Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ƙara so inda suke a tsaye momy kaɗai ke zaune tana kallon su tana sakin murmushi."


Cikin zolaya dady yace "Oh ni ƴan biyun Momy su zasu kayar dani ban san ranar da zasu girma ba su daina rigima da shagwaɓa, tunda sun girma sun ƙi yarda da hakan gashi yanzu suna shirin karya ni daga dawowa na."


Sakin sa sukayi suna dariya tare dan toro baki gaba suna ɗan bubuga ƙafafun su a ƙasa cikin shagwaɓa suka ce a tare "Gaskiya mu kam papa bamu girma ba har yanzu yan pici pici muke."


Gaba ɗaya ɗakin suka kwashe da dariya Dr Inusa yace "Kai lale ƴan biyu akwai rigima irin wannan shagwaɓa haka, da sauri suka koma mazaunin su suka zauna suna rufe fuska da murmushi kwance a fuskar su wai su sunji kunya.


Dariya duka ɗakin suka komayi sannan doctor ya koma cewa "Haka nake da su kai kasan cewa ma ƴan matan ne ke shagwaɓaɓi ni har ƴan mazan haka suke da girmansu gwaɗe gwaɗe basu jin kunya haka suke zama suyi ta zuba min shagwaɓa."


Dariya sukayi sannan dady ce "Yaran ne namu na yanzu duk sangartaci ne gata ya masu yawa, har wannan mara lafiyar wata ran haka yake Ali ne kaɗai ya nuna ya girma amma shima ba kullum ba idan ka tarda su suna yiwa mahaifiyar nan tasu shagwaɓa zaka ce wasu ƙananun yara baiwar Allah ai tana fama dasu ta iya ɗaukar rigimar kowa a cikin ni har tausayin ta nake idan suka mamaye ta suna mata rigima ba babba ba yaro kuma kamar haɗin kai lokaci guda suke aza tabara su ka dai gansu."


'To Allah dai ya raya ma musu cikin koyi da addinin musuluncin nikam duk sun fi takura man kan mahaifiyar tasu inda ina gari ta kullum suna liƙe da ni suna min taɓara ba kamar yanda mahaifiyar zasu mata ba su mata shagwaɓa kamar yanda suke ko fa bani ƙasar zakaga sun kirani suna ta zuba min shirme, ita mahaifiyar tasu kaga AFREEN ɗiyar ƴar uwar ta wato matar Alhaji Sadisu, idan kaga tana zuba mata shagwaɓa tana biye mata kamar wata ƴar jinjira sosai suka shaku da ita kamar zata mayar da ita ciki har dariya suke ban idan suna appelle video ita da ita suna shirmen su kwani ban dariya."


Lokacin da doctor ya faɗi sunan AFREEN sedai AFREED dake kwana yaji wani irin faɗuwar gaba dan har cikin baccin sa yaji an faɗi sunanta har sai da ya ɗan motsa ƙafar sa da hannu sa na dama amma ba wanda ya lura.


Dady yace "Hakane dama wata soyayyar Allah ke haɗa ta, ni kamayi batun Alhaji Sadisu ka tuno man da auren ɗiyar sa nan da sati ɗaya ban san ko ka sani ba?"


Dr Inusa yace eh na sani ya faɗaman shi yasa ma har yanzu banje Maraɗi ba so nake nayi tafiya guda da ta zuwa ɗaurin aure da sabida aiki, kuma madame ta kirani ta ce tana son zuwa hidimar bikin nace ta bari har ƴar lelan ta AFREEN za tayi aure sai su taho su duka a lokacin Inayah tayi nisa da karatu shi Aban ya riga da ya ƙarasa har ya fara aiki Fujai ne dai bai fara aiki ba tukuna sauran wata bakwai ya ƙarasa karatu sa ka kenan sai su zo tare baki ɗaya."


"To madala Allah masu albarka idan bikin ya tashi sai kamin magana mu tafi tare har da maman ƴan biyu za muje tare insha Allahu da ƴan biyun ma idan zasu je, ya jikin yaron naka." Dady ya ta tambayi doctor."


Dr Inusa yace "Ah jikin sa da sauƙi sosai nan da awa ɗaya zai farka insha Allahu tunda yanzu ya samu baccin kusan awa ɗaya."


"To madala Allah tashi kafaɗun sa." Inji dady


Nan doctor ya masu sallama ya fita dan ya barsu su gana da iyalansa, dady yace masa ya iskoshi office ɗin sa suyi fira yaushe gamo.


Doctor na fita dady ya isa kusan gadon AFREED ya ke kwance ya ɗan kamo hannu sa ya yayi masa kiss sannan ya shiga jero masa addu'oi, da ya gama ya nufi wajen matar sa ta kallesa da murmushi tayi masa sannu da zuwa sannan tace "Dady AFREED kaje direba ya mayar da kai gida kayi wanka sai ka kwanta ka huta tunda mu gamu a wajen AFREED ɗin kuma doctor yace da sauƙi sosai."


Dady yace "To shikenan madame in haka kike so ai shikenan."


Bai ƙarasa rufe bakinsa ba Ali ya ce momy da kema tare da dady kuka tafi gida da su Fariya sai ni na zauna da shi kamin ya farka sai su Fariya su yi masa girki su taho da shi ko."


Ba karamin daɗi dady yaji ba da yaji furucin Ali dan sosai ya keda buƙatar matar sa a kusa da shi tunda dai jinkin AFREED ɗin da sauƙi gara su tafi gida shi ta kula da shi, dan haka sai yayi saurin cewa "Eh to haka za ayi ku tashi mu tafi."


Ba musu suka miƙe suka fita tare da cema Ali sai sun dawo, shima Ali ya faɗi hakane saboda ya san dady yanzu ya dawo da gajiya ya na bukatar kulawar momy."


Suna fita ya koma kusa da AFREED ya zauna yayi tagumi yana kallon sa yan jiran farkawarsa,


Bayan awa ɗaya



KU BIYO NI DAN MI ZAI FARU


TA KU HAR KULLUM MAI KAUNAR KU


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸




Écrit



Par




*QUEEN ZEEFAT*



_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_




*Wattpad@nazichou*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


*_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_*



*Page* : 45 & 46



Suna fita ya koma kusa da AFREED ya zauna yayi tagumi yana kallon sa yana jiran farkawarsa.


Bayan awa ɗaya shiru AFREED bai farka ba kuma bai motsa koda hannun sa ba bare ayi tunanin zai farka, haka wata awa gudar tazo ta wuce shiru, Ali na zaune wajen awa biyu yana jiran farkawar sa amma babu ko alamun zai farka, bayan awa biyu da minti ishirin hankali Ali in ya yi dubu to ya tashi ganin har yanzu AFREED bai farka ba, shida ake ce ma sa nan da awa ɗaya zai farka amma har yanzu shiru, hakan yasa shi miƙewa da sauri ya tashi ya fita bai tsaya ko ina ba sai office ɗin Dr Inusa, amma sai yayi rinshin sa'a baya nan da sauri ya fito yana ƙoƙarin kiransa sai ga wata infirmière (nurse) ta fito daga wani ɗaki, kawai sai Ali ya tare ta yana tambayar ta dan Allah bata ga inda Dr Inusa ya shiga ba?"


Nurse din tace "Ai yana block opération (ɗakin tiyata)."


Ali da zufah ta Kariki ke masa yace "Tun yaushe yashi ga"


"Ya kai awa biyu da shiga dan ina saran nan ba da jimawa ba zai iya fitowa."


"Kamar nan da minti nawa kike ganin zai fito?"


To wallahi ban sani ba, inaga dai ba zai wuce minti talatin ba zuwa arba'in zai fito."


"Kai har minti talatin gaskiya yayi yawa ɗan uwana nacen cikin wani hali, dan doctor yace sai nan da awa ɗaya zai farka amma har ya haura awa ɗaya da minti talatin da biyar shiruko motsi baiyi ba, dan Allah muje ki du bashi ki gani idan kuwa akwai wani doctor dai zai duba shi kamin Dr Inusa ya fito to muje ki masa magana."


Infirmière ɗin mai kirki, gani hali da Ali ya shiga dalilin ɗan uwan sa tace " Eh akwai muje na kaika office ɗin sa sai kama sa bayani."

Suna kaiwa bakin ƙofar doctor kin sai nuser ɗin tace masa ka shiga da ga ciki ka sanar mashi, ni gaba zan ƙara akwai masu jirana."


