Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

banyi saurin faɗa mata ba na bari ne har muyi shawara dake ne, sannan na ɗan sama ta ido naga ko akwai wanda take so ko zata iya faɗa ko dai a ga wasu alamu haka to banga ko ɗaya ba inda bata boye bane."


Maman tace "To Allah tabbata da alkairi bari naje ɗaki na na dawo."


Tanti dake laɓe bakin ƙofar falon Alhaji alamu ta gama jin komai da suka tattauna tayi gudu ta ɓoye cikin wata ƴar coulouwar (corridor) dake bayan wajen dan itama tunda ta lura da akwai magana a bakin mijin nasu take ta son taji ko miye kuma ya ki faɗa masu idan suna su duka zaune waje guda tun a lokacin ta san cewa da Arahamat yake son faɗa wa ita ɗaya dan ta lura hada soyayyar da yake matane ta shafi waccan bakar yarinyar AFREEN mai kama da ita.


Maman na shiga ɗakin ta tanti ta fito daga laɓan da take da sauri ta sauka daga saman benan tayi shige ɗakin ta da sauri hankali ta a mugun tashe ta buɗe baki ita ɗaya cikin ɗaki ta fara magana kamar haka "Wane yaron za'a haɗa da AFREEN garde corps (Bodyguard) ɗin ministre (ministan) ko ministre ɗin gaba ɗaya shi ne zai aure ta, kai gaskiya baza ta saɓu ba wallahi da sake ace duk abinda nake ya tashi a banza kam, to ai ko garde corps ɗin ne bazan bari ayi auren nan ba bare a ce minister ne da kan shi da wallahi sai in da ƙarfi na ya ƙare bari na kira anty hawa na gaya mata."


Nan take ta dauki wayar ta nemo number ƴar uwar ta ta tura kira ta kara a kunne ringing ɗaya biyu aka ɗaga, hankali a matukar tashe ko gaisawa bata bari sunyi ba tayar ta na ɗaga tace "Aunty kinji kuma abinda suka ƙara jayo wa ko, wai aure za su ma wannan shegiyar yarinyar da duk burin mutan gidan ya na kanta, duk faɗi tashin da nake dan na hana ta aure har karshen rayuwar ta bai hana suka ƙara hango wanda zasu haɗata da shi kuma abin haushin ma kin san kowa?"


Yayar Wada suke kira da anty hawa da tayi shiru tana sauraran ta tace "A'a sai kin faɗa ai zan sani ko?"


Tanti tace "Wai ɗan gidan aminin Alhaji wannan injiniyan da nake baki labari cewa yaron sa ne keyin ministre de dépenses et de sécurité har nace da hamida ta isa aure da zanbi duk hanyar da zanbi in ga ya aure ta, amma ku inaso ko da ta biyu yayi da ita bayan nan da wasu yan shekaru, amma ina yanzu naji suna wannan banzan zancen bara digi naji yace uban yaron ne yake son a haɗa auren ba shi ba, amma bansan wane yaron daga ciki yake nufi ba tunda akwai yaron da ƙanwar matar sa ta muta ta bari tun yana jinjiri suka amshe shi suna kula da har ya girma a hannun su kusan yan sa'a guda ne shi ministan, shi ne ma garde corps (Bodyguard) ɗin ministre ɗin to shine nake tunanin wa ne daga ciki wanda za'a haɗa ta da shi, don gaskiya babu wada zan yarda daga cikin su yarinyar nan ta aure indai ina raye ko babu na zai kare sai na cika buri na na ganin yarinyar nan ta wulakanta, in bata auri nakasashe mugun matsayin ta tagayara ta zama abin tausayi wanda sai an taimaka mata ba, gaskiya hankali na ba zai ta taɓa kwanciya ba, ba dai sunce ita ta gaban goshi ba yaran mu duk kamar photo suke a gidan abinda AFREEN tace tana so shi ne ake yi a gidan nan ko da kuwa cikin mu ne iyayen muka ce bama so, anty ya kike ganin za'ayi?"


Sauke wata irin ajiyar zuciya Aunty hawa tayi sannan tace "Lale zama bai sameki ba ke a ganin zasu haɗa ta aure da wannan yaron da matsayin sa bodyguard ai sedai ministan shida zata huta girki ma sai anyi mata komai yi mata za'ayi ko da ruwa takeso a bata za'a ta, wa ya gayama ki za su kai ta inda za ta sha wahala, dan haka idan kina bada himma wajen ganin kin maida komai akan ɗiyar ki to idan kuwa ba haka ba kina nan kina kallon ruwa kwalo ya maki ƙafa, dan wallahi ki na kallo yarinyar nan zata nasara kanki ke kuwa ki faɗi warwas dan haka gobe tun safe ki zo mu koma gun mutumin nan wallahi tun kan yurin ya ƙare maki, kawai ƙaramar yarinya ta zame maku annoba ga gida, ita ce duk gidan nan a ka fi so ita ta fi kowa ilimin addini da boko ita ga shegin kyau kamar aljana ke wallahi idan bakiyi da gaske ba wannan kyau fuska da kyau ƙira da na hali da na komai duk ita ɗaya, wallahi wata rana ba minister ba shugaban kasar gaba ɗaya za'a ace ta aura ko sarki ke zaki kiji ma ance an zo neman auren ta daga wata ƙasar waje idan bakiyi da gaske ba, ke kuwa dake da ƴar tillon ɗiyar ki kun shiga uku, kinga likita babu kalar da bamu gani ba an ce babu ke babu ƙara haihuwa, haihuwar Hamida ma da yaya kika sameta saidai muka kashi kuɗi sosai kamin ki samu cikin, mu so ki haifo mana namiji ki ka samo mace a haka ma mungode, sannan kuka zama kamar wasu tsitacin mage a gidan."
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸




Écrit




Par




*QUEEN ZEEFAT*



_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_



*Wattpad@nazichou*





*_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_*


*Page* : 57 & 58

"Arahamat da yaran ta kawai ke abinda suke so sabida ta amshe gida yaran ta biyar har maza biyu ke da ɗaya ita kuwa wacen mafaɗaciyar da uku ita kuwa duk mata, kin ga kuwa idan yau Alhaji ya faɗi ya mutu har ƙorarki ana iya yi daga gidan nan dan haka nake so ki samu ki mallaki wasu ƙadarori na Alhaji kamin mai tonan asiri tazo dan kuwa ya na komawa ga mahaliccin sa, wallahi kin banu sabida abinda za'a baki na gadon yarinyar ki da na wankan da zaki masa bai taka ƙara ya karye ba dan a lokacin ne zakiyi dana sani wallahi kin tashi a tutar babu dan ma wai kinada ɗiya da shi da ace baki da kowa wallahi da kin fi banuwa."


"Wallahi haka ne Aunty ai duk sai naga bayan su sai na koma babu wanda ke faɗa aji in bani ba dan ba zanyi tallata ba sai Laraba dan wallahi bani tashi a taulauce kuma na mutu a haka gaskiya il faut que nayi arziki dan zan dinga zuwa Dubaï duk sati nima matan manyan su dama dani ba wai na zauna ina kallon kawai na wasu suna fantamawa ba yanda suke so ba ni banda ni wallahi da sake."


Anty hawa tace "Ah ai dai na faɗa maki tun ba yau nake sanar dake wannan abin kin ƙi ki fahimta kiyi abinda ya dace."


Tanti tace "karki damu anti yanzu dai mu fara maganin wannan matsalar kamin akai da wacen ɗin."


Da sauri Aunty hawa ta tari numfashi ta ce "Ke daka ta ai a bari ya huce shi ke kawo rabon wani duka za'ayi gobe idan Allah ya kaimu ba waje guda ba zamu je, sannan ki kira wannan ƙawar taki ita ma ta raka mu wajen wannan babban bokan na ta, sannan muje wajen wanda ya ke maki aiki nima na san guda uku duka zamu je ayi aiki mai yawa kowa ya yi kalan nashi se ki ga ya yi saurin ci dan wanga karon ko ƙur'ani take zazzage wa a kanta tana kwana da shi dole muyi galaba a kan ta ke dai kawai gobe ki fito da kuɗin isasshi."


"To shikenan anty Allah ya tada mu lafiya."

Ta amsa da ameen sannan suka ajiye waya


Tanti na ajiye wayar ta fara kai kawo cikin ɗakin ta ce yanzu najin sun ce zasu tuntuɓi AFREEN kan maganar idan ta yarda ni zan hure ma ta kunne ince ka ta yadda duk da naga kamar yanzu bata sanki jiki dani, amma zan gwada ko dai ta fara gane shirin da nake a kanta kai ba haka bane indai ba wannan munafuka Khairat kin ce ta fara hure ma ta kunnuwa dan naga ita ba wani yarda tayi dani ba, ko da yake itama zanyi maganin ta zan hana ta zaman lafiya da mijin nata, har sai ya watso ta gida insha Allahu kowa na shirya yanda zanga bayan shi ita fauziya ta daina farin cikin cewa tayi aure har yanzu mijinta bai yi mata kishiya ba zan yi abinda zai ƙara aure kuma irin kishiyar da zata maida ta kamar ƴar aiki za'a mata duka dai zan san yanda za'ayi, ba dai da ni suke ja ba za su sha mamaki duka sai na sa sun gane kurin su, sai na kuntata masu rayuwa kamar yanda yanzu suke cikin farin ciki mu kuma an mayar damu bare ga gida ba matsala zasu gani."


Da safe wajen ƙarfe tara bayan sun gama petite déjeuner (breakfast) 🍳🍜🥗🍱 papa yana dakin sa bai fita ba tanti ta shiga da sallama papa ya amsa mata sannan ta nemi guri ta zauna tace "Papan yara da ma inaso naje gidan Aunty hawa na duba ta kwana biyu bata ji daɗin jikin ta ba shine na ce bari na sanar maka."


Papa da idonsa ke ga télé (TV) ya juwo ya kale ta yace "Asha asha Allah ya bata lafiya kije kawai Allah koro sauƙi, amma ai kinsan bana son za'a fita a ƙi sanar da ni har sai ranar fitar ta zo ko."


Tace "Eh wallahi nasan wannan jiya da dadare ne take sanar dani wallahi shi ne yasa ban sanar da kai da wuri ba."


"To shikenan idan kinje kice ina gaishe ta da jiki."


Tace "Insha Allahu zan sanar mata"


"To shikenan ba damuwa tashi ki shirya kije dan ki samu ki dawo da yuri."


Tanti har ta miƙe zata fita sai papa yace "Karɓi wannan ki sayi ɗan abinda dubiya ki biya mata da shi."


Da sauri tanti ta karɓe 10000 da papa ke miƙo mata kamar yace zai fasa bata idan bata ƙarɓa ba da sauri.


Bata tsaya komai ba ta ga ɗaki, ta nufi nata ɗakin tana shiga ta faɗa toillet tayi wanka ta tayi shirya cikin dogon hijab inta tayi kamar wata ta kwarai ta fice daga gidan.


Maman na zaune ɗakin papa suna hira yace taje ta kira masa AFREEN itama ta dawo dan ayi komai a gaban ta.


Maman ta shi ta fita ta nufi ɗakin AFREEN tana shiga ta tardo ta makale da waya ta na hira da masoyin nata sallama tayi sannan ta idasa shiga ɗakin, AFREEN da ta kashe wayar tunda ta ji sallamar mahaifiyar ta ta ɗago ta kalle tace "Maman barka da warhaka."


"Yawa AFREEN na shigo kina waya ko har kin gama."


"Eh maman dama da fanna muke magana."


"Ok to ta shi mahaifin ki na neman ki."


Dam dam gaban ta ya faɗi bata san dalili ba, idan kiran Mahaifin ta ne ai ta saba dashi tun ba yau ba to miyasa yau taji faɗuwar gaba daga ance yana neman ta.


Ta ɗago tace wa maman gata nan tafe sai kawai taga maman har ta fice daga ɗakin jiki a sanyaye ta sauko daga saman bed 🛏️ ɗin ta ɗauki hijab ɗin ta nufi gun mahaifin ta, tana kaiwa bakin ƙofa ta yi sallama aka amsa ma ta sannan ta murɗa ta shiga kai tsaye duk jikin ta a mace ta nemi gu ta zauna kusa da ƙafafun mahaifiyar ta sannan ta ɗago tace "Papa gani maman tace kana nema na."


"Eh hakane AFREEN ni nace ta kira minke akwai maganar da za muyi dake inaso ki nutsu kiji abinda zan faɗa kin gane ko dan maganar tana da mahimmanci sosai."


Nan ma AFREEN taji gaban ta ya sake faɗuwa sannan ta ce "To papa ina sauraren ka."


Yace "Yawa kinga mahaifiyar ki nan jiya mukayi maganar da 'ita shi ne naga ya dace ke ma a sanar dake, dan haka ba wani abu bane nakeson faɗa maki illa inason faɗa maki cewa na maki miji."


Dam dam gaban ta ya yanke yayi wata irin muguwar faɗuwa ta ɗago da sauri tayi sauke idon cikin na Mahaifin ta suka yi ido huɗu da shi sannan da sauri kuma ta sunne kanta ta na kallon kasa tare da rumtse idonta da ƙarfi ta furta inna lilahi wa inna ilaihi raji'un cikin zuciyar ta.


Papa ba tare da ya lura da hali da AFREEN ta shiga ba ya cigaba da cewa "Yaron ne me hankali da nutsuwa da sanin ya kamata in taƙaice maki dai yaron kirki ne iyayen sa suka nemi na ba shi auren ki ganin dacewar haka yasa na amince masu ba tare da na nemi shawarar ki ba saboda sannan halin yaron da kuma la'akari da nayi da gidan da ya fito gidan tarbiyya, gidan mutunci ne gidan mayan mutane ne ina nufin iyayen sa datawan kware ne haka kuma nasan da za'a riƙe ki da daraja da muntunci saboda mahaifinsa amini na ne tare muke tun muna yara tare mukayi komai har aure da kuma karatu kinga mahaifiyar ki nan itama ta sanshi farin sani dan mahaifiyar yaron ma kawarta ce, amma wani hanzari ba gudu ba, AFREEN ba doli ba ne za'a yi maki zaɓi ne kuma shawara ce idan har kin ga zaki iya auren ɗan amini na idan kuma ba zaki iya ba, babu mai takura ki ko kina da wanda kike so duk babu wata damuwa ni farin cikin ki kawai nakeso ba na wani, idan kin ce baki amince ba, zan iya kiran injiniya in ba sa hakuri kuma na san zai fahimce ni dan haka kina da zaɓi AFREEN ɗin papa gayaman yanda kike so ayi, zanyi farin ciki da duk amsar da zaki ban, kuma gaskiya nakeson ki faɗa man abinda ke cikin ranki kada ki kuskure ki man ƙaya saboda baki saba yin haka da sauri zan gano inda kika dosa."


Cike da tashin hankali AFREEN ta ɗago ta kalli mahaifin nata taga ita yake kallo babu yabo ba fallasa cikin kwanciyar hankali ba ta ga alamun zai yi mata dole ba, kuma haka ta ga alamun ba zai ji haushi duk abinda zai fito daga bakin ta ba, da sauri ta mayar da kanta kasa ta na kallon kafet wani irin bugawa ne zuciyar keyi kamar zata fito waje kuka keson kubce ma ta amma tayi ƙoƙarin mayar dashi saboda idan ta bari kukan ya fito mata zai nunawa papa cewa batayi na'am da zaɓin sa duk da a cikin zuciyar ta hakan ne batason wanda papa ke shirin haɗa ta dashi sabida tana AFREED ɗin shi take so take kauna a cikin zuciyar ta ga halin yanzu duk da basu yi ko wata da haɗuwa ba har yanzu, gashi kuma papa na shirin faraƙa tsakanin su ita ya zatayi dan bai kamata tayi rejeté zaɓin mahaifin ta ba bai komai kawai zata aminci kodan papa ya gama mata komai a rayuwa ko a cikin gidan ya kan take farin ciki kowa da ita tayi farin ciki bai kamata ta yi masa butulci ba gaskiya...


Bata ƙarasa zancen zucin da take ba papa na cewa "Ke nake saurare AFREEN kaki kuskura ki yi ma kanki gashé ɗin farin ciki da ganin kin faranta man dan kuwa ina maraba da duk amsa da zaki bani saboda kinsan ce ta farko a cikin gidan mai min biyayya yanda ya kamata idan aka cire mahaifiyar ki dan gaba ɗaya halayyar kika gado, dan haka ina sauran ki faɗa man duk abinda ke ranki."


Wani murmushin ƙarfin hali AFREEN ta antayo ma Mahaifin nata sannan tace "Haba papa sai kasa naji kamar nafi ƙarfin kamin zaɓin abinda kaga yafi dacewa dani, sai kasa nayi tunanin na kasa ma biyayya yanda ya kamata papa, miyasa dan kayi min miji kuma sai kanemi shawara na kamar ni ce na haifi kaina dama ai a musulunci iyaye su suke zaɓa yaran su miji na farko to miyasa ni dan an zaɓa min kuma za'a nemi shawara na ai kawai umarni zaka ban papa kuma na bi umarnin wallah, ni kawai fata Allah ya sa haka shi ne mafi alkairi dan na san papa ba zaku taɓa yimin zaɓin wanda ba na gari ba na san da har da son da kake min yasa kayi min wannan gatan, ba abinda zan maka sai godiya da kuma godewa Allah da ya bani mahaifi irin ka duk wanda ya samu iyaye irin ku ai sai hamdalah ga rabbil izzati. AFREEN ta ja tayi shiru dan jin zuciyar ta nason karyewa yanzu nan zata iya fashewa da kuka abinda kuma bata son papa ya gane ta na cikin damuwa kan wannan zaɓin nasa, dan da zata iya ƙurma ihu a lokacin da papa ke sanar da ita da tayi sai dai bazata iya ba dan farin cikin mahaifin ta ya fiye ma ta komai.


Cike da farin ciki papa ke kallon AFREEN da ta duƙe kai tana kallon ƙasa sannan yace "Allah maki albarka Allah maki albarka Allah maki albarka AFREEN har yau har kullum ina alfahari da ku duka yaran da Allah ya bani ba ma kamar ke ban taɓa aza magana kika tsallake ta ba Allah maki albarka Allah baki ɗiyan dake ma za su maki fiye da yanda ki ke ma mu Allah ya saka maki da aljanna firdaoussi."


Ameen AFREEN da mahaifiyar ta suka amsa sannan papa ya koma cewa kin amince da zaɓi na, amma ke baki faɗa man ko ki nada wanda ki ke so ba?"


Da sauri AFREEN tace ba bu kowa papa ai da na sanar da kai."
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸




Écrit




Par




*QUEEN ZEEFAT*




_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_



*Wattpad@nazichou*


💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/

*_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_*




*Page* : 59 & 60


"To shikenan Allah maki albarka ki rubuto man a takarda duk abinda kike so ki kawo man koma miye idan dai bai fi ƙarfi na ba zan maki shi kuma in ba na saɓan Allah bane, sannan zan turo maki da wasu kalolin motoci guda biyu sabin fitowa har yanzu basu kawo nan ba ko a ƙasashen waje ba ko wane ya san su ba sai ki zaɓi guda na siya ma kamin bikin ki sai a kawo maki insha allah da akwai wasu shaguna da na buɗe da sunan ki a garin Niamey na ki ne duka haka kayan dake cikin, dama faɗa maki ne bayan, amma idan kika duba account ɗinkin zaki ga kusan kullum kuɗin cikin ƙaruwa suke, har ma kin taɓa min magana akan haka na ce maki ni ne nake ajiya a cikin account ɗin to ba haka bane na ki ne kawai kuma duk ribar da ake samu ce ga shagunan Allah maki albarka."


"Nagode papa Allah saka da alkairi amma gani nake kamar sunyi yawa papa duba da ba ni ɗaya ba ce."


"Karki damu da wannan ke ta ki kyautar ta musamman ce, amma suma duk na shirya wa kowa ta shi sedai suma ma ba yanzu zan basu ba sai duk nan gaba sedai a gaskiya tasu ba kai taki ba."


"To mun gode papa Allah ƙara arziki mai albarka Allah ƙara lafiya da nisan kwana Allah kare ka da ga sharin duk wani abun shari ameen."


Da Ameen papa da maman suka amsa sannan papa ya ƙara cewa "Allah maki albarka ta shi kije ku fara shirin bikin ki tun yau saboda wata ɗaya da kwana shida ya yi saura."


Gaban AFREEN ya ƙara faɗuwa kuma ta ƙara shiga damuwa sai taji kamar ta aza hannun a kai ta yi ta kuka amma ba dama, kuma sai ba ta nuna ma papa da maman hakan ba se miƙe da tayi cikin mutuwar jiki ta bar ɗakin.


AFREEN na shiga ɗakin ta faɗa kan gado ta shiga rusa wani irin kuka mai ban tausayi da tsuma zuciyar duk wani mai saurare gwani ban tausayi, saida tayi mai isar ta sannan tayi shiru duk idanun ta sun kunbura sunyi tulutu gashi kuma abun ga mai mayan ido ta ta shi ta shige bayi ta ɗauro alwala ta fito ta gabatar da sallah azahar da ta dalilin kiran sallah yasa ta daina kukan, a sujidar ta ƙarshe ce ta shiga rera wani sabon kukan mai ci rai tana faɗawa Allah "Ya Ubangiji ya Sarkin sarakuna ya mai samai da ƙasai ya hayyu ya ƙayyum, ta shiga dai yiwa Allah kirari sannan tace ya Allah idan har zaɓin mahaifin na alkairi ne a gare ni Allah kasa na yarda da shi hakan kuma naso wanda zai haɗa ni dashi na amince idan kuwa AFREED shine alkairi a gareni Allah ka wargaza shirin mahaifina ka barni da masoyi na wanda nakeso idan shima ba alkairi ba ne Allah haɗi da alkairi sannan kasa nayarda da shi kuma na so shi."


AFREEN dai tai ta jero addu'a ta na kuka mai tsananin sai da har taji kanta zai fara ciwo kan ta daina kukan ta bawa kanta hakuri, sannan ta ɗauki Alkur'ani mai girma ta shiga karantawa a nan ne ta ji salama taji hankali ya ɗan kwata yunin ranar ta kasa saka kofa ruwa ne a cikin ta bare abinci, sau biyu mahaifiyar ta na shigowa ta kira ta ci abinci sai ta tardo ta kwance ta lahe kamar mai bacci, alhali ba bacci take ba kawai daga taji takun tafiyar za ta shigo ɗakin tane sai ta yi maza ta yi kwace ta lahe kamar mai bacci, haka AFREEN ta yuni ranar ko kiran AFREED ta kasa ɗauka don gani take mi zata faɗa masa ya zai ɗauki zancen ta ya zatayi itama da son da take masa yanzu nan rabata da shi za'ayi, idan ta tuna haka sai ta shiga furta inna lilahi wa inna ilaihi raji'un, tare da rokon Allah ya kawo ma ta sasauci raɗaɗin dake cikin zuciyarta dan ba ƙaramin so take yi wa AFREED, saboda bata san ya akayi take son sa ya yi mata mugun kamu har take ganin bata iya rabuwa da shi duk ratsi, haka ma bata iya watsa ma Mahaifinta ƙasa a ido kawai ta bar ma Allah zaɓi.


Da wajen ƙarfe huɗu da rabi AFREEN na zaune saman darduma wanda tunda ta gama sallah la'asar ba ta ta shiba saboda tana karanto azkar ɗin yamma mahaifiyar ta shigo ɗakin da sallama ɗauke da bakin ta, ba tare da AFREEN ta ɗago ba ta amsa sallamar, maman ta nemi guri

Please Login or Register in order to submit comment