Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya juyo ya kallesa yace "Eh amma lafiya kake son zuwan ranar juma'a?"


"Ba komi." AFREED ya faɗa a taƙaice.


Miƙewa Ali yayi sannan yace "To shikenan yanzu dai kasamu kayi bacci ka huta ko ciwon kan nan naka zai rabu dakai."


A zuciyarsa yace "Da zan ganta ko naji muryar ta da yanzu nan na wartsake tunda itace ta sakamin ciwon kan, amma a fili sai yace " To" kamar wani ƙaramin yaro ga yanda yayi maganar.


Fita Ali yayi daga ɗakin sanadin ganin da yayi kamar bacci ya fara ɗaukar sa, tare da rufo masa ƙofar.



****** ******* *******



JUMA'A BABBA RANA


Ya tunda AFREED ya farka yake jinshi cikin wani irin farin ciki mara musultuwa sai fara'a yake haka kawai badan yasan dalili ba har ƴan gidan sai da suka fahimci haka daga gare shi, suna zaune suna karyawa yawa sai murmushi yake shi ɗaya, tanti ta lura da hakan tun shigowar sa falon ta gane cewa yau ɗan nata na cikin farin ciki ko dan gani da tayi masa yau ana magana yana saka bakin ba kamar kullum ba itama murmushi tayi ta kallesa tace "Yau ɗana lafiya na ganka cikin farin ciki haka sai wani sakin murmushi kake, ai ya kamata araba farin cikin nan damu dan muma mu tayaka murnar kodai sirika a samar min ne?"


Kamin AFREED yace wani abun Farisa tayi saurin cewa "Ko dai yaya kayi waya da Momy ne shiyasa kake ta farin ciki nidai kam kamar tanti yau na lura kana cikin jin daɗin."


Maida kallon sa yayi wajen Farisa ya sakar mata murmushi sannan ya dawo da kallon sa ga tanti yace "Lah Tanti wallahi ba haka bane kawai dai nima yau na tashi na tsintsi kaina cikin farin ciki da bansan dalilin sa."


Murmushi tanti tayi sannan tace "To Allah dawamar da kai cikin sa." Da ameen suka amsa su duka, sannan suka miƙe daga cin abincin suka koma falon, basu jima suna fira ba AFREED da Ali da Umar suka miƙe tareda cewa Tanti Aicha ( ƙanwar mahaifin AFREED dama sunanta Aicha to yanzu namai da su AFREED su ringa kiranta da tanti Aicha dan a banbantata da tanti kishiyar Maman AFREEN dan masu karatu su fahimta) su AFREED su kacewa tanti Aicha sun koma ɓangaren su kamin lokacin tafiya Sallah juma'a yayi haka."


Da to ta amsa masu sannan sukayi gaba abinsu, suna shiga ɓangaren su kowa ya nufi nashi ɗakin, AFREED zaune saman gadon da ƙur'ani a hannu sa yana karanta suratul kahaf kuma yanayi yana duba montre ( agogo) sabida ya matsu lokacin zuwa masallaci yayi ko zai ganta ba dan komai sedan yaji muryar ta.




****** ******* ******

Kamar kullum haka mutanen gidan su AFREEN suka tattara su tafi masallaci yau kam a tare suka tafi dan AFREEN bata bari suka barsu ba, mota papa da matansa sa ita ke gaba AFREEN na binsu a baya sannan motar su Fahad shida ƙanansa Imran sun jera tsaf kwanin ban sha'awa, Suna ƙarasawa masallaci su Fahad suka nufi wajan parking ɗin maza shi kuwa papa saida ya ajiye matan sa bakin masallaci mata sannan ya juya itakuwa AFREEN direct parking ɗin mata ta nufa ta paka tata motar sannan suka fito ita da ƙannanta suka jera suka nufi hayar shiga masallacin, sun ɗan jima da zuwa sannan aka tayar da sallah dan har nafila sai da sukayi, huɗuba ma suna can aka fara har aka ida tare da su.


Ana sallamcewa daga Sallah aka fara ɗauri aure da aka gama kowa ya fito banda su AFREEN wanda haka ya zama al'adar tane sai mutane sun rage suke fitowa, kuma gashi tanata dube dube ganin ko zataga ƙawarta dan duk yau basu haɗu ba kuma yau ba makaranta sukayi ba suna hutu, kuma gashi cikin masallaci duk mutane sun watse bata ganta ba sai take tunanin ko batazo, sai kuma tace amma tace man zata zo kodai tana ƙasa yau ba a sama tayi sallah ba bari naje na dubata, daganan ta juya ta kalli su Zeinab dake jiran ta tace "ku taso mu tafi." Ba musu suka tashi.


AFREED na bakin ƙofar masallaci yana ta wange wangen ina zai ganta ko yauma a parking ɗin maza ta ajiye motar ta?" Ya tambayi kansa tareda nufar hanyar wajan ko da zai ganta acan to dama idan mutun zaije parking ɗin maza sai ya bi ta hanyar masallaci mata kamin yake kai wajen parking ɗin na maza, hakane ta kasance yanzu AFREED na shirin wucewa ta ƙofar masallaci mata dan zuwa parking ɗin maza dan tun tuni Ali ya kecan yana jiransa, ita kuwa AFREEN ta fito kenan dan zuwa neman Hasina ƙawarta, dama ta rika da tace ma su Zeinab suje mota su jirata.


AFREED ya taho kansa duƙe yana dana waya itama ta taho ta kusa kawowa gun shi kawai sai taji ance "Bestyyyyyyy." ba tare da ta tsaya da tafiyar da take ba ta juyo da ƙarfi dan jin muryar Hasina shima ya taho ba tareda yasan da itaba kawai ji sai tayi ta bangaji mutum ai kuwa a take ta juyo da sauri a lokacin da wayar da ke ga hannu sa ta faɗi ƙasa, da sauri AFREEN ta tsuguna dan ɗauko wayar shima ya tsuguna a tare suka kai hannu zasu taɓa wayar aikuwa sai hannuwan su suka gamu da na juna a take sukaji wani yar yar tun daga cikin kwalwarsu har tafin ƙafafun su da sauri AFREED ya janye hannunsa dake saman na AFREEN sabida shi shok ɗin yafi jansa, a tare suka ɗago cikin sauri hankan yayi sanadiyar kwarewar niƙaf ɗin AFREEN ba tare da ta sani ba ko ta lura da hankan ba, cikin firgici da mamakin kyau irin nata AFREED ya waro idanso kuri 😳 yana kallon ta ba tare da yasan yayi hakan ba, gabansa na mugun faɗuwa, a zuciyarsa ya aiyana cewa anya wannan mutum, idan mutum ce kuma wane irin masifafen kyau ne da ita haka? A take ya ba kansa amsar cewa kai ba mutum bace dan gaskiya a cikin duniyar nan babu muntun mai irin wannan bala'iyayen kyau nata.


Ya dawo daga duniyar tunanin daya lula ne a lokacin da ya tsinci zazakar muyar ta na furta " Dan Allah kayi hakuri ba da gangan nayi ba." Tana faɗar haka tan miƙa masa wayar da ke ga hannuta."


Ƙoƙarin control ɗin kansa yayi ya ƙarɓi wayar da ta gama gogewa cikin zuciyarsa yake faɗin wallahi itace wace nake nema itace ke da muryar nan mai sanhi da daɗi sauraro dole ne tayi kyau koda na jin muryar ta, ai kasan ta haɗu, a take wata zuciyar tace masa idan fah ba mutum bace?" Sauri kauda zancen yayi sannan a fili kuma sai yace "A'a karki damu ba wani abu."


Murmushinta mai kwantar da zuciya da saka mutum natsuwa ta sakar masa kuma har yanzu bata san cewa niƙaf ɗin ta janye daga fuskarta ba sannan tace "Nagode."


Da sauri AFREED yayi saurin dafe daidai zuciyar sa da ke harba masa da sauri da sauri tareda lumshe idonsa sannan ya buɗe sanadin sakar mashi ƙayatacan murmushi shinta mai kashe matum jiki da tayi, tareda kallon lips ɗinta ƙananu suna matsi a hankali idan tana magana ga gefan kumatunta duka biyu na lotsawa koda kuwa magana take ba sai tayi murmushi ba, cikin zuciyarsa ya furta zata kashe ni, hankalinsa na ƙoƙarin barin jikinsa yayi saurin ɗaga mata kansa ya bar gun ba tareda yaso hakan ba, dan gudun kada ya bada kansa.


Itama juyawa tayi ta bar gun ta nufi inda aminiyarta ke tsaye tana kallon su, tana ƙarasawa Hasina tace "Kai besty yau kinyi babban kamu kinga yanda mutum can ke kallon ki duk ya wani rikice a kanki kuwa gashi niƙaf ɗinki kuma ta ɗage sosai, kowama ke yakema kallon ƙurila juya kika yanda mutane ke kallon ki kamar sunga sabuwar halitta."


Sai a sannan ta lura da niƙaf ɗin bata ga fuskar ta ai da sauri ta gyara zaman niƙaf ta daidaita ta sannan ta saketa ta rufe mata fuska rufe sannan ta juya taga wanda mutane suka taru suna kallon ta da sauri ta ja hannu Hasina suka nufi wajan motar ta ida su Zeinab ke tsaye suna jiran ta, sai a lokacin ta samu damar sauke ajiyar zuciya tace "Besty kinga abinda yasa nan nake ɓoye fuskata duba kiga wanda mutane suka taru suna kallon na wallahi duk sai najini a takure."


"Rabu dasu haba kallon kaɗai ke nasu, ina maki maganar mutuman nan da kika yadawa waya kinyi min shiru." Hasina ta faɗa tana kallon AFREEN


Murmushi AFREEN tayi tace to "Besty ya kikeso nace maki ni babu wani kallo da naga yanayi min kawai daga haɗuwa, shirme ne kawai irin naki, idan kuma wani kallon ya min to bai huce shima na mamaki ne kamar yanda sauran mutanen sukayi ba."


Hasina tace "Hum sedai in kece baki gani ba nikuwa nagani wallahi bama kamar rikicewar danaga yayi, ni kam nahango wani abu a cikin idansa wanda ke baki ajiye hankali ba bare ki gani, kuma ni wallahi naga kamar ma MINISTRE DES DÉFENSES ET DE SÉCURITÉ ne wallahi baki ga shima da babette a fuskar sa, amma firgici ganinki da yayi bai san ma ya cire shi ba."


"Kai besty mi zai kawo minister (minista) nan gurin ba tare da masu tsaron sa ba shi ɗaya haba kema dai kinsan hakan ba zai yiyu ba, da shine da a lokacin da na bangaje shi har nayi sanadiyar faɗuwar wayar sa to da yanzu matakan tsaron sa sun lalasani koda ace anesa da shi suke to yanzu zakiga sun rugo sunyi magani na, barema basa yin nisa da shi kullum suna liƙe da shi kamar shiwinggum, kuma da a ce anan yayi Sallah da kin dinga ji kukan motacin jami'an tsaron da suke kare lafiyar sa tun kamin a shiga masallacin, kuma gashi bama a maraɗi yake ba, yanzu haka ma bai taɓa zuwa garin nan ba, kinga ko a TV ba muji ance zai zo ba, dan haka ki bar ma faɗa kada ajiki.


Hasina tace "Kuma hakane fah to amma wannan yayi mugun kama dashi, ta yiyuwa ko wani ɗan uwan sa ne kuma fah kawata kusan sunan ku irin ɗaya ne ministan da tsaro, Shi AFREED ke AFREEN ni ina ma zaizo ya aure minke."


AFREEN ta taɓe baki tare da cewa kindaiji da shi ni mi zanyi da wani minister, KAMAL ɗin na ya ishe ni, shi kaɗai nakeso da kauna, kuma insha Allah shine mai gida na, yanzu dai ba wannan ba ku shiga mu tafi gida."


Gaba ɗaya suka shiga sannan ta tayar da motar sai gida..................






( nima sai nabi tawa hanyar nace bari na barsu hakanan har bayan kwana biyu kuma sai mu waiwayesu)









Fatan alkairi ZAMBA CIKIN AMINCI FANS🥰🥰🥰
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸



Écrit


Par



*QUEEN ZEEFAT*




_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_



*Wattpad@nazichou*




💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/



*_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_*



*Page* : 33 & 34



Ali na ganin AFREED ya ƙaraso gun motar yace "Dan Allah AFREED miye haka ka wani zo ka shanyani anan kamar wani kayan wanki tun ɗazu ina nan inata jiranka, tunkuna ma ina kaje kayi zamanka har ka jima haka nidai nasan tare muka fito daga masallaci muna cikin tafiya na waiga ban ganka ba."


Kollon sa AFREED yayi ya sakar masa murmushi kawai sannan ya buɗe motar ya shige, mamaki ne ya cika Ali kamin shima ya buɗe mazaunin direba ya shiga tare da tayar da motar yaja suka tafi.


A hanya sai sakin murmushi yake shi kadai, Ali ya juyo ya kallesa da mamaki yace "Wai AFREED lafiya kake kuwa naga sai sakin murmushi kake kai ɗaya ko wani abun ne ya samu."


Lumshe idonsa yayi tare da sakin ajiyar zuciya sannan ya buɗe su kan Ali yayi fuska kamar ba shine yanzu ya gama sakin murmushi ba sannan yace "Kai Ali sa idonka ya min yawa, toh sai da wani abu zan dinga murmushi ko baka taɓa gani na ina murmushi bane, har kake son damuna da tambayoyi???"


Juwowa Ali yayi ya kallesa kamin ya maida hankali sa ga tuƙi sannan yace "Hum in tayi wari munji."


Shiru AFREED yayi ba tare da ya tanka masa ba, sai lumshe idonsa da ya komayi kamar mai bacci tare da kwantar da kujerar sai ya ɗan gincira har suka kai kida yana a haka kamar mai bacci alhalin bahaka ba ne, kawai ya faɗa duniyar tunanin ta ne.


Suna shiga gidan Ali na gama parking ya buɗe motar ya fice, direct ɓangaren su ya nufa ba tareda yayi ɓangaren tanti Aicha ba, Ali na ganin haka a ransa yace "To mike damunshi ne har haka? sai kuma yace bari naje tanti taga dawowar mu sai naje na tambaye shi ko mike damunsa."


Yana shiga falon babu kowa, sai Khadijah ita kuwa tana jin ƙarar buɗe ƙofar ta ɗago dan ganin ko waye ya shigo aiko sai idanuwansu suka sarƙe cikin juna, murmushi Ali ya sakar mata yanajin wanda soyayyarta ke ƙara shigar sa, a zuciyarsa yace "Yakamata na fito na faɗa mata abinda ke raina kada wajan kallon ruwa kwalo ya mani ƙafa, idan haka ta faru kuwa bansan ya zanyi ba, sabida ba ƙaramin so nake mata ba."


Ƙarasawa yayi gun datake zaune shima zama yayi kan kujerar dake kallon tata, ita kuwa tun shigowar sa da suka haɗa ido tayi saurin duƙe kanta ƙasa bata sake ɗagowa ba har yazo ya zauna sannan tace cikin siririyar muryar ta "Yaya ina wuni, barka da juma'a." Ta faɗa ba tare da ta ɗago ba.


Kallon ta yake yana murmushi batare da ya amsa ba, jin shiru yasa ta ɗago dan taka ko bai jita bane, aiko sai take idanunta suka sauka cikin nashi, dam dam gabanta ya faɗi, da sauri ta ɗauke idanunta daga nashi tare da duƙe kanta, a zuciyarta tana cewa "ko dai yaya Ali ya naji abinda nakeji game da shine idan ko haka ne da naji daɗi."


Bata ƙarasa tunanin ta ta tsintsi muryar nacewa "Khadijah zaki iya aure wani garin ki bar maraɗi?"


Kamar daga sama taji tambayar tashi da sauri ta ɗago ta kalleshi suna haɗa ido ta sune kanta ba tareda tace komai ba amma cikin zuciyarta ta sai tace "Mizai hana yaya idai kaine mijin zan iya barin maraɗi na zauna duk ida kake, wani ɓangaren na zuciyarta yace kenan zakiyi iya tafiya ki bar mamanki da dadyn ki?" Atake kuma jikinta yayi sanhi.


Ali ya ɗan nunfasa yace "Khadijah tambayar yaki nake, ko bakiji minace ba?"


Cikin bugun zuciya ta buɗe bakinta ta ce "Ta ni yaya banda zaɓin kaina sai na Allah, idan Allah ya tsaro rayuwa ta akan zan bar garin nan ta dalilin aure to j'ai pas la choix, Ubangiji shi ne yasan daidai, kuma shine kan daidai ni ina farin ciki da duk inda Allah ya ajiye ni."


Wata ɓoyaya ajiyar zuciya Ali ya sauke sannan yace "Alhamdulilah hakane kuma ƙanwata kinada gaskiya to bani labarin samarin dan ni tunda mukazo nan ban taɓa ganin kinyi fira ba ko miyasa, ai yakamata ace yanzu aure za'ayi maki dan kam yanzu kin girma."


"Lah yaya saurayi kuma ni yaya banida wani saurayi dady bai barin mu kula samari kuma ni banda wannan ma duk a nawa nike da zan fara wani kula samari," Khadijah ta faɗa cikin shagwaɓar da ba tasan tayi ba.


Shagwaɓar da tayi ba ƙaramin tafiyar masa da imani tayi ba, a zuciyarsa wani farin ciki ne ya luɓeɓe sa jin cewa babu wanda yayi masa rigagin shiga zuciyarta, dan haka yanzu yanzu ba sai anjima ba zaiyi mata bayanin abinda kecin ransa, gyaran murya yayi ya ƙara gyara zaman sa tare da maida hankalinsa sosai akanta yace "Ƙanwata kinason na zaki aure ni."


Duk da abinda Khadijah keson jine ya fito daga bakinsa, sabida son da take masa amma haka bai hana gabanta faɗuwa ba, cikin sauri ta ɗago da niyar satar kallon sa aiko se idanunsu suka sarƙe cikin juna, da gudu ta tashi ta nufi sama tana murmushi direct dakin su ta nufa.


Shikuwa Ali baiyi ƙoƙarin tsayar da itaba sabida yasan dole zai bata lokaci tayi tunani, amma sosai ya cika da farin ciki sabida ganin hakan ma da tayi ya nuna masa ta amince da tayinsa, a fili ya furta "Alhamdulilah yaudai na faɗa mata Allah na gode da kabani ƙaurin gwiwar bai yana abinda ke raina." Murmushi ya saki tareda tashi ya bar gun shima ya nufi ɓangaren su.


Khadija na shiga ɗaki ta tardo Fariya da Farisa zaune saman gado suna fira suna dariya kana ganin su zaka gane cewa firar da suke suna jin daɗin ta, da gudu tayi wajen su ta faɗa tsakansu tare da rungume su tana dariya, kamin ta ɗan sassauta rungumar da ta masu tana kallon ɗaya bayan ɗaya, suma ita suke kallon cike da mamakin miyasa ta farin ciki haka, dan daga ganin yanayin aikasan tana cikin farin ciki mara misali, ganin mamaki ta suke kuma sun kasa cewa komai, kawai sai tajuyo ta sakesu baki ɗaya ta zaune tsakiyar su sannan tace "Sisters albishirin ku," Khadijah ta faɗa tana murmushi.

Haɗa baki sukayi da sauri wajen cewa "Goro" cike da zaƙuwar jin wane albishirin ne tazo masu dashi.


Sai ta ce "Fari ko ja?"


A tare suke cewa "Fari tass sœurette dan Allah yi sauri ki faɗa mana har mun ƙagu muji ko miye."


Tsalle tayi ta sauka daga saman gadon ta juyo ta na fuskantar su har yanzu dai murmushi ɗoke a fuskarta tace "Yaya Ali ya tambaye ina son shi zan auresh...... bata ƙarasa faɗar abinda tayi niyar faɗa ba sukayi tsalle suka sauka daga gadon tare da yowa kanta suka rungume ta su duka biyu har suna dariya da murnar jin wannan labarin har saida suka kai ƙasa da tsanani farin ciki da rungumar da suka ma juna, na saman kafet ɗin dake ɗakin suka faɗa tare dayin zama dirshan suna maida numfashin murna.


Fariya ce tayi ƙarfin halin buɗe bakinta dan sun kasa ma yi magana dan tsanin farin ciki tace "Wayo Allah sœurette Khadijah zata koma Niamey da zama zatayi aure garin mu tana yiyuwa ma a kusan gida zaku zauna ko a gidan mu ɗin dama ba tun yau nakeso kikoma gidan mu ba amma na kasa samun hayar da zaki koma ɗin, yanzu dai gashi yaya zai mayar mana dake weeeeeee tayi ihu mara sauti sosai tare da daka tsalle farin ciki sannan ta koma ta zauna da murmushi kwance a fuskar ta tace "Alhamdulilah."


Ita kuwa Farisa sai ta kamo hannuta na dama da duk hannayenta tace "Anty Khadijah to ke mi kikace ma yaya da yace maki hakanan injin dai kin amince?"


Murmushi tasaki tace "Ah har na koma antyn kenan, ashe duk zakuyi farin cikin hakan, kenan kuma kuna so na auri yaya Ali, kun san mi nima sosai na faɗa soyayyarsa a zuciyata amma ai kunsan da haka dan ba tun yau nake faɗa cewa ina son ba amma na kasa faɗa masa sai gashi shi da kansa ya furtamin hakan, amma ni bance masa komai ba yana min tambayar na ji kunya na gudo ɗakin ban tsaya ba."


Fariya tace "Ina ai dole ne ki koma anty tun yanzu, kuma hakan da kikayi shine daidai dama ba daga mutum ya faɗi yana sonka ba kake ce masa ka amince ba, hakan da kikayi ya nuna masa da amincewar taki yanzu kawai ya kamata tanti A'isha taji wannan dadaɗan labarin, dan a faɗa ma dady sai a saka ranar auren nan da yuri kokuwa Farisa?" Fariya ta tambayi Farisa tare da kallon ɓangaren da take zaune Farisa tayi saurin ɗaga kanta alamar eh ta na murmushi.


"Ah kijimin Sisters ɗin nan kawai daga magana kuma sai shirya aure ai kun bari har mu ƙarasa daidaitawa kamin akai maganar ga manya mana, wannan sauri haka kamar dai kune angon."


Murmushi sukayi sannan Farisa tace "Ah to mi za'a jira? Batun daidaitawa kuma ai kun riga da gun daidaita tunda kun daɗe da soyayyar juna a cikin zuciyar ku dan nasan yaya Ali ba tun yau bashi ma yake sonki baide faɗa ba ne dan haka mu alkairin abin kawai muke nema."


Fariya tace "Lale dai kama Allah sanya alkairi kawai zamuce yanzu ku tashi muje mu ci abinci sai mu dawo mu zauna mu fara tsara yanda bikin nan zai ƙayatar da yardar Allah."


Da ameen suka amsa sannan suka miƙe suka fita a ɗakin.


*****. ******. ******. ******


Ali na shiga ɓangaren su ɗakin AFREED ya nufa, tardo shi yayi kwance ya lumshe lumsashin idanunsa kamar mai bacci da murmushi kwance a fuskar sa, ba tareda yaji shigowar Ali ba sabida faɗa wa da yayi duniyar tunanin, saida Ali yace "frèro waini yau wane irin farin ciki ne kake ciki haka da kakasa sanarmin ne har yaushe ka fara ɓoyemin abinda ke damun ka?"


Ahankali AFREED ya fara buɗe idonsa kamar me tsoron idan ya buɗe su zaiga wani abin tsoro ko abin ƙi, ya sauke su kan Ali cikin kwanciyar hankali ya miƙe zaune yace "Ali kenan babu abinda nake ɓoye maka kawai dai nima yau tunda na farka na tsintsi kaina cikin wannan farin cikin da bansan dalilin yin sa ba kada ka damu kaji ɗan uwana idan da wani abu ai zan faɗama kaima kasani."


Ali yace "To shikenan nikam nazo maka da wani albishir mai daɗi."


"Dagaske ɗan uwa to faɗa man naji." AFREED ya faɗa cikin zaƙuwa.


Ali ya gyara zaman sa sannan yace "Yaudai nasamu na faɗa wa Khadijah cewa inason ta zata aure ni."


Waro ido AFREED yayi yace "Lah wai Ali da gaske kake kenan, yau ka samu ƙarfin halin faɗa to ya tace maka ita?"


"Batace dani komai ina faɗamata ta rufe fuskarta tana murmushi se kawai tayi saman da gudu, hakan na nuna min ta amince, tunda ba zata fito ta faɗa min hakan kai tsaye ba, kasan halin mata da alkunya."


AFREED yace "Hakane ɗan uwa ina taya ka murna sosai naji daɗin zancen dama ba tun yau nake cewa ka faɗama ta tun kafin wani ya riga ka amma tunda ta amince yanzu dai ya kamata kafin mubar garinan tanti Aicha tasan da zancen tunda kigin kwana biyar mu bar garin, kabari ni zan faɗa mata, ita kuwa sai ta sanarma dady."


"Eh haka za'ayi ɗan uwa."


Ali bai ida rufe bakinsa ba akayi sallama tareda turo ƙofar ɗakin AFREED Umar ya shigo, amsa masa sallamar sukayi kafin ya ke ƙarasowa gun da suke shima ya ne mi guri ya zauna sannan yace "Yaya AFREED wajanku nazo ku duka Allah ya taimake ni kuna tare, nazo ne muyi wata magana mai mahimmanci Allah yasa dai zaku goyi bayana kuma kusamin hannu ku masu albarka."


Murmushin shi mai birgewa yasaki sannan yace "To muna jin ka Umar ai tunda naji kace min yaya yau nasan da abinda zaka faɗa yanada mahimmanci, to faɗi muna sauraran ka idai maganar Allah da Annabi ce mizai hana mu saka maka hannu."


Ali yace "Sosai kam mu masu baka goyon baya ne akan komai idan dai bai saɓa wa Allah ba."


Murmushi Umar ya saki tareda sosai kansa sannan ya duke kansa yace "Yaya AFREED yaya Ali dan Allah ku taimaka ku bani auren ƙanwata kuma masoyiyata abar ƙauna ta Fariya ku taimaka ku min rai ba dan niba sai dan Allah, kuga dai kam ina da halin kwarai kuma zan riketa amana wallahi ba za'a samu matsala ba insha Allahu." Sai yayi shiru daganan yana jiran jin abinda

Please Login or Register in order to submit comment