Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Wayar ta janye daga fuskarta tana tashi zaune, “Aini shehi yamin”. Nace, “Okay to acigaba da gashi”. Dariya ta sanya tana ƙoƙarin komawa ta kwanta, ni kuma na miƙe dan naje na shirya abincin a dining, harna miƙe na dawo na sake zama. “Nabeelah niko kinga abinda na gani kuwa? Saifa naga kamar su Ummah kuka sukai?”. Kallona tai tana murmushi, “Nima dai ba komai na saniba akai, amma tabbas akwai wani abu da suka sani game dake wanda na lura shine dalilin kukan nasu”. Babu shiri na koma na zauna a kujerar sosai ina faɗin, “Game dani kuma Nabeelah?”. “Lah bafa wani abu mara ƙyau bane naga kamar kin ruɗe”. Ajiyar zuciya naɗan sauke duk da bawai na gamsu da amsar tata bane, na sake miƙewa na nufi kitchen. Abincin dana shirya a kuloli na fara fiddowa, ganin hakan Nabeelah ta taso ta tayani muka shirya komai. Falon muka sake dawowa muka zauna, Nabeelah ta fara zubamin surutu, nidai nawa murmushi ne, wani gurin kuma nakan jinjina wautarta sosai. zamanmu baifi da mintuna goma ba su Ummah suka fito, miƙewa nai ina musu sannu. Fuskokinsu ɗauke da murmushi suka amsamin suna zama. Ina fara zuba musu ruwan dana ajiye ya shigo falon da sallama.
            Tsokanarsa suka shigayi da faɗin ga ango ga ango. Yay murmushi mai sauti cike da girmamawa yace, “Sannunku da zuwa Ummahs, har ina tunanin kiranku a waya sai kuma na duba naga nama bar wayar a gida”.
     Ummah ƙarama tace, “Wlhy Go-slow ne ya riƙemu Son, amma da tuni mun iso ai”. Ledar hannunsa na amsa ina masa sannu murya ƙasa-ƙasa, ban jira amsarsaba ko kallonsa nabar wajen.

        Jay daya ɗan bita da kallo ya zauna yana amsa gaisuwar da Nabeelah ke masa, kafin ya gaida iyayen nasa da keta tsokanarsa yayi ƙiba a kwana uku kacal. Shidai murmushi kawai yake musu bai iya cewa komai.
     Nabeelah data san halin kayanta kuwa tuni ta miƙe tabi bayan Bilkisu dake kitchen tana wanke fruits ɗin daya shigo dashi. Tare suka ƙarasa suka fito.
           
      Koda nazo na sanar musu cewar ga abinci sai Ummah babba ta hau faɗa akan miyasa zan

fara girki, ai sai nayi sati biyu sannan. Murmushi nidai nakeyi kawai kaina a ƙasa, shima dai banji yace wani abu ba. Sai da ta gama faɗanne sannan naji ya bata haƙuri da cewar, “Ummah karki damu ai gara tayi, dan bazai yuwu muyita wahal dake ba”. Ummah tace, “Minene wani abin wahala anan, aida nasan zatai girkin dana kira nace karma ta fara”.
         Shidai ya lallaɓasu akan suzo suci abinci, daga baya saita cigaba da faɗan. Dariya Ummah ƙarama da Nabeelah sukayi jin furcinsa, nima dai saida na murmusa. Ni da Nabeelah muka zuzzuba musu abincin yanda kowa yake buƙata, Nabeelah ma ta zuba nata ta zauna, niko sai nai ƙoƙarin barin wajen, hannuna Ummah ta kamo ta zaunar dani a kujerar kusa da ita, “Maza zauna kici abinci, kina nufin mu kaɗai zakima wannan wahalar”. Kaina a ƙasa nace, “Ummah ai na ƙoshi, in ALLAH ya kaimu anjima zanci”. Bata saurareni ba ta hau ɗiba da cokalinta ta fara bani, bazan iya mata musu ba, dan haka dole na ringa amsa a kunyace, Nabeelah nata mana dariya ƙasa-ƙasa dan tana tsoron yi yaci ƙaniyarta. Dana ɗago saina kamashi yana kallonmu, hakan yasa na ƙara takura sosai. Ummah bata barniba saida ta tabbatar cikina yayi ƙat da abincin nan, suma sukaci sosai suna santi da sakamin albarka da yaba ƙoƙari na.
     Bayan mun kammala Nabeelah ta tayani gyara wajen, shi kuma ya zagaya dasu lungu da saƙo na gidan, inajin yanda suketa yaba gidan da jinjina halin girma irin nasu Ummu, a yanda suka hidimtamin babu dangin iya babu na baba sun cancanci yabawa mai girman gaske da ƙyaƙyƙyawar addu'a.

            A falon Jawaad su Umma suka yada zango, inda suka shiga tattaunawa akan batun Bilkisu da kuma kamannin Anuwar dana Jay. su Ummah sun dage akan cikin satin nan zasuje saudia domin ganin Umm-Anum, dan sunce lallai sunaji a jikinsu kamaninsa da Anuwar yafi ƙarfin kamanni, sunce zasu sanarma Alhaji babba dan su ɗunguma gaba ɗaya su tafi.
     Murmushi Jay yay yana gyara zama da fuskantar iyayen nasa. “Ummah banƙi ta takuba kam, amma sai nake ganin kamar dai kubari na fara zuwa tukunna, dan kunga bamu da tabbas hasashe kawai mukeyi, shima baba karmu sanar masa tukunna, yana a shekarun da baya buƙatar irin wannan ruɗanin a halin yanzun, yanzu haka da kunga yanda hankalinsa ke a tashe akan zancen Miemaa da zakusha mamaki, yana dannewane kawai, to kunga abin zai haɗe masa biyu. Insha ALLAH zanje masarauta nima anjima domin sakejin bayani dangane dasu yaran, duk da dai Miemaa tamin bayanin abubuwa da dama game da mamansun”.
     Duk sun gamsu da jawabinsa, sun kuma yi masa addu'ar fatan nasara, amma ita Ummah babba ma tariga ta tabbatar musu da tanaji a ranta kamanin nan bazasu zama kamanni na haka nanba, ita wlhy jima take kamar tai tsuntsuwa ta ganta a saudia. Shi dai Jay ya cigaba da lallaɓasu dan yanason abi komai a sannu kodan maganar Bilkisu data sanar masa tana zargin akwai sihiri a cikin al'amarin.
     Sun cigaba da tattanawa har zuwa la'asar, Jay ya fita salla su kuma sukai tasu a gida. Ƙyaututtukan da duk suka kawoma Bilkisu duk suka bata, kafin suyi shirin komawa.
           Godiya naita musu dukda bansan mike a cikiba har sai da Ummah tace ya isa haka nan, da ya dawo daga salla shima na sanar masa, shima dai godiyar yayi.
         Har bakin mota nai musu rakkiya da bama fadila nima tsarabar dana haɗa musu ta turaren wuta da fruits ɗin da basu sha ba sai kajin dana gasa guda uku na naɗesu batare da shima ya sani ba. Sai da suka fice daga gidan sannan muka koma cikin gida. Hannuna ya kama ya zaunar dani a kusa da shi yana faɗin, “Sannu da ƙoƙari Miemaa, nagode sosai da yanda kika karrama ahalina”. Murmushi nai masa, nace, “Nima ai ahalina ne yanzun, dan ƴan uwanka nawane, iyayena ne yazama dole a gareni na girmamasu, dan haka ka dainamin godiya dan ALLAH”. Baice komaiba sai jawoni da yay na haye saman jikinsa, ya sauke siririyar ajiyar zuciya yana lumshe idanunsa. luf na kwanta nima ina shaƙar ƙamshinsa, gashi daman barci nakeji sosai, ai tuni na fara lumshe idanu.
         Ɗagoni yay yana kallon fuskata, ya saka hannunsa ya shafi kumatuna, “Badai barciba ko?”. Buɗe idanun nawa nayi kaɗan na kallesa, g

anin ni yake kallo saina maidasu ƙasa da yunƙurin tashi daga jikin nasa, “ALLAH barci nakeji”. Zamansa ya gyara sosai yana kallona, sai dai yaƙi cewa komai, jinai idanun nasa sunmin yawa, dan haka nace, “Ko zaka ƙara cin abinci ne”. “Uhm, amma ba wancan ba” ya faɗa yana nuna Dining. Da mamaki na kallesa sosai, “To wanne? Ko wani za'a dafa maka?”. Hannuna ya kamo ya matso dani jikinsa sosai, a hankali kamar baya son yin magana yace, “Zona faɗa miki wanda nake so”. Yay maganar yana ɗaura kansa saman wuyana, yanda yake busan iskar numfashinsa a saman wuyan ya saka tsigar jikina tashi, na cije bakina da haɗiye yawu da ƙyar, abinda ya gwargwaɗa min a cikin kune ne ya sakani zabura naɗan kallesa, sai kawai na miƙe nabar wajen da ɗan gudu.
         Lumshe idanu Jay yay yana wani sassanyan murmushi, yabi hanyar falonta da kallo yana sauke ajiyar zuciya, ganin idan ya cigaba da zama a gidan jikinsa zai cigaba da mutuwa sai ya miƙe, ɗakinsa ya shiga, mintuna kusan goma ya fito ya nufi nata.

      Ina zaune a sofa ɗin dake ɗakin ina duba abinda su Ummah suka kawomin ya shigo, ban yarda mun haɗa idoba nace, “Yayanmu kaga abinda su Ummah suka kawomin”. Muryarsa a sanyaye yace, “Kin gode, ALLAH ya saka da alkairi”. Ɗagowa nai naɗan kallesa na janye idanuna. “Baka da lafiya ne?”. “Mi kika gani?” ya faɗa yana ɗaukar agogonsa dake kan mirror na. “Naji muryarka a sanyaye ne”.
      Murmusa yayi ya miƙomin hannun da zaisa agogon, babu musu na fara ɗaura masa. Harma na fidda rai ga samun amsa nikam, sai da na kammala ɗaura masanne ya ranƙwafo tare da sumbatar laɓɓana, cikin ƙaramin sauti yace, “Bazaki ganeba Miemaa”. Idanuna na ɗago na kallesa, ya ɗagemin gira ɗaya yana cije leɓensa na ƙasa. “Kimin addu'a zan fita”. Duk da banason fitar haka na daure nai masa fatan alkairi da dawowa lafiya, sake ranƙwafowa yay ya sumbaci laɓɓana da cewa “Amin” sannan ya fice.
     Na sauke ajiyar zuciya da tattare kayan na maidasu inda suke sannan na miƙe, gidan duk sai yamin babu daɗi, dan haka na saka silifas tare da hijjab na fito harabar gidan dan inɗan rage kaɗaici, na ɗan zazzagaya ina tsinkar flowers ɗin da aka ƙawata gidan dasu masu ƙamshi, sai gab da magriba na shige ciki, falonsa na nufa kai tsaye domin tunawa da kofunan dasu Ummah sukasha lemo ban kwasosu ba, na gama tattarewa zan fito idona ya sauka akan file daya ajiye a kan hannun kujera, ajiye kofunan nai na ɗaukesa da nufin kaimasa ɗaki dan nasan mantashi yay anan. Takardun dake ciki suka zubo ƙasa a mistake, ‘Ya salam’ na faɗa ina duƙawa na tattaro su, ido na tsirama ɗaya daga cikin takardar domin ganin sunan Dad ɓaro-ɓaro, mamaki yay matuƙar kamani, na koma na zauna a kujera ina dubawa daki-daki. Kai nane ya nema kullewa, daga gefe kuma zuciyata najin wani irin takaicinsa, waishi mutumin nan mi ya ke nufi da ƴan gidanmu ne? Na kula gaba ɗaya bayanan dake a file ɗin akan ƴan gidanne, sunan Dad, mom da yah Qaseem yafi na kowa fitowa ma, maidawa nai na dangwarar da file ɗin na ɗauka kofinan na fita ina ƙunƙuni, ko wankesu ban tsaya yiba na ajiyesu a kicin ɗin na fito. Ɗakina na shiga raina duk babu daɗi, Dad ya wuce duk yanda yake zato a gareni daga shi har zuri'arsa baki ɗaya, Dad yaymin abinda sauran dangina suka gaza yimin, Dad ya tallafi maraicina a lokacin da rayuwata ke walagigin ƙila wakala, ta sanadin gatan da Dad yay minne har shiɗin ya sameni ya aura, lokaci yayi da yakamata nasan komai dangane da aurenmu da shi da yanda akai na koma hannunsa ba Yah Qaseem ba, inason sanin ina Yah Qaseem yake ne shin? Miya faru ne ranar ɗaurin aurenmu har aka ɗauramin aure da boss?’. da wannan tunane-tunanen na shiga bayi, wanka nayo da alwala raina duk a dagule, na shafa mai sama-sama tare da zira siket da riga marasa nauyi a jikina waɗanda sam basu kamamin jiki ba. Hoda naɗan shafa kaɗan da lipsgloss na saka turare sannan na tada salla, bayan an idar ban tashi daga saman abin sallar ba na ɗauka Al-Qurani nahau karatu, har saida aka kira sallar isha'i sannan na tashi nayi har shafa'i da wutiri dan yanda nakejin idanuna na bauri nasan kwanciyar wuri zanyi yau.

          Koda na fito saina shiga k

icin na ɗauraye kofunan sannan nai zaman gyara masa fruit duk da raina a dagule yake, na shirya tambayoyi fal ina jiran ya dawo na shiga yi masa su. Nayi nisa a tunani har bansan ya shigo kicin ɗinba, ƙamshinsa da alamar mutum da najine ya sakani ɗagowa da sauri. Ajiyar zuciya naɗan sauke dan baƙaramin tsorata naiba da farko, nace, “Ni ALLAH kaban tsoro”.
        “Ai ke komai abin tsorone a wajenki daman” ya faɗa yana juyawa ya fita a kicin ɗin. Ɓata fuska nayi na cigaba da aikina, sai da na kammala tsaf na ɗoro akan tray tare da ruwa da lemo sannan na fito. Ganin baya babban falo saina nufi parlorn sa. Nanma baya nan, na ajiye tray ɗin na nema waje na zauna jiransa ya fito danna amayar da abinda ke a raina, duk da tsoron da nakeji kuwa. Kusan zaman mintuna talatin nayi sannan ya fito, ya canja kayansa zuwa wando da riga farare tas masu taushi alamar yayi wanka. Yanda ya kalleni na kula baiyi tunanin ganina a nanba, amma sai ya basar ya zauna yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya kamar wani saraki. “Bani remote ɗin can”. Miƙewa nai na ɗakko masa. Inata dai danne abinda ke raina dan son yin koyi da nasiha da dabarun da Umm-Anum ta koyamin. Sai da ya kunna television ɗin sannan yace, “Sun wuce”.
     Kallonsa nayi nace, “Su wanene?”. Kamar bazai tankaba ya maida hankalinsa ga labaran, harma na fidda rai sai naji yace, “Daga masarauta nake”. Duk da na fahimci waɗanda yake nufin sai nace, “Wai kana nufin su Anuwar?”. Kansa kawai ya ɗagamin. Na fahimci ransa a jagule yake, amma duk da haka banji zan iya haƙuri ban masa maganar su Dad ba. Ruwan dana tsiyaya na miƙa masa, ya amsa tare da haɗewa da hannuna, ɗagowa nai mukaima juna kallon ido cikin ido, murya a sanyaye yace, “Jibi idan ALLAH ya kaimu zan wuce saudia”. “Nidai dan ALLAH mu tafi tare, kuma ma ai ni ta sani ba kaiba”. Karon farko datun shigowarsa naga yayi fra'a, ya ɗan murmusa da zare kofin daga hannuna ya kai bakinsa, sai da yasha ruwan sosai ya ajiye kofin sannan ya sake dubana, “Kinada kuɗin jirgine?”. Da sauri nace, “Eh” cikin karsashi da ƙarfin gwiwa. Yace, “Yayi ƙyau hajjaju”. Yay maganar da buɗe plate ɗin dana rufe fruit dana yayyanko a cikin bowl ɗin glass. Cokali mai yatsu dana haɗo da shi ya ɗauka ya fara sha hankalin kwance kamar nace nasane🙄😒.
          Shiru falon yayi sai tv daketa subaɗi, saida ya sha kusan quarter sannan ya juyo ya kalleni, “Zo nan naji mike damunki ne?”. Mamaki ya kamani, ya akai ya fahimta? Saurin gyara yanayina nai da cewa, “Babu abinda ke damuna sai barci”. yaɗan tsuramin idanu sannan ya janye, “Tunda yau na fara saninki ko?. Taso nace”. Tashi nai zuwa inda yake ina kumbura fuska, ya fisgoni da ƙarfi na faɗa saman cinyarsa, ƴar ƙara na saki wadda ni kaina nasan ta shagwaɓace, “Shiiii” ya faɗa yana saka kankana a baki, bakinsa ya ɗora kan nawa ya sakamin kankanar dake bakin nasa cikin nawa. Na yamutse fuska kaɗan a raina ina faɗin ‘ƙazanta’. Ɗallar bakina da yay ya sakani sake ɓata fuska dan naji zafi, ya ɗage gira ɗaya da faɗin, “Nasan ai gulmata kikai a zuciyarki”. Saida na shanye sannan nace, “Nidai nasan banyiba ai”. Bai tanka minba ya cigaba da bani fruit ɗin shima yana sha, saida nace masa na ƙoshi sannan ya barni. Zameni yay na kwanta a kujerar kaina na saman cinyarsa, wannan damar dana samuce ta bani damar faɗin, “boss wai dan ALLAH wane laifi Dad yay makane?”. Kallona yay cikin ido ya watsar, ya maidama hankakinsa ga kallon labaransa hankali kwance. Iya kaiwa ƙarshe nakai da haushi, hakan yasa na sake maimaita tambayar kozai fusata ya bani amsa, amma nanma saiya shareni, aifa nakai ƙarshen harzuƙa, na fashe masa da kuka, “Wai miye laifin Dad ne da Yah Qaseem a gareka? Bayan tarin ƙauna da kulawa da suka nuna maka dagasu har Momy, ƴa fa suka ɗauka sukutum suka baka ka aura, basu ji komaiba suka sake bakani duk da kuwa ɗansu jininsune ya dace na aura, sannan ƴarsu da ke tsananin sonka ya dace ka aura kaima, boss bai kamata ace ka maida alkairi ta wannan sigarba, suɗin ƴan uwanane fa waɗanda sukaimin gatan da kowa ya gaza yimin, sune suka maidani mutum harna zama abin sha'awa ga irink.......” ruf ya rufemin baki da nashi, ya ɗagan

i cak batare daya sakimin bakiba yay bedroom dani, duk ƙoƙarin son ƙwacewar da nake ko gezau baiyi ba, dama ya kashe fitilar ɗakin sai na gefen gado kawai, dan haka sai kawai jina nai bisa gado, babu wani ɓata lokaci ya shiga juyani da zafi-zafi yanda yake so, gashi ya hana bakina damar neman ɗauki, yanda yake bi danine ya tadamin hankali, dan sam babu wani bi a hankali kamar ranar, sai dai kuma hakan bai hanashi kasancewa cikin nutsuwaba da min abinda zai gusarmin da hankali. Idan nace muku na gurzu fiye da ranar farko to ku ɗauka gurzuwa nai irin ta ƙarshen nan da faɗarta kawai takai a tausayamin, dan al'amarin ya zama kamar famine daga baƙar azabar dana sha a daren shekaranjiya. Muryata harta dasashe saboda kuka, ya kuma ƙi lallashina kosau ɗaya.
         Kamar ranar yauma shine ya taimakamin na gyara jikina, ya kuma sakani a ruwan zafi sosai sannan ya maidoni saman gadon ya kwantar batare da yace dani uffan ba, yamayi tamkar baijin kukan nawa, komawa yay bayin yaje yayo wanka shima, har lokacin ina shashshekar kuka na, muryarsa a dadushe kamar mai mura yace, “ALLAH idan bakimin shiruba na hawo gadon nan saina sake banbance miki aya da tsakkuwa, daga yau kuma dan ALLAH ki sake ahiga abinda babu ruwanki kinji ko”. Yana gama faɗa ya ficewarsa a ɗakin.
      Kukan na sake fashewa dashi ina danna kaina cikin filos dan karya ji, kusan mintuna goma da fitarsa naji ya dawo ɗakin, haɗiye kukan nayi na koma sauke ajiyar zuciya, bai tankaminba naji dai yanata kai kawonsa har na wasu mintuna kafin ya hawo gadon. A jikinsa ya sakani ya rungume batare da yace ƙala ba, mintuna kaɗan barci yay gaba dashi bayan yaymana addu'a, nima ajiyar zuciyata na cigaba da saukewa har barcin yay awon gaba dani.

★★★★★

         Da asuba shine ya tadani, kafinma na sakko a gadon yayi ficewarsa, na rakasa da harara sannan na sakko da ƙyar, wani irin zafi naji ya ratsani a wajen, sai ga hawaye shar, nasa hannuna na share ina jinjina muguntar maza a raina, idan dai haka za'a dingaji to miye abin daɗi anan da har mata suke zuwa suyi iskanci dan ALLAH?. Sai da na shiga ruwan zafi yanzunma sannan nai alwala na fito, naji daɗi sosai yanzun kam harda nutsuwa, ficewa nai daga ɗakin na koma nawa, sai fitilar waya na kunna dan sun ɗauke wutarsu. Ina idar da salla gado na haye nai kwanciyata ko azkar banyiba, banason yazo ya iskeni zaune, barci yaɗan fara fisgata naji ya buɗe ƙofar, ban motsaba balle yasan idanuna biyu, sai da ya maida ya rufe sannan naɗan buɗe kaɗan naga bayanan, ajiyar zuciya na sauke na gyara kwanciya abina.

         Taƙwas saura na farka, na sakko daga saman gadon ina matse fuska saboda ciwon da jikina kemin ta ko ina, bama dole nai ciwon jikiba kodan muguntar da akaimin, wanka nayi na fito nai shiri cikin wando da riga na parkistan da sukaimin ƙyau, nai ƴar kwalliya dai-dai misali sannan nasa turare da yafa ɗan gyalen kamar yanda sukeyi. Fitowa nai dan nema mana breakfast tunda ya roƙi Ummah akan a daina kawo abinci, a bazata na iskesa a babban falo zaune yana aiki. ‘Agogo sarkin aiki’ na faɗa a zuciyata cike da gulma. Ɗagowa yay ya tsatstsareni da mayun idanunsa, hakan yasa nai ƙasa da nawa, saida na rissina ina gaishesa sannan ya ɗauke kansa daga kallona, amsamin yay da tambayata wai ya jiki. “Ni lafiyata lau”. Na faɗa ina ɓata fuska “Haka akeso ai”. ya bani amsa a taƙaice. Miƙewa nai ina satar kallon kofin dake a centre table ɗin alamar coffee ya haɗa da kansa yasha kenan? Bance komaiba na nufi kicin, inaji a jikina kallona yake harna shige.
       Idanunsa ya lumshe da sakin murmushi yana ɗauke kansa daga binta da kallo da yayi, a fili ya furta, “Masu dangi, yauma ki ƙaramin maganarsu kiga yanda zamu kwashe anan gidan sarkin son ƴan uwa”.
             Gyaɗar dana jiƙa da farar shinkafa tun da daddare na wanke, na ɗakko farar kwakwa da dama na fasa na yayyankata itama na haɗesu waje guda da citta ɗanya da kayan ƙamshi dai-dai buƙatata na markaɗesu kasancewar akwai wutar da naita addu'a da fatan su kawo tunda nai sallar asuba, sai da sukai laushi sosai sannan na tace tsaf na ɗauraye tukunya na zuba, ban kunna gas ɗinba tukunna na ɗib

a wake gwangwani biyu da rabi shima nai zaman dakawa aɗan turmina, sai da yaymin yanda nakeso sannan na cire na wanke shima nai markaɗan ƙosai, saida na tabbatar na haɗa komai sannan na kunna gas, ban rufeba tukunyar kunun ba gudun karya taso ya zube saboda gafin gyaɗa, na saka ludayi ina motsawa a hankali har yay zafi ya fara kauri, cikin amincin ALLAH baiyi ƙurnu ba yay ƙyau abinsa sai ƙamshin gyaɗa da kwakwa ke tashi, na sauke tukunyar a ƙasa danya ɗan huce kafin na saka madarar dana dama. Suyar ƙosan na fara wanda dandanan na gama kasancewar bawani yawane da shiba, na zuba madarar a kunun sannan na zuba ma maigadi muma na juye mana namu, saida na gyara komai tsaf sannan na fito da namu a Dining na maigadi ma na fito dashi na ajiye gefe. Baya a falon, dan haka naɗan gyara tunda babu wani datti na azo a gani na saka turaren wuta. Ina kammalawa yana fitowa, yay tsaf cikin ƙananun kaya sai baza ƙamshi yakeyi.
            Baice dani komaiba ya ɗauki abincin maigadi ya fita, babu jimawa sai gashi ya dawo, lokacin ina a Dining ɗin ina ƙoƙarin haɗa masa nasa, kujera yaja ya zauna idonsa akan hannuna da har yanzu yake raɗam da ƙunshi.
      “Duk a yaushe kikai wannan?” na tsinkayi muryarsa a bazata. Kallonsa nai na janye idanuna, nace, “Yanzun”. “Kinyi ƙoƙari, ALLAH yay miki albarka”. Murmushin daban niyyaba na saki sai naji duk fushin nawa yay ƙasa, a hankali nace, “Nagode”. Shima murmusawa yayi kaɗan da ɗaukar ƙosan yakai bakinsa, ya lumshe idanu da faɗin, “Uhhhmm”. Kallonsa nai dariya na cina, na ɗauki cokali nasa gefensa alamar waiji. “Yarinya ai ba santi nakeba” ya faɗa yana jan kofin kunun dana ajiye masa a gabansa sosai. “Nima ai bance santi kake ba”. “Kin taimaki kanki to”.
         Murmushin na sakeyi ina ƙoƙarin haɗa nawa nima.
     Nayi mamakin yanda yaci sosai, ya ɗauki tissue yana goge bakinsa damin almar komai zamm da hannu👌🏼. “Nagode to” nafaɗa ina murmushi. Zagayowa yay ta bayan kujerar da nake ya ranƙwafo ya sumbaci kumatuna duka biyu sannan yace, “Kin gama mallake Jay da komansa Miemaa”.
          Hannu nakai na shafi fuskarsa ina faɗaɗa murmushina, dan naji yanda ya nuna jin daɗinsa da abincin.
      ya zagayo ta gabana ya nunamin kuncinsa alamar na sumbata. Dukda inajin kunya haka na daure na sumbacesan kamar yanda yake buƙata. Sassanyan numfashi ya sauke da juyamin ɗayan, nanma dai yi nayi ina mamakin rashin kunyarsa. “Jazakhillah bi jannah” ya faɗa yana kamo fuskata cikin tafukan hannayensa, kafin nace wani abu ya manne bakinsa da nawa.
       Yana saki na saka hannu na rufe fuska. yace, “Daga baya kenan. Bara naje Alhaji Babba na jirana zamuje wani waje”.
     Miƙewa nai tsaye nima, “To dan ALLAH ka kira Nabeelah tazo ta tayani zama, ALLAH babu daɗi kaɗaicin”. “Baga wuta ba, kuma nima aiba daɗewa zanyiba”. Cikin marairaicewa nace, “Idan suka ɗauke fa, kumafa ni tsoro nakeji”. “Jami'ar tsaro da tsoro”. Ya faɗa yana jan hancina. Bai jira amsataba ya fice yana faɗin “Aimana addu'a”.
     Da “ALLAH ya tsare” na rakasa inajin duk babu daɗi...................✍

Jiya kam Wattpad yay muku buƙulu, nayi typing tun dare zan baku na nemesa na rasa, wlhy sai sake wannan page ɗin nai cike da haushi, gashi dai sai dai kuyi maneji da shi😥.


ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka

1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

11 months ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment