Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

(stairs) dan zuwa dakin ta, umma ta karaso ta zauna kan kujerar da papa ke zauna, tare dacewa "yo shalelan taka tafiya tayi ta barka, dagowa yayi ya kaleta ba tare da ya ce mata wani abuba ya maida kalon sa a tv, ta koma cewa " hada wani kicihin biyu yarinya falo wai ita yar so, "du ba kai ke daure mata gindi ba tana abinda take so nan ma baice mata komi ba hankalin shi ma bai wajan ta, take umma ranta ya bace tace "kar dai mukaga lega wlh, adai juri zuwa rafi watarana tulun zai fashe. "Wato baban fauzia nice na ke maka magana kana shareni sabida 'yar zinariya ko, wato kenan ga mahaukaciya wada batada hankali tana magana ana shareta to alhamdulilah watarana za'aga ranar magana ta.

Tanti yara dake tsaye tana sauraren abinda umma ke gayi tace "haba Salamatou miye abin cika mutane da surutu kamar an jonaki kinyi magana d'aya kinyi biyu an shareki, to miyasa bazaki hakura da zancan ba kinata nanata abu d'aya, du kinbi kin takurawa yarinya da bata maki komi ba kawai don kiyaya, Tanti taja wani dogon tsaki... Bata ida rufe bakinta ba, umma ta tashi cikin tsawa tace" yimin shiru 'yar biya yar cusa kai inda ba'a san darajar ta yar' neman gurin zama gun miji da kishiya kina wani shishige ma ya'yan' ta don munafurci wai ke mai son su, dan mahaifin su ya dinga kalon ki da dajara dan kinibibi, to wlh anyi walkiya mun ganku sedai ayi ma wasu ba muba munafuka ai wlh na ganoki kar nake kalonku gaba d'aya ah to, kuma wlh ki fita haraka ta ki daina samin ido tunda ni ba 'yar biya bace ehe. Ta tab'a hannu tare da komawa ta zauna, tanti harta bude baki zatayi magana, papa ya dago ya watsama ta wani irin kalo mai nuna cewa yi tafiyar ki, ki barta batada hankali, yasa Tanti juyawa ta nufi dakin ta itama, tajin umma nacewa "kika ki tsaya ki fad'i abinda ke ranki in ba tsoro ba, yanzu kiga b'acin raina, Tanti dai tashige daki batace mata kala ba bare tajuyo ta kaleta.

Falon ya rage daga umma da papa sai wasu yara 'yan maza guda biyu dake zaune suna kalon umma dake ta masifa kamar an aiko ta, don tuni ya'yan umma su nufi dakin su tunda sukaji tafara banbami fada. Dan babban daga cikin daba zaya fuce 16 ans (years) ba ya mayar da kalon sa gun mahaifin nasu yace "papa mu zamu koma ban'garen mu don muje muyi revision, cikin kulawa papa ya dawo da kalon sa garesu yace " to maza ku tashi ku tafi kuyi karatu, ka dinga nunawa k'aninka ida bai gane kaji ko fahad. Wanda aka kira da fahad "yace insha Allah to ku tashi ku je Allah maku albarka suka amsa da ameen sanan suka fita daga falon gaba d'aya.

AFREEN na komawa daki ta nufi gun da take ajiyar kayan karatun ta na école (school) ta ciro papier (peper) da tashigo da ita d'azu taje tanemi guri ta zauna ta fara traité din exercice (exercise) din cikin nutsuwa.

Khairat na fitowa daga salle à manger (dinning) dama ita bata tsaya cikin falon ba direct dakin AFREEN ta nufa, tana shiga ta sameta tana exercice ta zauna kan kujerar da ke dakin, "tace ma soeur (yar uwata) miyasa kike damuwa da abinda umma tamiki kamar bakisan halinta ba AFREEN ta dago ta kaleta tare da sakar mata murmushi da yasa fossette (dimple) dinta fitowa, tace "bakomi gande soeur (big sis) juste (just) munafuka da tacemin ne ya d'an sosa min rai, amma yanzu ni harma na manta da abin, wanan exercice din ke gaba na. khairat tace "kin tabata tace "wlh kuwa soeurette (sister) "to shikenan bari na barki ki karasa karatun, idan kin gama kizo daki na muyi fira sai ma ki kwana a can "to anti na sai na shigo AFREEN ta fada. Khairat ta tashi ta nufi kofa ta fita daga dakin ta nufi nata.

30 munite AFREEN ta dauka tana traité din exercice (exercise) din kamin ta kamala, wayarta dake saman gado kamar jira take ta ida karatun ta dauki tsuwa tana neman agaji karasa wa tayi ta dau wayar mon amie intime (aminiya ta) taga yana yawo kan écran ( screen) din wayar murmushi ta saki tare da dauka kiran ta kai kune har ga Allah taji dadin ganin kiran hasina. Daga cikin wayar akayi salama ta amsa, hasina cike da jin kunyar kawar tata tace " kawata bakiyi bacci ba ina ta tunanin kiranki yanzu, ina gudun kinyi bacci kar na tayar dake.

"A'a banyi bacci ba ya kike, hasina ta dan nisa tace "lafiya lau, dan Allah kawata ki yi hakuri ki yafemin abinda da miki dazu wly ba da niya nayiba kanin fuskarki yayi min bazata, wlh bata kamantaki ba da irin wanan mugun kyau da nagani a gareki bane shiyasa, wlh kyau ki ya firgitani sabida wlh kyau ki bai musultuwa kawata, Allah dai ya tsareki ya kare ki daga sharin mutun da aljan da karfe bature ashe ba banza kike rufe fuskaki ba, dan Allah kiyafe min.

AFREEN dake sauraren ta sauke wata agajeriyar ajiyar zuciya tace " Ameen bai komi kawata kuma ni baki min komi ba inda ma kinyi na yafe maki "alhamdulilah na gode kawata Allah barmu tare, bari na barki ki kwanta sabida gobe akwai école (school) hasina ta fada, AFREEN "tace to kawata Allah tashe mu lafiya, ameen hasina ta fada tare da katse wayar.

AFREEN na ajiye wayar ta nufi armoir (wardrobe) ta dauko kayan bacci ta ta fita daga dakin.

Bangaren hasina kuwa tana katse kiran ta daka tsale tace "ashe batayi fushi dani ba Allah na gode ma da kaban kawar kirki irin AFREEN..........





Ina kaunar ku masoya ...........💞




Commenté

Et

Partager


Comment

And

Share


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZANBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


ECRIT:


PAR


QUEEN
ZEEFAT


Yar
Mutan
Niger

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/



Bismilahir rahamanir rahim



Page 5


Tana fita ta nufi d'akin Khairat da ke kusan nata da sallama ta shiga amsa mata sallama Khairat tayi dake bakin gado tana manipuler d'in wayar ta mike wa Khairat tayi taje ta kamo hannu AFREEN ta zaunar da ita bakin gado, tace "yawa 'yar k'anwata, ina aza baza ki zo ba?" AFREEN tace "mi zai hana anti? kawai natsaya yin waya ne." "waya kuma AFREEN, a cikin daren nan, to ko dai nayi k'ane ne banda labari ? "Lah anti wane irin k'ane kuma," "to ni sani nayi AFREEN, nufi na ko kinyi saurayi ke da toujour (kulin) kina cikin nikaf, bansan ko taya wani zai gan ki ba har yace yana son ki a cikin nikaf ba, an yi mutun kulin cikin nikaf kamar dai wanda yayi wani mugun laifi Police na neman shi, Allah dai shirye ki AFREEN."


"Hum anti kenan saurayi fah kika ce? wanan ai sai ku 'yan mata, ina ni ina saurayi yanzu duka ta nawa ni ke."


AFREEN ta fad'i maganar tana dariya tare da kalon 'yar uwar ta, itama Khairat dariya tayi tace "ke d'in ce ba 'yan mata ba? Tubarkallah god'aigo'd'ai da ke da 18 ans din shi ne zaki ce a ta nawa kike, baki isa aure bane ko miye nufin ki? ni dai naga har 'yan 15 ans an masu aure baran tana ke macha Allah da babu abinda kika rasa na manyan 'yan mata masu ji da kansu,"
"haba anti a 18 ans (years) a ka min aure ai rishin tausayi ne gaskiya ni ban wani isa aure ba yanzu, tu vois je n'ai même pas fini mon étude, kin ga kenan ban girma ba" AFREEN ta fad'a tare da yin murmushi.


Khairat tace "ah kenan sai muntun ya k'arasa karatu ne ya girma kuma ya isa aure? to tun yuri garama ki farka daga baccin da kike ah to, kingan ninan idan ahmad yace zai kawo kudin aure na a gobe, to wly yarda zanyi ah to mi kake yi da karatu ga sunnah manzon Allah saw, idan naje gidan nasa sai na karasa karatun a can, ke ni daga na k'arasa wanan shekaran shikenan bawani karatu da zanci gaba da shi, kedai rik'a min adu'a na karbi licence d'ita shekara nan shikenan nida école (school) munyi ban hannu sai d'akin miji insha Allah" ta fad'a tana dariya. "To ameen grande Soeur Allah ya taimaka kuma ya kawo miji na gari musha biki ranar akwai casu in Allah ya yada."

"Hum kinji kamar da gaske, ga ki nan wa ta irin ustaziya dake wane casu za kiyi gayi ne kawai kike" ita dai AFREEN murmushi kawai tayi bata ce komi ba.


"Yawa 'yar uwa na ma tuna kisan wai dazu na dawo daga gidan anti fauziya na had'u da wani a hanya wai shi abdul majid bari na nuna maki photon (pic) shi, yanzu ya turo min a whatsapp wai so na ya ke da aure kuma yace min ba garin nan yake ba dan tahoua ne shi, kedai ban matsaya na saurare shi da kyau ba Kawai nace mishi ni gaskiya ban nan gayin fira a titi sai yace na shigo motar sa ya ragemin hanyan nace nagode, babu yanda baiyi ba kan na shiga motar sa wai ya karaso da ni gida nakiya dad'a daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaki, ban san sa ba, ban taba gani sa ba shikenan sai na d'ane motar sa ya kawo ni gida kinji kamar wace bata da daraja da kamun kai, ko bama haka nan ba, in fah yana kawo ni daidai papa nazo wa ya gan ni to sai yaya, Lale yau da papa ya kakarya ni wlh." Khairat ta fad'a tare da shiga ma'adanar photo na wayar ta.


AFREEN tace "Lalai kam gara dai daba ki shiga ba ko ba dan ka papa ya gan ki ba ai se ka nema ma kan ka daraja."


Ta fido photon ta nuna wa AFREEN tace "kin ganshi fah sis?," "lah anti shima kyakyawa amma fah ya ahmed ya fi shi kyau, to anti ya batun ya ahmed naga kuma kinyi wani Abdoul majid, ko kun b'ata da shine?" AFREEN ta tambaye ta a tak'aice. Khairat tace "ah haba ahmed fah shi ne k'ark'ashi zuciya ta shine na ke so da kauna, wanda nake mafarkin ya zaman miji na insha Allah taya ma zamu b'ata, sedai wani inkon Allah kuma kawai dai na yada na bashi numéro (number) na ne sabida baka san yata Allah zata kasan ce da kai ba, tunda bakada masaniyar ko waye mijin ka ba sai wanda Allah ya zab'a maka."


''hakane kam rabin raina Allah kawo da mafi alkairi," Khairat ta amsa da "ameen petite Soeur, tashi kije kiyi wanka kiyi change kizo ki kwanta kinga akwai école gobe in Allah ya kaimu, idan kika dawo makaranta gobe mun karasa firar insha Allah."


Tashi AFREEN tayi ta nufi douche (toillet) wanka tayi tare da yi brossage din baki ta dauro alwala ta fito, direct wajan coiffeuse (dressing mirror) ta nufa tayi abinda yaza ma mata al'ada kamin ta kwanta, sannan ta wuce gun armoir ta ciro kayan baccin ta, sabida a d'akin ko wane cikin su akwai kayan d'an uwan shi a cikin nashi kayan sabida gudun irin haka, kamin ta dawo saman gadon ta kwanta tuni Khairat tayi bacci haura wa tayi itama kan gadon ta fara karanto adu'o in bacci tana idawa tayi bismillah ta kwanta kusa da Khairat, bata wani d'auki lokaci ba bacci ya k'washe ta.


K'arfe biyu daidai na dare AFREEN ta farka da adu'ar tashi daga bacci a bakin ta, sauko wa tayi daga kan gadon ta nufi toillette, shiga tayi ta wanke baki, ta dauro alwala, ta fito ta canza kaya ta d'auko hijab da darduma ,saka hijab d'in tayi tare da shinfid'a darduma ta koma bakin gadon kusa da Khairat, ta dan ja hannun ta tace"anti tashi ko yau ba zakiyi sallan ba ne."

Khairat ta buda idon da suka mata nauhi tace" s'il te plait AFREEN laisse moi dormir wly j'ai sommeil ("please AFREEN let me sleep wlh I'm sleepy)" "dan Allah Anti tashi mana" mtsss taja dan k'armin tsaki sannan tace AFREEN dan Allah ki barni wlh yau bacci nake ji sosai je kiyi taki kawai" daga haka AFREEN ta nufi kan darduma ta tada salllah, sai da ta kai karfe ukun dare ta na nafila kamin take sallame wa gabada ta mike ta ninke darduma da hijab ta mayar da su ma'adanar su, ta dawo saman gadon ta kwanta, ba itace ta farka sai wajan karfe 5:15, tashi tayi ta nufi toillette ta d'auro alwala ta fito ta nufi gadon ta tayar da Khairat, tare da gabatar da raka'atanul fijir sannan tayi sallah asuba, kur'ani' ta d'auko ta fara karanta wa, sai 6:30 kamin ta koma toillette minti 10 ta fito d'aure da serviette (tawel) cikin k'ank'anin lokaci ta shirya tsaf da ita cikin riga da jupe (sket) na atanfa da suka mata matuk'ar kyau macha Allah, ta ciro hijab tasaka da nikaf ga hannu, da jakar makarantar ta tace ma khairat, dake zaune har lokacin kan darduma.

"anti na tafi, sai na dawo" Khairat ta dago ta kale ta tace to a dawo lafiya Allah ya tsare" ta amsa da "ameen" tare da fice wa daga d'akin.


Tana fita ta nufi escalier direct d'akin mahaifin su ta nufa, tashi ga da sallama, yana zaune a falo kan darduma da kur'ani a gaban sa da alama karatu ya gama zauna wa tayi kusa da shi tace "papa ina kwana antashi lafiya" papa ya amsa da "lafiya lau AFREEN, har kin shirya, yau dreba zai kaiki ko kuwa da kanki za kiyi conduire (driving)?" tace "a'a dreba zai kaini yau bana jin conduire d'in" papa yace "ok to kinyi kari kuwa" " a'a amma yanzu zanyi kamin na wuce makaranta" papa yace "to shikenan ki samu fah ki kayar kamin ki wuce, karb'i kudin makarantar ki" papa ya fido da 1000f ya mika mata yace to a dawo lafiya" AFREEN tace "ameen papa na gode.

Daga nan ta nufi dakin mahaifiyar su ta gaida ta a gurguje ta fito sanadin gani da tayi ta kusa makara. kasa ta sauka tayi dakin umma ta gaida ta, umma ta watsa mata harara tace "in ban kwana ba kin gani kinibabiya Kawai nace ban son wanan gaisuwar dole ne sai kin gaida ni koni uwar kice" AFREEN batace komi ba ta juya zata fita wata yarinya da ba zata fuce 14 ans (years) "tace dan Allah anti AFREEN nazo ki wuce dani makaranta tunda ke da yuri kike zuwa idan natsaya jiran su marie zasu sa nayi retard (lati) dubi fah har yanzu ko shirya wa ba suyi ba bare ma ayi batun karyawa", da murmushi AFREEN ta juyo tace to ke kin karya ne" girgiza kai tayi tace "a'a yanzu zan karya anti" AFREEN tace "to shikenan d'auko jakar ki sai ki fito mu karya tare sai mu wuce" yarinyar tace "to anti gani nan zuwa."


AFREEN na fita yarinyar ta juya ta dubi mahaifiyar ta tace "umma gaskiya abinda kike yiwa anti AFREEN ba ki kyautawa, du gidan nan akwai me biyo ki har d'aki ya gaida ki inba ita ba, ko kin taba gani anti Khairat ta shigo dakin nan ta gaida ki, sedai idan kun hadu a falo, yanzu ma da ta gane halin ki ta daina gayar dake gaba d'aya, sabida irin wanan abin da kikewa anti AFREEN, amma ita anti AFREEN nasan da komi zaki mata ta ba zata daina gaida ki ba."


Wani irin mugun kalo umma ta watsa ma yarinyar tace "kinsan wlh Zeinab ki fita ido na, na rufe ke wace irin banza yarinya ce da ba ta san ciyon kanta ba ke dai ba ki kaunar ki ga an taba wacan munafukar yarinyar, to wlh ki kiyaye ni Zeinab, ko nuna maku da ake a gidan nan a fi son ta daku ko ciyo abin bai maki, to wly ki shiga taitayin ki, ki dawo hankalin ki ma in kina dawo wa."


Simi simi yarinyar da aka kira da Zeinab ta fice d'akin ba tare da ce ma umma komai ba.


AFREEN na fita daga d'akin umma ta shiga na Tanti ta gaida ta Tanti ta amsa tace "AFREEN har zaki makaranta."


"Eh" AFREEN ta fad'a a tak'aice tanti tace k'arbi zumu ki sha" tanti ta d'auko zumuwar ta mik'a mata, karb'a tayi tasha cuillère (spoon) guda ta mayar mata da sauran ta fita, take gun cin abinci ta nufa idan ta tardo Zeinab gama karyawa ta na jiranta, thé (tea) kawai ta had'a ma kanta tasha suka fice daga falon, direct inda dreba yayi tsaye da mota yana jiran su suka nufa, gaida dreba suka yi sannan Zeinab ta bude masu gidan baya suka shiga dreba ya tayar da motar ya doshi k'ofar fita daga gidan mai gadi nagani haka ya tashi ya wangale masu tamgamemiyar k'ofar gidan ya fice da motar.


Shiru kake ji cikin motar ba me cewa komi, can dai Zeinab ta katse shirun tace " anti dan Allah ki yi hakuri da abinda umma ke ma ki wly watarana zata gane ta dena maki hakan" AFREEN ta juyo tayi d'an murmushi me sauti wada seda kyawawan fararen hakoran ta suka bayana tace "kar ki damu k'anwata ni ban taba rike umma a zuciya ba, sabida nasan watarana sai labari bai komi kinji, itama umma uwa take a gare ni ,dan haka ni ba d'auki abinda take min a wani abu ba, ki ma daina min wanan zancan, in kina ban hakuri sai na ga kama kin nuna min umma ku ka dai ta haifa ban da mu," "anti wlh ba haka nake nufi ba" Zeinab ta fad'a da sauri, daidai nan a ka kawo k'ofar makarantar su Zeinab dreba ya ja ya tsaya, Zeinab ta bude k'ofar motar ta fita.


AFREEN tace "to petite Soeur (lil sis) a maida hankali da karatu a daina tsayawa wassa" Zeinab tace insha Allah anti, karfe 1:30 muke tashi ki tunawa dreba yada dawo d'auka na," tace "to insha Allah ayi karatu lafiya Allah ya taimaka Zeinab ta amsa da "ameen, bye bye my lovely anti ina sonki sosai Allah tsare ki" daga nan ta gudu cikin makarantar, dariya AFREEN tayi tare da girgiza kai tace "Zeinab sai shirme."


**********


Wasu manya manyan kuma had'ad'un motoci ne guda uku biyu bak'ake d'ayar dake tsaka fara ce tass mai masifar kyau, suka kunno kai cikin wani hatsabibin hamshakin kuma tangajejan gida, had'uwa gidan ba sai na fad'a kowa ya canka.........





Muje zuwa💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃




Commenté



Et



Partager



Comments



And



Share
💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003

🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZANBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

ECRIT:


PAR


QUEEN
ZEEFAT


Yar
Mutan
Niger





Wattpad@nazhabibou




BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM



Page 6



Chigar motocin keda wuya suka parcking a farfajiyar gidan bud'e k'ofofin babak'un motocin guda biyu akayi, wasu sojawa ne maji ya k'arfi guda bakwai suka fito daga cikin babak'un motocin sanye suke da kayan garde da gendarme hannayen su rik'e da manya mayan bundigogi fuskar su sanye da verre noir (glass baki), fuskar a matuk'ar murtuke kana kallensu zaka hango da babu alamun wasa ko tausayi a tare dasu to bare muntunci, in ka kallesu dole zaka razana.


Da gudu suka nufi farar motar da ke tsakiyar bak'ak'en motocin, suka zagaye ta gaba daya tare da haka bindigogin su, suna jiran fitowar na cikin motar, bud'e k'ofar gaba ta farar motar akayi wani farin dogon guy kyakyawa ya fito da tenu garde sanye a jikin sa, rufe murfin motar yayi ya tako da sauri ya zo ya bud'e k'ofar baya ta motar.


wajan minti biyar wanda ke banyan motar ya zuro wata k'ayattaciyar k'afa me d'auke da wasu tsadadun takalmi masu matuk'ar kyau ba tare da b'ata lokaci ba ya ida ziro d'ayar k'afar, daga bisani ya fito ma gaba daya daga cikin motar.


Wani had'ad'en kyakyawa saurayi ne mai jini ajika da ba zai wuce 30 ans ba, gashi da matuk'ar d'aukar hankali da ka ganshi dole ya birge ka, dogo ne mai doguwar fuska mai d'auke da d'an siririn sage iya bakin kunnuwa, café au lait ne shocolat colour, da d'an siririn hancin shi, sai dara daran idanun sa masu mugun haske da k'ayattacan bak'in a cikin su mai d'aukar ido da birgewa, da matsakaicin jiki dayasa tsayisa yayi daidai dashi macha Allah fatar jikin sa kad'ai zaka duba ka gane d'an futu ne babu alamar wahala a tatare da shi kuma daga ganin shi zaiyi miskilanci, a take zaka hango kwonciyar hankali, nutsuwa da kamala a tatare da shi.


Yana fitowa take nan garde corps (body guard) d'in sa suka k'ank'ame yuri guda tare da sara masa, ko kallon inda suke baiyi ba bare ya nuna alamun yasan abinda suke, fara tafiya yayi suka rufa masa baya garde d'in da ya bude masa mota shine baya da shi kamar zasu jera sauran kuma a bayan su.

Please Login or Register in order to submit comment