Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dazan taɓa saurara, keɗin kaddarace mai girma a gareni, makullin cikar dukkanin burkana. Kinsan illa nawa kikaimin ne?!!” yay ƙare maganar a tsawace da cafke wuyana ya shaƙe. A take jikina ya fara rawa na fara ƙoƙarin fisgo numfashi cikin kakari. Hankaɗani yay na bigi fuskar gadon. Azaba ta sakani fashewa da kuka na riƙe wuyana da duka hannu biyu. Wani irin matsanancin fushine ya tasomin jin dariyar da yake sake ɓaɓɓakawa yanzu ma, nace, “Ƙarya kake azzalumi, idan ka isa ka daina ɓoyemin kanka, matsoracin banza da wofi kawai, Bazan sake roƙoka ka barni ba koda hakan na nufin zakai nasara a kaina ɗin, sai dai na ɗauki alwashin in ALLAH ya yarda, inhar ƙazamin jikinka ya kasance shine ƙaddarata, nima nice zan zama ƙaddarar mutuwarka, dan da hannuna zan kasheka a ɗakin nan, a wannan daren la'ananne ALLAH fasiƙi kawai!!!”.
          “Hhhhhhh!!” ya shiga sake ɓaɓɓaka dariyarsa mara daɗin ji da tafa hannayensa. Gaba ɗaya ɗakin ya ɗauki sauti hakan yasa na kasa fahimtar taka maimai inda yake. “Da ƙyau Bilkisu, da ƙyau!, ashe kema kin fara koyon jarumtar mijin naki?, nine zaki kashe, ni ni ninan kikejin zaki iya ki kashe.....?!!!” naji an sake damƙar wuyana an shaƙe.
        A take jikina ya fara rawa, nasa hannu na daki cikinsa cikin gushewar hankali, dukda alamu sun nuna yaji zafi bai sakeni ba, sai ma dannani da yay baya ya maƙureni jikin fuskar gadon ya haye kaina. “Zanyi abinda ya kawonin, ada nayi niyyar barinki a raye tamkar sauran kicigaba da rayuwa kema, to amma tunda kince ke tsagerace saina shayar dake gidauniyar azabar mutuwa, k har wacece? Nawa kike? Da zaki zamewa rayuwata matsala.......”
    Yanda naima Jazuga ne ya shiga dawomin a rai, duk da shaƙar da yaymin cikin rahamar UBANGIJI na samu damar lalubar bed side drawer da naji a kusa da hannuna, kofin da boss yasha ruwa ban fiddaba yana a kai na jiyo, ALLAH ya bani sa'a fisgosa na ɗaga hannuna dake rawa da ƙyar na maka masa a gefen kunnensa. A take ya sakarmin wuya yana huci na shigar zafi..... Kafin ya dawo hayyacinsa na caka masa sauran kofin dake riƙe a hannun nawa, sai dai bansa a inane ba dan a kwai duhu a ɗakin har yanzun. ƙara ya saki yana sake kaimin wawura sai dai na zille harma na dire a gadon. Cafkoni yay cikin zafin nama ya maidoni baya kan gadon har saida nai ƙara dan azaba nima. Na gallama hannunsa cizo tare da halbinsa da ƙafa cikin salon trianing ɗin da muka samu duk da ba ganinsa nake ba. kokawa ce ta kaure a tsakanina da shi dukda yafi ƙarfina nesa ba kusaba. Amma kasancewar akwai taimakon UBANGIJI da kuma kowa yasan mata ALLAH kan bamu ƙarfi a irin wannan yanayin koda ace bazamu iya ƙwatar kanmuba kuwa. Kokawa muke bil haƙƙi da gaskiya dukda nice keshan wahala ban yarda ya kaini ƙasa ba. Cikin sa'a na kama ɗan yatsan hannunsa da yake neman sake kaiwa wuyana na murɗesa da azabar ƙarfi nai baya dashi. Jikake ƙaraƙassss ƙasss ƙasss ƙashin na bada sauti. Wahalalliyar ƙarar daya saki yay baya ta bani damar jan hannuna baya nima, sai na saɓulo da zoben dake jikin yatsan.
     A take Ɗakin ya ɗauki sautin wata murya mai ban tsoro da saka firgici, aka shiga faman faɗin, “Barmata shine kuskure mafi girma, ka karɓa maza ka fita karka tsaya akwai matsala!!”.
       Wani irin ɗagowa yay a zabure ya fisgoni muka tafi ƙasa tare ya murɗe hannuna da zoben ke a ciki zai ƙwace. Hakan yasa na shiga ambaton,
حَسْبُنَا اللهُ وَنِعْمَ الْوَكِيلُ.
Hasbunal-lahu wani'mal-wakeel.
      (ALLAH ne mai isar mana, kuma madalla da shi abin dogaro).
اَللَّهُمَّ اكْفِنِيهِمْ بِمَا شِئْتَ.
Allahummak finihim bima shi'ita.
     (Ya ALLAH! Ka isar mini su da abin da Ka so).
اَللَّهُمَّ لاَ سَهْلَ إِلاَّ مَا جَعَلْتَهُ سَهْلاً وَأَنْتَ تَجْعَلُ الْحَزْنَ إِذَا شِئْتَ سَهْلاً.
Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahlan, wa anta taj'alu-l-hzana idha shi'ta sahlan.
         (Ya ALLAH! Babu wani abu mai sauki sai abin da Ka sanya shi ya zama mai sauki, kuma Kai kana sanya tsanani idan Ka so ya zama sauki).
        Ƙarar da aka ƙwallah ta sakashi Hankaɗani kaina ya daki gadon, ya fita da gudu, na fasa wani irin gigitaccen ihu jikina na ɗaukar wani irin rawa, a take komai yay min ɗifff.......
        Fasa ƙarar Bilkisu tai dai-dai da ƙarasowar Jay jikin ƙofar falon zai buɗe dan isowarsa gidan kenan bayan yakai Ɓaleru ya ajiye a wani ɓoyayyen waje. cikin zafin nama ya faɗa falon batare da ya rufe ƙofar ba. Ledar dake hannunsa ma sakinta yay a falon. A gigice ya danna makunnar fitilar ɗakin ta kawo haske. Ya daka wani uban tsalle sai gashi gaban Bilkisu data sume. Da ƙarfi ya ƙwala kiran sunanta jikinsa na rawa dan har yanzu yana tattare da fushin ɓaleru ne, yay saurin maidata ya kwantar jin kamar gudun mutum ta bayan Windown ɗakin. Fita yay da gudu yana ƙwalama maigadi kira cikin matsanancin hargagi akan ya rufe masa gate. sosai maigadi dahar ya shiga ɗakinsa zai kwanta ya fito a gigice shima jin wannan mafaraucin kira, baƙaramin tashin hankali ya shigaba ganin yanda Jawaad yake nufosa tamkar mahaukacin zakin dake a yunwace. Ɗaukesa Jay yay da mahaukacin mari, “Waye ya shigomin gida? Ka gayamin wa kabama damar ya shigomin gida!!?”.
        Maigadi daya gama ruɗewa da marin da yasha yace, “Wlhy oga babu wanda ya shigo gidannan tunda ka fita, narantse maka babu wanda ya shig........” bai gama saurarensaba ya bar wajen, ta bayan Windows ɗinsu ya nufa kasancewar akwai wuta ko ina da haske. Take masa baya mai gadi yay da sauri shima dan bai fahimci abinda ke faruwa ba. Jay yaja wani mahaukacin birki yana kallon tsanin dake tsaye jikin katanga alamar koma wanene tanan ya shigo, kuma tanan ya fita. Naushi ya kaima bango da azabar ƙarfi yana faɗin, “Noooo!!”. Da sauri maigadi dake cikin tsoro ya riƙe masa hannu, “Oga dan ALLAH karka jima kanka ciwo”. Fisge hannunsa yayi dayin wani Uban tsalle ya ɗane katangar cikin ƙwarewar training da suka samu batare da ya kalli inda tsanin ya keba. Dirarsa can baya kawai maigadin yaji. “Na shiga uku ni gambo, mike faruwa a gidan wai?” mai gadi ya faɗa hankali tashe.    
       Babu abinda Jay ya gani sai sayin takalmi kawai da wani tsanin a baya, wajen siririyar hanyace data fita ɗoɗar har babban titi, hanyar tana taimakawa ƴan anguwarne wajen fita titi basai sunbi ta titin layinba dake da nisa da babban titi, ya dafe kansa dake wani irin masifar sara masa. Halin daya bar bilkisu a cikine ya faɗo masa a rai. Ya fiddo wayarsa a aljihu ya shiga haske-haske harya zagaya ta ƙofar gate yay knocking. Koda aka buɗe baiko kalli maigadi dake neman ƙarin bayani ba ya nufi cikin gidan.
      Yanda ya barta haka ya Koma ya sameta babu alamar numfashi tattare da ita. Tsugunnawa yay gabanta ya Rungumota da ƙarfi cikin ƙirjinsa jikinsa na wani irin tsuma na tsananin ɓacin rai, “Ubanwaye ya shigomin gida? Miyay miki?”. Yay maganar cikin raunin murya da ɗaci, jijiyoyin kansa na miƙewa ruɗu-ruɗu, zafafan hawayene ke kwarara a cikin zuciyarsa, a zahiri kam babu ko ɗigonsu sai idonsa daya kaɗa yay jazur. Ɗagata yay gaba ɗayanta ya ɗaura a kujerar dake ɗakin guda ɗaya ƴar doguwa, sai da ya gama bin ɗakin da kallo tsaf, ɗigon jini har a kan gadon ya gani, sai fasashen glass aƙasa zuwa gadon dake a yamutse alamar ansha dabbe a kansa. Kauda kansa yay yana rumtse ido da danne abinda ke yinƙuro masa tamkar zai faso ƙirjinsa ya fito mai alaƙa da Masifaffen kishi, sauran ruwan daya bari dake yashe a ƙasa ya ɗauka, a hannu ya zuba ya shafa mata a fuska. A take ta kawo wani nannauyan numfashi tare da miƙewa zumbur cikin zafin nama tana faɗin, “Saina kasheka, bazan barkaba yau, kasheka zanyi wlhy......” Saurin riƙe hannunta da take ƙoƙarin kaiwa wuyansa yayi da ƙarfi ya mannata jikinsa yana faɗin, “Kwantar da hankalinki ki nutsu nine”.
       Ƙamshin turarensa da naji ya sakani fashewa da kuka na ƙanƙamesa, “Boss shine, wlhy shine ke bibiyata tun a gidan Dad wai sai yamin fyaɗe, ya ɗau alwashin saiya ketamin mutuncina, yace nice cikar burinsa, saiya yimin yanda yayma su Amina, na shiga y......” ɗagota yay da sauri jikinsa na kakkarwa ya manne bakinsa da nata, sam baya buƙatar ji, bayason yaji komai a yanzu, zuciyarsa zata iya tarwatsewa idan ta cigaba da faɗa bazai iya ɗauka ba, yanada kishi mai tsanani akan dukkan abunda ya kasance nasa. hawayen da tun ɗazun yake fatan yinsu sunƙi suka shiga silalo masa a kumatu yanzun, yanda yake matan kawai zai baka tabbacin ba'a hayyacinsa yake ba. Yaja kusan mintuna biyar yana kissing ɗinta, tun tana ƙoƙarin son ƙwacewa harta nutsu ta miƙa wuya, dan ta kula da fushi yake sumbatarta. hawayensu ne masu ɗumi ke sauka bisa fuskokin juna. Saida yaga tayi laƙwasa sannan ya zare bakinsa cikin nata da sake rungumeta yana haɗiyar zuciya tamkar numfashinsa zaibar ƙirjinsa. Yanda ƙirjinsa ke sama da ƙasa sosai ya firgita Bilkisu, sai dai tai luf a jikinsa tana kuka dan dukkan abinda ya faru a waɗancan ranakun a yanzu tsaf suke dawo mata tamkar yanzune komai ke faruwa. Ɗaukarta yay gaba ɗayanta ya nufa ɗakinsa da ita, kai tsaye bayi ya zarce. Tanason tai magana sai dai babu fuska, dan haka ta nutsu shiru tanata share hawaye  da sauke ajiyar zuciya. Ruwa ya haɗa mai ɗumi sosai ya nuna mata alamar tai wanka ya fice.
      Binsa nai da kallo harya fice sannan na maida idona ga hannuna dake a rumtse, zobene mai azabar ƙyau da ɗaukar ido dana samu zamewa hannun tsinannen nan. Na maida hannun na rumtse ina cigaba da zubar da hawayen, mamaki nake a raina miyasa wancan zuwan da yaymin a gidan Dad ban taɓa tunawabama balle na sanarma wani? Nida sam bani da mantuwa amma gashi wannan ban taɓa tunawaba sai yau? Ko yaya akai hakan ta faru?. Da wannan zoben rumtse cikin hannuna nai wankan, da gasa jikina kawai nayi da ruwan daya haɗamin kafin nai amfani da sosonsa sama-sama dan wani irin ƙyanƙyami da takaicin raɓar jikina da la'anannen can yayi nakeji.
      Jay Ɗakinta ya sake komawa. Bai taɓa komaiba bayan kayan barci daya ɗauka mata ya kashe fitar ya rufo ɗakin. Ledar daya yasar a fali ya ɗauka ya koma ɗakinsa.
        ina kammala wankan yana shigowa, nai saurin komawa na duƙe dan bankai ga ɗaura towel ba, bai fasa shigowa cikin toilet ɗinba, sai dai kuma bani yake kallo ba, bathrobe dake ajiye ya ɗauka ya juyo inda nake, kafaɗuna kawai naji ya kamo ya miƙar dani, nai azamar rumtse idanuna dake cika da ƙwalla hannuna na naɗe a ƙirjina gaba ɗaya, ban buɗeba harya gama sakamin ya ɗaure igiyar sannan ya kama hannuna daga cikin bathtub ɗin ya fitar dani. Muryarsa a dakushe yace, “Yi alwala”. Juyawa nai naɗan kallesa, ganin shima ni yake kallo nai saurin maida kaina ƙasa tare da miƙa masa hannuna dake a dunƙule rumtse da zoben. A hankali ya tako inda nake ya kama hannun ya buɗe, jin bai ɗaukaba baikuma yi maganaba yasa na kallesa. Zoben ya kafe da idanu tamkar mai nazari, hakan ya bani damar ƙarema fuskrsa kallo dake a matuƙar ɗauren da ban taɓa ganiba nima. Ya ɗago jajayen idanunsa masu tsananin saka firgici ya kalleni. “Nashi ne?”. Kaina na ɗaga masa. Bai sake cewa komaiba ya ɗauke zoben yana sake nunamin nayi alwala. Nima ɗin bance komanba na barsa tsaye yana jujjuya zoben a hannunsa. Ina alwalar ya fita, babu jimawa ya dawo lokacin na kammala, fita nai na barsa, sai yanzuma nake tunawa banyi sallar isha'i ba ashe balle shafa'i da wutiri. Riga da hijjab dana gani a saman gadon na ɗauka na saka, na ɗauki abin salla dake ɗakin na shinfiɗa na tada sallar isha'i na miƙe nai shafa'i, bayan na idar na miƙe zan sake kawo shafa'i da wutiri na tsinkayi muryarsa yana dakatar dani. Dukda nayi mamaki haka nabi umarninsa, wani abin sallar ya shimfiɗa a gabana. Munyi salla raka'a biyu sannan mukai shafa'i da wutir. Juyowa yay ya dafa goshina bayan mun idar, a fili ya shiga karanto addu'arnan ga mai sabon aure,
اَللَّهُمَّ  إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا، وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا، وَشَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ.
Allahumma innee as-aluka khayraha wakhayra ma jabaltaha 'alayh, wa-a'oothu bika min sharriha washarri ma jabaltaha 'alayh.
          (Ya ALLAH ina rokon Ka laherinta da alhrin da Ka dabi'antar da ita a kansa, kuma ina neman tsarinka daga sharrinta da shaarrin Da ka dabi'antar da ita a kansa).
         Ya saki goshin nawa ya juya tare da ɗaga hannu yay doguwar addu'ar da banaji, dan haka nima nai tawa tareda yima iyayena addu'a da sauran musulmai baki ɗaya.
       Batare da yace dani komaiba ya miƙe, ficewa yay, babu jimawa sai gashi da kofi a hannu da filet, ina a inda ya barni zaune nidai banko motsaba, ledar ya buɗe ya juye gasashen naman rago daketa tashin ƙamshi saboda yanda aka sarrafashi cikin filet ɗin, kofin kuma ya saka fresh milk a ciki. “Taso kici abinci” ya faɗa yana zama akan sofa. Duk da bazan cinba ban musaba na tashi zuwa garesa jikina duk babu ƙwari ga ciwo yanamin ta ko ina saboda damben da mukaci da azzalumin can, ƙasa naso zama amma sai ya riƙoni na zauna kusa da shi, murya a sanyaye nace, “Naƙoshi, da yamma mukaci abincin da Ummah ta aiko dashi da rana”. Baice dani komaiba ya miƙamin fresh milk ɗin cikin kofin, amsa nai ita na kafa kai na shanye gaba ɗaya badan tanamin daɗiba sai dan buƙatar samun sanyi a cikin ƙirjina da yaymin nauyi. Jikina ko ina ciwo yay tsamu ga barci dama inaji. Amsar kofin yayi ya sake zubawa ya miƙomin, kaina na girgiza masa cikin marairaicewa dan kar yace saina shaɗin tilas. shanyewa yay ya miƙe ɗauke da filet ɗin naman da kofin. “Ga kaya nan ki canja ki kwanta”. Kaina a ƙasa nace, “To”. Juyawa yay ya fita, harna kammala saka kayan bai dawoba, na zauna bakin gadon ina ƙara tariyo abinda ya faru awanni biyu da suka shuɗe tamkar film ko mafarki. Gittawar da akai ta gabana ya sakani saurin ɗagowa, ganin shine sai na sauke ajiyar zuciya a hankali. Kwantawa nai da sauri ganin zai cire jallabiyar jikinsa na juya masa baya. Kusan mintuna goma sannan ya hawo gadon shima ya kwanta bayan ya kashe fitilar yabar ta gefen gadon kawai. na lumshe idanuna hawayen da suka taru min na silalowa, ni kaɗai nasan irin raɗaɗin da nakeji a raina da ruɗanin abinda ya hanani tuna waɗancan kwanakin da wannan shaiɗanin yazomin. saukar tattausan hannunsa akan kumatuna ya sakani buɗe ido a hankali kansa, fuskarsa gab take da tawa har muna shaƙar numfashin juna, dan akan filon danake kwance ya ɗora kansa shima, idanunsa dake kallon fuskata ya lumshe a hankali cikin salon lallashi yana mai sharemin hawayen da hannunsa dake akan fuskar tawa, cikin muryar raɗa yace. “Miyasa baƙya gajiya da kuka?”. Wasu hawayen ne suka sake silalo min, nace, “Na tsaneshi ne fiye da yanda kowa zai iya tunani”. Murmushi naji yayi mai sauti, hakan yasa na buɗe idanuna ina kallonsa, kallona yake shima,, “Kinsan minene?” kaina na girgiza masa alamar a'a, yace, “Na fiki tsanarsa Miema”. Murmushin da ban niyya bane ya suɓuce min a bazata. Gani nai shima yay murmushin idanunsa da suka rine jaa na wani irin ƙyalli kamar hawaye ya taru a cikinsu. nai ƙoƙarin jan fuskata baya dan kusancinmu yayi yawa, sai yay saurin maidoni gab fiyema da farko, yace, “Faɗamin miya faru? Kozan sami nutsuwa”. Hawayen ne suka sake silalowa, na maida idanuna na lumshe inajin yanda yake murza yatsansa babba saman fuskata, sauran huɗun kuwa kan gashina daga ƙeyya zuwa gefen kunne “A wani daren daya shuɗe, wanda tunani ko hasashe bai sake dawo dashi ba gareni, ranar da ya fara zuwa gareni.........................”.
       Na ƙare faɗa masa dukkan abinda ya faru har zuwa yau da fashewa da kuka mai cin rai, da ƙarfi ya jawoni jikinsa ya rungumeni tsam, jikinsa na wani irin rawar ɓacin rai, nima saina sake fashewa da kukan, dan koba komai na fahimci shima yanajin irin zafin da nakeji a cikin raina, nace, “Na rasa miyasa ban taɓa tunawa ba sai yau?, Inason nasan ko wanene shi? Miyasa duk waɗanan kalaman nasa a kaina? saina kasheshi, da hannuna zan kasheshi azzalummi maƙiyin ALLAH, sainai gunduwa gunduw.........”
           Jawaad daya saki murmushin takaici mai ciwo ya ɗagota daga jikinsa, babban ɗan yatsansa da yake share mata hawaye ya ɗaura akan laɓɓanta da faɗin,  “Shiiii!!. kisa a ranki zaki sanshi, bana buƙatar sake ganin kukanki, Ni Jawaad Abdul-aziz yusif insha ALLAHU zan gurfanar miki da shi a gabanki kan gwiyoyinsa, abinda yake bibiyar kuma zan tabbatar masa da yafi ƙarfinsa har abada a wannan daren”. Ya ƙare maganar da manna bakinsa saman nata batare da ya sake bata damar magana ba. Duk da yana tausayinta bazai iya barintaba, wani irin shauƙi da zumuɗin kasancewa da ita yakeji, ji yake tamkar ana ingiza zuciyarsane akanta, jiyake idan bai kasance da itaba a wannan daren kamar zai rasa komai ciki harda ita kanta, tun yana sarrafata da tunanin iya ƙaramin wasa ya barta har hakan yaji bazai yuwuba, zuciyarsa ingizashi kawai take na kaiwa ga ƙololuwar martabarta................✍

😜Saura kuma naji wani yay gulmar Jay ehe😣🤐🤣🚶🏻.

Barkanmu da dawowa.

A ranar asabar an samu kuskuren ɗakko page daga telegram zuwa WhatsApp, wadda tayo copy ɗinsa daga can bata ɗauka a jereba kamar yanda page ɗin yake, shiyyasa tallan zafafa goma ya koma tsakkiyar page, wasu sai sukai tunanin ƙwai cikin ƙaya ake talla wai. To ba haka baneba, dan ranar kam masu sai da zafafa goma saida kuka tsiyayar musu da man kansu tas🤦🏻😑 saboda kira. Waɗanan buks ɗin goma namu sune nake talla gasu ga mai buƙata dan karku bari a baku labari inhar kasan baka karantanba dan duk sunyi lagwadar daɗi aradu🚴🏼👇🏾 .

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.

Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899

sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[1/5, 7:05 PM] HASNA✍🏻: Bilyn Abdull 📚:
*TELEGRAM LINK ƊINMU*
https://t.me/joinchat/SBu4bmWd8skN4Zfr

WATTPAD

https://my.w.tt/TiR6HMHUNcb


Page 43

.....................A take salon wasan ya canja, bily da batai tunanin hakan daga garesaba a wannan daren duk da dai yau jinta take wani sakayau kamar an sauke mata kaya tuni jikinta ya fara tsuma, zuciyarta da jininta na wani irin tsitstsinkewa, gashi ya hanata dukkan damar da zatai ƙorafi ko magiya, juyata yake duk yanda yaso da zafafan salonsa masu rikita ƙwanya da zuciyar duk macen data mallakesa matsayin mahaɗin rayuwarta, ta rumtse idanunta da ƙarfi lokacin da yake karanto___
بِسْمِ اللهِ اللّهُمَّ جَنِّبْنَا الشَّيْطَانَ، وَجَنِّبِ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْتَنَا.
Bismil-lah, allahumma jannibnash-shaytan, wajannibish-shaytana ma razaqtana.
         (Da sunan ALLAH. Ya ALLAH! Ka nisantar da shaidan daga garemu, kuma ka nisantar da shaidan daga abin da Ka azurta mu da shi).
        Ƙanƙamesa tai da sauri jikinta na wani irin rawa cikin gigitar data risketa batare datayi hasashe ko shiyaryama zuwan wannan daren ba.
          Abinda yay matuƙar birge Jay da mamakin matar tasa shine Jarumtar da bai zatoba daga gareta, ko sau ɗaya batai yunƙurin hanashi yin yanda yaso da ita ba, ta miƙa masa dukkan ragama baki ɗaya cike da juriya da dauriya da sadaukarwa, sai saukar ɗumin hawayenta kawai yake ji da ajiyar zuciyarta tamkar zata shiɗe. (Uhumm) baiji daga garetaba dangane da ɗaga murya balle akai ga kwakwazon da duniya zata fahimci ana dai-dai wajen. duk yanda yaso yin juriya wajen binta a hankali shima dan nuna tausayinta hakan ya gagara, komai ya ƙwace masa a lissafi itaɗin kawai yake gani abu mafi daraja da martaba a garesa a wannan daren dama cikin duniyar baki ɗayanta. Ƙaunarta da tausayinta na ratsa dukannin tsoka da ɓargon jikinsa da jijiyoyi yana gaurayewa da jininsa, bashi da bakin musaltawa, bashi da kalaman kwatantawa, bashi da ƙarfin shelantawa, abinda kawai ya sani shine itaɗin tadabance, idan yace tadaban yana nufin tadaban har ƙarƙashin ruhinsa. Nutsuwar da ya daɗe yana hasashenta a zahiri da mafarkinsa daga gareta yama riski fiye da hakan.......
        A zahiri Bilkisu ta hana kanta kuka mai sauti, amma wahala iya wahala shanta take a hannun Jay, yanda kawai take fitar da numfashi ɗai-ɗai zai baka tabbacin baije da wasaba. Hawaye kam ai wasu basa direwa wasu ke gangarowa. shi kansa bai fahimci ya tafka ɓarnaba sai da komai ya lafa, Sosai tausayinta ya sake mamayesa, taimakon gaggawa ya shiga bata ta kowace hanya data dace. Yanda take kuka sosai sai hankalinsa ya sake tashi, amma haka ya daure ya gasa mata jiki dan yasan shine babban gatan dazai mata a yanzun. Sai da ya tabbatar ta samu ƴar nutsuwa sannan ya barta ta ƙarisa gyara jikinta shi kuma ya fito ya cire bedsheet ɗin da duk yaɗan ɓaci, tunani yake anya kuwa baiji mata ciwo ba?....... Da sauri ya waiga bayansa jin kukanta, zanin gadon daya fara jawowa ya saki ya nufeta dan bai zaton zata fito ba, tarota yay jikinsa yana magana a hankali dan shi kansa muryarsa gaba ɗaya ta wani dadushe kamar mai mura, “Miyasa zaki fito kinsan bazaki iya tafiya ba?” Yay maganar yana kwantar da ita akan sofa.
         Hawayen dake ziraromin na share, dan ni kaɗai nasan azabar da nakeji, babu inda kemin daɗi a dukan jikina, dai-dai da bakina ɗaci yakemin sam babu ɗanɗano, tausayin dukkan matan da aka kusancesu ta ƙarfin fyaɗe ya kuma mamayemin zuciya, shiyyasa Amina ta koma kamar wata ƙaramar mahaukaciya a lokacin.......
     “Ya isa haka kukan mana uhmyim, kinga jikinki harya ɗauki zafin zazzaɓi, ina cewa matar tawa jarumace ashe raguwace?”. Haushi maganarsa ta bani, dan haka nasa hannayena biyu ina kai masa ƙananun duka a ƙirji. Hannayen nawa ya riƙe yana ƙaramar dariya, “Oh to yi haƙuri jarumace, giwar mata, bara na duba wajen nagani bakiji ciwo ba”. Ƙanƙamesa nai ina sake fashewa da kuka, nace, “Ni dai a'a, banji wani ciwoba”.
       Jay yay murmushi kawai yana girgiza kansa, miƙewa yay ya ƙarisa cire zanin gadon ya shimfiɗa wani, rigarsa mai ɗan kauri data kai mata har cinya ya saka mata, yasa towel ya tsane mata kanta sosai gudun kar mura ta kamata, dama ga

jikinta yay mugun ɗaukar zafin zazzaɓi, tausayinta duk ya gallabi ransa, cak ya ɗauketa dan harta fara barci ya maidata saman gadon ya kwantar, so yake tasha magani amma baison tadata, dan haka ya ɗakko man zafi kawai ya shafa mata a jiki kozataji ƴar nutsuwa.
            Gaba ɗaya a hidimar Bilkisu Jawaad ya kusa cinye wannan dare, sai da ya tabbatar komai yayi masa yanda yake buƙata sannan ya samu shima ya kwanta, wani irin zafi yaji jikinta ya ɗauka, sai sauke ajiyar zuciya take a jajjere cikin barci, fuskarta ya ƙurama idanu yana kallon yanda ta ɓata fuska alamar dai bata jin daɗi har a cikin barcin. Yaɗan lumshe udanunsa ya sake buɗewa akan fuskarta yana wani ɗan murmushi, ƴar yarinyar nan itace ta nema zautar masa da tunani, “UBANGIJI mai hikima, UBANGIJI mai rahama da jinƙan bayinsa” yay maganar a fili tare

1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

11 months ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment