Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

message ne."


Eh nagani ai tunda naga inda yake gabatar maki da kansa AFREEN ke ce kike hani da yiwa ɗan adam wulaƙanci, amma kece yau ke shirin yin wulaƙanci ga ɗan uwanki Musulmi, bawani mugun abu ba yake neman gunki sonki ne kawai yace yanayi miyasa bazaki saurare shiba kiji da miyazo Allah kaɗai yasan yanda yasha wahala kamin ya samu numbaki duba ga wanda babu me number ki ko a family mu masu numbaki basu wuce muntun biyar amma yayi yanda yayi ya nemo numbaki sannan ya nemi labari a kanki ki basa dama mana kiji dami yake tafe." Firdaoussi ta faɗa tana mai kallon AFREEN.


AFREEN tace "Haba Firdaoussi kisan fah karatu nake babu soyayya a cikin tsari na yanzu sabida bazan iya haɗa karatu da soyayya ba kuma kina gani shima fah bai saniba bai taɓa ganin fuskata ba to ganinki duk ranar da ya gani ni akwai matsala kuma duka shekaru na 18 amma harzan fara cazawa kaina ƙwaƙwalwa a wani batun soyayya ina gudar wa kaina abinda bazan iya ba ne shiyasa amma banda wannan Ni banada niyar wulaƙanta shi sabida kin san hakan ba halina bane."


Firdaoussi tace "Yo ai rashin mayar masa da amsa shi zai iya fassara hakan da wulaƙanci kuma miye a cikin soyayya da ba zaki iya haɗa ta da karatu ba sannan ita soyayyar kika yiwa ƙanƙanta AFREEN shekara 18 din ne ba masu yawa ba ko so kike sai bayan ki sami degree da diploma sannan zaki nemi mijin aure a lokacin da yuri ya rigada ya ƙuremaki? to tunyuri ki fida wannan a ƙidarta daga cikin kanki kawai ki saurare shi koda kina cikin karatun ne kina iya yin soyayya harma kiyi aure can gidan mijin sai ki ƙarasa karatun hakan shine daidai ba wai ki tsaya jiran sai kin gama karatu ba sannan kuma ai ba munmunar kama gareki ba tunda muma muka iya jure kallon ki kowa ma zai iya idan har yasa ba AFREEN wannan fitinanan kyau da Allah yayi maki idan an gani ai za'ayi tunani ke kika tsara kanki kuma Allah kaɗai yasan gidan wadan zai wannan kyau naki ya adana wallahi dole mutum ya ganki zaice kamar aljanna dan masifar kyauki, haka dai Firdaoussi tayi ta nunawa AFREEN mahimmanci kula KAMAL da jin abinda yazo dashi har AFREEN ɗin ta yarda zata saurare shi ɗin.


Suna zaune suna fira Firdaoussi na nunawa AFREEN yanda taka mata ta mayar wa KAMAL da saƙo, aka buɗe ƙofar ɗakin aka shigo da sallama, Hasina ce ƙawar AFREEN wada suke school guda tashigo haka itama AFREEN taje ta tarbota ta rungume ta tare da cewa "Welcome besty tana murmushi tareda farin cikin ganinta sannan suka saki juna tare da nufar bakin gadon kusa da Firdaoussi suka zauna Hasina da Firdaoussi suka gaisa sosai sabida su san juna tun ba yauba ta dalilin AFREEN sannan sukaci gaba da fitar su cikin aminci da kaunar juna, bayan sallarsa azahar kuma bayan suci abincin rana Hasina tace ku tashi muje ku rakani KALLA TRANSA MALL suyo shopping, AFREEN tace "To muje daga can sai mu wuce gidan anti Fauziya."


Tare suka miƙe suka ƙara fesawa jikinsu turare sannan Hasina da Firdaoussi suka ƙara ƙara murza hoda ga fuskar su banda AFREEN da ita dama ba ma'abuciyar kwalliya bace uwa uba ita niƙaf ma take sakawa, fita sukayi a ɗakin AFREEN taje tayiwa maman sallama ta fito a falo ta tardo Zeinab tace "Zeinab jiki ki sako hijab ɗin ki mu tafi gidan anti Fauziya."


Da sauri Zeinab da mike ta faɗa dakin su dan doko hijab ɗin ta itakuwa AFREEN ta ɗaura niƙaf ɗinta sannan suka fito gun ajiye motoci suka sa AFREEN ta jawo motar sannan suka shiga dai dai nan Zeinab ta ƙaraso itama ta shiga me gadi ya buɗe masu get suka fice daga gidan.




**** **** ****

Yau Alhamis ranar da AFREED yayi wa Tanti alkawarin zuwa Maraɗi hak kuwa aka tun jiya suke Ali ya gyara kayan sa da na AFREED aka suma ƴan biyun Momy sun shirya misalin ƙarfe 9 na safe sukayiwa garin Niamey ban kwana suka ɗau hanyar Maraɗi tare da addu'ar Allah ya kiyaye hanya daga iyayen, a moto ta sukayo tafiyar sabida AFREEN yace bazai yi balaguro cikin ki jirgin ba don a kowane lokaci indan zai yi balaguro to a jirgi ne to wannan karon wace a mota yake sabida yanason yaga hanya sosai sannan ya hana duk wani escort ɗin sa biyo sabida baya don ta kura soyake yayi rayuwar kamar shi ba wani mai matsayi bane idan yaje Maraɗi, Ali ne kejan motar AFREED na zaune wajan mai zaman banza su kuwa ƴan biyun Momy suna baya ana ta ɓana rai sabida AFREED ya hana su bin jirgi yasa zasu wahala a mota, sosai Ali ke gudu da motar ita kuwa Tanti dandanan ta kiransu don jin idan suke, yau Tanti tana cikin farin ciki AFREED zaizo tun safe take ta gyare gyaren ta



Da yake lafiyayar motace sabuwa fil da ita ƙarfe 3:40 suka shigo garin Maraɗi wata sanyayar ajiyar zuciya AFREED ya sauke ya na jin kansa cikin wani matsanancin farin ciki alhamdulilah ya furta a zuciyarsa yace nayi nesa da takura da yanzu ana nan duk an zagaye da sunan tsaro ya sake cewa alhamdulilah.


Anguwar zaria Ali ya nufa bakin wata tangajejiyar get Mai kyau da ɗaukar ido Ali ya ja ya tsaya sannan ya dana hon da gudu mai gadi ya leko ta ƙaramar ƙofa dan ganin masu dana hon ɗin idansa bai sauka a kowa ba sai ga AFREED ai kuwa yana ganin sa ya ganesa tare da yin saurin rufe ƙaramar ƙofar ya wangale masu babba ƙofar a take Ali ya dana hancin motarsa a cikin gidan gudu mai gadi yayi ya bi bayansu tareda yafito mai ba flower ruwa ya mai nuni da ya biyo bayan sa a guje shima yabi bayan mai gadin, inda ake ajiye motoci Ali ya nufa yayi parking ɗin motar tasu kamin suke fitowa baki ɗaya duk a gajiye gudu gudu sauri sauri Tanti takeyi dalilin jin zuwan shalelen ɗan nata tana kawowa ida suke tayi saurin rungume AFREED tane cewa "Alhamdulilah yau gani ga ɗana AFREED Allah yayi zan ƙara ganin ka cikin garin Maraɗi na godewa Allah da ya kawo min ku lafiya" ta faɗa tana rabashi da jikin ta sannan ta juya ta kamo hannu Ali tace "Ɗana sannu ka da ƙoƙari AFREED ya baka wahala ya hana ku biyo jirgi ahalin shi ba tuƙa motar zaiyi ba kawai dan ya gajiyar min daku."


Murmushi Ali yayi, sannan ta mayar da duban ta gun su Farisa tace ku ƙaraso mana ƴan biyun Momy ƙaraso wa sukayi da murmushi kwance a fuskar su riƙe hannayensu tayi sannan tace "To ku huce muje ciki kusamu kuyi wanka ku huta ku ci abinci."


Hannu ta riƙe da su Fariya tayi gaba su AFREED na bin bayan ta tana jinta cikin da farin ciki haka suka ƙarasa cikin wani haɗaɗen falo mai girma man gaske duka suka zube a kujerun dake falon a matukar gajiye AFREED ya ɗago yace "Tanti ina yuni mun sameku lafiya?"

"Lafiya lau alhamdulilah yasu Falmata dafatan kun barosu lafiya."


Nan dai suka shiga gaisawa kamin AFREED ya miƙe yace da tanti shi zai yayi wanka sannan ya kwanta dan ba ƙaramar gajiya yayi ba sabida rabon da yayi balaguro a mota yanzu kusan shekara goma sha biyu kenan baisan zaiyi irin wannan gajiyar ba da jirgin zasu biyo, ɓangaren da aka gyara kawai da sabida shi da Ali ya nufa sabida yasan shine dan tun yana yaro yake, idan yazo nan ne suke sauka, kuma kullum gyara ɓangaren ake kamar akwai mutane a cikin kokuwa ace mamalakin yurin kullum yana zuwa wannan zuwa ma da zaiyi hada pinti aka canzawa ɓangaren aka fitar da kayan dake ciki aka zuba sabi masha Allah andai ƙawata ɓangaren sosai abin gwanin sha'awa.


Shima Ali Bin bayansa yayi, binsu Tanti tayi da kallo da murmushi ɗauke a fuskar ta kamin take mayar da kallon ta gun su Farisa tace "To ku ƴan biyu ku taso muje ku ci abinci tun da su wa'ican sun tafi su yi bacci su huta."


Fariya tace "Tanti muma bamu tare da yunwa sai gajiya idan muka yi wanka muka huta sai mu ci."


Tanti tace "To shikenan ku taso muje sai kuyi wanka ku huta kuma bin bayan ta sukayi, kiran ma su aiki tayi tace masu su shigo masu da kayan su cikin ɗakin sabida mai gadi da mai ban ruwa bakinsu falo suka shigo dasu.


AFREED sunayi Wanka suka yi sallar la'asar sai bacci kowane daga cikin su ya kwata kwanan gajiya, sune basu tashi ba sai da ana kiran sallarsa magariba, sukuwa su Fariya har saida Tanti ta tayar da su sannan suka tashi.


Wanka AFREED yayi tare da ɗauro alwala sannan ya fito a gagwace ya shafa mai da turare tareda zura doguwar jalabiya ya fito da sauri dan yaji ana ƙoƙarin tayar da sallah a masallaci dake kallon gidan yana fitowa ya gamu da Ali se kawai suka jera suka tafi tare sune basu dawo gidaba sai bayan sallar isha suna shigowa mai gadi yayi saurin tasowa yana cewa "Sannu da zuwa Alhaji ƙaramin da fatan an iso lafiya?"


Murmushi AFREED yayi yace "Lafiya lau baba mai gadi mun sameku lafiya?"


"Lafiya lau to sannu ku da zuwa?"


Da yawa Ali ya amsa sunan suka bargun duk masu aikin gidan sun san AFREED da Ali da zarar ance maka AFREED yazo to sun bar zama ba kuɗi ko da kuwa bai da su sai yaje ya karbo gun Tanti ko gun mijinta ya shiga raba musu tun yana yaro haka yake bare yanzu da yayi shekaru ba zoba gashi duka sun matsayin sa a yanzu suna sane da sai sun sha kuɗi sosai kamin ya tafi.


Suna shiga falon Tanti suka tardo tare da yaranta ƴan mata wato Khadijah da suke shekara guda da su Fariya sannan Amal mai bi mata sai kuma Ummi mai sunan kaka su AFREED ta wajan uba da gudu yaran suka tashi suka nufi su tare da rugume suna oyoyo yaya AFREED oyoyo yaya Ali banda Khadija da takasa ƙarasawa tayi tsaye a kusa da su ta sunkuyar da kai tana murmushin, don sosai take jin kunyarsu bama kamar Ali da take matukar so amma shi bai masan tanayi ba.


Da murmushi kwance a fuskar AFREED yace "To ku cikamu kada ku kayar damu sakin su sukayi suna dariya, cike shagwaɓa Ummi tace "Yaya ni sai ka ɗauke ni."


Murmushi AFREED yayi sannan yace "Kai mai sunan kaka har yanzu wannan shagwaɓar tana nan."


Jan hannu ta yayi ya zauna kan kujera ya ɗoketa ya aza kan ciyoyin sa yana mata dariya itama dariyar tayi, Amal kuwa ta kamo hannu Ali tace "Yaya zo muje ka zauna bari yaya AFREED da wacan rigima miyar."


Binta yayi suka zauna a ɗayar kujerar ya na mamakin yanda AFREED ya saki jiki ba kamar da idan sun zoba yau shine hada rugume Ummi yana surutu haka."


AFREED ne ya lura da Khadija dake tsaye tanata murmushi kanta a duge yace "Khadija ke kam yaushe ne zaki daina jin kunyar mutane ne wai?" zo nan naji miyasa kike da kunya haka ne kamar ɗiyar Fulani?"


Ƙarasawa tayi kusa dashi ta zauna a kasan kapet daidai ƙafafun sa, sannan tace "Yaya ina yuni ya hanya da fatan kunzo lafiya?"



"Lafiya lau mukazo Khadija mun sameku lafiya?"


Saida taƙara sune kanta sannan tace "Lafiya lau yaya ya kuka baro su Momy?"


"Lafiyar su lau kidaina jin kunyata kinji ƙanwata ki saki jikinki muyi fira."


Murmushi kawai tayi ta ƙara duke kanta seda ta daci kallon Ali kamin tace "Yaya ina yuni anzo lafiya?"


Wani haɗaɗen murmushi ya sakar mata wanda shi kanshi baisan yayi mata shi ba ita kuwa anan take wata soyayyar ta ƙara shigar ta ai da sauri ta kauda idonta daga gareshi. Ali ya amsa da "Lafiya lau Khadija ai ni yau ina fushi dake ne sabida kwata kwata yau baki ganina sai AFREED?"


Kara sunkuyar da kan nata tayi tana jin soyayyar sa na ƙara shigar ta sabida duk wani harafi da zai faɗa a maganarsa tsikar jikinta tashi take, tace "A'a yaya ba haka bane?"


Ali yace "Yane idan bahaka bane ba gashi gunsa kikaje kika zauna ba, to idan dai ba haka bane ki taso ki dawo kusana muyi hira."


Kasa tashi tayi daga inda take sabida ita kaɗai tasan halin da zata shiga idan har ta koma kusa dashi anan ɗin ma da take zaune ya ta ƙara bare ta koma kusa dashi."


Murmushi AFREED yayi yace Khadija tashi ki koma kusan sa shi nikam Ummi ta isheni abukiyar hira shi kuwa ai tunda surutu ya masa yawa ai ko mutum goma zai iya haɗawa yayi caca baki dasu."


Tayi niyar tashi sai ga su Fariya sun fito daga ɗaki, suna ƙarasowa nan cikin falon su shayo kwalliya masha Allah sai zuba kamshi suke.


Suna ƙarasowa suka nemi guri suka zauna tare da cewa "Tanti ina yaya Umar ne yazo ya kai yawo."


Tanti dake ta sauraran ɗiyan nata tun ɗazu tana murmushi tace "Yanan saman hanya tessaoua yaje tunda safe wajan wani aiki yanzu kunga ya shigo to wai da kukayi shirin fita abinci fah?"


Ali yace "Gaskiya dan ni yinwa nakeji kusan ni bana jimirin yunwa ko."


Tanti tace "Shikenan ku tashi muje kuci man ko kuwa a kawo abincin nan?"


Ali yace "Tanti akayo nan kawai sai ci a saman kapet."


Haka kuwa akayi suka nemi guri Fariya Farisa da Khadija sukaje su ɗauko kulolin daga kan dinning su ka kawo su nan cikin falon Khadija duƙa tayi servir ɗin su ta zubawa kowa sannan suka gewaya gaba ɗaya suka faracin abincin cikin farin ciki...........
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
ZAMBA CIKIN AMINCI
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


Écrit


Par


*QUEEN ZEEFAT*


_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_



*_Wattpad@nazichou*_




💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003



*_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_*



*Page* : 27 & 28


Suna cikin cin abincin Umar babban ɗan Tanti ya shigo falon da sallama ɗauke da bakinshi, gaba ɗaya suka ɗago tare suna masu amsa sallamar da murmushi ɗauke da fuskokinsu, da gudu ummi tashi daga kan ƙafafuwan AFREED taje ta rungume ɗan uwan nata, dariya yayi tare da ɗaukar ta sannan ya ƙarasa inda suke.


Mahaifiyarsa ya gaida ta masa da murmushi ɗauke a fuskar tana masa ya hanya, juyawa ya gun su AFREED yana dariya yace "Wata sabon gani broh yau kaine da kanka zaune cikin garin Maraɗi a cikin falon mama, yaude kam mama zata kwana farin ciki sabida kullum bakinta ya dauke da sunanka Ita dai AFREED, broh da ace lokacin damina ne yau da Allah sai yayi ruwa bansa wace addu'a bace mama tayi har Allah ya kaɗo mata kai yau garin nan."


Dariya sosai Ali yayi sannan yace "Kai AFREED kowa yasan baka son fita daga garin Niamey kowa nason ganin ka amma kaje ka zauna gu ɗaya."


Murmushi AFREED yayi yace "Umar irin wannan shari haka kamar dai ban taɓa zuwa Maraɗi nan ba to ni na dawo nan da zama bakiɗaya ma ta man shari sai ta ƙare, kai kuwa Ali ɗan sa ido duk abinku baku isa ku haɗa Ni da tanti ta ba."


Umar yace "Ba wani shari an san halinka ne ni yanda ma akayi ka zauna anata hira da kai haka ko ka iya ɗumine yanzu? dan nasan magana wahala take maka AFREED."


Ali yace "Ashe kaima ka gano haka tunɗa zu yake ban mamakin maganar nan da yake da har yanzu banji yace ya gaji ba."


Murmushi AFREED yayi baice komai ba sannan cema Umar "Yanzu dai zauna kaci abincin nasan ka kwaso yunwa idan ka gama sai ka ƙarasa min iskancin ai naga kaima ba zuwa garin namu kake ba."


Umar yace "Aidai nafika tunda ni ko wata uku bayin ba da naje garin naku ba."


AFREED yace "To anji zauna dai ka cika cikin ka tukun na."


Zama Umar yayi sannan ya kalli su Farisa yace "ƴan biyun Momy ashe daku akazo da fatan kunzo lafiya wannan gumkin ɗan uwan nawa injin dai bai ta kura ku ba a hanya."


Murmushi su kayi tare sannan sukace "Yaya ina yuni lafiya lau muka zo kuma babu abinda yaya yayi muna a tare suke maganar babu mai wuce ɗan uwan sa kamar ɗaya tasan abinda ɗayar zata ce.

Umar yace "Allah ya mashi sa'a da ace ya taɓa min ku ai dan yanzu na rama maku."

Murmushi AFREED yayi baice komai ba sabida ya fah gaji da maganar nan dan ba ƙaramin ƙoƙari yayi ba yau na magana mai tsayi da yayi har haka."


Umar ya dubi Ali yace "Gaskiya Ali kana fama ban masan ya kake zama da wannan ɗan uwan naka ba?"


Ali yace "To ya zanyi haka nan dai nike ɗan hakuri da shi kamin ya ɓata min rai na bigeshi ai matar sace ke da aiki nan gaba."


Gaba ɗaya suka kwashe da dariya har da tanti, AFREED ya kalli su Farisa ya game fuska kamar bai taɓa dariya ba yace "Kun wani zauna kuna yiwa mutan dariya dan samun yuri to maza ku bar nan tun kan raina ya ɓace nayi maganin ku." sumi sumi suka tashi su duka harda ummi suka bar gun dama su daɗe da gama cin abincin har sun gyara gun da suka gama.


Tanti da farin ciki ya cika mata zuciya ta kalli AFREED tace "Ji AFREED ka korar min yara ba sai ka bari ayi ta duramar nan da suba suma su rage dare tunda basu sami zuwa yawon ba."


AFREED yace "Tanti kawai sai su zauna suna jin hirar mutane kawai su rai namu."


Tanti tace Hum AFREED uwayan son girma."


Hira sukaci gaba dayi har dare ya soma yi sannan sukayi wa Tanti sallama suka koma ɓangaren su, suna shiga Umar yayi nasa ɗakin tare da ce masu ya shiga yayi wanka dan cewa yayi tunda su AFREED sunzo to yadawo ɓangaren su da zama ya baro nasa sai kuma idan sun koma tunda ɓangaren da su AFREED suka sauka yana ɗauke da ɗakuna huɗu ne.


Umar na shiga ɗaƙin shi Ali ya dubi AFREED yace "Broh yana ga yau kanta hira sosai ka saki jiki ana kwasa hira dakai don gaskiya kaban mamaki ko dai ka fara koyon yawan magana ne bansani ba?"


Kallon shi AFREED yayi sannan yace "Wallahi broh daurewa kawai nake sabida tanti tana farin cikin zuwana bai kamata nayi gum da baki naba dan gudun kar farin cikin nata ya koma ciki sabida rashin magana ta duk da itama tasan ban wani cika yawan magana nayi ba, amma bancin haka wallahi nan duk nagaji da maganar da nayi yau."


Ali yace "To haka da kayi yayi daidai yanzu sai kaje ka kwanta dan bakin naka ya huta tunda ma kaga dare yayi."


AFREED yace "Hakane bari naje na ɗan watsa ruwa sai na kwanta."


Daga nan kowa ya nufi ɗakin sa domin samun bacci da hutu mai kyau,sedai muce asuba ta gari su AFREED.


**** **** ****

AFREEN suna fita daga gida direct wajan shopping suka nufa suna ida shopping sukayi gida anty Fauziya, sosai tayi farin cikin ganin su haka su ka wuni gidan, a nan ne Firdaoussi ke yi Hasina maganar KAMAL, Hasina najin zancen tayi farin ciki sosai, ta ƙara bawa AFREEN kwarin gwiwar kula shi haka dai suka tasa ta a gaba suna nuna mata mahimmanci fara soyayya sukace dan Allah ta bashi dama.


Sai bayan magariba suka bar gidan anty Fauziya sabida saida suka mata girki, don sunce tunda sun zo ta huta gata da tsohon ciki na wata shida kuma mai mata aiki ta tafi garin su sabida rasuwa da kakar tayi shine taje gaisuwa, da zasu tafi anti Fauziya ta haɗa kowace daga cikinsu da leda ɗoke da kayan kwalliya da turaruka masu ɗadin kamshi, ita kuwa AFREEN turaruka kaɗai ta saka mata sabida tasan ita ba ma'abuciyar kwalliya bace.


Suna fita daga gidan anty Fauziya suka nufi anguwar su Hasina suka ajiye ta a ƙofar gidansu sannan suka nufi gida a bakin ƙofar gidan su Firdaoussi AFREEN taja ta tsaya sannan itama Firdaoussi ta sauka tana masu saida safe, idan masu karatu basu manta ba ai nace muku gida biyu ne a haɗe waje guda wato gidan Alhaji Sadisu mahaifin su AFREEN da na yayan shi Alhaji Adamu wanda shi Alhaji Sadisu ne ya gina wa ɗan uwan nasa dan haka suke makwabtan juna katanga ce kawai ta rabasu to Firdaoussi ɗiyar Alhaji Adamu ce kuma itace suke ƴan wari guda da AFREEN.


AFREEN na shiga cikin gidansu tayi parking ɗin motar ta wajan da suke ajiye motoci sannan suka fito ita da Zeinab suka nufi ɓangaren Hajiya Zakiya wato kaka su wada ta haifi mahaifin su, suna shiga suka tardo ta saman darduma da alama sallah ta ƙare, zama sukayi saman kujerun dake cikin folon sannan suka ce Mamy (Kaka) ina wuni ya yunin gida?"


Da murmushi take kallon su sannan tace "Lafiya ƴan albarka jikoki na sai yanzu kuka dawo daga gidan Fauziyar? ɗazu Sadisu ya shigo nan nake tambayar sa AFREEN dan naga duk yau baki shigo nan ba, sai yace ai kuna gidan Fauziya."


Murmushi AFREEN tayi tace "Eh Mamy wallahi sai yanzu muka dawo mun kama mata aiki ne kinsan tayi nauhi sosai cikin jikin tane ɗan wata shida amma saika kace yau ko gobe zata haihu da tsananin girman sa."


Hajiya Zakiya tace "Allah ya raba lafiya, ai ita Fauziya girman ciki ne da ita."


Da ameen suka amsa sannan AFREEN tace "Mamy ga tsarabarki inji anty Fauziya tace a kawo maki wannan kuwa da mukaje shopping na siyo maki dan ki motsa bakin ki."


Karɓa Hajiya Zakiya tayi tanata sa masu albarka da masu fatan samun miji na gari, sannan suka mata sallama suka koma nasu ɓangaren, basu sami kowa a falon ba dan haka kowace ta nufi nata ɗaƙin dan a gajiye suke, direct AFREEN tana shiga ɗakin ta toillet ta faɗa ta yi wanka tare da ɗauro alwala dan gabatar da sallar isha'i, tana idar da Sallah tayi shirin bacci cikin wasu haɗaɗun kayan bacci farare riga da wando masu mugun kyau, sannan ta saka dogon hijab har ƙasa ta fita daga ɗakin, ta nufi ɗakin mahaifiyarta da sallama tashiga, bata sameta a ɗakin ba, a sannan ne ta tuno da yau girkin maman ne kenan ta ɗakin mahaifin su, bata tsaya komai ba ta fita a ɗakin ta nufi ɗakin tanti zaune ta tardota ta na kaɗa wani magani da tasaka ma kindurmu tana motsawa, da spoon sai ga AFREEN ta shigo da sallama saida tanti ta ɗan firgita kamin ta basar tana mai amsa sallamar tare dacewa "Yawa AFREEN dama yanzu nake cewa bari naje na kai maki maganin nan ɗakin ki kuma naga kun dawo lafiya, tunda ma kinzo da kanki yi maza zauna kisha," ba musu AFREEN ta zauna ta karɓi kofin da maganin ke ciki tayi bismillah sannan ta kafa kai ta shinye ruwa tanti ta koma zuba mata a kofin ta karkaɗe ta mika mata karɓa tayi ta kuma shinyewa kamin take mayar ma tanti da kofin tare da miƙewa tana shirin barin ɗakin.


Da sauri tanti tace dakata AFREEN kada ki tafi baki ƙarasa shan maganin ba," dawowa AFREEN tayi ta zauna sannan tace "To tanti yi sauri ki ban bacci nakeji."


Da sauri tanti ta ƙara ƙaɗa mata wani maganin ta mika mata, koma ƙara kafa kai tayi ta shinye, sannan kuma tanti ta miƙa mata wani magani ƙule a leda tace "Ƙarɓi wannan idan kin shiga

Please Login or Register in order to submit comment