Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fitowa da ga bakunan mutane na yanda ta tari motar mutanen da suka fara ganin farkon al'amari da yanda ta tunkari mutanen zai baka tabbacin da gaske tanada kaifin zuciya akan aikinta”.
Cikin jin jina kai na tabbaci Jabeer yace, “Lallai maganarka tana akan gaskiya wlhy Aliyu, nifa abindama ya sake birgeni da ita shine, dukda mugun ciwon da taji, amma saita dake dan tabbatarma da duniya lallai ita ma'aikaciyar tsaroce ta gaske ba ƴar burgaba”.
Fuska shimfiɗe da murmushi Hafiz yace, “Sosaima kuwa Jabeer, dolene ƙaimin yarinyar ya burge kowa, dan kuwa da ƙwaƙwalwa tai amfani wajen fahimtar motar tana da alaƙa da rashin gaskiya, ta kuma nuna himmarta na sadaukarwa koda hakan na nufin zata cutu a wajensu, ta cancanci kowanne irin jinjina ga hukumarnan tamu, musamman idan akai la'akari da shigowarta cikin aiki jiya-jiya kawai, bana tunanin kuma an taɓama fita da ita wani aiki makamancin haka koda sau ɗaya”.
Duk wannan zance da suke faman zubawa akan yabon Bilkisu da jinjina himmarta Jawaad na zaune shima a cikinsu, yana sanye cikin baƙaƙen suit kamar sauran da a kullum suke ƙara masa kwarjinin kasancewarsa ma'aikaci, sai dai ya cire rigar sama, yana zaune ne kawai da baƙin dogon wandon da rigar ciki mai dogon hannu kalar kore mai haske, maɓallan rigar uku a buɗe, hakanne ya bayyana singlet ɗinsa kaɗan fara tas, yaci zanzaro, ya tsuke ƙugunsa da belt kalar shirt ɗinsa.
Abinda zai baka mamaki ko tari bai yiba akan maganar, baima nuna ya fahimci mi suke tattaunawarba sam, yana zaune ne ƙafa ɗaya kan ɗaya tamkar wani basarake, kansa sunkuye yanata faman danne-danne a cikin tab... ɗinsa ta kamfanin Apple, sam fuskarsa babu wata walwala, kuma ba'a tsuke take sosaiba.
Aliyu ne yakai dubansa garesa, tare da faɗin, “Ka fuskanci abinda muke tattaunawa game da yarinyarnan kuwa Jay?”...............✍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.Typing📲

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Page 4
...............Shiru tamkar bazai tankaba, kusan sakanni sha biyar kafin yay magana batare daya bar danne-dannen tab... Ɗinba balle ya kallesu, “Wace yarinya kenan?”. Yay tambayar cikin nuna halin ko'in kula balle su sami ƙwarin gwiwa akan ya jisun.
Duk kallonsa sukai da mamaki saboda yanda sukasanshi dason mutum mai himma, amma yanda ya amshi maganar ya matuƙar basu mamaki a yanzun.
Jabeer ne yace, “Yarinyar jiya daka bama jini mana Jay”.
“Humm” yace kawai ya sharesu bai sake tankawa ba, tsawon mintuna duk sun zura masa idanu suna jiran ƙarin bayani, dan sunyi tsammanin fara jin yabon yarinyar da ga bakinsa ma kafin su su furta, amma ya share kamar ya manta dasu ma a office ɗin.
“Wai boss lafiya kuwa?” Hafiz yay tambayar a wani yanayi.
Sai yanzune ya ɗago ya kallesu su duka, kallo irin a taƙaice ɗinan ya janye mayatattun idanunsa masu cikar gashi da haske tamkar madara, ya taɓe baki kaɗan kafin ya miƙe daga wajen ya nufin kujerarsa ta zama, dan da suna zaunene a rukunin kujeru da'aka shirya a office ɗin domin hutawa ko ganawa da baƙi na musamman.
Sai da ya zauna sosai ya juya kujerarsa tana fuskantarsu kafin yace, “Abun harinmu a yanzu shine mutuwar jami'inmu da sir Ahmad yamin bayani, minene shawararku akan hakan?”.
Aliyu ne ya samu damar faɗin, “Bincike akan shi ɗin wanene? Tunkan fara aiki a wannan hukumar har zuwa farawar tashi, tare da sanin masu bashi gudunmawa akan aikin da yazama sanadinsa, da kuma sanin a ƙarƙashin wa ya samu umarnin”.
“shawara mai ƙyau” Jawaad ya faɗa yana lumshe idanu da kwantar da bayansa jikin kujerar yana lilawa a hankali fuskarsa ɗauke da murmushi, kusan sakanni biyar kafin ya sake ɗagowa yana kallonsu da nazartarsu. Ya ɗauke idanunsa tare da sake komawa jikin kujerar ya kwanta, “Idan an sallamota daga asibiti zatayi bincike akan dukan bayanan Aliyu”.
Cikin matuƙar mamaki suka kallesa, cikin harɗewar harshe Jabeer yace, “wai kana nufin yarinyar?”.
Kallonsa kawai yay ya janye idanu, sai dai baice komaiba. Sun fahimci amsar kenan, dan haka Aliyu yace, “Amma boss baka ganin aikin zai mata girma? Musamman idan mukai dubi akan shine na farko?”.
Cikin halin ko in kula ya taɓe baki, ba tare daya kallesu ba yaja wasu takardu dake saman tebir ɗin nasa yana faɗin, “Maybe hakan, maybe kuma ba hakan baneba, naga kuma da kanku kun yarda da ƙwazonta, to miye kuma na kokwanto yanzun?”.
Babu wanda ya sake cewa komai. sai dai a ƙasan ransu duk sai suka kasance cikin nadamar kwarzanta ƙwazon yarinyar da yawa irin haka, dan a ganinsu bata kai ƙwarin da za'a sakata a irin wannan babban aikin hakaba mai haɗari, musamman idan sukai dubi da ko rose data daɗe a cikinsu baya bata irin wannan damar.
Takardar da ya maida hankali a kanta ya ɗago saitin Hafiz, “Hafiz wanene da wannan bayanan haka?”.
Tasowa Hafiz yay ya dawo gabansa, ya zauna a ɗaya daga kujerun gaban tebirin yana mai amsar takardar, nazarin mintuna biyu ya ɗago kai yana kallonsa, “Akan case ɗin yaron nan da aka samu makamai a shagonsu ne, Aliyu ne akan binciken kuma”.
Jawaad ya maida kallonsa ga Aliyu, hakan ne ya saka Aliyun tasowa ya nufosu shima.
__________★★__________
BILKEESU
_________________________________
Wani irin mayataccen ƙamshi ya shiga rige-rigen zirarawa cikin ƙofofin hancinanmu yayinda muke shiga motar da boss ya turo ɗaukarmu, batare da kowannenmu ya fargaba muka tsinci kawunanmu da lumshe idanu muna sake buɗe hancunan namu sosai. A haka yaja motar muka bar asibitin, tabbas wannan ƙamshine daya cancanci ajiyeshi a ma'ajin zuciya da ƙwaƙwalwa saboda ya kasance na musamman, bansan miyasa na kirashi na musammanba, sai dai kawai zan iya fassara hakan da kasancewarsa na musamman a duk lokacin da hanci ya shaƙa koda ba namuba. Naji tamkarma kar motar ta tsaya ace na daina shaƙar wannan ƙamshin, sai dai babu yanda zanyi dan hakan tilasne. A wannan yanayin muka isa gida, ya ajiyemu a gate ya juya, mukuma muka shiga ciki bayan mun masa godiya.
Mun iske gidan babu kowa, suna gidan rasuwa su duka, dan haka mukai zamanmu dagani sai Ummie da tace boss ya bata umarnin ta zauna dani harna warke tun a jiya. Ban tambayeta daliliba, kamar yanda itama bata kawo komai a rantaba game da hakan, sai dan tana ganin ya fahimci bani da wadda nakeda kusanci da shi sama da ita a station ɗin namu.

__★.:.★__________★.:.★__
JAWAAD
_____★.:.★__________★.:.★_____
Suna tsaka da cigaba da magana shi da su Aliyu kira ya riskesa daga office ɗin B.G, duk da kiran ya bashi mamaki daga shi harsu Jabeer ɗin hakan bai hanashi fita domin cika umarni ba.
Galala nai da baki ina kallon haɗuwa da tsari na office ɗin da Jawaad ya shiga, komai yaji babu algus. Banma kaina buƙuluba nabi ko'ina daki-daki da kallo a office ɗin, kafin na sauke idanu ga mai ikon faɗa aji na hukumar tasu. Danƙari, na ambata a zuciyata dan kuwa munzo ƙarshen zance, sam babu alamun fara'a balle sassauci tattare dashi, Jay ya miƙa gaisuwa cikin girmamawa kafin ya samu izinin zama daga gareshi.
“Sir Ance kana kirana” Jawaad ya faɗa cike da girmamawa.
A cikin maƙoshi ya bashi amsa da cewar, “Uhhm” daga haka yaja bakinsa yay tsit. Gani nai shima Jawaad ɗin ya sake kame kansa ba tare daya sake tankawa ba, kusan mintuna huɗu suna a haka kafin ya ɗago kai tare da juyama Jawaad fuskar lap-top ɗin dake gabansa, hotone mai motsi (video), Bilkisu ta bayyana tana harbi da bindiga har guda biyu a rikicin jiya, gaba ɗaya bidiyon bai wuce na minti ɗaya da wasu sakanni ba, saboda iya itaɗin kawai aka nuna, ƙarewarsa ce ta saka Jawaad kallonsa cikin rashin fahimta.
Cikin zafin rai da fusata ya zazzaroma Jawaad ɗin idanunsa jajaye, “Wannan yarinyar tanada izinin yin harbi ne kamar haka dama?”.
Jawaad da ya tsuke fuska shima ya girgiza kansa kawai.
“Ya akai tayi kuma?”.
Sai da Jay ya furzar da huci kaɗan kafin yace, “Sir bamu da wani zaɓine bayan hakan, domin musayar wutace, idan kuma bata da makamin kare kanta a hannu rayuwarta na cikin haɗari, musamman daya kasance da taimakonta muka riski masu laifin”.
“Hakan yana nufin shine matakin ƙarshe da kuke da mafita kawai?”.
Shiru Jawaad yay bai motsaba, sai maƙogwaronsa ne keta kai kawo a cikin wuyansa, yayi kicin-kicin da fuska.
“Da kai nake magana Captain!”.
“Sir nasan munyi kuskure, amma a duba uzirinmu muma, musamman na isa wajen a ƙurarren lokaci, sannan a duba irin rawar da yarinyar ta taka, duk da kasancewarta ƙaramar ma'aikaciya, wadda ta shigo jiya-jiya cikin wannan hukumar tamu, ta nuna ƙwazon da ya kamata a jinjinama ƙoƙarinta ba ƙalubalantar taba, domin kuwa ita bata da laifi, nine mai laifi dana bata bindigar”.
“Uhyim, kana nufin yanzu dai ka kareta?, sannan dukkan hukuncin da zai biyo baya zaka ɗauka kuma?”.
Shiru tamkar bazai amsaba, sai kuma ya ɗago idanunsa harsun kaɗa da ɓacin rai, a kasaushe yace, “Aimin duk hukuncin da za'ai matan babu damuwa”.
Shiru B.G yay kawai yana kallon Jawaad ɗin, yasan yaron dama akwai taurin kai, dan tun shigowarsa hukumar ƴan sanda ma da tsaurin ido ya shigo, kasancewar wanene mahaifinsa yasa aka hana kowa nuna masa yatsa, himmarsa da zafin nama ne ya saka aka maidoshi cikin hukuma DSS, shi kuma har cikin ransa yaron bai masaba, sanin dalilin kuwa wannan sirrinsane....
“Kaje zamu nemeka” B.G ya faɗa a daƙile.
Uffan Jawaad baice ba, ya miƙe kawai tare da yin salute nashi ya fice abinsa yana haɗiyar zuciya, duk wanda zai iya ganinsa a wannan lokacin dolene ya fahimci ransa a matuƙar ɓace yake, mai makon ya wuce office ɗinsa sai ya nufi office ɗin L.C, wato sir Ahmad barewa, canne kawai zai kai damuwarsa ya samo mafitar da yake buƙata.
Bayan yay knocking ƙofar aka bashi izinin shiga, ya riga da yasan ya gansa ta cctv, tunda ya turo ƙofar ya shigo sir Ahmad ya fahimci akwai damuwa, ya kafeshi da idanu kuwa, yayinda shi kuma Jawaad ɗin yaƙi yarda su haɗa idanu.
Sai da ya miƙa gaisuwa Sir Ahmad yay masa nuni da kujera alamar ya zauna.
Koda Jay ya zauna sai baice uffanba, sai ajiyar zuciya kawai yake faman yi, sir Ahmad yay murmushi irin nasu na manya masu kaifin tunani, kafin ya miƙe daga mazauninsa ya nufi firij ɗin dake a office ɗin, goran ruwa ya ɗakko ya miƙa masa batare da yayi magana ba, babu musu ya amsa, ya ɓalle murfin yana kai goran bakinsa, sai da ya shanye fin rabi sannan ya ajiye yana sauke numfashi a jajjere.
Wani murmushin Sir Ahmad ya kumayi, sannan ya zauna a kujerar dake kusa da Jawaad ɗin suna kallon juna “Captain! Lafiya kuwa? Waya zinguro mazajene?”.
Idanu Jay ya ɗago ya kalli Sir Ahmad, sai kuma ya janye yana shaƙar numfashi da zafi.....
“Jay!”
Sir Ahmad ya kirayi sunansa yana ɗora hannunsa bisa kafaɗarsa.
A karo na Biyu Jawaad ya sake kallon Sir Ahmad barewa, ya cije leɓensa da ƙarfi yana faɗin, “Daga office ɗin B.G nake Sir”.
“Na sani ai” cewar sir Ahmad yana murmushi.
Cikin sauri da tsagwaron mamaki Jawaad ya kalli Sir Ahmad, kallo irin na tuhuma.
Ƴar dariya sir Ahmad yayi, ya kuma kai hannu ya bubbuga kafaɗar Jawaad ɗin a hankali, “Kar kai fushi yarona, karkuma ka shiga ruɗani, banason ka manta kanka a cikin mutane masu kaifin basira, za'ai amfani da yarinyarne kawai ai wasa da hankalinka, kaga kenan an samo lagwonka da damar bama maƙiyanka yin wasoso a saman mutuncinka, kar kaga laifin B.G, shima sashi akayi, domin bana tantama umarni ya samu daga sama, sai dai wanene? Akan minene? Shine ban saniba”.
“Zuutt!” wani abu dake tsaye a maƙoshin Jawaad ya faɗa cikin cikinsa, ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, saboda dai Sir Ahmad ya dawo dashi a hayyacinsa da wuri...
Sir Ahmad ya miƙe yana murmushinsa na kamilallun mutane, ainahin kujerar zamansa ya koma ya zauna..
“Abin bai baka mamakiba ace iya inda take harbin kawai aka kawo masa, sannan kuma ita kaɗai, bayan kuma batakashin da kuka gwabza a wajen ku kusan goma ne”.
“Sir ai abinda ya matuƙar ɓatamin rai kenan, taya za'ai ace itace kawai za'a ɗauka?....”
“Saboda ita kaɗai tazo da salon da ya ajiye ruɗani a zukatan masu fargaba akan jajircewarka”.
“Salo kuma sir?!”.
“Yes! Jawaad, salo mai ƙayatarwama kuwa, andaɗe ba'a samu mai ƙaracin shekaru irinta da wannan ƙwazonba, abin ƙarin mamakin kuma gata mace, yarinyar da alama zata ajiye tarihi a wannan hukumar, dan alamomin hakan sun farane daga jiya”.
“Sir! to amma su wanene ke ganin hakan matsayin ƙalubale garesu? Miyasa kuma....?”.
“Nima ban saniba Jay”.
Shiru Jawaad yay na wasu sakanni kafin yace, “Saboda mi suka zaɓi hukuntata bayan karramawa ta cancanta dashi sir?”.
Sir Ahmad yay gajeruwar dariya idonsa akan Jay, yace, “Saboda ƙwazonta abin dubawane ga mai hankali, sannan abin tunani ga irin waɗanda basa buƙatarta, wannan shine aiki na farko da yarinyar tayi, kuma ba sakata akayiba, sai dai ƙwazonta ya girmi matsayinta da gogewarta a aikin, hakanne ya sakasu saka maka alamar tambaya (?), musamman daya kasance tare da kai aka fara ganin baiwar ta ta”.
Karan farko da Jawaad ya ƙyalƙyale da dariya harda dukan tebir ɗin gabansu, Sir Ahmad dake kallonsa shima murmushinsa ya faɗaɗa, ya juyo sosai yana fuskantarsa, har yanzu kuma fuskar tasa da sauran dariyarsa irin wadda kafin yayita akan kai ruwa rana,
“Sir kasan minene kuwa?”.
“Saika faɗa Jawaad”.
“Sun bani dariya ALLAH, danni Ko sunanta ban saniba fa”.
Dariya shima sir Ahmad ya shiga ƙyalƙyalawa, kafin yace, “Cakwakiya kenan, to tabbas kuwa daga masu wannan ƙullin abun ba haka bane ba Jawaad, kallon ƘWAI CIKIN ƘAYA sukema lamarin”.
“Nima na fahimci hakan a yanzu sir”.
“Yayi ƙyau. Miya faru jiya?”.
Tun daga farkon zuwansu inda abun ya faru har ƙarshe Jawaad ya bama Sir Ahmad labarin komai bai ɓoye masaba.
Kai kawai Sir Ahmad yake jinjinawa har Jawaad yakai ƙarshen jawabinsa, ya sauke numfashi kaɗan yana faɗin, “Zamu shiga meeting anjima, kuma nasan akan wannan maganarne, shawara ɗaya dazan baka yanzu shine, kai ƙoƙarin gano wanda ya ɗauki wannan bidiyon, sannan kayi gaggawar samo bidiyon da yafi wannan na wajensu tsaho, ka kumayi saurin rubuta bayanai akan komai ka tura office ɗin L.G tare da bidiyo ɗin daka samo ɗin”.
Kamar Jawaad zaice wani abu, sai kuma yay shiru yana miƙewa da faɗin, “Okey sir, zanyi ƙoƙari insha ALLAH”.
★★★★
Gaba ɗaya kan Jawaad ya kulle da wannan lamari, ya rasama ta yaya zai fassara al'amarin, maganganunsa da Sir Ahmad kawai ke masa kai kawo a cikin zuciya, tare da zuwansa office ɗin B.G, ya rasa ina zai kama ma shikam? Yana buƙatar ganin su Jabeer tare dashi yanzunan, sai dai tabbas bazai yuwu a station ɗinanba, dan yanzu dukkanin motsinsa abin bibiyane.
Ƙaramar wayarsa ya ɗauka ya turama Hafiz saƙo, kafin ya tura wayar aljihu bayan ya kasheta gaba ɗaya ma, wasu takardu ya ɗiba ya fito a hanzarce, hana kowa ya bisa yayi, ya shiga mota shi da Gimba kawai suka fice daga station ɗin.
Danne-danne yaketa famanyi a lap-top, hakan ya saka gimba kallonsa ta cikin madubi, “Boss! Ina zamuje?”.
Ba tare da ya ɗagoba yace, “A.Y Street”.
Cikin girmamawa Gimba ya amsa, tare da juya kan motar suka nufi hanyar gidan Jawaad ɗin dake anguwar A.Y street.
Sunyi wajen mintuna talatin da zuwa kafin su Aliyu su iso. A falo suka iskeshi har yanzu yanata faman danne-danne a lap-top, a haka ya amsa sallamarsu ko ɗagowa baiyiba ma. Sai da suka zauna da kusan mintuna biyu sannan ya ɗago ya kallesu, kallo ɗaya yayma Rose ya ɗauke kansa, hakan yay bala'in sosa ranta, dan akwai kwallin data shafa, an kuma tabbatar mata idan suka haɗa ido da shi zai haukace mata, yabar kallon kowacce mace da gashin arziƙi sai ita, amma ɗan rainin wayon tun'a station takeson su haɗa ido da shi hakan ya gagara...
“Boss! Lafiya dai ko?”.
Aliyu da ya kafeshi da idanu ya faɗa.
Lap-top ɗin ya ajiye yana faɗin, “Da dai sauƙi Aliyu, an yanka ne ta tashi”.
“Kamar ya?;” suka faɗa cikin haɗa baki su uku, rose ce kawai da bata fahimci hausarba batace komaiba.
Cikin takaici Jawaad yace, “Ƴan uwana wasan jiya ya koma yaƙi, kukan tsuntsuwa mai zanen kanari ya zame mana abin magana”.
Sun fahimci zaurancensa, saboda wannan yana ɗaya daga cikin salonsu, musamman akan aikin da suka samu gamayya da waɗanda basa cikinsu, sai dai basu fahimci dalilin zaurancenba a yanzu, saboda duk sune a wajen babu baƙon ido.
Jabeer yace, “Jay bansan miyasa ka zaɓi ƙin buɗe zancenba, bayan kuma duk mune babu wani bare a cikinmu?”.
Jawaad yace “Nima bansan miyasa harshena ya zaɓi hakanba Jabeer, sai dai saƙon kamar tun daga zuciyane”.
“Idan na fahimta, kamar zuciyarka na ɗarsa maka akwai ɗan baya ga dangi kenan a cikin tafiyar?”. Hafiz yay maganar cikin taraddadi.
Cikin sauke nannauyan numfashi Jawaad yace, “Bani da tabbas, sai dai zuciyata na rayamin akwai idon mikiya a bayanmu”...............✍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻[11/30/2020, 1:02 PM] HASNA✍🏻: Bilyn Abdull 📚:
Typing📲


Page 5
      
        .............Duk Kasa cewa komai sukai, sai idanu da suka zubama Jawaad tamkar wani bakonsu.
             Rose da zuciyarta ke tafasa akan rashin kallonta da jawaad baiyiba ta kasa daurewa, ta dubesu baki ɗaya a wani yanayi, “Boss wai mike fauwane? tai maganar cikin harshen turanci da tsare Jawaad da idanu tana fatan ta dace yanzun.
       A mamakinta yanzunma dai ƙin kallonta yayi, sai Lap-top ɗinsa ya miƙa mata kawai, ya koma ya zauna tare da ɗaukar tab.. Ɗinsa ya shiga tafa saƙo da hanzari.
      Gani nai Aliyu ya ɗago ya kallesa, yay masa wani salo da ido tare da cije baki, murmushi Aliyu yayi kawai ya maida kansa, kafin ya miƙe yabar falon, hakama Jabeer da Hafiz duk ya tura musu suma, Hafiz shima tashi yay ya fita, Jabeer kuma ya koma kusa da Rose dan kawai ya ɗauke hankalinta da aikin da Jay ya bata itama.
         Bayan fitar su Aliyu da kusan mintuna tara ya miƙe yabar falon ya nufi bedroom ɗinsa. Sai da ya kulle ƙofar kafin ya ciro ƙaramar wayarsa yay kiran Hafiz.
          “Hafiz yaya? An dace kuwa?”.
“Ba'a daceba Boss, amma ga shawara mana?”.
       “Micece shawarar taka?”.
“Mu bincika kowanne manhajar yanar gizo ko zamu dace wani ya ɗauka, kasan yanzu ba'a raba mutane da ƴan ɗauke-ɗauke a waya, maganar gano wanda ya kaima su B.G kuma ba abune mai sauƙiba ace yanzu da gaggawa, sai dai mu canja shawara ta wannan gaɓar”.
       “Na fahimceka Hafiz, yanzu kayi duk yanda ya dace, amma inaji a raina koma wanene yakai wannan bayanan yana da kusanci damu Hafiz, amma banason zargin kowa”.
       “Boss zargi dolene, kuma koma wanene ya daɗe a jikinmu, a sannu zamu cinmasa da ƙarfin ƙudirar UBANGIJI, dan shine ke haska mana hanya a dukkan lamuranmu”.
      “Insha ALLAHU Hafiz, yanzu dai sai na jika”.
      Yana yankewa yay kiran Aliyu shima, sai dai daga ɓangaren Aliyun an dace, dan ya turo masa dukkan bayanai akan Bilkisu da abinda ya shafi shigowarta hukumar tasu, da horon data samu, da ƙwazon data nuna tun a wajen horaswa, alaƙarta da Qaseem,  sai dai babu wani bayani kafin zuwanta gidansu Qaseem ɗin, hakkanne yaɗan tsayama Jawaad a zuciya, har yakejin dolene ya sake binciken, dan karfa nan gaba ta zame masa ƘWAI CIKIN ƘAYA kuma kamar yanda ƴan bayan fage ke hasashe.

         Daga ɓangaren Hafiz ma an dace daga baya, dan kuwa cikin amincin ALLAH ya samo bidiyon faruwar komai tun daga lokacin da Bilkisu ta kaima motar masu laifin caffa kafin zuwansu, har zuwa sanda abubuwa suka lafa.
        Yaci karo da Bidiyon ne a wani chennal na youtobe, bayan ya shiga manhajar Google yay Searching, sai dai abinda ya bashi mamaki yana kammala sauke video'n akan manhajar ta youtobe wanda ya ɗora ɗin ya saukeshi daga accaunt ɗin, hakan sai yay bala'in ɗarsa mamaki a zuciyar Hafiz, harya kasa haƙuri ya kira Jawaad ya shaida masa.
         Murmushi Jay yayi yana shafa kansa, “Ba abin mamaki bane Jabeer, musamman idan mukai la'akari da babu wata kafar yaɗa labarai da dama ta saki bidiyon mai tsawon hakan, sai wasu ɓangarori da dukansu iya inda muke musayar wutane kawai”.
       Hafiz yace “Hankalina sam bai kaiba sai yanzu kam, koma miye yake a ɓoye ALLAH zai bayyanashi ai, mudai domin ALLAH mukema ƙasarmu aiki, duk mai yunƙurin daƙilemu kuma ALLAH zai mana maganinsa”.
      “Insha ALLAHU kuwa Hafiz” Cewar Jay cike da takaici.

Kafin dare duk sun haɗa bayanan da ya kamata akan maganar, sun tura iya waɗanda Sir Ahmad ya umarcesu zuwa Office ɗin, L.G, sauran kuma sun adana a wajensu domin ya zame musu hujjar kare kai, hatta da bidiyon suma gutsira sukai suka tura, sauran kuma suka adana a wajensu.
      

    
                _______★__________
                           SHAHUDAH
     _____________________________

                   Tunda suka fara zuwa gidan rasuwarnan sau ɗaya taga Jawaad, harga ALLAH ita kuma dominsa take zuwa, a tunaninta idan suka haɗu zai matuƙar rikicewa da ganinta, musamman ma yanda ta sake canjawa da ƙyau mai ƙayatarwa, sosai ta gama shirya shika-shikan rama dukkan abubuwan da yay mata kafin ta yarda da buƙatarsa ta komawa gidansa.
     Sai dai abin mamaki da al'aj

abi dukkan tunaninta sai bai zama gaskiyaba, dan kuwa ko a randa suka haɗu kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa, komai kuma a kan idanun Mom ya faru, dan suna a falon mama Atika ne a washe garin rasuwar ya shigo da baƙi su Sir Ahmad da sukazo gaisuwa. Sarai idanunsa sun gane masa Shahudah, amma sai ya ɗauke idanu cikin nuna halinsa na ko'in kula da abu.
       Abin ya sosa mata rai sosai, amma saita danne da yaƙinin ƙila yayi hakane saboda ganin suna cikin jama'a. Koda suka koma gida sai basuyi maganar da Mom ba, saboda kowa ya dawo a gajiye wajen bacci yafi buƙata. Washe gari kuwa kwalliya tayi ta musamman dan Jawaad nanma babu sa'a, dan har dare da suka baro gidan bata sakashi a cikin idanunta ba, washe gari kuma suna isowa gate ɗin gidanne motar Jawaad ɗin ke fita da alama ya nufi office ne. Waɗanan akasin da akaita samune suka jefata a cikin damuwa har yau ta kasa daurewa.

      “Mom kinga abinda Bb ya kemin kuwa? Bayan ya kamata ace ya nuna zalamarsa da kewata na shekarun da muka kwashe bama tare”.
      “Huhm” Mom ta faɗa tana shafa kan Shahudah dake saman cinyarta, dan kuwa suna cikin bedroom ɗin Mama Atika ne ita da Shahudahn kawai, dan ta fahimci ɗiyar tata na tare da damuwa, yau tunda sukazo gidan ta shigo ɗakin Mama Atika bata sake fitaba, shiyyasa ta biyota, sai ta isketa cikin damuwa, hakanne ya sakata zama ta dora kan Shahudah a cinyarta tana shafawa, itakuma take bata labarin ruɗanin data shiga akan tarbar data samu daga wanda batai tsammaniba daga Bb ɗinta (Jawaad).
       Mom ta haɗiye abinda ya tsaya mata a maƙoshi tana sake yamutsa sumar Shahudah'n, “Kar taurin kan yaron nan ya ɗaga hankalinki fiye da haka Shahudah, ki barsa, ni da kaina zan sauke masa wutar dake ci a kansa, bara dai a gama hidimar rasuwarnan kinji”.
      Kai Shahudah ta ɗaga mata cike da shagwaɓa, har ƙwalla na sakko mata a kan kumatu tace, “Amma Mom wane mataki zaki ɗauka to?”..
    Mom ta share mata hawaye tana murmushi, “Karki damu Shahudah zaki gani, kedai sonake kicigaba da kwantarmin da hankalinki, nan kusa kaɗan zaki dawo ɗakin mijinki”.
        Kai Shahudah ta ɗaga mata tana murmushi da rungume mom. Murmushi mom tayi taci gaba da lallashinta cikin so da ƙauna.

Nikam nace, “Mai uwa a gindin murhu baya cin tuwonsa gaya ai Shahudah😋😜🤸🏼.

               ..::..★__________★..::..
                          BILKEESU
     ____★..::..★__________★..::..★____

          Kwanaki huɗu cir bana zuwa Office ina gida ina jiyyar hannuna, yayinda kullum Ummie ke tare dani, ƴan gidanmu kuwa basa yini suna gidan rasuwa, barci kawai ke kawosu gidan. A kwana na biyar nai shirin komawa aiki, dan naji sauƙi sosai, a kuma daren ranarne Yah Qaseem ya dawo, nayi farin cikin dawowar tasa, dan nikaina nasan idan nace banason Yah Qaseem na yaudari kaina, a ƴan kwanakinan da bayanan sosai nayi kewarsa.
       Tun a daren yake jeramin tambayoyi akan hannuna, bai samu amsa ko ɗaya ba daga

1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

11 months ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment