Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ba yace "Waye?"

"Nima ban sani ba Abbu."

"To jeki amma kada ki dad'e kuma ki kula da mutuncinki."

Ta amsa da "To" sannan ta tashi tafita bata tsaya bin ta kan Ufadi dake ta yada mata magana da jefa mata harara ba directe (direct) waje ta wuce.

Dayake da duhu a wajan sai haskin farin wata yasa tayita dubawa bata ga kowa ba, tana shirin juyawa ta koma taji ance "Sannun ki malama."

Da sauri ta waigo gun da taji sautin maganar ya fito, bata dai gane kowaye ba kawai sai ta k'ara matsawa kusan shi, aiko ta ganeshi tace "Lah kaine?"

"Eh nine ashe kin gane ni?"

"Haba ba dole na ganeka ba tunda sauran kud'in ka na guna, ai se in ka karb'e su kawai zan manta a lokacin nasan ba ha'kin kowa a kaina."

Waro ido yayi waje yace "Lah ashe ma zaki manta dani daga zarar na karbi kud'i na ko? Ko irin wanan d'an zumuncin ba za muyi ba dan mu ringa kaisawa."

Tace "A'a bahaka nake nufi ba idan dai mun had'u a hanya ai zamu gaisa."

"A'a gashinan kin fad'a da bakin ki cewa da zarar na karbi kud'in na zaki manta da ni."

"Oh Allah ba haka nake nufinufi ba ai d'an halak bai manta alkairi kaga kenan idan na manta ka ai na manta da aikairin da kamin, kuma nazama butulu kenan fah!! Kaga ko gaisawa ma bamuyi ba, ina yuni ka yuni lafiya?"

"Lafiya lau alhamdulilah da fatan kina lafiya, ya kwana biyu."

"Lafiya lau nake, kwana biyu sai alkairi bari nashi na karb'o ma kud'in ka Abbu ya ce kana dad'e."

"Abbu na ciki ne?

"Eh yana ciki."

"Shine kuma baza ki man tayin naje na gaidashi ba ko dai rowar baban zaki min?"

"Ko d'aya wallahi manta wa nayi shima Abbu d'in yace idan ka dawo karb'a cikon ka nace ya neman ka manta wa nayi."

"Woow!!! Har kin ba Abbu labarina ashe kema kina ciki?"

"Ina ciki kamar ya?"

"Share kawai, ko baki ciki to ni nagani kuma na k'aisa yi sauri kije ki sanarwa da Abbu zuwana."

Arahamat da ta kasa gane inda kalaman sa suka dosa kawai sai tasa kai ta nufi cikin gida ta nazuwa ta sanarwa Abbu cewa wanda ya taimaka mata da kud'in ne lokacin da a ka sabce nata ne ya zo. Abbu yace taje ta shigo dashi.

Komawa tayi ta gaya ma sa sok'on Abbu kannan suka dawo tare, da sallama ya shigo gidan, aka amsa masa lokacin Abbu na tsakar gida tare da uwar gida Ufadi sunna d'an tab'a fira k'asa k'asa duk yawan maganar Ufadi k'orafi yafi yawa.

Haka dai ya shigo ya samesu kansa duke durk'usawa yayi ya gaida amsawa sukayi cikin sakin fuska, Abbu yace "Bismillah yaro ga guri zauna" tare da nuna masa tabarmar da yasa Arahamat ta shinfid'a tashi yayi daga tsugun nin da yayi koma kan tabarmar ya zauna kansa na kollon k'asa ita kuwa Arahamat tana kawo tabarmar ta shigewar ta d'aki.

Gyaran murya Abbu yayi sannan yace "Yaro mi sunnan ka?"

Ba tare da ya d'ago ba yace "Sadisu?"

"Masha Allah Sadisu kana lafiya?"

"Lafiya lau."

"To madalah Arahamat ta zo da kud'in ranar nan tace kaine kabata wane dalili ne yasa kaba ta alhalin baka santa ba kuma tana yiwu ma baka tab'a ganin taba?"

"Eh wallahi nine naba ta sanadin ganin ta da nayi tana kuka sosai a hanya a lokacin gaskiya tausayi ta bani shiyasa natsaya na tambaye ta miya faru tace kud'in ta aka sabce kuma idan ta dawo gida tace sun b'ata f'ada za'a mata shiyasa sai na taimaka na bata kud'in to har neman canjin tayi da bata samu ba ta bar kud'in idan aka aike ta, kuma saida nayi nayi da itama ta rike sauran canji ta ki shiyasa nace ta nuna min gidan idan ta karb'o saura kud'in sai nazo na karb'a, amma baba a zahirin gaskiya yanzu ba karb'a kud'in nazo b...........

Bai k'arasa zancan ba Ufadi ta katse shi da cewa "Ji min munafinkin yaro to mika zoyi in ba karb'a kud'in ka ba, ko ka zo ne ka k'arasa lalata ta a cikin gidan uban ta kai malalaci wai wane taimakon kayi? ka b'ata yarinya yanzu wake taimako dan Allah ai sai dai bani in baka, ka lalata yarinya ka bata kud'i muku ma kace mana wai gani kayi tana kuka dan k'arya, ni dama tunda na ganka nasan ba d'an kirki bane diboka kayi kama da malal............

Bata k'arasa fad'in abinda zata fad'a ba a tsawa ce Abbu yace " Yiman shiru Ufadi wa yasaka ki acikin maganar nan ko kinji an kira sunan ki ne a cikin zancan nan ne."

"Ah to malam ga gaskiya sai naki fad'a dan dai ba'ajin tsoron Allah."

"Wallahi idan baki min shiru a nan ba ranki sai yayi mumunan b'aci manzon tsira SAW yana cewa fal yak'ul khairan aw liyasmut, to idan kisan ba alkairi zaki fad'a ba ki tashi ki bar min nan tunda dama ba gayato ki nayi ba, ko kunya ta bakiji a gabana kina ai batamin yarinya to nagaji dajin irin wad'an nan munanan kalaman naki kan y'ata kinan zargin ta akan abinda ke da kanki kin san ba gaskiya bane, ban san mi tayi maki ba kike mata haka."

Abbu ya k'arasa maganar ransa a matuk'ar b'ace sumi sumi Ufadi tata shi tana cewa "Ga gaskiya sai a hanani fad'ar ta" tashige d'akinta da sauri sabida tasan da Abbu ya zafi ba wasa.

Tana shiga d'akin kuma sai tace "Miyasa ma nake aibata yarinya can gaban yaron nan idan fa auren ta yakeson yi shikenan na b'ata auren, gaskiya da sake idan auren ta yazo nema kam zan san yanda zanyi na gyara maganar inaaaaaa mijin auren da nadad'e inason ta samu don taje ta bar min gidan in huta da jaraba kuma da rikon d'an da ba nawa ba, ai da sake koda ba neman auren ta ya zoba zan shiga in fita sai ya aureta tunda dai har ya kawo kansa gidan nan tun yaushe nake fatan Allah ya kawo man mafita na jefar da d'an mangoro in huta da k'uda ko kad'an banison ganin yarinyar nan a cikin gidan nan wallahi dole ma tayi aure ta bar min gida duk da cewa gidan ubanta ne amma yazama dole ta bar shi."

Ufadi ce ke ta wanan maganganu ita d'aya a d'aki."

B'angaren Abbu kuma Ufadi na tashi ya juyo kan Sadisu yace "To yaro bismillah ina jikan da mikazo dashi baya ga karb'ar sauran cikon kud'in ka."

Sai da ya d'an nisa tare da girgiza kai idonsa na kallon k'asa sannan yace "A gaskiya baba tun ranar da naga Arahamat ta kwanta min inason ta so kuma na aure ba na yaudara ba kuma ni ba malalaci ba ne baba idan kanaso ma kasa a yima bincike a kaina."

"To Alhamdulilah nayi farin cikin jin haka daga bakin ka dan daga nin kai yaron kirki ne, amma wanni hanzari ba gudu ba ni da na tambayi Arahamat ce man tayi babu komi a tsakani ku gashi kai kazomin da wani zance ya haka?"

"Et baba gaskiya ban fad'a mata cewa inason ta ba shiyasa kuma abinda yasa nayi haka dan kar tayi tunani sabida na taimaka mata ne yasa nace inason ta ko kuma ta fassara zancan da wata manufa, shiyasa na zabi har sai nazo maka da zancan tunkun na dalilin da yasa na mata wayo kan cewa ta nuna min gida su idan sai nazo na karb'i sauran canjin, a zahirin gaskiya ba karb'ar kud'in nazo ba ganika na kuma na fad'a maka manufata a kanta tunda nidai tun ranar dana bata kud'in nan manta dasu sabida ni gabad'aya na bata ba wai don ta mayar min da canji bane, dan Allah baba ina neman alfarma da a taimaka a bani auren Arahamat." Sadisu ya fad'a ba tare da ya d'ago da kansa ba.

Wani farin ciki ne ya mamaye Abbu sabida Allah kad'ai yasan yanda yake fatan Allah ya kawowa Arahamat miji na gari tayi aure ko dan ta futa da uk'uba Ufadi gashi da gani alamu wanan yaron mutuman kirki ne, sai dai Abbu bai nuna tsanani farin cikin da yake cikin sabida ma ka Sadisu yayi tunani ko an gaji da zaman ta a gidan ne alhali ba haka bane.

Abbu ya fad'ad'a murmushin yace "Gaskiya nayi farin ciki sosai da jin haka, amma miye sunan ka kai d'an waye kuma ina ne gidan ku a gari nan miye kuma sana'ar ka? kasan Yanada kyau nasan asalinka da halinka da abubuwan da baza'a rasaba na rayuwa tunda zancan aure fah babban abune ko ba gaskiya ba?"

"D'an murmushi yayi har kansa na duk'e yace "Hakane baba, da farko dai ni sunana Sadisu Asmane Sanga mahaifina cikaken d'an asalin garin Mali ne can ne garin su na iyaye da kakani dagin sa duka suna can, nima can aka haifeni ni da dangina baki d'aya mahaifiyata cikaka 'yar Niger ce haifafa garin zinder, yanzu ma a cikin garin Niamey muke da zama sakamakon rasuwar mahaifina muka tataro muka baro Mali kuma muka dawo Niger inada yaye mata biyu da namiji guda nine k'arami a cikin kuma nine banyi aure ba, kuma karatu ne ya kawo ni cikin garin amma nan da wata biyu zan k'arasa na koma garin mu, sanan kamin na baro gida ina d'an tab'a kasuwanci idan na koma gida kuma da k'asuwancin zanci gaba."

"Masha Allah Sadisu naji tak'aitacan labarin ka, da alamu bakayi kama da mutuman banza ba dan haka indai ni ke bada auren Arahamat to nabaka ita duniya da lahira kuma abisa amana kaga dai ita marainiya ce kada ka cutar da ita sabida amana na baka ita idan kaci amana ta Allah zai saka mata ko dan maraicin ta, kuma itama buzuwace gaba da baya kamar yanda ka lura mahaifiyar ta rasu wajan haihuwa k'anwata, kuma su uku ne ga mahaifiyar su har nima sune k'adai gare ni duk fad'i duniyar nan banida kamar su sedai shi baban wan nasu tunda gomnati ya turasa karatu a Canada har inda yau ke kwana ban gara sashi a idona ba yau kimanin shekara hud'u kenan, yana raye ko ya koma ka mahalicin shi Allah kad'e yasani ita kuma k'anwartata tana Arlit gun yar uwar mahaifiyar su, sedai wani hanzari ba gudu ba, kaje kasami ita Arahamat d'in kanemi soyayar idan ta amince da haka taji tana sonka alhamdulilah idan kuma bata amince sedai kayi hakuri sabida bazan mata doli ba duk abinda takeso to nima shi nakeso."

Wani sihirtacen murmushi Sadisu ya saki sannan yace "Alhamdulilah baba nagode da karamci da kauna da aka nuna min nayi farin ciki mara misiltuwa baba Allah kara lafiya da nisan kwana kuma insha Allah za'a ga wan su da ikon Allah ya na a raye bai mutu ba da yarda ubangiji, in Allah yaso ya yarda idan har Arahamat ta amince da aure na baza ka taba nadamar bani ita da kayi ba da ikon Allah."

Seda ya kara sunne kai san yace "Baba idan son samu ne ina neman alfarma har in ta amince nan da wata biyu a d'aura mana aure kamin na koma sai mu koma tare da ita sabida yanzu ina fita daga nan zan kira mahaifiya ta na sanar mata insha Allah."

Abbu yace "To Sadisu wata biyu baiyi kusa?"

Seda ya d'an sosa kai sannan yace "A'a baba."

Murmushi Abbu ya saki ciki zuciyar shi yace "Yaran zamani" a zahiri kuma sai yace "To karka damu kai dai kaje ka nemi soyayar ta in ta amince shikenan sabida ni najima ina shirya ma auren yarinyar nan da k'anwata."

Sun d'an jima suna tataunawa kamin daga bisani yayi wa Abbu sallama ya fita.

Yana fita Abbu ya k'wala mata kira a firgice ta farka sabida har bacci ya fara d'ibarta kawai sab'o hijab tayi ta fito taje gun Abbu ta durk'usa yace "Tashi je kiyi masa sallama tafiya zaiyi."

Da sauri ta d'ago ta kalli mahaifin nata tace "wa?" don ita har ga Allah ta manta da wani yazo gidan.

Abbu yace "Wa kuma? Sadisu mutuman daya taimaka miki ranar nan yana can waje yana jira."

"Oh wallahi Abbu har na manta da yazo gidan nan ni harma na fara bacci, kenan sad.... Bata k'arasa fad'in sunan ba sanadi nuhi fad'i da taji ya mata a baki sanan tace "Kenan Hakane sunan shi bari naje muyi sallama" haka ta fad'a tare da fita daga gidan.

Abbu yayi murmushi tare tashi ya shiga d'aki.

Tana fita ta tardo shi baki k'ofar gidan yana jiranta tace "Har zaka tafi?"

"Hum wai har zaka tafi?" yayin yanda tayi sannan yace "Bayan nakusa kwana a gidan ku sabida ke."

"Kwana a gidan mu kuma ka rufa man asiri nidai."

"To baki son na kwana a gidan kune? ni ina cewa yanzu mun zama 'yan uwa zan bar kwana a cikin makaranta na dawo da kayana gidan ku a sama min gun bacci? amma shine zakimin rowa."

Waro ido tayi da sauri tare da cewa " Yo zaka iya?"

"Yo mi zai hana?"

"To shikenan zan gayawa Abbu sannan."

Dariya yayi sannan yace "Kewa wasa nake maki."

Murmushi tayi tare da sun ne kai gyara tsayiwa yayi sannan ya kira sunan ta "Arahamat."

Amsawa tayi da "Na'am."

Yace "Ki nutsu ki bani hankalin ki nan zamuyi wata magana."

A sanyaye tace "To ina jinka."

Seda ya k'ara gyara tsayiwa sannan yace "Zaki aure ni?"

Kamar saukar aradu taji maganar da sauri ta d'ago ta dubeshi tare da yin sauri maida kanta k'asa wai itace yau wani ke furtama wanan kalmar da ba wanda ya tab'a mata ita shin mafarki take ko a farke take? da alama ba bacci take ba da gaske ne."

"Yanaji kinyi shiru ko baki ji mi nace ba ko baki fahimci mi nake nufi ba? In hakane bari na miki yanda zaki gane, Arahamat inason ki ina kaunarki fiye da yanda kike tunani sonki ya ratsa ko ina na jikina, shin zaki aureni?"

Da sauri tasaka hannu ta rufe mashi baki a lokaci guda kuma ruga da gudu cikin gida sabida jin kalaman sa take kamar ana mata ihu cikin kunne. Amma ba karamin farin ciki tayi dajinsu ba.

Yau sati biyu kenan da Sadisu ya baya nawa Arahamat abinda ke cin zuciyarsa kuma ta amince shakuwa da soyaya mai k'arfi ta shiga tsakanisu Sadisu kuwa har ya shedawa mahaifiyar sa kuwa tayi na'am da zancan yawaci ma idan yaje zance yana kiran Hajia Zakiya ya bata su gaisa da Arahamat wada tun tanaji kunya har yakai ta saki jiki suna fira sosai dan hajia Zakiya tace ita ba surukar ta bace kamar 'ya haka ta ke gunta, kuma hajiya zakiya ta shedawa yaronta ta cewa nan da sati biyu za'a zo kawo komi da komi na aure harda lefe, shima kuma har ya shedawa iyayen Arahamat.

B'angaren Ufadi kuwa ta rage tsangwamar da take yiwa Arahamat sanadin aure da zatayi taje ta bar mata gida.

Yau ta kama lahadi kuma yau ne ranar da za'a kai lefe shalele kuma auta a gun hajiya zakiya tunji jiya alhaji suley da wasu abukan sa biyu sukazo da komi da komi da za'a bukata. Haka yau ma suka d'auki niki niki kayan lefan sukai gidan su Arahamat ida a ka kashe kud'ad'e sosai sabida auren buzuwa fah sai mutum ya shiyar dole sai kasaka g'wala g'walai kuma ka siye rak'uma anyi bajin ta masha kuma ankashi kud'i akasa aure nan da wata guda.

Kawanci tashi ba yuya a wajan ubangiji yau ya kama saura sati biyu auren Arahamat da Sadisu, yau ne kuma tanti Fatima k'anwar mahaifiyar su tazo gidan gani tayasa Arahamat cikin farin ciki da anashuwa amma da taga ba da k'anwar a ka zoba sai murna ta koma ciki tace "Tanti oΓΉ est ma petie soeur (where is my lil Sister)."

D'an murmushi Tanti tayi tace " kwantar da hankalin sai saura kwana uku zata zo sabida Γ©cole (school) sai a sannan ne ta saki ranta nanfa tanti Fatima tashiga gyaran amarya.

Yau ya kama saura sati d'aya d'aurin aure Arahamat na zaune tsakar gida tana alwala taji anyi sallama da sauri kuma a firgice ta mik'e don jin murya da ko ta mutu bata zata iya mantawa da ita ba tsurawa k'ofar shigo wa gidan tayi tana adu'a Allah sa abinda take tunani ya zama gaskiya aiko wanda yayi sallama na shigo wa ta saki wata irin razananiya k'ara mai sauti sai wani tippppppp kake ji ta fad'i k'asa somamiya..........



To masu karatu mai ya tsoratar da Arahamat da yasa ta fasa ihu, sallamar wa taji ta firgice, wane abu ta gani har yasa ta suma?

Ku biyoni a next page don samin amsar wa'inan tambayoyin???? Amma sai kuyi comments kuma next page sosai zata k'ayatar daku. In bakuyi comments ba ba zanyi next page d'in ba.

Ina jiran comments d'inkuπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZANBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


ECRITE: πŸ“πŸ“πŸ“


_PAR_


*QUEEN ZEEFAT*



Yar
Mutan
Niger



Wattpad@nazhabibou




πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ
Hh
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/



_BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM_



~Masoyan wannan novel nasan kuna hakuri sosai akan d'aukar lokaci da nake banyi typing ba, to ina mai baku k'ara baku hakuri wallahi karatu ne yaman yawa, nima ba da son raina hakan ke faruwa love you more my FANS....😍😍😍😍~



Page : 13 & 14


Lafiya lau suka sauka cikin garin Niamey direct gidan hajiya Zakiya aka nufa dasu suna zuwa ta k'arb'esu hannu bibiyu da fara'a a fuskar ta ta masu tarba ta mutunci a falon ta suka sauka aka kai masu kayan su a cikin d'aki da zasu zauna, amma kayan Arahamat a d'akin hajiya Zakiya aka kai mata su cikin k'ank'anan lokaci aka cika gaban su da kayan ciye ciye da lashe lashe, tanti Fatima da Ufadi sunci sun sha amma banda Arahamat dake rakub'e yuri guda ta k'asa koda d'aga kanta har saida Hajiya Zakiya ta fito daga d'aki kamin tajata suka nufi d'akin ta sannan lalab'ata ta ci abincin tana gamawa tasa tayi wanka da sallah sannan hajiya Zakiya tasaka ta d'ane gado ta kwanta bata dad'e da kwanta wa ba bacci ya kwashe ta.

Sukuwa su Tanti Fatima na d'akin da aka tana domin su suma sunyi wanka tare dayin sallah suka kwanta don hutawa.

Arahamat ba itace tashi ba sai da ana kiran sallah magariba sannan hajiya Zakiya ta shigo d'akin ta tayar da ita.

Koma yin wanka tayi sannan ta d'auro alwala magariba tazo tayi sallah, tana gama hajiya Zakiya ta shigo mata da abinci ta d'an ci kad'an sannan aka shirya don kaita gidan ta dake cikin gidan hajiya Zakiya.

Ana gama shirya ta su Tanti suka nufi d'akin hajiya Zakiya suka tardo ta zaune bakin gado tasha ado tayi kyau sosai kamar balarabiya suma zaunawa suka, suka soma mata nasiha mai ratsa jiki tanata kuka, haka hajiya Zakiya ta shigo ta iskosu tace "Dan Allah ku barta haka zaku saka kwalliyar da aka mata ta goge daga ganin d'iyata ba mai kwaramniya bace nasan zata zauna lafiya da mijinta insha Allah, gashi tun kamin kuzo nan nasan kunyi mata nasihar kuma ta d'auka, gaskiya ku barta haka kuma insha Allah Arahamat ba zata maraici a gidan nan ba da yarda Allah, ni d'iyace kuka kawo min ba suruka ba don haka ku kwantar da hankalin ku, kuma ke Arahamat ki d'auke ni a matsayin mahaifiyar ki inason duk abinda Sadisu ya maki na k'untatawa ki fad'a min kiga hukuncin da zan yanke a kansa wallahi ko da kuwa kece mai laifin idan har ya nemi takura ki zo ki sameni ki sanar dani zaki sha mamaki insha taron dangi zamu masa" Hajiya Zakiya ta fad'i haka tana dariya.

Tanti tayi saurin cewa a'a zaluntar yaron albarkar nan zakuyi kenan to wallahi baku isaba zan kirasa na fad'a masa daga Arahamat tayi masa laifi ya hukunta ta sannan ya kirani ya sanar dani don wallahi mota zan tako daga Arlit har Niamey nazo nayi maganin ta sabida bani goyon rashin kunya da zata masa, sannan kuma ace shine mai laifi ko alama ki dai ji abinda na fad'a kuma kinfi kowa sanin zan iya aikata wa da haka kada ma ku taru kumasa taron dangi nima shigar masa zanyi ehe ga kuma Ufadi nasan itama tana bayana ah to."

"Ah wallahi ina bayan ki ai tare zamu biyu mota muzo hukunta ta ai tafi kowa sanin halina sedai ta ba wani labari ehe" haka Ufadi ta fad'a tana dariya.

Hajiya Zakiya ta yi dariya sosai, sannan tace "Kam ashe dai da kunga irin namu taron dangi sabida ko banza muda kenan mun fiku yawa, kuma kamin kuzo mu mun riga da mun gama namu hukuncin, sannan zanga wanda ya isa ya shigo gidan mu yace zai hukunta min yarinya wallahi da zaku sha mamakina."

Haka dai suka yita raha suna dariya har Arahamat ta daina kuka ta koma murmushi, daga dai bisani suka jata suka nufi da ita b'angaren dake nesa sosai dana hajiya Zakiya suka ce ta shiga da bismillah sannan da k'afar dama haka kuwa tayi, tubarukallah yayanta ba k'aramin kud'in ya kashe ba wajan zuba mata kayan d'akin ba, ba wani jimawa sukayi ba suka koma b'angaren hajiya Zakiya suka barta ita d'aya, tana nan zaune idan suka barta har Sadisu ya shigo d'akin da sallama cike da farin ciki ya nufe ta tare da cewa "Alhamdulilah yau Allah ya nuna min ranar nan da bazan tab'a mancewa ba haka dai ya sata ta shiga douche tayi wanka tare da d'auro alwala suka zo sukayi sallah ta neman albarka aure sannan ya bud'e ya d'auko plet ya zuba masu kazar da ya shigo masu da ita ta amarci kad'an Arahamat taci shima dan ya takura ne da suka gama ya tatara kyan dasuka b'ata ya mayar cuisine (kitchen) yana fita ta koma douche (toilet) ta k'ara wanko baki tafito
Sannan sukayi shirin bacci suka kwanta aranar dai sai Sadisu ya mayar da ita cikakiyar mace yana ta sa mata albarka ita kuwa sai kuka take.

Kwonci tashi babu wuya a wajan ubangiji gashi yanzu shekara guda kenan da wata shida da auren Arahamat da Sadisu har Allah ya basu k'aruwa ta d'an namiji wanda yaci sunan mahaifin Sadisu wato Asmane suna kiransa da Kalifa yaron ya taso cikin gata da soyayya tare da kulawar iyayensa da ma ta dangi gabad'aya.

Kalifa nada shekara uku da haihuwa ya kamu da rashin lafiya mai tsananin wada tayi sanadiyar tafiya da rayuwar sa, rasuwar Kalifa tayi matuk'ar girgiza wannan famille (family) ba kad'an ba, ba ma kamar Arahamat da seda aka had'a da adu'a kamin take dawowa hayacin ta.

Haka suka ci gaba da rayuwarsu cikin farin ciki da kaunar juna Sadisu na kasuwancin sa tsakanin Marad'i da Niamey sannan yana fita kasashan waje siyar kanyan sai dawarsa har lokacin da kasuwancin sa gabad'aya ya koma Marad'i, haka shima ya tatara iyalensa tare da mahaifiyar sa suka koma Marad'i da zama baki d'aya suka bar Adamu da iyalensa Niamey lokacin Adamu matansa biyu da 'ya'ya hud'u.

Kasuwancin Sadisu sai bunkasa yake yanzu yayi arziki sosai ba kad'an ba yayi fice babu wanda baisansa ba cikin garin Marad'i da kewayen ta kowa yasan alhaji Sadisu mai sayar da kayan gini a cikin farashi mai sauki harda sauran jahuhi na karsar Niger zuwa ake sayan kayan gini a shagugu kansa dake cikin Marad'i da Niamey yanzu kam ya zama millioniya Sadisu nada wani aboki wanda suka tashi tare tun lokacin da suka baro Mali suka dawo Niamey me suna sumana tare sukayi collège wato(secandiri school) har sukaje universsité tare inda Sadisu yayi karatu afanin kasuwancin shikuwa sumana ya karanta ingenier suna da shekara biyu a makarantar Agadez baban sumana ya mayar da sumana karatu a France inda can ya k'arasa nashi karatun shima

Please Login or Register in order to submit comment