Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kujerun gaban tebirin suna kallonsa suna kallon Rose dake kuka. Hafiz ya jawo kujerar dake can gefe shima ya zauna yana jan ƙaramin tsaki dan shifa Rose takaici take bashi da halintan nan.
         Ganin yamaƙi kallonsu Jabeer yace, “Boss wai mike faruwa ne?”. Bai tankaba bai kuma kallesun ba yanzuma, dama cikin damuwa yake, ya fito gida da fushi, ita kuma yanzu sake kunna zuciyarsa take tana cikowa saman ƙirji, idan kuma har ta bari takai masa wuya to lallai zatayi nadamar biyosa office ɗinsa tana masa ihu a kai.
       Jabeer zai sake magana Aliyu ya girgiza masa kai alamar kar yayi, Rose ɗin ya kalla da take kallon Jay tamkar zata haɗiyesa, kuma har yanzu kukan take, “Rose miya faru?”. Juyawa tai ta kalli Aliyu hawaye na sake ziraro mata, “Aliy na gaji wlhy, na gaji da wulaƙancin da boss yake min, dan na soshi shine ya zama laifi? Shekara nawa na ɗauka tare da ku, kuma ban gazaba wajen nuna masa ina sonsa tun yana tare da wancan matar tasa, ya cemin shi bashi da ra'ayin yin mace fiye da ɗaya, karka manta har suspension yasa aka bani

            “Mtsoww, kufa wataran shashashancinku yawane da shi wlhy, ku ajiye wannan shiriritan muyi abu mai muhimmanci, kosu sir Ahmad banje na gaida ba, so nake mu gama sannan, dan na dawo da ayyuka masu yawan gaske, amma inason na fara jin mike tafiya daga wajenku?”.
          “Akwai nasarori masu yawa da zasu sakaka farin ciki kuwa, dama mun barsu ne harka dawo muyi maka surprise”. Murmushi Jay yayi mai sanyi da jin duk ɓacin ran daya toshe masa ƙofar zuciya yana faɗawa. Aliyu ya ajiye masa files ɗin hannunsa. Ɗauka Jay yayi ya fara dubawa, a take fuskarsa ta bayyanar da annuri, sai da ya gama dubasu duka sannan ya ɗago yana kallonsu, “Woow! Ina alfahari daku sosai da sosai wlhy, gaskiya kunmin babban albishir mai darajar gaske, yanzu kuna nufin waɗanan duk sunzo hannu? Kun gama mana da waɗan nan ayyukan?”. Jabeer yace, “Ƙwarai ma kuwa, dan wanda yasa aka kashe jami'inmun ma yanzu haka gobe za'a miƙasa kotu”.
           “Masha ALLAH, gaskiya naji daɗi wlhy, kuma nayi farin ciki sosai, maganar yaran canfa?”. Jawaad ya faɗa yana miƙewa ya ɗakko wani file a drawer ɗin bayansa.
      Yanzunkam hafiz ne ya bashi amsa, “Ai boss maganar ƙungiya ta wuce duk yanda mukai zatonta, lokaci kawai zamu samu ko zuwa anjima sai muje office ɗin nasu kaga komai da idanunka zaifi, ko zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu”.
      “Hakan yayi Hafiz, mu barsa kawai zuwa gobe sai muje, kuma sannunku da ƙoƙari, Jabeer maganar matar nan fa, har yau baka kammala ba ne?”. Na kammala komai, sai dai abinda ba'a rasaba, shima akan binciken mitaje yi inda take ne, inason binciko ƴan uwanta ne kokuwa? Gashi yanzu ma na daina samun wayarta gaba ɗaya kuma”.
         Saurin kallonsa Jay yayi “Bata aiki wayar kokuwa?”. “An kasheta dai kusan kwana uku kenan, nafi kawoma raina matsalar caji ne”. Numfashi Jawaad ya ɗan sauke da faɗin, “Okay to ALLAH ya dafa mana, yanzu dai bara na leƙa na gaida su sir Ahmad, idan na fito zan ɗan fita wani waje, dana dawo saimu zauna akan wasu cases ɗin da muke dasu a ƙasa tunda kun kammala waɗannan”.
       Duk kai suka ɗaga masa, kafin duk su miƙe su fito, shi ya hau lifter yay sama su kuma kowa ya nufi office.
     
          Sai da ya shiga suka gaggaisa da oganninsa, office ɗin sir Ahmad ne ya zama ƙarshe, bayan sun gaisa shima da tattauna abinda ya shafi aiki Sir Ahmad ke cewa, “Nasan kasan Qaseem ya dawo ai?”. Da mamaki Jay yace, “Qaseem kuma sir!? Wlhy ban sani ba. Yaushe ya dawo?”. “Ya dawo kwana uku kenan, sai dai kuma yanzu haka sun killacesa, duk da shi ya dage akan shifa lafiyarsa ƙalau, shima Alhaji Ali ya kirani akan maganar wai ya kamata muyi wani abu a sakar masa ɗa dan baida wata corona”. Jawaad ya gyara zama yana ɗan murmushi da mamaki, yace, “To ALLAH ya kiyaye, amma kunje ɗin ku?”. “To Jay mu zamu biye musu ne, wannan hurumine na hukumar lafiya ai, kuma sunce nan da sati biyu idan bata basuga komai ba zasu sakesa ai”. “To ALLAH ya kaimu lokacin”. “Amin” sir Ahmad ya faɗa sannan sukai sallama ya fito.
      Bai koma office ba ya nufi inda Sadiq ke jiransa, buɗe masa mota yay ya shiga sannan suka fice.

★★★★

       Cikin Barrack sukaje wajen baba ƙaura, baba ƙaura na zaune yanata fiƙar tsinkayen iccen ƙwari Jawaad ya shiga da sallama shi da sojan da yay masa rakkiya. Ɗagowa baba ƙaura yay yana amsa musu da musu sannu da zuwa, ya nunama Jawaad wajen zama shi kuma wancan sojan ya fice. Sai da suka gaisa da tambayar ya kwana biyu sannan baba ƙaura ya kalli Jay yay murmushi da ɗauke kai. “Malam Jawaad kenan, mi kuma ya faru?”. Jawaad yaɗan murmusa yana kallon ƙwarin da baba ƙauran ya feƙe ya zube gefe kusan ashirin, “Baba na zone akan wata magana daka faɗa ranar a dajin nan”. “Tofa wace magana ce?”. Hannu Jay ya saka aljihun wandonsa ya ciro wuri da gurun nan na hannu sai zobe ya ajiye gaban baba ƙaura”. Kallon kayan baba ƙaura yay ya ɗauke kansa yana murmushi, “Kun sami huɗu kenan?”. Kai Jay ya jinjina masa. Cigaba baba ƙaura yay da aikin gabansa kamar ba zaice komai ba, kusan mintuna biyu sannan ya sake duban Jawaad ɗin da maida dukkan hankalinsa ga resa, “Yanzu ina ɗayan yake?”.

“Bamu ɗakkosa ba, yana acan gidan data zauna ɗin”. Baba ƙaura ya ɗauki zoben ya jujjuyashi sosai a hannunsa sannan ya ajiye, “Lallai kun samu damar amsar babban makaminsu, amma yaya akai kuka iya samun zoben nan? dan abune mai daraja ga mai shi”. Muryar Jay cike da ɗaci ya zayyane ma baba ƙaura komai da ya faru, harma da maganar fyaɗen da aketa bibiyar Bilkisu da shi da sai a randa ta cire zoben ta iya tunawa. Nannauyan numfashi baba ƙaura ya sauke, yace, “Ai dama na faɗa maka yarinyar akwai duhu dake biye da ita, wannan yana ɗaya daga ciki, amma akwai wanda ya fisa girma ma sai dai bansan minene ba,  ku cigaba da gayama ALLAH shi mai komai da kowa ne, ba ita kaɗai ba abubuwa da yawa zasu fito dalilin wannan zoben, dan duk inda maishi yake hankalinsa baya a kwance yanzu, har dama duk wanda ke zagaye a ƙungiyar shaiɗancin, ka turata gidan ta ɗakko wancan ɗayan wurin, idan har ta tarar an hargitsa ɗakin data ajiye to lallai mai bibiyarta da wannan sheɗancin na fyaɗe yana cikin wannan gidan, kuma shaiɗaninsu sun tabbatar masa wurin data cira a farko yana a gidan, an basa damar ya nemosa gudun karku haɗasu kamar yanda muke buƙata, dan inda tace maka ta ajiyesa babu wani shaiɗani da ya isa ɗaukarsa saboda darajar Al-Qur'ani, shiyyasa shi akace ya ɗakko, inaji a raina kuma bazai gansaba insha ALLAHU, dan daya gansa komaima zasu iya aikatawa a kanku domin halakaku baki ɗaya musamman ma ita, suma kansu basusan taka mai mai inda ya keba bayan sanin yana cikin ɗakin kawai”. Jay dake ta tauna lip ɗinsa na ƙasa sai jinjina kai kawai ya keyi, ya furzar da huci mai zafi a bakinsa yana sake jinjina kansa. Baba ƙaura yace, “Idan ta ɗakko ku yanka wannan gurun, ku zira zoben da wurin guda biyu cikin gurin, zoben ya zama shine a tsakkiyar wurin, sai ku ƙulle gurun ku ajiye. wannan ba tsafi bane, ba kuma wani shaiɗanci bane, zakuga abinda zai biyo baya insha ALLAHU, dan cikin sauƙi zakuyita gano abubuwa masu ban mamaki da al'ajabi insha ALLAH..............✍



ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[1/18, 4:58 PM] HASNA✍🏻: Typing📲

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO



Page 52
................Wata tarbar karramawar na sake iskewa wajen ƴan office ɗinmu nima, suka baibayeni mazansu da matansu suna mai tayani murnar aure da samun boss matsayin miji, su Ada iyayen gulma harda cewa na musu wayo nai wuf da boss. Ni dariyama suka bani wlhy. Na musu godiya da fatan suma ALLAH ya basu nasu musha biki. Fassara muku farin cikin dana tsinci kaina a ciki saboda dawowar su Nazifa station ɗinmu ɓata lokacine, muka sake rungume junanmu daɗi na ratsamu, a karo na uku mun sake kasancewa tare, ALLAH dai yasa muci amfanin wannan ƙawance har a gidan aljanna. Gaba suka tasani da sheri wai nayi ɓul dani kodai an samar musu baby?. Yinai kamar banjisu ba, da suka isheni sai nace suje su tambayo boss ɗin. Dariya suka sanya kowa na miƙewa duk suka koma mazauninsu da aka basu suma a office ɗin namu. Daga haka na samu lafiya daga iskancinsu.
Ban tarar da kowanne aikiba, Ummie ta sanarmin ai duk oga Jabeer ya bata ta ƙarasa ayyukan dana bari, naji daɗin hakan sosai, saina miƙe ƙafa ina hutawata, da wannan lokacin nai amfani wajen zurmawa duniyar tunane-tunane kala-kala, ciki harda neman amsar yanda akai aurena da Yah Qaseem ya fasu aka maida shi kan boss, sai abinda na gani yau a ɗakina da duk nama rasa wane tunani ya dace nayi akan hakan, dan duk wanda nayi mai ƙyau sai naga bai zauna da al-amarin ba sam, sai marasa ƙyawunne keyin dai-dai. Ban sakejin ɗuriyar boss ba har muka fita sallar zuhur, bayan an idar mun fito su Nazifa ke faɗin ya kamata muje muci abinci, dan wasu a cikinsu ma basu ko karya ba suka baro gida, nima ɗin sai yanzun na tuna ban karyaba, ruwan tea ne kawai a cikin nan nawa. Shiru nai ina tunani, ni dai banda damar cewa zan bisu wajen cin abincin nan boss bai saniba, ni kuma bana wani son zuwa Office ɗinsa.... Taɓanin da akai ne ya katse tunanina, na sauke numfashi da kallon Rebecca da hannunta ke a kafaɗata, "Matar nan ina kika tafine? anata magana". Murmushi na mata ina tura hannayena cikin aljihun wandona, "Ba komai, kinsan zuciya da tone-tone, inaga kuje kawai banajin wani yinwa nikam". Har Ummie ta buɗe baki zatai magana sai Zuhrah ta katseta, "Kai inagama fa bai kamata ta bimu ba mijinta bai saniba gaskiya, tunda yana cikin station ɗin shima ta fara sanar masa, yanzufa ba da bace da muka saba shirmen mu kai tsaye". "Hakane kuma gaskiya" cewar Nazifa tana komawa kalar tausayi. Fahimtar inda ta dosa yasa muka kwashe da dariya mu dukanmu, dan itama dai bai wuce nata auren da ya rage six weeks ta tuno ba. Office muka koma bisa shawar Zuhrah, ita da Ummie kuma suka tafi sayo mana abincin..
★★★★★★
Tunda suka baro cikin Barrack ɗin Jay ke ƙullawa da kwancewa, lumsassun idanunsa da launinsu ya gushe da ga farare zuwa ɗan jaa ya buɗe a hankali yana furzar da nannauyan numfashin da har sadiq sai da ya saci kallonsa ta mirror. Wayarsa ya ɗauka ya shiga daddanawa kafin ya saka a kunne dayin sallama, Munkaila na amsawa bai tsaya bi takan gaisuwar da yake masaba yace, "Zan tura maka wasu sunaye guda huɗu, inason daga nan zuwa yammacin gobe idan ALLAH ya kaimu a nemomin inda suke, sana'arsu ko aikinsu, abokan mu'amularsu na rayuwa dana kasuwanci". "Okay sir insha ALLAHU zanyi ƙoƙari, akwai ma waɗan can ayyukan na wajena guda biyu suma duk na kammala". "Saika haɗosu kawai". "Okay Sir" Munkaila ya faɗa cike da girmamawa.
Suna isowa cikin station ɗin baima jira Sadiq ya buɗe masaba ya buɗe da kansa ya fita, sallamar Sadiq ɗin yay akan yaje zuwa biyar sai ya dawo, shi kuma kai tsaye massallaci ya nufa saboda lokacin salla yayi.
Bayan an idarne ya fito zai koma office yaga su Bilkisu, sai dai su sam basu ganshiba dan hankalinsu baya ta wajen, yazo zai ɗan gittasu yaji hirar da sukeyi, ajiyar zuciya ya ɗan sauke da yaba hankalinsu, yanda yake musu kallon yara ƙanana bai zaton sunada zurfin tunani irin hakaba, dan daidai zai wucene maganar zuhura ke shiga kunnensa akan bilkisu bai kamata ta bisuba mijinta bai saniba. Sai da ya shiga office ya zauna sannan yay kiran gidan abincin da yaji su Ummie zasuje, umarni ya bada akan a basu duk abinda suke buƙata kar kuma a amshi kuɗinsu shi zai biya. Kasancewar sa babban Customer babu ɓata lokaci aka haɗa musu komai.
Su Ummi basu san wainar da ake toyawaba, sudai sukaga an haɗa musu abinci kala-kala harma da wanda basuce ɗinba, amma dai-dai abinda zasu iya cinyewa ba almabazaranci ba, sannan akaƙi amsar kuɗinsu, da suka matsa da tambaya aka basu amsa akan an biya. Sosai sukaita mamakin da tambayar waye ya biya ɗin?, babu wani ɓoye-ɓoye aka sanar musu.
Tunda suka dawo suka sanarmin yanda akai wajen sayen abincin sai naita mamaki akan yaya akai yasan zasuje? Shin kodai idanu ma yasa a sakamin ne? Kai bana tunanin hakan daga garesa, sai kace wanda bai yarda dani ba. waya na ɗauka na tura masa saƙon godiya da fatan alkairi.


Jawaad na zaune ya duƙufa aiki saƙo ya shigo masa, kasancewar Number da kowa ya sansa da itace ya zata akan wani aiki ne, dan ya kashe wayarsa da mutane masu muhimmanci kaɗai ke ciki, gudun kar Alhaji babba kosu Ummah su kirashi susan ya dawo, baiyi tunanin bily bace tunda bai saka Numbar ta anan ba, ɗauka yay ya duba, a mamakinsa sai yaga itaɗin ce ashe, yay murmushi da ɗan lumshe idanu ganin abinda ta rubuto, ajiye wayar yay kawai ya cigaba da aikin gabansa. Cak ya tsaya daga abinda yakeyi yana mai ƙure takardar daya saka sunayen da suka samo wajen Umm-Anum da ido, waya ya ɗauka da hanzari yay kiran Jabeer, yana ɗagawa yace, "Jabeer bama wani ya kawo min file ɗin matarnan".
Daga can Jabeer ya amsa masa da "to". babu jimawa kuwa sai gashi ɗan aike daga jabeer yay knocking, damar shigowa ya bashi.
Cikin girmamawa ya ƙame da sarama Jay kafin ya gaida shi, sannan ya ajiye file ɗin hannunsa. Ɗaga masa hannu Jay yayi alamar ya tafi kawai. Yana fita ya ɗauki takardar dake da sunayen bayan ya zagaye sunan macen dake a ƙarshe da jan biro, sannan ya buɗe file ɗin wajen Jabeer. tsai Jay yayi a zaune yana ƙarema sunayen kallo, sam babu wani banbanci hatta da sunan gari, waya ya ɗauka ya shiga dannawa. Kira yayi, bugu biyu aka ɗauka, bayan sun gaisa yace, "Malam Rabo, yanzun nan inason Ka binciko min Hajiya Safara'u a cikin ƙauyen nan naku, gashi nan zan turo maka cikakken sunanta da sunan mahaifinta nasan zaka gane, banason ɓata lokaci, yanzun nan nakeson kabar tasharnan ka tafi". "Insha ALLAHU kuwa oga yanzun nan zanbi motar datai lodi kuwa, koma na amshi mashin ɗin Madu naje yanda zanfi sauri". "Hakan yayi, ka zuba mai idan ka dawo sai a bashi wani abu shima". "To oga babu damuwa, sai ka jini".
Jay na ajiye wayar ya maida dubansa ga file ɗin yana bin komai dalla-dalla, dogon nazari ya shiga akan abinda ke cikin file ɗin da wanda ke a ƙwalwar kansa, 'Wato na fahimci akwai wani kuskure da nayi ƙwarai da gaske' yay maganar a fili yana dafe kansa, takarda ya ɗauka ya hau rubutu, sai kuma ya ajiye biron ya kwanta jikin kujera da faɗawa duniyar tunani.
Rasuwar gimba ta rikitashi ainun har yama manta abubuwan da ya kamata ace ya bibiyesu. Akwai Number ƙarshe da gimba yay waya da ita ya kamata yasan wanene ma? da wuri, sannan matarnan da gimba ya ambata ta gidan Alhaji kokino tabbas da itane suka taɓa haɗuwa a gidan Alhaji Kokinon, kuma itace tai aiki a gidansu kenan? Idan binciken ya zama dai-dai. Yaya akai hakan ta faru bai taɓa fahimtaba kai tsaye, kalamanta na wancan karon sun isa su bashi dukkanin amsar da yake buƙata. tabbas wani baƙon al'amarine da bai taɓa sakashi a lissafisa bane ya shigo masa kai yanzun nan musamman akan kashe Gimba da akayi yake tunanin da babu gaira babu dalili. Abinda yake tunanin ya faru akan kisan gimba ba shi bane ashe. Alhaji kokino sunyi abotar siyasa da Abba kamar yanda Ummuna ta faɗa, sun kumayi ta kasuwanci, indai har matarnan tayi aiki a gidanmu mizaisa ta koma can gidan tana aiki? Lokacin da aka sace Alhaji kokino itace ta bani dukkan sirrikan da nabi na samosa a hannun ƙaninsa, maganar gimba a al'amarin, yace akwai dalilinsa na zuwa aiki ƙarƙashina, na kuma nemeta zanji abubuwa masu muhimmanci. Idan har zan haɗa wannan maganar tashi da maganganunta na waccan ranar da muka taɓayi to lallai tamin farin sani kenan?. Miƙewa Jay yayi yana ɗan dukan tabirinsa da faɗin, "Yah ALLAH ". Ya sassauta tie.. ɗinsa yay ƙasa da shi, saima ya fincikesa gaba ɗaya ya jefa saman kujera ya shiga safa da marwa a office ɗin, duk da ac dake aiki hakan bai hanashi haɗa gumi ba, tun randa yasan akwai alaƙa tsakanin Alhaji kokino da Mr Gebrail ya saka ake bibiyar masa Mr Gebrail, ta hakane ya gano kuma alaƙar Mr Gebrail da ɗaya a cikin Uncle ɗinsa, idan ya dunƙule maganar waje guda hakan na nufin, Uncle ɗinsa, Mr Gebrail, Alhaji Kokino duk sunada a laƙa ta baɗini, dan a zahirance babu wannan alaƙar kota gaisuwa a tsakaninsu sai a ɓoye. dolene a daren nan a sato masa wayoyin Alhaji kokino, sai dai waye zai masa aikin? 'Dan dole ya kasance ɗan cikin gidanne zaiyi hakan' ya ƙare maganar a fili yana dafe kansa da furzar da huci mai azabar zafi.
Tunanin kiran bilkisu ne yazo masa a rai, dan kosu Hafiz bayason sakasu a wannan case ɗin yanzu, saboda ya haɗa da family nashi, sannan yanada sarƙaƙiyar yarda da wani, kai tsaye zai iya zama ganganci, bawai dan bai yarda dasu bane, dan su Jabeer sun wuce duk hasashen mai karatu a garesa, amma ciki ba'a yisa dan abinciba kawai ai. Bilkisu na ɗagawa yace, "Ina jiranki a office". Ya yanke wayar.
Kallon wayar kawai na tsaya yi da mamaki, to amma yanda naji muryarsa tamin kama da ta mai damuwa, miƙewa nai na fice, inajin Nazifa na tambayata ina zuwa? Ban sauraretaba na ɗaga mata hannu kawai. Koda nai knocking ba'a amsamin ba, dan haka kawai na shiga kaina tsaye. Nannauyar ajiyar zuciya na sauke ganinsa ba yanda nai zatoba, ya ɗago ido ya kalleni sannan ya maida ga abinda yakeyi. Takawa nai na ƙarasa garesa, murya a sanyaye nace, "Wlhy nazata ko baka da lafiya, ya aikin?". Baice dani komaiba ya nunamin wajen zama, shima zagayawa yay ya zauna a kujerarsa, yanda ya tsatstsareni da idanu duk sai naji na takura, na risinar da nawa ƙasa ina kallon yatsun hannuna. Numfashi naji ya sauke mai ƙarfin, kafin nace wani abu ya fara min bayani akan kiran, ya ƙare maganar da faɗin, "Dole ne musami wayar a daren nan, dan itace zata bamu haske akan komai da gaggawa, aikin nan kuma dole mu biyu kawai zamuyisa ni da ke kawai, ko su Aliyu banason na saka sai na gama fahimtar komai".
Naji daɗin karrawarsa gareni sosai, dan banyi zaton hakanba, na gyara zamana, "To ina ganin mizai hana muyi amfani da cikin ƴaƴansa ko ma'aikatan gidan?". Shiru yay yana kallona da goga ƙasan biro akan laɓɓansa, kusan sakan goma ya janye ya maida kan takardar gabansa, ɗan rubutu yayi sannan ya sake ɗagowa ya kalleni, "Wannan shawarar taki tayi, amma babu wani ƙarin bayani a kanta?". Tsai na ɗan ƙarayi na tunani kafin nace, "Akwai, ya kamata wadda zamu saka ɗin cikin ƴaƴan nasa ta kasance mace, sannan mu nuna mata za'a cutar da shine shiyyasa muke son wayoyin na wasu awanni kawai za'a maido mata ta maida masa bayan mun saka matakan tsaro. Ko baiyi ba?". "Ihum inajinki cigaba" ya faɗa cikin lumshe idanu. Naɗan sauke ajiyar zuciya da cigaba da faɗin, "Idan muka amsa maimakon mu ajiye wayoyin a hannunmu kawai muyi copy ɗin komai na ciki sai a maida mata ta maida masa zuwa safiya". Lallausan murmushi ya saki yana ɗagemin gira ɗaya, "Ashe matar tawa ƙwaruwa ce?". Yanda yay maganar cikin zolaya yasa na rufe idanuna da tafin hannu ina murmushi. Yace, "Thanks Miemaa, da duk kaina ya kulle". Nace, "Haba dai, kaine kanka ke kullewa?". "Oh ni ba mutum bane? Duk ma ba kece kika rabamin hankali biyu ba". "Nidai babu ruwana". "Humm", ya faɗa kawai yana miƙewa. "Kinga tashi muje, da zafi-zafi ake dukan ƙarfe".
Koda muka fito sai da ya shiga office ɗin Aliyu, babu jimawa ya fito riƙe da key ɗin mota, da kansa ya buɗemin na shiga sannan shima ya zagaya ya shiga, nidai addu'a nake a raina karyay gudu damu, yanda naci abincin nan na ƙoshi matsala za'a samu ai. Kasa daurewa nai na roƙesa karyay gudu dan ALLAH, ƙin tankamin yayi, sai ma waya daya ɗauka yay kira, kasancewar a Hans free ya sakata sai naji duk abinda suke faɗa, na fahimci da wani ma'aikacin gidan Alhaji kokinon yay magana, dan ya faɗa masa gamu mun taho ya fito mu haɗu a bayan layin. Dai-dai saitin wani shagon saida kayan abinci dake farkon layin muka tsaya, wani dattijon tsoho ya fito daga shahon, kallo ɗaya naga yayma motar ya ɗauke kansa, sai kuma naga ya buɗe ya shigo baya. Motar boss ya harba gaba batare da yayi magana ba. Nidai mamaki nake tayi a raina, wannan aikin namu gaskiya saida jajircewa da cire tsoro, sai kuma ka iya kowanne irin salo na mutane masu wayo. Gaba ɗaya muka fita daga layin muka shiga wani, shima muka fita muka shiga na gaba, yana tuƙin yana kallon mirror, na fahimci dubawa yake yaga ko ana binmu, ganin babu wani mai bibiyarmu sai yay fakin gefen babban titi da muka fito. Sai lokacin ne dattijon yay magana. "Na tabbata babu wani mai binmu insha ALLAH". Kashe motar yayi ba tare da yace komaiba, ya ɗan kalleni sannan ya juya yana kallon dattijon. "Wannan itace matata, sunanta Bilkisu". "Masha ALLAH, kai ALLAH ya sanya albarka ya bada zuri'a tagari". "Amin" ya faɗa, ni kuma na juya muka gaisa da shi yanata sakamin albarka.
"Baba wannan karonma aiki ya sake kawoni gidanku, kuma ina buƙatar taimakonka kamar wancan karon". "Karka damu ɗana, zan baka dukkan taimakon da kake buƙata insha ALLAHU". "Nagode baba, akwai dattijuwar mai aikin nan da naji kuna kira maman yara ko tana gidan har yanzun?". Jimmm mai gadi yayi kafin ya sauke numfashi, "Gaskiya bata nan, a ƙalla zata kai kusan wata biyu ma kenan bata gidan nan". "Aiki ta ajiye kenan?". "A'a bata ajiyeba, mudai bamusan miya faruba, rana tsaka ɗanta yazo yana nemanta wai kwana uku bai samunta a waya" kallonsa Jawaad yake cikin nazari, "Kana nufin Yazeed?". "Ƙwarai shi kuwa, to dalilin zuwan nasane muka fahimci muma bata gidan, ita dai Uwargida tace ta tambayeta zataje gida wajen rasuwar ɗan yayarta, to nidai ALLAH shine shaida ranar data cika kwana uku da tafiya naganta da idanuna ta dawo gidan lokacin ina sallar isha'i, to amma abin mamaki sai naji ana cigiyarta bayan kwana biyu wai bata gidan". "Ban gane bata gidanba? Kai kuma bakaga fitarta ba?". "Wlhy ban ganiba yarona, dan ita macece mai yawan barkwanci inhar zata fita a gidan nan kota shiga saimun tsokani juna, to a randa ta dawo da yake salla nakeyi sai ban kawo komai a rainaba, abinda ma ya ɗauremin kai da sukace su basu gantaba randa ta dawo ɗin". Shiru boss yayi alamar tunani, dan haka nikuma nace, "To amma baba a wannan daren kana tunanin zata iya fita?". "Gaskiya bazata iyaba ƴata, dan maman yara ma tana da ciwon ƙafa bata cikason yawan kai kawoba". "Hakan na nufin tana cikin gidan kenan kokuma an fita da ita a daren, ko kaine idonka bai nuna maka dai-dai ba?". "Wlhy bana ko tantama itace ta dawo da mangaribar nan, to ƴata wazai fita da ita kuma sai kace wata kaya batare da an gani ba?, shaiɗanin daya taɓa kwatanta hakama mijinki yasa an kaisa gidan maza ai". Murmushi nayi kawai, na ɗan juya na kalla

1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

1 year ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment