Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*QUEEN ZEEFAT*


_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_




*Wattpad@nazichou*




💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/



*_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_*



*Page* : 39 & 40


Daga haka ya ɗoke idonsa akansu sabida sosai ransa ya ɓace yarasa dalilin hakan gani yake idan yaci gaba da kallon su zai iya aikata abinda ba shineba kuma hakan ba girman sa bane jin yanda zuciyarsa ke suya ya saka shi barin gun ya nufi motar sa ya shiga ya tayar tare da barin gun.


Saida Ali ya waiwaya yaga babu AFREED babu dalilin sa kawai sai girgiza kai yayi dan ya san da tafiyar sa ne yayi, da zasu koma gida kuwa tanti A'ishah motar mijinta ta shiga da Farisa da kuma da Amal da kuma aouta tanti, tunda wanda ya kawo su yayi tafiyar sa.


Haka taro ya watse lafiya kowa ya kama gaban sa, su AFREEN na zuwa gida duk suka nufi ɗaki kowace ta watsa ruwa tayi sallah mangariba sannan aka fito cin abincin, suna tsaka da cin abinci papa yace "To AFREEN kujerar Makka da kika samu har guda biyar ya zakiyi dasu?"


Saida ta ɗan nisa Sannan tace "To papa da cewa nayi na bawa babban malamin islamiyyar mu guda sannan kaida maman guda guda sai kuma ɗaya zan bawa anma (wato mahaifiyar Fanna kawar AFREEN dake Diffa) ɗayar kuwa kaka na bawa (wato Hajiya Zakiya) sannan cikin kuɗin dana samu zan biyawa kaka malam (mahaifin Arahamat) shima kujerar Makkah.


Murmushi papa yayi yace "Masha Allah yarinyar kirki Allah maki albarka hakan da kikayi yayi dadai, amma keda aka bamawa miyasa baki fitar wa kanki ba AFREEN wannan kyautar kice yaci ace kema zaki ɗauki ɗaya duk ba zuwanki na farin bane ke kije a matsayin kujerar dakika bamawa Hajiya in kuwa kiyi niyya ne kin bata to kema kuwa zaki koma haji na biyu bana Insha Allah, zan biyawa kowa a gidan sai muje tare baki ɗaya banda ni da mahaifiyar ki kuma da Hajiya, kinga an samu ragowa kujera uku kenan tunda mu uku kiyimana kyautar kujerar haji yanzu baki ɗaya zamu tafi kowa ya sake sauke farali hada Ufadi (wato matar mahaifin Arahamat maman AFREEN idan masu karatu basu manta ba) sannan itama Fanna hada ita da kuma mahaifin ta kenan kinga su ukun duka, da kuma Hasina itama duk da ta taɓa zuwa yanzun ma zaku koma tare kamar yandata kasan ce farkon tafiyar ku Insha Allahu da Firdaoussi ɗiyar yaya Adamu tunda duk tare kuke abukan junana ne ya kamata ku koma tare."


Fanna ƙawar AFREEN najin haka ta tashi daga kan kujerar da take zaune tana cin abinci da hawaye farin ciki a fuskarta ta durƙusa gaban papa tana kuka tana godiya tace "Allah sarki ashe zanga wannan rana dan haka aka ce kada mutum ya fida da rai daga rahamar Ubangijin, ban taɓa tunanin wata rana zanje haji ba sai gashi sanadiyyar ƙawance Allah ya haɗani da mutane kirki masu su jin tsoron da ƙaunar mazon sa, papa mun gode mun gode mun gode Allah saka da alkairi, Allah ƙara lumka arziki mai albarka, Allah ya shirya maku ƴaƴan ku zuri'a ku baki ɗaya, Allah rufa maku asiri duniya da lahira, Allah saka maku da mafificin alkairi, ya biyaku da gidan aljanna, Allah hanaku jin kunyar duniya da ta lahira, Allah sa ku fi haka, ya ya kauda fitina da tashin hankali a tsakanin ku, ya Allah na roƙeka duk mai neman wannan zuri'a da shari ko wani mugun abu Allah ka da ka bashi iko ko kayi gaggawar mayar masa da kayanshi na gode papa iyayena ma sun gode godiyar ma ta gode," Sannan ta juya gun AFREEN ta ƙara fashewa da kuka tace "Ƙawata ƙawance na dake alkairi ne Allah kaɗai yasan miye dalilin yaɗuwar mu har muka ƙulla zumunta sabida ni na ɗaɗe da daina kallon ki a matsayin ƙawa sai ƴar uwa ta jini wada muka fito ciki ɗaya duk duniyar nan in aka fida maki iyayena to ban da kamar ki ƙawata sosai nake ƙaunar ki ko rayuwa ta zan iya baki wallahi samun mutane irin ku sai an tona na gode da kyaut........


Da sauri AFREEN ta rufe mata baki tare da tayar da ita tsaye tace ."Haba cœurly miye haka dan Allah, anya kuwa kin ɗoke a yanda kika faɗa? idan hakane miye abun wi mana wannan godiyar ni na ɗauke ki ne kamar yanda na ɗauki anty Fauziya ko anty Khairat, mun riga mun zama cikin ɗaya ki daina haka."


Papa ma cewa yayi "Gaskiya dai kam Fanna ni zaman mahaifin ki nake ba wani abu bane idan hakan ya kasance, je ki koma gun zaman ki ki ƙarara cin abincin ki kinjiko ƴata Allah maku albarka."


Duka wanda ke nan gun cin abincin saida ya ce ameen har anty Fauziya da tazo gun saukar tana jiran mijinta yazo ya ɗoketa, amma banda umma da tanti suda tunda papa yace zai biyawa Fanna da mahaifin ta Makkah da kuma kujerar da AFREEN ta bawa mahaifiyar Fanna ɗin suke ta hararen Fannar da jin haushin ta.


Suna kammala cin abincin suka koma falo sabida gajiyar da suke yau masu aikin gidan ne suka tatare dinning ɗin suka gyara wurin duk da ba wani ɓata sa sukayi ba, basu jima da zama a falon ba mijin anty Fauziya yazo tare da yaranta biyu sukayi ta wasa da dariya kamin suke masu sallama su bar gidan.


Papa ya kalli anty Khairat yace "Khairat yaushe kika zo ne? dan mu kam sai da muka ganki a wajan saukar nan."


Murmushi tayi tare da sade kanta ƙasa sannan tace "Tunjiya misalin ƙarfe 8 na dare nazo papa, amma sai na sauka gidan anty Fauziya sabida inason yi maku bazata sabida AFREEN dalilin kuwa shine ta matsa min da tambayar zanzo saukar su nace mata a'a shiyasa nace sai kawai kun ganin kamar daga sama ta kalli AFREEN ta dariya."


Itama AFREEN dariyar tayi sannan ta mata kallon zan rama."


Papa yayi murmushi yace "To masha Allah Allah maku albarka ya karatun naki.


Anty Khairat tace "Ai na kammala dady yanzu kusan sati biyu kenan sakamako ne kawai nake jira ya fito sai na koma na karɓa, abinda yasa ban dawo gida da yuri ba Tanti Maryam ta tsayar dani yanzu ma sabida saukar AFREEN ta bari nazo


(Idan masu karatu basu manta ba Maryam ƴaƴa mahaifin su AFREEN ce wato Alhaji Sadisu wada ke aure a garin Niamey, dakuma Fatima mai aure Mali)


Ba wani jimawa sukayi a falon ba suka bar iyayen su anan suku suka yada zango a ɗakin AFREEN, suna shiga suka zazauna bakin gado suna sakin murmushi, wata irin ajiyar zuciya Fanna ta sake sannan ta ɗoki wayar ta tana cewa "Bari na sanarwa su anma wannan abin alkairi dana farin ciki nasan idan sukaji wannan labari yau sedai kwana ɓarawo ya kwashe su."


Murmushi sukayi AFREEN tace "Ki bari har da safe mana."


Fanna tace "Cœurly ba zan iya ba nidai ki bari na faɗa ina bahaka ba ba zan iya bacci ba.


AFREEN tace "To ai shikenan ki kira su ɗin."


Kamin takai gayin kiran Khairat ta riƙe mata hannu tace "Dakata ƙanwata na faɗa maku wani abin farin cikin sai ku ji daɗin gaba ɗaya," hannun AFREEN ta kamo da hannunta na dama shi kuwa na Fanna na cikin hannuta na hagun sannan ta koma cewa "ina farin cikin gayamaku cewa Ahmad yace na faɗawa papa jibi zai turo iyayen sa gidan ma'ana zasuzo neman aurena." Khairat ta faɗa da ƙayatacan murmushi kwance a fuskar ta.


Da sauri AFREEN da Fanna suka ƙwace hannunsu daga nata suka rugumeta suna ihu farin ciki, kuma ihu ba wani mai sauti ba mai cike da hankali da nutsuwa.


"Alhamdulilah" suka faɗa a tatare sannan suka saketa baki yaƙi rufuwa su AFREEN sai kwasa dariyar farin ciki take ta ma kasa yin magana sai kallon Khairat ɗin take."


Fanna ce tayi ƙarfin halin cewa "Barka barka anty Khairat gaskiya na tayaki murna sosai farin cikin da nake ciki yau baya musultuwa gaskiya Allah ya tabbata mana da alkairi, ashe mun kusa shan biki ehe, kai Allah kaimu wannan rana akwai didima ashe, fatan alheri anty mu," sai suka ƙara rugumeta suna ta farin ciki.


Sai da sukayi mai isarsu sannan suka saketa, sai a lokacin AFREEN ta samu damar magana tace "Anty miyasa baki faɗawa papa dazun ba da muna falo ana hira?"


"Kunya nakeji AFREEN kedai zaki faɗa masa, nikam bana iyaba."


"Hakane kuwa ko ni idan nawane zanji kunya faɗa da kaina bari naje na faɗa masa yanzu tunda dare bayi sosai kuma a kira anty Fauziya itama a sanar da ita." AFREEN ta faɗa tana ƙoƙarin tashi ta fita.


Da sauri Khairat ta riƙo hannunta tace "Ke kuwa sister ki bari hada safe man irin wannan zazari haka."


Fanna tace "A'a antyn mu taje ta faɗa tun yanzu a bari ya huce shike kawo rabon wani gara ayita ta ƙare."


AFREEN tace "Ah ki barta ni kam yau din nan zan faɗa wa papa duka yanzu ƙarfe tara tana yiyuwa ma papa suna nan a falo." Ƙwace hannunta tayi tayi gaba abinta.


Tana shiga falon tayi sa'a papa na zaune shida umma suna hira tare da kallo, sallama tayi aka amsa mata sannan ta nemi guri kusa da papa a saman kafet ta zauna tare da duƙe kanta bata ce komai ba.


Papa ya zuba mata ido na kusan sakan talatin sannan yace "AFREEN ɗin papa yi magana mana nasan abu mai mahimmanci ya kawoki nan gashi kuma na hango farin ciki luluɓe a fuskar ki."


Ɗagowa tayi ta kalli papa tare da sakin murmushi sannan tace "Dama papa Ahamed ne ya cewa anty Khairat ta faɗa maku jibi iyayensa zasuzo neman aurenta shine tace tana jin kunyar faɗa nikuwa sai nace ta bari zan sanar da kai." Ta ƙarasa faɗar maganar da murmushi kwance a fuskarta.


Aiko papa ya washe baki yana ta fara'a cewa yake "Alhamdulilah alhamdulilah alhamdulilah Allah abin godiya kai masha Allah, to madala Allah ya kaimu jibin da rai da lafiya naji daɗi wannan labarin."


Kamin AFREEN tayi magana umma tace "Ah da ita baza tayi faɗa ba saike ƴar rashin kunya ko kika zo kika faɗa to ya maki kyau."


Keda ke can AFREEN bata ma ɗago ta kalle ta ba bare tayi tunanin zata tanka mata sabida tariga da ta saba da halin umma indai itace wajenta batayin daidai.


Papa ya kalli AFREEN yace "Tashi yi ta fitar ki kin jiko ƴar albarka, ba musu ta mike ta koma ɗakin ta, shi kuwa papa ya ɗauki waya ya kira ya'yan sa Adamu ya sanar dashi cike da farin ciki ya taya papa murna sannan suka ɗan taɓa hira kamin sukeyin sallama, haka ya kira maman yace ta sauko kasa yana son ganin ta, itama tanti ya kirata yace ta fito zasuyi magana, batare da jimawa ba duk suka halar a falon nan yake sanar masu abinda AFREEN ta faɗa masa cike da farin ciki suka taya juna murna, amma ko abinda ba'aso umma bata faɗa ba itama tanti da kaga yanda take barka kasan bata kai ciki ba, daga bisani kowa ya watse ya nufi nasa ɗakin.


Itama AFREEN tana shiga ta sanar dasu abinda papa ya faɗa sannan Fanna ta kira iyayenta ta sheda musu cewa sun sami kujerar Makkah farin ciki gun su ba'a magana ranar kam yuni sukayi hira yanda hajin nasu zata kasance sannan tace da safe zata kira mahaifiyar AFREEN da mahaifin nata suyi masu godiya shima baban Fanna yace zai kira papa yayi masu godiya daganan aka basu AFREEN suka mata godiya tare yiwa Khairat fatan Allah sa alkairi.


Fanna na gama wayar, AFREEN tace a kira anty Fauziya a sanar da ita, Khairat tace "Ai tariga kowaji."


Daga nan suka ci gaba da fira sai wajen ƙarfe 11 na dare kanan sukayi shirin bacci, yau Khairat a ɗakin AFREEN zata kwana AFREEN da Fanna ke kan bed ita kuwa tana saman wata ƙatuwar matala tayi ɗai ɗaya, AFREEN tayi addu'a ta kwanta tare da rumtse idonta ina sai bacci yace baya da yuri ga idanunta, dalilin kuwa shine daga ta rufe idonta sai taji cikin kunnuwanta maganar AFREED na dawo mata a lokacin da yake ce mata "Yakamata ki bar gun nan gaskiya sabida idon kowane gardi akanki yake duk da niƙaf ce a fuskar ki hakan bai kamata ba kowa na kalleki." Maganar nan ta kasa barin dodon kunnanta, kuma ta kasa bacci dan tana rufe idonta take jin maganar na dawo mata cikin kunnanta sai juyi take ta rasa mike damunta, har ƙarfe 1 dare tana kwance ta kasa bacci kawai sai ta tashi ta shige toillet ta ɗauro alwala, ta fito ta saka rigar ta doguwa ta sallah da babban hijab ɗinta ta kabarta sallah duk da lokacin tashinta sallar dare baiyi ba, amma haka ta dake tanata jero nafilfili dalilin bacci da ya ƙwaracewa idonta har saida aka yi kiran sallar farin sannan kwana ɓarayo ya ɗoke a nan saman dardumar.


****** ****** ******

Da kyar da taimakon Allah AFREED ya kai gida dan sosai zuciyarsa kemasa zafi kuma ya rasa dalilin haka, ya isa gida yayi parking ɗin motarsa ya fito ya nufi ɓangaren su direct ɗakin sa ya nufa ba tare da ya tsaya komai ya rage kayan jikin sa ya faɗa toillet ya sakar ma kansa shower 🚿 na ruwa masu sanhi dan so yake zuciyarsa tage zafin da take masa amma ina hakan bai samu ba har sai da ya gaji da dukan da ruwan kemasa ya fito dai lokacin ana kiran sallah magariba da sauri ya shirya cikin doguwa rigar sa ta zuwa masallaci yafito dan tafiya masallaci daidai lokacin su Ali da kowa da kowa suka shigo gidan, tsayawa ya masu nuni hannu cewa masallaci zai tafi ana shirin tada sallah, ba tare da ya tsaya jin amsar su ba ya nufi masallacin dake kofar gidan.


Ali da Umar da mijin tanti A'ishah da sauri suka nufi cikin gida dan ɗauro alwala ba tare da sun jima ba suka fito sai masallaci dan har an tayar da sallah.


Haka tanti da ƴan matan ta suma suka shiga suka fara sai gabatar da sallah suna kammala suka baje kan bed suna sauke numfashi gajiya, Fariya ta fara tashi ta nufi toillet tayi wanka sannan Khadijah tana fitowa Farisa ta shiga, haka Amal da ummi suna nasu ɗakin suna hutawa, suna gana shiryawa suka gabatar da sallah isha'i sannan gaba ɗayan su suka dawo falo dukan su a saman kafet suka zube sannan suka shiga hira suna cikin hira ne Farisa ta kalli Khadijah tace "Sister yau naga wata halitta dama akwai mutane masu mugun kyau kamar aljanu wannan yarinyar kyau ɗinta yayi mungun bani tsoro dan ko a India samun mai kyau irin nata sai an tona duk da tana zubi da indiyawa sabida idan ta shiga a cikin su ba za'a gane cewa ita ɗin ƴar Niger ce kuma ƴar maraɗi, amma dai mamanta ba'indiyace shi kuwa mahaifin ta balarabe ne ko? dan gaskiya sai in wannan yaren ne guda biyu suka haɗu har za'a samu damar samun mai kyau irin ta, lokacin da idona ya sauka kanta wallahi har saida na zabura kaɗan ya rage na zuba da gudu sai naga mutane nata zuwa wajen ta suna hoto sannan na yarda da muntun ce ba aljana ba, kuma danaga tayi karatu, ke ita har muryar ta daban take da ta kowa wallahi kinji yanda take sakin karatu cikin sanyayar ku zazaƙa muryar ta sosai yarinyar ta birgeni dubi fah ko ƙwayar idonta chocolat color ne.


Murmushi Khadijah tayi tace "AFREEN kenan kikenufi ai nima sau ɗaya na taɓa ganin fuskarta sai yau na biyu sabida kyau dake gare take rufe fuskarta ita da kanta tsoron kyau ɗin ta take har ƴan gidansu suna mamaki shi, kuma batun babanta balarabe ne ko mahaifiyar ta ba'indiyace ban sani ba wannan, abinda na sani shine mahaifin ta haifaffen garin Mali ne amma bansan mahaifiyar ta ko wace irin ce ba shima dalilin ƙanwarta Zeinab na sani tunda da ita muke gaisawa duk da ita AFREEN ɗin muke sa'a guda da ita, kuma wallahi babu ruwanta, gata da son mutane ga mutunci ga kamala uwa uba tsoro da addini da masu zama da ita sunce idan kana tare da ita to wallahi ba zaka taɓeba, sosai nakeson ƙawance da ita to ba sosai muke haɗuwa ba shiyasa, ai AFREEN tayi a rayuwa yarinyar tanada hankali sosai ga nutsuwa kuma ita kowa nata ne."


Amal tace "Wallahi anty Khadijah nima dana ganta saida naji tsoro gaskiya tanada masifafen kyau mara misali."


Farisa tace "Da garin nan nake da sai nayi ƙawance da ita wallahi."


Fariya tace "ina ma ya AFREED zai ganta yace yana sonta daga nan idan ta yarda sai ya aureta ta haifa mana yara masu kama da ita gaskiya da munji daɗin samun ta cikin zuri'armu kodan kyawawan halayen ta wallahi, dan na lura AFREEN ɗin nan matar manya ce iri su ya AFREED ɗin dasu ta dace Allah ba yayan mu ita ameen."


Khadijah har ta buɗe baki zatayi magana , kamar ance ta juya sai taga ga AFREED tsaye kusa da su, Ali da Umar da mahaifin sa suna ƙarasowa cikin falon, ganin Khadijah tayi shiru yasa su ɗaga kawanan su dan ganin miye yasa ta yin shiru suna haɗa ido da shi ya watsa masu wani uban harara, da sauri duk suka sada kansu suna muzurai kamar munafukai daga nan kowa ya shiga taitayin sa.


Basu wani ɓata lokaci ba a falon ba tanti A'ishah ta fito itama, sannan masu aikin gidan suka kawo masu abincin nan saman kafet gaba ɗaya suka gewaya suka ci abinci.


Suna kammalawa kowa ya nufi ɗakin shi, yau basu tsaya fira ba sabida gajiya da suke da.


AFREED na shiga ɗakin ya koma shiga toillet ya watsa ruwa sannan ya fito yayi shirin bacci cikin sanhin jiki duk yau jinsa yake wani irin, wayoyinsa da ke saman kujera dake cikin ɗakin ya ɗoko sannan ya nufi bed ɗin sa tare da kashe hutar ɗakin sannan ya ƙara ƙarfin AC dan mugun zafi yake ji kamar yanda zuciyarsa har yanzu bata daina yi masa zafi ba yana cikin yin addu'a shiga bacci wayarsa da itace duk wani ɗan uwansa ko iyayensa ke samun sa, itace ta ɗauki rururi, kollon wayar yayi ganin wanda ke kiransa bai sa ya daina addu'ar ba saida ya kammala sannan ya ɗauki wayar da niyyar maida kira sai ga wani kiran ya shigo, ɗoka yayi ya ƙara a kunan tare dayin sallama, ana amsa sallamar yace "Dady ina wuni, anyuni lafiya, ya gida, ya Momy, da fatan duk kuna lafiya?"


Dady yace "Lafiya lau AFREED da fanta kuma kuna lafiya?"


"Lafiya lau dady."


Dady yace "To madala yaushe ne zaku dawo."


AFREED yace "Jibi insha Allahu."


"To Allah kaimu, amma inason kafin ku dawo kuyi ƙoƙari kuje gidan aminina Alhaji Sadisu ku gaido shi na faɗa masa kana cikin garin nan kuma har kuna shirin dawowa shine yayi ta faɗa miyasa da zaku zo ba a faɗa masa ba aida kun sauka gidan sa, indai taiƙaice maka dai ya nuna min baiji daɗin rashin sanin zuwan kaba shine yace na bashi adress ɗin gidan A'ishah shi yazo ya ganka kamin ku tafi sabida rabonsa dakai tun kana jinjiri da yazo sunanka , sai kuma inya haɗu da hoton ka a TV, shine nace masa ya bari kai zaka zo har gida ka sameshi."


Sedai AFREED ya ɗan nisa sannan yace "Inshallah dady gobe zamuje kwai ka turoman da adress ɗin gidan sai muje nida Ali da Umar insha Allahu."


Murmushi mai sauti dady ya saki wanda har saida AFREED ya juwo shi sannan yace "yawa ɗan albarka yanzu zan turoma da adress idan Allah ya kaimu goben sai kuje, sai da safe Allah maku albarka.


Da ameen AFREED ya amsa sannan yace Allah kaimu safiya lafiya."


Daga nan dady ya kashe kiran komin minti 1 ba'a yi ba sai ga soƙon adress ɗin gidan Alhaji Sadisu ya turo masa ta whatsapp, yana duba bawa sai ya kashe data ya kwanta ai yana rumtse idonsa..............














Sai kunji ni a page ta gaba😜😜😜😜
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


Écrit




Par




*QUEEN ZEEFAT*




_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_




*Wattpad@nazichou*



💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/





*_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_*




*Page* : 41 & 42


Daga nan dady ya kashe kiran komin minti 1 ba'a yi ba sai ga soƙon adress ɗin gidan Alhaji Sadisu ya turo masa ta whatsapp, yana dubawa sai ya kashe data ya kwanta ai yana rumtse idonsa ya fara hango photon AFREEN lokacin da ta ke kallon KAMAL tana sakar mai wani ƙayatacen murmushi ana masu hoto, da sauri AFREED ya buɗe idonsa yana sauke ajiyar zuciya batare da ya tashi daga kwanciyar da yayi ba, ya ɗauki kusan minti 5 a haka kamin yake kara rufe idon nasa amma ina hoton AFREEN tana yiwa KAMAL murmushi ya ƙi barin ƙwaƙwalwar da idon AFREED, bacci yake son yayi amma hakan taƙi samuwa, ya ɗauki dogon lokaci a haka kamin yayi shawarar shiga toillet ya ɗauro alwala dan gabatar da sallah nafila saboda samun saukin raɗaɗin da zuciyarsa ke masa.

Shima a nan saman darduma bacci ɓarawo ya kwashe shi, washegari wajen misali ƙarfe 12am AFREED da Ali suka kuno hancin motar cikin anguwar su AFREEN ba tareda sun sha wahala ba suka samu wani yaro ya nuna masu gidan Alhaji Sadisu wato maihaifin AFREEN suna kawowa bakin ƙofar gidan Ali yaja ya tsaya tareda dana hon da sauri mai gadi ya fito tareda ƙarasowa kusan motar yana tambayar su wayesu sabida bai sheda su ba kuma yaga bakuwar fuska, haka motar ma bai taba ganita cikin gidan ba.


Murmushi Ali ya sakar ma baba mai gadi danji yana tambayar sa wajenwa sukazo kuma wasu ke nema sannan Ali yace "Baba ina yuni an yuni lafiya? Ai wajen mai gidan mukazo ko yana ciki."


Baba mai gadi najin haka ya saki murmushi yace "lafiya lau yaro, aya wajen Alhaji kukazo kenan ai kuwa yana ciki kun taki Sa'a dan ina gani yau ko fitama baiyi ba amma yasan da zuwan naku ko shiyasa bai fitaba, ku bari na buɗe maku ƙofar sai ku shigo daga ciki."


Shidai Ali baice masa komai ba, sai murmushi da ya sakar masa, juyawa baba mai gadi yayi yaje buɗe masu kofar, ba tare da ɓata lokaci ba Ali ya dana hancin motar su cikin gidan, daidaita motar yayi yayi parking ɗin ta sannan suka fito har yanzu shi AFREED babu abinda ya faɗa zaki iya cewa ma baya gun, Ali ya kalle shi yace "Ɗan uwa to yanzu waye za mu aika yaje ya sanar da zuwan mu?"


Hararar sa AFREED yayi sannan yamashi nuni da ido cewa ya tambayi mai gadi, murmushi Ali yayi yana girgiza kai cikin zuciyarsa yace "Ah yau abubuwan ke bisa kai ko maganar ma ba za'a min ba."


Bai ƙarasa tunanin da yake ba yaji baba mai gadi nacewa "Ku ƙarasa daga ciki mana."


Da sauri Ali ya juyo gareshi yace "Yawa dama baba munaso a sanar dashi mun ƙaraso, yasan da zuwan mu amma bamu faɗa masa cewa yanzu zamu zoba ace masa ɗiyan abokinsa ne Sumana."


Baba mai gadi

Please Login or Register in order to submit comment