Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*SHU'UMIN NAMIJI !!!*


*(Wannan labarin ƙirƙirarren labari ne, wanda na ƙirƙira, bakuma naso ajuya min shi tako wani siga....)*


*WRITTEN BY*
phatymasardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*


*DEDICATED TO MY LOVELY BROTHER KHABEER*


*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassocition*



*WATTPAD*
@fatymasardauna


*Вisмiιιαhirra hamanirrahiм*


*Chapter 1*


Wani irin gudu black colour car ƙirar RANGE ROVER ke falfalawa akan babban titin dake cikin garin *ABUJA* ...

Gaban wani irin makeken gate motar ta tsaya, minti kaɗan kuma ta soma wani irin ƙara kamar zata cire kunnen maisaurare, cikin mintuna ƙalilan maigadi da jikinsa ke rawa ya wangale makeken gate ɗin, da gudun bala'i ya cinna hancin motar tasa ciki, daga yanayin yanda yayi parking kaɗai ya'isa nusar dakai cewa wanda ke cikin motar, cike yake da iskanci haɗi da zallan taɓara... Duk yanda naƙosa wanda ke cikin motar yabayyana nasamu damar ɗauko muku hoton fuska da surarsa amma abun yaci tura, domin dai shegen ƙin fitowa yayi bare nasamu ganinsa.......

15 minutes ya kwashe cas batare daya sanyo kansa waje ba, a hankali yasako ƙafarsa waje wacce ke ɗauke da tsadadden black canvas mai ɗauke da fararen igiyoyi a samanta, a hankali yagama fito da duka jikinsa daga cikin motar, Masha Allah !! shine abun dana furta lokacin dana gama sauke idanuna akan shi, kyakkyawa ne ajin farko, haɗaɗɗen matashi maiji da kyau haɗi da zallan kuɗi uwa uba hutu, fari ne tas banda sajensa dakuma tulin gashin kansa babu abun dayake baƙi ajikinsa,, saurayi ne mai cikar zati da kuma haiba, yana da cikar sura dakuma ƙaƙƙarfan jiki, kallo ɗaya zakai masa kafahimci cewa mutum ne ma'abocin yin gym, kyakkyawar fuskarsa tana ɗauke da yalwatattun idanu masu ɗauke da brown eye balls acikin su, sannan kuma yana da dogon hanci gwanin burgewa, bakinsa kuwa ɗan ƙarami ne, mai ɗauke da ƴan saffa saffan laɓɓa light pink colour, gashin girarsa dana idanunsa a yalwace suke tamkar dai wanda yayi ƙari, wani irin haɗaɗɗen sajene yayi mawa fuskarsa ƙawanya, wanda kuma haddashi yaƙara wa fuskar tasa kyau, jikinsa kuwa gaba ɗaya a murɗe yake, sanye yake da White t-shirt fara ƙal ƙal da'ita, yayinda wandon jikinsa yakasance black pencil jeans wanda ya kamasa sosai, sai ƙafarsa dake sanye da black canvas, kunnensa kuwa saƙale yake da earpiece, da'alam dai ƙiɗan sa yake sha,, yayi matuƙar kyau sosai, fuskarsa tana ɗauke da wani asirtaccen murmushi mai ƙayatarwa da burgeqewa,, hanunsa riƙe da car key ɗinsa yadoshi wani haɗaɗɗen gini, dake cikin harabar babban gidan nasu, da'alama dai nanne babban falon gidan.....


Wata haɗaɗɗiyar Farar Mata wacce bazata wuce 47 years ba ke zaune akan ɗaya daga cikin haɗaɗɗun kujerun falon, tasha ado cikin wani irin danƙareren lace mai kyau da tsadar gaske, a zahiri idan kaganta zakai zaton batawuce 35 years ba, bakomai yasanya hakan ba fa ce tsananin hutu dakuma tsantsar jindaɗi da yabayyana ajikinta wanda hakan ya ɓoye asalin shekarunta,, iya gwala gwalan dake sanye a wuyanta haɗi da kunnenta, kaɗai ya'isa ya tabbatar maka dacewa itaɗin baƙaramar mai tarin dukiya bace.... Da wani irin fito yashigo cikin falon yanayi yana kaɗa makullin motarsa dake saƙale cikin yatsarsa manuniya,,

"Hello Mom "
saurayin yafaɗa cikin unigue voice ɗinsa...

Murmushi wacce aka ƙira da suna Mom tayi haɗe da cewa " Your Well Come My Son"

Bai amsa mata ba saima zama yayi akan kujeran dake kusa da'ita yana mai yunƙurin cire takalman dake ƙafansa......


*((Wannan salon na dabanne My Fans kubiyoni domin jin wanene *SHU'UMIN NAMIJI !!* *wayeshi ? menene halinsa ? wace gwagwarmaya za'a tafka ? Saikun biyoni zakusan komai, takunce dai Mrs Sardauna, kada kumanta wannan labarin yasha banban da sauran.... ))*

*(I'm sorry my fans Insha Allah zakujini da cigaban MENENE MATSAYINA ? a bubuwane suka shamin kaina shiasa kukajini shiru....)*


*10/October/2019*




*MRS SARDAUNA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SHU'UMIN NAMIJI !!*


*Written by*
phatymasardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*


*Dedicated To My Lovely Brother Khabeer*


*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

*WATTPAD*
@fatymasardauna


*Editing is not allowed 📵*

*Chapter 2*

"Inakaje ne wai *ΖAID* tunsafe rabon dana saka acikin idanuna ?" Mom tatambayeshi,

ɗan taɓe bakinsa yayi haɗe da cewa "aiki ne yaimin yawa a office, Labisat takawomin abinci.. " yanakaiwa nan a zancensa yasakai yafice daga cikin falon.... Murmushi kawai Mom tayi domin tafahimci cewa Shu'umanci'n Zaid ɗinne yatashi....

Wani irin haɗaɗɗen gini naga Zaid yanufa, wanda yake can gefe da makeken lambun gidan, key yasanya haɗi da buɗe wata ƙofa, wani irin haɗaɗɗen falo mai masifar kyau Zaid yashiga wanda nake tunanin nanne mallakinsa, Masha Allah, falo ne daya amsa sunan sa falo, cike yake da abubuwan more rayuwa, kujerune irin leather sit ɗinnan farare ƙal ƙal zube a tsakiyar falon, yanda kujerun suke da haske kaikace ba'ataɓa hawansu ba,, tsakiyarsu kuwa wani haɗaɗɗen brown chanies carpet ne shumfuɗe mai taushin gaske, wasu irin ƙawatattun curtains brouwn colour ne suka taimaka wajen sake bayyana kyawun falon, duk da cewa bawani tarkacen kayan ƙyale ƙyale bane a falon, amma hakan bai hana falon yin kyauba, kallo ɗaya zakamawa cikin falon katabbatar cewa mamallakin wannan katafaren falo, baƙaramin ɗan gayu bane,, tundaga falo Zaid yasoma cire rigarsa yawurga kan kujera, yana tafiya yana cire wandon jikinsa ahaka ya isa cikin haɗaɗɗen bedroom ɗinsa, saida yacire duk wani kayan jikinsa, kafun ya shige cikin bathroom ɗinsa, koda na leƙa cikin bathroom ɗinnasa saida nayi tsananin mamaki, wai ace banɗaki aka kashemawa kuɗi haka tamkar wani fadan shugaban ƙasa ? hmmm ALLAH yakyauta....

Fitowa yayi ɗaure da towel a ƙugunsa, yayinda jikinsa ke jiƙe da ruwa, gaban makeken dressing mirror ɗinsa dake cike da mayukan shafa haɗi da turaruka kala kala yanufa, saida yatsane ruwan jikinsa, kafun yasoma murza tsadadden lotion ɗinsa akan haɗaɗɗiyar fatan jikinsa,, komai dai cikin tsanaki yakeyi harya kammala,, riga da wando yakuma sawa, saidai wannan karon Blue colour garesu, sun kuwa matuƙar amsar jikinsa,, Wayarsa ƙirar iphone 11 pro max ne tasoma ruri alamar shigowar ƙira,, harta katse Zaid bai ɗauka ba, wani ƙiranne kuma yasake shigowa,, ɗan ƙaramin tsuka yaja haɗi da nufar inda wayar take,, Zee shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar, picking call ɗin yayi haɗi da kara wayar akan kunnensa batare da yace komaiba, "Hello Baby !! zee tafaɗa cikin wata irin shaiɗaniyar muryarta, ɗan ƙaramin murmushi yayi haɗe dacewa "Ya'akayi ne Zee ?" jin abun dayace yasanya Zee sake gyara zama haɗe da ƙara kashe murya tace " Ina guest house ɗinka pls Baby kazo... " Okay " yafaɗa a taƙaice haɗe da kashe wayar yacusa cikin aljihun wandonsa,, knocking ƙofar ɗakinnasa akashiga yi, cikin muryan faɗa faɗa yace "Uban waye ke bugamin ƙofa kamar yasamu falon Ubansa ?" Labisat dake tsaye riƙe da tire ɗin abinci ahanunta, taturo baki gaba haɗe da cewa "Bro nice fa, abincinka nakawo ma ka" tsaki yakuma ja haɗe da cewa "Oya maidashi fita zanyi, innadawo nazo naci " sumi sumi haka Labisat tajuya da abincin.....

Wata haɗaɗɗiyar Blue car yashiga haɗe da bata wuta yafice daga cikin gidan.....

Kaitsaye G.R.A yanufa inda acan guest house ɗinshi yake, yana zuwa maigadi ya wangale masa gate yacusa motar tasa ciki......

Jin tsayuwar motar shi yasanya Zee tashi da sauri tanufi hanyar fita daga falon, da sassarfa taje tafaɗa jikinsa haɗe da goga masa breast ɗinta, cikin kirsa tace " sannu da zuwa babyna,, wannan munafukin murmushin nasa yayi mata haɗe da cewa "Ƴan Mata yakike ?" "lafiya ƙalau " tabashi amsa daidai lokacin dasuka ƙaraso cikin katafaren falon,, janyeta yayi daga jikinsa haɗe da zama akan ɗaya daga cikin kujerun falon " Kawomin ruwa " yafaɗa daidai lokacin daya cire rigar jikinsa,, cike da kwarkwasa Zee tamiƙe haɗe da ɗauko masa goran ruwan faro acikin friedge,, karɓa yayi yakafa bakin gorar abakinsa, tas yashanye ruwan haɗi da cilli da goran ruwan hanu yamiƙa ma Zee akan tataho gareshi, aikuwa dama jira take dan haka taɓalle duka aninayen gaban rigarta, take manya manyan breast ɗinta suka bayyana,, kansa yanutsa acikin breast ɗinta, bayan yayi mata masauƙi akan cinyarsa, cikin salo yacire mata gaba ɗaya rigar dake jikinta, hatta breziya bai barmata ba, bakinsa yaɗaura akan nipples ɗinta, yashiga yi musu wani irin kalan tsotso yayinda hanunsa, ke kan bayanta yana shafawa ahankali, tuni Zee taƙara rikitasa da salonta, ɗaukarta yayi caɗak suka nufi bedroom, kwantar da ita yayi flat akan gado, bayan yacire komai najikinta, yanda yake wasa da'ita kaɗai yasanya Zee ficewa acikin hayyacinta, domin Zaid ƙwararrene awajen iya sarrafa mace,, cikin mintuna ƙalilan Zaid da Zee suka faɗa duniyar ashsha duniyar Mazinata, (Ya Allah kakaremu daga aikata Zina Ameen).......

*****

*ZARAH ! ZARAH !!* wata mata dake zaune kan tabarma keta kwaɗa gira,, "Na'am" wacce aka ƙira da suna Zarah ta amsa tana mai fitowa daga cikin wani ɗaki,, wata kyakkyawa matashiyar budurwa wacce bazata wuce 20 year ba tabayyana gaban wannan matar da ke aikin ƙwaɗa ƙira, cike da girmamawa tace Inna gani,, "Au dama tunɗazu kinajina iskancine yahanaki amsa ƙirannawa kome ?" matar tafaɗa tana mai gallamawa yarinyar dake duƙe a gabanta harara,, cikin tausasa murya Zarah tace "Kiyi haƙuri Inna wallahi, banjiki bane inacan ciki ina shirin makaranta, yau muna da lecture'n safe banso na makara " "Uwar Lecture kuke dashi da ubansa, inkinga kinfita agidannan to wallahi kinga mamin aiki nane " Inna tafaɗi haka tanamai tsakace haƙoranta da tsinken dake riƙe a hanunta,,,, cikin sigar lallami Zahra tace "Dan Allah Inna kiyi haƙuri idan nadawo sainayimiki duk abun dakike so " "Zaki tashi kisoma aikin dana saki ko kuwa saina mangareki banza mai kama da aljanu " Inna tafaɗa cikin faɗa , cikin sanyin jiki Zahra tatashi daga gaban Inna.... Wanke Wanke tafarayi sannan tayi sharan tsakar gida dana ɗaki,, saikuma hurawa Innar wuta, koda takammala aikin nata har 9 tayi, sam bataso ace yau tayi latti ba domin kuwa suna da lecture 8:00am, shikenan yauma lecture'n Sir Adam yasake wuceta kamar dai yanda yawuce ta wancan satin..... hijab ɗinta mai launin ruwan ƙasa tasanya, haɗe da saɓa jakarta a ƙafaɗanta, fitowa tayi tasamu Inna nazaune, bakin murhu tana ɗumamen tuwo, "Inna nizan wuce makaranta " Zahra tafaɗa,, "To uwar ƴan boko saikin dawo, aikin kenan bacas ba as saidai zuwa makaranta, da Mijin aure kika fito dashi, kikayi aure aida nahuta da wannan wahalar taki " Inna tafaɗa cike da bala'i.. Itadai Zahra batasake ce da'ita ƙalaba, tasakai tafice daga cikin gidan, tana fitowa ƙofar gida, zazzafan hawaye suka gangaro daga cikin idanunta, dasauri tasanya hanu tashare hawayenta, kana tacigaba da tafiyarta.........



((Wanene Zaid ? Wacece Zahra ? saigaba zakuji kosu ɗin suwayene, Wace alaƙace ke tsakanin Zaid da Zee ? mata da mijine kokuwa, iskancinsu kawai suke ? kubiyoni don sanin gaskiar al'amari... ))


*11/October/2019*



*MRS SARDAUNA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SHU'UMIN NAMIJI !!*


*Written by*
phatymasardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*


*Dedicated To My Lovely Brother Khabeer*


*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

*WATTPAD*
@fatymasardauna


*Editing is not allowed 📵*

*Chapter 3*



(sorry a chapter 2 nayi mistake nasa guest house ɗin Zaid na G.R.A, to ba G.R.A zansaba mistake ne, guest house ɗin Zaid na Maitama ne ba G.R.A )


Har takawo bakin titi bata samu abun hawa ba, gashi yau antashi da wani irin zafin rana, duk da cewa taran safe ne amma hakan baihana ranan bayyana zafin taba, tsaye tayi abakin titi tanamai ƙaremawa motoci da mashunan dake wucewa akan titin kallo, har izuwa yanzu mai adaidaita sahu ko ɗaya baizo yagil ma akan titin ba, takusan minti 12 tsaye a wajen kafun tasamu wani mai adaidai ta yaɗauke ta, kaitsaye babban jami'an da take karatu suka nufa.... Kamar koda yaushe abakin titi tace mai adaidaita ya sauƙeta domin dokace ba a shiga jami'an da motar haya, saidai idan motar kanka kokuma machine, nanma saidai in mallakin mutum ne... Ɗalibai ne iri da kala ke gudanar da harkokinsu acikin makaranta, wasu na hira da samari wasu kuwa na karatu, kamar dai yanda kukasan ƴan jami'a keyi,, kaitsaye tanufi gindin wata ƙatuwar bishiya wanda anan ƴan course ɗinsu ke tare, da'alama dai fitowarsu kenan daga lecture.... Da sallama ɗauke a bakinta taƙarasa garesu, bako wanne daga cikinsu bane suka amsa sallaman nata ba sai ƴan tsiraru, wasu ko da kallon banza suka rakata,, musamman ma ƴan matan dake wajen, koka ɗan hakan bai dameta ba domin dai hakan ba sabon abu bane a wajenta, musamman ma idan tayi la'akari cewa ita da su ɗin akwai banbanci, domin dukansu ƴaƴan manya ne itakuwa ƴar talaka ce futuk, shiyasa ma koda wasa bata yunƙurin haɗa kanta dasu,, zama tayi a gefen Aminiyarta Husna... " Yauma saida kikasakeyin missing lecture, anya kuwa Zahrah wanan exam ɗin da zamuyi baza'a samu matsala ba ?" Husnah tayi maganar fuskarta ɗauke da damuwa,,

ajiyar zuciya Zarah ta sauƙe, haɗe da cewa " Bansan yazan yi ba Husnah wallahi dole ce take sawa nayi latti gashi unguwarmu a kwai ƙarancin abun hawa " Zahrah ta ƙare maganar daidai lokacin da take ciro wani hand out a jakanta, "shikenan mukoma gefe saina koyar dake abun dana gane, domin ni wallahi lecture ɗin Mr Adam sam bana ganesa " Husnah tafaɗa tana mai yunƙurin miƙewa tsaye.... Duk da cewa tazo latti amma tafahimci darasin da Husnah takoyar da'ita, tamkar ma tananan akayi.......

Basu suka kammala lectures ɗin dasuke da shiba harsai 5 pm, a gajiye take liƙis uwa uba ga yunwa dake ƙwaƙulan cikinta, rabonta da abinci tun 10 am nan ma Husnah ce tasaya musu snacks da drinks a Cafeteria, ɓatare da ta tsaya wani abu ba tashiga Adai dai ta sahu tayi yo gida...


*MAITAMA*

Zaid da Zee kuwa ayar su suka sheƙe sosai, domin Zee har kuka saida tayi mawa Zaid, wanda hakan kuma ba baƙon al'amari bane wajensa, domin sau da dama idan yayi sex da Zee tofa saitayi masa kuka, na azaba ko na daɗi wannan ne kuma baisani ba,, tsaye yake agaban dressing mirror dagashi sai towel ɗaure a ƙugunsa, hankalinsa gaba ɗaya yana kan busar da gashinsa da yakeyi da hand dryer, Zee dake kwance akan makeken gadon ɗakin shame shame, kuwa ƙura masa idanu tayi, itakam Allah yasani, Zaid yana matuƙar burgeta, tanajin son gayen har cikin zuciyarta, saidai tasan cewa ko sama da ƙasa zasu haɗe, Zaid bazaitaɓa auren ta ba, saidai tana godemawa Allah ahakan ma daya bata daman raɓansa, domin raɓan Zaid ma sai mai sa'a, kuma sai macen da ta amsa sunanta mace ƴar gayu da aji....

Tsab yagama shiryawa haɗe dayi mawa kansa feshin turare mai daɗin ƙamshi,, Car key ɗinsa ya ɗauka haɗe da wayarsa, hanu yasa acikin aljihun wandonsa, kuɗi ya ciro bandir ɗin ƴan dubu dubu, ya cillamawa Zee akan cinyarta, batare da ya kalleta ba yace " Kada ki tafi sai kin kimtsamin gado na " yanakaiwa nan azancensa, yasakai yafice daga cikin ɗakin bakinsa ɗauke da fito,,, a maimakon Zee taji haushin yanda yamata, saima murmushin da tayi haɗe da lumshe munafukan idanunta, afili ta furta cewa "Allah kamallakamin Zaid amatsayin mijina".....


Tundaga Zauren gidan nasu ta ke jiyo tashin muryan Inna dana Baffa da'alama dai sana'artasu ta kullum sukeyi wato faɗa,, shahada kawai tayi tadoshi cikin gidan, domin dai tasan tana shiga tofa kanta faɗan zai dawo... Aikuwa a rubuce yake tana sawo kai cikin gidan, Inna ta ce "Kekuma uwar gantali saiyanzu aka tashi daga makarantar ?" cike da ladabi Zahrah ta rusuna haɗe da cewa " Baffa ina wuni "...."Daban wuni ba zaki ganni ? nace daban wuni ba zaki ganni ?? Baffa yakuma faɗa cikin tsawa, kai kawai zarah ta girgiza haɗe da nufar ɗakinta,, kwanciya tayi luf akan ƴar katifanta, zuciyarta cike da tunanin halin rayuwa dakuma yau da kullum....


Koda Zaid yabaro guest house ɗinsa bai zarce ko'ina ba sai wani babban Club ɗin dake cikin garin abuja, makeken Club ne mai kyau da tsaruwar gaske, irin Club ɗin nan ne daba kowa ke zuwanshi ba sai wane da kuma ɗan wane, Club ne na manyan guys, da kuma manyan ƴan mata, kamar ƴaƴan shugaban ƙasa da sauransu, amma idan dai har kai ba wani bane kuma ubanka ba kowa bane to fa baka isa shiga wannan haɗɗɗen Club ɗin ba, Zaid kuw yamaida wannan Club ɗin kamar ɗakin baccinsa, domin kuwa zaiyi wuya ace ya kwana ɗaya baijeba...
Zama yayi akan ɗaya daga cikin kujerun da aka ƙawata tsakiyar Club ɗin dasu, yana zama wata ma aikaciyar Club ɗin tanufu inda yake hanunta ɗauke da tire na glass wanda samansa ke ɗauke da glass cup guda biyu, da kuma zungureren tsadaddiyar kwalban giya, kasancewa duk wani ma'aikaci dake cikin hotel ɗin yasan, abun da Zaid ɗin ke sha idan yazo wajen... Duk yanda ma aikaciyar Club ɗin nan ke kwarkwasa Zaid baiko ɗaga idanunsa ya kalleta ba, domin shi baimaga macen dazai kula ba kaf cikin Club ɗin, balle kuma ita banza mai aiki.... Cike da nutsawa Zaid yakafa kansa ya kwankwaɗi giya son ransa, saida yayi tatul tukun yabar cikin club ɗin, bayan yayi waya da Asmee ƴar wani minister dake cikin Naija, cewa tazo ta samesa a guest house ɗinsa......

*WAYE ZAID ?*


Zaid tantirin Mazinaci ne kuma ɗan giya, uwa uba baida mutumci ko ƙaɗan, sannan kuma komai kayi masa baka burgesa, Zaid yana da Munanan halayya, Zina shine babban ciwon daya riga yayi mawa jiki da zuciyarsa ƙawanya, Zaid Mazinaci ne na ƙarshe, iskancin sa yake zubawa babu mai hanasa, domin dai iyayensa sunriga da sungama shagwaɓasa, bayajin maganan uban kowa, duk wata haɗɗɗiyar mace wayayya dake cikin garin Abuja babu wacce batasan Zaid ba, domin iskancinsa ya shahara yayi ƙarfi, kasan cewarsa kyakkyawan saurayi mai wanka da naira, yasanya wasu ƴan mata ke matuƙar ƙaunarsa, sannan kuma suke burin mallakansa, amma saidai sama yayiwa yaro nisa babban ma saidai kallo....




*MRS SARDAUNA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SHU'UMIN NAMIJI !!*


*Written by*
phatymasardauna
*🎈Mrs Sardauna🎈*


*Dedicated To My Lovely Brother Khabeer*


*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*

*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

*WATTPAD*
@fatymasardauna


*Editing is not allowed 📵*

*Chapter 4*



*Alhaji Ma'aruf Chanji* shine sunan maihafin Zaid, Babban mutum ne da ake da mawa dashi acikin Nigeria, yana da kuɗi sosai, sannan mutum ne mai kyautatawa na ƙasa dashi, bashi da rowa ko kaɗan, matarsa ɗaya *Hajiya Safara'u* kuma itace ma haifiyar Zaid, daga Alhaji Ma'aruf har Hajiya Safara'u shuwa arab ne, Allah yayi musu baiwar kyau ga dukiya, shekaransu biyu da Aure Allah ya azurtasu, da haihuwan ɗa Namiji, wato Zaid, Zaid dai kyakkyawan gaske ne, domin tsananin kyawunsa ke sawa yake shiga ran jama'a, Zaid tun yana ƙarami yataso da wani irin Shu'umanci, ga mugunta, haka zalika baruwansa da shiga harkan kowa, hatta iyayensa kuwa, gaisuwa kawai keshiga tsakaninsu, duk yanda suka so yasake dasu amatsayinsu na mahaifansa, amma abun yaci tura, Sosai Iyayen Zaid ke nuna masa tsananin ƙauna, da tattali, asalin sana'ar Alhaji Ma'aruf shine Chanjin kuɗaɗe, yayi ƙaurin suna a sana'ar, sannan kuma yatara maƙudan kuɗaɗe, ganin harkan nasa natayin gaba dukiyarsa na ƙara yawa, yasanyashi tattarawa yakoma America da zama, can ya cigaba da business ɗinsa, duk ko yanda yaso Hajiya Safara'u tabiyo sa America suzauna ƙiyawa tayi, saidai Zaid yayarda yabi mahaifinsa, inda a can yasoma karatun sa,, Zaid yanada shekaru goma a duniya mahaifiyarsa ta haifa masa ƙanwa maisuna Labisat, Labisat dai kyakkyawar yarinyace suna kama da Zaid, saidai a gaskia Zaid yafita

Please Login or Register in order to submit comment