Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta window dakin sa yana kallon AFREED yana hamdala da godewa Allah da ya bawa ɗan uwansa lafiya ganin AFREED ya nufo ɓangaren nasu yasa shi komawa ya zauna bakin gadon sa ya na tunani.


AFREED na shiga ɓangaren na su shima ya nufi nasa ɗakin ya tare da rage kayan jikin sa ya nufi toillet ya saka ma kanshi ruwa ta tare da ya jima ba ya fito ya shirya cikin kayan bacci ya ɗane gado ya shiga yin bacci har sai da aka kira sallar azahar sannan ya farka ya nufi toillet ya sake yin wani wanka tare da ɗauro alwala ya fito ya shirya cikin fara doguwar rigar sallah ya fito daga ɗakin da niyyar tafiya masallaci a bakin ƙofar fita daga falon nasu ya haɗu da Ali na ƙoƙarin buɗe ƙofar ya fita shima ya ƙara so ko kallon inda yake Ali baiyi ba bare yasa ran zaiyi masa magana, Ali ya buɗe kofar ya fice, mamaki sosai ya kama AFREED wai shine ya ke share wa haka to mi ya masa?" Yana cikin wannan tunanin yaji an tayar da sallah da sauri ya rufe kofar ya nufi masallacin, kusa da Ali yayi sallah saboda yana son idan sun dawo tare ya tambaye sa ko lafiya yake ta share shi haka, ana gama sallah kamin AFREED yake gama addu'oi déjà Ali ya ƙarasa tasa ya tashi ya fice daga masallacin yayi tafiyar.


Da mamaki AFREED ya ƙarasa nasa addu'oi shima ya nufi cikin gidan ɓangaren momy ya shiga a nan ya tarda Ali yana ta wasa da dariya shida su Fariya, yana ganin sa ya gimtse fuska har abin yaso bawa AFREED dariya sedai bai dara ba kawai sai ya nemi guri ya zauna ya na jiran saukowar momy.


Momy na saukowa ta nufe su da dariya tana masu sannu da shigowa su kuwa suka gaida ta ta amsa tare da nufar dinning, ita da Farisa suka ɗauko abinci daga saman dinning suka yo dashi falo, saman kafet suka ajiye suka jera komai nan kowa ya sauko ƙasa suka zauna suna jiran dady, shima ba tare da ɓata lokaci ba ya sauko sannan momy tayi servir ɗin kowa daga nan sukayi Bismillah suka fara cin abincin bakajin ƙarar komai sai na cokali suna gamawa AFREED ya mike yace "Momy zanje na kwanta na ɗan huta."


Murmushin manya momy ta sakar masa sannan tace "To a huta lafiya ɗan momy."


Daga nan ya nufi mahaifin da ya sunbace shi sai mahaifin na sa ya sha masa kai yace Allah maka albarka da Amin ya amsa sannan ya fice."


Da AFREED ya fita momy da dady da Ali da su Fariya suka shiga fira har firar auren su akayi, AFREED tun yana jiran shigowar Ali har bacci ya kwashe shi Ali bai shigoba, kuma shima Ali ya na sane ya ƙi shigowa saboda yasan yana can yana jiran sa.


Ali shine bai fito daga ɓangaren momy ba har saida aka yi kiran sallah la'asar kan suka fito shida dady dan zuwa masallaci a hanya suka haɗu da AFREED shima zai tafi masallaci sai suka jera suka tafi tare bayan AFREED ya gaida dady haka ana gama sallah suka jero tare, su nufo gida suna kawowa daidai ida zasu nufi ɓangaren su suka yiwa dady sallama, suka nufi nasu ɓangaren babu wanda yayiwa wani magana har suka shiga falon su, AFREED yaka Ali baida niyyar tsayawa suyi magana dan ganin da yayi ya nufi hanyar ɗakin sa yasa shi dakatar dashi ta hanyar cewa "Ɗan uwa inason magana da kai." cak Ali ya ja ya tsaya ba tare da ya juyo ba kusan minti biyar babu wanda yace wani abu daga cikin su Ali na ganin haka ya ɗaga ƙafarsa har zai fara tafiya, AFREED kuwa har ya kawo inda yake a tsaye kamo kafaɗar sa ya yi yace "Kazo ka zauna muyi magana."


"Ba zan zauna ba ka faɗi duk abinda kakeso ka faɗa ni inada abun yi."


"Dan Allah ka zauna maganar ba zata yiwu daga tsaye ba."


"To shikenan tunda kace dan Allah sedai ka yi sauri ka faɗi ko miye ni akawi abinda ke gabana."


Murmushi kawai AFREED yayi ya karasa suka zauna ɗaya daga cikin manyan kujerun dake falon, sai da ya nisa yace "Lafiya Ali naga kana ta share ni mi nayi maka haka mai muni da har bakason ganina, ko kuwa rashin lafiyar da nake kake so na koma, in baka gama jinya ta bane sai naji."


Da sauri Ali ya ɗaga kai ya kalle sa bai ce masa komai, AFREED ya ɗaura da cewa "Sai wani guduna kake ko dan ban da lafiya ne ko kuwa wani abu doctor yace inada wanda idan ka ci gaba da yi min magana ko kulani kai ma zaka kamu da shine ban sani ba."


Da wani irin sauri Ali ya ɗago ya kalli AFREED kallo irin na har akwai abinda zai same ka na guje ka ne, kamar AFREED ya san abinda Ali ke tunani yace "Ah to dole na faɗi haka rabon da kamin magana ko kamin sannu da jiki tun muna asibiti da na farka tunda ka taimaka min na shiga bayi na fito baka ƙara koda yiman magana Ali ba dole na faɗi haka ba."


Wanda Ali yaga damuwa ƙarara a fuskar AFREED waga alamun ya marairaice da gudun kada damuwar da ya shiga yanzun ta ƙara je fasa cikin wani ciwon ya sa shi saurin buɗe baki ya fara magana kamar haka "Haba AFREED a tunanin ka akwai wani da zai sameka na kujeka ko da kuwa abin ya fi ƙarfin tunanin duniya baki ɗaya duk faɗin duniyar ban da mahaifi na da Momy da dady ganin ka ina da wani da ya fika a rayuwa ta ne kenan baka san son dana kema maka ba da har zaka kalle ni ka faɗa min wannan zancen da mai hankali ba zai ɗauka anya kuwa kama ɗauke ni wanda na ɗauka kuwa ni kallon wanda muka fito cikin ɗaya nake maka wanda banida kamar sa a rayuwar nan, amma ina ga kai wanjan ka ba haka ba ne."


"Ni ba dan komai nan ke fushi da kai ba sai dan ka zauna har wata damuwa ta dameka har ka saka kanka a mugun tunanin da ya ke neman rayuwar ka wai ka kasa faɗa min idan ni ne ba zan taɓa boye ma komai ba, duk da nasan halin na rashin son magana da miskilanci da kuma zurfin ciki bai kamata ace ni ka kasa gayamin damuwar ka ba ko kana ganin bazaka iya faɗa ma su momy ba sai ka faɗa min idan muka kasa shawo kan abun sai mu san hanyar da za mubi mu faɗawa su momy, su sai su sa ma mana ma fita idan ta wajen su ba'a samu mafita ba, sai su taya mu gayawa Ubangiji lamarin da, samun abin yi daga, haka har asamu ma fita kasan ance addu'ar iyaye bata faɗuwa ƙasa banza."


Sai da AFREED ya sauke ajiyar zuciya sannan ya fara da cewa "Wallahi ɗan uwana ba haka bane ni irin son da nake maka ya ma linka wanda kake yi min sau dubu na kasa samun ta hanyar da zan sanar da kaine wannan babban lamarin da ke shirin samu na ko ma nace ya sameni, kai da kanka kunyar faɗa maka nake ban san ta ina zan fara ba domin samun damar yiwa tufkar hanci abin ne yanada wahalar fasarawa wallahi, amma yanzu banida wata mafita da ya wuce na sanar da kai ko da zaka taimaka min da wani abun ko da kuwa addu'a ce dan a gaskiya ina cikin matsala da tashin hankali sedai fatan Allah ya yaye mani wannan wahala."


AFREED ya ɗan nisa tare da niyyar sake yin wata maganar Ali yayi saurin dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu sannan yace "Karka damu ɗan uwana Allah zai shige mana gaba a cikin wannan lamari insha Allahu duk da ban san ko miye matsalar ba, amma tun ka fin ka faɗa man na ji ajikina akwai nasara akan hakan zaka samu nasara Insha Allahu komai zai warware da izinin Allah, amma yanzu kada ka faɗa man ko miye damuwar ka, ka bari na shiga wanka na fito sai ka faɗa man a nutse saboda na lura ka gaji, dan wannan ƴar maganar da kayi kamin na fito ka ɗan huta sai na zo har ɗakin ka sanar dani sai a nemo mafita da iznin Allah."


Murmushi AFREED yace "Wallahi kamar ka sani kuwa na gaji da maganar gudin kuma kar kace bana son faɗa maka yasa na so ƙarasa zancen." Daga nan suka rabu kowa yayi ɗakin sa.


Su AFREEN sai shirya shiryen bikin Khairat suke inda ya rage saura kwana goma ɗaurin aure amarya tayi wani freish da ita, tayi kyau sosai haskin anty Khairat ya fito ana ta gyara amarya saboda anty Fauziya ta dauko wata mata yar Diffa tana ta bawa amarya kullawa sannan ita maman tana nata ƙoƙarin wajen gani an gyara amarya sosai da sosai tana bata irin haɗa haɗen su irin na buzaye komai yima mata ake masha Allah idan ba sani Khairat kayi sosai ba, zaka iya ƙin ganeta idan ka ganta yanzun, wajen satin ta uku bata fitowa koda falon gidan su ne bare har takai farfajiyar gidan haka ko ganin ta ba'a bari sai dolin ta, ita da Ahmad kuwa sai ta waya don kam an hana sa ganin amaryar sa duk ya bi ya damu haka itama idan yace zai yi mata video call bata yarda kullum sedai yaji murya ta.


AFREEN ce tayi sallama ta shigo ɗakin taje kusa da yayar ta ta zauna tace "Wai anty Khairat kinga yanda kika koma kuwa, kina duba madubi anty kinga duk kin sauya kamar bake ba."


Ita dai Khairat murmushi kawai take sakarwa AFREEN, tashi AFREEN tayi taja hannun kai Khairat tace "Zo ki gani anty." Ba musu Khairat ta bi ta hannu ta na cikin na AFREEN dai dai mirror ta tsaya da ita tace "To dubi kanki a madubi anty ki ga wanda kika sauya anya kuwa ya Ahmad zai ganeki idan yan ganki kuwa kai anty wallahi yanzu har kin fini kyau."


Wani fari Khairat tayi da idanu sannan tace "Kai ƙanwar anty Khairat wannan taɗin ni ɗaya anya bai min yawa ba? kuma da kike cewa yanzu har nafi ki kyau, ta ya za ayi haka ta faru ina ni ina ke wajen kyau ai ko farcen ki ban kamo ba sister, duk kuwa kyau ɗin da zan yi bazan taɓa kamo ki ba yanzu kawai annurin amarci nekinsan ita amarya komin munin ta dole ne sai tayi wannan annurin, shi yasa kika ga haka amma ke kyawon ki na daban ne soeurette idan har ke ma naki auren ya tashi a ka fara maki irin wannan gyaran idan har kika duba madubi to zaki fara bawa kanki tsoron ma sabida wani kyau ne zakiyi irin wanda babu shi a cikin mutane wallahi wata irin haɗuwa zaki yi Allah dai ya nuna mana wannan lokaci musha didima."


Murmushin yaƙe kawai AFREEN tayi sannan tace "Duk da haka anty a halin yanzu dai kin fini wallahi."


"Hum na ji dai ƙanwata kina son sa kai na fashewa inji babu wata kamar ni."


"Wallahi ba hakane sister ba wai ina koɗa ki bane abinda na gani ne na faɗa."


To shikenan na yarda ƙanwata yanzu kuma waye ƙanin nawa faɗa man dan mun daɗe bamu yi fira dake ba kika faɗa da wanda kuma kike tare yanzu, dan gaskiya so nake ki samo muntun na gari mai amana wanda ba zai gudu ba tunda sauran duk mutanan banza ne."


"Kai anty ni nasan ko da kuwa sauran ba na kirki bane KAMAL mutuman arziki ne kawai dai abin daga mahaifiyarsa ne kuma Allah yayi ni ba matar sa bace, saboda nasan shi bai da niyyar cutana, anty kinsan yanda yake so na kuwa?"


"Haka ne nima na yaba da halayyar KAMAL gaskiya, shi ba zai iya yau darar ki ba, ko dan an ce ɗan Adam tara yake bai cika goma, amma ina da yaƙini sosai akan KAMAL ba zai cutar dake ba, kawai haka Allah ya tsara maku kuma sai ku rungumi kaddara ku gode masa ku roƙe sa ya haɗa kowa da rabon da na alkairi."



"Ameen AFREEN tace a taƙaice."

Wajen minti biyu babu wanda ya ce komai AFREEN na ɗan gyara ma Khairat kashin kanta da ya fito daga cikin adikon ta, ita kuwa Khairat ta faɗa duniyar tunani can dai ta ɗan nisa tace "Ni gaskiya soeurette lamarin ki na bani tsoro anya ba akwai lauje cikin naɗi ba kan wannan al'amari naki, il faut qu'on passe une bonne enquête sur ça vraiment ta situation m'étonne sincèrement."


Shiru AFREEN tayi na wajen second biyar sannan tace "Anty moi j'ai pas compris ce que tu veux me dire, quelle enquête on va faire sur ma situation, d'abord de quelle situation tu parles?"


Khairat tace "Hai sister ne fait pas semblant de me montrer que tu ne savais pas de quoi je parle."


"Wallahi anty je n'ai sais pas de quelle situation tu veux parlé."


"To d'accord na yarda baki gane ba ina nufin lamarin aurenki ya na so ayi bincike gaskiya ya za a ce kullum maganar aure sai ta kankama ana shirya shan biki kuma sai abu yazo ya lalace gaskiya ya kamata a duba lamarin nan, gaskiya ban yarda haka nan kawai maganar auren ki ke lalacewa ba, ina tunanin da akwai wani abu a ƙasa."


"Kai anty ki daina ki tunanin komai kawai daga Allah ne, kuma kalla tawa ƙaddarar kenan, kama ki saka komai a ranki harki Kai ga saka wani a zargi, babu wani abu da za a yi bincike a kansa kawai su wa inda muke haɗuwa muna rabuwa to fah ba alkairi tsakanin mu wannan shine kawai."







*INA MA KOWA FATAN ALKAIRI💃💃💃💃*






*Taku har kullun mai kaunar ku*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸



Écrit



Par



*QUEEN ZEEFAT*



_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_




*Wattpad@nazichou*




💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/



*_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_*



*Page* : 49 & 50


"Ke dan Allah jan cen mallama ki ajiye wa'azin ki a nan har ki fita a nan sai ki yima masu buƙata, tunda ko kina so ka ba ki so sai na faɗi haka, kuma a na hango maki abinda da ke kika kasa gani da idonki, amma wata rana zaki gane abinda na faɗa gaskiya ne, sannan kuma zan samu maman muyi wannan maganar tunda ke baki da hankali har yanzu ƙuruciya na damunki."


Shiru AFREEN tayi saboda ta kasa abinda zata ce wa Khairat ɗin, sai kawai ta saki gashin Khairat tace "Soeurette bari naje gun tanti dan marabina da ita tunda safe."


Khairat tace "To mara sani ciwon kai tantin mi kuma da zaki ce zaki tafi gun ta dan kawai tun safe baki koma gani ta ba ko ita uwarki ce da baki da tunani a na nuna maki Annabi ki rufe ido, to ni bari kiji na faɗa maki maganar gaskiya tantin nan da kike shi shi gema ni wallahi yanzu ban yarda da ita ba dan ina zargin ta sosai yanzu a kan wasu abubuwa dake faruwa a gidan nan."


AFREEN tace "Kai anty Khairat tantin na aza kema kinsan halin ta kin na sane da yanda take son mu da son ci gaban mu kamar yanda maman ke yi mamu kuma kema kin yarda da ita dan shiyasa kike alfahari da kyawon halinta."


Da sauri Khairat tace ga da ba, amma yanzu bari kiji na faɗa maki yarinya yanzu ni har nafi yarda da umma kanta ita dake masifaffiya, a san masifa da bala'i kawai ta ajiye amma bata *ZAMBA CIKIN AMINCI* gaskiyar ta lakadan take faɗa komin ɗacin ta amma ita wacen Sakinar muguwar boye ce."


Shiru AFREEN tayi tana yiwa Khairat kallon yaushe ta fara iya yiwa mutum sharri yaushe wannan halin zargin jama'a ya sameta ko dai duk auren ne ya sata ta zare haka.


Kamar Khairat ta san mi take tunani tace "Ban zare ba lafiya ta lau yarinyar, sanar dake gaskiya tace nayi, ki yarda dani tanti babu abinda ta aje sai *ZAMBA CIKIN AMINCI* dan wallahi ba ƙaramar munafuka ba ce gaya maki nake, ba son mu take ba kawai tana nunawa ne, indan baki yarda dani ba ki gwada tambayar wataran miye an fanin zumuwar da take baki kullum, ke kuma da bakida hankali kin bi kin sakankance wai ga wada akeso ko dai ake ƙi ba, da turaran da take baki kinayi tana cutar dake amma kin kasa gane hankan."


Da sauri AFREEN ta ɗago ta kalli Khairat tana mamakin yanda akayi Khairat duk tasan haka itada ko maman bata taɓa faɗa ba amma Khairat.


Wani ɗan ƙaramin murmushi Khairat tayi sannan tace "Kina mamaki ina nasani ko alors que toi tu n'a rien dit à personne (ke kuma gashi baki faɗawa kowa ba) to bari na faɗa maki hali na idan kin manta ki sani duk abinda na saka ma ido to sai na nemo cikin da wajen shi ina ga ki manta ko wacece Khairat shiyasa kike mamakin abu nan da ya fito daga baki na, to ki ma daina mamaki komai zan iya bincikowa inda har na damu dashi ko kin manta abinda na karanta ne, amma ki samu ki ɗanyi bincike kema zaki gano abinda na gano, waini bana ce tayin wani abu ba, amma nasan da akwai *ZAMBA CIKIN AMINCI* a lamarin ta kuma nasan watarana zaki ce na faɗa maki."


Shiru dai har yanzu AFREEN ta kasa cewa komai dan abun yayi mugun ɗaure mata kai sai can ta ɗan nisa tace "Anty bari naje na ɗan watsa ruwa sai na fito muje jardin (garden) muyi fira ko da yake ashe ke baki fita zan dai dawo."


Tace "To ƴar ƙanwata sai kin dawo."


Ba tare da tace mata komai ba ta fice daga ɗakin direct ɗakin maman tayi tana shiga ta tardo tana saka kayan da aka goge ma ta a wardrobe tayi sallama ta ƙarasa shiga ɗakin tace maman sannu da hutawa."

Maman wada tun shigowar AFREEN da tayi sallama ta ɗago tana kallon ta tace "Yawa AFREEN daga ina kike ɗazun na tura Zeinab kiranki tace man baki nan."


"Eh wallahi maman ina ɗakin anty Khairat."


"Ah ok to shikenan mi Khairat kin keyi yanzun."


"Babu abinda take na bari ta a zaune amma ta yiyu yanzu ta shiga wanka tunda naga gommage ɗin dake ga jikinta ya bushe, maman bari na tayaki mayar da kayan." AFREEN ta faɗa tare da tashi daga saman gadon ta nufi mahaifiyar ta."


Aa barshi AFREEN jeki ki huta kinji ko."


"Maman ba fa abinda nayi bare ace inda na gajiya naje na huta."


Eh duk da haka ki zauna ki huta ke da kullum ba kison kina hutawa sedai aiki ai rai nason hutu, yanzu kam na hutar dake ɗanewar ki kan gado ki kwanta ki ɗan huta koda kaɗan ne, kin ga ma na kusa ƙarasawa kingin abu huɗu na ƙarasa gyaran."


AFREEN tace "To shikenan maman bari naje nayi wanka sai na zauna na huta." AFREEN ta faɗa ta na ƙoƙarin miƙewa ta bar ɗakin mahaifiyar ta.


Maman tace "Aa ba sai kin koma ɗakinki ba shiga toillet ɗin na kiyi wankan ki tunda kina da kaya a nan sai ka canza idan kin gama shirya wa sai ki kwanta ki huta."


"To maman." AFREEN ta faɗa tare da tashi ta nufi toillet ɗin."


Ba wani jimawa tayi a toillet ɗin ba ta fito ta yi shirin ta cikin wata doguwar riga mara nauhi tare da ɗanewa saman bed ɗin mahaifiyar ta ta yi kwancin ta ba tare da ɓata lokaci ba bacci yayi awon gaba da ita.


Ali na gama wanka ya shirya tsaf ya fito daga ɗakin ya nufi na AFREED ya shiga tare da sallama, ya na zaune bakin bed ɗin ya faɗa duniyar tunani dan bai ma san shigowar Ali ba har saida ya dafa shi, da sauri ya ɗago yace "Broh har ka fito?"


Ba tare da Ali yace masa komai ba ya nemi guri kusa dashi ya zauna sannan yace "Broh ka fah san doctor ya hana ka yawan tunanin amma kaƙi daina hankan zai iya ƙara saka maka wani ciwon dan Allah ka daina ya ƙa faɗa man abinda ke yawan ɗaga maka hankali har haka sai mu nemi mafita tare da taimakon Ubangiji sai kaga komai ya daidai ta."


Wata naunauyar ajiyar zuciya AFREED ya sauke tare da juyowa yana kallon Ali sannan yace "Wallahi broh ina cikin matsala ban ma san daga ina zan fara faɗa maka abinda ke damuna ba."


Ali yace "Fara daga inda ya dace ɗan uwa."


AFREED ya ƙara sauke wata ajiyar zuciyar sannan yace "Broh ina wata yarinya wada sunanta yake kaman ce ceniya da nawa ana ce mata AFREEN idan ba zaka manta ba ita ce ta buɗe taro a lokacin saukar su Khadijah, wata ƴar doguwa ba zakace mata fara ba kuma ba zaka ce mata baƙa ba teint café au lait dai (chocolat color ) Kai tana da ma haske dan gaskiya ga wani ba za'a cema chocolat color, ba zaka iya cewa ma ba fara bace don gaskiya teint (fatar ta) ɗin ta tana da fari se dai ba can ba, ban san ko ka gane wada nake nufi ba, don ita ce damuwa ta."


Ali ya ƙurawa AFREED ido yana kallon sa yace "To ina jin ka na gane yarinyar wata mai zazzaƙa muryar kamar sucre yarinyar ta birgeni sosai ai seda nayi enregistrer (saved) ɗin muryar ta lokacin da tana karatun Alkur'ani, amma kai miye haɗin ka da ita da har ta zame maka matsala?"


AFREED yace "Babba matsala ma kuwa saboda ba a nan muka fara haɗuwa da ita ba don mu san juna tun kamin zuwa gun saukar nan, nan dai AFREED ya kwashe tun farkon haɗuwar da AFREEN ya faɗa masa har abinda ya keji game da ita da duk abinda ke saka shi cikin halin rashin lafiya duk a kanta babu dai abinda ya ɓoyewa Ali komai ya sanar da shi.


Ali da AFREED ya gama zayana masa komai da komai ya tsaya yana nazarin ɗan uwan nasa na kusan minti biyu, kuma daga bisani ko mi ya tuna sai ya kwashe da dariya yana tayi sosai har saida ya yayi mai isar sa."


A lokacin har ya ƙula da AFREED ya ɓata ran shi sannan ya miƙe ya bar gun ya koma wajen window yana kallon farfajiyar gidan, Ali na ganin haka ya tashi ya nufi gun AFREED yana gumtse dariya sa yace "Broh dan Allah yi hakuri zo zauna muyi magana."


A ɗan fusace AFREED yace "Naƙi na zauna ɗin ya zan faɗa maka matsala ta, amma ka zauna kana min dariya yau ga mai abun dariya naga da wasa ma ka ɗauki lamarin."


Ali yace "Wallahi ba haka bane ɗan uwa ke ɗin ne ka ban dariya, amma kayi hakuri zo muje muyi shawara samun yanda zamu bulowa wannan lamari a sauƙaƙe, komai zai daidaita da ka faɗa man da yuri da duk haka bata faru ba, amma insha Allahu yanzu komai ya zo ƙarshe."


AFREED naji abinda Ali ya faɗa ya bisa suka koma bakin gadon suka zauna, Ali ya ɗan saki wani ƙayatacen murmushi sannan yace "An zo wajen wai yaushe ɗan uwana ya faɗa soyayya banida labari har ta kai ga yi masa mummunan kamu haka, har take neman sa ɗan uwana ya rasa ranshi, wallahi yaya AFREED ban taɓa tunanin zaka so wata ƴa mace ba, har soyayyar ta tayi maka wannan kamun

Please Login or Register in order to submit comment