Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

stairs nayi mata salama lokaci zai kure ta fada tana me murda kofar falon tafita Tanti na mata Allah kiyaye hanya ta amsa da ameen tare da ficewa daga falon gaba daya
Wajen parking space ta nufa tac ciro makulin motar tareda nufar motar da tashigo da ita dazu ta bude ta tashiga ta tada motar tare da barin cikin parking space din ta nufi kofa mai gadi na ganin haka ya wankale mata kofar ta fita a guje sabida latin da tayi tafiyar minti 10 yakai ta makarantar parking space taje ta paka motar ta fito ta kule ta yin hanyar ajin nasu da aka riga aka shiga tsaya wa tayi bakin kofar ajin ta taba hannu daga ciki aka amsa da oui rentre(yes enter) tashiga da salama tare da gaida malamin ta nemi waje ta zauna malamin binta yayi da kalo har ta zauna kamin yaci gaba da explaind din lesson daya ke.




Karfe shida daidai suka fito daga ajin nasu ita da wata farar yarinya da bazata wuce shekarun AFREEN ba tsayisu yaso ya zo daya sai dai AFREEN ta fita da kadan itama kyaukyauwace yarinyar ba lafi sanye take da riga da sket na Atanfa sunyi matukar yi mata kyau sanye take da dan karamin hijab da baikama ta gwiwa ba, yarinyar tace AFREEN wai yaushe zanga fuskar ki dubi fah tun lokacin da muke dake, har gidan ku nasha zuwa baki taba bari naga fuskar ki ba basan ko sabida miyasa kike boyemin fuskar ki ne wai idan ma kin boyema kuwa ai ni bai kamata ki boyemin ba duba fa kiga yanda yanzu ko a hanya nagaki bazan sheda kiba inba tafiyar ki nagani ba AFREEN tace hasina kenan wlh ba abinda yasa ni ke boye wanan fuskar ta waba saida dalili babu wani dalili AFREEN idan dai kin dauke ni a matsayi kawa to ki nuna min fuskar ki yanzu ba se anjima ba gaskiya yanzu ai zanji kunya idan aka tambaye kamanin kawata nace ban saniba ai za'amin dariya ace du kawancan dake tsaka nin muma basanki ba AFREEN tace kiyi hakuri dan Allah kawata wlh watarana zan nuna maki fuska ta amma yanzu rishin ganin fuskata a gareki shine mafi alkairi a'a ni wlh bazan taba yarda ba gaskiya wata muguwar kama ce gareki daza kice wai rishin ganin fuskar ki shine mafi alkairi ka mardai wata aljanah
AFREEN tace wlh hakan da fada maki gaskiya ne hasina a'a kedai ki nunamin don wly idan baki nuna min yau ba kuma yanzu wlh bana shiga motar kiba kuma kawancan mu daga yau ya kare haba hasina meyasa zakice haka nan hasina tace kindai ji abinda nace ai ko to kinga ma tafiya ta da sauri AFREEN ta riko hannuta tace yi hakuri kawata muji mota sai na bude fuskar ki gani haka hasina ta bita suka nufi idan motar take tabude motar ta shiga hasina ta bude wajen me zaman banza ta shiga ta rufo kofar AFREEN nagani tashiga tayi saurin wiwa motar key tare da barin cikin makarantar hasina na mata masifa amma ko kulata ba tayi ba, bata tsaya ko'inaba sai kofar gidan su hasina, hasina na ganin ta tsaya takai hannun jikin kofar zata bude ta fita taji ta a kule fuska a matukar daure ta juyo daniyar masifan ce AFREEN lokaci guda tasaki wata irin kara hade da furta wa innahu suleymanu wa innahu bismilahir rahamin rahim, inna lillahi wa inna illaihi raji'un la'illaha illah anta subhanaka inni kuntum mina zalumin a tatare ta jero wa yanan adu'o in gaba daya a lokaci guda sanadiyar arba da tayi da kyaukyauwa fuskar AFREEN.



Ganin yanda ta firgice tana kokarin bude motar ta fita yasa AFREEN sauri bude mata motar da sauri ta fice daga motar ta shige gidan su kamar wada tayi wani mugun gamo da abin tsoro mafi tsoratawa a fadin duniya.



Commentรฉ

Et

Partager

Comment

And

Share



๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ
*ZANBA CIKIN AMINCI*
๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ


ECRITE:


_PAR_


*QUEEN
ZEEFAT*


Yar
Mutan
Niger


Wattpad@nazhabibou




๐Ÿ’ซโœจ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*๐ŸŒŸ
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_๐Ÿค

โ˜† *[ T.M.N.A]* โ˜† ๐Ÿ“–๐Ÿ–Š๏ธ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM




Page 3



AFREEN ta aza kanta saman steering din motar ta ce ga abinda nake gudu ya faru yanzu bansan yaza ta doki abin
ba da ban bude mata fuskan ba kuma tace ban doketa a matsiyin kawata ba dana bude mata fuskar kuma nasan yanzu ma gudu na zatayi wai wane irin kyau ne dani wanda mutane basu iya jure ganisa kodai wata kama gareni mai ban tsoro wada ni ban ganin ta sai na tare dani tare ta jero ma kanta wa'inan tambayoyin da taga batada mai amsa mata su yasa ta mayarda nikaf inta ta tayar da motar ta nufi gida,tana zuwa gida bayan mai gadi ya bude mata get ta shiga tayin parking motar a parking space tafito ta nufi cikin gidan ta na shiga falo da salama ta tarar da mahaifiyar ta dake zaune tana kalo gaida ta tayi sanan ta karasa kusa da ita ta zauna a saman carpet mahaifiyar ta ta amsa tace AFREEN yanzu dinma kin jima a makarantar injin dai lafiya



Lafiya lau Maman AFREEN ta fada a takaice tana mai cire nikaf din fuskar ta maido da kalon ta tayi wajan mahaifiyar tata cike da damuwa kamin takai ga magana Maman tace lafiya ki AFREEN naga kama akwai abinda ke damunki dubi fuska na Maman wai ni kyau gareni ko muni wace irin munmuna kama ce dani da duk wanda ya kaleni ya ke firgita alhali ni banga abin firgita a cikin tsarin halita na taba ko kama nike da mutanan boye ban saniba kodai da gangan mutane kemin hakane tunda ni ban ga abin tsoro a tatare dani ba AFREEN ta tambayi mahaifiyar ta ta da hawaye kwance cikin idon ta da alamun damuwa a tatare da ita Maman tace ko alama ba ko daya daga cikin abinda kika zayana a tare dake AFREEN maza mayar da hawayen ki kada kiyar da su zubo dole ne mutune su ringa firgita da irin kyau da Allah ya maki ba wani ba ma ko ni dake mahaifiyar ki mamakin wanan baiwar kyau da Allah ya maki nake AFREEN.


Yan magana nace wada yayi fari ya gama kyau amma ni tuni na karyata wanan magana tunda Allah ya azurta ni dake tunda kinga kedai ba za'a saki a layin farare ba haka ma ana bakake babu ke a ciki sedai asaka ki a tsakatsakiya amma kinga duda haka Allah ya miki kyau irin wanda baza'a iya musilta shi ba dan haka godiya ya kamata kiyi wa ubangiji da yabaki baiwa kala kala ba wai butulce mashi ba.


Kuma ina me gargadin ki da kada kiyi anfani da kyau da Allah ya maki wajan saba masa ki zamana me kyautatama sa komi rantsi duda banda shaku a kanki amma yanzu zamani ya canza kawaye ma na iya sauya ma mutun tarbiyar da iyayensa suka mashi dan haka ki kula AFREEN kisan irin kawayen da zakiyi mu'amala dasu ba kowa ake kawance da shiba.


Dan haka ki fida damuwa a ranki sabida kyau ki ba me tsoratarwa bane kawai dai dole ne ya firgita mutane bama karma a bazata mutun ya ganki, tunda wasu za su ringa tunanin cewa kedin munmuna ce shiyasa baki yarda aga fuskar ki wasu kuma suce kyau ne dake shiyasa amma baza su taba tunanin kyau naki ya kai haka ba wasu zasu ce ra'ayi ne da ganin dama ko suce da gangan ne yasa kike saka nikaf ba mai taba zaton dalili ki nayi haka kinga Maman ni yanzu harma na saba ban iya fita babu nikaf sabida dana fita mutane sai su dinga min kalon kurila wasu ma har guduwa suke wasu kuma mamaki nake basu kamar dai babu wanda ya fini kyau a duniya Maman kinsan a kawai masu kyau sosai wanda suka fini nesa ba kusa ba amma kuma nawa kyau se yadinga firgita mutane ga laraba wa da indiyawa nasan da cikin su a kwai wanda suka fini kyau nesa ba kusa ba amma su ba'ayi mamakin nasu ba sai nawa, hum AFREEN kenan bazaki ganeba ne kefa naki kyaun na daban ne indiyawa ko larabawa suma nasu kyau daban yake bama yanayin ki guda dasu kinga su a cikin suma za'a iya samun wanda kyau su zai iya firgita mutane fiye da naki to kinga ke yanayi kyau naki ne yake firgita mutane da basu mamaki badan wai ba za'a iya sami me kyau fiye danaki ba ne a'a ke hada baiwa da Allah ya baki me sa du wanda ya ganki yake ganin annuri da kyau suna karuwa a fuskar ki fiye da yada ke kike gani


Dan haka ki kula kiji tsoron Allah ki guji sabama ubangijin ki dan bai cancanci haka daga garemu ba Allah abin bauta ne dan haka mu bauta masa fiye da yanda ya umurce mu idan har za muyi ma kan mu adalci ma halicin ya cancanci mu kadaitashi ko dan rayuwa da ya bamu sadakar yi aiko ubangiji mu ya gama mana komi Allah dai ya kara mana imani da tsoron sa a ciki zukatan mu ya bamu lafiya da kwonciyar hankali mai daurewa ya tsare mu kuma ya kare mu daga duk wani iftala'i da sharin duk wani mai shari Allah yamana kyaukyauwan karshe yasa mugama da duniya lafiya.


AFREEN ta amsa da ameen Maman zata sake magana Maman ta katseta da cewa kada kikara ce wa komi AFREEN.

Tashi kije daki kiyi wanka ki futa kinga magariba ta gabato ba musu ta mike tace Maman wai ina anti khairat tace tana dakinta to Maman bari naje na shirya sai naje wajan ta
Tana juyawa idanun suka sauka cikin na tanti da take tsaye tun dazu tana sauraran su amma su ba su san tana wajan ba take ta sakar mata da murmushi tace tanti barka da wara haka tanti ta amsa tana mai mayar mata da murmushi tace tanti zanje inyi wanka ne zan fito idan nayi sallah tace to sai kin fito AFREEN ta nufi dakinta ita ko tanti ta karasa cikin falon.


******


Hasina a guje ta shiga falo gidan su tana wage wage da sauri mahaifiyar ta dake cikin falon ta mike tace subhanalahi ke lafiya kika shigo min falo a guje hasina data durkushe kasa saman carpet tana sauke ajiyar zuciya ta dago ta kali mahaifiyar ta tace ummi gamo nayi koko miye ni ban saniba gamo kuma hasina a ina .


wlh ummi nidai nasan mun fito daga aji tare da AFREEN wanan kawarta wa danake baki labarin nace mata yau ita zata kaini gida tunda direba daya kaini makaranta yake ce min da ya sauke ni zaiyi tafiya idan mun tashi na shiga napep to sai na matsama AFREEN kan cewa doli sai ta nuna min fuskar ta a yau inba haka ba zamu daina kawancan to sai tayar da zata nuna min tace muje mota muna shiga sai taja motar bamu tsaya ko'ina ba sai kofar gidan nan na juyo gunta daniyar balbaleta da masifa kawai mizan gani,
Hanisa ta dan nisa kanan taci gaba ummi kinsan mi nagani ummi ta girgiza mata kai hasina tace wata daleliyar yarinya mai masifar kyau nagani du yanda zan kwatanta kyauta ba zaki gane ba ummi wlh ba AFREEN nagani ba aljana ce sabida babu mai irin wanan kyaun nan acikin mutane to wani ummi ina ma tayi da AFREEN din da muka tafo tare nashiga uku ummi kawata naci kin hadari abinda yakara firgita ni ummi tunda muka biyo hanya nakema AFREEN masifa ta min shiru hakan na nufin cewa dama tun bisa hanya bada AFREEN nike magana ba oh Allah ka tsare AFREEN ka kareta daga sharin wanan aljana wlh ummi kyau din ta ya yuce musali hasina ta fada a firgice tana mai sake waigen kofar falon wai kar ace aljanar ta biyota


Komawa ummi tayi ta zauna tace haba hasina ya zaki ma kawarki haka yanzu ya kike su taji tunda kike ban labarin ta kina cewa ko a aji bata fida nikaf nasan da akwai abin take boyewa kuma tanada dalilin yin hakan ta yiyuwa sabida kyau inta yasa bata bude fuskar gudun faruwar abinda kika mata yanzu kewace irin birkitata ce da bazaki iya aje hankali ki tantance ba ka kikace ta nuna maki fuskar ta amma kuma sai ki saka mata da haka haba hasina baki kyauta kawai baki taba tunanin kyaun ta yake haka bane kuma gani fuskar ta ya zo maki a bazata shiyasa amma ba wata aljana dakika gani kawarki din daice AFREEN


Wata irin nauyayar ajiyar zuciya hasina ta sauke tare da kura ma mahaifiyar ta ido na wajan sakan 5 kamin ta nisa tace hakane fah zancan ki ummi sabida kamin ta yarda zata nuna min fuskar ta seda tace min nuna min din ba alkairi bane ba amma na matsama ta nayi wawanci sosai miyasa nayi mata haka oh ni hasina Allah shirya min halina ya fitar min da tsoro. Amma fah ummi ba laifina bane wlh kyau AFREEN ne ya wuce tunanin mai tunani kuma hakan yazo min a bazata ummi tace hakane yanzu tashi kishiga ciki ki futa sai ki kirata ki bata hakuri
Haka hasina ta tashi ta shiga dakin ta da tunani iri iri a zuciyar ta


******

AFREEN nashiga daki ta cire kayan jikin ta ta fada toillet wanka tayi tare da dauro alwala ta fito tayi wajen dressing mirror ta gama abinda take sanan ta nufi wardrobe ta sake ciro wata doguwa rigar tasaka tare da hijab ta nufi gun da take ajiye darmuma ta dauko ta shinfida tare hawa ta kabarta sallah.

Tana idar da sallah da adu'o inta ta nufi ma'ajiyar kur'anai da litatafan adini ta dauko kur'ani Ta koma saman darduma ta fara karantawa tana nan zaune a haka har aka kira sallar isha ta tashi ta mayar da kur'anin ta dawo saman darduma ta tayar da sallah tana idawa ta nike darduma da hijab ta maidasu ma'ajiyar su ta koma inda gadon ta yake ta doki dan kwalin rigar da ta ajiye a saman gadon tare da ribon ta daura dankwalin rigar da ribon a hannu ta ta nufi kofa tana bude kofar dakin suka ci karo da wata farar yarinya a bakin kofar kyaukyauwa ce itama bazata fuce 21 years suna da kamar jini a tsakanin su sai dai ita fara ceda sauri AFREEN ta saki kofar tana murmushi wanda har saida fossette (dimple) dinta suka bayana tayi tsale ta rugumeta tace wayo anti khairat nayi kawarki duk yau tunda safe da na ganki bansake ganin ki ba tunda zu nake tambayar Maman ke khairat tace to kuma shine in kinyi kewata shine bakije waje naba ai gashi nida nadamu dake nazo na ganki, AFREEN tace dagaske Anti khairat yanzu ma da kika ganin na bude kofar nan zan fita wajan kine zanje bakiga yanda na kagu naje na ganki ba dan Allah Anti khairat shigo mana tace a'a dama ai yurina kikayi niyar tafiya ko AFREEN ta daka kai alarma eh sai Anti khairat tace to muje daki na AFREEN tace to Anti karbi ribon din nan ki daure min sai mu fuce.
Karba ribon din Anti khairat tayi tace to juya AFREEN ta juya tare da since dan kwalin dake kanta khairat tace ni ban san ranar da zaki iya daura ribon a kanki ba tace wlh anti nima ban san ranar ba baki ga gashi nane yayi yawa ba gashi kuma da tsayi sosai ni ha tsoro ma yake ban Anti khairat tace to idan ya baki tsoro ki daina karba mana murmushi kawai AFREEN tayi batace komi sabida tagane mitake nufi tana gama daure mata gashi ta kama hannuta suka bar kofar dakin ta ce mu fara zuwa mu gaida papa kamin nan cike da zumudi AFREEN tace papa ya shigo ne khairat ta amsa da eh.






Aimรฉ


Commentรฉ


Et


Partager




Like

Comments

And

Share.


๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ
*ZANBA CIKIN AMINCI*
๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐ŸŒธ


ECRITE:


_PAR_


*QUEEN ZEEFAT*


Yar
Mutan
Niger


Wattpad@nazhabibou

๐Ÿ’ซโœจ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*๐ŸŒŸ
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_๐Ÿค

โ˜† *[ T.M.N.A]* โ˜† ๐Ÿ“–๐Ÿ–Š๏ธ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM_



Page: 4



AFREEN da khairat suka haura saman escalier (stairs) hannu khairat rike da na AFREEN direct kofar dakin mahaifin nasu suka nufa. khairat ta saki hannu AFREEN ta tura kofar tare dayin salama daga cikin dakin aka amsa masu salama tare da basu izinin shiga, kara turo kofar khairat tayi tareda sakai suka shiga a tare.

Wani datijo ne daba zai fuce 55 ans (years) ba, zaune saman daya daga cikin hadadun kujerun dake falon, launin fatar sa daya da na AFREEN sedai babu kama a tsakani su sai ta jini sabida AFREEN da mahaifiyar su take kama sedai ta dauko launi fatar mahaifin su, amma duda kamar da take da mahaifiyar ta tafi Maman kyau nase ba kusa amma kuma kana kalon ta zaka san mahaifiyar ta su ta debo, khairat kuwa tak tak da mahaifin su take kama sedai ta dauko farin mahaifiyar su.

Da sauri AFREEN ta karasa kusa da mahaifin nasu tare da zaunawa saman moquette (carpet) tace "papa na ina yuni, mahaifin nasu dake kalon ta tun shigowar su ya saki murmushi tare da aza hannu sa akanta yace "lafiya lau AFREEN din papa ya karatu. tace "alhamdulilah" yace "to madala Allah ya taimaka kuma Allah bada sa'a a maida hankali da karatu kinji ko, tace "insha Allah ya kasuwa papa yace "an gode Allah. Daganan khairat ta karaso itama kusa da mahaifin nasu ta zauna tare da gaida mahaifin nasu amsawa yayi tare da cewa "khairat ya makaranta kema wanan ce shekaraki ta karshe a universsitรฉ (university) sai an bada himma, kuma naga tunda kikazo shiru bakice zaki koma ba ya haka . khairat tace "eh wlh papa ai kasan mu yada karatun mu yake on peut faire plus d'un mois sans nous programmer un cours (we can do more than a month without scheduling a course), shiyasa nikuma da naji nayi kewar gida nadawo, amma idan satin nan ya kare cikin sati me zuwa zan koma insha Allah papa yace "to madala Allah ya nuna mana tare suka amsa da ameen "ku taso mu sauka kasa muci abinci "to papa suna zaune har seda mahaifin nasu ya mike ya fara tafiya sanan suka rufa masa baya.

Suna sauka en bas de l'escalier (down stairs) suka isko kusan kowa na gidan yana salle ร  manger (dinning) suka dai akejira, shiga suka salle ร  manger (dinnig ) din da salama aka amsa masu da sauri AFREEN ta shiga gaban mahaifin nasu kamin ya ida karasawa taja masa kujera da yasaba zama a table ร  manger (dinning table) ya karaso ya zauna tare da cewa "Allah maki albarka ta amsa da ameen ta ja tata kujerar dake kusa da papa ta zauna umma ta tashi zatayin servir (servin) din su sabida yau ranar girkin tane, AFREEN tamike tace "umma yi zaman ki bari nayi servir (servin) din. da karfi umma ta karb'e koshiyar (spoon) tace "ke bani ni ban iya munafurcin ki ba, karamar yarinya dake se kinibibin asara, yaushe nace inason ki taimaka min, munafukar banza da wofi, to ko uwarki bata isaba bare ke, ni matsa kiban gu, ta dan turata tayi baya zata fad'i papa yayi saurin riko ta, umma ta koma cewa "wai sai tayin ta abunda za'a cema ta yar kike to kowama dan kirkin ne.

Papa ya jawo AFREEN dake ya zaunar da ita hawaye cike da idonta yace "AFREEN maza yi zaman ki tunda bata son ki kama mata. wani yaro da bazaya fuce 12 ans (years) ba yace "Maman dubi yanda umma kema anti AFREEN fada hada tureta da kadan ta fad'i alhalin batayi mata komai ba, Maman kice ta bar mata fada kada tayi kuka maman ta juyo garshi ta na mai murmushi tace "laifi tayi shiyasa amma bakaga ta daina ba yace "to Maman mi tayi tace "yanzu dai yi shiru ci abinci ka ya maida hankali sa yayi ga abincin sa ya fara ci. Umma ta gala masa harara dai bai masan tanayi ba.

Papa ya kali AFREEN "yace maida hankali kici abinci ki kinji AFREEN tadago takali mahaifin nasu daidai lokacin da hawayen da take kokarin boyewa suka zubo. Subhanallah "AFREEN kuka??? Maza share hawayen ki, tashi dauko abinci mu koma cikin falon in baza ki iya ci nan ba papa ya fada yana mai mikewa.
Da sauri AFREEN ta mike tare da daukar assiete (plet) biyu nata dana papa, suka bar dinning d'in tare da koma wa cikin falon, papa ya zauna saman kujera, ita kuma saman tapis (carpet).

Papa yace" AFREEN miye kuma abin kuka daga maki magana tace papa baka ji munafuka tace min fah "to in tace miki hakanan sai mi bakin san bahaka nan bane ba, ta daga kai alamar "eh" to ki daina zubda hawayen ki sabida Salamatou,in ba haka ba to ta dinga maki abinda taga bakiso kenan, kina abudai kamar baki san halinta ba. haka dai papa yata bata baki har suka gama cin abincin,ta dauke assiete din takai cuisine (kitchen). Ta dawo ta dauko masu ruwa da jus (juice) da verre (cup) dukawa tayi kusan papa ta zuba masa jus (juice) sannan ta zuba ma kanta ruwa tasha, suna gamawa ta tatare komi ta mayar dashi ma'ajiyar sa.

sannan ta dawo wajan papa ta dan duka "tace papa zanje nayi karatu yace to 'yar albarka ayi karatu lafiya.

Daganan AFREEN ta nufi dakin ta. Papa na zaune falo 'yan ci abinci a salle ร  manger (dinning) suka shiga falon da alama sun karasa cin abincin.

Maman bata tsaya cikin falon ba ta nufi escalier

Please Login or Register in order to submit comment