Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata tunani, ta kalleta cikin takaici tana janye hannunta.
A zatonta zataga nadama a idanun Shahudah akan abinda sukaso aikatawa, amma sai taga saɓanin hakan.
Cikin dariya Shahudah tace, “Wai wannan faɗan nasa kikema kuka? Tab amma baki da wayo, mutumin da a gabanki ya komamin ƙaramin yaro shine mazuransa yanzu zasu ɗaga hankalinki, wlhy naso ya biyemin kiga abin dariya, ashe shegen idonsa ya hangoki, ni........”
A harzuƙe Amrah ta ɗagama Shahudah hannu, “Ya isheki haka malama, ni wlhy bamma san bakida wayoba sai yanzu dana dawo cikin hankalina, bansan miya lulluɓe ganina ba har na iya yarda naga abinda zan shekara dubu ina nadama, Shahudah wannan ba wayewa baceba, dan ALLAH ki dawo akan ƙyaƙyƙyawan tunani na mutanen ƙwarai masu riƙo da addinin ALLAH, yanzu dan kawaifa ki birgeni kika jawoni nazo na laɓe dan naga yanda kike maida Yaya Jawaad kamar ba shiba a shinfiɗa, sirrinku, innalillahi, na shiga uku ni Amrah, wlhy naso tafka kuskure kam yau a rayuwata” da gudu Amrah ta fice daga falon tana kuka.
Shahudah da jikinta yaso yin sanyi, amma zuciyarta dake ɗorata a shawarar banza tai saurin bijiro mata shaiɗaniyar shawarar da take bata sai tayi dariya tana taɓe baki, a fili tace, “Sun wani damu mutane da maganar sirri-sirri, uwarmiye sirri anan? Waima shegiyarnan Amrah da BF yafi talatin a cikin wayartace take faɗar kallonmu ni da Bb zaisata na dama, Mtsoooww aikin banza kawai, ni wlhy dama nayi mamakin yanda ya biyemin cikin sauƙi, mutumin da idan ina bukatarsa sai ya gama yanƙwalani kafin ya bani haɗin kai, amma ɗazun dandanan sai gashi ya miƙa wuya kamar yau ya taɓa sanina, munafiki kawai”.
Ta ƙare maganar da juyawa ta koma ɗakinta.



...................................................


Dukkan abinda ya faru tsakanin su da Jawaad sai da suka sanarma Hajiya Humaira mahaifiyar Shahudah, ba karamin tashin hankaline ya risketa ba jin wai Jawaad ma ya bama Shahudah goyon bayan ta zubar da ciki.
To mi kenan? Mi yake nufi? Bayason ya haihu da ita ko kuwa haihuwarce gaba ɗaya baya so?.
Basu da mai basu amsa, shiyyasa suka shiga dogon tunani wajen tattaunawa da juna, harma suna tunanin ko dai Jawaad raina musu wayo kawai yakeyi, anya kuwa baisan wani abuba game da shirinsu akan sa?.
Gashi ALLAH ya basu lusarar ɗiya da bata fuskantar komai na rayuwa sai wawanci, dolene susan abinyi akan Shahudah kafin ta aikata zubar da cikin nan, su kuma sake taku akan murɗaɗɗen halin Jawaad da duk bin ƙwankwantonka baka isa gane inda ya dosa ba kai tsaye.


.................................................

Bayan an idar da salla ne Jawaad ya shigo gidan, kai tsaye ɗakinsa ya nufa, shirin fita yayi, bai wani jimaba ya fito riƙe da takardu guda biyu a hannunsa.
Ɗakin Shahudah ya shiga da sallama a ƙansan maƙoshi, bata amsaba, dan dama can ita bama damunta sallamar tayiba, idan kuma anyi mata bai zamar mata tilas ta amsa ba.
Tana tsaye cikin ƙananun kaya sket da riga masu ƙyau, yanda sket ɗin yake har ƙasa ne ya tabbatar masa da shirin fita takeyi, dan sam Shahudah batajin kunyar fita anguwa daduk suturar data tare gabanta, indai ka cire waɗanda tasan sunyi ƙananu da yawa, amma ita dan ta saka wando da riga ma ta yana ƙaramin gyale wannan ba damuwarta bane, a ganinta ai tayi shigar mutuntawa ma.
Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta, dan haushin abinda yay mata gaban Amrah ya sata jin haushinsa.
Shima halin ko in kula ya nuna a kanta, ya ajiye takardun hannunsa saman tebirin gaban gadon tare da biro a tsakkiyarsu.
Dukda ta gani sai bata kula saba, jakkarta ta rataya a kafaɗa fuska a ɗaure tace, “Ina kuɗin zanje wajen Doctor, dan wannan cikin yau bazai kwana a jikina ba”.
Bakinsa ya taɓe yana mata wani kallon banza, yay taku biyu gira ɗaya a ɗage yana jan tsakin da ya shigar mata har ƙasan zuciya.
“A tunaninki nima wawane irinki? a haukarki na yarda a zubda cikin ne da gaske? To lallai har yanzu ke bagidajiyace inhar maganata a gabansu zaisa ki aminta da ni har haka, Hudah! gane ainahin Jawaad abune mai matuƙar wahala ga kowa, ko ke da kikai kusanci dani na kusan watanni takwas baki iya fara nazartar komai game daniba balle su, hhhh tunanin Jawaad kullum banbanta yake da na kowa, wannan takardun biyu, ɗaya ta cak ɗin kuɗi ce, ɗaya kuma babu komai cikinta tana jiran abincine. Idan har kina kan bakanki na zubarmin da ciki bazan hanaki ba, ki faɗi adadin kuɗinma da kike buƙata zan rubuta miki kije ki zubar, ammafa zaki zubar da shine bada igiyar aurena a kanki ba, idan kuma kin shirya barinsa ki haifa kinada lasisin cigaba da rayuwar aurene da Muhammad Jawad Abdul-Aziz yusif kenan. zaɓi ya rage naki, kafin na dawo sai naji bayani akai”.
Yana gama faɗa yay ficewarsa ya barta tsaye tamkar wata gunki........


_________________________
BILKEESU
_________________________


............Hanunta da ya sauka jikinane ya saka duhu mamaye ganina.

Yanda Bilkisu taja wani nannauyan numfashi lokaci ɗayane ya saka Uwargida dake a fusace kallonta, hannunta ta janye da ga ƙirjin bilkisun tana maidawa saman fuskarta, sam bata numfashi.
Uwargida taja tsaki tana sauka a gadon, ruwa mai sanyi sosai ta ciro a ƙaramin firij ɗin dake ɗakin ta ɓalle murfin ta watsama Bilkisu.
Nannauyan numfashi Bilkisu tayi.

Na buɗe idanuna da ƙyar bayan fitar numfashi na daya fara nisa daga gangar jikina, akan Uwargida dake gabana tsirara na saukesu, nai saurin maidawa na rufe jikina na wani azabar rawa, jin motsin zata sake dawowa kaina ya sani tashi cikin azama ina matse jikina da kare ƙirjina da ta yaga rigar ya fita fili.
Cikin muryarta mai razanarwa tace, “Wacece ke? Waya turoki cikinmu?”.
“Wlhy babu wanda ya turoni gareku sai ƙaddadarar rayuwa, dan ALLAH kirufamin asiri ki barni na tafi, wlhy bana buƙatar aikata wannan abun a rayuwata, na miki alƙawarin har duniya ta tashi babu maijin sirrinku a bakina hajiya”.
Wata dariya ta saki tana matsowa jikina, murya ƙasa-ƙasa tamkar mai raɗa take min magana, “Ƴammata waya gaya miki muna tsoron sirrinmu ya fitane? Hakan ba matsalarmu bane, kisa a ranki kamar yadda ƙaddara ta kawoki cikinmu itace zata wajabta miki zama damu, kina da sura mai ƙyau da zaki mori lokacinki, matana biyar dana aura, nakumayi alƙawarin daga su bazan sake auren kowaba, sai dai ɗanɗano, amma ganinki yasa naji alƙawarina bazaiyi tasiriba, dan tun jiya dana ganki kika kwantamin a rai, da tsantsar kwaɗayinki na kwana a daren jiya, ki kwantar da hankalinki zan jiyar dake daɗi, tare da mallaka miki dukiya mai tsoka da saikin wucema tsaranki. Sonki da nake na gaskiya zai hanani yimiki fyaɗe, duk da kuwa kin ɓatamin rai da maganganun da kike faɗama yarana, da watace bakeba yau ta aikata hakan wlhy saina kasheta, amma ke bazanyi hakanba, bakuma zanyi mu'amula dake ta ƙarfiba, zan biki a hankali harki saki jikinki dani kema ki soni, dan haka daga yanzu kin dawo zama sashena”.
Rumtse idanuna nayi da ƙarfi hawaye masu zafi dana tara a cikinsu suna rige-rigen fitowa, ta janye jikinta daga gareni tana sauka, riga mai igiya naga ta ɗauka ta sakama jikinta, ta buɗe ɗakin ta fita tana faɗin, “Ki buɗe drawer ɗinnan duk nau'in kayan da kike buƙata zaki samu a ciki, karna dawo na sameki kina wannan kukan, dan na tsani kuka, sunana Uwargidan farin ciki, burina kullum na saka duk wanda ya raɓeni farin ciki kawai”.
Harta gama ɓaɓatun ta ta fice ban kalletaba, na kwashi kusan mintuna goma ina kukan nawa tare da sambatun yanda kullum duniyata ke garawa da sabon salo mai saka ruɗani, maimakon haske kullum duhu nake sake gani, maimakon fahimta kullum toshewar basira nake sake gamo dashi, maimakon canji kullum tsanani nake sake gamo dashi, maimakon cigaba kullum ci bayane yake zoma rayuwata, shin haka rayuwata zata ƙare kenan?. Na sake fashewa da wani irin kuka mai cin zuciya, jinake tamkar nama kashe kaina kozan huta ne.

Ban sake ganinta ba, dan bata sake shigowa ɗakinba, ni kaɗai na wuni a cikinsa, nayi yunƙurin fita amma naji an kulleni ta baya, sai wajen ƙarfe biyu wani saurayi ya kawo min abinci, ni bamma taɓa ganinsa a gidanba, baimin magana ba ban masaba, ya ajiye ya juya ya fita abinsa, inaji ya sake kulleni ta bayan.
Ko kallon inda abincin yake banyiba, danni yanzu komai na gidan ƙyankyaminsa nakeyi wlhy, tunda nasan kuɗin siyen komai ta hanyar wannan ƙazantar suka sameta.
Gadonma tuni na sakko na dawo ƙasa na zauna, amma sanyin tayis dake shigata yasa na kasa jurewa na miƙe na koma saman gadon na zauna.
Yunwa da ƙishirwa duk sun gallaba mini, rabona da abinci tun jiya da safe da su ƴar daɓas suka takurani naci indomie ɗinsu.
Babu abinda ke tadani zaune sai salloli, har zuwa dare kuma ban sake jin motsin kowa ba a gidan, sai bayan isha'i saurayin ya kuma kawo min abincin dare, ya ɗauki kwanikan rana zai fita dasu sai yajisu da nauyi alamar banci abincinba.
Ya ɗan kalleni da mamaki, kamar zaiyi magana sai kuma naga ya share, ya ɗiba kwanikan ya fita abunsa..
Na darenma da ya kawo ƙin ci nayi, haka na kwanta abina da yunwa, dan harna fara sallar dare rashin ƙarfin jiki ya sani komawa na kwanta, dan nakasa tsaiwar, na komayi a zaune shina saina fara ganin jiri, dole dai na haƙura gaba ɗaya na zube a tsakar ɗakin barci yay awan gaba dani badan na shirya ba.

Da asuba dana farka da ƙyar na iya gabatar da sallar asubahi, ina zaune ina addu'a Uwargida ta shigo.
Batace dani komaiba ta wuce ciki, a gabana babu kunya ta cire kayanta ta ɗaura tawul ta nufi ban ɗaki.
Bani da damar fita a ɗakin tunda a kulle yake, hakan yasa na maida kallona ta inda bazan gantaba koda ta fito.
Ta jima a cikin bayin kafin ta fito, “Babyna kin tashi lafiya” ta faɗa cikin salon yaudara.
Ba ƙaramin ɗacine ya mamaye zuciyata ba, hakan yasa nai banza da ita ban amsaba.
A mamakina sai naji tayi murmushi mai sauti, tace, “Karki bar wata ƙofa da zatasaka raina fara zafi a kanki kinji, ina sonkine shiyyasa kike samun sauƙi da ga wajena”.
Daga wannan maganar bata sake tankaminba, tai shirinta cikin shiga ta alfarma tanata zabga kamshi, sai kace ba itace shugabar sheɗanun nanba.
Gaban kwanikan abincin jiya taje ta buɗa, ganin banciba ne ya sata faɗin, “Kai-kai wai bayan ƙuntata kanki harma horon yunwa kikema Kanki? Rufamin asiri kar wannan ƙyaƙyƙyawan jikin dana ɗorama buri ya lalace matata”.
Babu shiri na juya na kalleta da tsagwaron mamaki akan fuskata, wannan matar lallai zuciyarta ta rigada ta gama bushewa, idanuna da sukai nauyi kawai naɗan lumshe na maida kaina na jingina da gadon.
Ƙamshin turarenta da ya yawaita a hancina da motsinta ya sani tabbatar da tana a kusa dani, hakan yasa naƙi buɗe ido, ta kama hannuna tana murzawa cikin wani salo na shaiɗanci.
“Haba gimbiyar mata, kiyi haƙuri haka nan, dan bazaki taɓa kuɓuta daga gareniba, na rufe dukkan ƙofofin da hakan zata iya faruwa ma, ki cire komai a ranki ki bada kai bori ya hau kinji, idanma tsoron shiga wuta kikeyi ai kafin tsufa yazo mana zamu bari ko”.
A hankali na buɗe idanuna saboda jin furucinta na ƙarshe, ba tare da na shiryaba na sakar mata murmushi ina kaɗa kaina a hankali, banso mata magana ba tsawon zaman da zanyi da ita, amma a wannan gaɓar sai na kasa jurewa hakan, “Hajiya waya faɗa miki anama ALLAH wayone? Wakuma ya baki albishir saikin tsufa zaki mutu?”.
Hannuna ta saki da sauri tana ƴar dariya ta mike, “Humm Ustazu sauri nake, ajiye waɗannan tambayoyin naki kinji, ki daure kici abinci zanje anguwa na dawo, dan gobe ne za'a mana baiko ni da ke, sai kuma a tsaida ranar da za'a ɗaura mana aure”.
Da kallo kawai na iya binta harta fice, inaji ta sake kulleni.
Sam na nema hawaye na rasa a idanuna, kuma ko kukan zuci ma na kasa yi, ina nan zaune niba mai tunaniba ba kuma gunkiba har hasken rana ya buɗe sosai, saurayin dake kawomin abinci ya shigo ɗauke da ture a hannunsa, yanzunma baimin magana ba ya ajiye tiren ya ɗauki abincin daren jiya ya fice abinsa.
Nima kala bance masaba, dan maganar da Uwargida ta ambatamin akan baikon nan ta toshe dukkan tunanina, ni Bilkisu mace ƴar uwata take dangatani da aurenta?.
“Hummm” na faɗa a fili ina maida kaina na kwantar a jikin gadon, yanda cikina ke murɗawar yunwa ya sani jin ya kamata naci abincin koda kaɗanne.
Tiren da saurayin ya ajiye na jawo gabana, na buɗe kular farko farfesune na naman kai, sai ɗayar kuma soyayyar doya da ƙwai, sai ruwan shayi a ƙaramin filas, an zuba kayan shayin cikin kofi da aka ɗoro a tiren.
Takarda mai rubutu da aka shinfiɗa akan tire ɗince taja hankalina.
Na ja kular da aka ɗora ta lulluɓe kusan rabinta gefe.

*ALLAH YASA KIN IYA KARATU?*
*_Kar kiyi abinda wani zai fahimta akan takardarnan, dan ɗakinnan akwai cctv a ciki_*

Abinda na fara cin karo da shi kenan a rubuce, hakanne ya sakani nutsuwa, naci gaba da ƙoƙarin haɗa shayi a kofin ina bin sauran rubutun ƙasan ina karantawa.

*_Na miki alƙawarin zan taimakeki, saboda baki dace da zama a wannan gidanba, Uwargida mahaifiya tace, inason ki saki jikinki da ita, duk abincin dana kawo miki kicisa dan wlhy bazan cutar da keba, insha ALLAHU gobe idan munkai da rai zan kuɓutar dake a wajen bikin baikon sheɗancin data ambata miki, dan inhar zaki cigaba da ƙuntata kanki bazata bari ki fito a ɗakin nanba, in kuma har kina a ciki bazaki samu damar barin gidan nanba, sakin jikin da zakiyi kamar kin amincewa buƙatartane kawai zai taimaka mana._*

Bansan wani nannauyan numfashi ya suɓuce mani ba, na share hawayen da suka kwaranyomin, cikin sauri na zuba abinci naci kamar yanda ya shawarceni, nakuma tashi na shiga wanka, dirowan tata na buɗe na ɗauki doguwar riga baƙa na saka.
Ina nan zaune kusan sha biyu da rabi saurayin yazo ɗauke da wani abincin, nayi mamaki, dan ba'a irin wannan lokacin yake zuwa ba, sai dai zuciyata ta bani yanason fitar da rubutun da yayo minne, tattare kwanikan safen yayi, cikin wani dabara yaymin magana da idanu dake tabbatar min da abinda ya rubuto.
Yanzunma daya fita dai sake rufeni yayi, banci abincinba har saida nai sallar zuhur.
Zuwa yanzu naɗanji ƙarfin jikina, na gama babu jimawa Uwargida ta shigo, sosai mamaki na karanto a fuskarta gani na ba'a yanda ta barni ba.
Ta dire jakar hannunta tana faɗin, “Babie kece kuwa?”.
Cikin danne ɗacin da nakeji na kalleta da murmushi a fuskata, “Nice hajiya, bayan fitarki nayi nazari akan maganarki, sai naga ma to idan na matsawa kaina barinku ina zanje?, na amince da bukatarki kawai”.
Shiru Uwargida tayi kamar bata amince da magana ta ba, sai naga ta nufi wata ƙofa, ashe nan ma ɗakine, kusan mintunanta goma da shiga ta fito, babu tsammani naji ta rungumeni tana murna sosai.

★★★★★

Tun daga haka sai Uwargida taita nan nan dani kamar zata maidani ciki, tanayin wanka taja hannuna muka fito falon, falon nan ya haɗu, haɗuwar da idan na zauna misaltashi ma ɓata lokacine.
Zuwa dare na sake gaskata maganar saurayin, dan kuwa ta gama amincewa dani, harda zaunawa tana ƙara bani sirrikan arziki dake cikin harkar tasu, ni dai jinta kawai nake ina sake neman tsarin ALLAH da sharrinta a zuciyata..............✍🏻




https://youtu.be/5xN4SGMIzME

Garzaya ka saurari littafin *SAUYIN ƘADDARA*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*_ALƘALAMI TV_* ta shigo gari, tasha mai ɗunbin abubuwan ilmi, akwai littatafai na soyhayya da zasu dinga zuwa muku bisa tsaftataccen karatu, sai kuma gudunmawar hanyoyin da amarya da uwar gida zasu gyara jikinsu hankali kwance daga cikin gida basai wata taci ko sisinki ba.

Shin duk wannan gara ɓasar ka yarda ayita babu kai?🙆🏻🤔.

Maza garzaya ALƘALAMI TV dake dandalin manhajar youtobe kajiyo abubuwan bukatarka a sauƙaƙe.

Na zaune baiga gariba masoyanmu🤤🤤😋⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀

A danna mana subscribing domin tabbatar da ƙaunarmu😍😍❤❤🥰🥰😘😻😻👌🏻


*_ZAFAFA BIYAR_*🔥🔥🔥
*(SABON TAKU)*

*_NESA TAZO KUSA_*

*_KEWA TA QARE_*


*'YAN BIYAR DINKU NE SUKA SAKE DAWOWA DA KANSU BA AIKE BA*


*_Abishir a gareku makaranta litattafan hausa,ga 'yan biyar dinku sai sake tasowa da k'arfinsu d'auke da wasu ZAFAFAN LABARAn nasu har guda biyar rigis kamar wancan karon_*

*_idan kin taba kasancewa cikin tafiyar zafafa wancan karon basai an gaya miki ba,kinsan yadda tafiyar ta kasance_*

*Zakin Nadiya*

*Khaliphan Aysha*

*Amaan* *Ummukulsoom*

*Arkel / Maryam*

*Shamsu / Aliya*


*wannan karon kuma da wanne salo suka zo muku?,lallai akwai zazzafan kafce fiye dana baya cikin labaran da wadan nan zafafan marubuta zasu zo muku dasu,sunayen littafan nasu sune*



*Mamuhgee*
❤️ _QAUNARMU_

*miss xoxo*
♾️ _IGIYAR ZATO_

*Hafsat rano*
🖤 _DAURIN GORO_

*Billyn abdul*
🏃🏾‍♀️ _GUDU DA WAIWAIYE_

*huguma*
🤞🏾 _ALKAWARIN ALLAH_



*Ga mai buqatar kasancewa cikin tafiyar tamu,zai biya naira 500 ga dukka litattafan biyar,mai buqatar biyu zai biya 300,mai buqatar uku zai biya 400,mai buqatar hudu zai biya 450*





*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*



*Munyi kun gani,hausawa sukance wai sai an gwada akan san na qwarai,idan bakisan dad'in tafiyar ba tambayi wadanda aka tab'a damawa dasu*🤞🏾🤞🏾🤞🏾🤞🏾


*_Mallaki naki kici gashin kanki,da'a baki labari gwara ki bayar_* 🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻*_Typing📲_*




*_🧺ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!🧺_*


*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_Wattpad:-_* _BilynAbdull😉_


*______________________________________*
*_BOOK ONE_*
_Shafi na goma sha biyar_
*______________________________________*


...........Washe gari ma dai naga gata wajen Uwargida, yanda na saki jikina da ita sai itama ta sake yarda dani ɗari bisa ɗari, dan har barina tai naje wajensu ƴar daɓas.
Yanda suketa sinne kai basason mu haɗa ido sai suka bani mamaki, amma sai ban nunaba, dan na lura kunyata sukeji.
Nima dai a kunyacen nake dasu, amma sai na dake tamkar baniba, nanko ƙasan zuciyata a matuƙar tsorace nake da kowa na gidan, nakan danne zuciyata bana kukan zahiri sai na zuci, tunanin iyayena dasu Firdausi yana sake gallabar zuciyata.
Tun a yammacin ranar naga anata shigowa da drinks da wasu kayayyaki a kwalaye, tsoro ya sake kamani, danfa tabbas da gaske wannan sheɗaniyar takeyi, cigaba nai da neman tsarin ALLAH da sharrin kowannensu a zuciyata.


★★★★★★

Washe gari aka tashi da shirin baiko kamar yanda Uwargida ta faɗa, tun da rana manyan hajiyoyi suka fara isowa gidan, abin idan ka gani zat tashin hankali, sam banyi tunanin wannan ƙazantar tayi girma da yaɗuwar haka a cikin al'ummar musulmai jinin hausa fulani ba, wanda ma baka taɓa zato ko tsammani ba saika ganshi a wajen.
Yara ƙanana ƴammata duk an tsundumasu wannan ƙazamar harka, mafi yawansu kuma saboda abin duniyane, gashi idan kana sauraren hirarrakinsu zaka fahimci sanadin waya suka haɗe da hajiyoyin a yanar gizo, bansan hawaye sun fara wanken fuskaba, sai da naji ɗigarsu akan hannuna, nai saurin gogewa ina haɗiyar rai.
Kowa ya ganni sai ya yabama ƙoƙarin Hajiya, suna kurantata wai ta more, dan inada karuwan jiki, dukda ba wata ƙyaƙyƙyawa bace a fuska kuwa.
Wasu mata kuwa su biyu sai hararata suke, ni ban saniba ashe wai matan hajiyarne, waisu nan kishina sukeyi.
Kai jama'a, ALLAH kai mana tsari da asararriyar rayuwa dai.

Anmin wankin kai saikace wata amaryar data samu miji, sannan aka kawo mai kwalliyar da zatamin, bansan yanda zan musalta muku ɗunbin tashin hankalin da nake cikiba a wannan lokaci har aka gama kwalliyar.
Duk wannan shiri da akeyi bikin zai gudana ne bayan sallar isha'i, amma abinda zai baka tsoro babu wanda naga yayi salla a cikinsu koma ambatarta a bakunansu.
An kawomin wata riga mai ƙyau da zan saka, harda takalma da sarƙa da nake zaton ta gwal ce, dan ƙyawunta a ido kawai ya isa ka shaida hakan.
Dakatar dasu nayi akan inason sai nayi sallar isha'i, da mamaki kuwa sai naga abun ya basu dariya, ni dai ban kulasu ba naje nai sallata, bayan na idarne na duba takardar da saurayinnan ya bani ɗazun da rana a ɓoye, bayanin danaga yayi a ciki ne ya sakani miƙewa da sauri, kaya na buɗe drawer ɗin Uwargida na ɗauka, na saka tare da gyara jikina tamkar ba niba, a yanda na fito inba sani kaimin na tsiyaba bazaka taɓa gane niceba, balle dama tunda akaimin kwalliyar babu wanda ya ganni a cikinsu har Uwargida.
Cikin taimakon ALLAH na fito falon cikinsu ina taku da yauƙi, na saki jikina tamkar nima irinsu ce, duk da na fahimci wasu suna min kallon rashin sani, amma harkar ta wayewace sai kowa ya amsheni ba tare da bincikeba.
Uwargida ta miƙe akan zataje ta fito dani, hakan yasa wasu manyan mata suka bita ɗakin, suna shiga watar gidan na ɗaukewa baki ɗaya.
Jikina har rawa yake na ajiye takalma da jakka tare da sarƙar danasa ta gwal ta uwar gida na fito da lalube, dan dama a hanyar ƙofar fita na zauna kamar yanda saurayin ya shawarceni.
Ina fitowa kuwa ana kama hannuna, cikin raɗa yace, “Karki damu nine”.


1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

11 months ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment