Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaga tama buɗe da kanta, ya leƙa babu alamar mutum, kai da ganima ba'ayi amfani da ruwaba yanzun dan bayin a bushe yake ƙamas. fitowa yay da sauru yana faɗin, “Wlhy bayanan ashe”. Shaƙosa Alhaji kokino yayi yana faɗin, “Idan baya nan dan ubanka ina yaje?!” sosai hankalin kowa ya ƙara tashi, dan ya koma musu tamkar wani zararre. Jikin driver sai rawa yake dan yaji shaƙa, Alhaji kokino ya wullar dashi gefe ya shiga ɗakin da kansa. Hakan yasa Hajiya ta sake take masa baya duk da a tsorace take. Abun mamaki duk kayan baba maigadi babu su, sai abinda ba'a rasaba waɗanda sam basu da wani muhimmanci ga mai su. A yanzune hajiya ta fahimci lallai akwai abu a ƙasa kenan. A fili tace “Mi hakan ke nufi to?”. Cikin tsananin tashin hankali Alhaji kokino yace, “kezan tambaya Nafisa, shikenan kin kasheni Nafisa, taya za'ai har wani ya kawo baƙon ido gidan nan kai tsaye ki yarda da shi harki bashi damar shigarmin ɗaki?!!”. “Wlhy Alhaji ni....” hankaɗeta yay gefe batare da ya jira ta ƙarasa faɗaba, ya fice da saurinsa yabar mata ɗakin, kuka mai tsuma rai ta fashe da shi a ranta tana mamakin miyasa baba maigadi zaiyi haka? Shekaru nawa suka ɗauka tare bai taɓa cutar da suba sai a yanzun? shin minene maigadi yasa Larai ta aikata ne? Ta tuno fitarta ɗazun lokacin da take mata tambaya akan ina taje ita da aka saka aiki? Tabbas ba cikin nutsuwa larai ta bata amsa da cewar yana ta fita sharewa ba, amma da yake bata kawo komai a ranta ba sai bata zargeta ba.

SAUDIA

           Hankali tashe Anum ta ƙwala kiran sunan Abbu da Anuwar dake falo suna jiran shayi, har rige-rige. isowa suke cikin kicin ɗin, ganin Umm-Anun yashe a ƙasa yay masifar ɗaga hankalinsu, Anuwar ya tallafo kanta ya aza bisa cinyarsa yana mai fashewa da kuka, Abbu ne yay ƙarfin halin komawa ya ɗakko goran ruwan zam-zam ya dawo, a hannu ya zuba ya shafa mata a fuska. Ta kawo wani irin nannauyan numfashi da gurnani, ƙara ɗiba yay ya zuba mata a fuskar, nanma tagwayen ajiyar zuciya ta sauke a jajjere. Matsawa yay sosai yana ambatar ainahin sunanta, BILKEESU! BILKEESU!!, BILK...... Da sauri ta buɗe idanunta tana amsawa da “Na'am BAB......” sai kuma tai shiru ta kasa ƙarasawa ta kafe Abbu da ido, saurin janyewa tai ta maida kan Anum, sai kuma ta kalli Anuwar da take a jikinsa. Cikin ɗan rawar baki tace, “Jawaad!”. Abbu da Anuwar suka kalli juna, sai kuma suka kalleta, zaune ta tashi tana raba idanu a kansu, sai kuma tai saurin dafe kanta tana faɗin, “Ya ALLAH”. Riƙe mata kan Abbu yayi yana faɗin, “Sannu, kinga tashi muje ɗaki”. Bata musaba ta yarda ya taimaka mata suka fita, sai faman lumshe idanu take saboda jiri.
     Kwantar da ita yay a saman gado ya ɗaura kanta bisa cinyarsa, umarni ya bama Anuwar ya ɗakko masa wani magani a ɗakinsa, babu jimawa Anuwar ya dawo, cayay ya zubashi a abin turare, nan danan hayaƙi mai ƙamshi ya fara tashi a ɗakin, shi kuma ya shiga karato addu'oi yana tofa mata. Cikin mintunan da basu gaza biyarba barci yay awan gaba da ita. Duk ajiyar zuciya suka sauke, kafin Abbu ya gyara mata kwanciya suka fito falo suka barta.
     Cikin ɗaurewar kai Anuwar yace, “Abbu Yah Jawaad fa ta kira”. “Naji Anuwar, amma lallai akwai wani abinda ya faru inaga, dan yanayinta yayi kama dana wadda ta dawo hayyacinta gaba ɗaya, dan a farko sunan baba zata kira ganin nine yasa tai shiru”. “Abbu to kona kira Yah Jawaad ɗin muji?” kansa ya ɗaga masa alamar eh.

★★★★★★★

         Su Jawaad na zaune a falon Alhaji babba sun rufu kan bilkisu da keta juye-juye a ƙasa da kukan kanta suna mata addu'a kira ya shigo wayarsa da Numbers ɗin ƴan saudiyyane kawai a ciki, ɗagawa yay yana miƙewa, daga can Anuwar ya gaishesa, sama-sama ya amsa masa da tambayar “ina Ummuna?”.
      “Gata a kwance barci ya ɗauketa, dan tana kitchen zata haɗa mana shayi kawai sai ta faɗi, ALLAH yasa Anum na tare da ita, sai dai abin mamaki ana saka mata ruwa ta kawo numfashi saita fara ambatar Baba saboda Abbu da ya kira sunanta, ni kuma tana kallona saita kirani da sunanka”. Lumshe idanu Jawaad yayi hawaye masu zafi suka ziraro masa saman fuskarsa, kafin yace wani abu yaji maganar Alhaji babba a bayansa. “Mi kuke ɓoyemani?”.
     Duk da gabansa ya ɗan faɗi sai ya matsa ya rungume Alhaji babba ya saki wani irin kuka mai tsuma zuciya wanda bai taɓa sanin ya iya irinsaba. Cikin matuƙar tsorata Alhaji babba shima ya riƙesa hannu bibbiyu, “Muhammad karka rikitar dani, minene ya faru dan ALLAH? Kai ne da kuka kuma?”. “Abubuwa da yawane suka faru baba, sai dai dan ALLAH kaimin alfarmar yimaka bazata a kansu daga nan zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu”. “Namaka Jawaad, ALLAH yay maka albarka”. Ɗagowa Jay yayi yana jinjina kai, Alhaji babba ya share masa hawayen, da ƴar tsokana yace, “Yau maza sun koma mata kenan?”. Murmushin ƙarfin hali kawai Jay yay masa, amma bai iya cewa komaiba.
      Ciki suka koma inda suka samu Bilkisu taɗan samu barci, tana jikin Batool da bata wuce gida ba. Kallonsu yay sannan ya kalli Bilkisun, “Baba bara mu wuce gida, shi baba zai kwana nan gidan kafin zuwa safiya idan ALLAH ya kaimu, kema Batool ki tashi kije gida dare nayi, amma dan ALLAH karki gayama su Ummah komai sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zakuji koma mike faruwa”. Kanta ta jinjina masa, tace “To ya ya za'ai da mai sunan hajiya, bai kamata a tada taba tunda yanzu ta samu barcin”. “Karki damu bara na ɗauketa kawai”.
         Cak ya ɗauki bilkisu duk da yana jin nauyin su Alhaji babba, sai dai babu yanda zaiyi idan ba haka ɗinba. Sallama yay musu ya fito, Batool dake biye da shi ta buɗe masa baya ya kwantar da ita, sannan ya koma mazaunin driver ya zauna, ita kuma ta nufi inda driver ke jiranta. Kusan tare suka bar anguwar. Sai da ya isa gidane yama tuna da Sadiq da ya baro a office, hankalinsa a tashe ya ɗauka waya yay kiransa, bugu ɗaya kuwa ya ɗaga, “Sadiq badai kana nan kana jiranaba har yanzun a station?”. “Ina nan wlhy Oga, harma dasu oga Aliyu”. “Ya salam, kayi haƙuri kaji, ka tafi gida kawai dare yayi, suma kace musu ina gida karsu damu”. Daga can Sadiq yace, “To oga”.
     Bayan ya ajiye wayar ya buɗe ya fito, sake ɗaukar Bilkisu yayi zuwa cikin gidan, ya shinfiɗeta a gadon ɗakinsa sannan ya koma motar ya ɗauka wayoyinsa. Kiran Anuwar ya sakeyi, ya tabbatar masa har yanzu Umm-Anum barci take, Abbu ya bama wayar sukaɗan yi magana sannan ya kashe, ya zauna a bakin gadonsa ya tsirama Bilkisu dake barci ido, gani yay harma taɗan rame masa a kwana biyun nan, wani tausayinta ya kamashi, matarsa ta isa a kirata jaruma a ko ina, shi harma baisan yanda zai musalta yaya ya keji a kanta ba, gadon ya hau ya rungumeta a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya a jajjere kamar wanda ya haɗiyi wuta.

          DAREN ALKAIRI KO RUƊANI?.

     Dolene mu ambaci wannan dare da sunaye masuma yawan da sukafi haka a ɓangarorin mutane masu yawa. Jawaad, Alhaji babba, baba maigadi, Maman Amina, Yaya sule, Abbu, Abu-Siddiq, Anuwar, Anum, aunty Mahfuzah, da wasu gungun mutane sun ƙare wannan dare daga farkonshi har ƙarshensa wajen miƙama UBANGIJI godiyarsu da kukansu, a tsakkiyarsa ALLAH ya bama bilkisu da Umm-Anum damar farkawa suma sukabi ayarin masu bautar ALLAH da raya wannan dare da ƙiyamul laili.
          A ɓangaren Alhaji kokino kuwa da duk mai alaƙa da wannan tunkuya wannan dare ya kasance daren tashin hankali da ruɗani a garesu. Babban tashin hankalinma shine kowa ya gaza fasalta kamannin bilkisu a gidan balle ai maganar samun hotonta, sannan baba maigadi tunda suke dashi basu taɓa tambayarsa garinsu ba, abinda kawai suka sani daga ƙauye yake, wane ƙauye? Shine basu saniba, bayan kuma ya kai kusan shekara ashirin yana musu aiki, tsabar bashi bane a gabansu ba basu taɓa bibiyar komai nashi ba a rayuwa, dan shi Alhaji kokino wani irin mutum ne da abinda ke damuwarsa shine kawai mai muhimmanci  a garesa. Bai taɓa takaicin wannan baƙar halayyar tasaba sai a yau ɗin nan.
            Tun a daren aka baza jami'an tsaro neman baba maigadi, sai dai shiru kakeji, sudai sunce suna kan aikinsu. Daga can kuma tushen tsafinsu sam an kasa ganin inda su Bilkisu suke, abinda kawai suka gani shine an fasa tukunya.
      A daren duk wani mai alaƙa da wannan ƙungiya aka sanar masa gobe akwai mitin, duk inda kake dolene ka dawo dan gagarumin mitin ne mai muhimmancin gaske.

SAUDIA

          Tunda aka idar da sallar asubahi a ƙasar Abbu ya zaunar da Umm-Anum ya zayyane mata komai da ya sani game da ita dan su gwada suga ko hankalinta ya dawo jikinta sosai. Aiko a take ta shiga rairai masa kuka da roƙon Abbu akan ya kaita wajen ƴan uwanta, tanason tagasu, ita ba zata sake kwana a saudia ba sai ta dangana da ƙasar haihuwarta.
     Da ƙyar suka lallasheta shi da Su Abu-Siddiq da su Anuwar. saboda gudun zuwan irin wannan ranar a bazata yasa Abbu bai taɓa sakaci da duk wani abinda zai taimakesa akan fita ƙasar ba idan Umm-Anum ta dawo hayyacinta, dan haka ya bata haƙuri akan ta kwantar da hankalinta zasu tafi a yau ɗin nan komai dare insha ALLAH.
           Gari na ƙarasa wayewa suka fita shi da ɗan uwansa Abu-Siddiq, abinka da manyan mutane cikin amincin ALLAH sai gashi cikin awa uku sun kammala dukkan wani abinda ya dace, jirginsu zai tashi ƙarfe sha ɗaya na agogon ƙasar. cike da farin ciki suka kirasu a waya tunkan su ƙarasa akan su fara shirin tafiya. Ai Umm-Anum da Anum sunfi kowa ɗoki, Anuwar kam ai ba'a cewa komai, kayansa ya loda na fitar hankali, a cewarsa saiya more ƙasarsa da ƙyau, ya kuma more ƴan uwansa da bai sani ba. Sudai dariya sukaita masa kawai.

__________________________________

         Da safe na tashi Alhmdllh, dan babu ciwon kan sam sai rashin jin ƙwarin jiki, ganin gidan yay ƙura naɗan tashi na fara gyarawa, amma yana shigowa sai ya hanani yace na barsa anjima Nabeelah zatazo ta gyara, yanzu muɗan sake kwanciya zuwa goma saimu fita zuwa gidan Dad zan ɗakko ɗayan wuri ɗin nan da nace na taɓa tsinta.
    Haka kawai sai na samu kaina da faɗuwar gaba mai tsananin gaske, dan kuzarin dana tashi da shi ya ida kakkaɓewa gaba ɗaya. Barcin da yaso muyi sai ya ƙauracema idanuna, harma shi yayi nasa ni idona biyu inata saƙawa da kwancewa, ga mafarkin danayi a daren jiya kafin na tashi naga yana salla nima nayo alwala sai dawomin yake a cikin rai. Da tunane-tunane na cinye nawa lokacin barcin, harma goman tayi ya farka. Kallon tuhuma yayta bina da shi akan banyi barciba, na dai fuske abina bance da shi komaiba. Tare mukai wanka, hakama shiri da taimakonsa na shirya dan duk bani da wani ƙarfin zuciya balle akai gana jiki kansa. Muna gama kimtsawa mun fito sai ga Nabeelah da breakfast.
         Zama mukai mukaci, koma nace yaymin ɗura, dan ko lauma ɗaya ban iya kaiwa bakina ba, sai da taimakonsa, daga ƙarshema sai na ringayin yunƙurin amai, dole ya ƙyaleni da iya abinda naɗanci muka fita muka bar Nabeelah a gidan akan bazamu jimaba zamu dawo, dan dama ai yau juma'a ce..

         Tunda muka bar gidan babu mai iya ƙwaƙwƙwaran motsi, nai shiru inata kallon hanya da sauke ajiyar zuciya, shima haka yay shiru idanunsa a rufe.
         Kai tsaye ya bama Sadiq umarnu akan yay horn a ƙofar gate ɗin, haka kuwa akayi, Sadiq yayi horn, sai da baba maigadi ya leƙo, ganin mune sannan ya buɗe gate ɗin.
    Kasa fitowa nai sai da ya fita sannan ya zagayo ya fiddoni, jikina ya ƙarayin sanyi, ga hawaye sun cikamin ido, narasa dalilin shiga irin wannan yanayin haka?. Yah Salman da ya fito daga sashensu daga shi sai wando da singlet yay turus yana kallonmu, boss yi yay tamkar baima gansa ba, sai nice nace, “Yah Salman!”. Da ɗan rawar baki ya amsa saboda wata muguwar harara da boss ya zuba masa, kafin ya ƙara da faɗin wani abu yaja hannuna muka shige falon da sallama.
      Mom na zaune tayi wujiga-wujiga da waya a hannunta, da alama magana ta gamayi a ciki, sai Aamilah a gefenta ta zabga tagumi. A tare duk suka kallemu da waro idanu na maɗaukakin mamaki da al'ajabi. Bayan boss na koma na laɓe, shiko ko'a kwalar rigarsa murmushi ma yaketa zubawa. Zama yayi ya kamo hannuna ya zaunar a gefensa.
       “Mom kun tashi lafiya?”. “Kuka ta fashe da shi kawai tana nunamu da hannu, sai dai tama kasa magana gaba ɗaya. “Kinga kwantar da hankalinki Mom, ba wani abune ya kawomu ba na tashin hankali, abu matata zata ɗauka mu tafi, “Miemaa tashi muje”. Kasa tashi nai dan nima jikin nawa rawar yakeyi hawaye na gudu akan fuskata, ya finciki hannuna yay ciki dani batare da ya saurari Mom ba, Aamilah dama bata iya furta komaiba dan tsorata.
    
    Tsaye Jawaad yay yana kallon ɗakin, dan an bala'in hargitsashi tamkar ɗan adam bai rayu a cikinsa ba. Lallai maganar baba ƙaura ta tabbata. juyawa yay ya kalli Bilkisu da itama tai kasare tana kallon ɗakin da mamaki na gaske. “Ina kika ajiye?”. Hannu ta ɗaga da ƙyar ta nuna masa jakar islamiyyarta da ita kaɗaice zaune a inada ta barta ba'ako motsata ba. Yana ɗora hannunsa akan jikkar Dad da basusan yana garinba ya shigo ɗakin tamkar an jehosa..............🤔😱✍


ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
 [2/12, 7:51 PM] Wasila: Bilyn Abdull 📚:
Page 56

................A yanda Dad ya faɗo mana ya sakani zabura nai baya zan faɗi, Cikin sa'a boss ya taroni jikinsa, nannauyan ajiyar zuciya na sauke wadda tai dai-dai da wadda shima Dad ɗin ya sauke yana dafe kansa. Sai kuma ya juya ya kalli bayansa da faɗin, “Kai Humaira kedai lamarinki sai ke, wlhy na zata wani abunne ya faru da yaran nan kikaimin wannan irin kira na ujila haka”.
         Cikin tsananin ɓacin tai Mom dake kallon Dad tace, “Hakama zakace Alhaji? Yanzu tsabar wulaƙanci yaran su shigo babu neman izini cikin gidannan har su wuto nan kai tsaye tsabar raini amma kace hakan ba zama wani abuba?”.
         “Haba Humaira, yanzu nan wanene baƙonki a cikinsu? Jawaad dai ɗanki ne, tun bai kai hakaba yake shiga har ɗakin barcinki ma balle cikin gidanki, hakama itama Bilkisun ɗiyarki ce, dan aure ya ɗauketa daga gidan sai kuma ya zama laifi dan ta shigo, mtsoww, dan ALLAH kisan kin girma”. Dad ya ƙare maganar da raɓata ya fice cikin ɓacin rai. Da kallo Mom ta bisa ranta na matuƙar suya, sai da ya ɓacema idonta sannan ta juyo garemu. “K yanzu bakiji kunyar zuwa gidan nan ba butulu? Wlhy nayi nadamar saninki a rayuwata, da nasan zaki zamarwa rayuwar zuri'ata tauraruwa mai wutsiya da namiki addu'ar ƙare rayuwarki cikin masifa har abada, dan da bazan taɓa amincewa kin raɓemu ba, amma ni da kaina zanyi maganinki. Kai kuma lusari shasha, yarinya ƙarama ta gama tawaiwaye rayuwarka da tsafi ka kasa ganin kowa da gashin arziƙi, inda Abdul-aziz ne ke raye ai da bakai masa hakanba, kaje ai duniyace, wanda bai zoba ma jiransa take wlh Jawaad”. Tana gama faɗa ta fice abinta tana huci tamkar wata kumurcin maciji.
         Juyawa nai na kalli boss hawaye na zirara bisa kumatuna. Fuskarsa babu wani alamar damuwa. Yama fiske abinsa tamkar ba'ai komai ba, ƙasa na sulale zan durƙushe ya taroni jikinsa, rungumeni yay cikin ƙirjinsa yana ɗan bubbuga bayana, kusan mintuna uku muna a haka, baice komaiba ni kuma inata zubar da hawaye masu zafi da ƙunar zuciya saboda kalaman Mom. “Boss dan ALLAH ka faɗamin yanda akai aurenmu ko nima zan daina tuhumar kaina da cin amana, ta yaya za'ai mijin yayata ya koma mijina rana tsaka? Bana ganin laifin Mom dan kalamanta gaskiyane a gareni, ni.......” Shiiiiii!!!!” ya faɗa yana ɗagoni da ɗan ranƙwafowa dan ya fini tsaho, ya ɗaura hannunsa saman bakinsa. Ruf kuwa na rufe bakin nawa ina cigaba da kallonsa tamkar idanuna zasu zubo ƙasa dan tashin hankali. Sassanyan Murmushi yay min da kanne min ido ɗaya, yay zipping bakinsa alamar karna sake magana. Kaina na girgiza masa hawaye na sake gangaro min saman kumatu, baki na buɗe zanyi magana ruf ya rufemin shi da nashi batare da ya bari na ƙarasa faɗaba, wata irin sumbata mai cike da sirrika masu wahalar fassara yake aikamin, tun muna tsaye bisa ƙafafunmu har hakan ya nema gagararmu mukai baya zamu faɗi, saurin riƙe bango yay muka jingina jikinsa. Ganin yana neman wuce gona da iri nai ƙoƙarin ƙwatar kaina dan na fahimci yama manta nanɗin ba gidanmu bane. Da ƙyar na samu ya barni, muka ƙurama juna idanu, tunda nake ban taɓa juriyar kallon tsakkiyar idanunsa a tsahon lokaci kamar haka ba. Ya matso da fuskarsa dab da tawa har muna shaƙar numfashin juna, wani munafukin murmushi da bai wuce laɓɓansa ba ya sakarmin, sai dai hakan bai hana dimples ɗinsa da nake tsananin burgeni loɓawa ba, ya lumshe idanu a hankali sannan ya buɗe yana ɗaura ɗan yatsansa saman laɓɓana da suka gama shan wajala a hannunsa yanzu. Cikin magana raɗa-raɗa yace, “A wasu lokutan baki yana ƙarya, yana yaudara, yana ha'inci. itako ZUCIYA abinda ke cikinta kawai take kuwwa a kansa, agaban kowa, a kuma ko ina. k wacece a gareni bakina yayi ƙanƙantar lissafa miki, wani jinin sai an tsaga ake ganesa a jini, karki zama mai gaggawa, karki zama mai wasiwasi, karki zama mai sakaci, dan bakowa bane mai ZINARIYAR ZUCIYA irin taki”. Ya ƙare maganar da ɗaura ɗan yatsansa saitin zuciyata. Kallon inda ya nuna ɗin nayi kafin na ɗago shima na kallesa, ya ɗagamin gira ɗaya da ɗan ƙyaƙyƙyafta idanunsa da suka koma sirkin jaa, “Ke ɗin ta dabance, idan nace tadaban ina nufin tadaban a kowanne daƙiƙa na bugun zuc

iya da numfashina Bilkisu”.
      Kamar wata sakarai haka na bisa da kallo harya fice a ɗakin. Gaba ɗaya ya birkicemin tunanina, kalamansa suna dai-dai da tambayoyin jarabawa masu wahalar gaske da ruɗani ga ɗaliban dake zana jarabawar ƙarshe ta barin makaranta. ‘Mike nan?’ na faɗa a fili batare da tunanin mai bani amsarba........
      Sanin hakan da nai ya sakani bin ɗakin da kallo tamkar baƙona, sai kuma na juya jiki a sanyaye na fice daga cikinsa. Idanuna akan boss da ke zaune bisa kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya suka fara sauka, sai Dad da Mom dake zaune suma kusa da juna, Yah Salman na daga can Dining zaune da waya a hannu, sai Aunty Aamilah dake jikin ƙarfen bene ita kuma a tsaye. Takawa nai a hankali gaban Dad na durƙusa, hawayene ke zarya a kumatuna masu zafi da saka ƙunar zuciya, “Dad ina kwana” ta faɗa muryarta a ɗarare. Murmushi yayi yana gyara zamansa, “Ɗiyata yau da kanki a gidan nan? Ko dai ɓatan kai kikayi?”. Hawayen da suka cikamin ido suka gangaro akan kumatunna, na ɗago kaina ina kallon Mom da girgiza ma Dad kaina. “Kayi haƙuri Dad, nasan ni ɗin mai tarin laifukace a gareku waɗanda a kullum nike cike da damuwa da kunya a kansu, Dad wlhy banci amanarku ba, har yanzu bansan dalilin da yasa kuka auramin shi ba a maimakon Yah Qaseem, Dad  inajinka a rainane tamkar mahaifina, banason nazama silar ɓacin ranka kona minti guda kai da Mom, banason ka ringa kallona matsayin tauraruwa mai wutsiya, dan ALLAH kace ka yafemin, ka samin albarka kuma, ka roƙamin gafara wajen Momy da ƴan uwana suma, ALLAH ne ya ƙaddara komai a nasarata, sai dai ya sanyaka ka zama sila, ka nunamin hanya a lokacin da mafi yawan al'umma suka rufemin tasu, ka haskamin rayuwa a lokacin da duhu ya lulluɓeta, ka zamemin gata, a lokacin da nake ƙasƙantacciya, duk wanda zaiga bilkisu a yanzu harta birgeshi kaine silar komai..........”
        Dad da yaji ƙwalla sun cika masa ido yasa hannu ya ɗaukesu yana ɗan murmushi da saurin dakatar da bilkisu, kafaɗarta ya kai hannu zai kamo sai kuma ya fasa, murya a sanyaye yace, “Haba ɗiyata ni bakimin komaiba wlhy, duk abinda kikaga ya faru a rayuwar ɗan Adam rubutaccene a littafinsa, ke yarinyar kirkice abin alfaharin kowanne uba, inajinki har cikin raina nima Bilkisu, duk kuma abinda ya faru kema ba laifinki bane namune, ALLAH yay miki albarka ya albarkaci rayuwar aurenku ya baku zaman lafiya kinji, aje aita haƙuri, karki sake yin kuka domin hakan, ina fatan dai babu wata damuwa ko?”. Bilkisu tasa bakin gyalenta ta share hawayen tana gyaɗama Dad kanta, “Ba komai Dad, shiɗin mutumin kirkine, kullum ƙoƙarinsa yaga ya ƙyautatamin, zaɓin da kukaimin ƙyaƙyƙyawan zaɓine da nake alfahari da shi, na kuma tabbata har ƙarshen rayuwata insha ALLAH bazanyi nadama ba, nagode sosai da kulawarku a gareni”.
        Kallon inda Jawaad ke zaune tamkar baya a falon Dad yayi, cikin ƙara sanyaya murya yace, “Nagode sosai Jawaad, dama bana tsamanin saɓanin hakan daga gareka, ALLAH ya ƙara muku zaman lafiya.
         Jay ya ɗan ɗago idanunsa tare da tura wayarsa cikin aljihu. Kallon ido cikin ido sukaima juna shi da Dad, irin kallon da kowa shi yasan ma'anar nasa. Jawaad ya janye idanunsa yana wani shegen murmushi da sake ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, kafin yace wani abu Mom taja wani wawan tsaki tana miƙewa tabar falon.
          Duk muka bita da kallo banda boss da ya basa abinsa hankali kwance. sai da ta gama hayewa benen Dad ya sauke nannauyan numfashi yana sake kallon Jay, “Tana cikin fushine sosai akan damuwar ɓatan Mamana, duk inda muke tunanin samun yaron nan an gaza samunsa Jawaad, dama koda bakuzo nanba ni da kaina zanje gidanku akan maganar. Ka taimakemu dan ALLAH ”.
      Kafin Jawaad yay magana Bilkisu dake share hawaye tace, “Dad wani abunne ya faru da aunty Shahudah'n?”. Kansa ya jinjina mata cike da matsananciyar damuwa ya labarta musu komai, shi dai Jay baice ko uffanba, sai Bilkisu da keta sharar ƙwalla ita da Aamilah. Daga ƙarshe ma sai ya miƙe abinsa yana kallon bilyn, “Tashi mu wuce” ya faɗa a daƙile. Kamar bily zata fasa kuka dan takaicinsa, ta buɗe baki zatai magana ya zuba mata wata uwar harara..... Tsam ta mi

ƙe tana haɗiye sabon kukan dake neman taho mata, “Dad zamu wuce”. Kallon Jay Dad yayi, “Jawaad bazaka bar mana ita ta yini ananba?”. Shiru yay kamar bazaice komaiba, sai kuma ya kalli agogon hannunsa ba tare da ya kalli Dad ɗinba yace, “Zamuje office ne”. “Shike nan to, kuɗan jirani”. Dad ya faɗa yana miƙewa.
       Jakar islamiyyar ya ɗauka yay ficewarsa batare da yacema bily komaiba.
        Da kallo kawai na iya binsa harya gama ficewa, naja numfashi ina danne zafin da zuciyata kemin, bansan miyasa boss yake hakan gasu Dad ba? Yana ƙara sakamin ruɗani da wasiwasine akan abinda naketa ƙoƙarin ƙaryatashi a zuciyata tun randa nai gamo da wallet ɗin nan...... Dawowar Dad ta katsemin tunani na, ya miƙamin leda babba mai ƙyau yana murmushi, “To ɗiyata ga tsarabarki nan, akwai kuɗinki na kayan ɗaki danai niyya sai dai hakan bata faruba, insha ALLAHU kafin kije gida zakiji alert, ALLAH ya ƙara zaman lafiya”. Hawayen da suka ziraromin na share, na durƙusa har ƙasa ina masa godiya da addu'oin fatan alkairi. “Babu komai Bilkisu. karki damu tashi kuje yana jiranki”. Jinjina masa kai nayi na miƙe, na kalli inda Aunty Aamilah take

1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

11 months ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment