Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suma ƴan biyu na ganin haka gaba ɗaya suka faɗa jikinta suna kuka tana tayasu an rasa mai bama wani haƙura ko magana sun kasa, sai Ali da ke cewa "Momy dan Allah ki faɗawa AFREED kada ya mutu ya barni banida wani ɗan uwa da ya wuce shi bani da abokin hira banida abokin dariya, shine abokin na na wasa na faɗa na rigima kuma shine ɗan uwana na komai ma Mom ko ke bakinsa tsakanin mu ba, to in ya mutu da wa zanyi daga ni har shi ba wasu abokai garemu ba , mu dai ne abokan juna mu yanzu ya zanyi?"


Momy ma sai hawaye take zubar wa tarasa mi zata cewa Ali duk sun kama sun riƙe ta suna kuka, ɗago su tayi gabaki ɗaya ta shiga share masu hawaye sannan ta fizgo magana da kair cikin dangana tace "Kuzo mu nemi guri mu zauna mu daina zubar da hawaye a banza muyi masa addu'a samun lafiya yanzu ita AFREED ke buƙata gun mu ba kuka ba."


Zaunawa sukayi saman kujeru dake gab da ɗakin da AFREED ke ciki kowa nata addu'a amma har yanzu hawaye basu daina zuba ba daga idanuwan Fariya da Farisa ba shi kuwa Ali idanu sun mashi ja kamar gauta, momy ta juyar da fuskar ta cen tana ta share hawaye saboda bata son su ga ita ma ba ta daina kukan ba dan kar ta ƙara ɗaga masu hankali amma duk inda hankalin ta yake a tashe yake saboda gudan jinin ta abu ma fi soyuwa a gare ta na kwance kan gadon asibiti ba lafiya, rashin lafiya da basu ma san halin da yake ciki ba, a cikin zuciyarta tace "Ya Allah ka tashi kafaɗun wannan yaro nawa Allah ka yaye masa damuwar da ke tattare da shi ka bashi damar cinye wannan jarabawar."


Tsam Ali yayi ya miƙe kamar an tsilike shi ya dawo bakin ƙofar ɗakin da aka shiga da AFREED ya konkwasa yace "Kai wai mi kuke yiwa ɗan uwa na ne da ba zaku fito da shiba wallahi zan karya ƙofar nan idan baku fito man dashi ba, idan kuwa kuka yarda kuka kashe min ɗan uwa wallahi sai nayi kashe ku kuma."


Su Fariya na ganin yanda Ali ya zare yana gayi abubuwa irin na masu taɓin hankali suka sake ƙare fashewa da wani sabon kuka, suna ganin kamar idan likitocin sun fito zasu ce masu AFREED ya mutu ne.


Momy na ganin haka tayi saurin tashi ta kamo hannu Ali ta zaunar dashi sannan tace "Haba ɗana ɗan albarka miyasa zaka dinga irin haka zaka ƙara tayar mana hankali ne idan muna ganin ka cikin wannan halin idan kaida ke namiji baka sa juriya ba mu mata ya kakeson muyi, dan Allah kayi hakuri kayiwa ɗan uwan na ka addu'a Allah ya tashi kafaɗu sa, narasa wace irin soyayya ce ke tsakaninun haka, na tabbata ko kaine a cikin wannan halin AFREED zai iya shiga tashin hankali fiye da haka ma inada tabbacin cewa yan da shima yake ƙaunar ko su Fariya bai ƙauna hakanan, sosai wannan haɗin ƙan naku da soyayyar dake tsakanin ku ke matuƙar birgeni ni kuma take faranta min rai har yasa nale jin daɗi mara musultuwa dan nasan ko bayan raina Ali ba zaka taɓa kukan rashi uwa ko dangi ba, wannan haɗuwar kawunan naku kesa ni manta cewa akwai wata wada ta tsuguna ta haifeka bani ba, dan wallahi mantawa nake da cewa kai ɗin ɗan yar uwata ne, ni a kullum kallon ka nake a matsayin wanda na duka na haifa kamar AFREED da ƴan biyu, ina fatan Allah ya ƙara haɗa min kanku ɗiyan albarka na ta na faɗa tana share hawaye.


Juyowa Ali yayi ya rungume Momy yana share hawayen sa shima yace "Dan Allah momy kiyi hakuri na daina kukan wallahi hankali na a mugun tashe yake gani nake kamar za su fito su ceman ya mutu wallahi da bazan taɓa yafewa kaina ba momy, kuma ni a rayuwar nan ba nida wata uwa sai ke ni ban sa ɗaɗin tawa mahaifiyar ba dan ko kamanin tama bansani ba sai a hoto ta kawoni duniya sai ta tafi ta barni bakina da ita addu'a dan samun rahamar Ubangiji da soyayyar dake tsakanin ɗa da uwa in bashi ba bu wani abun, in badan mahaifina dake raye ba ni nasa da bazan taɓa sani cewa dake da dady ba kune kuka haifeni ba dan kun riƙe ni matsayin ku na iyaye fiye da wasu iyayen ma, da akwai wani matsayi da ya fi matsayin iyaye a wajen ɗa ga iyayen sa to da na baku matsayi wannan matsayin dan kune komai na rayuwa ta sai kuma mahaifin na, ina mama(mahaifiyar Ali) addu'a cewa Allah ya sadata da Mala'ikun rahama kuma ya sadamu a aljanar Firdaoussi." Ali ya faɗa ya ƙarasa share hawayen sa kuma har yanzu yana rugume jikin Momy, itama a boye tana share hawayen ta dan bai kamata ita dake babba ba tayi tayi abu kamar wata karamar yarinya dan tasan suna gane tana cikin ta shin hankali zata iya tayar masu dana su, dama gashi a tashan yake dan ta nuna masu dauriya ne suma suke ɗan rage damuwa.


Kamin momy tace wa Ali wani abu wayar ta ta ɗauki rururi da sauri ta duba tana ganin dady ne ta tuna da ta shiga tashi hankali nan ta ma manta bata faɗa masa halin da ake ciki ba, da sauri ta saki Ali ta shiga ƴar couloir (korkorda) da ke bayan ɗakin da AFREED yake ta ɗaga wayar sallama yayi tayi shiru ya kara ta biyu babu amsa sai yace "Mama ƴan biyu kina jina kuwa, kodai yau sai angama min jan ajin irin naku na mata kamin za'a amsa min, oh kodai dan ɗazu da safe kin kirani ne ban ɗaga ba? wallahi ina wajen meeting wayar kuma tana cikin bureau na (office)."


Shiru batace komai ba dan ita tana ƙoƙarin mayar da kukan da ke shirin zuwar mata idan ta yarda ta buɗe baki da niyyar yin magana."


Kusan minti uku yana jiran yaji tace wani abu amma shiru sai yayi tunanin ko ta kashe wayar ne, saiya sauke wayar a kunanan shi ya duba amma yaga ba kashe kiran bane tayi, sai yaci ka da mamaki yayi saurin mayar da wayar a kunanan sa tare da cewa maman ƴan biyu (da yake haka yake kiranta da shi) laifin nawa har yakai a ƙiyi min magana wallahi ina meeting ne shiyasa ban ɗaga kiran ki ba, Ni bansan nayi wani laifi ba in ba wanan ba, dan haka kiyi hakuri idan wani laifin ne nayi da ban sani ba shima ayi hakuri Allah ya huci zuciyar uwar gida na kuma uwa ƴaƴana masu albarka, ko dayake nasan anjima zaki huce bari na kashe zan ƙara kiranki anjima (ya faɗi hakan cikin zolaya kuma yasan da yace zai kashe to zatayi masa magana, ah ni tsofaffi da soyayya).


Momy najin alamun dady zai kashe wayar cikin sauri da wani irin kuka da ya kubce mata tace "Dady AFREED." Ta faɗa ba tare dama sunan ya fito da kyau ba sabida kukan daya ci ƙarfin ta, kuma ta ƙasa ƙarasa abinda tayi niyyar faɗa."


Ai dady najin kukan matar shi farin cikin shi abin alfahari sa kuma mafi soyuwa a cikin zuciyarsa ai sai hankalinsa ya tashi iya tashi baisan lokacin da ya faɗi sunanta ta zane ba yace "Falmata lafiya mike faruwa ya naji muyar cikin tashi hankali haka rabon da naji ko na gani kiyi kuka tun rasuwar yar uwarki kuma ƙanwar ki mahaifiyar Ali ko kuma tashin hankali irin wannan dan Allah faɗa min mike faru yawe ya rasu ko ya tayar min da hankalin ki ko waye babu lafiya? wallahi tun safe da natashi naji hankali na ya ƙi kwanciya naso na kiraki kuma mutane suka azazaleni sai na fito mun shiga meeting, haka ba dan hankali na ya kwanta ba na bisu muka shiga meeting sannan kuma ina fito na tarda appelle manque (miss call) ɗin ki kawai sai gabana ya faɗi dan Allah daure faɗa min abinda ke faru kisan hankali na ya ƙara tashi."


Cikin kuka da ta ɗan rage tace "Dady AFREED dama AFREED ne......." Kuma sai kuka ya kwace mata ta kasa ƙarasa abinda tayi niyyar faɗa.


Ai kuwa hankalin dady in yafi dubu to ya tashi jin abin ma saman kan ɗan sa ne gudan jininsa abin kaunar sa, da sauri cikin ɗaga muyar cike da tashin hankali yace "Maman ƴan biyu daure ki faɗa miyasa mi yaro na da kuka boyemin, mike faruwa dashi ne idan kuka yar wani abun ya sameshi dani daku ba zamu shirya ba, kada ki yarda ki faɗa man cewa bashi da rai?"


Hankali momy ya ƙara mugun tashi ganin har mahaifin nasa da take gani zai yi dangana amma ya rikice har haka wai wane irin so ne suke yiwa AFREED haka dan ma Allah yasa basa nunawa sosai da babu san ko AFREED zai iya zama mai wani juyayan hali ba duk da ko yanzu ɗin halin sai a hankali uwa uba miskilanci, kawar da wannan tunanin tayi, lokacin da taji dady AFREED ya daka mata tsawa yana cewa "Ba zaki faɗa min abinda ya sami yarona ba."


Da sauri momy itama cikin dusashewar muyar tace "Dady AFREED wallahi nima ban sani ba ina ganin ciwon sa ne ya tashi nima ina cikin falo nida su Farisa, Ilya direba ya shigo yace man ga Ali cen ya tafi da AFREED asibiti kuma AFREED ɗin baya cikin hankalin sa yana tunanin a some yake lokacin da ya tafi da shima, ba tare da na tsaya ya ƙarasa maganar saba, na shige ɗaki na saɓo hijab ya kawo mu asibitin muna zuwa kuwa har an shiga dashi urgence (emergency) mun tardo Ali a bakin ƙofar ɗakin dayake cikin, nayi masa tambayar duniyar nan ya faɗa abinda ya sami AFREED ya kasa faɗa min sai kuka yake da kair na samu na rarashe sukayi shiru kuma mun kusan awa huɗu anan har yanzu babu likitan da ya fito daga ɗakin ma bare su faɗa mana hali da yake ciki kwata kwata hankali na yaƙin kwanciya na kasa daurewa zuciyata ta ƙarye gani nake zan rasa shine abu shiru haka dan Allah dady AFREED kayi wani abu."


Sai a sannan dady ya sauke wata ajiyar zuciya, ba dan hankali sa ya kwanta ba a'a dan dai shin ke namiji kuma shine babban indan bai kwantar masu da hankali ba ko ya nuna dangana ba to su ya zasuyi, ɗan nisawa dady yayi cikin sanyayar muryar mai kwantar da hankali yace "Ke kina kuka yaranki nayi wa zai bawa wani haƙura a cikin ku gashi kuma ke ce babba idan baki nuna dangana da kawaici ba su ya kike so suyi kuje asibiti kuyita koke koke kamar wasu maras hankali kece babba fah ke zaki basu haƙura ba wai ki biye masu ba ayita kukaba, je ki ƙara kwantar masu da hankali sannan ki rarashesu da ikon Allah, Allah zai tashi ƙafaɗu sa in Allah ya yarda zai sami lafiya, sannan batun inyi wani abun bai taso ba nida bani gari, ke koma a gari nake ba zanja da ikon Allah ba, ba zan iya bashi lafiya ba saidai wanda ya aza mashi shi zai yaye masa wahala nima kuma ina a hanya nan da ƙarfe biyu jirgin mu zai sauka insha Allahu faɗa man wani asibiti kuke dan ina sauka nan zan wucike."


"Clinique HADAMALAH" momy ta faɗa a taƙaice.


Ok ta Dr Inusa kenan ai abokinna ne gayamin number ɗakin da yake zan kira yanzu Dr Inusa na faɗa masa yaje ya duba shi da kanshi kamin na karaso."


Momy tace "Bon ɗakin dayake ciki numéro (number)45 amma idan sun fito dashi za a kaishi ɗaki personnel inda zai huta ba za'a haɗasa da kowa ba yanzu zanje nasa Ali yaje ya biya kuɗin babban ɗaki mai komai da komai a cikin."


"Eh hakanan ya kamata yi sauri ki koma gurin su kin barsu su ɗaya yanzu haka suna cen su na kukan."


Momy tace "To shikenan sai kazo Allah ya kawo ka lafiya."


Da ameen dady ya amsa tare da kashe wayar, dady na kashe kiran momy ta koma wajen su Ali tace "Ya je ya biya kuɗin ɗakin da za'a saka AFREED idan an fito da shi. ba musu Ali ya miƙe ya nufi inda ake biyan kuɗin."


Shiku dady ya na gama waya da momy ya kiran Dr Inusa ya sanar da shi Dr Inusa najin cewa ɗan abokinsa ne kuma a matse yake, yasa shi saurin miƙewa ya kashe kiran dady ba tare da ya bari ya idasa jin abinda dady zai ce ba ya tashi ya nufi ɗakin da AFREED ke ciki su momy na nan zaune saida sukaga muntun ya buɗe ɗaki ya shige suka ƙara baza ido.


Dr Inusa bai fi minti talatin da shiga ba sai gashi ya fito, ida su momy ke zaune ya nufa yace "Madame kune ku ka kawo AFREED Sumana ko naga kama"


Da sauri momy da su Farisa su ka miƙe momy tace "Eh mune."


Dan murmushi ya saki yace "Kun kwantar da hankalin ku biyoni office."


Momy tace "To." Tana ƙoƙarin kiran Ali a waya dan ta faɗa masa cewa ya tardosu office ɗin Dr Inusa.
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸




Écrit



Par



*QUEEN ZEEFAT*


_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_




*Wattpad@nazichou*



💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/



*_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_*



*Page* : 45 & 46



*Wanene DR Inusa*

Dr Inusa wani shahararren likitane da yayi suna a faɗin duniyar nan kuma da yasan aikin sa, yayi karatu sosai a fannin ciwu wuka da yawa dake damun ɗan Adam, yayi karatu akan ciwon dake damun fatar jikin ɗan adam yana da ilimi akan ciwon ƙwaƙwalwa da ciwon ido ciwon haure da irin wanda ya shafi mata da na kwada dana sihe da na zuciya dama sauran ciwuka da ban zana ba, dan haka yayi fice ko ina a san shi, da Alhaji Sumana dadyn AFREED da kuma Alhaji Sadisu mahaifin AFREEN da shi Dr Inusa duk abokan juna ne tun suna yara, shi ya fi su yin karatu mai zurfi dan yana kasashan waje yana karatu duk su dadyn AFREED da papan AFREEN sukayi aure dan haka baisan matan su ba, itama Arahamat mahaifiyar AFREEN wato matar Alhaji Sadisu, yasan tane dalilin auren ƴar uwar ta daya ke.


Sosai yayi yawon duniya, dan kasanshan duniya ɗaya ɗaya ne baje ba, ba tare da ya ƙarasa karatun sa ba yayi aure ya auri Jannah (wato ƙanwar Arahamat mahaifiyar AFREEN) haɗuwar sa da Jannah kuma ta dalilin abokinsa ne Ibrahim (wato ƴayan su Arahamat da Jannah) da suka game wajen karatu a New York (in masu karatu basu manta ba Ibrahim na wani aboki ɗan masu arziki da suka haɗe wajen karatu a kasashen waje), yanzu suna zaune a Dubai yanzu haka, ba gari guda suka zauna ba sabida yawan tafiye tafiye da mijin nata keyi yau in suna wannan ƙasa gobe suna wacen Niger kaɗai idan zai taho sai ya barosu saboda karatun yaransu da suka saba da irin na ƙasar waje, ya shahara sosai a aikin sa kuma ya ƙware iya ƙwarewa fiye da tunanin mai karatu, ya san aikin sa sosai dan har a ƙarsa wajen neman sa suke zuwa idan wani abu ya ƙaƙare masu to da ikon Allah shi zai warware sa sabida ya nemi ilimi sosai yanzu haka cikin neman sa yake, idan yazo Niger yana wata uku bai koma gun iyalinsa ba saboda ya malaki asibiti guda huɗu biyu a babban birnin Niamey ɗaya a Maradi ɗaya a Zinder, yana wata ɗaya a cikin asibitin sa da suke cikin garin Niamey yaje Maraɗi ya wata ɗaya ya koma Zinder yayi wata ɗaya, to shi duk mara lahiyar da yayiwa aikin da ikon Allah sai yaji sauƙi sedai idan ciwon ajali ne mara lafiyar yake ko kuma ciwon da bai shafi asibiti ba.


Kamar wata baiwa ce Allah ya bashi dan taimakon al'umma duk ta dalilin wannan aikin nasa ya zama wani shahararren mai arziki, kuma baisa tsada a cikin harakar yiwa mutum magani cikin asibitin sa ba, dan haka kowa najin ya zo gari ko lafiyar ka lau zaki ga mutane na tafiya ya duba su.


Suna shiga cikin office ɗin na Dr Inusa yace su zauna, momy dai sai binsa da kallo take ta matsu ya faɗa mata halin da ɗan ta yake ciki suna cikin, suna zauna wa suka fara gaisawa sannan yace "Madame nasan baki sani ba amma nasan kin koda a bakin mijin ki ne kunji sunana, mu abokan juna ne tun muna yara dalilin da yasa baku sanni ba ni bana wayan zama a nan kuma idan nazo ayyuka sun min yawa ban samu dama na leƙaku bare har mu gaisa shima mai gidan naki sai in yana gari yake zuwa mugaisa har nan asibiti ko ya isko ni ɗayar, shima Alhaji Sadisu haka yake oisko ni asibiti idan naje Maraɗi ai nasan kisan shi, amma shi nasan matar sabida ita ɗin yayar mai ɗakina ce."


"Kema kuma nasan ƴaƴan ki maza da ɗaya daga cikin ƴan biyun nan sabida Alhaji Sumana ya taɓa kawo ɗayar nan tana ciwon ciki an yi katari lokacin ina gari ni nama duba ta, ba tare da na cikaku da surutu ba bari na faɗa maku abinda ke damun ministan namu wato AFREED."


Bai ƙarasa rufe bakinsa ba Ali ya turo ƙofar da sallama ya shigo, cike da sakin fuska ya amsa masa sannan Ali ya ƙarasa gab dashi ya duka yace "Dady ina kwana ya aiki."


Dr ya saki murmushi tare da shafa kan Ali sannan yace "Lafiya lau alhamdulilah ashe ɗan uwan naka ne ba lafiya."


"Eh wallahi dady"


"To miyasa a lokacin da kuka kawo shi baka zo ka faɗa man ba tunda ai kunsan ina gari dan shekaran jiya ma ranar asabar a nan kuka yuni ko?"


Ali yace "Wallahi dady duk na rikice na marasa mizan yi shiyasa na kasa tuna ma da kana nan."


Dr Inusa yace "To shikenan tashi ka zauna insha Allahu ɗan uwan ka zai samu lafiya duk ku kwantar da hankalin ku."


Ali ya nemi guri ya zauna yana jiran ji ƙarin bayani.


Dr yayi yasu rubuce rubuce a saman wata pepper sannan ya ɗago yace "Ba komai bane ke da mun AFREED sai tunani damuwa wanda haka yayi niyyar saka mashi ciwon zuciya sedai an riga da an shawo kan matsalar insha Allahu ciwon ba zai ƙara tashi ba sai wani abu daga Ubangiji dan sosai aka shawo kan matsalar, sai kuma taimakon da kuma zakuyi mashi shine a daina barin shi yana zama shi ƙaɗai hanka na bada gudunmawa wajen saka shi tunani ko da bai zai yi maku magana ba ku dinga zama kusan da shi kuna hira ta wasa da dariya tun yana shiru har sai yakai ya saka maku baki a zancen ku, kuma wajen aiki ya daina zuwa har na tsayi sati biyu saboda ya ƙara warware wa, a daina barinsa cikin damuwa kuma a guji abinda zai ɓata masa rai har na tsawon watanni shida kuma kada a yarda ayi wani abu da zai tayar masa da hankali sosai har na tsawon watannin nan da na an bata sannan yanzu idan har ya ji sauki kada ku matsa masa dole sai ya faɗa maku abinda ke damun sa dan baiyi niyyar faɗa ba kuka sa shi dole, zai iya shiga damuwa kuma a kuma ƴar gidan jiya ciwo ya dawo sabo idan yayi niyya shi zai faɗa maku da kanshi cikin lalama, idan aka yi haka insha Allahu komai zai dawo normal da ikon Allah.


Sai a lokacin momy ta sami damar magana tace "Mungode sosai wallahi ba ƙaramin daɗi naji ba dajin cewa zai samu lafiya kuma an shawo kan matsalar, godiya muke Allah ƙara ilimi."


Ameen Dr Inusa ya faɗa sannan ya ƙara da cewa "Zaku iya shiga ku ganshi nasa an tanadi special chambre sabida shi ni nace ka wanda ya ƙarɓi kuɗin komai a wajenku har na ɗaki da Ali yaje biya, sabida nima ai ɗana ne, idan na masa aiki ai kamar nayiwa yaro na ne fata na dai Allah bashi lafiya."


A tare suka amsa da ameen sun Fariya dai sun zama ƴan kallo sai bin kowa na office ɗin suke da kallo sun ƙasa magana da sosai ɗan dattijon nan abokin dady ya birgesu sabida yanda suka lura ya ƙare da aikin kuma daga gani baida matsala wayis ne ba ruwan sa da ɗaukar kai duk da arzikin da Allah ya masa bai ɗauki kansa wani abu ba, sai ma sauƙin kai da yake dashi sosai, su da suke ganin a na nuna sa a télé (TV) basuyi tunanin za su ganshi mai sauƙin kai haka ba.


Farisa tace kin zuciyarta"Ashe shine ya duba ni da na yi ciwon ciki ni ban ma lura ba lokacin ina halin rashin lafiya, da ace masu kuɗi da ilimi zasu ɗauka cewa ɗaya suke da kowa da duniya ta gyaru."


Farisa na zancen zuci bata masan har su tashi suna niyyar fita ba sai da momy tace mata "To ke mi kike jira?" sannan ta dawo hankali ta bi bayan su.


Shikuwa ya cigaba da duba takardunsa.


Suna shiga ɗakin da AFREED ke kwance a ciki wani kamshi mai ɗadi ya bigi hancin su ga ɗaki tsaf tsaf kamar ba a cikin asibiti ba sedai ace masha Allah a guje Fariya da Farisa suka ƙarasa idan AFREED ke kwance yana baccin wahala da abin sérum (ƙarin ruwa) a hannu sa kwana yake cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, duk suka riƙe masa hannu suka fara kiran "Yaya yaya tashi daga bacci kayi mana magana dan Allah ko faɗa ne kayi mana kaji yaya."


Ali ne ya ƙaraso ya katsa masu tsawa tare da cewa "Baku da hankali ne baku ga ya samu bacci ba amma kukeson ta yarda da shi baku san ma yanda akayi ya samu bacci ba amma kukeson sai kun tashe shi maza ku matsa daga nan."


Da sauri suka ja da baya dan sun san Ali bai taɓa masu irin haka ba yanzu ma sun san da dalili duk sai suka nemi kujera suka zauna momy ta kalle su ta girgiza kai tana murmushi a ranta tace "Yau fah ba zaku gane kan Ali har in ba gani yayi ɗan uwan na nasa ya buɗe ido sun koma gida lafiya mai ba." Sannan ta ƙarasa ta zauna kusa da AFREED tana kallon fuskar da bakin sa kamar zai yi magana


Suna a haka Dr Inusa ya shigo da magungunan da yada ce AFREED ya dinga sha har sai sun ƙare Ali ya miƙawa sannan yace "Nan da awa biyu zai faraka insha Allahu sannan zai ji sauƙi sosai dan haka kada kuyi magana sosai har sai ya tashi dan gaban kansa, su kuwa wa'inan magungunan idan ya tashi abashi wani abu mai ɗan nauhi ya ci sai ya sha."


"Ok dady mun gode za ayi yanda kace."


Murmushi Dr Inusa yayi ya ce "Ku daina gode man ai nima ɗana ne."


Ya juya zai fita daga ɗakin har ya kai bakin ƙofa ya buɗe sukayi kiciɓis da dady zai shigo wanda dirowarsa kenan garin, gama hannu sukayi suna dariya tare da gaisawa sannan suka koma daga ciki a tare."


Su Fariya a na ganin dady sai aka shiga farin ciki da gudu suka taso suka rungume shi shima ya riƙe su sosai suna mashi sannu da zuwa Ali ma ya taso

Please Login or Register in order to submit comment