Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko Allah zaisa ya ganta cikin anguwar koda zata wuce ne, don wallahi shi idan yau bai ganta ba ana iya samun matsala, amma mi Ali ya nuna masa bai isa yaƙi zuwa saukar masoyiyarsa ba, dan haka babu wanda ya iya ya tashi ya shiga wanka dan ya shirya shima ya bisu badan yaso ba, amma ya ɗau alwashin, suna dawowa Sai yaje masallacin nan dan yau bata yiwuwa ma ya iya kwana ba batare da ya saka ta a idon sa ba, koda kuwa bazai samu damar gani fuskarta ba.


Duk sun na bakin motocin su AFREED kaɗai suke jira aikuwa sai gashi ya fito cikin wata irin dakakiyar shada Green kamar pomme (apple)🍏dumkin rigar iya kar ta bakin gwiwa da wando shima ya kamasa daidai musali da hula wanda iya ajiyar hular ma akan AFREED na daban ne, takalmin sa kalar shada ne agogon sa ma haka komai da komai dai yayi macin Masha Allah kayan sunyi matuk'ar masa kyau sosai suka ƙara fito da class dinsa ga wani uban kamshi da yake zubawa sai kace da ruwan turare yayi wanka, kannansa ma se da suka shagala da kallon sa kama tun daga Ali har zuwa ummi ya ƙaramar cikinsu, har tanti A'ishah ma ba'a barta a baya ba wajan kallon shalelen ɗan nata, Farisa ta saki murmushi a cikin zuciyarta tace "Dole ne yayana tun ba yau ne nagano cewa ka iya dressing cikin jinin ka yake ba Allah Ubangijin ya kare mana kai abin alfahari mu."


Daidai nan AFREED yaƙaraso gun, Ali ƙamewa yayi ya sara masa sai kace suna bakin aiki, sannan yace "Woow mutume na irin wannan dressing haka kamar zakaje zaɓen wanda yafi iya dressing ko kuma na kyawawa wai kaga yanda kayi matuƙar kyau kamar kaine ake yiwa saukar ko kuma kaine saurayin mai saukar."


Hararen Ali yayi ba tare da yace masa komai na ya nufi wata haɗaɗiya Prado green wada ta ɗan ciza color ɗin ya buɗe yacema tanti ta shiga su tafi sabida shi zaiyi driving da kansa dan yau yana sha'awar tuƙi, kuma haka kawai yake jinsa cikin farin cikin, batayi musu ta buɗe baya ta shiga kamin take ƙarasa rufa ƙofar Farisa ta ɗan matso da sauri ta buɗe gidan mai zaman banza ta shige, sabida tace sedai AFREED ya mata abinda zai mata amma kam ba zata shiga motar su Ali. Shima shigayayi bai ce mata komai ba ita Amal tashi gidan baya kusa da tanti A'isha ya tayar da motar , su Ali na ganin haka shima ya buɗe motar su ya zauna wajen zaman direba shima Umar ya buɗe wajan mai zaman banza ya shige, Fariya da Khadijah kuwa suka shige sannan Ali ya tada motar shikuwa AFREED har an wangale masa ƙofa ya fita Ali na binsa a baya, ƙwayen Tanti A'isha kuwa har sun riga da sunje makarantar kawai jiran tanti ne suke da kuma ita kahdijah da za'a yiwa saukar............





Muje zuwa.....😜😜😜😜😜



🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Écrit



Par



*QUEEN ZEEFAT*



_Ƴar_
_Mutan_
_Niger_



*Wattpad@nazichou*




Barka barka *Mom Lalla* (sis sajida) ina tayaki murna ƙarasa littafinki mai takai ( *MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR)* gaskiya ki zuba ilimi da basira a wannan littafi yayi ma'ana sosai fiye da tunanin mai tunani Allah ya biyaki da gidan aljanna, gaskiya kin nishaɗan tar damu mun ƙaru da abubuwa sosai a ciki Allah ya yafe maki kurakuran dake keci, Allah ƙara basira da ƙarfin ido sai mun haɗu a sabon littafin ki wanda muke fatan samu kafin azumi💃💃💃💃💃💃




💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/




*_BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM_*


*Page* : 37 & 38


AFREED da Zeinab sun saka wata rantsatsiyar shada golden color wada KAMAL ya kawo masu an masu ɗumkin doguwar riga ba'ayi kwalliyar komai ba a rigunan amma yankan rigar kaɗai abin kallo ne, masha Allah ɗumkin ya karɓe su sosai ba ma kamar AFREEN sosai doguwar rigar ta zauna ajikinta ɗas, suka saka farin hijabi dogo har ƙasa sannan AFREEN ta ƙara da wata golden ɗin niƙaf mai mugun kyau, sai fara safa da ke sanye da ƙafarsa da takalmin musu ɗan tsini golden, sosai ta fito kamar wata cikakkiyar balarabiya irin larabawan na Sudan


Firdaoussi da Fanna da Hasina sukaci ankon da aka fido ta saukar ta wani haɗaɗen materiel fari da maron ɗin hijab, suma kuwa nasu hijab ɗin har ƙasa, bayan sun gama shirin nasu tsaf suka fito falon suka tarar da iyayen nasu suma su gama shiryawa suna jiran saukowar papa dan su wuce wajan saukar, haɗa kakar su AFREEN Hajiya Zakiya za'a je wajen saukar.


Iyayen nasu nata murmushi jin daɗin ganinsu cikin kamala kamin wani yace wani abu Hajiya Zakiya tayi saurin cewa "Ah masha Allah ƴan jikokina kunyi kyau Allah maku albarka" ƙara kai dubanta tayi gun AFREEN kamin tace "Ke kam AFREEN har yau bazaki iya haƙura da wannan abin rufe ido ba? Anyi mutum shi kullum fuskar sa a kulle kamar munafiki, ke dan Allah cire mana wannan abin da sai maras gaskiya ke saka shi, ke kuwa da gaskiyarki haba dan Allah." Hajiya Zakiya ta faɗa tana hararen AFREEN dan ta bata haushi sabida yawan saka niƙaf da takeyi.


Murmushi AFREEN tayi sannan tace "Kaka kinga kin fara ko, to ni wallahi bana fitar da ita ba kawai se ki sakamin ido."


"Kijimin ja'irar yarinya Arahamat ina guje maki zafi kina cewa na saka maki ido, to kada fida man ai dan kanki, ga dangin ki nan kowa da fuskarsa buɗe saike kin wani kayo wannan tashin hankali kin saka."


AFREEN ta ɗan turo bakin daga cikin niƙaf tace "Eh anji ɗin kuma ni ban saka tashin hankali ba ehe."


Arahamat mahaifiyar AFREEN tace "Barta dai mama ai ita ce zataji zafin ba wani ba."


Hajiya Zakiya tace "Ah to Arahamat ke ganar min hanya ni kam sai nafasa zuwa wajan saukar nan tunda naga wada akewa saukar ta gama zama fitsarariya."


Da sauri AFREEN taje ta zauna kusa da Hajiya Zakiya tare da riƙo hannu ta tace "Haba kakata mi yayi zafi haka ai idan baki jeba saukar nan ba, ai ba zatayi armashi ba, kuma cewa kin fasa zuwa nima kam zan cire kayan nan nayi zama gaskiya."


Murmushi Hajiya Zakiya tayi tace "Ina ai bazan fasa zuwa da wasa nake jikokin nawa har biyu su na sauke Alkur'ani mai girma sai naki zuwa nasaka masu albarka haba ai ba zai yiwu ba, kuje muje kawai." ta faɗa tare da miƙewa daga inda ta ke zaune, duka ƴan falon suka kwashe da dariya, daidai na papa ya fito shima cikin shirin sa.


Batare da ɓata lokaci ba suka fice daga falon suna isa harabar gidan suka tarar da Fahad da Imran da yan aikin gidan maza da mata hata mai gadi da matarsa da yaransu uku sun shirya suna jiran su domin halartar wajen saukar, banda mutanen da sukazo taya aikin wato yan uwa da abunkan arziki na nesa da na kusa wanda tun ɗazu direbobin gidan suke jida suna kaisu islamiyya.


Papa ne ya isa kusan motarsa ya fitar da ita daga wajan parking sannan AFREEN shikuwa Fahad ya riga da ya fitar da tasa motar, papa ya buɗe ma Hajiya Zakiya gidan baya yace tashiga, amma ƙiri ƙiri tace kam bazata shiga ya saka matan shi su tafi dan ita kam motar Fahad zata shiga, haka kuwa akayi ta shige motar Fahad gidan bayan shikuwa Imran ya zauna wajen mai zaman banza shi kuwa Fahad mazaunin direba, motar papa kuwa Arahamat ke wajen mai zaman banza, umma da tanti gidan baya, papa mazaunin direba, motar AFREEN, Fanna ke mazaunin direba sabida sunce kam yau ba zasu barin AFREEN yin tuƙi ba, AFREEN zaune wajen mai zaman banza, sai Hasina da Zeinab da Firdaoussi gidan baya.


Sauran motocin guda uku kuwa ƴan aikin gidan ne da direbobin gidan da mai gadi da matarsa da ƴaƴan sa a ciki, motar su AFREEN ta fara fita sabida gani da sukayi lokaci nason ƙurewa sannan ta papa baya ta Fahad sannan na ma'aikatan gidan wanda da suka fito saida suka tsaya mai gadi ya fita ya kulo gidan kamin suka kama hanya wada a lokacin motacin mutanen gidan sun kusa ƙarasawa makarantar islamiyyar.


Suna ƙarasawa islamiyya, AFREEN da Zeinab su kayi saurin fita daga motar suka nufin gun ƴan saukar suka nemi gu suka zauna sabida lokacin fara saukar ya kusa, so anan ne wani malami yazo kusa da AFREEN yace mata ai ba nan ne gun zaman ta ba ga inda aka tanada can domin ita sabida ita ɗaya ce za'a yiwa saukar hada da ta littatafan addini tunda suka shiga filin saukar ake bin su AFREEN da kallo sosai shigarsu ta ɗauki ido mutane wasu kam mamaki suke a ina yarinyar ke samu niƙaf ta ko wane kalan kayanta abin na matuƙar ɗaure masu kai sosai yake basu mamaki, bare niƙaf ɗin da ta saka kala golden ga adon Stone dake mugun kyalli.


Lokacin da suka shigo AFREED kanshi duƙe yake yana ɗane danen waya ya dai ji Ali dake kusan shi yace masha Allah, kuma hakan baisa ya ɗago ba, dan ganin abinda Ali ke faɗawa masha Allah.


Ba musu AFREEN ta bi bayan malamin nan har suka ƙarasa gun wata haɗaɗiya kujera sannan yace mata nanga ne gun zamanta, cikin ladabi ta juyo ta kalli malamin tace "Malam da na zauna tareda su can ɗin zan fi sakewa, kaga tunda muka shigo mutane ke bina da kallo ina ga na zauna ana ni ɗaya zan takura, amma idan can ne, sai na zauna a bayan su kaga na kare kaina daga kallo mutane."


Murmushi malamin yayi yace "AFREEN wannan daraja Allah yayi maki godema sa kawai, dolene ki zauna anan sabida yurin da ke ya dace najima banga yarinya mai kwazo da basira irinki ba, wannan baiwar da Allah yayi maki itace yau har ta saka aka wareki daka cikin duban jama'a aka kawo ki nan yarinya 57 da na miji biyu ake yiwa saukar nan amma babu wani da ya kamo koda farcan ki ne bare kafarki, kuma zancen mutane na kallo ki ba wani abu bane, tunda basu ma fara kollon ki ba, sai idan kin fara karatu tunda ai baki manta cewa kece zaki fara karatu duk a cinkin yawan mutanen ga, ke zaki buɗe hilin saukar muyarki mutane zasu faraji da kuma daga ƙarshen muyar dai nan taki ce zata rufe filin saukar nan da addu'a dan haka ki kwantar da hankalin ki fiskanci abinda ke ganki ba yau bane kika fara haka."


AFREEN tace "To shikenan malam." Murmushi malamin yayi kamin ya bar gun nata.


Taro har taro yuri ya cika sosai da sosai idan kaga yanda ɗan adam ya taru a wajen zakayi tunanin cewa duniyar ce baki ɗaya ta haɗu a wajen alhalin ko kaso 1 bai kai ba a cikin ɗari ba.


Babban malamin wato mai islamiyyar ne yaje ya hayo kan manbari ya yi gyaran murya tare da yin sallama sannan yace mutanen su dawo da hankalinsu wajen ɗaya za'a fara sannan yayi wa mutane godiya halartar taron nan da sukayi, sannan ya ƙara da cewa "Ba tare da ɓata lokaci ba zamu kira malama kuma ɗalibar mu, mai hazaƙa kamilala yarinya mai nutsuwa da tarbiyya mai hankali da girmama kowa da kowa koda kuwa ta girmeka zata baka girman ka wada tasan ya kamata mai jin tsoron Allah, kowa na ƙoƙari sosai a makarantar nan kowa nada hazaƙa sabida mukam mun yarda da ɗaliban mu, sedai babu wanda ya kamo ƙafar wannan ƴar albarkar yarinya, zato zo ne ta buɗe mana fili da addu'a sannan tayi karatun.


AFREED najin yanda malamin ke taɗa wannan yarinyar amma bai ɗago daga duƙin da yake ba yana dana wayar sa, har saida Ali yace masa "Wai AFREED miye haka kaida kazo gun sauka kuma shine ka wani buge da dana waya, dan Allah ka ajiye wayar nan ka kalli abinda ya kawo ka nan."


Ba tare da AFREED ya ɗago ba yace "Ali kaga kada ka takura man, da ma banyi niyyar zuwa ba kuka ta kuraman, idan kuwa angaji da gani nane a gun nan sai nayi tafiya ta dama inada abinyi."


Ali yayi murmushi yace "Hum ai babu inda zaka kana nan tare da mu har sai an kammala saukar ehe."


Ko kollon sa AFREED baiyi ba bare yayi tunanin ya amsa masa, Ali ya mayar da hankali sa wajen saukar AFREED kuwa ya ci gaba da aikin da yake a wayar sa.


Can cikin lasipika babban malamin yace " Ba wata bace wannan ɗiyar albarka sai *AFREEN SADISU ASMANE SANGA* , ta fito tazo ta buɗe mana taro da addu'a."


AFREEN ta taso daga inda take zaune ta nufo malamin a nan take idanun jama'a suka dawo kanta, Ali yaro ido dalilin jin suna mai kama dana AFREED taɓo yayi yace "Broh kaji wata mai kalan sunan ka ashe za'a sami mai irin sunanka kuma mace kai amma nata yafi naka daɗi masha Allah."


Keda kecen AFREED in ya tanka to kin tanka bai ma ɗago ba bare Ali yayi tunanin samun amsa kuma badan baiji shi ba, da Ali yaga haka ya san ba tanka masa ba zaiyi, sai ya mayar da hankali sa gun da yafi masa mahimmanci.


AFREEN na ƙarasowa gun manbarin malamin ya sauka ya mata nuni da ta hayo kan mimbarin, ba musu ta ɗale kan tayi sallama kamin ta ke gabatar da kanta, lokacin da tace "Ni sunana *AFREEN SADISU ASMANE SANGA* ina ma kowa barka da zuwa."


Lokacin da AFREED ya ji muryar AFREEN na gabatar da kanta da sauri ya ɗago harda ƴar zabura yayi jin muryar da ba zai taɓa mantawa da ita ba a tarihin rayuwar sa, sosai yayi mamakin ganinta yurin nan, dan sosai ya gane ta duk da tana cikin niƙaf, lokacin ɗaya yaji wani sanhi ya ziyarci zuciyarsa, murmushi yayi can ƙansa zuciyarsa yace "Ashe anan ne zan ganta, daban zoba dana yiwa kaina."


Bai an kara ba yaji zazaƙa muryar ta ta fara addu'a buɗe taro, sosai ya nutsu yana sauraran yanda zazaƙa muryar ta ke fitar da sautin lafiyayar ƙira'a mai daɗi sauraro, duk mantawa yayi da wajan mutane suke kawai shi gani yake shi ɗaya ne a gun kuma shine kaɗai ke sauraran dan haka ya shagala sosai da kallon ta ko kyafta idon sa baiyi, har ta fara karatun Alkur'ani tana kuka sosai ba har muryar ta na shaƙewa, wani mungun tausayin ta ne ya ɗari a zuciyarsa ba tare da ya an ƙara ba yaji wasu ruwa masu ɗumi sun sauko masa a fuska, bai kai ga shafe hawayen da suka zubo masa ba yaji muryar Ali nacewa " woow broh ban taɓa jin wani na karatun Alkur'ani ya birgeni naji kamar kar ya daina irin yarinyar nan sosai ƙira'ar tayi daɗi zakace wata balarabiya."


Sai a sannan ya tuna da gun sauka ne suke da sauri ya share nasa hawayen dan kada Ali ya gani, sabida yasan idan ya gani iskanci zai masa, sai kuma ya fara yan wange wange yana kallon mutane gurin duk sai yaji duk baiji daɗin ba ganin idon mutane akanta kowa ita yake kallo sai yake jin inama ace yana da ikon da zai je yace ta dakata da karatun nan ta tafi gida, haka dai ya dingajin ba daɗi a zuciyarsa duk da cewa bawai ganin fuskarta ake ba amma hakan ma ji yake inama ace kowa zai daina sauran muryar nan a barshi shi ɗaya ya saurara haka kawai yaji zuciyarsa na masa zafi.


Yanata zancen zuci har AFREEN ta kammala karatun ta koma gurin zaman ta, kowa na ta santin karatun sai ji kake ana macha Allah, papa baki ya ƙi rufuwa sai jin daɗin yake sosai nan daga bayan shi ya ji yasu mutane nace "Allah yayiwa iyayen wannan yarinyar albarka da suka sakata a islamiyya da kuma ita karan kanta yarinyar" sosai papa yake jin wani farin ciki na shigar sa, sai ya juya yace Amin nagode, sukuwa harda tambayar ko shine mahaifinta sabida kamar da suka gani sunayi sai papa ya amsa masu da eh daga haka suka fara masa fira harda masu karɓar number sa sukace dan ayi zumunci, sannan da ɗaya ɗaya ɗaliban da ake yiwa saukar suka fara tashi suna yin karatu har duk suka kammala karatun, sannan aka shiga raba kyaututtuka wa ƴan saukar.


Har yanzu dai AFREEN ce farin bawa kyauta, ga lasipika babban malamin yace "Alhaji Issa ɗan canjin shine zai bawa AFREEN kyauta (Alhaji Issa ɗan canji shine mijin tanti A'ishah wato tantin AFREED).


Alhaji Issa ya miƙe yana gyara malumalu dinsa ya ƙarasa ida AFREEN take tsaye kusa da kyaututtukan, ya ɗoki kyautar da aka tanada dan ita yana murmushi ya miƙa mata sannan ya saka hannu sa cikin Aljihu ya fitar da jika Talatin (50000) yamiƙa mata, risinawa tayi ta ƙarɓa tare dayi masa godiya, kafin Alhaji ya koma inda yake zauna, wani shima ya fito ya bawa AFREEN rafar ƴan 1000 da baisan iya adadin suba ya bata sannan yace "Allah maki albarka yarinya kiriƙe halinki kada ki canza shi."


Ta amsa da ameen tana godiya, haka mutane sukayi ta tashi suna bata kayauta har saida taji bazata iya rikesu a hannu ba dama wasu ta riga da ta ajiye a ƙasa, anty Khairat ce ta taso ta ƙara so inda AFREEN take tsaye da kyaututtuka kamar zasu rufe ta, tana ƙarasowa tace "Sannu ƴar ƙanwata."


Da mamaki ta juyo tana kallon Khairat amma ta kasa mata maga, kollon yaushe tazo garin ne take mata "Khairat na ganin haka ta lumshe idonta sannan ta buɗe su tace "Maida hankalinki wajan ƙarbar kyaututtukan ki daga baya nayi maki bayani." ba musu ta juya ta ci gaba.


Sannu a hankali AFREED ya tashi daga gun dayake zaune ya nufi idan zai sada dashi da AFREEN da takunkumi a fuskar sa gudun kada mutane su sheda ko shi waye, Ali ya zuba masa ido yana kallon sa da tambayar ina kuma zaije, yana ƙarasawa gun AFREEN da Khairat da babban malamin da su suke tayaya karbar kyaututtukan ya je gab da ita ya tsaya ya fido da key ɗin mota da sheck na miliyan ɗaya CFA ya miƙa mata sannan ya gusa sosai gab da ita yayi magana cikin wata muryar mai kama da ta raɗa yada babu wanda zai jiyoshi yace "Yakamata ki bar gun nan gaskiya sabida idon kowane gardi akanki yake duk da niƙaf ce a fuskar ki hakan bai kamata ba kowa na kalleki, sannan kishiyar hajin bana hadake duk da nasan kin taɓa zuwa dan na tsinkayi haura Makkah a bakin ki kwanaki nan da muka haɗu, ina tayaki murna malama AFREEN Allah ya riƙa Allah sa aci anfanin abin, sannan Allah bada ikon anfani da abinda aka sani, ga kuma kujera huɗu daban sai ki zaɓi wanda zaki bawa dan kuje hajin a tare." yana gama faɗar haka yajuya ya bar gun.


Dam da dam haka AFREEN taji gaban ta ya faɗi lokacin da AFREED ke mata magana, ɗago da idonta tayi ta bishi da kallon har sai ya kai gun zamanshi ya zauna, ya mayar da duban sa kanta, suna haɗa ido ya kashe mata ijiyarsa guda da sauri ta ɗauke kanta daga gareshi tare da sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya. Babban malamin makarantar tayiwa bayinin kyautar da AFREED yayi mata dan haka ya dauki lasipika ya fara dacewa, "Jama'a mungode Allah saka da alkairi yarinyar nan AFREEN ta gode da kyaututtukan da duk aka bata dan ta cancanci hakan, yarinya ce da samun irinta wannan zamanin sai an tona, masha Allah ta samu kyaututtuka masu dama, wani bawan Allah ya bata kyautar kujera maka biyar da mota da sheck na miliyan ɗaya sannan wani ya bata babur biyu da 100000 da sauran su an gode an gode Allah saka da alkairi KAMAL ma ya bata mota da 300000 da sauran wasu abubuwa, duk wanda ba a faɗi tasu kyautar ba suma angode kyaututtukan ne da yawa tsayawa faɗa kyautar da duk mutane suka mata bata lokaci ne.


Sosai AFREEN ta gane AFREED duk da yasa abin rufe hanci da baki, ƙara ɗagowa tayi ta kallesa, ai kuwa suka haɗa ido sabida shima ita yake kallo dan ya kasa daina kallon ta da sauri AFREEN ta kauda kanta shikuwa ya saki murmushi.


Yana gama faɗa aka shiga kiran sauran ƴan saukar ana basu nasu kyaututtuka da 100000, dan sosai alhazzan Maraɗi sukayi wasa da salla wajan bawa ɗaliban kyauta cikin kuwa da mahaifin AFREEN da maman ta Arahamat, ana kammalawa AFREEN ta ƙara rufe taro da addu'a wannan karan da kyar muryar ta ke fita sabida kuka da tasha haka yanzun ma wasu hawayen ne ke ƙara bin kuncin ta, idon AFREED na kanta dan haka duk sai take jita a takure, ta kammala addu'ar, suka fara ɗaukar photo ita da ƙawayen ta na makarantar ida suka matsa mata cewa yau dai kam sai ta fida niƙaf a masu photo babu yanda ta iya sai da ta cire niƙaf ɗin aikuwa kallo ya kuma gareta mutane na ta mamakin kyau irin nata, sosai wasu ke zuwa a masu photo tare kawai dan ta birgesu wasu kuwa dan su aza a status a total kuri, wasu kuwa dan gulma, aka fara mata tare da ƴan gidan su da su Fanna da Hasina suna ta arerewa abinsu suna farin cikin, haka wajan su AFREED suma ana ta masu photo tareda Khadijah da ƙawayen tanti A'ishah shi kuwa AFREED hankalin sa bai ma wajen su yana ida AFREEN ke tsaye tare da ƙawayenta suna photo dan ƴan gidansu sunyi tafiyar su.


Sosai ya shagala da kallon ta yana cikin kallon nata ya tsinkayi KAMAL wajenta yaje yace ƙawayen nata dan Allah su bashi aronta dan za'ayi masu photo ita kuwa AFREEN bata iya yi masa magana ba kuma ba ta ɗago ba ta kallesa ba, da su Hasina sukaga ha sai suka bar masu gun, ɗan duƙawa yayi yace "Yau ko ga gayar dani ba za'ayi ba kuma kinwani buɗe man fuskar ki sai kallon ki ake to kizo muje daga can ayi mana photo ko biyu ne kinji."


Ba musu ta bishi ida mai daukar hoto ke tsaye yana jiransu har suka ƙarasa wajen mai daukar hoton ba tace dashi komai ba, suna zuwa mai hoton ya fara masu, ana cikin yi mai hoton ya ɗauka yace madame ki kallesa sai kiyi ɗan murmushi sai a ɗauka hankan zaiyi kyau sosai, aikuwa haka ta faru, ta saki wani tsadaden murmushi tana kallon KAMAL daidai lokacin da hakan ta faru akan idon AFREED aikuwa zuciyar AFREED tashiga wani irin motsawa tana wani yin sama tana dawowa sosai zuciyarsa kemasa zafi dalilin gani KAMAL da AFREEN da yayi an masu hoto hada murmushin ta mai tsada take sakar masa, a cikin zuciyarsa yake cewa "Wanene wancen da har ya samu wannan damar, miye haɗinsa da ita, kadai saurayin tane? Dam dam dam gabansa ne yayi wata muguwar faduwa har sai da ya riƙe zuciyarsa sai yaji ba KAMAL ba har AFREEN ɗin haushin ta yakeji kamar mi, sai kuma ya koma yace "To koma waye ɗin tane mike ruwana a ciki."










Taku har kullum mai kaunar ku💖
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZAMBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


Écrit


Par





Please Login or Register in order to submit comment