Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai sai ya tashi ya nufi toillet ya dauro alwala ya fito, shimfiɗa darduma yayi ya fara jero nafilfili ya na kai wa Allah kukan sa cikin ikon Allah ya samu sasauci sosai daga abinda ya ke ji a zuciya sa, shine bai samu bacci sai wajen ƙarfe 4:00 sannan bacci ɓarawo yayi awon gaba dashi, kuma cikin ƙananan lokacin kiran sallah asuba ya farakar dashi cike da magagi bacci dake cinsa ya tashi ya shiga bayi ya watso ruwa a gaggauce saboda yaji ana shirin tayar da sallah ya na fitowa ya zura jalabiyar sa fara ya nufi masallaci, a ƙa'idar AFREED idan an idar da sallah asuba bai baro masallaci sai rana ta fito, amma ana gama sallah tare da yin adu'oin sa na bayan sallama daga sallah kawai ya taso yayi tafiyar sa cikin gida ba tare da yayiwa ko da dady ina kwana ba, hasali ma bai ma lura dasu ba har Ali dake kusa dashi, bacci kawai yake son yaje yayi, da mamaki Ali ya bishi da kallo, a zuciyar sa yace "To shi wancan lafiya kuwa ko dai duk soyayyar ce?"


Murmushi kawai Ali yayi tare da girgiza kai yace "Sabon shiga dole ne ya kasa controlling ɗin kasa." Sannan ya juya ya ci gaba da addu'ar sa.


AFREED na shiga ɗakin sa ya faɗa saman gadon sa ya shiga rankon bacci shi ne bai farka ba sai wajen 11 na rana yana tashi yayi miƙa tare da salati sannan ya faɗa toillet ya yi wanka ya fito ya shirya cikin shirin sa na tafiya office yayi kyau sosai saboda irin masu jikin nan ne wanda komi ka saka ya yi ma kyau, fitowa yayi a gaggauce saboda yayi latin zuwa aiki gashi har sha biyu na rana ya kusa tunda yau juma'a sauka guda sukeyi sai sun kai har ƙarfe ɗaya da rabi na rana a office, da sauri ya shiga ɓangaren maman shi ya gaida ta sannan ya cema "Ali ya tashi su wuce office." Ali da yake a shirye shi kaɗai kawai yake jira ya miƙe ya nufi ƙofa shi ma ya biyo bayansa,


Momy ha sun kai ƙofar falon Momy tace "Ba zaka ƙarya ba zaka fita."


Yace Momy zanyi idan na dawo."


"A'a wuce ko thé (🍵) ne kasha babu kyau fita ba'a ci komai ba."


Ba musu ya nufi dinning inda Momy har ta riga sa kaiwa ta haɗa masa thé (🍵) ta miƙa masa ya ƙarɓa ya sha sannan ya fice daga falon wanda Ali har ya kai gun motar shi kaɗe yake jira yana fitowa garde corps (Bodyguard) dinsa suka miƙe tare da nufar motocin su don kowane group da motar sa su wajen goma sha biyar, a cikin kowace mota da mutun biyar a cikin ta sai mota da AFREED ke shiga shida Ali da direban sa a ƙala suna fita da mota huɗu ko biyar wataran har bakwai, da sauri suka shiga gaida sa, su sunyi tunanin yau Bama za'a je wajen aiki ba tunda sun ga rana tayi.


Cikin ƙananan lokaci suka isa ma'aikatar tasu ana gama parking yayi saurin buɗe ma kansa ƙofar motar ya nufi ciki da sauri suma Bodyguard din suna ganin haka suka mara masa baya da sauri wanda shi Ali har ya riga da ya cin masa, haka kuma ya shige gabansa da sauri ya buɗe masa office ba tare da ya tsaya watawata ba ya faɗa office ɗin da sallama a bakin sa, direct kujerar zaman sa ya nufa ya zauna nan take, shi ma Ali ya nemi kun zaman sa ya zauna ya tsura masa ido bai ce masa komai ba dan yasan duk wannan saurin da yake dan yayi lati ne kuma gashi an kusa tashi, AFREED ya shiga duba file ɗin dake gabansa cikin kwanciyar hankali ya fara aikin da ya tarar masa saboda jimawa da ya yi bai je office ɗin ba, ciki minti 40 ya kammala komai da komai a sannan yakai hannun sa kan téléphone☎️ ɗin dake saman table ɗin ya dana kira,
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸




Écrit




Par




*QUEEN ZEEFAT*




_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_




*Wattpad@nazichou*





*_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_*



*Page :* 53 & 54


"Tana fara rigin aka ɗaga a takaice yace "Amina ki zo office ɗin nan yanzu." Bai jira jin abinda zata faɗa ba ya katse kiran tare da ƙara duba file ɗin dake riƙe da hannu sa. Ko minti biyu ba ayi ba da katse kiran sai gashi ta kwonkwosa Ali ya bata izinin shigowa sannan ta buɗe ƙofar ta shigo da sallama, duk kansu suka amsa sallamar amma sai dai shi AFREED in ba kusan sa kake ba ba zakaji ya amsa ba, sannan ta gaida shi ya amsa sabida da ya shigo yana sauri bata samu damar gaida shi (wato Amina secrétariat ɗin AFREED ce)


Cike da ladabi ta ɗan gusa kusa dashi tare da yi kasa da kanta kaɗan tace "Yalaɓai gani."


Ba tare da ya kalle ta ba ya mika mata file ɗin dake ga hannun sa ta karɓa sannan yace "kije bureau ɗin ministre (minister ) Aliyu ki kai masa kice injini, idan hali gobe nakeso ya dawo man dashi."


"D'accord chef."


Sannan ta juya ta fita a office ɗin, sai a wannan lokacin ya ɗago ya dubi Ali ya sakar masa murmushi sannan yace "Ɗan uwa mu koma gida na riga na kammala abinda ya kawo ni."


Murmushi shi ma Ali ya mayar kamin yace "To muje ai naga yi baka da dama shiyasa ban takaka ba har ka ida."


AFREED ya yi murmushi yace "Wallahi kuwa amma yanzu tunda na ida ai shikenan."


Daga haka suka miƙe suka nufi kofa suka fice daga office ɗin basu tsaya ko'ina ba sai gida.


Ɓangaren AFREEN kuwa ta kasa gane kanta saboda tunda safiyar Allah ta waye take ta riƙon wayar ta ko zata ji AFREED ya kira amma shiru, haka rashin kiran nasa ya dame ta har zata zauna ta na tunanin yaye inta shi da ta damu dan bai kira ba daga fara kiran ta jiya, sosai hakan ya bata mamaki, amma kuma sai ta basar


AFREEN har ta fida rai da AFREED zai kirata sai ga kiran nashi ya shigo wajen ƙarfe 4 na yamma bayan sallah la'asar waya na ta rigin tana kallo bata ɗaga ba kamar dai ba kiran take jira ba, sai ga kira na biyu shima yana gab da katse wa ta ɗaga tare da yin sallama AFREED najin ta ɗaga saida ya sauke wata irin ajiyar zuciya mai sauti har sai da taji dan shi ya ma fida rai da zata ɗaga.


Amsa mata sallama yayi, kamin ya koma cewa wani abu tace "Ina yuni?"


Wani farin ciki ne AFREED yaji ya luluɓe don kawai sai yaji yau ya kira cikin sa'a sabida kamar yaji maganar ta cikin sakin fuska, saida ya saki murmushi kamin yace "Lafiya klau" da fatan kin yuni lafiya kuma kina cikin koshin lafiya?"


Ƙasa ƙasa ta amsa da "Lafiya lau"


Yace "Ya gida ya su maman da kowa da kowa"


Ta amsa da "Alhamdulilah"


Nan dai suka ɗauki kusan minti biyar bawanda ya ƙara cewa komai amma zuciya AFREED sai bugawa take da ƙarfi fat fat fat yana tsoron ƙara mata maganar soyayyar sa ta ƙara fashe mashi da kuka can yayi ta maza yace "AFREEN dan Allah kiyi tunanin kan maganar da nayi maki jiya wallahi ina matuƙar sonki idan har kika ƙini zan shiga wani hali ki taimaka dan Allah."


Kusan kamar second talatin bata ce komai bai sai kuma tace "Inshallah zanyi shawara a kai."


"Zuwa yaushe zan samu amsar?"

"Nan da sati haka, ko yayi kaɗan?"


"Ki taimaka AFREEN wallahi sati ya yi min yawa ina laifin kice anjima."


"Ina anjima ya yuri gaskiya, ai ko tunani ban fara a kai ba."


To dan Allah ki tausaya wa rayuwa ta AFREEN kice gobe."


Saida ta ɗauki kusan minti ɗaya batayi magana ba kuma sai tace "To shikenan amma goben sai da dadare in ka yarda."


"To shikenan ba damuwa Allah ya kaimu goben lafiya."


Ya samu saken biyu bai ce komai sai kuma yace "Dan Allah zan iya kiran yau da dadare mu ɗan yi fira?"


Saida tayi ɗan jim kaɗan tace to ba laifi amma ba da dare ba sosai."


"To shikenan an gama ranki ya daɗe yanda kika ce haka za'ayi sai na kiraki ɗin."


Saida tayi ɗan gajeren murmushi sannan tace "To ba damuwa."


"Ki gaida ƴan gidan."


"Za su ji insha Allahu."


Sannan ya katse kiran cike da farin ciki yaje ya samu Ali ya sanar masa yanda sukayi da ita nan take shima ya taya shi farin ciki."


Kamar yanda yayi mata alƙawari dare bayi ba sosai ya kira ta bayan anyi sallah isha suka dan taɓa hira ta kusan minti arba'in sannan yayi mata saida safe, haka ga goben ma yayi mata kira uku kamin na dare, dare nayi ya kirata kamar yanda ya saba bayan anyi sallah isha, nan suka gaisa ya tambaye ta alƙawarin da tayi masa na bashi amsa yau, bata wani bata lokaci ba ta ce masa ta amince, farin ciki kamar ya kashe AFREED a ranar jiyake bai taɓa shiga farin ciki irin na wannan ranar ba nan suka shiga fira soyayya mai ratsa zuciyar masoya, da yake AFREED ba gwani bane wajen gayin kalaman soyayya tunda bai ta yi ba amma duk da haka ya ƙoƙarta sun sha soyayyar su harda dare yayi sosai sannan suka yiwa junansu sallama badan sun so ba, sai dan lokacin sallah dare da AFREEN keyi yayi, tunda ga wannan ranar soyayya mai tsanani ta shiga tsakani AFREEN da AFREED dan ko basu awa ɗaya basu ji muryar juna ba.


Kwanci tashi babu wuya a wajen Ubangiji yau yakama saura kwana guda auren Khairat kuma yau ne dadyn AFREED da docter Inusa zasu zo Maraɗi dan su halarci ɗaurin auren diyar aminin su wato Alhaji sadisu da ake yi gobe misalin ƙarfe takwas na safe.


Sun baro garin Niamey ƙarfe tara daidai amma da yake mota personnel ce ƙarfe huɗu nayi su na cikin garin maraɗi, a wani gida injiniya Sumana dake cikin anguwar Zaria, gidan ko ina a share a gyare kamar dai da mutane a ciki, ba su wani ɓata lokaci ba sukayi wanka suka huta, sai ga kiran Alhaji Sadisu ya shigo wayar injiniya Sumana yana tambayar su har yanzu basu ƙarso ba, yace masa su ji ma da ƙaraso wa dan sunyi har wanka sun huta, nan ya tambaye sa inda suke ya sanar da shi sannan Alhaji Sadisu ya ce gashinan zuwa ya ɗauko su zuwa gidan sa tare, da an riga da anyi abincin tarbar su bansu, ba tare da sunyi musu ba suka amince, kusan minti ashirin da gama wayar sai gashi yazo basu wani bata lokaci ba suka kule gidan tare da da shiga motar Alhaji Sadisu suka ɗauki hanyar gidan sa wani minti ashirin ɗin suka ɓata kamin suke isa gida, direct ɓangaren Alhajin suka nufa, suna shiga suka sauka saman mayan kujerun da ke falon daga nan suka ƙara gaisawa, sai ga uwan gidan suna shigowa da ɗaiɗaya suna gaisawa, nan fa aka fara servir ɗin su aka cika falon papa da kayan ciye ciye da lashe lashe kamar sunzo restaurant daga ƙarshe AFREEN ta shigo da sallama da juice 🥤 ɗin gwaba da yaji kayan haɗin sosai sai kamshi yake a hannun ta daga ji kasan zai yi ɗaɗin ɗanɗano, ciki shigar ta ta ƙaton hijabi har ƙasa tana shiga ta duka har ƙasa ta gaishe su da ladabi kan ta a duƙe."


Kallo injiniya Sumana ya bita dashi sannan ya amsa gaisuwar ta, sannan AFREEN ta mike ta fice, tana fita injiniya ya kalli Alhaji Sadisu yace "Alhaji wannan ma yarinyar Arahamat ce ko saboda ga kama nan masha Allah kyakkyawa da ita har ta fi maman ta, se kuma ta ɗauko kalar fatar ka ba tayi hasken mahaifiyar ta din ba, ni ina tunanin daga Khairat Arahamat bata da wata yarinyar sai in maza ashe akwai wannan."


Murmushi papa yayi kamin yace wani abun docter Inusa yace "AFREEN ba ɗiyar jannah kenan ai yanzu da muka yi waya da ita take ce min dan Allah idan zan dawo na zo mata da yara ta wato AFREEN."


Wani murmushin papa ya koma yi sannan yace "Ai jininsu ya haɗu da jannah sosai fiye da yanda kake tsammani."


Injiniya Sumana yace "Hakane yanzu nan zata iya yin wata shawara da jannah bata yi ta da mahaifiyar ta, amma nikam da za'a ban ita na bawa yaron nan AFREED, da ya kasa fitar da wace ya keso gashi nan kannin sa har saura wata biyu auren su so yake sai ya gama zama tuzuru nasan ko zaiyi auren, yaro sai taurin kan tsiya babu wanda banyi ya fitar da wace ya ke so ba ya ki ko dan a saka masu rana ɗaya da yan uwansa amma yaki." Dady ya fada dan ɓacin rai kaɗan a fuskar sa


Murmushi Alhaji Sadisu yayi sannan yace "Ai kam da nayi farin ciki idan hakan ta faru zumunci mu zai ƙara ƙarfi sosai, ko maman su nasan da sai tayi farin ciki sosai da hakan kuma Allah sa alkairi ne zamu haɗa."


Docter Inusa ma murmushin ya yi kamin yace gaskiya hakan kuwa abu ne me kyau, kuma insha Allahu alkairi ne gashi ma sunan yaran nawa kusan irin ɗaya ne AFREEN da AFREED kamar wasu yan tagwaye kuma dukan su akwai hankali da nutsuwa sosai a tatare da su daga gani zaman su zai yi armashi insha Allahu, sedai wani hanzari ba gudu ba ya kamata Ku sanar dasu ko sun amince ba auren dole zaku masu ba, dan ba kusan ko wani daga cikin yana da wanda yake so gaskiya a basu zaɓi."


Da sauri injiniya Sumana yace "Ko alama bazan sanar da AFREED komai ba sedai ya ga amarya komai nine zanyi dama na faɗa masa idan har ya yarda ya kaini bango zan nema masa matar da kaina, gashi kuma yanzu na samu yarinya mai hankali da tarbiyya ɗiyar aminina ai babu abinda zai hanani yi masa auren nan, sedai in ita yarinyar ce bata so ko kuma tana da wanda take so nan babu wanda ya isa ya mata dole wallahi ni ne nan zan tsaya mata har sai an aura mata wanda take so." Nan ranshi a ɗan ɓace ya ida maganar."


Alhaji Sadisu yace kwantar da hankalin injiniya insha Allahu haɗin zai yiwu kuma zai zama alkairi da yardar Ubangiji, duk da banjin cewa AFREEN na da wani sauri bayan wancen, da har bata faɗa min ba amma zan tuntuɓe ta, kuma zan faɗa maka shawara da na yanke daga nan idan ta amince sai muyi abinda ya dace dan nasan zata min biyayya insha Allahu.


Farin ciki gun injiniya Sumana ba'a magana kamar ance masa yarinyar ta amince ko kuwa gashi har an kaita gidan sa a matsayin matar AFREED, shima docter Inusa ya nata farin ciki kamar wata ɗiyar sa.


Daga nan suka sauka saman kafet suka fara cin abinci, sosai suka ci suka koshi, suka yi hamadah tare da ci gaba da fira su, sai wajajen ƙarfe goma na dare suka yiwa papa sallama suka kuma ma sauƙin su duk da babu yanda papa bayi ba su kwana a gidan suka tare da cewa haba Alhaji kai baka ga yanda baƙi suka cika gidan ba mu koma masaukin mu zai fi gobe in Allah ya yarda zamuyo samakon ɗaurin aure, haka suka ɗauki motar aminin na su suka tafi da ita,


Washegari tun ƙarfe biyar kowa na gidan sai shirin ɗaurin aure suke, kamin karfe takwas tayi har kowa ya shirya ga gidan ya cika makil da yan ɗaurin aure, waje ko hanyar yucewa babu sai ka ɗan karkata kamin kasa mu shi ga gidan iyayen gidan mata gaba ɗaya sunci shiri cikin wasu narkakun shadadodi na ganin na faɗa kana gani kasan a kashi kuɗi a wajen nan, haka yaran gidan su ma da kalar tasu shadar mai mugun tsada.
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸




Écrit




Par




*QUEEN ZEEFAT*





_Ƴar_
_Mutun_
_Niger_



*Wattpad@nazichou*



_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_



*Page* : 55 & 56

Sai kam ta AFREEN da tafi ta kowa haɗuwa dan ko ta iyayen nasu sai tayi saboda son da Alhaji Sadisu ke yiwa AFREEN ya saka komai na ta daban yake a gidan ta fito ta yi shar da ita, kamar wata matar shugaban kasa, kowa sai yaba kyaun ta da mamakin irin wannan kyau na ta mara misali, sai mutane ke mamakin kyau irin na AFREEN Ita dai tafi mahaifiyar ta kyau nesa ba kusa ba amma kana kallon ta ka san ita ta haife ta sabida suna ɗan kama sedai maman ta ta fita haske sosai, kalar fatar mahaifinta ta ɗauko mai ɗan duhu da sheƙi da haske wanda ba za'a iya saka ta a layin farare ba, sai ƙwayar idon ta dake kalar chocolat color amma cikin su fari tas ne mai walk'iya da ɗaukar ido har da ɗan ƙaramin baki da surcecen hanci har baka masha Allah.


Ƙarfe takwas daidai duban jama'a suka shaida ɗaurin auren Khairat Alhaji Sadisu da angon ta Ahmed sufiyane bisa sadaki 100000F CFA, kamin kace mi labari har yaje ga kunnan Khairat wace ana gayama ta, tayi hamdalah ga Ubangiji a cikin zuciyar ta, taron ɗaurin aure ya watse lafiya ida aka maida taron yinin biki, Alhaji yana cen kofar gida cikin inuwa wata babba bishiya tare da abokansa kusan su goma suna ta fira su cikin farin ciki.


Biki ya yi biki ida aka shirya amarya cikin wani haɗaɗan lace marron ta haɗu har ta gaji da haɗuwa, nan fa aka fitar da ita babban falon gidan ana ta photo, nan su AFREEN an shirya cikin wani haɗaɗan matériel blue 🔵 sai sheƙi yake mutane na ta photo da ita kamar ita ke amarya.


Ƙarfe takwas daidai na dare aka tafi kai amarya gidan mijinta ta sai wajen tara da arba'in yan kan amarya suka dawo, masha Allah taro ya watse lafiya sai fatan zaman lafiya tsakanin ango da amarya.


A gajiye su AFREEN ƴan kai amarya suka dawo gida, direct ɗakin ta nufa ta faɗa toillet ta yi wanka tare da ɗauro alwala ta zo ta gabatar da shafa'i da wutiri sannan taje gan mirror ta ɗauko wayar ta kashe tun farkawar ta da asuba bayan tayiwa AFREED Barka da safiya ta kashe ta ɗan ta samu tayi bikin ƴar uwar ta hankali kwance da nutsuwa.


Wata ranar asabar da dadare ya kama sati uku kenan da ɗaura auren Khairat bayan ƴan gidan su gama cin abincin a dinning baki ɗaya suka koma falo, suna ta fira hada mai gidan wato mahaifin su AFREEN a nata wasa da dariya, sai papa ya miƙe ya masu saida safe ya nufi saman shi da yake maman su AFREEN ke aiki bayan kamar minti goma sai ita ta mike ta bi bayan shi, sannan AFREEN itama ta nufi nata ɗakin., Haka da ƙaɗan kaɗan kowa ya watse ya nufi ɗakin shi a ka bar falon tsit tunda kowa ya kama gaban sa.


Maman na shiga falon papa ta sameshi a saman kujera a zaune yana nazarin wani abin ya yi tagumi, da sallamar ta shiga ya ɗago ya dube ta sannan ya amsa sallamar tare da sauke ajiyar zuciya, kusan shi ta zauna tare da riƙo hannun sa ta saka cikin nata hannun tace "Mijina na lura da akwai abinda ke damun ka kasa faɗa min dan na lura da maganar da kake son faɗa nice kake son gayama amma kaki samun courage ɗin sanar dani, kasani babu abinda muke boyewa juna koma miye kada kaji shaƙar sanar dani komiye saboda a ƙarƙashin ka nake kuma kana da iko dani gara ka faɗa dan tun yuri musan abunyi idan kuwa umarni zaka bani duk wannan ka cenci haka, saboda tun bayan auren Khairat na lura da akwai magana a bakin ka Alhaji na ka daure ka sanar dani ko nima hankali na zai kwanta."


Saida papa ya sauke wata ƴar gajeriyar ajiyar zuciya sannan yace "Allah kuwa kamar kin shiga zuciya ta ɗan ina shaƙar sanar dake abinda ke raina gaskiya, amma ba komai yanzu tunda kince haka bari na faɗa maki," sai da ya gayar zaman sa sannan yace "Ba wani abu bane nakeson sanar dake ila ina son faɗa maki cewa nayi wa AFREEN miji wato ɗan gidan injiniya Sumana in ba zaki manta yaron sun taɓa zuwa gidan shida ɗan uwan sa wanda lokacin haihuwar sa kema kin halarci sunansa in bazaki manta to shine nakeson sanar dake narasa ta kowace hanya zanbi dan Kada kice na yanke hukuncin aurar da ɗiyar mu, ban sharwace ki ba dan maganar da nake maki har mun saka rana auren sani da yaya na Adamu da Dr Inusa se kuma shi mahaifin yaron Alhaji Sumana mun tsayar da wata biyu, ida yau yayi saura wata ɗaya da sati ɗaya, dan kuwa tun zuwan su bikin Khairat mu ka saka wannan ranar idan ki ka yi lissafi zaki ga hakane."


Maman seda ta ɗauki kusan minti biyar bata ce komai ta tsurawa papa ido tana nazartar sa sannan ta sauke ajiyar zuciya tace "Allah ya sa haka shi ne ma fi alkairi, tsoro na ɗaya shi ne in ba mijina ne ya fara nemawa ƴarsa auren ɗan su ba dan gudu ka su dinga mata kallon matar cushe, kuma kada ace ganin ana ta saka ranar aure ta ana fasawa ya saka shin yin haka ko a ganin shi ba zata samu wani wanda zai aure ta ba amma in dai babu ko ɗaya a cikin to ni ina farin ciki da hakan, kuma Kanada incin zaɓawa AFREEN miji sabida ɗiyar ka ce kai keda hakki da ita ba wani ba."


Murmushi Alhaji Sadisu ya yi ya ƙara riko hannun ta dake cikin nashi kamin yace " Allah maki albarka Allah ya biyaki da gidan aljanna sosai har yau har gobe bani da kamar ki a cikin mata na Allah ya biya ki da mafificin alkairi, sannan batun na cusa masu ita ko tunani zata rasa mijin aure ko ɗaya babu hasali ma shi ya fara kawo man magana kan yana son a yi haɗin zumunci, dalilin ganin AFREEN da yayi lokacin da tazo kawo mana ruwa ga ranar da suka zo ya nuna min yana son yaron da ita. Da wasu hujoji da ya sanar min ya saka na amince."


Itama murmushin ta mayar masa sannan tace "To shikenan Alhaji na Allah ya sa alkairi ku ka haɗa sedai ku sanar masu dan Kada ku shiga hakkin yaran ku dan ita dai nasan ba zata ƙi yi ma biyayya ba."


Papa ya amsa da ameen tare da cewa insha Allahu zuwa gobe zan sanar mata dama abinda yasa ki kaga

Please Login or Register in order to submit comment