Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ɗoke masa hankali da da nutsuwar ba sai dayaje kwanci bacci da dadare, yanda kasan yanzu ne take maganar haka ya dingajin kalaman da ta ɗinka faɗa wa ƙawarta na dawowa cikin dodon kunnansa zazaƙa muyar nanta ta ke mugun bugun kunne sa kwata kwata ya rasa ya zaiyi, gabaɗaya yakasa bacci ya rasa miye dalilin da yasa ya kasa mantawa da muryar, shida baisan ta ba fuskar ta ma aɓoye take, yanzu idan cewa za'ayi ya nuna ta acikin jama'a ba zai iya ba indai ba da kalar shigar da ya ganta ba zai sake ganinta to a lokacin nan ne zai shedata, sosai tunanin ta ya adabi rayuwarsa, har yana ce Allah sa ba matar aure, idan kuwa matar aure ce ya zanyi a take wani sashe na zuciyarsa yace masa idan ma matar auren ce ko akasin haka miye haɗinka da ita da ka zauna kana tunanin ta AFREED, ita ba wata yar uwar ka ba amma duk kabi ka damu da ita haka, a fili kuma sai yace miyasa na damu da ita ne zauna ina tunanin ta ko dai taimako takeda buƙata ne? amma ai banganta cikin yanayin masu neman taimako ba hasali da mota tazo ko ba tata bace ba ai zai iya yiwuwa ta gidansu ce."


AFREED da yaga tunanin AFREEN na neman zaman masa matsala kawai sai ya tashi daga kwanciyar dayake yana jan ɗan ƙaramin tsaki, tare da miƙewa baki ɗaya ya nufi toillet ya ɗauro alwala sannan ya fito ya shimfiɗa darduma ya shiga yin ƙiyarmar lailih, saida akayi kiran sallar farko ta ƙarfe huɗu dare kamin bacci ya fara fizgar shi, ba tare da ɓata lokaci ya sallame daga sallar da yake ya nufi lafiyayen bed ɗin sa ya kwanta a take wani bacci mai dadi da mafarkai kala kala ya yi awon gaba dashi.


***** ***** *****
AFREEN nazuwa gida tayi parking motar a ƙofar gidansu sannan suka fito su duka a motar suka shiga cikin gidan suna shiga falon suka tarda maman zaune tana zaman jiran su, Maman na ganin su ta sauke ajiyar zuciya sannan tace "Miya tsayar da ku harhaka baku dawo ba? kunsa hankalin mu duk ya tashi yanzu nan papan ku ya shiga ɗaki dan sauya kaya yaje neman ku a masallaci sabida anyi ta kiran wayan ki yana ƙara ba a ɗagawa, sai daga baya da na shiga ɗakin na tarar da wayar a saman bed ɗin kika barta."


AFREEN ta saki murmushi tace "Maman ku kwantar da hankalin ku mana babu idan mukaje duk lokacin da muka ɗauka bamu dawo ba muna masallaci."


Maman tace "To ai chikenan tunda gashi Allah ya dawo daku lafiya bari naje na faɗa ma papan naku."


Tana ƙoƙarin tashi saiga mahaifin nasu ya sauko da key mota a hannu sa maman na ganinsa ta koma idan ta shi ta zauna, magana ya fara a lokacin da yazo ya zauna yace "AFREEN ɗin papa ina kuka tsaya hakane yau?"


Kallon mahaifin nata tayi cike da kaunar sa tace "Papa babu inda muka tsaya muna masallaci mota na ne na ajiye a inda maza ke ajiye tasu motar ba tare da nasani ba ina sauri munyi lati zuwa kuma ana shirin tayar da sallah, saida muka fito ne Zeinab ke sanar dani a can na ajiye shine muka bari saida mutane suka tafi sannan mukaje na fitar da motar."


Murmushi papa yayi sannan yace "Dama nasan babu inda zakije ba tare da kin sanar damu ba Allah maku albarka yanzu ku shiga daga cikin ku fido hijaban ku sai kuzo kuci abinci."


Da to suka amsa su duka harda Hasina sannan suka wuce ɗakin AFREEN, su Zeinab kuwa suka nufi ɗakin mahaifiyarsu, suna shiga Hasina tace "Besty wai ya maganar KAMAL ne baice dake zaizo ba?"


"Kai besty wallahi Ni har na manta dashi ma wallahi amma yace man yau zaizo ya ga papa ni kuma ma na kasa faɗa ma papa maganar zuwan nasa wallahi ko maman bazan iya faɗa mata ba, kuma bai kamata yazo ba, ba tare da na sanar dasu ba kinga hakan bai kamata," AFREEN ce ta faɗa ta ƙoƙarin cire hijab ɗin jikinta."


Ajiyar zuciya Hasina ta sauke tace "Wallahi har naji dadi besty, dan gayawa papa wannan mai sauƙi ne, kawai tanti zaki faɗa mawa sai ta faɗa masu baki ɗaya sabida nasan da itace kaɗai zaki iya faɗa ma."


AFREEN tace "Hakane duk na ruɗe narasa ya zanyi shiyasa ma na manta da na faɗa wa tantin."


Hasina tace "To ai yanzu na tuna maki."


Wata nauyaya ajiyar zuciya AFREEN ta sauke tace "To muje muci abinci, muna ƙarasa wa sai naje na faɗa wa tantin, sannan muje na faɗa wa maman da papa zanje gidan ku tunda yau bazamu makarantar yamma ba."



Fita sukayi a ɗakin sannan suka nufi dinning inda su Zeinab ke zaune suna jiran fitowar su ba tare da ɓata lokaci ba aka zubawa kowa abincin sannan suka fara ci, suna ƙarasa cin abincin AFREEN da Hasina suka nufi ɗakin tanti, suka tardo ta tana ninke kayan ta sallama sukayi tare da nufar gefen bed ɗin suka zauna AFREEN tace "Tanti sannu da gida kikawo na ƙarasa nike maki kayan."


Murmushi tanti tayi sannan tace "Yawa AFREEN, kibar shi ai nama ƙarasa AFREEN, tanti ta faɗa tare da dawo kusa da su ta zauna tana cewa "AFREEN faɗamin mike faruwa naga alamun da magana a bakinki."


Murmushi AFREEN tayi tareda sade kanta ƙasa sannan tace "Tanti dama.....dama." sa kumai tayi shiru ta kasa gayin abinda tayi niyar faɗa."


Gaban tanti ne ya wanke ya faɗi har saida alamun tsoro ya bayyana a fuskarta tana addu'ar Allah yasa ba abinda take tunani bane, kamin take basarwa tace "Gayamin mana ma fille tsakani na dake babu wannan kunyar."


Saida AFREEN ta ƙara duke kanta ƙasa sannan tace " Tanti dama..... Wanine yace zaizo ya gaida ku, dam dam gaban tanti ya faɗi da ƙarfi a lokacin AFREEN har ta riga da ta fice daga ɗakin dan kunya sai ta jin abin gashi banba rakwai wai itace saurayi zaizo gunta."


Hasina ta dawo da tanti daga duniyar tunanin da lula a lokacin da take cewa " Tanti shine takeson ki faɗa wa papa dan ita ta kasa yanzu ma da kyar na taso ta gaba da ta faɗa maki."


Murmushi yaƙe tanti tayi sannan tace "Aiko AFREEN akwai kunya nima wai dan muna yawan fira ne da ita har ta iya faɗamin insha Allah zan faɗa masu shi da maman ta Allah kawo sa lafiya wane lokaci zaizo?"


"Bayan sallar isha'i." Hasina ta faɗa a taƙaice.


To shikenan babu damuwa sosai nayi farin ciki da jin haka na kusa shan bikin ɗiyata Allah nuna min lokacin nan da alkairi."


Murmushi Hasina tayi sannan ta tashi ta fita tabi bayan ƙawarta. Tanti na zaune a inda suka barta kusun minti 10 tana zaune tana saƙa da warwara sannan ta tashi ta nufi ɗakin maman, tana shiga suka gaisa sannan ta faɗa abinda suka tattauna tsakanin ta da su AFREEN cikin da farin ciki take faɗa maman abinda AFREEN ta faɗa mata. Murmushi Maman tayi sannan tace "Hum AFREEN sarkin kunya to kije ki faɗa wa mahaifin nasu kamin ya fita dan yasan dazancen."


"A'a maman Fauziya mi zai hana ke ki faɗa masa." Tanti ta faɗa tana kai duban wajan maman.


Maman tace "A'a ki daije da kanki waka abakin mai ita tafi daɗi sabida ke a ka baiwa saƙon kuma kunfi kusa keda d'iyar taki."


Dariya tayi tace ƙwarai kuwa bari na tashi dama wannan saƙon farin ciki nidai ce ya kamata na faɗesa." Sannan ta miƙe ta bar ɗakin ta nufi ɗakin papa, ta tardo shi zaune cikin falon sa yana karatun jarida kujera da ke fuskantar sa ta zauna ta fara koro masa da bayani.
Cikin ƙanƙanan lokaci farin ciki ya bayyana a fuskar papa yace "Masha Allah AFREEN ta fara hankali da har iya kula wani har ta bashi damar zuwa gidan nan wannan wane mai sa'a ne haka? To Allah kayosa lafiya."



Da ameen tanti ta amsa sannan ta tashi ta koma ɗakin ta, ita kuwa AFREEN har sun tsufa gidan su Hasina maman Hasina taji daɗi ganinta har tarasa ma ina zata saka ta dan farin ciki, bayan sallar la'asar AFREEN tayi masu sallama ta tafi gida bayan Hasina ta nuna mata yanda zata karɓi KAMAL idan yazo sabida ita sabon shiga ce a wannan fannin."


Bayan sallar isha'i AFREEN tayi wanka ta shirya cikin wani haɗaɗen ɗumki na atanfa da aka mata doguwar riga sosai rigar ta kamata ta mata mugun kyau ba kwalliya tayi ba sai kwali da tasha wanda ya ƙara fito da hasken idonta wanda suka bada wani irin kala mai kyau maron ɗin cikin su sai wawalniya yake ko kai kewa ka kalleta dolene ka ƙara kallon ta. Amma gabanta sai faɗuwa yake tana tunanin ya KAMAL zaiyi idan yaga fuskarta kadai yaje shima ya tsorata da ita shikenan ya daina sonta bayan kwana biyu nan dayake kiranta suna gaisawa yasa ta fara sakin jiki dashi, kada yaje ya mata kallon aljana kamar yadda kowa kemata idan suka ga fuskar dan wasu ma har guduwa suke.


Tana zaune tana saƙa da warwara taji wayar ta ɗau ringin aikuwa sai gabanta ya yanke ya faɗi har saida ta riƙe daidai gun da taji ya buga din, addu'a tayi sannan ta ɗauki wayar takara a kunne tare da yin sallama, daga cikin wayar aka amsa sallamar tare da cewa "Sarauniya ta gani a ƙofar gida."


Da To ta amsa sannan ya katse kiran, tashi tayi ta fita ta tardo Zeinab da Safina zaune a falon suna kallo kusa da Zeinab taje ta zauna tace "Zeinab tashi kije nayi baƙo a waje ki shigo da shi."



"To anti." Zeinab ta faɗa sannan ta miƙe ta fice.


Maida duban ta tayi ga Safina tace "Sister tashi kije ki faɗa wa su papa gashi nan ya ƙaraso."


Itama miƙewa tayi ta nufi ɗakin papa sannan AFREEN ta koma ɗakinta ta zauna......


Zeinab na fita ta tardosa zaune cikin motar yana dana waya ƙarasa wa tayi gun motar tayi sallama sannan tace "Ina yuni yaya ance ka wucike daga ciki."


Kallon ta yayi sannan ya saki murmushi yace "Lafiya lau ƙanwata, to shikenan bari na fito."


"A'a yaya da ka shigo da motar a ciki mana"


A'a ƙanwata Bama sai na shigo da ita ba tunda ba jimawa zanyi ba."


"To ba damuwa yaya." Zeinab ta faɗa tare da juyawa zata koma ciki.


KAMAL yace "Ah ƙanwata ki bari mu shiga tare man, ya faɗa tare da ƙoƙarin fitowa daga motar, tsayawa tayi sannan ya fito daga motar, masha Allah KAMAL fari ne dogo mai ɗan kakabran jiki kyakkyawan gaske ajin farko. Ƙaraso yayi inda take cikin ƙayataciyar tafiyar sa sannan yace " Mutafi."


Jerawa sukayi suka shiga gidan suna kawowa ƙofar da zata sada su da falon ya ja ya tsaya Zeinab ta juyo ta kalle sa tace "Yaya Lafiya naga ka tsaya."


Murmushi yayi sannan yace "Lafiya lau mu shiga ."


Buɗe ƙofar Zeinab tayi tashi ga da sallama shima haka ya shiga kansa aka kasa yana kallon ƙasa da sallama ɗauke a bakin sa, papa ne zaune a falon ya ɗago ya kalleshi tare da amsa masa sallama sannan yace "Ƙaraso mana yaro."


Ƙarasawa yayi tare da zubewa kasa saman kafet tare da gaida papa kansa a ƙasa ya ƙasa ɗagowa ya kalli sirikin nasa, sannan papa yace "Tashi ka zauna mana ya ka zauna a ƙasane nan fah gidanku."


Murmushi KAMAL ya saki da har yau kansa a ƙasa sannan yace "A'a papa nan ma ya isa."


Murmushi papa yayi a cikin zuciyarsa ya na faɗin wannan daga ganinsa yaron kirki ne, amma a fili sai yace "To shikenan."


Ba tare da ɓata lokaci ba aka cika masa gabansa da ƙayan ciye ciye da lashe lashe sannan papa yace masa "To bismillah."


Girgiza kansa yayi alamun a'a, papa yace "To kodai bakasan yanzu nan yazama gidanku ba kaima ka cire kunya mana ni kamar mahaifi nake a wajan ka, saki jikin ka yaro."


Murmushi KAMAL yayi sannan ya ɗauki kofi ya tsiya juice ya sha sannan ya ajiye."


Sannan papa ya kallesa ya fara masa tambayoyi kamar haka............


Ina sonku irin sosai ɗin masoyan wannan littafi........





Bon Mardi 💖💖💖💖

Happy Tuesday💞💞💞
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


Écrit



Par



*QUEEN ZEEFAT*



_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_



*_Teemah_* ina jinjina maki game da ƙoƙarin comments sosai nake jin daɗin idan naka comment ɗin ki sannu ki da ƙoƙari Allah saka maki da alkairi.





*_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_



*Page*: 31 & 32



A nutse papa ya dubi KAMAL yace "To yaro mi sunan ka sannan inane gidan ku kuma mike tafe dake a game da yarinyar nan AFREEN?" papa na kaiwa nan yayi shiru.



KAMAL ya gyara zaman sa da kyau sannan ya ƙara sada kansa kasa yace "Papa ni sunana KAMAL mahaifina Alhaji Aminu mai gyaran TV, gidan mu kuwa yanan cikin anguwar buzu ɗan zambaɗi wajen shagon Sagir mai ƙarfuna, ni kuwa ina aiki a baba ma'aikatar ƙera leda dake cikin garin Maraɗi ta wajan hanyar anguwar ƴan belbelu, sannan inada shagon biyu cikin grand marché ( babba kasuwa) kuma inada shago biyu a ƙaramar kasuwa wanda nikeda yara masu tsare min su, kuma duk ina sami lokacin ina zuwa Dubai wajen sayo kaya kamar lace, antafa shada da dai sauransu, kuma abinda ya kayo ni gun AFREEN shine aure🙈 papa wallahi ban zo da wassa ba da aure nazo, kuma nutsuwar ta kamalarta da addini ta ya ja hakalina gareta ba dan wai na taɓa ganin fuskarta ba ɗan ko yanzu dana ke maka maganar ban taɓa ganin kamanin ta ba a whatsapp sai nayi nayi ta turoman da photon ta amma taƙi, duk da haka banji haushin ta sedai ma da tayi hakan birgeni tayi, kuma ni ko ya take to naji nagani inason ta a haka.


Papa yace "To masha Allah KAMAL duk na gamsu da bayan nan ka, kuma na yaba da hankalin ka sannan duk garin nan babu wanda baisan mahaifin ka mutuman kirki bane dan haka nidai na baka AFREEN, sai kaje ka sameta dan ku daidai ta kanku."


Wani farin ciki ne😊 ya sauko wa KAMAL, baisan lokacin da ya furta "Nagode papa Allah saka alkairi."


Murmushi papa yayi sannan yace dashi "Bai komi bari naje nasa a turo maka ita sai ku gaisa." papa ya faɗa tare da miƙewa ya bar gun ya nufi ɗakin Umma yana shiga ya tardo su Zeinab zaune bakin bed ita kuwa umma tana toillet dubensa ya kai ga Zeinab yace "Tashi kije ki mayar da KAMAL ɓangaren saukar baƙi sannan sai ki sanarwa da AFREEN cewa taje su gaisa."


Haka kuwa akayi tana zuwa tardo shi zaune ida papa ya barshi bai motsa ba ta ƙara so ta sanar da shi saƙon papa sannan ya miƙe ya bi bayan ta, tana raka shi ɓangaren baƙi ta fito taje ta gayawa AFREEN sannan ta dawo ta ɗoki abin motsa baƙi ta kai masa sannan ta fito.


AFREEN na fitowa ta nufi ɓangaren baƙi amma ta kasa shiga tsaye take bakin ɓangaren sai zare ido take kamar mara gaskiya ita ganin abin take gashi nan, wai itace saurayi yazo wajan to ita idan tashiga ma ya zata ce mashi abinda ba sabon ba, gashi ita sabon shiga ce a wannan fannin to ya zatayi? Tana ciki yi wannan tunanin taji ƙarar tafiya ai bata san lokacin da ta buɗe ƙofar ba ta shige da sallama a bakin ta, yana zaune yana dana wayar sa, da sauri ya ɗago sanadin jin zazaƙa muryar ta na yawo cikin kunnuwa sa, sakin wani haɗaɗen murmushi yayi sannan ya taso ya ƙaraso ida take tsaye yace "Oustaziya na bismillah ki zauna mana ba musu ta ɗaga ƙafar ta ta nufi gun manyan kujerun dake falon ta zauna, ba tare da ta ɗago fuskarta ba dake duƙe.


Shima yadawo ya zauna kan kujerar dake fuskantar ta yana murmushi😊 ba tare da ta ɗago ba tace "Ina yuni" take yanke yaji wani farin ciki ya luluɓe shi.



Yace "Lafiya lau Oustaziya na da fatan na sameki lafiya."


"Lafiya lau," ta faɗa a taƙaice ba tare da ta ɗago ba.


Murmushi ya koma yi sannan yace "Yau ma ba za'a bani damar ganin wannan kyakkyawar fuskar ba, ko nayi lafine da akeson hukunta ni ta wannan fannin."


Girgiza kai tayi sannan tace "ba haka bane"


Wani murmushin ya ƙara saki cike da farin ciki dan ba ƙaramin jin daɗin muryar ta yake ba sannan yace "To a taimaka min dan Allah a ceci rayuwa ta tunda dai yau gani na kawo kaina, a nuna min wannan kyakkyawa fuskar ba dan halina ba na ƙagu naga fuskar nan dan Allah."🙏🏻🙏🏻



Ji abinda ya faɗa yasa AFREEN ba dan taso ba sabida tana gudun kar ya ga fuskar shima ya ji tsoron ta har ma ya gudu daga gidan nasu, fara ɗago fuskarta tayi a sannu sannu kamin take ida ɗago fuskartata ta sauke manyan idonta cikin nasa ba tare da tasan idon nasu zasu sarƙe cikin na juna ba.


Saida yaja baya a ɗan firgice 😿😳kamin yake Furta "Tsakiyar ya tabbata ga Ubangiji da ya halicci wannan halitta, AFREEN dama haka kike da kyau badan ina cikin gidan ku da a lokacin da naga wannan fuskar taki da nace gamo nayi, ce ba banza kike rufe fuskar kiba AFREEN gaskiya ni me sa'a ne da nayi irin wannan zaɓin, yanzu nan na ga ribar rufe fuskarki da kike da ace baki saka niƙaf da yanzu wani ya kwashe min ke tun kan in ganki, amma yanzu ke tawace ni kaɗai dole ne na ƙara maki kwarin gwiwar saka niƙaf dan adana min wannan kyakkyawa fuskar har na kilace a gida na wanda ko abokai na ba zan barsu su gangi ba my AFREEN inason ki sosai dama ni tun farko shigar ki ta alfarma da hankali da nutsuwa da addini suka ja hankalina a kanki abinda yasa, sai gashi nazo naga ashe babban kamu nayi Allah na gode maka," a take ya sauka daga saman kujera da yake ya kai goshisa ƙasa yanayi wa Allah sujida tare da gode masa.


AFREEN murmushi☺️ tayi tare da saurin kai hannu ta ta rufe fuskarta, kamin shi kuwa ya ke ɗagowa ya koma saman kujera ya zauna yana binta da wani mayatacan kallo.


Daga nan dai ya samu suka ɗan gaisa dan kwata kwata ta kasa sakin jiki suyi fira sabida tsananin kunyar sa🙈 da take ji, kamin daga bisani ya mata sallama ya tafi ba dan ya so ba kawai dan ya lura dare ya farayi, amma in ba haka ba babu abinda zai sa ya bar gun, kofa bazata masa magana ba matsala indai har zata barshi yayi ta kollon ta, haka na saukar masa da wata nutsuwa da farin ciki.


Tunda ga wannan ranar soyayya mai ƙarfi ta kulu tsakanin KAMAL da AFREEN, duk ranar da tace masa ba zatayi karatu ba to ranar wajen ta yake zuwa su sha fira sosai har baison ya barta kamar dai ace ya ɗoketa ya kai gidan sa yake ji.


Sannan duk ina yazo gidan kullum sai ya shiga ya gaida iyayen ta da kuma kakata Hajiya Zakiya.


Kuma gashi duk lokacin da yazo ya kawo mata wani abu to idan taƙi amsa sai ya kira Zeinab ya bata yace ta ba AFREEN idan sun shiga cikin gida. haka har sai ta fara nunawa Tanti kamin ta kaiwa mahaifiyarta haka kuma tanti bata daina bata maganin da take bata ba.


Kwanci tashi babu yuwa a wajan Ubangiji yau ya kama saura kwana takwas saukar su AFREEN, dan haka sunata ta shirye shirye a islamiyyar su yanzu aji aka bawa AFREEN nayiwa yan saukar gyaran karatu, kasancewar ita ta daɗe da yin saukar Alkur'ani mai girma, yanzu kuwa za'a mata saukar tahafiz ne da litattafan addini da ta karance ce kuma ta hadace, idan kaji AFREEN na karatun Alkur'ani mai girma tana bawa ko wane harafi haƙinsa ba kuskure ko ɗaya a ciki zaka iya cewa duk duniya tafi kowa iya karanta shi da bashi mahimmanci.





****** ****** ****** ******


AFREED ne kwance ya lumshe idonsa kamar mai barci, amma ba haka bane, ya faɗa duniyar tunanin, tunanin da yarasa sa dalilin da yasa yakeyin sa, kwata kwata hankali sa ya kasa kwanciya a kan abinda ke addabar zuciyarsa, a take ya azawa kansa tambayar miyasa nakasa manta wa da muryar tane wane dalilin ne yasa nakejin wani abu na tsiramin a zuciyata a duk lokacin da na tuna muyar ta, miyasa duk sanda nake zaune ko nake kwace sai tunanin ta ya addabi rayuwa ta, miyasa kullum nakeji muryar ta cikin dodon kunnuwa na kuma hakan na sakamin faduwar gaba da sakani, cikin damuwa, miyasa tsikar jikina ke yawan tashi akan ta minayi mata, kodai itaɗin ba mutum shiyasa ta addabi tunanin na ɗan gaskiya zaƙin muyar ya huce misali pourquoi je pense a elle ( why nake wayan tunanin ta), d'abord qui est-elle ( who is she)?????


Wannan tambayoyin ne AFREED ke ta aza ma kansa kuma yara sa mai bashi amsa su, tashi yayi zaune ba tare da ya buɗe idon shi ba yanajin yada kansa ke sara masa, buɗe ƙofar ɗakin a kayi aka shigo har yanzu idonsa a lumshe suke, duk da yaji buɗewar kofar hakan bai sa ya buɗe su ba, Ali ne yashigo sannan yayi sallama, can ciki AFREED ya amsa wanda in ba kusan sa kake ba to ba zakiji ya amsan ba, kuma ya amsan sabida sanin mahimmancin sallama, da badan haka to babu wanda zai sashi buɗe bakin.


Ƙarasowa Ali yayi shi ma ya zauna bakin bed sannan ya kalli AFREED cike da damuwa yace "Frèro wai mike damunka ne? Ina lura dakai kwana biyu baka cikin walwala tanti duk ta damu.


Sai a lokacin ya buɗe shanyayun idanunsa da sukayi ja sosai kamar an watsa masa barkono sanadin ciwon da kansa yake da kuma damuwa ta taru tayi masa yawa, ya sauke su akan Ali sannan yace "Babu komi broh kawai kaina ne ke yawan yimin ciwon kwanakin nan."


Da sauri Ali ya kai hannu sa saman goshi AFREED, ai da sauri ya janye sanadin jin wani irin zafi sosai sannan ya maida kallon sa akan AFREED a gigice yace😳 "Tashi muje asibiti AFREED ya kake zama da irin wannan ciwon kan haka, in wani abu kuma ya sameka fah kasan ba zan taɓa yafewa kaina tashi muje bari na sanarwa tanti halin da ake ciki," daga nan Ali ya miƙe da niyyar zuwa ya sanarwa tanti ( ƙanwar mahaifin AFREED).


Da sauri AFREED ya koma hannun sannan dakyar ya ɗaga bakinsa yace "Ali ba wani babu bane mai tsanani ka kwantar da hankalin ka, yanzu da nasha magani na kwanta na huta yanzu nan zakaga na wartsake, idan kaje ka faɗa wa tanti ai zata tayar da hankali tane sosai."


Sai Ali ya kura masa ido na ɗan lokacin kamin yace " ka tabbata?"


Murmushin ƙarfin hali AFREED ya sakar masa sannan yace "Insha Allahu."


Wajen ida AFREED ke ajiye magunguna Ali ya nufa ya ɗoko masa kalla biyu sannan ya nufi firjin ɗin dake ɗakin ya ɗoko masa ruwa, kamin yake nufarshi da magungunan da ruwa, ya dawo ya zauna daga inda ya tashi ya ɓalla masa maganin da ruwa ya basa ba musu ya ƙarba yasha, sannan ya lumshe idonsa ya kwanta yace "Ali yau wace rana ce?"


Ali yajuyo ya kallesa ganin idonsa a lumshe sai yace mashi "Laraba."


Saida ya ɗoki minti biyu sannan yace "Kenan saura kwana guda juma'a to Allah ya kaimu."


Da mamaki Ali

Please Login or Register in order to submit comment