Godiya yayi mata sannan ya kama hannun ƙofar office ɗin Dr da ta kawo shi, kawai kamar ance ya juya sai ya tsikayi Dr Inusa na tafowa ai da sauri ya saki ƙofar ya nufe sa ya faɗa masa cewa AFREED ya ƙi farfaɗowa."


Bata tare da ya ƙarasa jin bayani Ali ya shige ɗakin da AFREED ke kwance a ciki dama sun kawo bakin kofar ɗakin.


Suna shiga ɗakin suka tardo AFREED zaune da ƴan biyu a kusa dashi suna jero masa sannu da sauri Ali ya ƙarasa kusa dashi yace "Kai ɗan uwa yaushe ka farka ina can hakalina ya tashi da naga baka farka, yanzu ina kema ciwo?" Ali ya faɗa yana ta taɓa shi, da ido kawai AFREED ya bishi bai ce masa komai.


Dr ya ƙaraso inda suke yana mai sannu da murmushi a fuskar sa sannan yace "Minista ya ƙarfin jikin?"


AFREED ya ɗaga idonsa ya duba shi sannan yace "Da sauƙi."


Doctor yace "To madala yanzu ina kema maka ciwo sannan kuma mi kake ji?"


AFREED yayi shiru bai ce komai ba saida Dr ya ƙara mai maitata masa tambayar sannan a matuƙar gajiye da magana yace "Alhamdulilah babu inda ke mani ciwo dady."


"To masha Allah tashi kaje cikin douche ka wanko bakinka sai kazo ka ci abinci da ɗan thé (tea) sai kasha magungunan ka."


Ba musu AFREED ya miƙe ya nufi douche (toillet) yana kaiwa baƙin kofa yayi tagata zai faɗi da gudu Ali ya yi wajen sa ya riko sa yace "Yi sannu man AFREED kada ka faɗi in ba zaka iya ba sai kace na rakoka ba da fa yanzu ka faɗi kuma sai ka ƙara tayar mana da hankali dan Allah kabi a hankali."


AFREED dai baice masa komai ba ya buɗe ƙofar douche ɗin ya shige, bai jima ba ya fito ya na tafiya ya na dafa bango sabida jiri yake gani Ali yaje ya riƙo shi suka dawo bakin gado ya zauna.


Fariya ta haɗa masa tea mai kauri da zafi kamshi sai tashi yake, ta miƙo masa ba musu ya ƙarɓa sabida yunwa ya keji sosai. Cikin ƙaƙanan lokacin ya kammala sannan ta zubasa tuwon shinkafa da biyar kuɓewa ɗanya ta ji kifi da man shanu, nan ma bai musa ba ya ƙarba ya sabida abincinsa ne wanda ya fi so, bai ci wani da yawa ba ya ajiye, Ali na ganin haka yace "Dan Allah AFREED ka ƙara mana regarde tu n'as pas beaucoup mangé (bakaci sosai ba)."


Da kyar AFREED ya buɗe bakin kamar mai raɗa yace "Na ƙoshi."


Sanin cewa AFREED idan ya riga ya furta ya ƙoshi to komai za'a yi masa ba zai ƙara cin komai ba dan haka Ali ya miƙo masa ruwa ya ƙaraba ya sha sannan ya ɓalo maganin ya mika masa da wasu ruwan marasa sanhi haka ya ƙarba ya sha duk abinda ke faruwa akan idon Dr Inusa, yana ganin AFREED ya kammala duk abinda aka saka shi ya sakin murmushi ya ce "Masha Allah yarona Allah ya ƙara baka lafiya." Sannan ya ƙara tambayar abinda ya keji yace masa baijin komai sannan ya fita ya bar ɗakin.


A lokacin AFREED ya kamo hannu Ali yace "Ali ka sa dady ya rubuta mana takardar sallama na ji sauki babu abinda ke min ciwo yanzun, nagaji da zaman asibitin.


Ɗan hararen sa Ali yayi yace "Naƙi na saka ya bamu sallamar bancin kaje kana wani banzan tunani ka kana shirin hallaka mana kanka."


"To nace ban iya zaman ka saka a sallame mu ko na tashi nayi tafiya ta ba tareda....."


Bai kai ga ƙarasa sa abinda yayi niyyar faɗa ba aka turo ƙofar ɗakin aka shigo, Momy da dady su ka shigo da murmushi ɗoke da fuskar su ganin AFREED zaune har yana magana sallama sukayi tare da da ƙaraso wa gun da gadon da AFREED ke kwance da sauri momy ta riƙo sa ta masa sannu tace "Ɗan albarka na ka farka, Allah na gode maka da ka tashi ka faɗun wannan yaro, yanzu mike maka ciwo?"


Murmushin ƙarfin hali AFREED yayi sannan yace "Momy ina yuni da fatan kin yuni lafiya, dady sannu da zuwa anzo lafiya, dady yaushe kazo."


Farin ciki ne ya mamaye zukatansu baki ɗaya sannan momy tace "Lafiya lau ɗan momy ya jikin naka?"


Kamin AFREED ya bata amsa dady ya kamo hannu sa ya shiga shafa kansa da hannu sa na dama yace "Yau nazo yarona momyn ka tayar mana da hankali ba dole nazo ba shiri ba, ga yanda nazo na tarar da kai na'aza ma rasa ka zamuyi amma kaga Allah da ikon sa ya tashi ƙafaɗun ka cikin ƙanƙanan lokacin naga alamun har gida zaka iya tafiya ma ko ba haka na tara kana faɗa wa Ali ba."


Murmushi AFREED yayi tare da duƙe kansa ƙasa, nuni yayiwa Ali da yazo ya taimaka masa yayi Sallah haka Ali yazo ya kamasa suka nufi toillet ya shiga ya ɗauro alwala sannan ya fito Ali ya kamasa ya kawo sa har gun darduma da Momy ta shinfiɗa masa ya fara gabatar da sallah azahar da ya kammala bai bar saman darduma ba ana suke ta fira shida dady, momy, Ali, da kuma Fariya da Farisa suna nan a zaune akayi kiran sallah la'asar dady da Ali har da AFREED mara lafiya suka nufi masallacin da ke cikin asibitin saboda yace zai iya takawa da kan sa har masallacin dan kuwa yanzu ya daina ganin jirin da ke diɓarsa tun farkawarsa haka kuwa suka tafi masallacin a tare, idan kaga AFREED sai kace wani cikakkin mai lafiya dan lafiya lau yake takawa ba wani tangaɗin marasa lafiya, Momy kuwa da ƴan biyu suka gabatar da tasu sallah a ɗakin da suke jinyar AFREED.


Ba'a ɗauki wani lokaci ba su dady suka shigo cikin ɗakin wannan karon su huɗu ne suka shigo har da Dr Inusa, AFREED ya nemi gurin ya zauna bakin gado da ya tashi, duk suka ƙara so bakin gadon suna kallon sa, Dr Inusa ya kalli momy yace "Madame naga yaron naki ya warware ko dai gida yake da buƙatar zuwa tunda yayi saurin korar rashin lafiyar."


Kamin momy tace wani abun AFREED yayi saurin cewa "Eh dady wlh naji sauƙi zan iya ta fiya gida ko da kaina ne."


Duk ƴan cikin ɗakin suka kwashe da dariya suna masa dariya shima ɗan murmushi yayi ya sune kansa.


Dr Inusa yace "To madala yaro na amma duk da haka sai gobe insha Allahu zan baka sallama, dan na ƙara ganin yanayin jikin ka, zuwa goben yanzu ka yi shiru ka rage magana amma kada kayi bacci, kai Alhaji biyoni office akwai abinda zamu tattauna."


Murmushi dadyn AFREED yayi sannan yace "To muje."


Suna fita AFREED yace "Gaskiya ni momy ban ce zan iya bacci a nan ba a barni naje gida goben da safe idan Allah ya kaimu sai na dawo a dubani."


Wata ya ƙaramar harara momy ta sakar masa tace "Wato ni daka raina zaka faɗa wa wannan banzar maganar shi Dr Inusa da dadyn naku da suna nan mi ya hanaka faɗa masu haka to babu inda zaka a nan ɗin zaka kwana, in badan ma Allah yaga tausayin mu ya ga halin da muka shiga ya taimake mu ya baka lafiya, da a lokacin da muka kawo kane, ka ga halin da kake ciki ko iya magana kanayi shasha kawai maza imani shiru ai kaji abinda doctor yace."


Badan yaso ba AFREED ya kame bakinsa ya yi shiru gudun kada ya ƙara magana ya ɓata ma mahaifiyar sa da rai, dan haka babu yanda ya iya ya jingi na da abin gado ya shiga tunani.


Bangaren dady da Dr Inusa kuwa suna shiga bureau ɗin doctor suka nemi gurin zama suka zauna a wata haɗaɗɗiyar ƙatuwar kujera dake cikin office ɗin, sannan suka sake gaisawa, tare da ɗan taɓa fira sannan Dr Inusa yace "Yawa abokina dama abinda yasa nace ka biyo ni wata shawara nakeso muyi akan AFREED." Sai kuma ya ɗan yi shiru.


Ganin yayi shiru yasa dady cewa "To ina jinka doctor saida Dr Inusa ya gyara zaman tare da yin gyaran murya yace "Alhaji ya kamata a yiwa AFREED aure hakan ne zaisa ya rage duk wani tunani da yake yawan damun sa har yake ƙoƙarin saka masa ciwon zuciya, kuma idan ka bincika bai wuce dalilin mace ne ya shiga wannan halin da yake ciki ya kamata asamu ma fita, ku tuntuɓe shi idan har yanada wace yake so ya fitar da ita sai ayi gaggawar zuwa neman aurenta gidansu saboda AFREED ya kai mizanin aure yanzu, yana da buƙatar wace zata ringa taimaka masa da shawarwari da kuma lamura na yau da kullum."


Sai da dady ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Hakane doctor nima abinda nake tunani kenan wallahi kamar ka shiga zuciyata wallahi, amma maganar cewa saboda mace ne ya shiga wannan halin gaskiya ina tamtama, abinda kuwa yasa nace haka shine AFREED bai kulla mace, kada a kai ta nesa ma kasan ko cousins ɗin sa mata bai cika kulawa ba bare har ya kulla wata a waje."


"Duk da haka abokina yanzu ba zaka taɓa gano bakin zaren ba sai ka bincika zakasan ko daga ina matsalar take, idan kuma kasan da babu wace ya ke so to kawai ka nema masa mai hankali da nutsuwa ko cikin cousins ɗin sa ne sai ka aura masa ko da bai sonta zai sota daga baya."


"To shikenan babu damuwa insha Allahu zan je na duba mashi wada zata dace dashi sai kawai a haɗa su."


Doctor yace "A'a ba hakanan ba za'a yi sai ka fara tuntuɓar sa kaji babu wace yake so kannan sai ka yanke hukunci."


Ok Insha Allahu haka za'ayi yanzu sai da safe za a sallame shi ko."


"Eh sai da safe insha Allah."


Bayan haka suka ciga ba da fira tafiya bikin auren Khairat ɗiyar Alhaji Sadisu yayar AFREEN, daga bisani kuma suka bar office suka nufi dakin da aka kwantar da AFREED.


*Washegari*


Da safe wajen ƙarfe 10 na safe AFREED ne kwance kan gadon asibiti yasha wasu ƙananun kaya masu masifar kyau wanda su Fariya su kawo masa tun jiya da yayi wanka yau ya saka bayan ya fitar da na bacci da ya kwana dasu, idan ka ganshi zakace bashi ne mara lafiyar ba, shi ne ya yiwa mai jinya rakiya sai wani game fuska yake shi a dole ya gaji da zama asibiti, Ali na lura da hakan shima ya game ta sa fuskar dan ba ƙaramin zafi AFREED ya ke ji ba, shi a ganin sa sabida min zai ki faɗa masa damuwa sa da har ta kai sa ga rashin lafiya, Ali gani yake da ya faɗa masa abinda ke damun sa da damuwar bata kai ga saka masa ciwon zuciya da sun haɗa kai sun shawo kan matsalar ko kuwa su nemi mafita kamin haka ta faru, amma shine ya ki faɗa masa, dama akwai abinda AFREED zai iya ɓoye masa kenan?


Ali na cikin wannan tunanin dady da doctor suka buɗe ƙofar ɗakin tare da sallama a bakin suka shigo, da ma momy da ƴan biyu suna daga gefe suna fira Ali ne ke kusa da gadon AFREED ɗin ya na dane dane a waya sa shikam fushi ma yake da AFREED ɗin dan ganin ya samu lafiya kuma ya ƙi sanar dashi damuwar sa, su dady na shigo wa doctor ya dubi gun da su momy suke a zaune ya buɗe baki da niyyar zai magana ƴan biyu suka katse sa ta hanyar gaida sa cike da kulawa ya amsa sanan yayi wa momy sannu da gida tare da tambayar mai jiki. Sannan ya juya wajen AFREED.


Yana ƙarasawa bakin gadon shi da dady AFREED ya tashi zaune ya gaida shi cike da sakin fuska suka amsa sannan doctor ya kama hannun sa na dama yace "My son ya ƙarfin jiki."


Ɗan murmushin yaƙe AFREED ya saki sannan yace "Jiki da sauƙi dady ai na ma warke yanzu babu abinda nake ji."


Murmushi doctor ya saki sannan yace "Ah yarona irin wannan zuba haka dan ka nuna min kaji sauki saboda ka matsu ka tafi gida to sai gobe, takarda sallama da nazo maka da ita ma bari na koma da abita."


Murmushi AFREED yayi tare da sun ne kansa yana susa kai wai irin yaji kunyar nan dan shi kam babu abinda yake so yanzu kamar ya ganshi gida.






*_Kumin afuwa masoyansa ZAMBA CIKIN AMINCI kwana biyu banada dama ko yanzu ma kokarin ne nayi wa jan gani na faran ta maku.....*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸




Écrit



Par




*QUEEN ZEEFAT*



_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_




*Wattpad@nazichou*




💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/





*_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_*



*Page* : 47 & 48


Doctor ya koma cewa "To na sallame ka tunda dai baka ce komai, amma kuma sai ka rage saka kanka a damuwa kaji my son komai yayi tsanani yana tare da sauki idan kayi hakuri komai zai zo ya wuce, idan kuwa ƙaga abin yafi karfin tunanin ka to ka nemin ɗan uwan ka kuyi shawara idan baku samu mafi ta ba ku nufi iyayen ku da maganar sai kuga komai ya zo da sauƙi, sabida ƴan magana sun ce duk abinda babba ya hango yaro ko ya hau dutse ba zai hango ba, duk abinda ya shige maku duhu ku fara kai maganar ga manya sai kuga Allah da ikon sa ya sa an shawo kan matsalar."


"Insha Allahu dady hakan bazata sake faruwa ba." Inji AFREED


"In ta ƙara faruwa kuma fah ya kakeso na maka?"


"Ba ma zata faru ba dady." AFREED na faɗin haka duka ɗakin suka kwashe da dariya jin yanda yayi maganar kamar karamin yaro, banda Ali daya game fuska shi a dole fushi yake da AFREED.


Ba tare da ɓata lokaci ba suka yiwa doctor sallama tare da gangama kayansu suka saka a mota Ali ya nufi motar da yazo asibitin da ita inda AFREED ya riga da har shiga Ali kawai yake jira, Ali na shiga ya zauna mazaunin direba ba tare da ya ko kalli AFREED ba shima AFREED bai kulla sa ba sabida lura da yayi yana ta cin magani, Ali ya tayar da motar ya bar hararbar asibitin haka dady shima ya tayar da tasa motar wada momy da ƴan biyu ta ke ciki suka kama hanya, har suka ƙara so gida babu wanda yayi wa wani magana tsakanin AFREED da Ali kawai dai sunyi tafiyar kurame ne, Ali nayin parking ya fice daga motar ya nufi hanyar ɓangaren su da kallo AFREED ya bisa yana tunanin shin mi yake damu Ali yake wani share shi a zuciyarsa yace "Ko dai fushi yake dani ne to mi na masa ko dai wani ya taɓo sa shida bai fiya yin fushi ba ko miye aka masa nasan babba ne, idan kuwa ni yake ma fushi na san da an jimawa zai daina ba saboda bai iya fushi dani."


AFREED na cikin mota yana wannan tunanin baisan lokacin da su momy suka shigo gidan ba sai da yaji dady yana ce masa "Mi kake yi a cikin motar?"


Da sauri AFREED yayi firgigit ya juyo tare da cewa "Babu komai." Sannan ya buɗe motar ya fito shima ya nufi ɓangaren su, su momy suka tsaya suna kallon sa har ya shige sannan suma sukayi nasu ɓangaren, Ali dake tsaye

Please Login or Register in order to submit comment