Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da sumbatar goshinta da laɓɓanta da sukai jazur sosai saboda wahalar da sukasha a hannunsa. ‘Yanda take mai sanyi haka komanta yake mai sanyi’ ya ayyana a ransa yana rungumeta tsam cikin jikinsa har saida ta motsa sannan ya sassauta mata. A haka shima barci ɓarawo yay awon gaba dashi.

★★★★★★

          DARE MAIBAN MAMAKI.

        Dolene mutane masu yawan gaske su kira wannan dare  da sunan dare maiban mamaki da ruɗani tare da tashin hankali ga wasuma maybe. Dan kuwa lokacin da Jawaad ke angwancewa a lokacin wasu cikin matsanancin ruɗani suke, dan duk wani azzalumi dake da alaƙa da wani ɓoyayyan sirri daya shafi waɗanan ma'aurata da hikimar UBANGIJI ta dunƙule waje guda wannan shine mafarkin da suka tsinci kansu a ciki a wannan dare.
       (Ƙudirar UBANGIJI ta tabbata, rahamarsa ta yalwata, izzar mulkinsa ta Ƙaddara haɗewar jini dake cikin  jinin da kuka salwantar, azzalumai lokaci yayi, UBANGIJI ya ƙulla rugujewar zaluncinku ta inda bakuyi zato ko tsammani ba, wannan ruɗanin shine nai muku hasashe, kuma gashi ALLAH ya tabbatar dashi, dama na faɗa muku wannan shukar saita fito da izinin UBANGIJI tai yaɗon da zata zamewa rayukanku barazana, nakuma tabbatar muku kafin kubar duniya sai kun wulaƙanta, duk wanda yaci amana dolene amana ta cisa shima, gashi kuwa ALLAH ya tabbatar da hakan, ku fara gudu maƙiya ALLAH, na ce ku fara gudu tun yanzu.......”   
            Dukkanin wanda keda alaƙa da wannan mummunan kalamai a cikin mafarkin a wannan dare hankalinsa a tashe ya wayi gari, domin dai wata shukace da suka binne a wasu shuɗaɗɗun shekaru take nuni da tayi tsiro da yaɗo harta saki ƴaƴa, suwaye ƴaƴan? A ina suke? Tayaya aka samesu bayan irin da suka shuka sunada tabbacin basu bar ko fure ajikin itaciyarsa ba, itaciyar kanta saida suka busar da ita balle ai tunani tayi yaɗon ɗa? Mike shirin faruwa dasune? A ina kuskuren yake? Ya akai mai gidauniya bai taɓa gano musu hakanba? Shima bai gani bane? Kokuwa ya gani ya ɓoye musu?.

      Lokacine zai basu wannan amasar damu kanmu masu bibiyar labarin😵.

★★★★★★★

             Rashin yin barci da wuri ya sakasu makara da asuba, dan sanda Jawaad ya farka wasu masallatan ma harsun kusa idar da salla, akan fuskar bily ya sauke idanunsa dake cike da barci, ya sauke siririyar ajiyar zuciya tare da tashi zaune da ita a jikinsa, idanu itama ta buɗe a hankali, sai dai suna haɗa ido tai saurin maidawa ta rufe tana ɓata fuska. Murmushin da bai niyyaba ne ya suɓuce masa, a zuciyarsa yake ayyana ‘sai shagwaɓan tsiya’ A fili kuwa sumbatar laɓɓanta yay, cikin raɗa-raɗa yace, “Good morning my Heartbeat”. Saurin cusa kanta tayi cikin ƙirjinsa. Iska ya hura mata cikin kunnenta yana murmushi, “Ko a ɗan ƙarane” yay maganar yana ƙoƙarin cusa hannaunsa cikin rigarta. kukan taɓara ta sakar masa da sauri jan jikinta baya. “Matsoraciya” ya faɗa yana sauka daga gadon gaba ɗaya.
                Lamo nayi kwance zuciyata na tariyomin dukkan abinda ya wanzu a daren na jiya daya tara abubuwa masu yawa a cikinsa, darene da zuciya bazata iya mantashiba ta kowacce irin siga, dan yazo da abubuwa kala-kala a cikinsa. Har yanzu jikina akwai zazzɓi, ga ciwon kai da bala'in ciwon jiki, babu inda bayamin ciwo a jikin nan nawa wlhy. Ina jin motsin fitowarsa amma nakasa motsawa, tunanima nake tayaya zanyi t

afiya ni balki........? Cak aka ɗagani sama, wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke ina ɓoye kaina a ƙirjinsa dan banaso ko ido mu haɗa, wata irin matsananciyar kunyarsa nakeji fiye da da. jina kawai nai cikin ruwan zafi, hakan yasa na ƙanƙamesa sosai. A cikin kunnena yace, “Sorry daure, kaɗan za'ayi”. Kaina na ɗaga masa ina haɗiye kukan dake neman tahomin. Yanda ruwan yaɗanyi zafi sosai sai naji daɗi dan har jikina ya gasamin gaba ɗaya dukda inata noƙewa,  har aka gama hannayena suna naɗe a ƙirjina. Saida ya bani towel na ɗaura sannan na samu nutsuwa duk da dai shima bawani babba bane amma yafi dai babu. Matsowa yay zai ɗaukeni bayan na kammala alwala. kaina a ƙasa cikin dakusashiyar muryata nace, “Zan iya tafiya da kaina”. Baice komaiba ya ɗan matsa baya ya bani hanya. Cikin dauriya na fara tafiya a hankali ina matse idanu, dan  zafin nakeji, sai dai ba sosai dazai cutarba,  bakamar na daren jiya dana ringajin tamkar ana yayyankani da wuƙa ba.
       Kallonta Jawaad yake cike da nazari harta fice, yanda take tafiyan batason haɗa ƙafafunta sosai ya sakashi jin dolene ya dubata kodai ya jimata ciwon da gaske?. bayanta yabi  shima. taimaka mata yay ta saka doguwar riga da hijjab shima ya saka jallabiya ya jasu jam'i duk da garima harya waye.

            Bayan sun idar fita yay daga ɗakin, babu jimawa sai gashi ya dawo ɗauke da madaidaicin kofi daketa fidda turiri. Kwance ya sameta a inda tai sallar ta ƙudundune da hijjab, tea ɗin ya ajiye ya ɗakko magunguna ya ajiye sannan ya ɗagota jikinsa harma ta fara barci, “Sorry, tashi kisha tea da magani saiki kwanta”.
         Duk yanda na marairaice masa akan na ƙoshi bai saurareniba, sai da ya tabbatar nashaye tas sannan ya bani maganin nasha. Da taimakonsa na koma saman gado, harna fara lumshe idanu naji yana buɗemin jiki, sauri buɗe ido nayi da riƙe masa hannunsa ina ɓata fuska, dan nazata ƙarawar zaice zaiyi. “Na shiga uku, dan ALLAH kayi haƙuri, wlhy ka maimaita mutuwa zanyi”.
      Dukda ta bashi tausayi saida yaji dariya na neman kufce masa, ya dai daure ya haɗiye kayansa yana wani binta da kallon ƙasan ido, harta fara hawaye. Ɗauke idonsa yay daga fuskarta batare da yace komaiba ya maida inda yake son ganin.Ya kuwa ji mata ciwon da yay hasashe, sai dai bamai ɗaga hankali bane, amma zaiso a dubata gudun kuskure, tsabar son ya tsokane saiya ranƙwafo kanta kamar da gaske abinda take gudun zaiyi. jiyay kawai ta fashe masa da kuka jikinta ya fara rawa kamar wadda ta hango dodo. Dole ya danne dariyar da keson ƙwace masa ya rungumta. “Wasa nake miki niba ƙarawa zanba yi haƙuri”. Da ƙyar ya samu tai shiru har barci yay awon gaba da ita saboda maganin daya bata yana saka barci, ga kuma dama bawani isashen barci sukaiba. Sai da ya tabbatar barcinta yay nisa sannan ya gyara mata kwanciya ya sauka daga gadon bayan ya lulluɓeta da bargo. Dukda shima barcin yake buƙatar yi bai kwanta ba, wayarsa dake a drowan gefen gadon ya ɗauka ya fita falo.

10:30am

            Ring ɗin wayarsa ne ya sakashi farkawa daga barcin daya ɗaukesa anan falon bisa doguwar kujera, kwance yake a rubda ciki, hakan ya sakashi miƙa hannu bisa centre table ɗin dake gab dashi ya lalubi wayar batare da ya buɗe idanunsa ba, guntun tsaki yayi sannan ya buɗe idonun da ƙyar ya kalli wayar. Ganin Jabeer ne ya sakashi ɗagawa yasa wayar a kunne, cikin muryar barci ya amsa masa sallama suka gaisa. Daga can Jabeer ya sanya dariyar shaƙiyanci, “A lallai boss Mamin mu batazo da wasaba, ka kalli agogo kuwa? Kaine da barcin safe har goma da rabi?”. Idanu Jay ya lumshe ya sake buɗewa akan agogon falon, kafin yace, “Kai ka sani dai ɗan sa ido” yay maganar yana tashi zaune da ƙyar. Dariya Jabeer yayi daga can, “Bari nakira anjima, dama akan maganar da mukai dakai jiya ne”. Jawaad ya ɗan sauke numfashi a hankali, “Karka damu gani nan zuwa station ɗinma”. Kafin Jabeer yace wani abu ya yanke wayar.
      Ɗakinsa ya nufa inda ya tarar bily na barcinta har yanzu, sai da yaje gareta ya taɓa goshinta, zazzaɓin yaɗan sauka amma ba duka ba. Baice komaiba ya ƙarisa bayi domin yin wanka.
          Shiri yayi cikin ƙananun kaya da sukai mas

a ƙyau, yana fesa turare ya jiyo ana knocking turaren ya ajiye ya fita, yasan bazai wuce Nabeelah ba, dan ya kira Ummah yace ta turo masa ita, Ilai kuwa itace ɗin tsaye a bakin ƙofar, Nabeelah da Ummah ta sakata zuwa akan dole kawo breakfast taja baya ganin Yah Jay ne ya buɗe ƙofar yau da kansa, saurin durƙusawa tai ƙasa tana faɗin, “Yayanmu dan ALLAH kayi haƙuri, na tuba wlhy bazan sakeba, ranarma suɓutar bakine”. Shi dai baice mata komaiba ya bata hanya ta shigo, juyawa yay ya koma ɗakinsa. Ta sauke ajiyar zuciya da ƙarisa takowa cikin falon sosai, basket ɗin hannunta ta ajiye saman centre table ta zauna tana waige-waigen ta inda Bilkisu zata fito, zamanta babu jimawa ya fito daga ɗakin yana waya, basket ɗi  data ajiye ya yaye ɗan ƙyallen da aka rufo a kansa, kulolin ya buɗe duka, baice komaiba ya zauna a kujera da faɗin, “Tashi Ki haɗa min coffee”.
       Nabeelah da aka nutsu kamar ba itaba tace, “to” tana miƙewa, tasan wannan ƙyaletan da yay ba yana nufin ya bartaba, akwai abinda yake shiryawa, Ummah ce dukta jamata, tayi alƙawarin bazata bari su sake haɗuwaba har sai bayan wata biyu, amma aunty Batool ita da Ummah yau suka zuga Abbah yace itace zata kawo breakfast. Ummah bata wasa wa yaranta akan aikin gida da girki, duk taɓarar Nabeelah da shegen surutu komai ta iya na mata, sai dai son jikin jaraba, wani lokacin sai Ummah tai mata wuju-wuju akan aiki take tashi tayisa. Kitchen ta nufa ta haɗa masa coffee mai daɗi kamar yanda tasan yanaso sannan ta kawo masa. Har yanzu wayar yakeyi, dan haka yaymata nuni da abincin da hannu. Komawa ta sakeyi ta ɗakko filet tazo ta haɗa masa abincin shima ta koma gefe ta zauna, tana son tambayar Bilkisu tana tsoron sake yin laifi a garesa.
         Abincinsa ya cigaba da ci yana wayar har zuwa wani lokaci, kafin ya ajiye ya maida hankali ga cin abinci kaɗai. Ita dai tana zaune ne tanata satar kallonsa da gulmarsa a zuciya harya kammala ya miƙe yana goge baki da tissue, yay magana batare da ya kalleta ba. “ki tabbatar kin gyara gidan nan, idan kin tashi karki nutsu kiyi da ƙyau kinji, ki kuma tasheta da rawar kankin nan kiga yanda zan sauya miki kamanni”. Fuska Nabeelah ta kumbura tana faɗin, “ALLAH kuwa yayanmu ni yanzu na daina rawar kai”. Juyawa yay ya zuba mata harara ya nufi hanyar fita, harya kama handle ɗin ƙofar kuma sai ya juyo, “Idan ta tashi ki kirani”. “To yayanmu”.
  
         Sadiq da tun ɗazun yazo gidan saboda kiran da Jawaad yay masa akan yazo zasu fita, ya taso daga wajen maigadi da yake zaune suna hira ganin Jawaad ya fito, sai da suka gaisa sannan ya buɗe masa ƙofar ya shiga ya zauna. Zagayawa yay shima ya tada motar suka fice a gidan bayan sun gaisa da maigadi daya buɗe musu gate.
      Duk da ba aikine ya kawosa office ɗinba saida ya shiga suka gaisa da Sir Ahmad da yayta tsokanarsa. Office ɗinya ya buɗe ya shiga, komai tsaf babu wani datti sai ƴar ƙurar da ba'a rasaba. Yana zama babu jimawa su Aliyu na shigowa.
        Yanda suke wani binsa da kallon shaƙiyanci ya sakashi haɗe fuska yana harararsu. “Malamai miye namin wannan kallon ƙurullar?”. Dariya duk suka sanya masa hatta Aliyu da bai cika tsokana ba. Jabeer yace, “Kuji kama kaifa jama'a, waya ce da kai wani abu anan dan ALLAH?”. Jay ya sake zuba masa harara yana ɗauke kansa, “Ai nasan zakuce ɗinne musamman ma kai da babu abinda ka iya sai shegen gulma ko mace ta shafa maka lafiya”. Yanzunma dai dariyar suka sanya suna cigaba da masa sherin wai ƙyallin angwaci yake kamar wata ɗan daren sha biyar.
       Shiru yay musu sukai sherinsu suka gama sannan suka zauna.
          Hafiz ya maida dubansa ga Jay dake duba file ɗin da Jabeer ya basa, “Boss wai mike faruwane haka? Gaba ɗaya mun kasa banbance komai tun daga yinin jiya har safiyar yau ɗin nan? Gashi kuma kazo office bayan munsan kana hutu?”.
           Jawaad ya ajiye takardun yana sauke nannauyan numfashi, miƙewa yay ya ɗakko wani file a drawer bayansa, yana daga tsaye ya ranƙwafo ya dafe tebirinsa da duka hannayensa, dara-daran idanunsa da tun daren jiya haskensu bai gama dawowa ba ya zubamasu Aliyun, cikin ɗacin murya yace,“Hafiz nima wannan amsar n

ake nema, nakasa fahimtar komai, komai sake ruɗar dani yake da dilmiyani a kogin ruɗani..... a daren jiya wani ya shigar min gida domin cutar da Miemaa, lokacin inacan wajen kama ɓaleru”.
       A tare suka ɗago suna kallonsa fuska cike da tashin hankali. Har haɗa baki suke wajen tambayar baidai cutar da itaba ko?.
      Kansa ya girgiza musu yana miƙewa tsaye sasai, “Babu abinda yay mata, sai itacema ta jijji masa ciwo, ta faɗamin a bubuwa da yawa masu kamanceceniya da yanda akaima matar Jabeer fyaɗe.
      Jabeer yace, “Boss da gaske?”. Kansa ya sake jinjinawa kawai yana mai datse haƙwaransa waje guda saboda azabar zafin da zuciyarsa ke masa.
      Su duka ukun tsaye suka miƙe, suma cikin zafin ran da akan daɗe ba'aga Jabeer da shi ba yace, “Boss anya ba Qaseem bane?”.
      Kafeshi da idanu Jay yayi kafin ya janye yana wani ɗan murmushi mai ƙona zuciya,  “Jabeer! Ba Qaseem bane, a yanzu bashi nake zargiba sam, tako wace siga na auna Qaseem bai hau mizanin bincikena ba, Idan har wanda nake zargi ya zama shiɗinne da gaske to lallai ƙungiyace dasu, dan adaren jiyan Miemaa ta samu nasarar cirar zobe daga hanun wanda ya shigo gidannan, kuma zoben tabbas na taɓa ganinsa a hannun kusan mutum huɗu, abinda ya kuma ɗauremin kai basuda wata alaƙar zahiri dake a bayyane su duka huɗun kuma”.
         Aliyu ne yay ƙarfin halin cewa, “To boss indai basu da alaƙar zahiri tayaya zamuyi tunanin haɗasu a kamanceceniyar laifi?”.
        “Ƙyaƙyƙyawar tambaya Aliy” Jawaad ya faɗa yana fuskantarsa da ƙyau, hannayensa duka biyu ya zura cikin aljihun wandon sa ya zagayo ya sake zama a kujerarsa. suma duk komawa sukai suka zauna.
      Jay ya ɗauki coffee ɗin da Hafiz ya ajiye masa yakai baki yana faɗin, “Akwai kamanceceniya mai yawa Aliy, musamman idan muka saka abubuwa da yawa da suka faru a tsakanin nan a mizani guda, babu abinda yafi ɗaukar hankalina wajen kamantasu sai maganar fyaɗen nan, dan haka zamuyi amfani da wannan damar mu canja salon bincikenmu. Fyaɗen da akaima Amina, Matar Jabeer, Nazifa, yayar Ummie, da ƴar mai aikin gidansu Nazifa daya faru kwanannan duk basu da banbanci, a tunani na hankali da yazo a zahirance zai bama mai nazari wahala wajen fahimta musamman daya kasance ba'a guri ɗaya al'amarin ya faruba, hasalima ba lokaci gudaba, idan har zamuyi aki da hankali kuma amsar ƙarshe itace ba mutum ɗaya ke aikatawa ba kenan. Da akwai aikin dana shirya dunƙule yaran suyi da, dan a jiya harma na sakasu zuwa gidana zamuyi magana sai ban koma gida akan lokaciba, to yanzu zamuyi amfani da wannan damarne, saboda su abin ya faru da wasunsu, sunsan zafi da raɗaɗin da akeji”.
           Cikin farin ciki Hafiz yace, “Wannan tsarin yayi wlhy Boss, amma nima ga tawa shawaran”. Gaba ɗayansu hankalinsu suka maida ga Hafiz ɗin, ya gyara zamansa sosai yanda zai faɗi komai dalla-dalla. “Kunsan a yanzu bazai yuwu kai tsaye mu iya binciko waɗanda akaima fyaɗe irin nasu ba, fitowarma fili zaisa masu aikatawar su ɗauki mataki suma, haka bayyanar yaran kai tsaye zai dawo da hankalin masu aikatawar kansu”.
      “Ƙwarai kuwa hakane Hafiz”.
“Yauwa to mizai hana mu taimakama yaran su buɗe wata ƙungiya haka ta ƙarɓar ƙorafin waɗanda akaima fyaɗen koma a wane yanayine, matanmu su zama sune masu ƙungiyar a bayyane, mukuma mu koma ta bayan fage wajen tsayawa tsayin daka ga masu shari'a su ringa yanke hukuncin daya dace cikin ƙanƙanin lokaci, na tabbata hakan zaisa mu sami dukkan damar da muke buƙata kodan sakacinma da kotuna keyi akan wannan matsalar, kunga mun jefi tsuntsu biyu da dutse guda, zamu sami abinda muke buƙata, zakuma mu taimaki yaran da ake zalinta musamman waɗanda iyayensu basu da ƙarfi akan tsaya masu bayan an cutar musu da ƴaƴansu”.
        Tafama Hafiz suka shigayi dan shawarar tashi tamusu yanda suke buƙata. A take kuma suka tsara komai yanda ya kamata. Suna cikin tattaunawar su Zuhrah suka iso office ɗin kamar yanda Jay yay kirasu tunkan ya baro gida akan su samesa nan.
       Ummie ce tai musu jagora har office ɗin na Jay, Sai da suka gaishesu duk cikin girmamawa kafin su basu izinin zama. Shine ya fara magana cikin dakewar nan tasa da

kowa ya sani musamman akan abinda ya shafi aiki, “Inason ku bani dukkan hankalinku nan”. A take duk suka sake nutsuwa garesa fiye ma da yanda yake buƙata.
         “Ku dukanku a yanzu zaku kasance wajen aiki ɗayane, ina mai gargaɗarku da bama buƙatar wasa, daga yau zaku ajiye wani ƙawancenku gefe kuyi aiki tamkar bakusan kankuba, zaku fito a ƙungiyance domin karɓar kukan iyayen da akaima ƴaƴansu fyaɗe. Wannan itace hanya ta farko da zaku iya fahimtar dukkan abinda kukai buri. Sunan ƙungiyarku, lauyoyin da zasu taimaka muku, harma da alƙalai mun tanada, ku naku kawai sauraren duk waɗanda matsalar ta shafa. Baku kaɗai bane a ƙungiyar, akwai matan su Jabeer, dan irin matsalar data faru da ke Nazifa da sister ɗin Ummie data rasu da Amina itace irin hanyar da akabi akaima matar Jabeer fyaɗe kafin aurensu da wasu ƙawayenta biyu data sani”.
        Duk kallonsa sukai cike da ɗunbin mamaki, Nazifa dake sharar hawaye tace, “Yaya kuma suma ba'a gane wanda yay musunba har yanzun?”.
       Cikin tsananin takaici Jay yace, “Ba'a ganeba, hasalima daga ƙarshe a lalace shari'ar ta ƙare tunda babu wasu hujjoji da zasu tabbatar da wanda ya aikata ɗin. Abinda yasa mukai tunanin kufito a ƙungiyancan dan bazai yuwu mu iya gane waɗanda akaima irin wannan kalar fyaɗen ba saita siyasa, suma waɗanda akayima ɗin ta wasu hanyoyi wasu rashin gata ya sakasu sunyi shiru, wasu kuwa sakacin shari'a yasaka zancen wucewa tamkar ba'ayiba. Ku jami'an tsarone shiyyasa muke fatan ƙungiyar da zata fito daga ƙarƙashinku ta banbanta da sauran ƙungiyoyin, mukuma zamu tsaya a bayanku mu baku dukkan gudunmawa ta ɓangaren shari'a dan acanne ake ruguza komi da make ƙwarin gwiwar ƙungiyoyin dake faɗi tashi akan wannan matsalar. Dan haka aikinku zai kasance da manufa biyu....”
            Kasancewar hakan burinsune sai duk suka amsa cike da farin ciki da zumuɗi.
       A nutse Jay ya ƙarayi musu bayani suma su Aliyu suka ƙara musu da nasu.
       

★★★★★★★

           Ring ɗin wayatane yasa na farka, na buɗe idanuna da ƙyar ina tashi zaune, saman mirror ɗinsa na hango wayar, dan haka na sauka a kan gadon ina cije baki, duk da Alhmdllh naji daɗin jikina bakamar a daren jiya ba da ɗazun da safe, ganin Ummu ce da kanta tai kirana na ɗan zaro ido waje na ɗauki wayar da har ta katse, ina ƙoƙarin kiranta kiran ya ƙara shigowa, cikin ladabi na ɗaga tamkar ina a gabanta na gaisheta Ina hawaye.
     Daga can gimbiya tai murmushi tana gyara kishingiɗar da tayi jikin mai martaba, “Haba ɗiyata, miye kuma abin kukan, baki da lafiyane naji muryarki haka? Ayi haƙuri to, shiyyasa naƙi kiranki ai sai yau, duk kuna lafiya ko?”. Kaina na ɗaga tamkar ina gabanta nace, “Lafiya lau Ummu, barci na tashi ne, sai kaina dake ciwo kaɗan, inasu Safah? Tun jiya naketa zuba idon zuwansu amma shiru”. “kisha magani to, ALLAH ya ƙara sauƙi, Karki damu zasuzo insha ALLAHU, yanzuma na kirakine akan zuwansu Anuwar anjima kaɗan dan zasu wuce gobe idan ALLAH ya kaimu”. Cikin jin daɗi na share hawayena Ina faɗin, “ALLAH ya kawosu lafiya Ummu, to suzonan su kwana dan ALLAH”. “A'a babu batun kwana ɗiyata, ai ba'a kwana gidan amarya, zasuzo dai zuwa dare su dawo, ki tabbatar mijinki da Anuwar sun haɗu dan munyi waya dashi ɗazun yace baya gida”. “Insha ALLAHU Ummu zanyi ƙoƙari”. “To shikenan, sai anjima na kiraki kinji, kidage da shiga ruwan zafi karkiyi son jiki”. Kunyace ta kamani, a raina ina tunanin kodai shine ya sanar mata..... “Kina jina” magarta ta maidoni hankalina. “Eh Ummu”. “Bawai ina nufin ki shiga ruwan zafi idan babu abinda ya faru ba, tunda nasan kina fashin salla, bakuma saina buɗe miki abinda nake nufiba, ayita haƙuri danshi zaman aure haƙurine, allah yay miki albarka”. Hawayena na share nace, “Amin Ummu nagode”.
           Rashin ganinsa a ɗakin ya sakani jin daɗi bayan na ajiye wayar, cikin dauriya na gyara ɗakin tsaf, na fito ɗaukar kayan shara naga Nabeelah, sosai naji daɗin ganin nata, itace tace nabar sharar ita zatayi, ban musa mataba na shiga nai wanka da sake gasa jikina sosai, hakan ba karamin nutsuwa ya ƙaraminba. Koda na fito saina koma ɗakina nai shiri, ina cikin shirin Nabeel

ah ta kawomin abinci, dan tunda taga yanayina ta tambayeni lafiya nace mata banida lafiya duk sai naga jikinta yayi sanyi. Yunwa nakeji sosai shiyyasa na zauna naci abincin. ɗakinsa na sake komawa ɗaukar maganin dan naji daɗinsa, ina buɗe box ɗinne Nabeelah ta shigo da sallama da waya a hannu, a kunne kawai ta sakamin batare da tayi maganaba. Ɗagowa nai zan tambayeta wanene? Muryarsa ta shiga dodon kunnena.
       Saida na lumshe idanu na buɗe sannan na amsa masa sallamar tasa,
          “Amarsu kin tashi?”. Ya faɗa cikin zolaya.
       Jinai tamkar na nutse dan kunya, dukda bana gabansa, nai saurin saka hannuna na rufe fuskata ina murmushi da faɗin, “Nidai ALLAH a'a”. Ina jiyo sautin murmushinsa shima, yace, “Nidai nasan amaryata amaryace ƴar gaske, yaya jikin naki?”. Batare dana buɗe fuskarba nace, “Da sauƙi”. “Alhmdllh ai haka akeso, kinci abinci ko?”.
     “Uhm naci”.
  “Tom kisha magani ki sake kwanciya ki huta karki biyema surutun Nabeelah, Gimbiya ta kirani akan baƙi zasuzo kuyi sallama, zanyi ƙoƙari na dawo da wuri nima insha ALLAH. ga Sadiq nan zai kawo cefane Nabeelah tayi girki”.
        “ALLAH ya dawo dakai lafiya to”.
“To nagode, amma mizan ɗan samune Noor-Jahan?”. A marairaice nace, “Mi kake so?”. yace, “Komai aka bani inaso mana”. Duk da ina tsananin jin kunya nace, “To rufe idonka”. “Na rufe ruf Matar Jay”. Yay maganar cikin sanyin murya kamar ba shiba.  da saurin na yanke kiran ina dariya, ina gani ya sake kira naƙi ɗagawa, saima maganin na ɗauka na fita falo wajen Nabeelah.

       Babu jimawa da zamanmu Sadiq ya kawo cefanan da yace, karon farko da zan fara girki a gidana dukda Nabeelah tace na barmata zatayi kar yazo ya gani yay faɗa, ban sauraretaba dan nima inason ƙarfafa jikina ai. Tare mukai girkin cikin nutsuwa da salon da Umm-Anum ta sake koyar dani, dan danan gidan ya kaure da ƙamshi, muka kammala tsaf muka gyara kitchen ɗin sannan.
     Kusan ƙarfe uku na rana saiga su Anum, Anuwar, Abdul-Rahman, Abdur-raheem, Ameen, Meenal, Amaturrahman, Amatullah. Tuni muka rungume juna dasu Amaturrahman kamar mun shekara da rabuwa, su dai su Abdur-raheem dariya suketa mana.............✍

Inacan ina muku dogon page, kunanan kuna ƙwalama sunana kira😣😫, ku baku ganeba ne, duk randa nai posting da wuri to nayi typing ɗin dare ne ya kwana, idan kuma ban samu damar yiba dole sai randa zan tura nakeyi, ga aikin gida ga uzurorin rayuwa🤦🏻😓, gashi yanzu anzo gangara typing ɗin na buƙatar nutsuwata sosai, amma idan naga wani Comments ɗin har mamakin mai rubutashi nakeyi wlhy. ALLAH dai ya dafa mana kawai, duk ƙoƙarinka baka isa yima kowa yanda ya dace ba, ALLAH kaɗai ka iyama ɗan adam da halinsa wlhy😂🚶🏻🚴🏼.

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA

1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

1 year ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment