Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kicin tanacewa "Wallahi anti duk abinda na faɗa akanki gaskiya ce ba shirme ba."


Murmushi AFREEN tayi tare da girgiza kanta tana cewa "Allah shirye ki Zeinab, a tare suka shiyar dinning ɗin tsaf.


Zeinab tace "Anti wallahi duk in kinyi girki sai naji idan inaci kamar karna daina."


Wani murmushin AFREEN ta koma yi sannan tace "Dan Allah Zeinab surutun nan naki ya isa haka kada kikai gasamin ciwon kai jeki kiyi wanka sai ki fito ki karya kinji ƴar albarkar ƙanwata."


Kollon AFREEN ɗin tayi sai tace "To shikenan anti na mai tsada."A guje ta kwasa da nufi ta bar gun da sauri AFREEN ta tsayar da'ita tace "Zeinab ban hanaki gudu ba wai ke ba zaki iya tafiyar hankali ba dole sai kin haɗa da gudu?"


"Lah anti na manta yi hakuri daga yau na daina insha Allahu," sannan tabi hanyar ɗakin nasu ta shige. Ita ma AFREEN ɗakin nata ta nufa.


Tana shiga ɗakin ta ta wuce toillet dan yin wanka, bata tare da ta ɓata lokaci sosai ba ta fito da tawel ɗaure a ƙirjinta bakinshi iya cinyoyinta ɗaya tawel ɗin ɗaure akanta kusan wani drawer ta ƙarasa ta buɗe ta fito da abin busar gashi sannan ta rufe drower taje gun soket ta saka abin busar da gashin sannan ta fara busar da shi tana kammalawa ta mayar da shi ma'ajiyar sa tareda komawa gun mirror ta zauna ta fara shafe shafen mai da turaruruka humra masu mugun kamshi mai gigita tunanin masoyan da haɗaɗen kamshi mai kwantar da zuciyar duk wani ma'a buci son kamshi ta ƙarasa shafe shafen ta nufi wardrobe ta fitar da wasu haɗaɗu English wears riga da wando riga puple wando baƙi a take ta haɗe cikin ƙananun kayan ta wanda suka kamata sosai suka fito da gaba ɗaya surar jikinta ba ƙaramin kyau tayi ba idan ka ganta kamar ka saɓe ta ka gudu, komawa tayi gun mirror ta dauki turaren feshe kala uku ta shiga fesawa jikinta idan ta fesa wannan ta ajiye ta fesa wannan zakace wani babban bahon turare ne aka malayar a jikinta da kuma ɗakin nata sabida wani haɗaɗen kamshi ne ke tashi a jikinta da kuma ɗakin gabaɗaya ita dama ba ba'a buciyar yin kwalliya ba kuma ba dan wai bata iya bane kawai bata yine tana kammala kominta ta koma kan gadon ta kwanta tare da janyo wayar ta kuna data tana chatting da kawayenta.


Wani group ɗin familyn sune ta shiga tareda yin sallama tare da tura emoji na sannun ku ai kuwa kamar jiranta suke suka mata ca ah AFREEN kece yau da magana a group ɗin kullum ke karatu karatu ba damar ki hayo ayi fira wasu kuwa suna ah sis munyi miss ɗinki ya karatu duk tayi ta basu amsa daidai da saƙon kowa, tana cikin chatting ɗin Zeinab ta shigo ɗakin tare da sallama sannan ta ƙara so inda take tace "Anti inji papa ki fito mu ƙarya ke ɗaya ake jira."


AFREEN ta tashi zaune sannan tace "Jeki kice ganinan zuwa."


"A'a anti zanjira ki mufita tare wallahi anti AFREEN kinji wani kamshi mai sanyin ɗaɗi dake tashi a ɗakin nan da jikinki lale anti kina jin ɗaɗinki kuma idan nace komai naki na daban sai kiyimin gardama amma ko bani ba nasan watarana wani zai faɗa maki ko kuwa har antaɓa faɗa maki hankan wa ya sani."


"To sarkin ƴan iya magana nidai bari na ɗauko hijab ɗinna mu wuce," ciro hijab ɗin ta tayi daga wardrobe tasaka har yana jan kasa sannan ta kama hannu ta suka fice a ɗakin, kowa ya halarta a gun cin abincin sune kawai ake jira suna zuwa suka zauna AFREEN ta gaida iyayenta sannan ta zubawa kanta abinci baki wanda zata iya ci kamin papa yayi bismillah ya fara ci sannan kowa dake wajen suka fara ci al'adar gidan suce duk idan zasu ci abinci sai papa ya fara kaiwa bakinsa kannan iyayen su mata sai yaran daga babba zuwa ƙarami shiru bakajin ƙarar komai sai ta spoon can maman da ke hankalce da AFREEN tace "AFREEN abincin nan fah sai kin cinye shi naga kamar bakai sonci, kuma miye abin saka hijab dan zakizo nan, anyi mutum kullum cikin hijab dai wai baki gajiyane?"


Murmushi tayi sannan tace "Kai maman ai zan cinye shi insha Allah ba wani dayawa bane, kuma ƙananun kayane a jiki na shiyasa na saka hijab gudun kada wani ya shigo."


Kamin maman tayi magana dan ƙaramin ƙanansu wato Imran yace "kai anti kedai kinason saka hijab ne."


Dayake kusanta yake sai ta ɗan shafa kanshi tace "Autan maman ai na sabane da kaima mace ne ai da zan koyama ka ne ya ƙaratu injin dai nata ƙoƙari?"


"Karatu alhamdulilah, Allah ya sawaƙe ko dani macece bazan yarda nayi ta saka hijab kullum kamar wani kala."


Duk wa'inda ke gun su kwashe da dariya banda umma da duk haushi suke bata, sai Fahad da yayi murmushi dan bai cika yin magana ba kokuwa kace ka ganshi yana dariya sai ajima sabida shi magana ma wahala take mashi bare yayi dariya idan yana ga yuri zaya iya ƙinyi magana duk abinda kuwa za'a ce har abada gun ba zai ce komai ba wani lokaci ba har mantawa ake da yana gun kusan halinsu guda da AFREEN saidai itata ma fishi yin magana.


Papa yace "Imran bakada dama"


"Wallahi papa da gaske nake inada ni mace ne bazan iya irin na anti AFREEN ba gaskiya."


"To kuma sai Allah ya fito dakai a namiji." papa ya faɗa yana murmushi.


Aiko da sauri Imran yace "Inda naji daɗi kenan."


Nan ma dariyar sukayi sun tsagaita dariyar ne Tanti tace "Gaskiya AFREEN ki rage saka niƙaf da mayan hijaban nan naki idan bahaka ba taya zaki wani zai gangi yace yana sonki har kiyi aure nida nakeson ace tare dake da Khairat za'a aurar a lokaci guda kinga maman Fauziya zata dinga mana kurin cewa zata aurar da ɗiyar ta amma kinga idan auren Khairat da naki yazo lokaci guda babu batun mana kuri."


"Ah to faɗa mata sabida kunfi kusa." maman ta faɗa


Ita kuwa AFREEN duƙe kanta tayi tare da cewa "Kai Tanti aure nikuma tun yanzu."


Tanti tace "Ban gane miki nufi da tun yanzu ba kina nufin baki isa aure bane ko miye? to ko Zeinab yanzu aurar da ita ake bare ke masha Allah da kika girme mata sosai sabida kin bata kusan shekara 6."


AFREEN dai kanta a ƙasa bata ƙara cewa komai ba."


Sai papa yace "Haba Sakina jimin kinason hana min ɗiyata ƙarasa cin abinci duk kinsa taji kunya, ai irin su AFREEN har gida Allah ke kawo masu nagartacan miji nagari wanda zai kula da ita ko bayan ba ran mu insha Allahu zakusha mamakin kalar mijin da zaizo mata har gida ba tareda ita kanta ta shiryawa hakan ba."


Tanti tace "Hum to muna zuba ido mu gani tunda ka ƙule mata gidin amma nidai kam dole a rage saka niƙaf ɗin nan sabida so nake na aurar da ɗiyata da yuri ah to."


"Karki damu ai zata sumu ne koda kuwa cikin niƙaf ne shi aure Allah ke haɗa shi kuda ke ƙanin sabida saka niƙaf ɗin da take yi samarin za suyi tunanin matar aure ba haka bane budurwa nawa ke saka niƙaf amma kuma ta sami mijin aure ai Allah ya banbanta mai aure da mara aure ko da kuwa cikin niƙaf ɗin ne za'a iya ganewa." Papa ya faɗa tare da kallon gun da AFREEN take da har yanzu bata ɗago da kanta ba.


"Allah sarki to Allah nuna min wannan ranar da AFREEN zata zo tace anti ga sirikinki nan yazo gaidaki kai ranar kowa sai yaga kwasar shoki aka kara kwashewa da dariya har yanzu dai banda Umma da suka gama ɓata mata rai ƙiris take jira ta fashe, AFREEN ma sai da ta ɗan murmusa


Haka dai suka yi ta raha da farin ciki har aka kammala cin abincin, AFREEN ta ɗago ta dubi mahaifin na tace "Papa anjima inason zanje gidan anti Fauziya na kwana biyu ba mu haɗu ba sai ta waya, idan mun taso daga islamiyya sai na biya tacan daga sai nayo gida."


Kamin papa yayi magana Zeinab tayi "saurin cewa "Dan Allah anti ina zuwa nima na jima bangan taba." da khair ta samu tayi maganar dan tunɗazu take son tayi magana tanason tsoma bakin ta cikin cikin firar da suke amma umma ke hararen tana mata nunin da inta kuskura tayi magana sai tayi maganin idan suka gane ɗaki."


Aikuwa itama umman da sauri tace "Jacan dan Allah da bakinsa san ciwon kanki ba ni anya kuwa Zeinab ba hurhuran ki akayi min a asibiti ba irin wanga abu na kutsa kanka inda ba'asan darajar kaba to dan ubanki babu ida zakije shegiya mai kama da maƙiyan ta kwakwata na rasa yanda akayi baki yo halina ba ko da yake yawan zama tare da masu mugun hali ai dole ki koy........


Bata ƙarasa faɗar abinda tayi niyar faɗa ba papa ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu sannan yace "Wallahi salamatou ki fita daga idona na rufe yanzu gabana kike zagin yarinya nan ta uwa ta uba ko kunya bakiji kuma ko kara babu, in ba abinki ba aikece mai mugun halin babu mai fatan ya yi hali irin naki kuma kaki koma sheganta min yarinya dan ni ubanta gani a kusa, abu na biyu shine sai taje gidan yar uwata dan baki isa ki rabamin kan ɗiyaba."


Dama tunda papa ya fara magana Fahad da Imran suka bar gun haka Safina da Amira da hamida ma su bar gun yayi saura daga maman sai tanti da umma da kuma AFREEN da Zeinab, maman har ta miƙe zata bari yurin papa yace ta dawo ta zauna."


Sannan ya juwo gun su AFREEN yace "Ku tashi kuje daga lokacin zuwa islamiyya yayi kuyi tafiyarku daga can sai ku wuce gidan Fauziyar hada su Safina kuje ku duka kukai mata ziyara."


AFREEN ta kalli papa da murmushin ɗauke afuskarta ta ce "To shikenan papa mun gode."


Yace "Akwai saƙo dana bayawa mamanku nace ta bada aikaiwa Fauziya tunda zaku tafi to ku tafi mata dashi."


Insha Allahu papa AFREEN ta faɗa tare da barin gun itama Zeinab tabi bayan kowa ya koma nasa daƙin umma sakin tsaki tayi tare da barin gun bin ta papa yayi da kallo har ta ɓacewa ganinsa ransa du a ɓace ya juwo da niyar yin magana maman tayi saurin cewa "Dan Alhaji na kada kabari abinda umma Zeinab tayi ya ɓata maka rai idai halinta ne ai ka riga ka saba kuma ina mai tabbatar maka da watarana zata daina dan Allah kayi hakuri ko kaɗan bani kaunar ganin bacin ranka mijina."


Aiko a take papa ya washe baki yana cewa "Allah kuwa sarauniya ta?" ɗan shiyasa nakeson zama a kusa dake kullum kina faranta raina baki bari wani ya bata min shi dan haka kullum nike ƙara godewa Allah da ya banike a matsayin mata aurena."


Haka dai datijawan nan sukayi ta faɗawa junansu kalaman soyayya kamar dai wasu ƙananun yara, Tanti dage zaune wajan da suka gama ɓata mata rai ta sulale ta barsu nan ba tarare da sun saniba dan kuwa su sun ma manta da tana yurin zauna a riga da an tuno da soyayya yarinta.


AFREEN na shiga cikin ɗaƙi komawa tayi kan gadon ta kwanta sannan ta kuma janyo wayar da ta bar datar a kune ne tun da zata fita kumawa tayi cikin group ɗin da ta bari suna hira taga yau duk maganar da suke akan tane nafa itama ta biye masu suna ta fira cikin nishaɗi da farin ciki kamin daga can taga saƙo wata sabuwar number ya shigo mata fita tayi daga group ta koma wajan bakuwar number kamin ta buɗe saƙon sai tayi ta tunanin to wacece ta turo mata da saƙo ta danganta saƙon da na mace ne sabida tasan babu namijin da yasan number ta inba cousins ɗin taɓa kuma sun ɗin ma ba kowa keda ita ba saƙo ukune aka turoma ta ta baƙuwar number.


Buɗe saƙon tayi a take gabanta ya yanke ya faɗi da sauri ta tashi zaune cike da firgici tana ƙara karanta abinda ke cikin saƙon tana ganin kamar ba gaskiya bane abinda ta karanta, cikin ƙanƙanan lokaci jikinta yafara rawa dandanan yanayin ta ya canza ƙarara ake hango tashi hankali a tare da ita bata masan lokacin da wayar ta kubece ta faɗi ƙasa ba saida taji ƙarar faɗuwar ta


Batabi ta kan wayar ba ta faɗa duniyar tunani.


Ga saƙon kamar haka..................................


Ku biyoni don jin wane irin saƙone ya firgita AFREEN har haka
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Écrit


Par


*QUEEN ZEEFAT*


_Ƴar_
_Mutun_
_Niger_



Wattpad@nazichou




💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003



_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_



Page : 25 & 26


Buɗe saƙon tayi a take gabanta ya yanke ya faɗi da sauri ta tashi zaune cike da firgici tana ƙara karanta abinda ke cikin saƙon tana ganin kamar ba gaskiya bane abinda ta karanta, cikin ƙanƙanan lokaci jikinta yafara rawa dandanan yanayin ta ya canza ƙarara ake hango tashi hankali a tare da ita bata masan lokacin da wayar ta kubece ta faɗi ƙasa ba saida taji ƙarar faɗuwar ta


Batabi ta kan wayar ba ta faɗa duniyar tunani.


Ga saƙon kamar haka: *ASALAM ALEIKUM MALAMA AFREEN DA FATAN KIN WUNI CIKIN KOSHIN LAFIYA, NI SUNANA KAMAL A GASKIYA TUN DA NA GANKI NAJI KIN KWANTA MIN DUK DA BAN TAƁA GANIN FUSKAR KI BA AMMA NAJI INA ƘAUNAR KUMA NASAN KE BA MATA AURE BACE SABIDA SAIDA NA BIBIYEKI HAR NAGANO DA HAKAN KO NUMBER WAYARKI SAIDA NA WAHALA SOSAI WALLAHI HAR NA FIDA RAI DA SAMU SANNAN ALLAH YA TAIMAKE NI NASAMU AFREEN WALLAHI BADA WASA NAZO BA NI AUREN KI ZANYI DUK DA BASANIN KAMAN NIKI NAYI BA ZAN ZAUNA DAKE DA KO WACE IRIN KAMA KO DA KUWA DAGA BAYA NA NA GANKI WALLAH KE MAI KYAUCE KO AKASIN HAKA WANNAN BA MATSALA TA BACE, KAWAI ADDINI DA NA LURA KINADA SHI YAJA HANKALI NA GA REKI AFREEN INA SONKI INA ƘAUNARKI DAN ALLAH INA JIRAN JIN HUKUNCIN DA KIKA YANKE DAN ALLAH BANDA SHARIYA MASOYIYATA INA JIRAN JI RA'AYIN KI A KAINA KUMA IDAN AN BAN DAMA NAZO HAR GIDA NA GABATAR DA *KAINA*
*

AFREEN da ta faɗa cikin duniyar tunani a can cikin ƙasan zuciyar take waye wannan a ina ya samu number na ya'akayi yayi bincike a kaina yasan banda aure kuma yasan sunana duk boye kaina da nake saida aka samu wanda zai nemo asalina.

Ƙarar da wayar tane tayi ya dawo da ita duniyar tunani data lula da sauri da duƙa ta ɗauko wayar da ta faɗi ƙasa kamin ta ɗago tana duba screen ɗin ganin me kiran nata yasata sakin wani sanyenyen murmushi a take ta ɗauki kiran ta kara a kunne tare dayin sallama da murmushi ɗauke a fuskar ta, daga ci wayar aka amsa sallamar tare dacewa "Hum sister ashe kina a raye amma kika manta dani har haka?"


Wani murmushin AFREEN ta ƙara saki sannan tace "Haba rabin raina kin san hakan ba halina bane wallahi karatu ne ya ɓatar dani ga na école ga na islamiyya inba dan haka ba ai kinsan ba zan iya mantawa dake ba dan Allah ki hakuri my Fanna kina raina ban manta dake ba."


Daga cikin wayar wada aka kira da Fanna tace "To shikenan my rabin rai ƙorafi ya ƙarɓu nasan da ba zaki manta dani ba to ya kwana da yawa kuma yaushe ne sabkar ku ta tahafiz?"


"Kwana da yawa sai alkairi cœurly (heartly) nan da sati ukune saukar insha Allah oubien tu va venir pour participer (ko zowa zakiyi dan ki halarci saukar)?"


"Oui cœurly je veux venir s'il plaît à dieu comme on sera en congé d'ici une semaine je veux vraiment participer pour la deuxième fois à ta sauka comme ta première sauka j'étais à Maradi et aussi même celle là je participerai insha je viendrai de Diffa jusqu'à Maradi juste pour entendre ta voix entrant de lire le coran pour la deuxième fois devant beaucoup de personnes woow Macha Allah que le bon dieu nous montre ameen,("Yes heartly I want to come please God as we will be on leave within a week I really want to participate for the second time in your sauka as in your first sauka I was in Maradi and also even this one I will participate insha Allah i will come from Diffa to Maradi just to hear your voice coming in to read the quran for the second time in front of many people woow Masha Allah may the good god show us ameen)."


"Woow je serai très heureuse si tu viendras cœurly (Woow I'll be very happy if you come heartly) tu va venir quand? (yaushe zakizo)?"


"Kai cœurly irin wannan gaggawa haka, ai ni nace zan zo? to ki zuba ido bazata zan miki." Fanna ta faɗa


AFREEN tace "Haba cœurly kada kimin surprise (bazata) mana ki sanar dani koda lokacin zaki shigo bus ne please."


Dariya Fanna tayi tare da cewa "To zan duba naga ni idan zan iya sanar dake ina papa da maman da tanti da umman Zeinab duk ko lafiya ko?"


"Lafiya lau suke alhamdulilah, ya su anma da baba suke ina ƴar ƙanwata Aicha da Sagir? wallahi nayi kewarsu sosai kamar dai na bar maraɗi nazo na ganku nakeji amma dai idan zakizo tare da Aicha zakizo ko?"


Fanna tace "A'a ni daya zanzo sai ki bari idan zan dawo sai ki biyoni kizo ki gansu in har kewar ta gaskiya ce."


"To shikenan zan nuna miki kuwa nayi kewarsu."


"Dan Allah ki gaida min su anma sosai da sosai idan kuwa Aicha na kusa ki bata wayar mu gaisa."


"Bata kusa ta tafi islamiyya Fanna ta faɗa a taƙaice."



AFREEN tace "Idan tazo ki gaida min ita."


"Zataji insha Allah cœurly wallahi sai nakeji kamar ace har yanzu a gari guda muke nima ki gaida min ƴan gidan baki ɗaya sai anjima dama nayi kewarki ne sosai nace bari na kiraki."


"Wallahi cœurly sosai nima nayi kewarki amma insha Allah sai kun dawo Maraɗi ko kuwa mu haɗe a University guda zamu dai kasan da juna yuri ɗaya insha Allahu."


Fanna tace "To Allah ya yarda wai ina Hasina? kwana biyu itama bamu gaisa ba ki gaida min ita."


"Zataji insha Allahu," AFREEN ta faɗa ataƙaice.


Sannan Fanna tace "Sai musake waya naji anma na kirana." Ba tare da ta jira abinda AFREEN zata cewaba ta katse kiran ta tafi idan mahaifiyarta ke neman ta.



**** **** ****

*WACECE FANNA*

Fanna Musa ƙawar AFREEN ce tun suna yara a tare sukayi primary da secandary mahaifinta da mahaifiyarta barebari ne na garin Diffa aiki ne ya dawo dashi Maraɗi kuma hakama yanzu aikin ya ƙara mayar da shi mahaifar sa wato garin Diffa, sanadin ƙawace da muguwar shakuwar da ke tsakanin AFREEN da Fanna yasa iyayen kula amintaka wato maman mahaifiyar AFREEN aminiyar Anma ce mahaifiyar Fanna sabida maman batada wata abukiyar shawara kamar anma haka papa suna mutunci sosai da baban Fanna, yanzu haka Fanna da iyayen su koma Garin Diffa da zama sabida aiki da ya dauke su ya mayar da su can kuma dama nan ne garin su na haihuwa.




**** **** ****

AFREEN na gama wayar idon ta suka ƙara sauka kan saƙon da kamal ya aiko mata a lokacin ya ƙara turo da wasu saƙunan ku san guda huɗu bata bi ta kan saƙon ba kawai ta'ajiye wayar ta nufi wordrobe don canza kayan jikin ta zuwa na islamiyya, akayi sallama tareda buɗe ƙofar aka shigo amsa sallamar tayi tana kollon bakin kofar, Firdaoussi ce cousin ɗin ta shigo da sauri AFREEN ta saki hijab din datake ƙoƙarin sakawa da gudu ta nufita ta rungume ta sakin murmushi tare da cewa "Sannun ki da zuwa cousin wallahi tu m'a beaucoup manqué (I miss you a lot) naji daɗin ganin ki tana faɗi haka tare da rabata da jikin ta itama Firdaoussi tana murmushi tace "Gashi ai ni da nafi kewarki nazo naganki cousin yanzu dai kam kin rage ziyara."


AFREEN tace "Firdaoussi ko ranar naje gidan ku ba kainan ke ɗin ce da wayon tsiya."


"Ah habadai AFREEN da kikaje baki sameni ba ai sai kikirani duk abindab nake sai na barshi na zo kuma kinga mama bata sanar dani kinje ba nasan ko ta manta."


"Eh nasan mantawa tayi amma naje wallahi ko sati ma ba'ayi ba, yanzu dai zo ki zauna na barki a tsaye naje na kayi maki abinda zaki ci." tare da jawo ta ta zaunar da ita saman babbar kujerar dake cikin ɗakin.


Firdaoussi tace "Kai cousin wallahi a ƙoshe nake sai da nayo breakfast daga gida kamin na fito yanzu kinga fah yanzu ƙarfe tara da rabi ne kawai ban daɗe da yin kariba, yanzu idan da dambu nama ki kayomin da ruwa masu sanhi sannan ki kara gudun AC dakin nan zafi sosai naje kodan nabiyo ranane."


To shikenan ƴar uwa kiyi kamar kina cikin ɗakin ganinan zuwa," AFREEN ta faɗa tare da ɗaukar remote ɗin kuna AC ta ƙara mata gudun ta sannan ta fice a ɗakin.


Bata jima ba ta dawo da plet dauke a hannu ta ɗayan hannu kuwa da jus (juice) mai sanhi sosai da kofi ta'ajiye a gabanta tace "Sarkin son dambun nama to bismillah taso kici kinyi sa'a akwai shi jiya maman tayi shi." AFREEN ce ke maganar


Ɗagowa daga ɗan kishingilan da tayi tana murmushi shi tace "Kai AFREEN nice ma sarki cishi kenan ai duk son dambun namana ke kinfini ai nima dake na koya, ya nagangi da kayan islamiyya ko tafiya zakiyi ne?" Firdaoussi ta faɗa


AFREEN tace "Eh wallahi shirin islamiyya ne nayi baga hijab ɗin can ba da na ganki na jefar dashi a wajan can dan murna, amma tunda kinzo bari naje na sauke su Zeinab a islamiyya sai na dawo muyi hira nasan dai ba banza ba aka zomin ziyara ba da safan nan."


Murmushi Firdaoussi tayi tace "Sai kin dawo bari nima nagama cin abincin na sai naje na gaida su maman sabida da nashigo falon babu kowa, kuma nasan zan samu gani papa tunda nasan yau yana gida na kwana biyu banzo na gaida sa ba yau zanje na ɗan zanta da ubana."



AFREEN tace " To shikenan bari naje na dawo to kamin nan kin gama komai, nufar idan ta jefar da hijab ɗin ta tayi ta saka sannan ta fita a ɗakin da niƙaf a hannu ta.


Tana dawo ta tardo Firdaoussi tana kallo a wayarta da sallama tashigo ɗakin kamin take fida hijab ɗin ta linke ta mayar dashi ida yake tare da fida kayan islamiyyar suma ta nike sannan ta saka wata haɗaɗiyar dagowar riga mara nauhi sabida Allah yayiwa AFREEN son saka riga doguwa don yawancin kayan jikinta dogayan riguna sunfi yawa, dawowa tayi kusa da Firdaoussi ta zauna Sannan tace "To sis toshi muyi hira."


Miƙewa Firdaoussi tayi zaune sannan tace "Malama AFREEN que babu komai a wayarki sai wa'azi."


AFREEN tace "To miki keson nasaka a ciki banda wa'azin ƴar uwa."


Murmushi sukayi su duka kamin suka ci gaba da fira. Firdaoussi tace "Yawa AFREEN yanzu ina ɗaukar wanki naga anturo miki da wani sako baki bayar da amsa ba se kawai na'ari bakin ki naci maki dusa na mayar maki da sakon."


AFREEN najin haka ta gane ko wane saƙo take nufi da sauri tace "inna lilahi wa inna ilaihi raji'un miyasa kika mayar ban fah San ko waye ba kawai naga ya turo man da

Please Login or Register in order to submit comment