Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai ba, hatta su Shahudah bin bayansu sukai, yayinda wasu a cikinsu kuma suka nufu kaima iyayensu rahoto.

Dr Tayyeb na ƙoƙarin fitowa daga ɗakin da Umm-Anum take dan ya sanarma su Ummah su shiga an cire mata drip yaci karo da Ummahn dake riƙe da Anuwar. Murmushi ya ɗanyi yana ja baya ya koma cikin ɗakin da juyawa ya kalli Umm-Anum dake kallonsu da murmushi yace, “Yauwa hajiya, dama zan sanar muku ku shigo ta tashi normal Alhmdllh, dan zama mu iya sallamarku kamar”.
Kafin Ummah tace wani abu Uncle Sulaiman dake a bayansu cikin tsananin kiɗima yace, “Bilkisu!”. Da sauri Umm-Anum ta maida dubanta gareshi, sai kuma taɗan waro idanu waje itama tace, “Yayah Sulaiman!”. Cikin matuƙar rawar jiki ya afka cikin ɗakin, babbar rigarsa har tana neman taɗesa Dr Tayyeb yay azamar tarosa yana faɗin, “Subahanalillhi, Alhaji yi a hankali”.
Duk da Umm-Anum batajin ƙwarin jikinta hakan bai hanata sakkowa daga saman gadon ba. Sakkowar tata kuma tayi dai-dai da faɗowar Uncle Uwaisu da sauran ƴan gidan su Jawaad ɗakin.
“Wlhy itace da gaske!!” Uncle Uwaisu ya faɗa yana jan birki da ɗaga hannaye sama tamkar wani zararre.... Kafin wani a cikinsu ya samu damar sake tofa tashi Nabeelah ta kutso tsakkiyarsu jikinta na rawa, “Ummah! Ummah!! Ummah!! Ku kalla television, ku kalli abinda ya faru dasu Yayanmu a wajen ƙwato Alhaji babba, m....m..matsafa Ummah, wlhy matsafa suka gano acan.....”
Uncle Sadiq ne yay azamar rarumar remote ɗin television ɗin ɗakin ya kulla, anko haske dai-dai inada ake fiddo su Uncle Nasir daga cikin gidan daga su sai jajayen ƙyallaye, Jawaad na rungume da Alhaji babba yana shafa masa ruwa a fuska za'a sakashi cikin helicopter shi da wasu a cikin waɗanda aka ceto.
A take ɗakin ya ruguntsume da tsananin tashin hankali da ruɗani,
Umm-Anum ta fashewa da kuka tana dariya kuma, cikin wani ƙarfin zuciya ta ɗaga murya wajen faɗin, “Rana dubu ta ɓarawo, ɗaya tak ta mai kaya”.
A take ɗakin yay tsit, suka juya gaba ɗaya suna kallonta a wani irin yanayi mai wahalar fassara a fuskokinsu................✍


Nima dai kam na tsinci kaina a yanayin har takai alƙalamina da faɗuwa a ƙasa batare da na shirya hakanba😳🚶.


Kuyi manegi babu editing yau🤒🚴🏼




ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
[2/12, 7:52 PM] Wasila: *_ƘWAI CIKIN ƘAYA!!_*


Bilyn Abdull ce


Page 60


_ASSALAMU ALAIKUM MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR... 🙋🏿‍♀️🙋🏿‍♀️INA KUKE NE? 🔊🔊KU MARMATSO, DOMIN ZAMAN JIRA YA KARE, HAZIKAN MARUBUTAN NAN DA SUKA HADA HAZAKA DA KAIFIN TUNANI SUN SAKE ZAGE DAMTSE SUN ZO MU DA WASU SABBIN SALON RUBUTUN SU, WADANDA ZASUWA’AZANTAR, SU NISHADANTAR, KANA SY DILMIYA KU A KOGIN KAUNA, BASU TSAYA ANAN BA SALON RUBUTUN SU YA SAKE ZUWA DA SABBIN TSARE TSARE NA DARUSSA DABAN DABAN, DA KUMA HANYOYIN GYARIN JIKI DA WAJE._

_KADA KU MANTA MARUBUTAN ZAFAFAN DAI SUNE WADANDA SUKA YO MUKU HAR KASHI BIYU A SHEKARAR 2020 DATA GABATA,: WUTSIYAR RAKUMI DA GUDU DA WAIWAYE NA BILYN ABDULL. 2-DAURIN BOYE DA ALKAWARIN ALLAH NA SAFIYYAH HUGUMA.3-BURI DAYA DA QAUNAR MU NA MAMUH GEE-4- SAUYIN KADDARA DA DAURIN GORO NA HAFSAT RANO. SAI 5-KAI MIN HALACCI DA IGIYAR ZATO NA MISS XOXO.._

_A WANNAN SABUWAR SHEKARAR TA 2021 MA HAZIKAN MARUBUTAN SUN SAKE DAWOWA DA WASU SABBIN DA’DADAN LITTATTAFAN NASU:_

_1_

_* SAFIYYAH HUGUMA* MARUBUCIYAR KUNDIN KADDARA DA ABADAN TAZO MUKU DA SABON LITTAFIN TA MAI SUNA: *(SIRADIN RAYUWA)💜*_

_2_

_*HAFSAT RANO* MARUBUCIYAR GUGUWAR SO DA RUHI DAYA, TA ZO DA SALON NATA LITTAFIN MAI SUNA: *(ABINDA KE CIKIN ZUCIYA..*)💘_

_3_

_* MAMUH GEE* MARUBUCIYAR TARAYYAH DA EZNAH, TAZO DA SABON ZUWA MAI SUNA: *(MIN QALB)❤️.*_

_4_

_*MISS XOXO* MARUBUCIYAR NAUFAL DA SAIFUL-ISLAM, TA YUNKURO DA WANI MAI SUNA: *(KIBIYAR AJALI)*💜_

_5_

_SAI MARUBUCIYA *BILLYN ABDUL* WADDA TAYO MUKU KWAI CIKIN KAYA, DA CIKI DA GASKIYA TA YINKURO DA WANI MAI TAKEN: *(YANKAN BAYA)*💝_

_RIGIJI GABJI DUKKAN WADANNAN LAGWADAR DADADAN LITTAFAN BIYAR ZASU ZO MUKU NE INSHA ALLAHU AKAN FARASHI MAI RAHUSA KAMAR HAKA;_

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*+234 903 234 5899*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

*09033181070*

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR🔥



Page 60

...............Umm-Anum na kuka tana dariya duk a lokaci ɗaya ta nuna tv'n da yatsanta manuniya, cikin wani ƙarfin zuciya ta ɗaga murya wajen faɗin, “Rana dubu ta ɓarawo, ɗaya tak ta mai kaya”.
        A take ɗakin yay tsit, suka juya gaba ɗaya suna kallonta a wani irin yanayi mai wahalar fassara a fuskokinsu. Kowa ya gagara cewa komai sai kallonta kawai da suke. Ta share hawayen da suka gama wanke mata fuska tana kallon Ummah babba. “Mariya a kaini wajen baba”. Da ƙyar Ummah babba ta iya gyaɗa mata kai a hankali. Bata ƙara cewa komaiba ta gyara mayafin jallabiyar ta data naɗa tamkar yanda larabawan Saudia keyi, Batool ta ɗakko mata takalmanta zuwa gabanta, dafa Batool ɗin tayi ta saka dan ƙafarta ciwo take mata kaɗan-kaɗan, tun jiya bata gama saki ba har yanzun.
        ta maida dubanta ga su Uncle Sulaiman dake tsaye tamkar sojoji, har yanzu babu wanda ya iya gaskata ruɗani da al'ajabin da idanunsu ke gani a zahiri da magiji. Hannayenta🙏🏻 ta haɗe waje guda tana ɗan murmushi, “Ku gafarceni, ganin Mahaifina a yanzu gareni yanada matuƙar muhimmanci”. Bata jira amsarsu ba ta raɓasu ta wuce abinta Batool da Anum da Nabeelah sukabi bayanta.
 
              Da kallo suka bita tamkar wasu wawaye harta fice ita da zugarta. Ummah ƙarama da babba suma sukai yunƙurin bin bayansu. Uncle Sulaiman ne ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, cikin sanyin jiki da rawar murya yace, “Hajiya Mariya a ina kuka samu Bilkisu? Tun tsahon wane lokaci kuma?”. Kanta ta girgiza masa tana share guntun hawayenta itama, “Bani da ikon amsa waɗan nan tambayoyin Alhaji Sulaiman, inaga mu bari har sai lokacin da Yayah taso hakan da kanta, na tabbata zatazo ta sameku har gida insha ALLAHU. Mun barku lafiya”. Ta ƙare maganar da kama hannun Ummah ƙarama suka fice suma.
             “Uncle wacece ita ɗin wai?”. Shahudah da idanunta ke lullumshewa saboda hajijiyar da take gani ta tsananin tashin hankali ta faɗa tana dafe bango. Saurin ruƙota matar Uncle Sadiq tayi jikinta na rawa itama. “Shahudah!!” ta faɗa daɗan ƙarfi ganin jikin Shahudah ya fara saki alamar neman suma takeyi itama. Ruɗewa ɗakin ya ƙarayi, masu share hawaye suka ƙara ƙarfafa kukansu da sauti, yayinda wasu suke zubewa ƙasa daɓar tsabar shiga ruɗani da abinda ake nunawa har yanzu daga gidan tv.

__________________
  STATION
_____________

                Da taimakon Jawaad da Qaseem aka fita da Mom zuwa mota, Qaseem ya shiga baya ya riƙeta yana kuka da kiran sunanta da roƙon karta tafi ta barsu, “Mom Please ki tashi, dan ALLAH karki tafi ki barmu muna sonki, idan kika tafi abin zai mana yawa Mom, idan kika tafi wa zamu kalla muji daɗi”. Ya ƙare maganar da kife kansa bisa fuskarta yana cigaba da kuka, shi kansa bai taɓa sanin shi rago bane mai rauni irin haka ba sai a yau, gani yake kaf duniya babu wanda ya kaisa shiga ruɗani da tsananin tashin hankali.
     Har Jawaad daya ja motar ya fice daga station ɗin Qaseem nata kuka rungume da Mom. A haka suka isa General hospital, inda suka tadda ƴan jarida da jama'ar gari cike anan ma, har takai da ƙyar ƴan sandan da aka zuba ke control ɗinsu. Burin kowa yaga gawarwaki da mutanen da aka ƙwato wajen su Dad. A haka dai aka samu shiga da Mom ciki da ƙyar. Darajar waɗanda suka kawotan yasa akai mata amsar gaggawa da miƙata wani ɗaki.
         
         Motar su Umm-Anum na shigowa asibitin ana shiga da Mom ciki, gurin a cinkushe yake da mutane, hakan yasa suka rasa hanyar da zasubi su shiga balle susan ta inda zasu fara. Aunty Batool ce tai tunanin kiran Jawaad, dan haka ta ciro wayarta daga bag ta fara nemansa, harta tsinke bai ɗaga ba, bata gajiba ta sake kira, nan ɗinma dai harta tsinken bai ɗagan ba. Kanta taɗan dafe zatai magana sai idanunta suka sauka akan Jawaad dake magana da wasu police su uku da alama suna masa bayani ne akan yanayin da asibitin yake ciki na cikar mutane da ƴan jarida.
     “Alhmdllhi ga yayanmu ɗin canma ai”. Dukansu inda take kallo suka kalla, kafin wani ya samu yin magana Anum da Nabeelah suka nufi inda yake, sai dai kafin su ƙarasa aka dakatar dasu a tsawace. Bayani Nabeelah keson ma police ɗin daya tsaidasun amma yaƙi saurarenta, hakan yasa ta fara masa magana da tsiwa dan sun roƙesa amma yana neman cin zarafinsu ma. Hayaniyarsu ta jawo hankalin Jay ya juyo. A bazata yaga ƙannensa, ya ɗan ɗaura hannunsa na dama saman goshinsa da keyi tamkar zai tsage saboda azabar ciwon kai. Da sauri ya kalli police ɗin da suke tare yana nunasu Anum ganin wancan ɗan sandan da suke tare ya ɗaga hannu zai mari Nabeelah amma ta duƙe. “Kaga, cemasa ya barsu suzo”. Amsa masa yay da to, yana nufar inda su Nabeelah suke, yay saurin riƙe hanun ɗan sandan daya sake ɗaga hannu zai mari Nabeelah dan bakinta yaƙi mutuwa saboda haushin baƙar maganar daya faɗa musu dan sunce su ƙannen Jay ne wajensa zasuje. A harzuƙe ɗan sandan ya juya zaiyi magana sai yaga ogansu, saurin gyara yanayinsa yay zai masa bayanin abinda ya faru tsakaninsa da yaran sai yaji ogan nasa yacema su Nabeelah suje wajen Jay ɗin. “Oga kasan mi sukayimin kuwa?”. Murmushi yay masa da ɗan buga kafaɗarsa, “Komi sukai maka kayi haƙuri. ƙanen yallaɓai Jay ne”.

          Da kaushin murya Jawaad daya tsare su Nabeelah da rikitattun idanunsa yace, “Miya kawoku nan?”. “Uh...Uhm Yayanmu bamu kaɗai bane, Ummu ce tace a kawota wajen Alhaji babba”. Nabeelah ta bashi amsa tana laɓewa bayan Anum idanunta cike da tsoro.
        Da sauri Jay ya hau waige-waige, saiko idanunsa suka sauka akan Batool da su Ummah da suma kallonsu sukeyi. Batare da ya sake cewa komaiba yabar wajen zuwa inda su Batool ɗin suke.

          Umm-Anum data rage a mota bata fitoba hango Jay ya nufosu ta fito da ƙyar dan jikinta duk babu daɗi, kallo ɗaya zakaima idanunta kuma kasan tayi kuka sosai, dan sun kumburi sun kumayi jaa.
       Sauri riƙeta Jawaad daya ƙaraso yayi, ya taimaka mata ta tsaya akan ƙafafunta sosai tana sauke ajiyar zuciya, “Ummuna miyasa kuka fito? Kallafa ƙafarki ta kumbura?”. Maimakon ta bashi amsa sai tambaya ta jefa masa, “Ina Bilkisu?”. “Amma Umm......” “Ni dai ina yarinyata nace maka?”. Numfashi ya sauke da ɗan ƙarfi yana lumshe idanu sai kuma ya buɗe lokaci ɗaya, “Tana ciki Ummuna, sun saka mata drip ne saboda ta suma acan, amma inama ganin ƙila ta farka yanzun dan tun ɗazun Dr Bello ya sanarmin ta farfaɗo”. “Alhmdllh, babana fa”. Yanzu kam ɗan murmushi ya mata da sumbatar hannunta, “Shiyyasa naga idanunki sun kumbura ko Ummuna, kinyi kuka?”. Kansa ta dungure tana ƴar hararsa, yay murmushi da kama kunnuwansa alamar na tuba.

★★★★

         Sun fara shiga ɗakin da aka kwantar da Bilkisu, kamar yanda Jawaad yay hasashe sun iske ta farka, tana zaune jingine da filo wata Nurse na bata abinci da takeci da ƙyar dan warin asibitin yay masifar addabarta, farkawarta amanta biyu saboda warin asibitin, yanzu ma Dr Bello ne da kansa yasa aka kawo mata abincin dan taci tasha magani kafin Jay yazo ya ɗauketa kamar yanda ya sanar masa.
         Gaba ɗaya tayi wani zuru-zuru, idanunta sunyi masifar kumbura da ƙanƙancewa, sannan sunyi jajur a ciki. shigowar su Jay yayi dai-dai da zaburarta ta sakko a gadon saboda tahowar amai, Nurse ɗin ta ajiye tray'n abincin da sauri tana ƙoƙarin kamota amma tuni takai toilet. Duk rufa mata baya sukai cikin tashin hankali, sai dai duk a ƙofar bayin sukaja birki, Jay da Nurse ɗin ce kawai suka sami damar shiga. Sosai hankalin Jay ya tashi ganin yanda bily ke yunƙurin amai tamkar zata amayo hanjin cikinta, Nurse ɗin na riƙe da ita tana jera mata sannu da shafa bayanta. Matsowa yay kusa da ita shima ya ruƙo hannunta. Da ƙyar aman ya tsagaita, ya taimaka mata da kansa ta wanke bakinta, sai numfashi take saukewa a wahale, kwantar da ita yay a ƙirjinsa tausayinta mai tsanani yana ratsashi, a ƙasan ransa kuma tunani yake ‘mi taci haka?’.
        “Ka kaini gida, banason warin asibitin nan”. Ta faɗa murya can ƙasan maƙoshi tana sake lafewa a jikinsa da shaƙar ƙamshin turarensa da yake ɗan dawo mata da nutsuwarta. Ɗago kanta yay ya saka fuskarta cikin tafukan hannunsa suna kallon juna, “Mi kikaci haka?”. Ya faɗa cikin tashi daskararriyar muryar yana raba idanu akan fuskarta tamkar zai gano abinda ke damunta anan ɗin. Matsawa tai zata sake kwanciya a jikinta tana faɗin, “Banci komaiba, warin asibitinne banaso nidai”.
            “Jawaad yaya dai?”. Ummah ƙarama ta faɗa kafin ya samu damar sake tambayar bily.

         Da sauri naja baya daga jikinsa dan na manta bafa mu kaɗai bane, bango na dafe saboda jikina babu ƙarfi. Ban iya fahimtar amsar daya bataba dan hankalina baya a garesu, tadai riƙe hannuna ta kamani muka fita sunata jeramin sannu.

       Jay da duk damuwa ta sake lulluɓesa ya fita domin son ganin Doctor dan yazo ya duba Bilkisun ko akwai wata matsala data sakata aman ne.
      A ƙofar ɗakin sukaci karo da Dr Bello da Nurse ɗin dake tare da bilyn, da alama itace taje tai kiransa. Fuskar Dr Bello washe da murmushi ya miƙama Jay hannu, “Dadyn baby ai bansan ka shigoba ma”. Duk da Jay bai fahimci sunan da yay kiransa da shiba sai yaɗan saki fuska kaɗan amma ba murmushi yayi ba, yadai sassauta ta daga cinkushen da take. Doctor bai gajiyaba ya sake faɗin, “Dama sister ce ke sanarmin madam na amai, wannan babyn da alama soja ne, dan nakula zai wajiga madam da yawa tun yana ɗan ficit”. Yanzunkam dai sosai Jay ya kallesa da alamar tambaya, sai dai ya gaza cemasa komai. Lura da hakan da Dr Bello yayne ya sakashi yin murmushi suka ƙarasa shiga ɗakin da Bily take, inda su Umm-Anum suka zagayeta sunata jera mata sannu, kanta na'akan cinyar Ummah babba.
      Sai da ya gaisa da su sannan yayma bilyn sannu, kanta taɗan ɗaga masa kawai alamar amsawa, ya sake kallonta da murmushi ganin tanata faman rufe hannci, juyawa yay ya sake kallon Jay dake tsaye hannayensa duka a aljihu shima yana kallon bilyn. “Congratulations dear Friend, madam na ɗauke da babien mu ɗan sati shida. Ma'ana tana ɗauke da ciki ɗan wata ɗaya da sati biyu”.
          Babu shiri Bily ta janye hannunta daga saman hanci tana waro idanu waje, ganin duk yanda suka zuba mata ido suna murmushi yasa taji kunya, saurin juya baya tayi taja gyalen Ummah babba ta rufe fuskarta ƙirjinta na wata irin bugawa da sauri-sauri.
        Su Ummah kam fuskokinsu washe da murmushi sunata jerama UBANGIJI godiya da kirari, gaba ɗaya sai damuwar da suka yini da ita ta ɓace ɓat. Ubangayya da tunda aka fara cakwakiyar nan babu mai cewa yaga haƙorinsa a waje a take ya saki wani lallausan murmushi yana mai lumshe idanu, duk wata damuwarsa sai yaji ta gudu, farin ciki ya mamaye gurbinta. Dariyar su Ummah ce ta sakashi buɗe lumsassun idanunsa dake jajur, yay murmushi a karo na biyu yana girgiza kansa ganin iya shegen da Anuwar keyi shi da Anum da Nabeelah. Ya dage sai rawa yake yana waƙar larabawa shi a dole yayi ɗa ko ƴa, yayinda Anum da Nabeelah ke tayashi.
     Cikin dariya Ummah ƙarama tace, “Yarona dama haka kake da iya shege ina ganinka wani ustazu?”. Umm-Anum dake murmushi tana kallon Bily da duk abin nan da ake taƙi kallon kowa tace, “Kaɗanma kika gani indai Anuwar ne, dama can Ustaz ɗin da babu Ustazai ne”. Dariya su Ummah da Batool da Dr Bello suka sanya, Jay dai murmushine har yanzu a saman fuskarsa, kunyar iyayensa ta sakashi dakewa abinsa yanata dai kallon bilyn ta ƙasan ido.
     Aunty Batool tace, “Lallai ta maganar Doctor babyn nan namu soja ne, inba soja ba wannan gumurzu da akashawo amma ko gezau baiyiba saima nuna kansa da yayi wa duniya”. Sosai nanma suka sanya dariya, Dr Bello yace, “Gaskiyarki Sister kam, ALLAH dai ya inganta, kema saiki daure kiyi aure ki samo mana namu”. Duk kallon Doctor sukai banda Jay da Bilkisu dake ɓoye, Batool ta zuba masa harara. Shiko murmushi yayi abinsa yana sosa ƙeya waishi yaji kunyar su Ummah. Cike da tsokana Anuwar yace, “Su Aunty Batool kodai-kodai gidan Doctor zamu ɓulla ne?”. Duka takai masa ya kauce yana dariya, Doctor Bello ya kama hannun Anuwar yana faɗin, “Yauwa ɗan ƙanina tayani yaɗa manufa”. Yay maganar suna ficewa daga ɗakin.
          “A to mukam wannan indai na ƙwaraine ai bashi zamuyi Batool”. Umm-Anum ta faɗa tana kallon Batool ɗin. Ƙasa tai da kanta batace komaiba. Ummah ƙarama tace, “Yayah wlhy bansan ko Dr Bello da wata matsalaba, mutum kirkine ɗan manyan mutane, sai dai babansane ɗan rigima, amma shima bawai ta ashsha ba”. “Ato Alhmdllh, bara nazo na fara shirin aurar da ɗiya kenan”. Murna Nabeelah da Anum suka fara, ita dai Ummah babba batace komaiba, hakama Jay uffan baice ba, yayi kamarma baya a ɗakinne, idonsa gaba ɗaya yana akan motsin matarsa.

★★★★★★★

              Koda suka baro ɗakin da bily take da sallama daga Doctor gaba ɗaya sai suka nufi ɗakin da aka kai Alhaji babba, daga shi sai baba maigadi a ɗakin, jikin Umm-Anum har rawa yake, sai da Batool ta riƙeta, cike da sassarfa ta ƙarasa gaban gadon da Alhaji babba ke a ƙwance an saka masa na'urar taimakon numfashi, sosai jikinta ke ɓari, ta durƙushe ƙasa tana kamo hannunta cikin nasa da fashewa da kuka tana kiran sunansa. “Baba kaine haka? ka tashi baba kaga BILKEESUN ka, nadawo gareku baba, baba ka buɗe idanunka ka kalleni dan ALLAH kozanji sassauci babana farin cikina” ta ƙare maganar da ɗaura kanta a gefen hannunsa tana kuka mai tsuma rai. Suma su Ummah hawayen sukeyi har Bily, Batool da Nabeelah da Anum. Anuwar ma hannu ya saka ya ɗauke nasa ƙananun hawayen tare da ƙarasawa ya durƙusa ta ɗayen gefen kakan nasa daya fara gani a yau karan farko na rayuwarsa, Anum tazo kusa dashi ta tsugunna itama tana ɗaura hannunta akan na Anuwar dake riƙe dana Alhaji babba. Jawaad dai yana kallonsu, sai dai bazaka taɓa fahimtar yanayinsa ba, kamilar fuskarsa ta shanye komai.
      A hakanli Alhaji babba yaɗan motsa hannunsa dake riƙe a cikin na Umm-Anum, saurin ɗagowa tai tana kallon hannun, ya sake motsashi a karo na biyu tare da kansa. tsitt ɗakin yay duk suka zuba masa ido. Sake motsawa yay fiye dana farko, sai kuma ya buɗe idanunsa a hankali ya sake maidawa ya rufe saboda nauyin da sukai masa, sake buɗewar yayi a karo na biyu, dishi-dishi ya fara hango Jawaad dake tsaye daga can ƙofar ɗakin yana facing nashi, ya ɗan kafesa da kallo tamkar dai yanason gano wanene?. takowa Jay yay a hankali zuwa gaban gadon, ya tsaya kusa da Umm-Anum tare da ɗan ranƙwafawa yanama Alhaji babba murmushi, hannu ya saka da kansa ya cire masa na'urar da aka saka masa. cikin magana a hankali yace, “Tsoho mairan ƙarfe!”.
     Karan farko Alhaji babba yay wani ɗan murmushi kaɗan da sake motsa hannunsa sai ya jisu duka biyu an riƙe. “Babah!” Umm-Anum ta kira sunansa cikin sanyin murya. Cikin wata irin faɗuwar gaba Alhaji babba ya juya saitin inda yaji muryar da bazai taɓa mantawaba a rayuwarsa, to kodai mafarki yakeyine har yanzun? Ya ayyana a ransa yana ware idanu akan Umm-Anum dake kallonsa tana murmushi da hawaye.
       Ya mata kallon kusan minti ɗaya kafin ya sake juyowa ya kalli Jay, sai kuma ya kalli Anuwar da Anum, ya sake maidawa ya kalli Ummah ƙarama da babba da Batool, Bilkisu da Nabeelah, cike da ƙarfin hali ya yunƙura zai tashi zaune dan ba'a ƙaramin ruɗani ya tsinci kansaba. Saurin riƙesa Jay yayi yana girgiza masa kai. Alhaji babba ya kalesa cikin muryar dake nuna bashi da lafiya yace, “Jawaad mafarkin dana sabane ko? Yo inba mafarkiba a ina nikam zanga mahaifiyarka ido da ido irin haka? Dan ALLAH kaga karka tadani a barcin nan barni nayi tayi ko ALLAH zaisa itama Rahmah da Maryam da Amina da Adamu zasuzo gareni duk mu haɗu anan”.
          “Baba ba mafarki ka ke ba, Bilkisun ka ce a gaske gabanka, nice na dawo gareku, ni ce ban mutuba baba”. Umm-Anum ta faɗa tana rushewa da kuka. Ai yanzunkam babuma wanda yaga sanda Alhaji babba ya tashi dingangan zaune yana riƙo hannun Umm-Anum cikin nasa duka, jikinsa sai rawa yakeyi, hannunsa ya ɗaura saman idonsa ya murza, ya kai kuma kan fuskarta ya shafa. Tabbas ba mafarki yakeba Bilkisun sa ce a gabansa, bilkisun daya rasa kusan shekaru ashirin dashida, bilkisun daya fidda rai da gani a wannan duniyar dukda yana tsananin ƙwaɗayin hakan. “Bilkisu dama kina raye?”. ya faɗa da tsananin rawar murya.
         “Ina raye baba, ganima ALLAH ya ƙaddara sake haɗuwarmu, na godema UBANGIJINA daya saka ka kasance mai tsahon ran da zan dawo na tadda, da ace na dawo baka raye bazan taɓa daina yima mutanen nan munanan addu'oi ba har randa numfashina zai yanke”. Fashewa Alhaji babba yay da kuka, ya kamo kan Umm-Anum ya ɗaura saman cinyarsa ya rungume yana sake fashewa da kuka mai ban tausayi da tsuma rai.

             Da ƙyar Jay da Doctor suka samu damar lallashin Umm-Anum da Alhaji babba, harma dasu Ummah dasu Bilkisu, sai dai fa Alhaji babba ya tubure akan ya warke a sallamesa ya tafi gida, anyi lallashin duniya yace sam baisan wannanba wlhy shifa bazai kwana a asibitin nanba koma mi za'ayi.
     Ganin ya rikice musu harda hawaye Jay yace Doctor ya basu sallama kawai, sai su sami likitan dazai dinga zuwa gida yana dubashi babu damuwa. badan Doctor yasoba ya basu sallama.
       Jay da Anuwar ne suka kama Alhaji babba aka kaisa har mota, yayinda itama Ummah ƙarama ke riƙe da Bilkisu da keta dauriya da ƙarfafa jikinta dukda batajin daɗinsa sam, sai dai ƙasan ranta wani irin farin ciki takeyi da barin asibitin da zasuyi. Motar ta musu kaɗan, dan haka suka shiga ta Aliyu da suka iso asibitin babu jimawa suma dan an ƙaro jami'an tsaro cikin asibitin saboda mutane dake neman kawo ruɗani, acewarsu sunason suga gawawwakin da waɗanda aka

1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

11 months ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment