Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai wanda yace mata ufan sai ma dai umma mahaifiyar zeinab da ta rakata da harara.


Tana zuwa ta tarda AFREEN zaune a saman sallaya tana jan tazbi sallama tayi bayan wai har ta shiga ɗakin, kallon ta AFREEN tayi ɗan ita rabon da su haɗu har ta manta saboda yanzu ta rage shiga harakar ta tuna ta nuna ta bijire ma Mahaifin kan zaɓin da ya mata, ai take yanke kuma gaban AFREEN ya faɗi tunowa da tayi cewa za'a aurar da ita ga wani wanda ba AFREED ba, a take mood ɗin ya sauya har ida take zaune tantin ta ƙara da ta ajiye mata abincin tace gashi nan nace bari na kayo maki har ɗaka dan na lura tunda ki kaga sati biyu ne yayi saura ɗaurin auren kike cikin alhinin rabuwa da iyaye ko iya fita falo bakiyi bare nayi tunanin zaki je ki gaisa da mu.


Gaban AFREEN ne ya yanke ya faɗi jin saura sati biyu auren ta, saboda ita yanda ta ɗauki zancen kamar ba da gaske ba haka yasa ta manta da wani lokaci auren ya kusa sosai hankalin ta yayi matuƙar tashi sedai bata nunawa tantin, wani sankaran murmushi da ta sakar mata tace "Nagode tanti."


Tanti tace "Ba komai yi maza kici dan naji mahaifiyar ki na cewa yanzu Wada zata maki gyaran zata zo har an gyara ɗakin da zaki komai domin hakan."


Nan ma dai gaban AFREEN kara faɗuwa yayi amma sai ta daure tace "Toh."


Sannan tantin ta tashi ta bar ɗakin dan ta mance boka yace mata kada ta bari AFREEN tayi Bismillah ga abincin da ta saka maganin, dan haka ta fice tana jin daɗin burin ta ya kusan cika.


Tana fita AFREEN ta buɗe abincin ta fara ci tare da Bismillah bata ci wani sosai ba dan jin yanda hankalin ta ya kasa kwanciya saboda ganin yanda auren da ta manta da shi yake ta matsowa, ta shiga damuwa iya damuwa hankalin ta ya ƙara mugun tashi, dan haka ta kasa zama a kan darduma ta koma saman bed ɗin ta ta shiga rera kuka mai cin rai har saida taji alamun mahaifiyar zata shigo ɗakin nata sannan ta tashi da saurin ta faɗa douche (toillet) ta ci gaba rera kukan ta har kanta ya fara ciwo kamin take fara wanka da sauri sauri dan taji mahaifiyar ta na kiranta.


Yana saura sati ɗaya auren AFREEN, duk amarya ta bi ta kare ta rame duk ta lalace sai kyau ɗin nan nata kamar ƙara mata shi ake yi don gyara jiki da ake mata da kuma haɗa mata kayan mata da ake, AFREEN saboda halin da take ciki duk ta koma abin tausayi, kullum kuka abincin ba ta wani cika ci ba, in yau lafiya gobe ba lafiya tun ya sauran sati biyu auren tabi ta firgice idan an tambaye ta mike damun sai tace ji take bata iya rabuwa da iyayen ta duk abin ya bi ya dameta haka mahaifiyar ta zata zauna tana bata baki tare da kwontar mata da hankali.


Zata nuna kamar ta kwontar da hankalin nata sannan mama ke barin gun, hasina kawarta kaɗai ta san halin da take ciki, kuma kasa har yanzu sanar ma AFREED cewa ita ga aure za'a mata, amma a yau ta yanke shawarar sanar dan haka ta sanar wa da hasina da ta dawo gidan da kwana tun da auren kawar ta ta ya yi sauren kwana goma da ita ake komai da komai na shirye shiryen biki kuma ta taya ƙawar ta jimami da ƙara mata kwarin gwiwar yiwa iyayen ta biyayya.


Dan ta nemeta akan ta taimaka ta sanar wa AFREED aurenta dan kar yaji ga wani yace ta ci amanar sa, amma dakyar ta samu shawo kan hasina ta yarda zata faɗa masa, dan haka dan haka yau safiyar ranar asabar ya kama saura sati ɗaya auren nata suka yanke shawarar kiransa su sanar masa.


Suna zaune daga ita sai Hasina cikin ɗaki bayan taci kuka ta ƙoshi, ta mika hannu ta ɗoko wayar ta dake bisa gadon ta dana kira a number AFREED da ta saving ɗin ta da sunan Destiny, tana ta ringing har ta katse bai daga ba dama haka ne idan zata kirashi ba zai daka ba sai ta kashe ya maida mata kira yanzu ma hakane ta kasance, tana katse kiran nashi ya shigo saida ta kusa tsikawa kanan ta ɗaga ta mikawa Hasina wayar gaban Hasina da na AFREEN na faɗuwa Hasina kara wayar a kunan tare da sallama cike da sanhin jiki, daga cen AFREED ya saki murmushi ya amsa sallamar yace "ƙawar mu kece a wayar da fatan kina lafiya ya gida."


Hasina tace "Lafiya lau alhamdulilah ya gida ya aiki."


A takaice AFREED yace "Lafiya klau ina kawar taki ne dama inason muyi magana dake."


Tace "Bata kusa noma kam maganar nake so muyi shiyasa ma na kiraka da number ta."


"Ok to ina jinki idan ki sanar da ni noma sai sanar dake nawa abin da zan faɗa maki."


Hasina tace "A'a fara sanar dani taka maganar sai na dan ni tawa maganar tsayi ne da ita."


Ayi haka naga fa kike ka fara neman sanar dani hakan na nufin maganar nada muhimmanci kada na katse ki kuma."


"Ah bai komai ai ni na baka damar hakan."


Yace "To shikenan dama ba wani abu bane faɗa maki illa tambaya ce nakeson yi maki akan kawaki, dan Allah nasan ke baki rasa sanin abinda ke damun, dan ta sauya min sosai ka saurin kuka daga nayi mata wata magana haka cikin fira sai kiga ta fashe min da kuka kuma ta daina sakin jiki dani badai kamar yanda muke a da ba dan ni gaskiya abin na damuna kuma idan nace mata zan zo Maraɗi dan nazo gidan sai kiji ta hana ko kuwa idan nace zan Turi Iyaye na nan sai ta ce a'a dan Allah mi hakan yake nufi kodai ta daina sona ne ban sani ba, idan kuwa hakan ta faru ai ban koma yin numfashi dan rayuwa ta ta zo ƙarshe."


AFREEN dake sauren duk wani abinda yake faɗa saboda wayar a handsfree take, ta waro ido waje kawai sai ta fashe da kuka mara sauti dan kar yaji tana kusa, sannan tayiwa Hasina nuni data katse kiran.


Katse kiran Hasina tayi sannan tace "Besty ki bari na sanar dashi gara ayita ta ƙare idan har kika bari yaji ga bakin wani to ba fah zai taɓa fahimtar abinda zamu fahimtar da shi ba wallahi."


"To bakiji furicin da yayi bane ina gudun yaje ya rasa ransa ta dalili na dan Ali ɗan uwansa ya sha sanar dake halin da yayi ta shiga ta dalilin son da yake mani wallahi nidai....


Bata ƙarasa faɗin abinda tayi niyar faɗa ba kiran shi ya koma shigowa wayar ta aiko sai da ta ɗan zabura, Hasina tace "Kin ga besty ya maido kiran ki daure ki bari a faɗa masa dan a fitar dashi daga duhu wallahi gara ya sani yanzu da har sai an daura maki aure yaji labarin lokacin zai fi shiga halin da kike gudu ya shiga kuma Ni nasan mi zan sanar masa."


A haka AFREEN ta amince da a ɗaga kiran sedai kamin Hasina ta ɗaga kiran ya katse, ba tareda ɓata lokaci ba ya maido wani kiran."


Hasina tace "Yawa aboki kaji na katse kiran ko mama ce kirani shiyasa."


Yace "To shikenan ina jinki."


Saida da Hasina ta sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya sannan tace "Yawa aboki dama nima sabida wannan changement ɗin ne yasa na kora dan a samu mafita , saida ta ɗan nisa sannan taci gaba dacewa "Ai dai kasan irin son da AFREEN ke maka, kuma koni shaida ce AFREEN ko sauro batason ace ta dalilin ya shiga wani hali bare mutum sanan kuma kai da take so take kauna, ya kamata kayi tawakali ga Allah akan samun AFREEN ko rashin ta a gare ka idan kana hakan na nuna rashin juriya ka akan jarabawar da yake maka sai yaga kamar ka kasa gode masa ne, dan babu wanda AFREEN takeso kuma take kauna sai kai ɗin nan dai AFREED dan haka batada wani buri da ya huce taga kun malaki juna , sedai hakan da wahala dan kuwa wata matsala ta riga da ta Kunno Kai a tsakanin ku bani da tabbacin idan burin ku kai da ita zai cika a gaski......


Hankali a matukar tashe AFREED ya dakatar ta Hasina ta hanyar cema mata "Dakata Hasina ki daina man dogon bayani i man maga yanda zan fahimta dan Allah ki daina kwane kwane dan tunda kika fara magana gabana ke faɗuwa, narasa dalili amma sai nakeji a zuciya ta bana son jin abinda kison fahimtar da ni amma duk da haka ina sauran dan Allah imani da wara wara dan Allah."


"To ka kwantar da hankali sai na faɗa maka ta yanda zaka fahimce ni da kyau."


Ba zan iya ba Hasina dan Allah ke dai kawai ki sanar dani zan fahimta a haka ma.


Hasina taci gaba da cewa "Matsala ce ta taso wani abokin papa ya zo ya nema ma ɗan sa auren AFREEN tun wata biyu da suka huce yau ya kama saura sati ɗaya ɗaurin auren kuma ta kasa bijirewa umarnin iyayen dan sun gama mata komai a duniya, amma kasani AFREEN kullum cikin kuka take da rashin lafiya ta dalilin son da take maka kuma ganin canjin da kayi na wasu yan kwanaki a game da ita to ta wannan dalili ka ko abinci bata ci haka iyayen ta har yanzu basu san da batason auren ba gayama nake ko waya ma basu taɓayi da wanda ake kokarin haɗa ta da shi, shi bai san ta ba ita bata sanshi ba kenan kada kayi condamné kin ta akan hakan ko kuwa kai ka saka kan a wani hali saboda ita kawai kasa ma kanka cewa tuncen da Allah ya rubuta ba zaku taɓa zama a inuwa guda ba dan wallahi AFREEN tana son kamar ta mut yanzu abinda nake faɗa batada wata isasa lafiya, AFREED kayi hakuri dan idan ka tayar da hankali itama ba zata taɓa samun sukuni a rayuwa ta kawai ku ɗoki hakan a matsayin ƙadarar ku."


Kaskas sukaji ƙarar faɗuwar wayar AFREED sannan shima yabi wayar, shi ƙarar faɗuwar AFREED ya saka AFREEN sakin wani irin matsanancin kuka mai ban tausayi ta rugungume Hasina tana faɗin dan Allah besty ki taimaka min kada ace ya mutu inna lilahi wa inna ilaihi raji'un wallahi idan wani abu ya samesa bazan taɓa yafewa kaina ba na shiga wallahi shi nake bari naje na faɗawa papa banison zaɓin ya taimaka ya bani wanda nakeso kada na rasa shi na shiga ukuna,' daga nan itama AFREEN ɗin numfashi ta ya farayin sama ta kokowar dawo dashi amma ina sai gata ta idan faɗawa a jikin Hasina jikin ya saki alamun ta suma,


Ai dake taya ƙawar tata kuka tana ganin yanda AFREEN ta some ta saki wata irin ƙara itama tana jijigata tana faɗin besty dan Allah ki tashi besty kada ki mutu ki barni Inna lilahi wa inna ilaihi raji'un besty dan Allah ki tashi kada kiman haka taimaka ki tashi sai mu sanar da su papa cewa kina da wanda kike so, Hasina da taga kuka da kururuwa basu gyara ta kawai sai ta sauka a gadon a tsiyace ta ta aza da gudu tana kiran maman maman AFREEN, da gudu duka ƴan gidan suka yo falo hankali a tashe suna tambaya lafiya miya sami AFREEN ɗin amma tsabar ta buɗe kasa cewa kumai tayi sai jan hannun maman take ta na nuna mata ɗakin AFREEN, bakita AFREEN da maman kawai yake faɗa,


Ai a kuke mahaifiyar AFREEN ta kwasa ta nufi ɗakin da hannu ta riƙe da na Hasina sai zeinaf da ta mara masu baya a guje ita sai tanti da umma da ha gware sukayi wajen shiga ɗakin sai kuma kannan zeinab da Hamida da kuma mutanen da suka farazu wa bikin, duka dai suka kwasa a guje suka nufi ɗakin AFREEN, maman na shiga ɗakin direct ida AFREEN ke kwance ta nufa tana ta jijigata ta na kiran sunan ta amma ina AFREEN ko jinta batayi haka zeinab da Hasina sai kuka suke suna kiran sunan ta zeinab cewa take Aunty AFREEN dan Allah ki tashi kada ki min haka bani da kamar ki a rayuwar nan idan aka cire iyaye to wa zai dinga mani faɗa da nasiha dan Allah ki taimake ni ki tashi , maman ta tura Hasina daukaruwa a fridge tana kawowa aka zuba ma AFREEN amma ko motsi nan fa suka ƙara rikicewa dan tsananin firgici mantawa ma sukayi da batun asibiti zeinab ce wannan tunani ta bare da tace ma kowa komai ba ta yi wani irin tsalle ta dira a gadon ta fita ɗakin a guje dai dai tana shirin fita a filin dan zuwa kiran Fahad ya zo akai AFREEN asibiti sukayi kicibis da papa ya na kokarin shigowa falon wanda har sai da ta ban gajesa ba tare da ta masan tayi ba da sauri papa ya riko hannun ta yana tambayar "Lafiya mi take ma gudu mai ya faru da ita dawa."


Jin muryar papa yasa ta juyo a gigice tace "Papa Aunty AFREEN bata motsi papa taki tash......"


Ai papa baisan lokacin da ya saki hannun zeinab ba ya nufin ɗakin AFREEN cikin sauri sauri gudu gudu."


Ita kuwa tana ganin ya saketa taba fasa abinda tayi niyya ta koma kwasa a guje ta nufi ɓangaren su Fahad, tun a bakin kofar shiga falon ta ke kwalla masa kira ya Fahad ya Fahad ya Fahad, ya ciki ɗakin sa ya duba litattafan shi na makaranta dan jibi suna da jarabawa yaji irin wannan kiran da zeinab ke masa yasan ba lafiya dan basa irin haka da ita tun ba wasa yake dasu ba, ba ma haka ya cika yiwa kannan nasa baga ba dan shima akwai shegai miskilanci, a daidai ƙofar shiga ɗakin nasa sukayi haɗu a birkice tace "Ya Fahad muje a kai Aunty AFREEN asibiti dan Allah ta kamo hannunsa ta na jan sa a rikice."


Riƙe hannun ta yayi yace ke kwantar da hankalin ki faɗa miya sami AFREEN ɗin, tace "Ni bansani suna ɗaki ita da Aunty Hasina sai ga anty Hasina ta fito a guje ta na ce mana Aunty AFREEN muna zuwa muka tarda ko motsi batayi an zuba mata ruwa taki tashi tana faɗa masa tana kuka."


Ai ko shima a guje ya kwaso dai bakin ƙofar shiga bangaren su suka gamu da imaran, shima bai tsaya wata wata ba ganin yanda suka wasa a guje shima ya bi bayan su har sai da ya wuce dan shi kan kame da gudu ya shahara da kyar za kuyi yar tsere ka wuce shi gaskiya samun mai wuce shi a gudu to sai an bincike kuma sai an wahala haka kawai Allah ya yi shi.


Kamin su kai ga ɓangaren iyayen nasu suka haɗu da papa ya ɗauko AFREEN a hannun zasu je asibiti, Fahad karɓar makulin motar yayi daga hannun papan nasu ya yi sauri ƙara sawa wajen motar ya buɗe aka saka AFREEN baya da ka kwance kamar matata, maman tashiga Ida aka saka AFREEN ta aza kanta saman ciyowin ta, shima papa ya shiga ya aza ƙafafun AFREEN saman jikinsa Hasina ta buɗe wajen mai zaman banza ta zauna Fahad ya shiga mazaunin direba, ya rufe motar ya tada ya ya fice a gidan suka dauki hanyar asibiti, Imaran shima ya ɗoki mota ɗaya ya shiga tanti da umma da kannan zeinab a baya shi yana mazaunin direba zeinab kuma ta gaba kusa da shi.


Ita kuma Hamida da yayan alhaji Sadisu da suka zo mata su biyu sukuwa direba ya ɗokesu sai asibiti ya zamana gidan sai ƴan tsurarun mutane da kuma masu aiki da mai gadi.
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸



Écrit



Par




*QUEEN ZEEFAT*


_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_



*Wattpad@nazichou*

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝
☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/




_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_



*Page* : 63 & 64


AFREED na sakin wayar sa kasa donjin abinda Hasina ta faɗa masa duk ta fashe amma bata mutu ba kuma bai katse kiran ba, sannan kuma shi ba suma bane yayi tafiya ne yayi ya zauna a kasa dabas shine AFREEN ta kamar ya faɗi kasa tayi tunanin wani abu ne ya sameshi shiku wa ya zama dabas ya kama kansa da hannu bibbiyu da yake jin yana sara masa kamar zai tsage jin kukan AFREEN da abinda take yasa hankali da kara tashi amma kuma yaji bakin sa ya yi masa nauyi saboda ya kasa masa masu magana, wanda ita ma Hasina ganin AFREEN na kuka ma manta bata kashe kiran ba, jin ihu Hasina lokacin da AFREEN ta suma yasa shi fita hayacin da sauri ya nufi inda wayar tasa ta faɗi ya ɗauka ya kara a kunne ya na kiran Hasina lafiya miya faru jin tana cewa kada ki mutu ki barni ki tashi dan Allah ya saka shi ƙara rikicewa a gigice ya tashi yana kiran sunan ta kamar tana jin sa dan ko Hasina dake idon ta biyu bata ji sa ba duk da wayar a handsfree take tsananin rigicewa itama ko jinsa ba tayi, AFREED ya kasa yanda zai yi sai yawo yake cikin ɗakinsa shi ɗaya hankali a tashe, duk abinda ake yanaji daga fitar Hasina daga ɗakin har shigowar su maman da shigowar papa da fitar su a ɗakin don kaita asibiti duk yaji, sai a sannan ne ya katse kiran ya yi zaune a saman gadon sa ya yi tagumi dan ya rasa abinda ke masa daɗi ji yake kamar ya tashi ya tafi Maraɗi ya keji amma ina tuna ita ɗin ta wani ce ba tashi ba sai ya jikin ya masa sanyi lakwas.


Cikin kankanin lokaci ya kira number Hasina yafi a ƙirga amma tana ta sonner ba'a ɗaga ba, abinda bai sani ita da kanta bata san ida tata wayar take ba har ta AFREEN dan kuwa duk nan ta sake su da ta rikice.


Shima ya kasa taɓaka komai kansa sai wani mugun ciwo yake masa kar ya fida shi ya aje, ga farfaru idanunsa su yi wani irin mugun kamar gawauta dole kaji tsoro idan ka kalli cikin idonsa a halin yanzu.


Su na zuwa asibiti urgence (emergency room) akayi da ita cikin gaggawa, Hasina da maman da zeinab sun kasa zama sai kai da kawowa suke, papa da Fahad da Imran kusan ɗakin da aka saka a tsaye sauran suna zaune duk sunyi tagumi, duk sun rasa abinda ke masu daɗi, banda tanti da a fuskar ta ne kaɗai ta nuna kallar tausayi, amma a zuciyarta cewa take Allah sa tayi paralysé (ciwon shanyewa ɓaren jiki).


Wajen awa uku likitoci su kayi akan AFREEN sannan wani docter ya fito suna ganin su duka suka nufi shi suna tambayar sa ya ake ciki, murmushi docter yayi sannan yace "Ku kwantar da hankalin ku yarinyar ku tana lafiya kawai tarin damuwa ne ya mata yawa sai jinin ta da ya ɗan hau kaɗan amma da ikon Allah mun samu mun daidaita shi yanzu babu wata matsala komai normal, dama abinda yasa muka jima a kanta numfashi ta ne yayi mugun bamu wahala kamin musamu ya daidaita saboda yayi nisa sosai ga barin jikinta to amma da yake Allah ya nufa ta da sauran kwana a doron duniya kunga asamu an shawo kan matsalar, yanzu haka lafiyarta lau sai dai rashin ƙarfin jiki, kuma zai daina ne a sani sanu sai dai munyi mata allura bacci, ta samu bacci karku damu amma ba zaku samu ganin ta yanzu ba sai ta farka dan tana da buƙatar bacci, abinda kuma zai hana a baku sallama a yau shine munason muka yanayin jikinta zuwa gobe da safe sai na baku sallama inshallah." Doctor na faɗar haka yayi gaba abinsa.


Duk wanda ke wajen saida ya ɗaga hannun sama ya faɗar alhamdulilah tare da murmushi kwance a fuskar sa amma banda tanti, sai a lokacin maman da zeinab da Hasina suka ɗan kwantar da hankalin su har suka nemi gun zama suka zauna tare da yi mata addu'a, a nan maman ke tambaya Hasina mai ya faru har ta shiga wannan halin.


Sai a lokacin ta tuna cewa ashe dole a tambaye ta miya faru ita kuma bata shirya abin faɗa dan haka sai tayi kamar bataji ba abinda maman tace ba, har sai da maman ta sake ta tambayar, ta ɗago tana in ina sannan ta daure ta gyara maganar tare da cewa "Maman babu abinda ya faru daga fa muna cikin fira tana faɗaman cewa ita fah bata son barin gidan su bare garin baki ɗaya, gashi nan har Niamey za'a kaita alhali duk dangin ta suna maraɗi shi kenan sai ta fara rera kuka na shiga rashin ta ai fah da kukan yaci karfin ta sai kawai gani nayi ta sulale a kan jiki ta zube saman bed sumamiya."


"Maman da bata fahimci ƙarya Hasina ta sheƙa mata tace "To ba dole tayi hakuri ba, ni da aka kayoni gidan mahaifinta tun daga Agadez har Niamey da kuma daga Niamey ɗin muka yo nan mi yasame ni ko wa nasani a cikin garin banda mahaifin ta, sai ita taki yarda da hukuncin Ubangiji?


Ita dai Hasina bata ce komai ba, sai zeinab da tace "Maman ita ma fah zata jure kawai kun san hakan sai ta faru kuma idan ta samu watani ai ni cen gun ta zan koma dan ni idan bata gida bana iya zama gaskiya."


Harara maman ta sakar ma zeinab sannan tace "Kun dai ji da shi keda ita ai kusan halin ku guda." Murmushi kawai zeinab tayi.


Ba'a wani ɗauki lokaci ba ta farka suka runtuma duka cikin ɗakin suna mata sannu duk sai taji ba da taga yanayin iyayen duk hankali su a tashe saboda ita da sauri ta kamo hannun mahaifin tace "Papa kuyi hakuri na tayar maku da hankali wallah je pas l'attention de le faire kawai Allah ya kawo.


Murmushi papa ya sakar mata sannan yace "Karki damu farin ciki family sadisu, dama hakan zata iya faruwa yanzu abu mahimmanci shine Allah ya baki lafiya."


Murmushi tayi tare da faɗin "Ameen papa."


Kowa hankali shi ya kwanta gani da sauki sosai, ƴan uwa da abokan arziki sai shigowa suke suna duba har da Adamu ƴaƴan papa da matan sa da ɗiyan ida Maryam cousin ɗin ɗiyar Abba Adamu Wada suke kusan sa'a ɗaya ita ta zo duba ta har ta ce ita wajen AFREEN zata zauna, idan ita Hajiya Zakiya kaka su da ta biyo Adamu ta zo tana ta masifa ta cikin gida amma a kasa sanar da ita jikata ba lafiya da so akayi sai ta mutu kamin a sanar dani ko babu dai wanda ya tamka mata."


Wasu motoci ne guda uku masu masifar naga sun kun kai a cikin asibitin suka nufi gun parking sukayi daidaita suka tsaya da sauri naga direban motar da tafi kowace mota haɗuwa naga ya fito yaje ya buɗe kofar baya, wata kyakkyawa ƙafa naga an fara zurowa sannan a ƙara fido da ɗayar kamin mai ƙafafun ta fito baki ɗaya, baki da hanci da na saki tare da waro idanu ina mai furta tubarukallahu ahasanul kalikin ne Masha Allah saboda ganin wata haɗaɗiya kyakkyawa nagartaciya mata da tafito daga cikin motar nan kai cewa ma matar nan na da kyau zai iya zama zagi ne wallahi

Please Login or Register in order to submit comment