Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register




Takawa yake sannu sannu cikin k'asaita da izza da nuna isa kamar d'an sarki sukuwa garde corps (body guard) d'in su na biye da shi karma jela. A haka har suka kawo wani babban filin gida mai girman gaske ga kyau mara misali mai d'auke da b'angare guda fud'u duk manya, hanya wani katafaren b'angaren suka nufa, gab da zasu kai bakin k'ofar da zata sadaka da falon b'angaren, garde d'in dake kusa da shi ya juyo ga garde corps d'in ya masu nuni da hannu alama suyi tafiyar su, juyawa sukayi suka bar gun shi kuma yayi saurin shiga gaban sa kamin yake karasa wa ga k'ofar shi ya rigasa kaiwa ya bud'e maya k'ofar, sa kai yayi cikin falon tare da sallama shima ya bi bayan sa tare da rufe k'ofar.


Wata had'ad'iya mata ce zaune cikin k'ayatacan falon cikin d'aya daga cikin had'ad'un kujerun dake falon. Itama dai ba fara bace kuma baza'a kirata da baka ba kyakyawa ce sosai masha Allah.


D'agowa tayi tare da mayar da kalon ta garesu tace "Oyoyo filston (d'ana) sannun da dawowa" ta fad'a lokacin da ya karaso kusa da ita ya zauna a k'asa tare da aza kansa saman cinyar ta, ta cire masa fular dake kansa tana shafa lalausan gashin kansa, tace "Shalele mike damun ka, ko gajiyar aiki ne?" d'aga mata kai yayi alamar eh, lokacin da garde d'in da suke tare ya karaso shima ya zauna a k'asa kusa da matar yace"Mama ina yuni ya wunin gida" shima aza hannun tayi saman kanshi da murmushi a fuskar tace "Lafiya lau abba na ya gajiyar aikin ku? gaskiya kuna fama."


Yace "Wlh aiki da godiya mama kuma bama gajiya tunda mun riga da mun saba, sedai irin wada ba'a rasa" sake sakin murmushi tayi tace "To Allah ya taimaka kuma ya taya ku rik'on wanan kujera da aiki da gaskiya, Allah kare ku daga sharin mutun ko aljan da sharin karfe Allah tsare ku da tsare warsa."

Yace "Ameen mama mun gode Allah ja da kwana ya kara lafiya" Ta amsa da "Ameen Allah maku albarka."

Shi kuma miskilin yana nan har yanzu baice komai ba sai kawai ya amsa da ameen a zuciyar sa.


Can ya nisa cikin wata irin tausashiya kuma nutsatsiyar murya irin kamar an ma sa dolin nan, yace "Mama dan Allah kiyiwa Ali magana ban son abinda yake man," Tace "Mi kuma yake ma filston nasan kafa da rigima kamar d'an k'aramin yaro."


Da kayr ya iya bude bakin sa kamar wanda akama dole yace "Mama wai fah Ali sai ya ta yi min abinda ba na so, na fad'a masa cewa ya daina sara min, ko kuma idan ya gani ya tsaya k'ame yana wani k'auda kai gefe ba ma yason mu hada ido, ko kuma idan zan fito a mota sai ya bude min," sai da ya sauke ajiyar zuciya alama ya gaji da maganar da yake, sannan ya nisa yace " ko ki ji yana kirana da wani chef, ji fah miye wani chef da ko dad'i ji babu kamar bai san suna na ba, wlh Mama ki masa magana gaskiya in bai bari ba zamu b'ata a da ai ba haka yake min ba, sai yanzu ko fah magana bai so yana min bare ma gun aiki," mtsss ya dan ja tsaki kamin yaci gaba.


"Mama inada wanda zamuyi fira ko shawara ne, bayan shi amma kuma sai yayi ta yi min haka gaskiya ba jin dad'i abin nan, ban ma san miyasa akasa shi a matsayin garde corps d'in na ba" ya fad'a tare da koma wa ya kwanta saman cinyar mahaifiyar tasa yana me hararan Ali da ke gefe, murmushi Ali yayi tare da sosa kai.


Mama ta kalesu ta girgiza kai tana murmushi sannan tace "Umm AFREED sarkin rigima to ba aikin sa yake ba ai aikin sa ne haka shiyasa, kuma shin d'an uwan ka ne shiyasa aka aza sa a matsayin garde corps d'in ka sabida in yana kusan ka ba wani wanda zai cutar da kai sedai kawai wani ikon Allah" d'an turo baki yayi kamar karamin yaro har zaiyi magana kuma yayi shiru.


Sannan mama ta mayar da kallon ta gun Ali tace "Kai kuwa abba na ka daina yin haka ku koma yanda kuka taso tun yarinta, kada matsayin da yake dashi ya sa ka d'in ga gani ko ya fika, to ba haka bane babu abinda ya fika, manzon tsira (SAW) yace ba wanda ya fi wani a wajan ubangiji sai wanda ya fi ji tsoran sa, dan haka ka daina kawai tunda bai so kaga kai d'an uwansa ne kuma aminin sa ba wani bare ba." wani k'ayattacan murmushi Ali ya saki yace "To shikenan Mama na daina amma banda bude mota ina nufin zan dinga bude masa mota indan zai shiga ko zai fita, idan bai yada ba to ba zan daina duk abinda na saba ba" Ali ya fad'a yana dariya tare da kallon gefan da AFREED yake, wani irin kallo AFREED ya watsa wa Ali me nufin zan mu had'u, yace a shagwabe "Mama kinji shi ko!!! Mama tayi dariya tace "Umm ni dai ba ruwa na kun fi kusa, ku wuce kuje ku rage kayan jikin ku sai kuzo na zuba maku abincin, mikewa sukayi a tare suke ce d'accord.


Fita sukayi daga falon suka nufi nasu b'angaren direct d'akin AFREED suka shiga d'akin ne wanda ya amsa sunan sa d'aki, kana ganin shi kasan na ya'yan manya ne 'yan futu kuma sangartaci, suna shiga AFREED ya juwo ya kali Ali.


Yace "Wane gulma ne ya kawo ka d'aki na?" Murmushi Ali yayi yace "Eh an shigo d'in, ko fitar dani zakayi" wani mugun kallo AFREED ya watsa masa yace "Ai kasan zan iya tunda d'akin na wane, sai lokacin da naso muntun zai shigo, haka lokacin da naso za'a fitar min a d'akin, wata muguwar dariya Ali ya saki yace "Eh d'aki naka ne amma ku zanga wanda ya isa ya fitar dani, a nan zanyi wanka kuma ana zan kwana."


K'wafa AFREED yayi tare da shigewa doushe sabida ya gaji da maganar da yake, yana fitowa d'aure da tawel a k'ugun sa daya a kafad'a ya rufo kofar doushe (toillet) d'in tare da sa makuli ya kule ya ciro makulin ya nufi gaban coiffeuse (dressing mirror).


Ali na ganin ya zauna ya tashi ya nufi doushe d'in ya murda k'ofar ya jita a kule murmushi d'auke da fuskar sa ya juyo ya kali idan AFREED ke zaune ya nufi ya tako a hankali ya nufi gun sa yace "Haba mutumi na miye abin wani rufe k'ofar toillette d'in ka san fa shiga zanyi," ko kallon inda Ali yake baiyi ba bare ya amsa masa, kara fad'ada' murmushi sa yayi yace "Wai dan na ce bazaka iya fitar dani a d'akin ka ba shine ka rufe doushe d'in, to wlh da wasa nike ka isa ma har kayi yawa yi hakuri ban makulin kaga fah an kusa kira magaribah ka ban nayi na gama na fito ko na shirya kamin ayi kiran sallah, nan ma dai shiru bai ce masa komai ba "Dan Allah fah nace AFREED, sai lokacin ya juyo ya kalesa yace "daba sai ka k'wataba nagani d'an raini hankali, in badan gulma, ba ga d'akin ka can ba amma ba zaka ba dan kawai ka takura man zanyi maganin ka, shi dai Ali yana tsaye bai ce komai ba sai murmushi yake d'auko makulin yayi ya mika masa karb'a Ali yayi tare da juyawa ya bar gun ya nufi doushe d'in yasaka makulin ya bude sannan ya juyo yace "Ba dole yaro ya ban makuli ba ya na gudun kada nayi k'asa k'asa dashi, da sauri ya shige doushe d'in tare da kulo k'ofar.


Wani k'ayattacan murmushi me k'ara masa kyau da kwantar da zuciya AFREED ya saki tare da girgiza kai cikin zuciyar sa yace zaka fito ka same ni.


Shirya wa yayi cikin bakin wondo 3 quart (3 quater) da riga fara mai k'ananun hannu wa ya kali kansa a madubi, nida kaina nasan ina da kyau ne AFREED ya fad'a cikin zuciyar sa yana murmushi d'aukar wayar sa dake saman gado yayi sannan ya kwanta a gadon yana dane dane a wayar. Yayi daidai da fitowar Ali daga toillette yazo ya shirya shima kamar yanda AFREED yayi sedai shi na sa kayan jaune (yelow) da fari ne, sannan yazo ya zauna kusa da AFREED, yace "Wai mutumi na yaushe ne zaka tafi marad'i, naji kana cewa zaka d'auki ko da hutun kwana biyu ne ka je ganin tanti Aicha sabida tana tayi ma k'orafin baka zuwa gun ta."


Maido kalon sa yayi gun Ali "Yace nima ban saniba wanan aikin ne zai bar muntun zumucin, ai hutun sati zan d'auka idan nasamu dama kawai da naje sai na d'an huta."


Ali yace "Gaskiya kam idan kayi mata sati zata daina yawan k'orafin da take, sabida ko jiya sai da ta kira mama ta fad'a mata" sauke ajiyar zuciya yayi yace "Itama dai tanti ta cika k'orafi, ni kamar wata mace za'a dage da sai na wani je idan ma a garin nan take da da sauki" seda ya dan yi shiru na kusan minti 2, kamin yace "Da yake sada zumucin zan je nayi kuma dan ta damu dani ya sa ta ke son gani na, bai komi zanje insha Allah ina fatan Allah ya bani iko" Ali ya d'an tabe baki kanan yace "Da daidai zai fi."


Suna cikin tataunawa a kayi kiran sallah magaribah tashi sukayi don yin alwala AFREED ya shige doushe d'in sa, shima Ali fita yayi tare nufar nasa d'akin da bashi wani banbanci dana AFREED ya fad'a toillette dan d'auro alwala."


AFREED na fitowa ya nufi armoir (wardrobe) d'in sa ya ciro jalabiya (doguwa farar riga ) kusan a tare suka fito suka nufi masalacin da ke lik'e da gidan nasu.


*********


Marad'i...

Har cikin makarantar su AFREEN direba ya shiga da motar daidai inda ake tsaya wa ya ja ya tsaya AFREEN ta bude murfi matar tafita direba ya juya ya bar makarantar AFREEN ta juya da nufin barin gun da direba ya ajiye ta, taji an kira sunnan ta juyawa tayi , hango hasina na nufo ta murmushi ta saki daga cikin nikaf sai wanda ya lura zai gane hakan.

Tsaye tayi tana jiran k'araso war hasina, tana k'arasowa gun AFREEN tace "Abikiya ta ustaziya ko ina nata rufe rufe da shi, dake da shigar ki duk ku na birgeni da nima zan iya da na dinga yin irin shigar ki k'awata, in jin dai kin huce daga fushin da kike dani?"


kamo hannun ta AFREEN tayi tace "K'awata kin fiya surutu gaskiya, mi kika min da zanyi fushi dake in dan abin jiya ne yasa kike cewa hakanan kima daina sabida ni ban d'auke shi abin fushi ba ki barmin wanan zance da na riga na manta."


Hasina tace "Allah ko k'awata?" Kai AFREEN ta d'aga alamar eh, rugumeta hasina tayi tace shiyasa nike son ki k'awata baki fushi baki da rik'o tu est trés simple plus que je le pense, que le bon dieu nous laisse ensemble ma chérie," AFREEN ta amsa "Da ameen ma puce tare cewa ke cika ni mana ki wuce muje classe (class) kada profe de comptabilité ya shiga kinfa san halin sa da ko k'afar sa ya aza bakin classe ba me shiga shikenan sai ka jira fitowar sa" sakin ta hasina tayi ta kamo hannun ta tace "To muje."


Suna shiga ajin kowa ya dawo da kalon sa wajen su 'yan ajin nasu nata ga 'yan biyu nan sun shigo "To indai k'awatawancan ku ya kai yau hasina kisa ta bude fuskar ta mu gani" wata daga cikin 'yan ajin tace "Mi zaku gani ga munmunar fuskar AFREEN sabida munin ta fah ne yasa bata barin a ga fuskar ta sai ta nuna wai ita ustaziya, kar dai muga lega ah to ni na dad'e da gano munafurcin ta."


Kwashe wa da dariya 'yan ajin sukayi, a hasale hasina na ta warce hannun ta daga na AFREEN zata nufi gun wada tayi maganar da sauri AFREEN ta riko hannun ta tace "Haba k'awata na aza karatu kika zo a makarantar nan ba fad'a da cece kuce ba, rabu da ita mu ba muda wanan lokacin abinda ya kawo mu za muyi mu koma gida kinga shiru ma ai magana ce."


Koma wa tayi ta zauna ranta a matukar b'ace tama kasa magana sai huci take AFREEN tace "Haba wai hasina miye abin fushi a ciki kin maganar nan da zaki bar ranki ya bace ai sai taji dad'in cewa taci galabar b'ata miki rai, dan Allah saki raki man nida tayi ma abin ma raina bai b'aci ba se ke sai a sannan hasina ta saki ran ta tare da cewa "Ai ni sai a min abu na hakura idan a ka maki kuma na kasa hakura da bari na ki kayi naje na koya mata hankali wlh ba k'armin haushi ta ban ba."


AFREEN tace "Yi hakuri dai k'awata idan muka biye mata mun taru mun zama d'aya kenan" kwafah hasina tayi tare da hararen wace tayi maganar.


Wada tunda taga hasina tayi kukan kura da nufin ta shak'o ta ta sha jinin jikinta. Daga haka malamin su ya shigo suka fara karatu..............
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZANBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


ECRITE:


_PAR_


*QUEEN ZEEFAT*


Yar
Mutan
Niger


Wattpad@nazhabibou

💫✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🤝

☆ *[ T.M.N.A]* ☆ 📖🖊️

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM_


Page 7



K'arfe sha biyu daidai suka fito daga aji dama duk ranar da suke comptabilité ko fitowa récreation (break) basayi sai sunyi awa biyar a cikin classe, dan haka a gajiye suka fito, hasina tace "Wash Allah k'awata wly duk na gaji, ga yanda comptabilité ke caza k'wak'walwa ga kuma gajiyar zaman awa biyar ai dole mutun ya gaji wlh," AFREEN tace "Hakane k'awata akwai gajiya kam amma daga mun k'arasa shekara nan wahala ta k'are insha Allah," Hasina ta girgiza kai tace "Allah sa muna cikin masu sa'a Allah kawo k'arshan wahalar mu" AFREEN ta amsa da "Ameen" daidai lokacin da suka kawo bakin k'ofar makarantar sun tardo direban har yazo d'aukar AFREEN.

Hasina tace "K'awata ke har anzo d'aukar ki ma, kije kawai da yamma mun ha'du amma k'awata ki daina saka nik'af mana dan Allah."

Saida ta juyo ta kalleta tace "Je peux pas kallo na ake sosai wasu ma su ma kamar zasu cinye ni wlh sabida kallon k'urila da suke man, nikam banga abin kallo a tatare dani ba, kyau naga akwai wanda suka fini to miye na wani damuna da ido wlh hakan na takura man sosai ba, ina fad'a maki a nik'af ma ban tsira ba bare na bude fuska na hakan ya fi min kedai, na riga da nasa ba idan nace maki zan iya fita a haka to wlh nayi k'arya kunya ma nake ji."

Hasina tace "Shikenan amma taya kike gani zakiyi saurayi a cikin nik'af."
Hararen ta AFREEN tayi tace "Ni ba su ne a gabana kada ki k'aramin wannan zancen su a dole sai sunga fuskar mutun ne zasu ce suna son su kenan fuskar ce suke so ba mutun ba mtsss ku ne samari su ka dama amma ban dani ba wallahi. Wai haka sis Khairat tace man, bari naje direba na jira na."

D'ariya Hasina tayi tace "Gaskiya k'awata bakida dama to yi hakuri."

murgud'a mata baki tayi sannan tayi gaba abinta tace "k'awata seda yamma in Allah ya kaimu. Murmushi Hasina tayi, kamin AFREEN ta k'arasa tasu motar direban su Hasina yazo a tare suka bar bak'in makarantar.

Direba nayin parcking AFREEN ta fito tare da cewa "Baba direba ka juya ka d'auko Zeinab yanzu sun fito itama," direba yace "Yanzu kam d'iyar albarka" daga nan AFREEN ta nufi cikin gidan, tana shiga falon ta tarar da Maman da Tanti a falon da sauri Tanti ta mike ta tarbo ta tare da cewa "oyoyo d'iyata ya gajiyar makaranta" murmushi ta saki tace "Wlh Tanti akwai gajiya kin san fa yau awa 5 biyar mukeyi a cikin aji muna d'aukar darasi ba hutu."

Tanti tace "Kai yau alhamis ba da gobe juma'a kuna shan zama sai hakuri daga bana da yarda Allah kun k'are muje ki yi wanka da sallah sai ki samu ki huta, tace to bari na gyada maman tare da kallon inda mahaifiyar ta take wada tun shigowar AFREEN da ta juyo ta kallesu ta mayar da kanta a tv, tace "Maman ya yuni gida" juyo tayi tace "Lafiya lau AFREEN kun taso ko? Jeki ki fito kizo kici abinci" amsawa AFREEN tayi da "Toh" tayi gaba Tanti na biye da ita suka shiga dakin, AFREEN tace "Wash Tanti duk nagaji" ta fada tana mai cire nik'af da hijab sannan ta rage kayan jikinta ta shige douche (toilet).


Bin bayan ta da kallo Tanti tayi har ta shige douche tare da sakin wani kalan murmushi mai nufin abubuwa da yawa wanda ita kadai ta san min hakan yake nufi tashi tayi daga bakin gadon da take ta nufi armoir tare da ciro ma AFREEN wata bleu (blue) d'in doguwar riga mara dogon hannu tare da hijab sannan tazo ta shinfid'a mata darduma ta aza kayan a gado sannan ta juya ta fita.

Minti biyu bayan fitar ta dawo d'oke da abinci ta ajiye kan moquette ta koma bakin gado ta zauna tana jiran fitowar ta.


Ba b'ata lokaci AFREEN ta fito ta nufi gaban madubi ta zauna ta fara shafe shafan ta na turare tana gamawa ta tsane gashin ta da abin busar da gashi, sannan ta taso tazo baki' gadon ida Tanti ta ajiye mata kayan da ta d'auka ta saka tace "tanti nagode" Tanti tayi murmushi ta ce "Miye kuma abin godiya dan nayi wa 'yata abu."

Murmushi itama tayi wanda ya sa fossette d'in ta fitowa tasaka doguwa riga tana me mika ma tantin chouchou ta saka mata k'arba tayi ta saka mata tace "Yi maza kiyi sallah ga abinci nan na kawo maki bama sai kinje table a manger (dinning) ba." Saka hijab kinta tayi ta nufi darmuma da tanti ta riga da shinfid'a mata.


Tana idar da sallah ta tashi ta linke dardumar ta maryar da ita ma ajiyar ta, dawo wa tayi gun da tanti ta ajiye mata abinci ta zauna ta bud'e tayi bismilah ta fara ci, tanti dake zaune bakin gado ta dawo da kallon ta gun AFREEN tace " Yaushe ne saukar ku."

AFREEN dake cin abinci ba tare da ta d'ago ba tace "Nan da wata guda da sati biyu insha Allah."

Tanti tace "to Allah ya kaimu gaskiya d'iyata kina da k'ok'ari sosai kinga fah an yi miki saukar alkur'ani mai girma tun da dad'e wa yanzu gashi za'a yi maki ta tahafiz (saukar harda) da litatafn adini to Allah taimaka a ci gaba da bada hima, yima za ki cinye abinci ki bani assiéte d'in na mayar sai ki kwanta ki futa kamin lokacin école d'in yamma yayi."

"Ai nama goshi" AFREEN ta fada tana mai mikewa ta koma cewa "Tanti gaskiya kina ji dani irin wanan hidimar da kike man ai ko mahaifiyata sai haka sedai nace Allah ya biyaki da gidan Aljannah ina alfahari dake a matsayi matar mahaifina ku abukiyar zama gun mamana sabida Tanti ke ba kishiya ba ce sedai abukiyar zama ke uwace ta gari wada samun irinta a fad'in duniyar sai an tona, yanzu ba kowa bane zai iya kula da d'an da banasa ba, mun gode sosai da kulawarki da soyayar ki a garemu."

Ajiyar zuciya Tanti ta saki tare da sakin murmushi tace "Haba AFREEN idan kika cemin haka ai sai naga kamar baki d'auke ni a matsayi uwa ba, gaskiya bana so ki daina."

"To tanti ai yaba kyauta tukwici dole ce ta sa nace haka amma na bari bazan sake ba kiyi hakuri." mikewa tanti tayi tare da d'aukar assiète tace to "Shikenan ya wuce tashi kije ki kwanta ki huta kan ajima sai na shigo na tayar dake kinji ko."

Tace "To tanti wai ina anti Khairat najita shiru ko batanan ne."

"A'a barci take shiyasa", daga nan ta juya ta bar dakin. Murmushi AFREEN tayi ta d'ane gado ba da jimawa ba barci ya kwashe ta.


**********

Niamey.......

AFREED da Ali na dawo wa daga masallaci suka nufi b'angaren Mama suna shiga suka tarar da ita ta gun salle à manger (dinning) da hannu ta masu nuni da su k'araso gun ta suka k'arasa kowa ya ja ma kansa kujera ya zauna tayi servir d'in su.

Sun fara cin abincin kenan Ali ya dago ya kali mama yace "Mama ina su fariya tunda munka dawo aiki ban gansu ba" dariya mama tayi AFREED kuwa yayi murmushi yace "Gaskiya mama yau girkin ki yayi dad'i" irin wannan santi haka". Ali Sosa kan sa yayi tare da cewa "Kashe yanzu nan wai santi ne nayi gaskiya mama girki yayi dad'i sosai, amma su na ina wly seda na fara cin abincin ma na tuna Allah bar mana ke mamamu" tace "Amin abba na, suna gidan tanti ku d'azu karim yazo ya tafi da su daga tasuwar daga école kaya kawai suka canza ya tafi dasu, amma yanzu nasan suna bisa hanya tunda bacan za su kwana ba."

"To Allah dawo dasu lafiya Ali ya fad'a AFREED da mama suka amsa da "Ameen."

Ba su kai ga rufe baki ba a kayi sallama aka shigo falon, wasu 'yan mata ne da ba zasu wuce 18 ans ba suka shigo kyawawa kamanin su guda wankan tarwada masu matsakaicin jiki tsayin su daidai da su bai masu yawa ba da kagan su kasan yan biyu ne, da gudu suka nufi salle à manger guda ta rungume Ali guda kuwa AFREED.

"Oyoyo su yaya tun mun taso makaranta bamu ganku ba" murmushi AFREED yayi yace farissa ni narasa ranar da zaku girma wallahi? a tare suka sakesu tare da zuwa suka zauna suka saki murmushi a tare fariya tace "Mama wai yaya na tambaya yaushe zamu girma? 'Yar dariya tayi tare dace "Sai ranar dana kaiku d'akin mijin ku." da sauri farisa tace "To yaya kaji mama ta fad'a maka.

Yiyai kamar baiji ba yace "Mita ce" fariya tayi saurin magana tace "Mama tace sai ta mana aure," hararen wasa yayi mata yace "Ko kunya baki ji" dariya tayi ta sunne kai, Ali yace "Fariya aure takeso mama tunda har a gaban mu take maganar aure."

Da sauri tare da zaro ido fariya tace "Wallahi mama ba haka nake nufi ba kawai na maimaita abinda kika fad'a ne , shine nayi laifi."

Girgiza kai mama tayi sannan tace "Sai mi idan aure suke so tunda ku manyan banza har yanzu kun kasa fitar da mata kuyi aure, ai dole su na ma su aure ko hakan zai sa ku manyan ku san ciwon kanku, ku na kallo zan wanke su na kaisu d'akin su, amma kuma mahaifinku na dawo wa zan sa ya zab'a maku wada ya ga dama ya aura maku."

Da sauri AFREED da Ali suka waro ido suna kallon ta a tatare sukace "A zab'a mana kamar ya? Sai kace wasu mata, auren dole kenan fah wanan ai sai mace, mu da ba mata ba."

"Haka kuka ce to kuyi fatan Allah dawo da mahaifinku lafiya ku ga ikon Allah, zanga abinda zakuyi idan muka yanke hukunci a kanku."

"Dan Allah Mama ki daina fad'ar haka gaskiya duk a nawa muke da za'aga kamar mun jima ba muyi aure ba, Mama ki kwantar da hankalin ki kina nan har gida zamu kawo maki su ki gansu insha

Please Login or Register in order to submit comment