna ta kallon shi cike da mamaki shine kuwa ko wanine me kama dashi, tare da tambayar kansu lokacin da ya shigo gidan da ta inda ya fito?

D'ago ta yayi daga jikin sa yana cewa "Dan Allah kuyi hakuri soeur (sister) wallahi ninan nafi ku damuwa sabida ku nan kuna ganin juna nikuwa ni kadai ne a can ba wanda nasani, kumin uziri mana tunda ba kusan abinda ya hanani zuwa gareku ba."

Sai a sannan Tanti Fatima ta sami damar magana tace "Oh Allah Ibrahim ashe kana raye? munan har mun sadak'ass muyin tunanin ka koma ga mahalicinka ashe Allah

Please Login or Register in order to submit comment