Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

basa nuna maka irinta, abinda ya ƙarama farin cikin nawa armashi kuwa ganin harda matasan samarin ƴaƴan sarki masu zamani da lokacinsu a cikin gidana, kuma sun sake dani tamkar jininsu kona rayu a cikinsu ne. Abdul-raheem ne dai baida yawan fara'a da magana, amma shima bashi da wulaƙanci. Abincin kuma da aka jera musu zama sukai sukaci sosai har ana santi, Abdur-Rahaman harda cewa dama yunwarsa ya tara dan yazo yaci girkin amarya. Amaturrahman ta ɗauki filo ta saka masa waiji wai santi yakeyi. Nan take faɗa ya kaure tsakaninsu, ni wlhy dariyama suka bani, idan kana tare da triple ɗin Ummu dolene drama ɗinsu take baka dariya, shi Abdul-raheem baya magana, amma idan ya mulmulo baƙar magana ɗaya sai tayi kamar ta kar mutum dan takaici, shikuma Abdur-raham babu haƙuri saiya rama, Amaturrahman kuma zuga. Gefe kuma Ameenullah da Meenal ma cashewa akeyi, hakama Anum da Anuwar. Wannan caskalen nasu ne ya sake ƙara armashin hirar tamu da nishaɗi sosai. Kiran sallar la'asar ya saka samarin fita salla, mukuma mukayi a gida.

★★★★★★

         Ana idar da sallar la'asar Jawaad ya baro station, kai tsaye anguwar su Hudah ya nufa, sadiq yay fakin dai-dai ƙofar gidansu Amina inda Jay ya bashi umarnin tsayawa. Jay daketa rubuce-rubuce batare da ya ɗagoba yace, “Sadiq yimin sallama a gidan nan”. “To Oga” Sadiq ya faɗa yana buɗe motar ya fita. Ƙofar gidan su Amina ya ƙwanƙwasa tare da yin sallama. Kusan mintuna uku Aminar ta fito sanye da hijjab tana amsa masa. “Assalamu alikum. Malam lafiya kuwa?”. Amsa mata sallamar Sadiq yayi, sannan ya nuna motar, “Dama oga ne yace aimasa sallama”. Cikin rashin fahimta Amina tace, “Oga kuma? Wanene kuma oga?”. Batajira amsar Sadiq ba ta fito zuwa motar, knocking glass ɗin tayi har sau uku, Jawaad da har yanzun hankalinsa na akan rubuce-rubucensa ya saka hannu ya sauke glass ɗin batare da ya ɗagoba. Amina taɗan zaro ido da ɗora hannunta saman baki, “Oh wlhy bansan kai bane Yaya Jawaad, ina yini?”. Ɗagowa yay ya kalleta da amsa mata, duk da fuskar dai babu walwala bai ɗaureta tamauba, “Mama na nan?”. Kanta ta jinjina masa, “Eh tana nan ka shigo”. “Okey” ya faɗa yana maida kansa ga abinda yakeyi. Juyawa tayi ciki ita kuma domin sanarma maman.
       Sai da Jay yaja kusan mintuna huɗu sannan Sadiq ya buɗe masa motar ya fito. yana fitowa Amina na leƙowa dan sunji shiru, itace tai masa iso har cikin gidan, mama na zaune daga ƙofar ɗaki gefenta da tabarmar da aka shinfiɗa masa.
         “Lale marhabin, yau angone a gidanmu?”. Ɗan murmushi Jawaad yay ya zauna a tabarmar yana faɗin, “Ayi haƙuri Mama bamuzo mun muki ya gajiya ba”. “A'a nikam ku riƙe ban gajiyar ku, dan an mana babban ya gajiya, ɗawainiya kan ɗawainiya Jawaad baka gajiya? Anyi hidimar azumi akayi ta salla shekaranjiya kuma saiga saƙo, ALLAH ya saka da alkairi ya jiƙan mahaifa kaji, ALLAH ya azurtaku da zuri'a tagari mai albarka”. Kan Jay a ƙasa yana ɗan murmushi yace, ”Amin mama”. Amina ta ajiye masa kunun ayar da sukayi ta sake gaishesa da tambayar Bilkisu.
            Zama Jawaad ya gyara ya fuskanci mama sosai, “Mama wani taimako nazo kimin Please”. “Inajinka Jawaad, ka faɗa kanka tsaye, inhar baifi ƙarfinaba zan maka da izinin ALLAH”. “To nagode sosai Mama, nasan tun dawowar su Hudah ƙasarnan kike aiki a gidansu bayan rasuwar mijinki, sannan kaf anguwarnan da ƴan gidan nan suke mu'amularsu kawai, a zaman da kikai dasu nasan dolene zaki san abubuwa masu yawa dangane dasu, musanman ma akan duk wani ma'aikaci da yake aiki a gidan”. “Wannan gaskiyane Jawaad, dan mijina kansa kafin ya kwanta jiyyar ajali

Alhaji Ali ne ya koma masa kamar amini”. “Alhmdllh, inason sanin maigadin nan nasu ke da shi waye ya riga wani fara aiki?”. “Ya rigani farawa, danshi tunma ana gina gidan shine maigadinsa har aka gama suka tare”. “Okey, yanada mata ne?”. “Tunda nake da shi ban taɓa ganin iyalinsa ba, sannan ban taɓa jin ance yau ya tafi ganin gidaba, dan har tambayarsa nama taɓayi game da hakan lokacin inason bada wasu kaya sai nake tuntuɓarsa ko yanada iyali na haɗasu ya kai musu?. Sai cayaymin ai suna gida, daga wannan amsar ya shiriritar da zancenma gaba ɗaya. Nikuma ban sake tuntuɓarsa game da suba gaskiya”. Shiru Jawaad yayi yana nazarin maganganun Mama, kafin yaɗan huro iska da gyara zamansa. “Amma mama kin taɓa ganin wani abu dangane dashi na rashin gaskiya haka”. “Gaskiya ban taɓa ganiba, saboda shifa mutumne ma da baida yawan magana sam, kafin kaga firarsa da mutum tai tsawo akan daɗe, kodan ba abokina hirar nawa bane oho”. “Kukun gidanfa, yakai shekara nawa shikuma yana aiki dasu?”. “Shima tunda suka tare yake, a gidan na sanshi”. “Mai bayin fulawa fa?”. “Eto shine dai kafin shi kusan mutum uku sukai aiki”. “Miyasa suka bari to? Ko ba'a baku albashin daya dace ne?”. “Ai Jawaad idan ta yawan albashine babu wani mai aiki da zaiso barin aiki gidan Alhaji Ali, zan iya rantse maka a cikin dubu irinsa dake fita haƙƙin ma'aikacin gidansa da albashi mai tsoka sai an tona, sannan duk abinda masu gida zasuci kaima mai aiki zakaci, wulaƙanci da rashin tarbiyyar ƴaƴansa ne kawai matsalar ma'aikatan gidan, amma masu bayin fulawarnan da suka taɓa ajiye aiki wlhy bansan dalilinsu ba, dan daina ganinsu kawai mukai mudai koma sallama basuyi damuba”. “To amma baƙwa zaman mutuncine dasu har zasu ajiye aiki baku saniba?”. “Sosai ake zaman mutunci wlhy, dan wanda na tararma a gidan idan kaga yanda ya ɗaukeni tamkar uwa, amma daga zuwa ganin gida bamu sake ganinsaba sai wani mukaga an kawo”. “Zan iya sanin garinsu su duka biyun?”. “To gaskiya anan gizo ke saƙar dan na manta, amma zanyi ƙoƙari na tinano insha ALLAH”.  “ALLAH ya bada iko to, drivern su fa?”. “Shima basu taɓa canjawaba”. “Kafin ku wasu sun taɓa musu aiki ne?”. “Akwai ƴammata biyu da suka fara musu aiki kafin mai gidana ya rasu mu fara”. “Miyasa suka bari? Kodan an sameku?”. “Wannan bansaniba kam Jawaad, nidai kawai nasan kafinmu wasu sunyi musu aiki, amma ai nasan kaima kasan duk waɗanan abubuwan tunda kana zuwa gidan”. Murmushi Jawaad yayi, “Sanin dazan musu bazai kai na wanda yake rayuwa dasu yini da kwana ba, Mama inason naji wani abu dangane da fyaɗen Amina, tana ina?”. Mama tai ɗan murmushi, “Oh ni, yanzunan Bilkisu bazata haƙura da maganarnanba? Abinda ya faru ya riga ya faru ai sai haƙuri kuma”. “Karki damu Mama, binciken yanada amfani, dan inma ba'aiba haka za'a cigaba da wulaƙanta rayuwar yara cike da zalunci, ita kanta Miemaa ɗin a zaman datai gidan anshayin farautar rayuwarta akan hakan ai”. Cikin tsagwaron mamaki Mama tace, “Bilkisun?”. “Eh wlhy Mama”. Mama tai sagade al'ajabi na neman kasheta, ta sauke nannauyan numfashi da faɗin, “Bilkisu akwai zurfin cikin tsiya, koda wasa bata taɓa faɗiba wlhy. Saima dagewa datai akan gano wanda yay ma Amina, to ALLAH ya ƙara tsarewa, tunda dai kuma basuci galaba a kantaba ai Alhmdllh”. Ta ƙare maganar da ƙwala kiran Amina.
      Amina ta fito daga ɗakin tana amsa mata. Gurin da Mama ta nuna mata ta zauna, Jawaad ya kalleta da ƙyau. “Amina! Randa akai miki fyaɗe suwaye a cikin gidan can?”. “Yaya daga maigadi sai kuku”. “Ina mutanen gidan sukaje?”. “Yah Qaseem da Salman dai sun fita aiki, Momy kuma itada Aamilah ne suka fita, sannan Bilkisu tana makaranta ita”. “Wanene ƙarshen fita a gidan?”. Shiru Amina tayi alamar nazari, kafin tace, “Kamar Aamilah ce”. “Waye ya fara fita kuma?”. “Yah Qaseem”. “Waye ya fara dawowa?”. “Momy da Aamilah nidai na farka na gani bayan na farfaɗo” “Toke dama kina barcin rana a gidanne? Kokuwa a ranar kika fara?”. “Wani lokaci nakanyi idan nasan Mama ta fita dan karna dawo gida ni kaɗai. Da yake akwai ɗakin masu aiki sai nake shiga ciki na kwanta”. “Kafin ranar wani yataɓa miki maganar banza a gidan ne?”. “A'a

babu wanda ya taɓa”. “Mikikaci ranar a gidan? Ina nufin Abinci ko abinsha?”. “Banci komaiba bayan abincin safe, dana kammala aiki kuma saina zauna zanɗan huta, tunawa da wani sauran lemo dana ganine lokacin da zan saka wasu a fridge yasa na miƙe na ɗakkosa na shanye, daga haka ban sake sanin ina kaina yakeba sai farkawa nai na ganni cikin mummunar ƙaddara ”. Ta ƙare maganar da fashewa da kuka. Shiru Jawaad yay yana kallonta da nazarin maganarta. “Dama kina shan lemo a gidan kenan?”. “Eh inasha Yaya, dan indai ɓangaren Abincine ba'ai mana shamaki da komai, abinda sukaci muma shi mukeci babu hantara kuma ”. “Alamu sun nuna Dad baya gidan, lokacin kwanakinsa nawa da tafiya?”. “Eh kamar dai zai kai kwana goma inaga”. “Da yaushe ya dawo?”. “Kwana biyu dayin abun”. “Wane mataki ya ɗauka?”. “Da farko ya nuna damuwarsa, har ya bada kuɗi a kaini asibiti, amma daga baya daya fahimci yaransa ake zargi saima yayta faɗa ya kuma ja baya da al'amarin, yay mana korar kare da ƴan sandan da Yaya Sule ya ɗakko dan bincike”. “ALLAH ya ƙyauta to, ai kinyi karatu ko?”. “Eh nagama secondary school”. “Kin amshi result ɗinki? Kuma yayi ƙyau”. “Eh Yaya, credit ɗina taƙwas”. “Masha ALLAH, ki shirya gobe idan ALLAH ya kaimu Sadiq zaizo ya kaiki wani waje, saiki tafi da takardun, jeki abinki”. Tashi amina tayi tana masa godiya da addu'oin gamawa da rayuwa lafiya ta koma ɗaki.
     Jay ya maida hankalinsa ga Mama, “Mama bara na wuce, zata iya yuwuwa kiga na sake dawowa. nagode sosai”. “Babu komai wlhy Jawaad, ALLAH ya saka maka da alkairi, bara kaga na ɗakko maka ɗanyar awara da nayi ɗazun da safe ka kaima ɗiyata dan tana sonta sosai”. “To mama ALLAH ya saka da alkairi, ita Amina yaushe zataje mata ne?”. Mama dake murmushi tace, “zuwa satin sama zatazo insha ALLAH, kusamu yanzu kuma ku huce gajiya basai an dameku da hayaniya ba”. Murmushi kawai Jay yayi baice komaiba.

         Koda Jay ya baro gidansu Amina family House ɗinsu ya nufa, yay ƙoƙarin shishshiga ko ina ya gaishesu da musu godiyar hidima har wajen Mama Atika data amsashi sama-sama, daga baya kuma ta koma lallashinsa akan ya saka ɗan-fir'auna ya saki Shahudah kodan son da take masa ya maidata ɗakinta. Yana wannan murmushin nasa na rainin hankali yace to zaiyi hakan tai musu addu'a. Daga haka ya baro sashen nata ya leƙa yaga jikin Mama Badiyya da sai godiyar ALLAH kawai, zaman asibitin ne anyi har angaji an maidota gida, amma kullum lkitanta na zuwa dubata, su Uncle Sulaiman kuma tsaye suke akan al'amuranta basa wasa da ciwon mahaifiyar tasu da aka rasa kansa. Daga nan ya shiga sashensa ya ɗauki wani akwati ya fito suka fice daga gidan.
            Hankalinsa kuma yay gida gaba ɗaya, duk da yaso zuwa ya duba ɓaleru sai wani gefe na zuciyarsa yafi ƙwaɗaita masa wucewa gidan, koba komai yana da ƙyau yaje yaga halin da ƴar mutane take ciki, ya kamatama ace yau a gidan ya yini ya bata dukkan kulawa da tattali, amma muhimmancin aikin nan daya saka gaba dole ya daure ya fito ɗin.
       Bayan sun iso gidan Sadiq ne ya kwasar masa kayan ya bisa dasu a baya, suna zuwa ƙofar falon ya amsa, duk da yasan suwaye sukazo gidan hakan bai hanashi jin kishi ba saboda jin dariyar maza. Ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shiga falon da sallama ciki-ciki. Su Abdul-Raheem duk suka amsa masa suna miƙewa tsaye domin girmamawa a garesa, Ameen yazo ya amshi kayan hannunsa duk suna jera masa sannu da zuwa banda Anuwar da tun shigowar Jay yay mutuwar tsaye, su kansu su Abdur-rahman duk baki suka saki suna kallon Jawaad sai kuma su koma su kalli Anuwar dan yau suka fara ganin Jay su. Jin yanda falon yay wani irin tsitt lokaci gudane ya saka Jawaad da tun shigowarsa gabansa ke wata irin faɗuwa ɗagowa ya kallesu. Idonsa ƙyam ya sauka akan Anuwar tamkar wanda magana ɗisu ya janyo. A take kansa ya shiga wata irin juyawa tamkar mai ganin hajijiya. Amma kasancewarsa gwanin dakiya sai ya dake ɗin ya kafe Anuwar kawai da kallo kamar zai haɗiyesa da idanun.
          Anuwar da bazai iya jurewaba kansa ya riƙe da hannu biyu ya koma zaune daɓar saman kujera. Cikin rawar jiki Anum ta ƙarasa gabansa tana faɗin, “Bana faɗa makaba kace ƙ

arya nakeyi, kagani ko tamkar kai, Anuwar wlhy bari kaji yay bagana muryarku iri ɗaya ne shima. Anuwar da ya kasa bama Anum amsa ya wani rinƙa fisgar numfashi da ƙyar yana sake matse kansa cikin hannayensa yana jujjuyashi. “Anum kaina zai fashe, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, wash ALLAH kaina......”       
           Yanda yay maganar tamkar numfashinsa zai ɗauke baki ɗayane ya kuma tadamana hankali mukai kansa mu duka. Duk yanda nake zumuɗin son ganin yanayin dazasu shiga idan sun haɗu da juna sai hankalina ya tashi. 
       Ƙarar da Anum ta ƙwalla ce ta maido Jawaad da shima yake riƙe da kansa hayacinsa yay kan Anuwar jiki na rawa. Karɓarsa yay daga cinyar Anum ya maidosa jikinsa yana girgizashi. Sai dai ina numfashin Anuwar ya ɗauke ɗaf, Nabeelah da tun zuwan su Anuwar ta shiga ruɗani hartai masa video cikin hikima batare da kowa ya saniba ta matso tana faɗin, “Yayanmu a kawo ruwa ka zuba masa?”. Kansa kawai ya jinjina mata yana cigaba da ɗan bubbuga fuskar Anuwar da girgizasa. Nabeelah na kawo ruwar Abdul-raheem ya amsa, shine ya shafama Anuwar a fuska, wani irin nannauyan numfashi ya sauke. Jawaad ma ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi yana lumshe idanunsa ya buɗewa akan Anuwar da shima ya buɗe nasa a hankali, kallon juna suke kallo irin na ruɗani da al'ajabi, basu da suke ganin kamainin nasu da junaba hatta su Bilkisu al'amarin ya kuma ruɗar dasu, dan ita saima yanzun data gansu a waje ɗaya ta sake tabbatar da hukuncin ubangiji, dai-dai da wani ɗan ɗigon baƙi dake gab da kunnen Jay akwaishi a jikin Anuwar shima exactly yanda na Jawaad ɗin yake.......
      Jawaad ya kwantar da Anuwar jikin Ameen a hankali ya miƙe yabar wajen dan jikinsa wani irin tsuma yakeyi, idan kuma yay wasa shima hajijiyar zata iya kwasarsa ne takai ƙasa kamar yanda taima Anuwar.

       Ruwa na ɗauka da sauri nabi bayansa dan tafiya yake yana haɗa hanya, Zaune na samesa a saman gado ya riƙe kansa da dukan hannayensa biyu, saurin ƙarasawa inda yake nayi ina faɗin, “Boss lafiya?”. hannuna ya riƙo cikin nashi tare da fisgoni na faɗa jikinsa, wata runguma data nema saka ƙirjina buɗewa yay min, ƙaramar ƙarar da nai ta sakashi sassautamin, muduka muka shiga sauke numfashi, munkai tsahon mintuna biyar a haka kafin ya miƙe dani zaune sosai a bakin gadon ya zauna tare da riƙo hannuna ya zaunar dani a kusa da shi. “Wanene wannan Miemaa? A ina kika sanshi?”. ƙasa nai da kaina dan gujema kallon daya kafeni da shi. saurin ɗago fuskata yayi muna kallon juna sosai, “Please Miemaa ba batun kunya mukeba, ki faɗamin wanene shi?”. “Bansan wanene shiba nima, sai dai nasan shiɗin ɗan Umm-Anum dana zauna a wajen tane, mamarsa itace na zauna wajenta a saudiyya sati biyun nan”. “Saudia?, kina nufin daga can yazo nan?”. “ƙwaraima kuwa harda ƙanwarsa ma Anum”.
     Yace, “Innalillahi... mi hakan ke nufi? Wane irin kamannine wannan? Babu ta indafa yaron nan baya kama dani Miemaa?”. “Irin wannan ruɗanin nima na shiga a randa muka fara haɗuwa dasu, da yay magana wlhy nazata kaine, sai daga baya na iya fahimtar ba haka baneba, amma boss kafin Mamah ta rasu bata haifa maka ƙani bane?”. Yanda ya kafeni da idanunsa ya sakani yin ƙasa da nawa gabana na faɗuwa. Ya ɗora duka hannayensa saman fuskata ya ɗago, “Bilkisu Mamata ba rasuwa tayiba”. Yay maganar yana sakin fuskata ya miƙe zumbur yana girgiza kansa. saurin riƙo hannunsa nayi nima ganin zai fita a ɗakin, “Miya faru?”. Saurin dawowa yay ya sake zama. Muryarsa har sarƙewa take yace, “Inason ganin mamar yaran nan”. Bansan lokacin danai wata zabura ba nima ina faɗin, “Ganinta ba matsala bane, amma dan ALLAH da gaske kakeyi mama ba rasuwa tayi ba? To tana inane?”. Yanda nai masifar rikicewane ya sakashi kamo hannuna ya maidani inda nake ya zaunar shima yana wani kafeni da idanu fiye da ko yaushe, “Labarina mai tsahone, namiki alƙawarin a yau zakiji komai daya shafi mijinki, dan kema a yanzu kin zama ɗaya daga cikin family na, kobabu alaƙar jini a tsakaninmu ke matata ce, amma tabbas kamar yanda baba ƙaura ya faɗa Ƙaddarata tana tare da taki”. Cike da mamakin kalamansa nake kallonsa, amma fahimtar danai baya cikin hayyacin

sa, shiyyasa nai tunanin yana buƙatar yafara yin wanka yaci abinci sannan. nace, “Kayi haƙuri to ka fara yin wanka kaci abinci sannan dan magriba na gab”. Baice dani komaiba sai kallona da yakeyi har yanzun, hakan yasa na miƙe na shiga bayi. Ruwan wanka na haɗa masa, inda na barsa anan nazo na sake samunsa. Sai dai yanzu riƙe yake da kofi a hannu alamar yana shan ruwa. “Ga ruwan can?”. Idanunsa ya ɗago ya kalleni da miƙomin hanunsa na haggu. Baya naja ina maƙe kafaɗa nace, “Kaje kayi wanka bara na duba su Anuwar ɗin”. Muryarsa ƙasa-ƙasa yace, “Dama ɗazun kin kashemin waya, yanzu kuma nace kizo zaki gudu, laifi biyu kenan nasan maganinki ai, zaki biya bashinsune”.
       Saida na kusa zuwa ƙofa sannan na juyo ina faɗin, “To nima idan na kiraka a waya ka kashe shikenan ai ka rama ko?”. Miƙewa yay yana ɓalle maɓallan rigarsa, “Ai nafi ƙarfin ramawa ta haka yarinya”. Tsayawa nai ina kallonsa fuskata a marairaice, “To gani na dawo ai, amma dan ALLAH faɗamin ta yaya zaka rama? Nifa ɗazun wlhy bansan mizan baka bane shiyyasa na kashe”. “Kin tabbatar?”. Kaina na ɗaga masa. Yay murmushi kawai batare da ya sake cewa komaiba. Hakan yasa nace, “Naje dan ALLAH? Kaga an barsu su kaɗai”. Kansa kawai ya ɗagamin. Nikam tuni nai waje. Mamakine ya kamani ganin falon wayam, na leƙa ɗayan falon har zuwa ɗakina nanma babu kowa, a rikice na fito harabar gidan saina iske babu motarsu, abinda ya sake ɗaure kaina har Nabeelah babu itama. Dawowa nai ɗakinsa danna sanar masa saina iske harya shiga wankan, da sauri na ɗauki wayarsa dan tawa babu kuɗi ciki na shiga laluben sunan Ummu. Bugu biyu kuwa ta ɗaga tamkar dama jira take. Kafin tai magana nai sallama dan karta ɗauka ko shine, ko gaisheta ban tsaya yiba nace, “Ummu.......” katseni tai itama da faɗin nasan mizaki tambaya kwantar da hankalinki, Anuwar ne ya sake suma shiyyasa nace su taho gida, yana da Asthma shiyyasa gashi basu taho dako inhaler ɗinsa ba ma, sun faɗamin komai daya faru yanzu ina mijin naki shi?”. Ya shiga wanka Ummu, ya kumace zai sanarmin da komai daya shafesa”. “Alhmdllh mu dama wannan muke jira ai, saiki nutsu sosai ki fahimci komai yanda yake, ta hakane zamu tabbatar da abinda yake gaskiya, sannan nasan zai iya cewa zai biyosu idan ya fito yaji sun taho, karki faɗa masa Anuwar ɗin yana cikin wani haline, nafiso sai zuwa da safe idan ALLAH ya kaimu inma zaizo ɗin kuzo tare”. “To Ummu insha ALLAHU zanyi hakan, amma inaji a raina wlhy abinda muke zargin gaskiyane, dan yace mamarsa bata rasuba”. “Da gaske?”. “Wlhy kuwa Ummu”. “To shikenan bara na barki karya fito”.
       Ummu na yanke wayar kuwa na goge kiran na dawo ɗakin na ajiye masa wayarsa, fita na sakeyi domin yin salla nima dan anata kira.

     Koda Jawaad ya fito a gaggauce yay shiri ya fita massallaci, bai kawo komai a ransa game da rashin ganinsuba a falon, yayi zaton sun tafi salla matan kuma sun shige ciki, yanayin da yake ciki kuma ya saka bai kula da babu motarsu a harabar gidanba.
     Ana idar da salla gida ya nufo, dai-dai Bilkisu itama ta fito daga kicin tana haɗa masa abinci a d/table. Tsayawa yay kawai yana kallonta daga cikin falon...
     Jin idanu na yawo kaina ya sakani ɗagowa nima, cikin sanyin murya nace, “Ga abinci”.
     Ɗauke kansa yay daga gareni, ya tako zuwa dani ɗin yaja kujera ya zauna, “Su suna ina?”. “Sun tafi”. Na faɗa ina ƙoƙarin zuba masa abincin, Da sauri ya ɗago ya kalleni, “Bangane sun tafi ba, miyasa?”. “Takawane ya kira yace su koma gida hakanan”.
       “Aiko dolene na nabi bayansu dan zuciyata ta kasa samun nutsuwa, inason yima yaronan  tambayoyi”. Saurin zuwa nai gabansa murya a sanyaye nace, “Kayi haƙuri zuwa safiya mana, nima akwai abubuwa da yawa dazan faɗa maka game dasu wanda tunda naga kamaninka dasu naita samowa dama dan na kawosu gareka”. Murmushi yayi ya jawoni kawai ya rungume a jikinsa batare da yace komaiba.............✍

Maganar gaskiya man kaina ya gama tsiyayewa antafi yajin aiki daga yau😓😫🚶🏻.


ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAF

SAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.

Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899

sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.[1/11, 4:18 PM] HASNA✍🏻: Bilyn Abdull 📚:
Page 46

..................Tsaf muka kammala komai tare da shi, kiran sallar zuhur da akayine ya sakashi fita ya barni ina ƙarasa sauran abubuwan. Nima a gurguje na ƙarasa komai na fito yin sallar. Na idar kenan ina addu'a naji ana sallama, kafin na miƙe na fita ganin wanene Nabeelah ta shigo ɗakin.
     Murmushi mukaima juna, ta ƙaraso ta rungumeni tana faɗin “Amarsu ta ango mai daɗin suna, bara na faɗa a hankali kar yauma nai suɓutar baki ya jini ya markaɗa”. Dariya ta bani sosai, dan haka na shiga yi. “Hum ke dariyama abin ya baki, wlhy kaɗan daga aikinsa yamin casar gyaɗa indai yayanmu ne. Ina fata baya nan?”. Toilet na nuna mata da ahannu ina faɗin, “Yana ciki kuwa”. Sosai ta waro idanu waje da faɗin, “Na shiga Uku dan ALLAH da gaske kikeyi?”. Yanda ta rikice ɗinne ya sakani sakeyin murmushi, na ajiye abin sallar dana linke, “Wai ke kaɗai kikazo ne?”. “A'a ni da su Ummah ne fa, suna falo”. Ban bata amsaba na fito batare dana cire hijjabin ba.
       Tunda na fito suka zubamin idanu har abin ya bani kunya, na ƙarasa inda suke kaina a ƙasa, har ƙasa na durƙusa inai musu sannu da zuwa. Cikin fara'a suka amsamin har suna haɗa baki wajan faɗin nazo garesu. A kunyace na kuma tashi naje gabansu dab zan sake tsugunnawa Ummah babba ta riƙoni, tsakkiyarsu ta zaunar dani tare da rungumeni jikinta tana sauke wani nannauyan numfashi daya bani mamaki matuƙar gaya, itama Ummah ƙarama saita riƙo hannuna da faɗin, “ALLAH yaymiki albarka kinji, lallai ƙaunar da muke miki da gaske ta wuce ta surukuta kawai”. Ban fahimci zancen nataba nidai, na ɗago daɗan satar kallon Ummah babba da naga kamar tana hawaye. Kaina na maida a ƙasa nace, “Bara na kawo muku ruwa”.
      Ummah ƙarama da itama na ga tana share hawayen tace, “Bara mu fara yin salla ɗiyata, dan ta riskemu a hanya saboda go-slow ɗin garin nan da baya ƙarewa”. Kaina na jinjina musu tare da miƙewa nai musu jagora har cikin ɗakina. Sai da na saka musu abin salla sannan na fito dan na basu waje suyi.
            Kwance na iske Nabeelah na danna waya, na zauna kujerar dake kallonta, “K bazakiyi sallarba madam?”.

1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

11 months ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment