Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

boss ɗin dake saurarnmu sannan na maida ga baba, "Baba a wannan ranar mota nawa ta shiga gidan ta kuma fita bayan dawowar maman yara?". "Babu wanda yazo tunda Alhaji baya gari ma, sai wani yaro ɗan dogo baƙi mai dogon hanci da ya kanzo lokaci-lokaci idan Alhaji na nan, to ni a ranarma da yazo ɗin saida na sanar masa baya nan ai Alhaji, sai yace ai ya sani saƙo zai bama hajiya inji Alhajin. Daga haka ban sake tofa komaiba na barshi ya shiga ni kuma na shige ɗakina, to baifi mintuna goma sha biyar da shigaba ma naji yana horn nazo na buɗe masa ya fice". "Kasan sunansa baba?" "A'a gaskiya ƴata, ban saniba wlhy".
Waya boss dake saurarenmu ya ɗauka ya shiga daddanawa, kafin ya miƙama baba wayar yana faɗin, "Shine wannan?". Amsa baba yay ya kalli hoton, cikin jinjina kai da murmushi yace, "Tabbas shine kuwa ɗana". "Baba ka tabbata?". "Babu tantama a zancena". "Shikenan mun gode, bara mu maida kai, sai dai zamu iya dawowa gareka a ko wane irin lokaci". "Babu damuwa wlhy ɗana duk sanda kake buƙatar wani abu ka kirani". Godiya muka sake masa, ya tada motar yay reverse, a wani wajen muka saukesa saɓanin inda muka ɗaukesa.
Jin yayi shiru sai na ɗan kallesa, "Hoton wanene ka nuna masa dan ALLAH?". "Zaki gani yanzun" ya faɗa yana karya kan motar muka shiga wani layi. A ƙofar wani gida madaidaici yay fakin, ganin zai fita nima sai na buɗe na fita. Mun gaisa da samari uku da alama ta nuna suke tsaron gidan, yanda suke gaishemu cikin girmamawa nasan lallai shine ya ajiyesu. Ɗakin farko dake a gidan muka shiga, inda muka iske matashin saurayi zaune, shigowarmu ta sakashi miƙewa yana murmushi da mana sannu da zuwa. Na buɗe baki zan amsa kawai naji tass!!!.
Idanu na zaro baki a hangame ina kallon boss da ya saukema saurayin mari, ban gama fita a mamakinba naga ya hau dukansa. Dukansa yake ta ko ina, a take jikina ya fara rawar tsoro, nasa hannu na rufe fuskata ina ambaton "innalillahi....." da sauri na buɗe fuskata jin ƙarar ɗana kunamar bindiga, nai masifar sake zazzaro idanu waje ina faɗin, "Boss badai kashesa zakai ba?". Harara ya balla min ya ɗauke kansa yana huci.
A tare muka saki ƙara ni da saurayin saboda harbinsa da yay a ƙafa, zufa ta shiga rige-rigen karyo masa, jikinsa na wani irin rawa, ko kallon inda nake baiba ya ranƙwafa kan saurayin yana hure bakin bindigar dake ɗan hayaƙi da faɗin, "Kaga bindigar nan cike take taf da alburusai, kuma idan zan ƙarar dasu tas a sassan jikinka babu mai tambayata yaya nai da su?, wannan harbin danai maka na ƙaryar daka mince, idan wata ta biyo bayanta yanzun kuma wlhy saina faffasa gaɓɓanka ɗaya bayan ɗaya da alburusan nan kafin na aikaka lahira dan ubanka. Ina kakaita itama?". Jikin ɓaleru na rawa ga jini na malala a ƙasa cikin hakkin kuka da azabar shigar harsashi yace, "Bansan wacce kake maganaba oga, dan ALLAH karka kasheni, nayi kuskure a farko amma wlhy bazan sake kwatantashi ba". "wani rainin hankalin zaka sakemin?" ya faɗa a taƙaice yana sake ɗaure fuska da ɗana kunamar bindigarsa.
"A'a wlhy oga ba haka bane ba, na tuba dan ALLAH zan faɗa maka komai, bata a garin nan". "Amma ranar ca kaimin baka da alaƙa da Alhaji kokino, bama ka sanshiba ko?" ya faɗa yana ɗora masa bindigar a saman kai. a take jikin ɓaleru ya ƙara ƙarfin mazari, harya jiƙe wandonsa da fitsari, "Oga kawa ALLAH da MANZONSA karka kasheni, ka yafeni, komi kake buƙata yanzu wlhy zan makashi, harma abinda baka saniba zan faɗa maka". Ƙafa Jay ya saka ya danna ƙafar ɓaleru daya harba. Ya sake sakin wata wahalalliyar ƙara jikinsa na karkarwa.
Da sauri nazo na riƙe hannunsa ina hawaye. Janye ƙafar tasa yay ya juyo yana kallona da wani murmushi irin na tsagwaron muguntarnan, ya lakacemin hanci da faɗin, "Ki rage wannan tausayin malama". Rungumesa nai da sauri ina faɗin, "To dan ALLAH kayi haƙuri ka barshi haka tunda yace zai faɗa mana".
"To na barsa" Jay ya faɗa yana ballama Ɓaleru da keta kukan wahala harara da shafa bayan bily data lafe a jikinsa. Sai da ya tabbatar tayi shiru sannan ya ɗagota ya share mata hawayen tas da sumbatar goshinta.
Jikkata ya amsa ya buɗe, ya fiddo biro da ɗan littafi dake ciki ya jefama ɓaleru, duk da halin da yake ciki haka ya ɗauka ya rubuta masa address ɗin. Yana sharar hawaye da sauke numfarfashi yace, "Oga gidan akwai matakan tsaro sosai, hanyar da zaku iya fiddota cikin sauƙi itace kiran masu tsaronta da wayar Alhaji kokino". Uffan baice masaba, saima waya daya kira, mintuna kaɗan saiga ɗaya daga cikin masu tsaron gidan ya shigo. A daƙile yace, "A cire masa wannan bullet ɗin a tsaida jinin". Da girmamawa ya amsa da "Yes Sir" hannuna ya kama kawai muka fice, sai binsa nake da kallo da ɗunbin mamaki, ban taɓa zaton tsaurinsa ya kai hakaba, nikam tsoroma yake ƙara bani yanzun.
Sai da muka fara tafiya sannan yay magana hankalinsa nakan tuƙi, "Tunaninmu na samun wayar kokino yana a kan hanya, wannan tsoron da tausayin naki kuma dole ki cireshi dan aikinmu baya buƙatarsa". Kallonsa nayi sai naga bani yake kallo ba, yama fuske abinsa tamkar bashine yay maganarba. Nima bance komanba amma sai juya lamarin nake a rai, 'sai kace a cikin film? kai anya kuwa ban sako kaina inda yafi ƙarfina ba? Wani ƙarfin zuciyar ai sai maza dole'.
Da wannan tunanin a raina muka iso wani waje saɓanin station da nai tunanin zamu koma. Fakin yay sannan ya ɗauka waya yay kira. Yanda ya kwantar da murya tamkar ba shine ya gama hargagi yanzunba sai ya bani mamaki, jin kuma da mace yake maganar dan a hans free yasa sai naji wani abu ya dunƙulemin a ƙirji na takaici. Ƙin kallona yay ya cigaba da wayarsa, "Kiran da nai miki yanzu ai ya tabbatar miki ban manta da ke ɗinba". Cike da yanga daga cikin wayar akace, "Kai dai kanason kare kanka, shekara biyar ai ba kwana biyar bace". Baki naga ya wani taɓe da ɗauke kai kamar yana a gabanta, a zahiri kuma sai ya sake kwantar da murya da faɗin, "Tom nayi laifi, amma nima bana ƙasar ai, yanzu ma dai akwai wani taimako da zakimin akan Dadynki". tace, "To yanzu na fahimci dalilin kiran, tunda ba taɓa kirana kayiba, inma na kira baka ɗagawa" "Humm" ya faɗa batare da ya bata amsar zancen nata ba, "Yanzu dai bazakimin taimakonba na nema wani?" "Ah haba, kaima kasan bazan iyaba ai, ko karan gidanka ka aiko da buƙata ai zan biya masa balle kai ɗin da kanka" "Yayi" ya faɗa a taƙaice, sannan ya cigaba da faɗin, "Wani ƙulli da ake sonma Dadynki mukeson kwancewa batare da ya saniba, dan haka mukeson ki ɗebo mana dukkan phones nashi a daren yau zuwa safiya insha ALLAH za'a dawo dasu ki maida masa batare da ya saniba". Jimmm tai alamar tunani, kafin ta sauke numfashi da faɗin, "Tab wannan aikin baiyi girmaba kuwa Jay, Dady fa ko Momy bai bari ta taɓa masa waya balle mu, to ta inama zan fara hakan?". "Yanda za'ai ɗin ke ya kamata kiyi tunani, inba hakaba komai zai iya faruwa da shi, idan kuma kin zaɓi komai ya farun akan ki bada haɗin kai a taimakesa kafin ya farun to babu damuwa sai anjima....." da sauri tace, "A'a tsaya-tsaya, ka bani lokaci zanje nayi tunani, nanda magriba idan da yuwuwar hakan zan turo maka saƙo, dan matsalar shine kasan shi business yake, komai dare kuma amsa waya yakeyi, to tayaya za'a ɗauka har sai zuwa safiya a maido bai fahimta ba?". "Kidaiyi ƙoƙari mugani". "Shikenan sai ka jini" ƙitt ya yanke wayar tare da juyowa ya kalleni. ɗauke kaina nai gefe batare da nace komaiba. Shima ɗin baice min ɗinba, saima sallama da naji ya sakeyi alamar wata wayar.
kiran oga Hafiz yay aka yayma su Jabeer magana su zo su samemu a office ɗin da aka buɗe na karɓar cases ɗin masu fyaɗen nan, dan yanada buƙatar sanin komai a yau ya fasa gobe, amma kafin sannan su fara turo su Ummie sannan, kafin su su biyo bayansu nanda mintuna talatin.
Duk da abin ya bama Hafeez ɗunbin mamaki sai bai tambayi dalili ba ya amsa masa da to kawai, dan yasan zai musu bayani. Wayar ya ajiye yana sauke numfashi, ya kamo hannuna cikin nashi tare da saka ɗayan hannunsa ya juyo da fuskata garesa. "Na matan ne ya motsa?". Yay maganar gab da fuskata yana wani ɗagemin gira. Fuska naɗan ɓata nace, "Miye na mata?". "Kishi mana" ya bani amsa da lakacemin hanci. Bansan sanda murmushi ya suɓucemin ba nace, "Nidai ai ban faɗaba". "Ai shi ba sai an faɗaba, a fuska ake ganoku". Mintsininsa nai a hannun da yake murzamin cinya. Ya ɗauke da sauri yana faɗin, "Ouch!, muguwa". Dariya na ƙyalƙyale da ita, dan yanda yay da fuska kamar wani ƙaramin yaro.
Murmushi Jay yay yana kwantar da kansa a kafaɗarta da lumshe idanu dan dama soyake yaga ta dawo cikin walwalarta.
Babu jimawa sai gasu Zuhrah sun iso, cayay na fita na samesu mu shiga wajen tare, shi zai jira su Oga Aliyu.
"Anacan anashan soyayya an barmu" cewar Ummie sanda na iso inda suke. "Ya ranki ne?" na faɗa ina mata gwalo. Dariya su Zuhrah suka sanya mana, Ummie kuma tace, "Fari ƙal, muma ai tana tafe garemu, a lokacin wasu sun tsufa". "Ko kuma mun zama gwanaye ba" na bata amsa ina mangare ƙeyarta.
Yanayin yanda aka tsara wajen ya birgeni sosai wlhy, ga matansu Oga Jabeer sunata aiki tuƙuru, gaisuwa mukai cikin girmama juna suna tsokanata wai har mun dawo daga Honeymoon ɗin. Dariya kawai nayi bance komaiba. Muka rungume juna da Amina ina tambayarta ya mama da yaya sule?.
Babu jimawa da zamanmu su boss suma suka shigo, bayan anyi ɗan gaishe-gaishen juna matar Jabeer data kasance shugaba ta fara mana jawabin cigaban da aka samu musamman ma ni da Boss da bamusan yanda ake ciki ba.
"Ƙasarnan danƙare take da cases na matsalolin fyaɗe, wasu sunma kai kotun amma rashin gata yasa an watsar da shari'oinsu, daga baya an saki waɗanda suka aikata laifin, wasu ko tsoro yama hanasu fitowa su faɗa. A yanzu haka dai munada ƙararraki kusan saba'in da uku a cikin kwanaki goma sha shidda kacal da shelanta ƙunyar, mun gama bincike akan ashirin da ɗaya kamar yanda muka sanar maka, mun tabbatar da gaskiyarsu kuma harma munsa an kama wasu daga cikin masu laifin, wasu kuma muna kan fakonsu, sai cases Goma sha huɗu masu kamanceceniya da irin wanda muke nema".
Kai Jawaad keta jinjinawa yanajin daɗi da ƙaunar abokan nasa, ya ajiye file ɗin hannun nasa da matar Hafiz ta bashi yana gyara zama, "Wace shawarace da ku yanzu akan goma sha huɗun da muka samu? Dan kunga idan muka haɗa da baƙwai ɗin dake ƙasa sun zama ashin da ɗaya kenan".
Aliyu yace, "Hakane, ni dai a nawa ganin shine mu fara bincike akan gidajen da duk abin ya faru, dan abinda zai baka mamaki da ɗaure kai waɗanda abin ya faru dasu dak ƴaƴan masu gidan ne, ko ƴaƴan ƴan uwa, kuma babu gidan talaka, ƴaƴan talakawan da tsautsayin ya hau kansu duk masu aikine a gidajen".
"Shawararka tayi Aliyu, yanzu zamu rarraba yaranan cikin ofisoshin waɗanda abin ya faru a gidansu a gobe idan ALLAH ya kaimu, kowacce zata lurar mana da abu biyu, na farko zobe, na biyu sana'ar mutumin ko aikinsa".
Duk kai muka jinjina masa na gamsuwa, daga haka aka ƙara ɗan tattaunawa muka fito bayan an damƙama kowa aikin da zaiyi.............✍




ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[1/22, 9:04 AM] HASNA✍🏻: Billyn abdul:
Page 54

................Kanmu duk muka ɗaga mata, da amsawa da “Insha ALLAHU mama zamuyi ƙoƙari, a cigaba da tayamu dai”.  rakkiya tai mana har soro. Ganin ya nufi mota na dubesa cikin rawar murya nace, “Yayanmu gidan Dad ɗin fa?”. Bai tankaminba yaja hannuna ya turani mota shima ya shiga, Sadiq ya tayar muka bar anguwar.
         Kallonsa nake idanuna cike da ƙwalla, ya juyo shima ya kalleni fuska a cinkushe. “Kinsan idan kika bari hawayen nan suka zubo sai ranki yay matuƙar ɓaci wlhy!”. Ƙasa na maida kaina ina ƙoƙarin haɗiye kukan dake neman ƙwace mani, bai sake kulaniba har mukaje gida, kowa ɗakinsa ya nufa zukatanmu duk babu daɗi, sai da na rufe ƙofar sannan na saki kukan da ya hanani yi amota irin mai cin rai ɗin nan kuwa. Harnai wanka na fito hawaye basu daina min gudu a kumatuba, a haka na saka wando da riga marasa nauyi nai sallar magriba, ina idarwa na fita kitchen, banji motsinsa ba harna kammala girka abinda zamuci, na ɗauki na maigadi zan fita na kai masa mukaci karo a ƙofa zai shigo. Uffan baice mani ba ya miƙamin hannu alamar na bashi. Bashi nayi na juya ciki shi kuma ya tafi kai masa. Ɗakina na nufa dan banyi sallar isha'i ba, ina farawa ya shigo. Ganin ina salla sai ya juya yana faɗin, “Idan kin idan ki sameni falon baƙi”.
              Koda na idar ban cire hijjabin ba na fita, ruwa na ɗauka sannan na nufi falon baƙin, nai sallama suka amsamin da bani izinin shiga. Dattijon tsohon nanne da muka haɗu da shi ranar akan zancen maman yara, na ajiye ruwa na zuba musu sannan na zauna muka gaisa. Miƙewa na sakeyi dan na kawo masa abinci, ban jimaba na koma da abincin, sakamin albarka baba yay tayi, shi kansa boss na fahimci yaji daɗin hakan da nayi. Abincin ya faraci, boss kuma yana cigaba da latsa wayarsa ta fama, tashi nai zan barsu yace, “Dawo ki zauna, magana zamuyi da shi yanason komawa da wuri”. Na amsa masa da “to” na koma na zauna. Cikin ƴan mintuna Baba ya kammala cin abincinsa yana sake sanya mana albaka, sai da ya sha ruwa sannan ya maida hankalinsa ga boss. “Yauwa ɗana ina saurarenka”. Ajiye wayar boss yay yana furzar da huci. “Baba kamar yanda na fara maka bayani shine ta wace hanya kake gani zan iya shiga gidan domin ɗakko abinda tace? Matsalar shine a ɗakinsa tace abin yake, ɗakinma a tsakkiyar ƙarƙashin gado”. Baba ya jinjina kansa yana gyara zama, “Wato ɗana, ba wai ɗaukar ko shigar bace matsala ma, dole al'amarin sai da lura, su shaiɗanun mutane irin waɗan nan al'amarinsu baya buƙatar fuska da fuska, kamar yanda suke ƴan yaƙin sunƙuru haka masu cinsu da yaƙi ya kamata su kasance suma”. “Hakane baba”. “Yauwa to kagani ni a nawama tunanin wannan aikin kam da mace yafi dacewa ta wani ɓangaren, wani ɓangaren kuma namijinne, ɗakinsa dai bazai shigu gareka matsayin namijiba cikin sauƙi”.
      “Baba to mizai hana ni kawai naje”. Na faɗa kaina tsaye babu ko ɗar a raina. Shiru duk sukai suka zubamin ido. Cikin jinjina kai baba yace, “Shawararki kam abar dubawace, sai dai kuma ai bazai yuwu kije kai tsaye ba, sai dai mu duba wasu ƴan dabaru haka?”.
       Kafin nayi magana boss yace, “Baba bazai yuwu taje ba, mudai sake wata shawarar”. Murmushi naga baba yayi kawai, cikin rawar murya nace, “Miyasa to? Yanzu idan bajeba wa zamuce zamu saka wannan aiki? Ni a ganina baba zai iya ya kaini gidan matsayin jikarsa, insha ALLAHU ni kuma zan ƙarasa sauran aikin inhar na shiga gidan dai da matsayin da zan iya shiga wasu ɓangarori shikenan”.
       Shiru yay bai tankaba, baba yace, “ƴata idan mijinki baya so karki matsa, dan gaskiya wannan aikine mai haɗarin gaske, inaga zanje na ƙara tunanin wata hanyar, kuma sai ku sakeyi, yazam dai kafin safiya idan ALLAH ya kaimu ya muna da abinda muka riƙe, dan na tabbata nan da kwana biyu zai dawo daga tafiyar da yayi yau da safe. zan koma dan banason a farga da bani bane a gate ɗin”. Godiya mukai masa ya tashi yay masa rakkiya, ni kuma na koma ciki ina ƙunƙuni, dan insha ALLAH zanta lallaɓasa nikam harya amince naje nai wannan aikin da kaina. Ganin halin da maman yara take ba ƙaramin zaburar da zuciyata yayiba, na fahimci al'ummata na buƙatar jajurtattun mata irin su ma

man yara, wayasan shekarun data ɓata domin bibiyar wannan tukunyar? Amma gashi har tana a cikin magagin wahalar da aka bata bataji ta gajiyaba da son cimma ƙyaƙyƙyawar manufarta ba.
      Jin an taɓani na sauke sassanyar ajiyar zuciya, kujera yaja ya zauna idonsa a kaina har lokacin. Kallonsa nai cikin ido ko gezau babu a karo farko na tarihin rayuwata, dukda bugun ɗari-ɗari da zuciyata keyi haka na daure na dake ban cire idanuna ba, “Kar kace a'a, dan ALLAH, mune ya dace muyi aikin nan basai mun saka kowa a ciki ba, sannan bamu da isashen lokacin zaman yin tunni ko binciken wanda zaiyi mana ma.  ɗiyarsa ta ɗakko mana wayoyi ba shine ke nufin zata ɗakko mana wannan ba kuma”.
           Gani kawai nai idanunsa na ƙyalli tamkar hawaye sun taru a ciki, ya girgizamin kai a hankali yana kauda kansa, hannunsa nai saurin kamowa cikin nawa, ya sake juyowa ya kalleni, nawa hawayen ne suka silalo a hankali saman kumatu, “Please yayanmu karkace a'a, nima ka barni nai hidima ga Umm-Anum kamar yanda tayi a gareni tun batasan wacece ni a gareta ba, har raina jin ahalinka nake a zuciyata da ɓargo, idan ka hanani yin wannan aikin zanji matuƙar zafi a raina bakuma zan daina jiba har na koma ga ALLAH, dan zanke ganin kamar ni ɗin dan ba ahalink.....”
      Jawoni kawai yayi jikinsa ya rungumeni batare da ya barni na ƙarasa faɗa ba, da sauri-sauri zuciyarsa ke harbawa a ƙirjinsa, kamar yanda nima tawa keyi, cikin kuka na sake cewa, “Please Yah Jayyyy”.
       Jawaad ya lumshe idanunsa a hankali yana wani cije lip ɗinsa na ƙasa da ƙarfi, “Jay” sunane da mafi yawan mutane ke kiransa da shi, bai taɓajin ambatar sunan da wani banbanci na daban ba ga mai faɗarsa sai yau a bakinta, musamman ma data ja “y” ɗin ƙarshe sai yaji gaba ɗaya tsigar jikinsa ta tashi.
      Ɗagoni yay a hankali na sake zama sosai a kujerar dining ɗin, ya riƙe fuskata a cikin tafukan hannunsa yana sharemin hawayen da babban yatsansa, muryarsa a shaƙe yace, “Miyasa kema kin iya rigima ne Miemaa?, aini Kin riga kin gamai min komai a rayuwa tunda kika zama sanadin haɗuwata da mahaifiyata”. Sake ɓata fuska nai alamar tahowar wani kukan, nace, “To dan ALLAH ka barni na cika ladana”. Murmushi ya ɗanyi mai ciwo yana sake turani cikin jikinsa, “Shike nan bar kukan haka, zanyi tunani daga nan zuwa safiyar da yace insha ALLAHU, ALLAH ya zaɓa mana abinda yafi alkairi”. “Amin” na faɗa ina murmushi.
          Yau shine ya bani abincin da kansa, bayan mun kammala ya taimaka min muka tattare kwanikan zuwa kicin, ina wankewa yana ɗaurayewa har muka kammala sannan muka fito bayan na kammala tanadar abinda zan haɗa mana breakfast insha ALLAHU da safe. Yau kam bamuyi zaman wani aiki ba, brush kurum mukai da yin shirin barci muka kwanta. Babu jimawa barci yay awon gaba damu kuwa. Kusan ƙarfe uku na dare ya tadani, alwala mukai muka shiga yin nafilfili domin miƙa buƙatarmu wajen mahaliccin kowa da komai, mai rahama da ƙari ga bayinsa. Bamu sake kwanciya ba sai da mukai sallar asubahi, da yake a gida yayi shima muna idarwa ya jani muka haye gado, zanyi magana yasa tafin hannunsa ya rufemin baki ruf. Dole na haƙura muka kwanta, barci kuwa yay cak damu zuwa duniyarsa.

       Bamu farkaba sai 8:11am, nice ma na fara farkawar, na waro idanu a waje dan ganin makarar da nake gudu dai ta tabbata, jawoni yay zai maida ya sake kwantarwa nace, “takwas fa ta wuce boss”. Buɗe idanunsa yayi yana ɓata fuska, da alama ba haka ya soba. Da ƙyar ya iya tashi muka shiga wanka tare, a gaggauce mukai muka fito, batare da mun tsaya neman abinci ba muka shirya, tea ɗin dana haɗa manama cayay muje masha a mota, shi dai maigadi ya miƙa masa nasa tare da kuɗi akan ya sayo bread mun makara yau. A motar kuwa muka sha tea ɗin abin dariya da tausayi (lol😂😜). Aiko yau ina rakasa office na fito dan ban kammala aikin jiyaba nima, a ƙofar office ɗin naci karo da rose, ko kallonta banyiba nai gaba abina, harna sauka ƙasa ina jiyo idanunta dake yawo a jikina, nidai ban fasa neman tsarin ALLAH da ga sharrinta ba harna ɓace abina.
  
     Kusan sha biyu da wasu mintuna ya kirani akan idan anfito salla nazo na samesa. Amsa masa

nai da to ana idarwa kuwa can na nufa, shi kaɗaine a office ɗin yanata ayyuka, duk da da alama shima yanzu ya shigo ɗin, ban zaunaba har sai da ya bani izinin zama. Tasowa yay daga kujerarsa ya dawo ɗayar dake kallon wadda na zauna, ya kamo hannayena cikin nasa yana mai tsareni da idanunsa nan masu takurani. “Miemaa na amince kije gidan Alhaji kokino, amma da sharaɗi”. Cike da ɗoki nace, “Minene shaɗarin?”. “Sharaɗin shine kwana ɗaya kacal da yini biyu zakiyi, idan yayi tsaurine kikai biyu, sannan tare zamuyi aikin dan bazan taɓa barinki ki shiga wannan aikin mai haɗari ke kaɗai ba”. Rungumesa nai saboda jin daɗi, hannu biyu ya amsheni yana murmushi, nace, “Na yarda da duka sharaɗin, ALLAH ya bamu sa'a da nasara”. Yace, “Amin Beejay, yanzu zaki tashi Sadiq ya kaiki gida kiɗan shirya, shine zai kaiki inda zaku haɗu da baba, sai ya ƙarasa da ke”. “Wow da wuri haka?, insha ALLAHU zaka sameni fiye da yanda kai tunani, kaida kaitamin addu'a boss ɗinmu abin alfaharinmu”. Ɓata fuska yay cikin wasa yace, “ke da wa?”. Ganin yanda yay da fuska ya sakani ƙyaƙyƙyawa da dariya, “Ni kaɗai mana, sai su oga Jabeer ”. Hararata yay, “K nifa kibarma kirana da wani boss na gaji da ji”. Kunya naji sosai, dan haka na ɓoye fuskata a ƙirjinsa ina dariya.

★★★★

       Duk yanda muka tsara hakance ta kasance, bayan sallar la'asar muka isa gidan Alhaji kokino, cikin shiri nake irin na ainahin garorin yaran nan na ƙauye da ko karatu basu taɓa samu ba, ga matarsa kam mun samu tarbar mutuntawa, ƴaƴan gidanne dai sai a hankali, dan gaba ɗaya halayensu baimin ba, sai wani famar min kallon banza suke, musamman mai son boss ɗin nan. Shiru nai na maƙure jikin kuje alamar tsorata ta baƙunta. Baba mai gadi da suka gama gaisawa da hajiya ya juyo ya kalleni, “K Larai! Baki iya gaisuwa bane? nifa banason wannan ɗabi'ar banzar kin sani”. Muryata na rawa nace, “Ina wuni hajiya, mun sameku lahiya?”. Dariya yaran suka bushe da ita duka falon, irin wai ƙauyancina ne ya basu dariyar. Ita dai hajiyar Murmushi tayi tana cigaba da kallona, tace, “Lafiya lau Larai, yasu mamar taku?”. “Lahiya lumi suke aradu hajiya, tace tana gaiheki”. Saboda dariya har ƙasa suke faɗuwa daga saman kujerun. A raina nace, ‘Wawaye kawai’.
      Baba ne da yake ɗan murmushi shima yace, “Hajiya dama tazo daga ƙauye ne can anguwar tudun birji wajen ƴar uwar mahaifiyarta, to saita iske wai sunje suna ko ina, kuma sai jibi zasu dawo, shine nace data koma kuma ai wahala goma da ashirin tazo nan saita kwana idan suka dawo sai taje, ALLAH yasa dai ban wuce gona da iriba?”. “A'a Malam baka wuceba kam, ai kaga anyi zuminci tunda dama kaƙi kawo mana iyalanka shekara da shekaru, ni nagode sosai da wannan ziyara”. “Nima nagode hajiya, bara na koma bakin aiki to ga tanan”.
      Ganin zai fita nai ƙwalƙwal da idanuna alamar kuka, “Kaka anan zaka barni?”. Juyowa yay da ɗan faɗa yana min daƙƙuwa, “Kinci gidanku Larai, nanɗin cin mutane ake bare kice za'a cinyeki? To idan hakan bai mikiba tashi ki kama hanyar ƙauye idan su Rakkiyar sun dawo sai ki dawo”. Baki na tura ina maƙe kafaɗa, “Ni alkur'an a'a”. “Ke kuma kika sani ja'ira kawai”

1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

11 months ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment