Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah."

"Ba wani ni za kuma wayo baku isa ba." AFREED da ke kallon su baice komi ba yace "Ali gaka tashi mu tafiyar mu inaga Mama ta gaji damu tunda so take mu bar mata gidan ta shiyasa takeso muyi aure duk a nawa muke ba wani girma mukayi ba amma Mama ta dage sai munyi aure."

"Umm!!! Dube su ko kunya basa ji wai suce ma kansu a nawa suke mahaifin naku ai na nan tafe cikin satin nan zanga in kun girma ko baku girma ba ko su fariya ba sucewa basu girma ba barku k'artin banza k'artin wofi."

Mikewa AFREED yayi tare da barin gun ya koma cikin salon Ali ma ya biyo bayan shi suka zauna kan kujerun.

Farisa tace "Gaskiya mama kada a yiwa su yaya auren dole a barsu su zab'a ko mu ai ba a mana auren dole ba bare su kinga Mama ki barsu kina zaman ki zasu kawo maki surukai."

"Humm ke kinga alamu aure a gaban su kin tab'a jin sun yi maganar aure ko da sau daya ne shekaru ja suke kuma mutun bai cika mutun sai ya ajiye iyali, lokacin kowa zai dinga kallon ka da daraja, kinga k'ara Ali da AFREED shi zai iya samo matar aure to AFREED fah ko kallon mace bai yi bare har tayi mashi yaji ya na son ta har yayi maganar aure, bai da wanan niyar ko kadan a zuciyar shi."

Fariya tace "Hakane Mama kuma kinga hada lokaci bayi ba idan lokaci yayi su zasu fitar da kansu ba sai kun masu maganar ba kidai d'an k'ara masu lokaci kinji Mama."

To shikenan zan k'ara masu lokaci muga yanda Allah zaiyi....

Tashi sukayi suka bar gun cin abincin tare da kiran mai aiki dan tazo ta gyara wurin cin abincin.

Suma shigo wa sukayi cikin falon tare da zauna saman moquette (carpet) mahaifiyar ta su kuwa ta zauna kan d'aya daga cikin kujerun dake solon (falon) d'in. Sun jima suna fira kamin su AFREED suka mike su masu saida safe tare da barin falon su ka nufi nasu b'angaren.

Suna shiga kowa ya nufi d'akin shi don yi shirin bacci...........



**************

Tuchen Labarin:

Alhaji Asmane Sanga haifafan kasar Mali ne kuma rik'ak'en dan kasuwa ne, yana da da shaguna uku na sayar da shadodi wanda sukayi fice a k'asar ta Mali sabida bubu kalar shadar da babu a cikin shagu nan sabida idan kaje wani gun baka samu shada ba shi nashi shagon idan kazo zaka samu shiyasa yayi fice kowa yasan da shagu nan sa a k'asar, yana da mata guda mai suna Hajia zakiya wada ita yar kasar Niger ce a jahar Zinder su had'u ne a ta dalin zuwan da ya tab'ayi Niamey bud'e wani katafaren shagon shadodi a garin, ita kuma ta zo yin soutenance kinta ta karshen karatu, to tunda ya ganta ya kwalafa rai a kanta saida Allah yayi har ya aure ta dama iyayen ta ba wasu masu k'arfi ba ne to ko da suka ga mai kud'in danda nan suka amince a ka d'aura aure a kaita Mali, shekarasu guda da aure Allah ya bata haihu ta samu d'iya mace aka samata fati, Fati na da shekara uku aka haifi Mariama, sannan Adamu, da shekara biyar a ka haifi sadissu, to tunda ga kan sadissu haihuwa ta tsaya, yara sun tashi cikin gata da tarbiya ta kowane fanni da karatu islamiya da na boko babu wanda suka bari a baya.

Sadissu na da shekara 12 a duniya Allah yayi wa alhaji Asmane Sanga rasuwa saka makon wata irin rishin lafiya metsanani da ta same shi ta tsawon sati biyu, wani dare juma'a yace ga garin ku mutuwar da ta girgiza matar shi da ya'yan shi amma banda dangin sa, sabida ana yi sadar uku suka zo ma da matar margayi maganar ce wai tatara ta koma garin su ta bar masu yaran su zasu kula dasu da dukiyar tunda suma iyayen su ne ta nuna masu kan bata yarda da abinda suke so ba sudai bata gadon ya'yanta su tatara su bar masu garin, suka nuna mata da ba haka nan ba, to da ta gane dukiyar yaran ce suke son ciyewa, sai tace masu su bar mata yaranta ta tafida su in yaso sai su rike dukiyar can su dinga juya masu, aiko suna jin haka a take suka amince dama su dukiyar ce suke so wani daga cikin su yace to hakama yayi,Tare da miko mata 20000 wai suyi kudin Mota, girgiza kai tayi alamar bazata k'arba haka wanda ya miko mata da kudin ya mayar abinsa cikin aljihu da tak'i amsa tare da cewa "Yaushe zaku tafi."


Tace "Gobe insha Allah", suka amsa da "Allah ya kaimu," tare da juya wa suka bar gidan.


Tun daren ranar Hajia zakiya ta fara had'a kayan ta da na yaranta tare da taimakon babba yarinyar ta Fati, suna cikin gyaran kayan fati tace "Umma lafiya kike ta hada kayan mu" saida umma ta nisa kamin tace "dagin mahaifinku ke son na bar musu kasar sabida dukiyar da d'an uwansu ya bari su ce na barku a hannu ni kuwa nace ban yada ba sabida Allah kadai yasan kalar rayuwar k'uncin da za kuyi a hannun su sabida dama tun mahaifinku na da rai ba kaunar mu suke ba ni daku gaba daya, sabida ni ina 'ya Niger sukuwa 'yan Mali kuma suka so ya auri 'yar uwarsa yaki kuma shima ba kaunar sa suke ba kawai dan yana da arziki ne tunda shi kadai ne shima ga maihaifiyar sa duk sauran 'yan uba ne, amma bai tab'a nuna masu banci ba ko na bar ku nan wahala zaku sha shiyasa zan tafi daku."


"Umma muma bamu yarda ma ki bar mu gunsu k'arfar ki k'afar mu to dukiyar Abba mu fah su zaki bar mawa."
"To dama sabida mi suke so na barku don su rike dukiyar sa ne, ni kuma nace su rik'e d'in su bar min ku don ku fiye man komi a duniyar nan shi ne dalilin amince war su."


To mama ke da ba aikin da kike baki kasuwar komi to dami zaki rike mu yakamata ko wasu 'yan kud'i su baki ko wata kasuwa kiyi."


"Hum yaro yaro ne karki damu Fati Allah na tare damu , kuma bancin haka akwai wata millions 10 da tarkardun wani gida na mahaifin ku dake cikin garin Niamey da ya tab'a bani kamin ya kwanta rishin lafiya yace na ajiye masa kuma kada na fad'awa kowa, to kinga idan Allah yayi masu albarka shikenan a cikin su zan samu na k'arasa biya muku kudin makaranta mu d'anyi abinda ba'a rasa ba shi kuwa gidan muje cikin mu zauna, da yarda Allah ba zamu tagayaraba Allah dai ya ru fa mana asiri duniya da lahira."


Da "ameen" fati amsa wada ta fahimci inda uwar ta dosa.

Da ganan suka ci gaba da gyaran kayan, su na idarwa ta tataro yaranta ta fad'a masu da gobe zasuyi tafiya zuwa kasar Niger kuma ba zasu dawo kasarnan ba har abada amma bata sani ba kosu watarana suji suna son gani dangin mahaifin su to fah baza ta hanasu zuwa sada zumunci ba, ta had'a da cewa nasan kuma kowa nan ku nason yi min tambaya? Ban baku wanan damar ba sabida yanzu banida kyakyawa amsar baku ha bani da wata isha shiyar nutsuwa don haka kowa ya bar tambayar shi har watarana, daga haka kowa yayi gum da baki sa ba damar yin tanbaya.

Washe gari da safe wajan karfe 9 sun gama karyawa..............
,

Muje zuwa.......



Godiya ta musan man a gareku masoya na💞
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZANBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


ECRITE:


_PAR_


*QUEEN ZEEFAT*


Yar
Mutan
Niger


Wattpad@nazhabibou

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM_









Page 8


Washe gari da safe wajan k'arfe tara sun gama karyawa kenan se ga dagin mahaifin su biyu sun shigo, ko salama babu tare da cewa "Yo zakiya har yanzu baku tafi ba?" juyowa tayi da sauri sabida kamar daga sama taji maganar tunda bata ji shigowar su ba, da ido ta bisu tare da watsa masu wani mugun kallo tace "wai ku mi mu ka tare muku? duka yau kwana biyar da rasuwar bawan Allah nan amma duk kun bi kun takura man, nina ce zan tafi kuma ni nayi niyar tafiya, idan naga dama sai na yi zamana kuma ba yanda za'ayi dani tunda gidan nan na miji na ne da ya'ya na, sai in nayi ra'ayi ne zan tafi ba wai tilasta min zakuyi ba idan naga dama ba ida zani, ku dai kawai ku gode ma Allah inason koma wa k'asata ta haihuwa, da ba dan hakanan ba wly da ba abinda zai sani barin nan d'in wallahi se dai kuyi duk yanda zaku yi Ah to, tunda nawa d'iyan sun girma suma sun isa kula da kansu kuma da dukiyar mahaifin, amma duk da haka na zab'i na tafi da ya'yana sabida a zauna lafiya to kuma sai ku dawo kuna takura man? mun bar muku dukiyar a hannun ku kuma ai kun san hak'i ci zalin marayu ba sai na fad'a maku ba in kun gyara kun sani inbaku gyara ba ma kun sani, sudai sun bar komi nasu hannun ku duk yanda kukeso kuyi daidai ne wallahi kuma kuyi niya ku fita ku bar min gida sabida komi na maku ku kuka ja, idan mun tashi tafiya zan bayar da makulin gidan akai muku sabida ba abinda zanyi da shi ehe."

K'wafa tayi tare da mayar da kallon ta ga abinda take ran ta a matuk'ar b'ace.

Tsaye sukayi sina kallon ta baki bud'e suna tunanin yaushe matar Asmane ta samu baki maida magana, juyawa suka yi suka bar gidan tare da mamaki da tunani iri iri duk jikin su yayi sanyi.

Su na fita k'ofa guda ya kalli guda yace "Anya wanan matar ba so take ta zame mana matsala ba kuwa?" nisa wa wanda aka yiwa tambaya yayi yace "Wallahi ni kuwa tausayi ta bani vraiment elle à besoin d'un peu du temps pour qu'elle puisse se soullager de ce qu'elle resent a cause de la mort de sont mari,sa fait que 5 jours que son mari est decèder, c'est pas bon ce qu'on est entrand de faire, comme maintenant elle a besoin de notre soutient parce qu'elle n'a personne ici que nous et ses enfants (really she needs a little time so that she can relieve herself of what she feels its fact that 5 days that her husband died, it's not good what we are going to do, like now she needs our support because she has no one here but us and her children).

Wani shek'ek'e d'ayan ya kalle sa yace " Ban gane mikake nufi ba, kanaso ka nuna min cewa ka saduda sabida tayi wani w'azin ta can da barazana to Wallahi ahir d'inka mudai bazamu fasa abunda mukayi niya ba Suley sedai kai ka hakura."

Wanda aka kira da Suley yace "To nidai Wallahi na fida hannu na daga cikin wanan rishin gaskiyar na ku na son ku handame dukiyar marayun Allah da basu ji basu gani ba ba ruwana ba hannu na ciki, idan Allah ya tashi k'watar masu hakin su, wallahi naga dai tun uban yaran nan na da rai yake mana abin arziki duk da nuna masa banbanci da muke, muna nuna masa shi d'in uba kad'ai muka had'a da shi, amma shi bai tab'a banbanta mu da kanshi ba, ko ya d'oki wani bare da muhimmanci fiye da mu sabida abinda muke masa amma bai tab'a nunawa ba dan haka ni ba ruwana ku kuje kuyi Allah bada sa'a."

Juyawa yayi tare da komawa gidan ya sami yaran sun gewaye uwasu na kuka gaba d'aya hada uwa tasu, duk'awa yayi kusa da su yace "Dan Allah Hajia kiyi hakuri ki yafe man ni wallahi babu ruwana acikin abinda suke niyar yi, ki tatara 'ya'yan ki ku bar musu garin nan idan har zaki iya, indan kin ga zaki tsaya karb'a gadon yaranki toh ni me taimakon ku ne wajan ganin an k'watar maku hakin ku daga garesu, ko dan d'an uwana Asmane kun cancanci abubuwa da dama daga gareni sabida mu bai tab'a mana wani abu ba mara kyau kulun shi Alkairi ya ke fata a gare mu ba sharri ba duk da nuna masa k'iyaya da muke shi bai tab'a k'in mu ba Allah nagani dan haka duk abinda kuka yanke ina tare daku duk rantsi duk wuya, shi kuma da ya rigamu gidan gaskiya Allah ya jikan sa ya masa rahama ya sa ya huta." da ameen suka amsa.

Sannan Hajia zakiya ta share hawayen ta tare da cewa "Nagode alhaji Suley kai ne kad'ai mai hali na gari dama tunda na ganka a cikin su nasan ba da son ran ka hakan ke faruwa ba ni da 'ya'ya na mun yafe maka Allah bar zumuncin kuma ni na riga da na wanke hukuncin barin k'asar nan ta Mali tunda ba mahaifata bace dama sabida shi mijin nawa nike zaune a cikin ta amma tunda wanda yafi mu son sa ya karb'i abinsa ba zan zauna ba, haka yaran nan da abina zan tafi sabida in suna gabana hakalina zai fi kwanta kuma idan Allah ya yada za su diga kawo maku ziyara sabida basuda wanda yafi ku, su kuma da sukeso son cinye masu dukiya suje sunci kad'an watarana sai labari, aka rasama mutum bare daud'a duniya bai komi wallahi su suka sani." daga nan tayi shiru tare da goge hawayen da suka zubo mata sukuwa yaran suna tana kuka.

Sauke ajiyar zuciya Suley yayi yace "Amma naso kiyi zaman ki ko dan makarantar yaranki duk da yanzu a cikin hutun karshan shekara ne." saida ta dan nisa kamin tace "Bai komi idan munje zan canza masu makaranta in Allah ya yada tunda karatun Mali da na Niger kusan d'aya ne ba wani banbanci."

"To shikenan amma ita Fati ki barta ta zauna gu na sabida ita tana shekarar ta karshe a université (university) bai kamata a fitar da ita ba idan ta k'arasa shekarar sai ta koma wajan naki, nima ko zan samu ladar rikon maraya kuma na samu damar sauke hak'in da d'an uwana ya tafi ya barmin ko da kuwa a kan tane kad'e zanyi murna haka, ga kuma soyayar da ke tsakanin su da isma'il d'an waje na, da sabida wata ma nufa tawa da zuga naso hana auren su amma yanzu ina goyan bayan had'in nan d'ari bisa d'ari yanzu ne nasan zafi da mahimmancin d'an uwana da baya nan ina ma zai dawo gare mu dan zan nuna masa matsananciyar k'aunar da nake masa kawai ina dane wane sabida a lokacin gurb'atacan halina ya dane mai kyau d'in mugun abu kad'ai ke cikin zuciya ta......

Bai k'arasa maganar ba sabida kuka da ya ci k'arfin sa.

Suma yaran sake fashewa da kuka sukayi mai ban tausayi, Shima alhaji Suley kukan yake sosai kamar wani k'armin yaro mahaifiyar su ma kukan take mai tsanani sabida mutuwar yanzu take dawo masu sabuwa kamar yanzu ne yarasu, sun zama kalar tausayi gaba d'aya ba mai ba wani hakuri.

Sun k'washi kamar minti sha biyar a haka kamin alhaji Suley ke tsagaita nasa kukan yace "Gaskiya munyi babban rashi Allah dai ya jikan sa da rahama, kuyi hakuri yanzu ne kuke da bukata ta a matsayin mahaifi kuma nine nan zan shige maku gaba insha Allah s'il vous plait pardon moi (please forgive me)."

Hajia Zakiya ta tsagaita nata kukan tare da cewa "Alhaji ni ba zan hanaka Fati ba sabida kaima kana da iko a kansu a matsayin ka na wan mahaifin su, amma da'ita zan tafi idan Allah ya sa hutun nasu ya kare sai ta dawo insha Allah nayi maka wanan alk'awarin idai da rai da lafiya, kuma gobe tunda asuba zamu barin garin nan insha Allah sai in sun dawo ganin ku kuma, ita kuma idan sun daidai ta kansu itada isma'il to sai nafi kowa murnar had'in nan kuma komi na hannun ka na baka wuk'a da nama kawai kayi abinda ya dace a yanzu basu da wani gata sai Allah se kai uba garesu dan haka banida damuwa da hakan kuma mu baka mana komi ba idan ma kayi mun yafe."

"Yanzu tun goben zaku tafiba zaki bari ku kara kwana biyu ba?" tace "A'a tafiyar dai zamu yi insha Allah zafi mana zaman nan d'in, kallon yaran yayi tare da mikewa yace to Allah kaimu goben, bin kan yaran yayi da d'aye d'aye ya na shafawa a sanu ya futar "Allah maku albarka ya jikan mahaifin ku kuma ya baku hakuri da juriya rashin sa tare daku."

Da ameen suka amsa sannan ya kali Hajia yace "To ni zan tafi anje ma zan dawo muyi ban kwana insha Allah." Tace "Ba damuwa saika dawo."

Daga nan ya fita ya bar gidan yana mai tausayin su har cikin rashin, umma ta ci gaban da lalashin 'ya'yata har suka hakura kowa ya tashi ya shiga harakokin gaban shi banda sadissu dake zaune har lokacin ya na tunani, daga bisani ya mike ya nufi k'ofa tare da barin gidan ga baki d'aya.

K'arfe hud'u daidai na dare bus d'in su ta bar cikin k'asar Mali don zuwa Niamey a kasar Niger Allah da ikon tun suna gani duhun asuba har gari ya fara wayewa sannu a hankali ha rana tafito haka har yamma tayi duk inda lokacin sallah yayi haka direban motar zaya tsayar da mota kowa ya fito yayi sallah, har Allah da ikon sa ya kawo su cikin k'asar Niger a garin Niamey suna shiga k'arfe biyar da minti goma yayi, suna saukowa daga cikin bus (car) d'in Hajia zakiya tayi wani k'ayatacan murmushi tare da cewa "Alhamdulilah yau na dawo k'asata da zama Allah nagode ma."

A take suka tatare kayansu da aka fido daga cikin motar tare da nufi gun da masu taxi ke tsaye suka musu magana taxi biyu suka d'auka sabida yawan kayan su duk da sun bar wasu a can.

Wata k'ayataciyar anguwa suka nufa tare da yiwa masu taxin k'watance gidan da zasu sauka bakin wani had'ad'en gidan masu taxi suka ja suka tsaye fitowa suka mahaifiyar tasu ta sake sakin murmushi ta sake furta alhamdulilah ala kuli halin, bud'e jakar ta tayi ta fito da key d'in gidan ta bude sannan ta dawo ta biya masu taxin kud'in su, kamin suka dinga jidar kayan su suna shiga gidan da su masha Allah gidan ba k'aramin kyau gare sa ba suna shiga suka gyara abin gyarawa sannan kowa ya nufi d'akin sa don yin wanka, da suka gama shirin suka dawo falo suna neman abinci sabida yinwar da suka k'waso a hanya.

Da suka buga suka buga basu sami komi a cuisine (kitchen) ba sai a ka tura Adamu nema masu abinci kamin ya dawo akayi kiran sallah magarib haka kowa ya nufi nasa dak'in don gabatar da sallah. Sai banyan sallah isha'i Adamu ya shigo gidan d'auke da abinda ya siyoo masu."

Umma ta dube shi tace "Yanzu Adamu sai yanzu ka dawo duk da kasan muna jin yinwa sosai" saida ya d'an nisa yace "Wallahi umma saida na wahala kamin nasamu abin siyowa."

Suna gama cin abincin kowa ya nufi dakin shi don yin bacin gajiya. Haka safiya na wayewa Fati da Mariama suka tafi kasuwa siyar kayan abinci da abinda ba'a rasaba sunna dawo suka nufi magasin (store) suka shirya komi sannan a ka fara hada hada had'a abincin rana haka suka ci gaba da rayuwa cikin farin ciki da annashuwa, yayiinda Hajia ta bud'e kanfanin siyar da shada da lace da atanta ida ta aikawa alhaji Suley kud'i ya na siyo mata shadodi daga mali yana aiko mata lace da atanfa kuwa haka take zuwa da kanta Nigeria ta saro tazo ta siyar masha Allah sanu a hankali kanfanin nata na ciganba cikin yardar ubangiji.

Konci tashi ba wuya a wajan ubangiji yau ya kama saura kwana hud'u a koma école (school) da marecan ranar alhaji Suley ya kira umma yake tambayata ya butun da wowar Fati makaranta Mali? tace "ka kwantar da hankalin alhaji insha Allahu alk'awarin da nayi maka yana nan ban tada shi ba nan da kwana biyu zata zo in Allah yayada" daga cikin wayar aka amsa "Da Allah ya kaimu."

Da dadare Hajia Zakiya ta tada ma Fati maganar kan cewa jibi zata tafi Mali insha Allah sabida da d'azu alhaji Suley ya kira kan maganar, mayar da kanta k'asa tayi tace "Umma gaskiya ni ban zan koma ba."

"Ko sabida mi kika fad'i haka?" ba tare da ta d'ago ba tace "Kawai ku kuna nan ni ina can ban iya zama ida baki nan gaskiya umma kawai kice wa baba ya yi hakuri."

Sak'e umma tayi tana kalon ta kamin tace "Ki k'wantar da hankalin kin Fati kije kawai ki k'arasa karatun ki can d'in Allah na tare dake kuma baban ku Suley da matar sa za su kula dake kamar yanda zanyi, ga isma'il saurayin ki zai fi kowa kula dake sedai ki rike mutuncin ki, idan baki son zama Mali wa yasaki fara soyaya da d'an uwanki wanda kinsan tôt ou tard tu va retourné laba de que tu sois sa femme (sooner or later you will return to the fact that you are his wife) kiyi hakuri ki tafi tunda mahaifinku na son zuwanki." D'ago da kanta tayi ta kalli mahaifiyar tasu tace "To umma Allah ya kaimu da "Amin" ta amsa sannan ta bar gun.........

Ranar da Fati zata tafi ta had'a mata shatara ta arziki don ta kaiwa 'yan k'asar Mali, har gidan bus (car) suka rakata tana ta kuka su ne basu dawo gida ba har saida suka ga tafiyar motar su tana kuka tana d'aga masu hannu har suka ba'ce mata itama umma saida ta saki 'yan k'walla.

**************

BAYAN SHEKARA HUDU

Abubuwa da yawa sun faru wanda cikin shekaru hud'un nan hada auren Fati da Isma'il wanda suke zaune a k'asar Mali cikin so da k'auna tare da kwonciyar hankali da nutsuwa da yaron su guda Abdallah hada tsohon ciki a jikin itama Mariama tayi aure a Zinder inda take d'auke da tsohon ciki, shi kuwa Adamu ya kamala karatun shi yana kulla da kanfanin mahaifiyar su da matar sa guda wada umma ce ta had'a auren su tare da d'iyar 'yar uwar ta dake garin Maradi, yana zaune yuri guda mahaifiyar sa da matar sa, shi kuwa sadissu yana université (university) ta garin Agadez yana shekara karshe ta doctorat.

Arzikin mahaifiyar su hab'aka yake masha Allah komi na rayuwa sunada shi sai abinda ba'a rasa saba sabida Hajia Zakiya tayi arziki sosai ba wanda bai santa ba a cikin garin Niamey, yanzu ba abinda zasu ce sai suce alhamdulilah Allah ya gama masu komi a rayuwa.

Watarana sadissu ya fito daga cikin makaranta zai d'an zaga gari a lokacin yana da 28 ans masha Allah kyakyawan saurayi dashi mai jini ajika kamanin sa na Malienne sun fito sak kamar mahaifi sa dogo dashi abin birgeewa da ko wace mace 'yan mata bouzaye na ta haukan shi amma shi ko ta kansu bai bi duk da kusan yanda bouzaye keda kyau da har idan ka kalleso bakason ka d'auke ido, amma shi ko akansa, a yanda ya tsara ma kansa baida ma lokacin soyaya a yanzu sai ya kamala karatu, kwatsame yana fito daga université ya d'an yi nisa da makarantar tasu ya kai bakin titi har zai tsalaka hanya yaji kuka kamar na mace a

Please Login or Register in order to submit comment