Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma yayi aure yama riga Sadisu da wata biyar sannan akayi na Sadisu har yanzu amintarsu nanan sai ma k'ara k'aruwa take yanzu haka shike kula da da kampanonin Sadisu dake Niamey sannan shike sanar da Sadisu abubuwan da yaka mata ya siya don azuba a kampani sabida shi aikin gini yake, sumana ingenier ne shi.

Banyan rasuwar d'an Arahamat da shekara biyu Allah ya koma ba wata haihuwar ta d'iya mace wada aka saka ma Fauziya shekara Fauziya biyu da watani aka haifi khairat, khairat nada shekara hud'u aka haifi AFREEN wada saida ta sha wuya wajan haihuwar ta alhalin sauran a sauk'ak'e haihuwar ta zo mata, kamin a yaye AFREEN Sadisu ya zuba masu haji suka tafi shida Arahamat da hajiya Zakiya da Fauziya wada a lokacin shekara takwas da haihuwa.

Bayan wasu shekara hud'u Arahamat ta sami wani cikin ta haihi d'an namiji inda ya ci sunan Fahad, Fahad nada shekara d'aya Sadisu ya auri Salamatou (umma) wada irin fulanin nanne masu sayar da hura a hanya kuma ta nan suka gamu da Sadisu sedai fitinaniya masifafiya ce tashin hankali ba irin wanda bata iya ba, ga kishi da rashin ilimi batada tunani ko kad'an sabida muguwa jahilace batada ilimi ko misk'ala zaratan itadai tashin hakali kad'ai ta iya bata buk'atar ganin mutun cikin farin ciki batayi sanadiya b'ata masa rai ba tun Arahamat bata gano halinta ba hata gane ta ta daina biyemata dama ita ba mai son tashin hanli bace.

Salamatou nada 'ya'ya biyu Zeinab da Safina, Allah ya koma bata Arahamat ciki wanda hata fida rai da samunshi sabida Fahad shekara sa shida da haihuwa sannan aka sami k'anan sa imran, itama Salamatou ta koma haihuwa ta sami Amira.
Sannan Sadisu ya k'ara aure, ya auri Sakina(Tanti) itama ya san tane ta dalilin zaman majalisa da suke a k'ofar gidan su Sakina wasu nacewa asiri ne suka mashi sabida tarasa mujin aure ta lak'e masa gashi har yayata da k'anwarta suna gida basu yi aure ba kuma saida takai shekara 37 sannan ta samin auren Sadisu sannan ta taushe kunan ta da maganar yan anguwa tayi aurenta ita kuwa mahaifin ta marok'ine (ma'ana irin masu gid'a ganga da kirarin nan ne idan za'ayi aure ko suna).

Saida Sakina tayi shekara bakwai a gidan Sadisu sannan ta sami haihuwa, inda ta haifi Hamida to itama tun daga shi haihuwar ta tsaya...

Arahamat na d'a biyar: Fauziya tayi aure kuma da d'an ta guda me suna humaid sai khairat da AFREEN sannan Fahad sai auta imran, ita kuma Salamatou da 'ya'ya uku: Zeinab, safina da Amira ita kuwa sakina da d'iya guda wato Hamida wada a halin yanzu shekara shida ke gareta.

AFREEN Allah yayita da rashin son kwaramniya ga rashin magana don idan ba niya tayi ba tana iya yini batayi magana ba banyan ta gaida iyayenta da safe to bazaka karaji maganar taba sai in taso ga ilimi da Allah ya mata na Γ©cole (school) da na islamiya sabida da shekara 12 aka mata sauka alkur'ani, nan da 'yan watani kuma za'a mata ta harda izo sitin, a Γ©cole kulum ta farko take zowa AFREEN ga kyau kamar ita tayi kanta ga tsari uwa uba nitsuwa da kamala, hausa sun ce d'an adama tara yake bai cika goma ba dana ce ita AFREEN komi ma ta had'a da zance ita goman ce daidai.

Kuma Abin birgewa a gidan su AFREEN shine duk yaran gidan suna da ilimi amma basu kai ga AFREEN ba ita duk ta fisu sedai karamin k'aninta imran ita ya d'ebo wajan ilimi gashi ma har yana son ya fita sabida shima tun yana shekara goma aka masa sauka alkur'ani mai girma kuma ilimin dage garesu duk gadon sa sukayi wajan mahaifin wato Sadisu dan ba k'aramin ilimi ne da shi ba don gaskiya Allah ya bashi sai kuma su AFREEN wanda gadon ilimin sai yazo masu ta hanya biyu wajan mahaifin da mahaifiyar su don itama Arahamat ba bayaba yajan ilimi duk suma na mahaifin suka gado.

Ibrahim yayan Arahamat yayi aure hada d'iyansa uku kuma ya koma Canada zama sanadin zuwan mai gidan sa daga Canada har Agadez nema sa alfarma ya zo yaci gaba da masa aiki har ta dalilin zuwan mai gidan nasa Niger shi mai gidan nasa ya musulunta ganin haka yasa mahaifin su Arahamat ya yarda ya koma garin na Canada ya ci gaba da aikin sa kuma ya tafi tare da iyalensa, amma duk k'arshen shekara yana zuwa ganin gida shida familyn sa gabad'aya.

Jannah kuwa k'anwar Arahamat itama tayi aure idan ta auri wani hamshakin mai kud'i suna can suna rayuwar su a London
Haka dai rayuwa tayita ci gaba da kasan cewa har kawo yanzu............



Cigaban labarin............



Sai mun had'u a next pageπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ



Taku har kulum mai kaunarku❀️



"QUEEN ZEEFAT"πŸ“πŸ“ ✍



ina yinku irin sosai d'in nanπŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°



Alhamdulilah....



Sai mun had'u a next page nan bada jimawa ba insha AllahπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZANBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


ECRITE: πŸ“πŸ“πŸ“


_PAR_


*QUEEN ZEEFAT*


Yar
Mutan
Niger


Wattpad@nazhabibou




πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/



_BISMILAHIR
RAHAMANIR RAHIM_



Page: 15 & 16



Cigaban Labarin.....




AFREEN ce zaune saman kan darduma a d'akin ta da alama sallah ta k'arasa alkur'ani na a gaban ta, ta na karan tawa cikin sanyayar muryata mai zak'i da dad'in sauraro, bud'e k'ofar d'akin nata akayi Khairat ce ta shigo tare da isa bakin gado ta zauna tana sauraran dad'ad'a kira'a dake fitowa daga bakin k'anwartata.


Saida AFREEN takai karshan surar ta alkaf da take karan tawa sannan ta d'ago ta kali Khairat dake kallon yanda take karatun ta cikin nutsuwa da kamala tace "Anti Khairat ina kwana kin tashi lafiya???"
"Lafiya lau AFREEN da fatan kema kin tashi lafiya, gaskiya yada kike karatu yana matuk'ar birgeni dubi yanda karatun ki ke fita da kyau duk wani harfi kina basa hakinsa sabida nutsuwar da kikasa a cikin kuma da mahinmancin da kika basa ga k'ira'ar mai d'adin sauraro Allah dai miki albarka Allah d'aukakaki Allah sa kifi haka kuma sa kiyi anfani dashi ameen ya Allah baki miji na gari wanda zai kula dake da k'arfafaki a kan adiniki fiye da yanda kike 'yar k'anwata ina alfahari dake," Khairat ta fad'a tana me sanki murmushi.

AFREEN ma murmushin ta mayar mata sannan tace "Ameen, Lafiya lau na tashi anti amma ai duk karatuna ban kaiki ba anti kinfini fitar da hakin ko wane harfi inda ko aka zo kan k'ira'a ban ma kamoki ba, amma a hakama ba karamin godiya nikema Allah da ya lafiyar da nake samun damar karatun nan."

"Kai kai AFREEN daina fad'ar haka ina ni, ina ke wallahi ke ta dabance 'yar uwa ina duk wanda ya sami wanan baiwar taki ya gama morewa a rayuwa haba ma soeur daina maida kanki baya kina had'a kanki da ni, regarde fah yanzu saukar tahafiz d'in alkur'ani za ayi maki da litatafai nan da 'yan watani, toh ni fah sauk'ar kallo kad'ai akamin amma duk da haka nagodewa Allah sabida nafi wasu sosai, ai ke AFREEN taki ta daban ce ba kowa ke samun irin takiba."

Har AFREEN tabud'e baki zatayi magana, sai Khairat ta rigata dacewa "Kinajiko AFREEN zuwa nayi muyi wata shawara, tun jiya da dadare naso muyi maganar nan tunda inasa ran zakizo d'akina kina ki kwana sai najiki shiru har nayi bacci."

"Eh wallahi karatu nayi har kwana ya kwashe ni a ida nayi karatun sai dana farka sallar dadare naga ashe saman darduma na kwana."

"Ok to shawara nakeso kibani kinji k'anwata sabida wataran kin fini tunani da hagin nesa."

"To Anti ina jinki Allah bani ikon baki ta k'aurai."

"Ameen, AFREEN kinsan sati uku da suka wuce na tab'a ce maki nayi wani saurayi Abdul Majid ko?" Khairat ta tambayi AFREEN tare da kallon ta, kad'a kai AFREEN tayi alamar eh.

Sannan Khairat ta ci gaba da cewa "To kinsan ban bari yazo gidan nan ba bare har yazo ya gaida papa sedai muyi waya da shi kuma kulum matsamin yake akan yanaso yazo ya ga gidamu sannan ya gaida papa da Maman, amma naki amince wa sabida ni idan yazo gidan nan basan ya zancewa papa ba alhalin yasan da zaman Ahmed to idan nace yazo ya gaida su papa, papa cemin zaiyi ko na b'ata da Ahmed ne yasa na kawo masa wani gashi kuma kowa yasan cewa Ahmed yazo yanemi aure na a wajan papa idan na kawo wani kuma za'ayi tunanin mun b'ata ne, gashi kuma shi Abdul Majid ya matsamin so yake yazo ya gaida su papa sannan idan papa ya yarde masa nan da sati biyu iyayensa zasu kawo kud'in aure, to ke Soeur ya kike ganin wanan lamarin zai kasance?"

Saida AFREEN tayi gyaran muryan sannan tace "To Soeurette (yar uwata) yanzu wanan lamari gyaran shi yana wajan Allah kuma ya wajan ki kuma wanan matsalar kece kike da ikon magani ta ba kowa ba sabida ragamar lamarin nan tana hannu ki kuma ba wata matsala babba ce, mai saukin warwarewa ce amma idan kin so hankan ko ba gaskiya ba."

Khairat tace "Ban gane mikike nufi ba iman da wara wara ko zan gane dalilin da yasa kika fad'i haka."

"To sis abin dubawa anan shine shi dai Ahmed saurayin kine dan kukai kusan shekara uku kuna tare kowa yasan ku tare shi kuwa Abdul Majid duka ko wata bakuyi da had'uwa ba dubara ta rage taki ki fida wanda kikeso cikin su sannan kada ki manta da abinda papa zaice idan har kika k'ara kawo masa wani alhalin sun ajiye magana da iyayen Ahmed akan idan kika k'arasa makaranta zasu kawo kud'in auren da sa rana baki d'aya kinsan mi papa zaice? Girgiza kai Khairat tayi alamar a'a, "To cewa zaiyi baki isa kisa ka shi ma magana banza ba ko kuwa shi zaki kunyata ko ki maida shi k'aramin mutum sabida wanan lamari da kika d'auko har k'ananan mutanece, amma in tambayeki man shi baki son Ahmed kin ne har kike k'okarin kawo wa su papa wani?"

A'a inason shi mana amma kuma nafara son Abdul majid shima."

To Γ§a veux dire que kina iya barin Ahmed ki koma ga abdul Majid tun da har kika fara tunanin kawo shi gun papa, to walahi anti idan baki cikin hankalin ki to tun wuri ki dawo hayacin ki anti Khairat sabida idan kika bar yaya Ahmed bazaki tab'a samun kamar shi ba sai wani ikon Allah bare idan cin amanar sa kika yi Allah zai kama ki walahi Anti yaya Ahmed mutun ne na gari ga addini da sanin yakamata dubi yanda yake girmama iyayenki kamar nasa walahi samin irin shi sai an tona bare yanzu da duniya ta lalace, banson kije kiyi abinda kuma daga baya zai ki koma dana sani dan haka kaki ma fara walahi," AFREEN ta fad'a tare da kallon 'yar uwartata.

Kai sister walahi duk kin sarar min da gwiwa walahi amma duk da nace haka ba yana nufin zan daina kula Ahmed ba ne sabida inason sa har yau amma idan na bawa Abdul Majid damar yazo yaga su papa ba wani abu bane idan cikin su biyu wanda yariga kawo kud'in sa gidan mu sai ayi dashi, amma tunda kince haka gaskiya zan rabu da Abdul Majid dama ba wani son sa nake ba zan fad'a masa gida an riga da an min miji shikenan sai murabu lafiya sabida gaskiya nasan idan na auri wani wanda ba Ahmed zan iyasa shi cikin wani hali amma Ahmed shi ne ya dace dani ni da kaina na sani kuma ina nema zab'in Allah, bari na barki ki tashi kiyi shirin Γ©cole (school) lokaci na tafiya ni ma dai ranar lundi (monday) zan koma ga karatuna yi maza ki shirya ki fito muyi kari," Khairat ce tayi wanan maganar tare da mikewa ta fita daga d'akin.

Tana fita AFREEN ta tashi ta kintsa d'akin sannan ta shiga wanka a gagauce ta fito sabida ta lura da ta kusa yin retard (lati), tana fitowa ta shirya cikin wata had'ad'iya dokuwa riga bak'a batada kwaliyar komai amma ta had'u bare da tasaka ajikin ta sai ta k'ara fito da kyayon rigar masha Allah, sab'o zunbulelan hijab d'in tayi tasaka tare da rike nik'af a hannun ta ta saka takalmi mai dan tsini sannan ta fito tayi yanda ta saba saida ta nufi d'akin kowa ta gaida shi a d'akin tanti ne ta d'an jima sabida kulum idan ta shiga gaida ta to za bata wata zumuwa tasha sannan ta kad'a mata wani magani cikin madara ta bata, duk wanan abin da Tanti ke bawa AFREEN idan ta shiga d'akin ta AFREEN bata tab'a gayawa uwarta ko wani kuma bata tab'a tambaryar Tanti ko maganin miye take bata ba sai ita Tanti idan taji bata tambaye ta saitace "Wai AFREEN miyasa bazaki tambaye ko maganin miye nike baki ba, sedai da na baki sai ki karb'e ki shanye idan ma na cutarwane ke dai kin sha kenan nan ya cutar dake d'in babu ruwanki?"

Sai AFREEN tace "Kai tanti ai nasan bazaki cutar dani ba miyasa kuma zan tambayeki? kamar dai ban yarda dake ba."

Itama Tantin sai tace "A'a AFREEN yana dai kyau kisani sabida gudun zarki."

Zarki kuma Tanti? Kamar dai bansan ki ba haba dan Allah ni walahi nayarda da ke d'ari bisa d'ari nasan bazaki cutar dani ba ni ko maman ban gayama bare har naji zargin a zuciya ta."

"A'a aini dad'ewa na fad'a mata AFREEN sabida banson abinda zaije ya dawo ayi dibin cutar dake zanyi walahi nikuwa maganin bakine da na tsari nike baki sabida lura da nayi mutane na yawon samiki ido da nuna maki bakin ciki k'irik'iri ko bakin umma kad'ai ya isheki ga yanda take nuna maki k'iyayya k'irikiri ba'asan abinda mutun zai iyayi ba duniya ba gaskiya, Allah dai maki maganinta."

AFREEN tace walahi ni tanti umma ko ganin ta banyi sabida nasan duk abinda take wata rana zata daina walahi ko kad'an ban rik'eta ba koda na minti d'aya ne bare har ya zama nasaka ta a zuciya ta kulum ina fatan Allah sa tagane, ko da kuwa ace ta tsaneni nasan da wata rana zata so ni kuma nasan da k'inane kawai take bata nufana da wani shari sai dai fatan Allah sa tagane."

To ko yanzu da AFREEN ta shiga d'akin tantin haka ce ta faru suna ta irin wanan firar har lokacin da tanti ta jefoma AFREEN tambayar cewa "Wai AFREEN kulum kina min firarki ta makaranta ko kuma ta k'awayenki ko kuwa ta wani abu dai haka amma baki tab'a yimin firar saurayin ki ba ko miyasa ko baki son na sanshi ne na'aza mukai lokacin da ba zaki iya boyemin wani abuba ko dan nabaki shawara?"


"Lah tanti walahi har kinsa ma naji kunya dama tanti har zakiyi tunanin akwai abinda nake boye maki wanda nake zaunawa muyi fira dake muyi shawara ko da Maman ba mayi haka, tanti nifa karatu nake yanzu samari basa gabana walahi babu wanda nake kulawa karatuna kawai nakeyi."

"A'a AFREEN wajan karatu daban kuma yin saurayi daban to zaunawa zakiyi har sai kin gama karatu sannan ayi batun aure a'a to ko alama gaskiya ki daina saka wanan nik'af d'in sabida kowa da ya ganki sai yayi dubin matar aure ce gashi Allah yayi maki kyau amma kina boyeshi to gaskiya da sake ni surikina nakeson gani ah to."

Da gudu AFREEN ta baro d'akin tana dariya tare da cewa "Walahi tanti kinsa na daina shigo d'akin nan naki."

Wani irin murmushi tanti tayi tace "Hum zaki dawo ga hanya yarinya muje zuwa dai."

AFREEN nafita daga d'akin tayi hanyar barin falon gaba d'aya sabida tayi lati bama zata iya tsaya wa yin kari ba ta nufin motar ta ta shiga ta kuna tare da barin gidan ta nufin makaranta.

K'arfe shad'aya na rana AFREEN ta dawo daga makaranta, tana shiga falon gidan ba kowa a cikin direct d'akin ta nufa tare da rage kayan jikin ta shige toilet tayo wanka juma'a sannan ta fito k'ara shiryawa tayi cikin wata dogowar riga vert (green) mai ratsi jaune (yellow) ta saka hijab green da takalmi green sannan ta d'auki nik'af ta bar d'akin tare da shiga d'akin Khairat da sallama Khairat ta amsa mata sallamar sannan AFREEN tace "Anti kin shirya ne mu tafi masallaci kinga fah har 12:30 tayi sabida ke d'aya zan iya tsaya ma dan ko su zeinab idan basu shirya ba sedai su wuce tare da papa sai mu dawo tare gaskiya bana son k'arfe 1:00 tayi ban tafi masallaci ba."

Al'ada gidan su AFREEN ce duk ranar juma'a 'yan gidan gabad'aya kan babba kan yaro mace da namiji har mai gadi kowa da kowa dai a gidan harta iyayen su mata tafiya masallaci suke dan yin sallar juma'a, a baban masallaci cin juma'a na sahaba dake cikin garin Marad'i.a

AFREEN ke d'auka yaran a mota su tafi Khairat ma ta tafi a motar ta idan kuwa taga dama sai bi AFREEN su shiga tata motar tare da yara su tafi masallaci, shikuwa papa ya kwashi matan sa su tafi tare, Fahad kuwa ya d'auki motar sa su tafi shida Imran sabida makaranta ma tare suke zuwa.

To yau ma haka ce ta faru AFREEN suka tara gabad'aya aka rufa gidan suka nufi masallaci don yin sallah juma'a kuma duka cikin su AFREEN ce kad'ai keda nik'af.



Sai mu had'u da next pageπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ



Taku harkulin mai kaunar ku❀️πŸ₯°πŸ’“



"QUEEN ZEEFATπŸ“πŸ“βœπŸ»



Inayinku irin sosai d'in nan masoyan 🌸ZANBA CIKIN AMINCI🌸 alkairin Allah ya kaimaku duk inda kukeπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*ZANBA CIKIN AMINCI*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


Γ‰CRIT:


_PAR_



*QUEEN ZEEFAT*




Yar
Mutan
Niger



Wattpad@nazhabibou



πŸ’«βœ¨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟
_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝

β˜† *[ T.M.N.A]* β˜† πŸ“–πŸ–ŠοΈ

https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM



Page: 17 & 18



Tangamemiyar ma'aikata ce mai matuk'ar kyau, ma'aikatar karshe ce wajan tsaruwa a saman k'ofar ma'aikatar da mayan harufa an rubuta *MINISTÈRE* (wato ma'aikatar ministoci, inda ko wane minister keda babba kuma had'ad'en office) sojoji ne sosai gewaye da ma'aikatar daga cikinta har wajan ta tsaro ke akwai sosai, wasu had'ad'un motoci ne guda biyar suka kuno kai a cikin ma'aikatar suna gama parking sojojin da ke cikin motocin guda hud'u suka fito da sauri tare da nufar cikon motar ta biyar, duk suka tsaya a tsaye kyam kamar an dasa su tare da haka bidigogin su irin ma su jiran tab'in nan su sakar maka alburushi, gaban motar aka bud'e Ali ne ya fito ya nufi k'ofar baya ta motar ya bud'e, kusan minti biyu da bud'e k'ofar sanan na cikin motar ya ziro kyakyawa k'afar sa mai sanye da wasu had'ad'un takalmi masu mugun kyau Kana ganin su kasan bana na k'ananun kud'i bane.


Ida fito da k'afar guda yayi kamin ya k'arasa fitowa gabad'aya, sai a sannan na gane da AFREED ne ya had'e colin wata dakakiyar shada bleu (blue) da tayi matuk'ar d'aukar jikinsa dan ba k'aramin kyau kayan suka masa ba.


Jerawa sukayi shida Ali suna tafiya sannu sannu cikin kwonciyar hankali da nutsuwa kamar basa son taka k'asa su kuwa garde-corps (bodyguard) d'insa na take masu baya abin kwanin sha'awa masha Allah, kana ganin AFREED da Ali zaka iya tunanin 'yan biyu ne sabida suna matuk'ar kama da juna, sedai AFREED ya fishi tsayi shikuwa Ali ya fi AFREED haske.


Suna shiga cikin katafariyar ma'aikatar k'ananun ma'aikata na kwasar gaisuwa amma hannu kawai AFREED ya samu damar d'aga masu 'yar karama tafiya suka Ali yayi Saurin k'arasawa bakin k'ofar Wani bureau (office) wanda sama k'ofar bureau (office) d'in an rubuta *MINISTRE DE DÉFENSE ET DE SÉCURITÉ* (wato ministan sojoji da na tsaro).
Masha Allah baban office ne k'ayatace wanda ya amsa sunan sa office don table ma da kujerun dake cikin bureau (office) d'in kad'ai abin kalo ne.
AFREED da garde-corps d'in sa na ida k'arasawa bakin k'ofar office d'in bai tsaya komai ba ya shige ciki sukuwa suka tsaya a bakin k'ofar kamar an dasasu, directe (direct) wajan luntsumemiyar kujerar sa da ke gaban table d'in bureau sa ya nufa ya zauna da bismillah ya fita da hular dake saman kansa tare da fad'in oh mon dieu (oh my god) ya duk'e tare da aza hannayan sa da kan sa a saman table d'in dake gaban sa.


Ali dake bakin k'ofar tare da garde-corps ya kalesu yace "biyun da suka saba tsayawa a bakin k'ofar su tsaya ku kuwa sauran kuje kuyi wanda kuka saba har a nemeku da sauri suka sara masa tare da cewa d'accord monsieur (ok sir) biyu suka tsaya sauran sukayi gaba shi kuwa ya fad'a cikin bureau (office) d'in AFREED tare da rufo porte (door) d'in yaje ya zauna cikin d'aya daga kujerun dake fuskantar AFREED.


Kalon AFREED ya tsaya yanayi na tsawon minti biyu kamar wanda keson gano wani abu kamin ya d'an nisa yace "Wai frΓ©ro (broh) mike damunka ne tun fah jiya da dadare bayan mun dawo daga gun dady naga kamar baka cikin walwala na tambaye ka Kuma kamin shiru dan Allah yanzu dai ka fad'a min kwakwata nima ka saka hankali na ya k'i kwanciya duk na damu walahi bana son ganin ka a haka."Ali ya fad'a da damuwa k'arara a fuskar sa.


A hankali AFREED ya d'ago ya kalli Ali tareda sakin boyayar ajiyar zuciya sannan yace "FrΓ©ro ( broh) mi kake ganin zai dameni da ya wuce abinda dady ya mana magana akan shi jiya."


Wani k'ayatacan murmushi yayi sannan yace "Dama nasan babu abinda zaiyi mugun daga maka hankali kamar wanan maganar da dady yayi amma miye abin d'aga hankali kan abu me sauk'in irin haka."


Wani uban harara AFREED ya narkawa Ali kamin yace "Mike me sauk'i a cikin abinda da dady ya fad'a ko ka d'auka da wasa yake ne, ko dai dan kai a shirye kake ne sabida kasan duk fad'a a kaina aka sauke kai banda kai shiyasa kake wani cewa sauk'i ne da shi."


"Hum AFREED kenan banga miye abin tada jijiwoyin wuya abinda wanan abin sauk'i ne dashi kamar yanda na fad'a maka kasan ko miye sauk'i shi?"


Girgiza kai AFREED yayi alamar a'a.


D'an nisawa Ali yayi tare da gyara zama sannan yace "AFREED abinda ya kamata kayi ana shine kayi gagawar fitar da matar aure tun kafin dady yayi maka auren da bakaso, wato ya zab'a ma matar da kanshi ga mata nan iri iri sunna kawo kansu gareka amma baka kulasu ka darje kawai ka zab'i d'aya a cikin masu kawo maka hari, dubi fah wanan farin jinin da Allah ya maka yanda mata da kansu suke kawo maka talar kansu amma kana sharesu, gashi babu inda Allah ya rage ka AFREED kayi niya kamin lokacin da dady ya iba mana ya k'are."


"To wai kai Ali da kake tacewa nayi niya nayi niya tayaya kana ganin ni ko secrΓ©tariat ta (My secretary) ban ida tantance ta ba itada kulum tana shigowa office d'in nan fiye da so goma a rana to ko ita akace yanzu na gwadeta to wallahi a saramin babban aiki to tayaya zan kalli wata harnaji inason ta gashi kuma na fison na fida mata da kaina tun kan dady ya zab'a

Please Login or Register in order to submit comment