Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganin muguwar kama da matar take da AFREEN ɗin, a take zuciyar sa ta fara raya masa cewa kodai AFREEN ce matar da aka aura masa ɗin, amma ina inda itace ai da ba haka ba kawai ta fara maya kizo ne da duk abinda ya gani sai yaga kamar ita.


Hardai Momy Jannah ta gama masifar ta suka tashi sukayi tafiyar su Ali dai na ta masa dariya a hanya yana cewa ashe dangin fitina aka aura maka.



Dadare aka shirya AFREEN cikin wata irin narkaka shada pink kalar kayan da aka saka mata a ɗakin ta da kuma painting ɗin dake ga gidan, shada ta sha aiki blue 🔵 Masha Allah da AFREEN da shada duk sun haɗu iya haɗuwa ta saka takalmi blue 🔵 gyale blue 💙 sarka blue Kai komai blue 💙 aka mata kayin kyau wanda AFREEN tayi ɓata lokaci ne dan ko ba kwalliya ita mai wani irin ni'imtacen kyau bare yanzu da aka haɗa da kwalliya bare ita da bayi take yi ba to ya kuke ganin zata zama a daren, kowa sai santin kyau da tayi ake Masha Allah.


Angaye basu jima ba suka zo ɗauka amarya, da ke ta zuba wani uban kamshi mara misali na turarukan ta da aka haɗa mata iri iri na barebari na buzaye na larabawa na Ethiopia gasu nan dai ba'a cewa komai sai fatan zaman lafiya da ango.


Ana ɗaukar amarya gidan surukan ta aka fara kaita inda suka samu tarba ta karamci kamin ake nufa da ita gidan wooow Masha Allah gidan AFREEN ya haɗu iya haɗuwa komai na gidan pink sai ratsin blue da ke akwai kaɗan kaɗan shoglass da ke akwai ta tura ta kai bakwai huɗu saman uku ƙasa.


Ƴan kan amarya basu wani jima ba suka yi tafiyar su bayan Momy Jannah da su Aunty fauziya sun ƙara mata huɗubar Zama Da miji yanda zata kama abunta hannu bibbiyu tana kuka na fita hankali har suma sai da suka koka dan ta basu tausayi matuƙa amma babu yanda suka iya dole su tafi su barta dan suma duk haka suka ji Fanna da Hasina kaɗai suka zauna cewa har abokan ango su zo sai su tafi dasu.


Bayan wani lokaci ango da abokansa suka shigo suna ta raha ango na zaune kusa da amarya bai nunawa kowa cewa baya sonta ba amma a ɓoye kamar ya shaƙeta ta mutu yakeji, su Hasina zasu fita ta riƙe tana ta kuka tana cewa dan Allah kada su barta har yanzu yakan rufe ba'a buɗe ta ba.



AFREED ya dawo daga rakiyar abokansa bai zarce ko ina ba sai ɗankin da AFREEN ke ciki har yanzu da mayafi liƙe da fuska ta da ƙarfi ya ja mayafi ya yi jifa dashi gefe yajuwo da karfi yace "Kai sai....


Ai ba ƙarasa faɗar abinda yayi niyyar faɗa ba idon suka sauka a kan kyakkyawar fuskar AFREEN da ta sha kuka take cikin yinshi ma zaro ido yayi ya rasa bakin magana da shi niyyar sa ya mata wulakanci amma mi sai ya Wada bai taɓa tsammanin gani ba da sauri ya koma kusa da ita ya zauna jikinsa har rawa yake, ya kamo hannun ta, ita tunda suka yi ido huɗu kukan ta ya tsaya cak tana wani mugun mamaki. AFREED cikin i......ina..... Yace "ke..... ce ..... ko gizo kike min AFREEN ya muza idonsa ya ƙara murzawa ya buɗe su ga fuskar ta ya gudun kada ace mafarki ne yake.


Ita ma AFREEN cikin rawa jiki tace "Ya akayi haka."


Cike da farin ciki AFREED ya mata yara irin runguma mai kyau duk ya rikice ya rasa ma mi zai faɗa, ai sai hawaye suka shiga ganga to masa daga cikin ido yakai kusan minti goma yana rugume da ita kamin ya saketa ya ɗaga hannu sama yana gode ma Allah da hawaye tafi a fuskar sa, hamdalah sukayi su duka ta rada yiwa iyayen su godiya da suka yi masu wannan haɗin sunata kwarara ma iyayensu addu'a.


Da farin ciki ya ishe su sai suka tashi suka nufi toillet suka ɗauro alwala suka yi nafila raka'a biyu ta suna godewa Ubangiji sannan ya fita ɗauka kazar da Ali ne ya siya guda biyu ya bashi ɗaya ba dan ya so ba ya amsa ashe zata mashi rana, ya shiga kitchen ya ɗauko plet da cofi ya kawo masu har ida take a zaune ta kasa kara ɗaya ido ta kalle saboda kunya, da khair ma yasa mu ta ci kazar kaɗan dan ya ɗan lalaɓa ko son wani abu ya taɓa baiyi kamar wata jinjira.


Har dai suka gama ya umurce ta da ta je tayi wanka shima zaije yayi ya dawo.


Yana dawowa har tayi wanka ta shirya cikin kayan baccin ta haye gado ta rufe da da bargo Dan a garin a dan sanhi ga kuma sanhi ac, shima ya zuwa bai tsaya komai ba ya sama ɗakin key ya kashe huta ya dawo kusan ya kwanta tare da sakata cikin jikinsa ya na shafa gashin kanta tanjin shi ta lahe dan duk a tsorace take, da shafa ya koma sha fa mata kunne daga nan ya kuma ga bakin har dai ya kasa jurewa ya shiga aika mata wani zafafen kiss daga nan kuma salo ya canza, a ranar dai AFREEN ta wahala iya wahala Allah ne ya kare bata suma ba dan sai AFREED ya maida ta cikakar mace sannan ya raga mata badan ya kaushi ba shima kiran sallah asuba ne ya fargar da shi cewa ya illata ɗiyar mutane Sannan kuma ya koma lalashi.


Da safe Momy ta ai ko masu da abun kari duka gidan biyu wato gidan Ali da AFREED.


Su Hasina suka zo mata bankwana anan take shaida masu cewa ashe masoyin ta papa ya aura mata.


Sati biyu da auren suka shirya sukaje gidan su AFREED gaida iyayen sa nan Momy ta sakata ɗaki ta haɗo mata kayan mata da turaruka irin nasu na barebari.


Bayan shekara takwas wata class lady ce na tsikaya cikin wani katafaren gida wanda dukan shi glass ne ina ƙara kura ido na hango AFREEN ce tayi ƴar ƙiba ta ƙara kyau fatar jikin sai sheƙi yake dan hutu wannan form ɗin tata ta kara fitowa, da wasu kyawawan yara guda uku namiji biyu mace ɗaya wanda tun haihuwa ta fari ta haifesu shi bata ƙara haihuwa ba sai yanzu da take ɗauke da tsohon ciki


Hasina tayi aure Ita a nan cikin garin Niamey da yaranta biyu Fanna kuma tana Dubai babban ɗan Momy Jannah ya aure da yarta guda sai zeinab ita ɗan Momy Jannah na biyu ya aure ta suna Turkiya, Fariya da Farisa duk sun haihuwa Farisa ta samu ƴan biyu duk mata ita kuwa Fariya ta samu namiji Khadijah matar Ali ita ma yaranta biyu mace da namiji zeinab ana ɗauke da tsohon ciki.


Maryam tayi aure da yaranta uku tun da tana saurin haihuwa


Umma zeinab ta rage masifa da ma ita sharin shaiɗan ne amma ku gidan malamin tsibo bata sani ba bare gidan boka ta nemi alhaji Sadisu da Arahamat gafara yanzu suna zaman lafiya.


Ita kuma tanti daren da AFREED ya sadu da AFREEN ta haukace ta bi duniya babu wanda yasan ida take ta girbi abinda ta shuka


AFREED da AFREEN kullum sai ƙara son juna suka cikin aminci


*ALHAMDULILAH*


*ALHAMDULILAH*


*ALHAMDULILAH*




Anan na kawo karshen wannan littafi Mai taken *ZAMBA CIKIN AMINCI* kuskure da nayi Allah ya yafe mani sai mun haɗu a sabon littafi na dai zai zo na ba da jimawa ba.




*Bisallam*





*Sai mun haɗu a sabon littafi na ina ma kowa fatan alkairi*


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment