Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗaki ki zuba shi cikin abinda kike turaren huta ki turare jikinki baki ɗaya sannan ki kwanta."


Ba musu ko tambayar na miye, nan ma AFREEN ta koma ƙarbar maganin ta nayi wa tanti saida safe, tanti ta amsa da Allah tashe mu lafiya tana ƙara jadada mata cewa kada tayi bacci ba tayi turaren maganin nan ba dan taga bacci sosai a idanunta.


Da to AFREEN ta amsa sannan ta nufi ɗakin ta, da shigar ta ɗakin ta dauki abinyi turaren huta ta saka a soket, sannan ta zuba magani ta turara ma jikinta shi kamar yanda tanti tace mata, tana gama turare jikinta da maganin kanta yar fara juyawa, da sauri ta fida wayar abin yin turaren a soket ta nufin gadon ta a dadafe da kyar ta iya yin addu'a barci sannan ta kwanta tanajin yanda kanta ke juya mata kuma tsikar jikinta na tashi a hankali a hankali barci ya fara figarta har ta samu bacci ya kwashe ta bakiɗaya.


Ƙarfe biyar daidai na asuba AFREEN ta farka lafiya lau da addu'a tashi daga bacci a bakin ta lalubo wayar ta tayi tana duba lokacin, da sauri ta duro daga kan gadon da furta "Inna lilahi yani irin bacci ne ya kwashe ni yau haka har ban farka sallah dare ba," tana faɗar haka a lokacin har takai bakin kofar toillet buɗewa tayi ta shiga, bata jima ba tafito bayan ta ɗauro alwala tazo ta shinfiɗa darduma ta tayar da raka'a tanul fijir, tana ƙarasawa ta koma mayar da sallah asuba, da ta ida baki ɗaya ta shiga karanta suratul kahaf sabida yau safiyar juma'a ce,


6:30 ta kammala karatun ta shi tayi toillet dan yin wanka, minti 15 ta ɗauka kamin take fitowa daga wanka sannan tayi komai da ya zame mata al'ada idan ta fito daga wanka, wardrobe ta nufa ta fitar da wani haɗaɗen lace bakin da design puple riga da siket ta saka dumkin ya kamata sosai shi bai mata yawa ba kuma shi bai matseta ba sosai kayan suka zauna mata ajiki dan ba ƙaramin kyau suka mata ba gashi dama jikin AFREEN irin jikin nan ne wanda komai kasa kyau yake maka, haka ta fito kamar wata ba indiya shar da ita tayi kyau masha Allah duk da kwali ne kawai ta saka a idonta amma tayi matuƙar yaɗuwa kamar ka saceta ka gudu, a gagwace ta ciro dogon hijab ɗin ta puple da niƙaf ɗinta itama puple Wada akayi wa ado da duwatsu farfaru masu shegin ƙaili, ƙara feshe jikinta da turare tayi ta saka takalmin puple masu ɗan tsini sannan ta saɓo jakar makarantar ta tafi daga ɗakin, AFREEN tayi wannan shigar ne sabida su a makarantar su ba'a saka uniform kowa da kayen da yakeso yake zuwa makarantar.


Ta tafi da niyar hawa escalier (strais) dan zu gaida papa da maman suda ke sama, sai ta tsinkayi muryar Zeinab nace "Anty AFREEN gamu nan."


Juyowa tayi ta gansu su duka ƴan gidan zaune kan dinning har da papa kowa dai na wajen, ita kaɗai har babu a wajen cin abincin, juyawa tayi ta nufi dinning ɗin tana zuwa ta sakar masu murmushi tare da gaida iyayen na ta sannan ta ja kujera ta zauna ta zuba ma kanta abin breakfast ɗin sannan ta fara ci da sauri sauri, papa ya kalleta yace "Kici a hankali mana AFREEN kada ki sarƙe."


Tsayar da cin breakfast ɗin tayi tare da mayar da kallon gun papa tace "Papa sauri nake yau nayi lati 7:30 muke shiga gashi 7 har da minti 12 kuma idan nace bazan karya ba, ba barina zakuyi na tafi ba."


Papa yace "To maida hankali kici dan gaskiya bazaki school baki ci komai ba." ci gaba tayi da cin abincin."


Tanti da tunda AFREEN ta zauna take bin ta da kallo tanisa tace "Masha Allah ɗiyata kinyi ƙyau gaskiya ke ba ƙaramar kyakkyawa bace."


Ɗagowa AFREEN tayi da murmushi tana kallon tantin tace "Nagode my tanti adoré."


"Karki damu gaskiya ce na faɗa, amma a zuciyarta sai tace "Narasa wane irin masifafen kyau ne kega yarinya nan kamar aljanna to Allah dai ya tsare."


Umma kuwa dogon tsaki taja tsusssssss sannan tace "Cusa kai Allah raba mu da neman yurin zama, wajan biɗar a sanka har a mance dakai."


Babu dai wanda ya tanka mata dan sun rigada sun san hali, AFREEN kuwa miƙewa tayi tana cewa "Maman na ƙoshi zan yuce kada nayi lati."


Maman da papa da tanti da sauran ƙannanta banda umma suka mata fatan a dawo lafiya, amsawa tayi da ameen sannan tace "Zeinab yau ki bi direba sauri nake idan muka taso daga makaranta zan biyo na ɗauko ki keda su amira kinjiko?"


Da fara'arta tace "To anty Allah kiyaye hanya."


Da ameen ta amsa sannan ta juya zata tafi tanti tace "AFREEN baki sha zumar ki ba yau."


Ba tare da ta juyo ba tace "Kashe na manta kawai sai ta nufi ɗakin tanti ta sha zumar ta fito ta ƙara masu sai ta dawo."


Har ta kai bakin ƙofar falon papa ya ɗaga murya yace "Ki tafi a sannu bana son tuƙin gaganci."


Ba tare da ta juwo ba tace insha Allahu papana sannan ta fita.


Ƙarfe sha biyu na rana su AFREEN suka fito daga aji, jerawa sukayi itama da Hasina suna tafiya suna fira har suka kawo inda AFREEN tayi parking ɗin motar ta, ta buɗe zata shiga Hasina tace "Besty yau zakizo masallaci?"


Murmushi mai sauti AFREEN tayi tace "Mi zai hana besty saide in banda lafiya ko wani cikin ƴan gidan mu abinda ban ma kan mu fatan hakan duk da dai ita lafiya bata samuwa kullum."


Hasina tace "To shikenan besty sai mun haɗu a masallaci, bari na shiga ki ajiye bakin babba ƙofar makarantar dan nasan yanzu direba na bakin ƙofa yana jirana," shiga sukayi su duka sannan AFREEN ta tayar da motar suka bar cikin makarantar, saida AFREEN ta kaita har kusan motar da direba yazo ɗaukar ta sannan taja tatsaya Hasina ta fita tana ƙara jadada mata sai sun haɗu masallaci, sannan taja motar ta nufi makarantar su Zeinab.


12:40 suka isa gida AFREEN na parking motar duk suka fita, shiga falon sukayi da sallama babu kowa a ciki, dan haka duk sai suka kama gaban su, AFREEN na shiga ɗakin ta ta cire kayan jikinta ta saka wata doguwar riga mara nauhi tazo ta dan kwanta saman bed ɗin tareda sauke ajiyar zuciya ta gajiya.


Ƙarfe ɗaya na rana na bugawa AFREEN ta tashi da kwanciyar da tayi ta faɗa toillet don yin wanka zuwa sallar juma'a.


Ta fito cikin shigarta ta zuwa masallaci sai tashin kamshi take, duguwa riga ce baƙa sanye a jikinta da aka yiwa kwalliya da Stone ruwan gold rigar tayi masifar kyau, da hijab ɗin ta kalar golden, takalmin ƙafar ta ma golden ne amma wannan karon plat ne ta saka maras tsini, haka ma niƙaf inta golden ce ita ma, sabida yawan saka niƙaf da AFREEN take yasa kusan kowane color na hijab ɗin tanada kalar niƙaf ɗin ita kanta batasan iya adadin yawan hijab da niƙaf da takeda ba, uwa uba kayan sakawar ta bata iya musilta yawansu, dan sun lumka yawan hijaban da takeda, duk da ana fitar da zakar kayan a kowane lokaci amma kuwa kullum cikin dumka sabi ake ko aje shopping don siyo dogayan riguna da ƙananun kayan dan zaman gida, gashi kuma idan papa ya fita ƙasashen waje ya siyo masu kaya irin na can dan sosai take da riga da wando irin na Pakistan da kuma riga da buje na kanti irin na ƙasashen waje.


Ta tardo su Zeinab ita kawai suke jira dan papa da matan sa har sun rigada sun tafi, haka Fahad da Imran, daga su sai masu gadi da suke jiran su fita su kule gidan dan zuwa masallaci Mamy kawai da mai aikinta ake bari cikin gidan.


A gagwace suka fito suka shiga mota ta tayar da motar suka bar gidan, gudu take sosai sabida ganin da tayi lokacin tayar da sallah ya kusa gashi kuma har Zaria ne masallaci yake dan daga anguwar su zuwa anguwar da masallaci yake ya akwai nisa sosai


Tana zuwa bata matsaya lura da inda zata yi parking ba kawai ta nufi idan maza ke parking ta ajiye tata motar sannan suka nufi cikin masallacin basu daɗe da shiga ba aka tayar da sallah.


Ana idar da sallar malamai suka shiga yin ɗaurin aure da ya gabata ana gamawa mutane sukayi ta watsewa sannu sannu, a ƙa'idar AFREEN ne idan aka ida sallah sai mutane sun rage sosai kamin take jawo ƴan ƙananan ta su fito tare da ƙawarta Hasina dan tafiya gida.


Hakama yau ta kasance saida mutane suka rage yayi sauran ƴan tsiraru sannan suka fito, har taje zata nufar parking ɗin da mata ke ajiye motocin su, Zeinab tayi saurin cewa "Ai anty ba ana kika ajiye motar ba wajen parking ɗin maza kika ajiye ta."


Da sauri AFREEN ta juyo tana kallon ta tareda waro idon ta alamun firgici tace "Ya akayi har haka ta faru oh ni AFREEN ina hankali nane yaje har nakai mota can na ajiye ban saniba? kuma ke Zeinab kina gani amma kikaƙi sanar dani."


Zeinab ta ce "Wallahi anty dan naga kina sauri ne kuma an kusa tayar da sallah shiyasa amma naso faɗa maki."


"To wanzu dai ba wannan ba ta yaya zan ɗauko mota a parking ɗin ƴan maza tsakanin da Allah ya zani inshiga yurin nan, gashi yanzu nasan da su Fahad sun riga da sun tafi gida, da ba sai nasa ya fito man da ita ba."


Dariya sosai Hasina tayi sannan tace "Besty miye abin wani ɗaga hankalin ki haka? kamar wada idan taje ɗaukar motar mazan cinye ta zasuyi, ki kwantar da hankalin ki muje na rakaki ki fitar da motar ki da kanki baki ga mutane duk sun watse ba tana iya yiyuwa ma motar takice kaɗai cikin gurin nasan yanzu haka ma kowa ya fitar da tasa sabida kinsan maza da uzuriruka."


Sai a sannan ne AFREEN ta ɗan ji sanhi a zuciyarta sai tace masu "To ku tafi mu tafi."


Suna tafiya suna fira har sun kusa ƙarasawa yurin parking ɗin kamar ance AFREEN ta ɗaga kanta aikuwa sai ta tsinkaye shi tsaye jigine da motar sa kansa duƙe ya na danna wayar sa da alama wani yake jira, a take gaban AFREEN ya wanke ya faɗi, kawai sai taja ta tsaya, da kallo su Hasina suka bita sannan Hasina tace "Malama lafiya kikayi mana tsaye kokin fasa ɗauko motar ne?"


Da hannu AFREEN ta nuna mata AFREED da ke tsaye jigine da motar sa yana dan ne dan ne a wayar sa sannan ta marairaice tare dacewa "Kinga da namiji a wajan abinda nayi gudu kenan fah."


Duka suka juyawa suka dubi gun da AFREEN ke nunawa. Ɗan ƙaramin tsaki tsussss Hasina taja tare dacewa "Dan Allah malama ki wuce muje idan zakije bakiga ko lura damu baiyi ba harakokin gabansa ya ke sannan kuma daga motarsa sai takice cikin wajen, kuma ba wani abu zai mana ba kawai muje muma muyi kamar ba mu ganshi ba ki ɗauko motar mu fito c'est tout."


Ba dan taso ba haka ta bisu har suka ƙarasa gun, yaji shigowar su wajen parking ɗin amma ko ɗagowa baiyi ba ya kalle su bare yasan ko su wanene haka kawai dai yaji gaban sa ya faɗi, bai kawo komai a ransa ba sai ma cewa da yayi *la'ilaha illah anta subhanakah inni kuntun mina zalumin* , ya karanta addu'ar nan ne sadin jin dayayi gabansa ya faɗi sannan yaci gaba da abin da yake.


Bai an kara ba yaji maganar Hasina nacewa ma AFREEN "Besty dan Allah yau idan kika ajiye ni gida ki shiga ku gaisa da ummi dan ranar nan tana tambaya ta ke kuma ma ki daɗe ba ki shiga gidan mu ba sedai ki ajiye nia bakin get kiyi tafiyar ki."


AFREED na cikin tunanin mi ya kayo mace wajan parking ɗin maza ko dai tare da mijinta ne take, bai ƙarasa tunanin da yake ba yaji zazaƙa muyar AFREEN mai sanyi da taushi da ɗaɗin sauraro ta dakin dodan kunnansa shi a lokacin da tace cikin sanyayar ta "Wallahi kinga ban faɗa wa maman da papa ba cewa zanjima ko zan biya yani gun Kinga faɗa déjà yau mun ɓata lokaci ba mu koma gida ba, yanzu haka hankalin su nacan ya tashi zasu ce ko lafiya har yanzu bamu dawo ba, gashi fa ke har anguwar ali dan sofo mai uban nisa nan zan kaiki kinga ko kamin mukai ki mu dawo mun karancin wani lokaci."


Tunda ta fara maganar AFREED ya juwo yana kallon ta sosai ya shagalta da kallon ta kamar yana ganin fuskar ta, kuma kamar mai son gano wani abu a tatare da ita, sabida saida ya bisu duka da kallon kamin yake yarda da cewa wada dai ke cikin niƙaf ɗin dai itace ke maganar, sabida yaga baki kowace a rufe sannan yana hango yanda bakinta ke motsi daga cikin niƙaf ɗin sosai a lokacin yaji wani abu ya cakar masa zuciya ba tareda ya shirya jin hakan ba, riƙe daidai satin da yaji abin yayi yana mai lumshe idonsa, kwata kwata baiji ɗaɗin shurun da yaji tayi ba a lokacin da ta kai ƙarshen zancen ta............





😜😜😜😜😜😜😜😜😜😜😜😜😜😜😜😜😜😜😜
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸



Écrit


Par



*QUEEN ZEEFAT*



_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_



Wattpad@nazichou





💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/



*_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_*




*Page* : 29 & 30



Tunda ta fara maganar AFREED ya juwo yana kallon ta sosai ya shagalta da kallon ta kamar yana ganin fuskar ta, kuma kamar mai son gano wani abu a tatare da ita, sabida saida ya bisu duka da kallon kamin yake yarda da cewa wada dai ke cikin niƙaf ɗin dai itace ke maganar, sabida yaga baki kowace a rufe sannan yana hango yanda bakinta ke motsi daga cikin niƙaf ɗin sosai a lokacin yaji wani abu ya cakar masa zuciya ba tareda ya shirya jin hakan ba, riƙe daidai satin da yaji abin yayi yana mai lumshe idonsa, kwata kwata baiji ɗaɗin shurun da yaji tayi ba a lokacin da ta kai ƙarshen zancen ta............


"Bawani nan Besty idan kika kira Maman kika faɗa mata cewa zaki kaini gida daga can zaki shiga ku gaisa da ummi ba abinda zata ce dan haka, ki kira maman yanzu nan ki faɗa mata idan kuwa gidan mune ba zaki ba to shikenan har kaini ɗin bana so ki bari zan je na tari adaidaita sahu ya kaini gida ko ma na kira direba kawai," Hasina ta faɗa tana ƙoƙarin bari gun ranta a ɓace.


Da sauri AFREEN ta kamo hannuta da niyyar tsayar da ita gani ranta ya ɓace sannan tace "Dan Allah Besty kiyi hakuri ba gidanku bane banason zuwa wallahi, amma tunda kin matsa bari na kira maman ɗin sai na faɗa mata, ko kuwa mu yaje na sauke su Zeinab a gida sai na gayawa maman cewa zanje gidan ku na dawo daga nan sai mu wuce."


Wani murmushin farin ciki Hasina ta saki sannan tace "Ko kega ƙawata dan shiyasa nake son ki, kinga maman bazata hanaki zuwa gidan mu, gashi kuma tare zamu tafi, kai ummi sai tayi farin cikin gani ki yau ku tafi mu tafi."


Murmushi AFREEN tayi sannan ta buɗe motar duk suka shiga sannan ta tayar suna ƙoƙarin barin gun Ali ya ƙaraso har lokacin nan AFREED bai daina kallon ta ba har ta shige mota, Ali na ƙarosowa yace "Broh na tsayar dakai ko? yi hakuri nasan bakason jira." Firgigit AFREED yayi tare da saurin juyowa yana kallon Ali


Ɗan hararen sa AFREED yayi sannan yace "Dan Allah muje kawai ka wani je kayi zaman ka, ka wani shanya mutane a nan."


Murmushi Ali yayi kamin yake buɗe motar ya shiga mazaunin direba shi kuwa AFREED ya buɗe wajen mai zaman banza zai shiga sai ya juya idan AFREEN suka ajiye mota da zunmar son ya ƙara ganin ta ko da kuwa ba zai samu ganin fuskar ta ba, ko zaiji idan zata ƙara buɗe baki tace wani abu, amma sai yaga wayam aiko sai ya shiga wage wage ko ƙurar motar bai gani ba bale kuma su na cikin motar, cikin zuciyarsa yace to ina sukayi ko sunyi tafiyar su ne ni ban maji lokacin da ta tayar da motar ba har suka tafi, to wacece ita???


Bai kai ga samun amsar tambaya da yake wa zuciyar sa ba ya tsinci muyar Ali nacewa "Wai AFREED mikake jirane da ba zaka shigo mutafi ba, kodai ka fasa tafiya gidan ne?"


Sai a lokacin AFREED ya dawo daga duniyar tunanin da ya lula, tare da ƙarasa shiga motar cikin nutsuwa da kwanciyar hankali sannan ya rufo murfin motar, lumshe idonsa yayi tare da kwantawa jikin kujerar ya shiga tunani yana jin yanda wani abu ke shigar sz ya na ratsa jinin jikinsa, da ƙarfi gabansa ya daɗi a lokacin da ya ke ma kansa tambayar kadai matar aure ce na zauna ina kallon ta Inna lilahi wa'inna illaihi raji'un ya akayi haka ta faru mima ya kaini kallon ta? Ni komi kyau mace ba isheni kallo ba amma na buge da kallon mai niƙaf ma da yanzu haka ko kyau bata shi, da sauri ya furta astagfirllah a tunanin sa a zuciyarsa ya furta kalmar ta istigfari ashe a fili ne sai Ali ya juwo ya kalle sa yaga idonsa a lumshe suke kamin yake maida duban sa ga tit sannan yace "AFREED magana kake?" shiru baice masa komai ba amma yaji abinda ya faɗa.


AFREED ya koma cewa a zuciyarsa "Wacece ita, tanada aure ko kuwa, miyasa ta ajiye motar a parking ɗin maza? a take yaba kansa amsa da cewa amma naji tana cewa Maman zatayi mata faɗa idan taci lokacin da yawa bata koma gida ba, hakan ya nuna ba tada aure kenan, to idan hakane miyasa take saka niƙaf, bata son aga fuskarta ne kokuwa wani kuma salon muna furcin ne irin na mata? amma naga a garin nan mata na son saka niƙaf , to miye manufar su tayin hakan, nikam na tsani naga mace na saka niƙaf sai naga duk munafurci ne da son kallon maza daga cikin niƙaf ɗin, can wani ɓangare na zuciyarsa yace " Wai ina ruwanka da ita daga gamuwa da yarinya ka wani zauna sai tunanin ta kake itada ko saninta bakayi ba, kuma ko fuskarta baka gani ba miye matsalar ka da ita ne da ka wani damu da ita? atake yaji haushin kansa na kallon mi ya tsaya yana yi mata shida bai taɓa ganin mace ba ya zauna yana kallon ta ba ko da wada fuskarta ke buɗe bare wannan, to dafa kamashi tayi yana kallon ta fah, da kawai rainasa zatayi wani kuma abinda ya zuba, shida mata ke kawo kansu gareshi yana ƙin kula su amma shine yau ya bige da kollon wata, watar ma dake cikin niƙaf, ɗan karamin tsaki yaja tare da furta "Ta ma ban haushi." Atunanin sa a zuciyarsa ne ya fali haka amma ashe maganar ta fito fili.


Saida yaji Ali na cewa "Lafiyar ka kuwa frèro sai magana kake kai ɗaya tare da jan tsaki wa ya taɓa minke ne dama tun da nafito daga masallaci naga kana kallon wata mota, ko na cikin motar ne ya ɓata maka rai yanzu nasaka a ne moshi tun na ɗauki number motar sanadin ganin da nayi kana kallon motar sosai da na cikin motar nayi gudun ace ko wani abu yama, tunda nasan zaka iyaƙi faɗa man a nan take har sai mun tafi gida."


Da sauri AFREED ya ɗago daga kwancin da yayi saman kujera tare da buɗe lumsashin idonsa ya ƙurawa Ali su a lokacin da yaji yace ya riƙe number motar dan jin ko dagaske ne ya riƙe number motar, amma yanayin wani tunanin kawai sai ya koma ya kwanta tareda lumshe idonsa kamar mai shirin yin bacci,


Ali kamar yasan abinda ke cikin zuciyarsa yace "Eh na ɗoki numba motar idan da wata matsala ne ka faɗa min a ɗoki mataki tun yuri guda kar ya mana nisa, ka kama fuska kasaka abinda ake rufe baki da hanci karmar wani mai gudun kamuwa da cutar Corona virus, wai kai a dole ba kaso a gane kaine MINISTRE DE DÉFENSE ET DE SÉCURITÉ ɗin da ake yawan nunowa a TV, ba dole mutane su maka abinda sukaga dama cikin rashin sanin matsayin ka ai kaine zaka jawa kanka AFREED da ka bayana kanka babu mai yarda yayi koda hada ido da kai bare harma yayi maka batanci, to faɗa man miya faru? Dan nasan daga ina zan fara neman mai motar."


Hankali kwance cikin gajiya da sauran surutun da Ali yake masa dake mai saka masa ciwon kai AFREED ya buɗe bakinsa yace "Babu komai."


Ali ya sake da baki yana kallon AFREED da ya Koma lumshe idonsa sannan yace "Ai dama nasan bazaka ce komai ba to idan tayi wari munji ɗan rainin wayo kawai."


Shi dai AFREED baice da shi komai ba sai ɗan murmushi da ya saki mai tafiyar da zuciya a duk wanda ta kallesa.


Ali na shirin sake yin wata maganar, AFREED kamar wani me ganin sa shida idanuwon ke lumshe yace "Dan Allah Ali kada ka ƙara cewa komai surutun nan naka nason sakamin ciwon kai haba anyi mutum sai wayan magana."


Hararen sa Ali yayi sannan yace"Eh anje anyi wayan maganar ai surutu ma rahama ne kuma nafi ka kaida kake nan dunkum kamar gumki."


AFREED dai bai ce masa komai ba har suka ƙarasa gida shima Ali bai ƙara magana ba, suna zuwa bakin get ɗin gidan Ali ya dana hon mai gadi ya wangale masu babba ƙofar suka shige ciki, ba tare da bata lokaci ba Ali yayi parking ɗin motar suka fita tare da nufar ɓangaren tanti, suna shiga suka tardo kowa na kan dinning suka kaɗai ake jira a fara cin abincin, ba tare da sun tsaya komai suma suka nufi dinning tare da yiwa tanti sannu da gida sannan suka zauna, Khadija ta tashi tayi servir ɗinsu, shiru gun yayi ba kajin motsin komai sai na spoon, can tanti ta ɗaugo tace "AFREED mi ya tsayar daku naga yau kun jima har hankali na ya fara tashi wallahi."


Murmushi yayi tare dacewa "Wallahi wannan banzan ne ya tsayar da mu ya je ya buɗi guri yayi zaman sa a cikin masallaci ban ma san miye yayi aciki ba."


"Eh anje anyi ko zakayi wani abune, mi ya hana da kaga najima kaƙi tuƙa motar kayi tafiyar ka?" Ali ya faɗa yana yiwa AFREED murmushin mugun ta.


AFREED yace "Au haka ka faɗa to ba laifi ai zaka gani."


Su Farisa da su Khadija nason yin dariya amma babu dama sabida gudun kada AFREED ya watsa su, sai Umar da tanti ne suka ɗan dara sannan Umar yace "AFREED da Ali kamar kusu da mage kuke kwata kwata ba ku iya zama gu guda ba kuyi barkwanci ba, shirman nan da kukeyi ko su Fariya basa yin sa."


AFREED dai shiru yayi baice komai ba sai ma miƙewa da yayi tare dayin gaba abinsa batare da ya gama cin abincin ba, saboda tunda ya ji muyar AFREEN daga masallaci yake jin kansa ba normal ba, duk jikinsa yayi masa sanhi ya ma rasa mike masa daɗi, gashi yama rigada ya manta da yaji zazaƙa muyar wata a masallaci, bai taɓa kawo cewaba rashin ƙarfin jikinsa da bayaji ba yana da nasaba da jin muyar AFREEN dayayi baisan muyar

Please Login or Register in order to submit comment