Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke tsumar tsoron ganin yanayin Jawaad tace, “My son lafiya kuwa....?”
Kansa ya ɗago yana wani kaɗa hannunsa ya matse wayarsa tare da miƙewa tsaye sosai, a kausashe yace, “Ba ɗaba, Jami'in tsaro na hukumar ƴan sandan farin kaya *_JAWAAD ABDUL-AZIZ YUSUF_* ne wannan, munzo ne domin gayyatar mutane uku na gidannan zasu amsa mana wasu ƴan tambayoyi a office Hajiya”.
Idanu sosai Mummy ta zaro, Shahudah kam ai neman faɗuwa ƙasa tayi, Rose kuwa dake mata kallon tsana ta tarota tana fadin, “Madam kulafa”.
Shiko Jawaad ko kallon inda Shahudah take baimayiba dama.
Aamilah cikinta kam ya ɗuru ruwa, harta fara ƙaramin fitsari a pant ɗinta😝.
Dai-dai nan Jack da Salman suka shigo, dan yajene ya gama shirin jirgin da zai tashi a safiyar gobe dashi zuwa ƙasarsa kamar yanda Qaseem ya bashi shawara, sam basuyi zaton zuwan Jawaad gidan a daren yau ba, ko a ƙofar gida da sukaga motoci basu kawoma ransu shineba tunda shi dai Salman yasan Jawaad baida Securitys.
Mummy zata sake magana Jawaad ya daka mata tsawa yana faɗin, “Hajiya nace wannan ba ɗanki bane, jami'in tsarone a gabanki ki kama kanki”.
Ba Mummy ba hatta dasu Hafislz kansu tsawarsa ta firgitasu, dama tunda suka iso gidan mamaki ya kamasu, dan dai a saninsu wannan gidan Gwaggonsa ce, kuma gidan surukansa. Furicinsa sosai ya sakasu a ruɗani, ya kuma basu umarnin tafiya da Shahudah da jack da Aamilah.
Yana gama lissafa da waɗanda za'a tafi ya doshi hanyar barin gidan cikin takun bajinta mai ɗauke da izzar fushi.
Gaba ɗaya ji da ganin Mummy sai ya toshe ɗaf, bibiyu ma takoma ganin mutane saboda ruɗani da mamakin Jawaad.
Kukan da Aamilah ke yine saboda tafiya da za'ai dasu ya maido Mummy a hayyacinta, duk roƙo da magiyar da takema su Hafiz babu wanda ya saurareta, umarnin boss ɗinsu kawai suke ƙokarin cikawa, duk da zukatansu a ƙulle suke da wannan aiki sukam yau.
Lokacinma da suka fito dasu Shahudah tuni Jawaad ya shige mota abinsa, ya lumshe idanunsa da sukai masa nauyi, jijiyoyin kansa sun fito raɗa-raɗa bisa kansa, duk yanda yaso kiyaye irin wannan ranar sai da Shahudah tai ƙoƙarin zuwanta, to lallai kam zai tabbatar musu shi *_ƘWAI cikin ƘAYA_* ne, gashi dai abinso ga kowa, sannan kuma abin haɗari ga kowa, da kayi kuskuren ɗaukarsa kasha sukar ƙaya, ƙilama kana taɓashi ya iya fashe maka.
Tsabar ya manna musu hauka cayay a kaisu a ajiye, shiko yace a wuce gida dashi yana buƙatar hutawa.

★★★★★

Ana fita dasu Shahudah Mummy ta zube ƙasa ta fashe da kuka tana ƙwala kiran sunan Jawaad.
Salman ne yazo ya ɗagata shi kansa jikinsa sai tsuma yake, gaba ɗaya Jay ya rikiɗe masa a idanu tamkar ba shiba, da ƙyar ya iya taimakawa Mummy ta miƙe suka koma cikin falo.
Shine yay ƙoƙarin kiran Dad ya sanar masa, sannan Qaseem daya fita, dan baya gidan komai ya faru.
Ya kira Mama Atika ya sanar mata itama.
Kafin kace mi komai ya hargitse, magana ta fara fitowa a family house ɗin su Jawaad, dama daga can kuma Maman Zaitun ta kira itama ta sanar da kama Zaitun da akazo akayi ba tare da sunsan mita aikata ba.
Lokacin da motar Jawaad ta shigo gaba ɗaya gidan ya ɗauki zafi.
Yasan abindama yafi hakan zai faru dan haka ya shiryama kowa a gidan akan wannan case ɗin, kallon wani baiyiba a cikinsu ya shige sashensa ya kulle kansa.
Sama ya haye abunsa canma ya kulle har Windows yandama bazaiji kiran waniba a cikinsu, ya kuma kashe duk wayoyinsa suma.


********

Ana cikin haka Mummy da Salman suka iso gidan nasu Jawaad.
Yayinda shi kuma Qaseem ya zarce office a tunaninsa Jawaad yana can dasu Aamilah, sai dai ya iske kosu bama akawo canba, kenan wani waje daban yasa aka kaisu?, kuma an tabbatar masa Jawaad bai dawo office ba tun fitar da yay da yamma.
A fusace ya nufo gidansu Jawaad ɗin, inda ya iske hankulan kowa na gidan a tashe, duk da dai wasu na dariya a ƙasan rai da jinjina abinda Jawaad ɗin ya aikata a bazata.
Duk knocking ƙofar da suke masa baiko motsaba balle suyi tunanin zai buɗe su sami yanda suke buƙata, duk da yana jinsu yay kunnen uwar shegu dasu, wankansa ma yayi, yay shirin kwanciya bayan yayi shafa'i da wutiri, duk da yasan barci da wahala ya ɗaukesa.

Ganin Jawaad yaƙi buɗe ƙofa adaren sukaje suka sanarma kakansa abinda ke faruwa, baiyi mamaki ba, dan dama sune suke ɗaukar Jawaad kamar baisan mi yakeba saboda ya zuma ƴarsu ido tana yanda ta gadama, a gabansu shima ya gwada wayar Jawaad ɗin amma switch up.
Numfashi Baba ya sauke a hankali yana faɗin, “Wayarsa a kashe take, gashi nikuma ba ƙafar kirkiba balle nace zanzo gidan a daren nan, muyi haƙuri zuwa safiya za aimasa magana insha ALLAHU zai fidsosu, wauwtace irinta Jawaad kawai”.
Duk yanda dai suka so ganin su Shahudah basu kwanaba dole suka haƙura tunda babu mafita, aiko ranar anan gidan Mummy ta kwana.

Kamar yanda ya saba yauma sai da ya fita sallar asubahi ya sami salla a cikin jam'i, duk yanda su Uncle Uwaisu sukaso ritsashi basu samu wannan damarba, dan yafisu ƙwarewa a wannan fanin.
Cikin nutsuwarsa yay shirin fita tsaf cikin baƙaƙen Suit da rigarsa ta ciki fara, yayi ƙyau dan dama mai ƙyawunne, tun daga falon sama ya hango Suraj cikin samarin gidan yaron Uncle Uwaisu ne,
Sai da ya haɗa tea ya sakko ƙasa riƙe dashi a hannu yanata turiri, tunda ya fara sakkowa daga steps ɗin benen Suraj ya zuba masa idanu, komai na Jawaad abin so ne, kodan tarin nutsuwar da ALLAH yay masa.
Suraj ya mike domin girmama wa ga Jawaad ɗin, sai da Jay ya zauna a kujera maicin mutum ɗaya yana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan shima Suraj ɗin ya zauna.
“Yah Jay barka da safiya”.
Jawaad dake juya cokali cikin kofin tea ɗinsa ya amsa a dakensa, “Barka dai Suraj, lafiya dai ko?”.
Murmushi Suraj yay yana risinar da kai ƙasa, “Lafiya lau Yaya, dama su Abbane sukace na kiraka, wai suna jiranka a sashen Mama”.
Shiru Jay bai amsaba, sai da ya shaƙi iska ya fesar sannan yace, “Tom zanzo”.
Daga haka yay gum da bakinsa.
Mikewa Suraj yay yayi masa sallama ya fita.

Jawaad yaja siririn tsaki yana kai kofin shayinsa a baki, sai da ya kammala shan tea ɗin tas cikin nutsuwa kuma sannan ya miƙe ya fita, dama ko basu kirasa ba yayi niyyar zuwa wajensu.

Kamar yanda ya saba dakewa da shanye ɓacin rai yanzunma hakan yake, ya iso sashen Mama Atika a tsumensa alamun babu wasa ko ɗaukar abinda bai masaba ga kowa.
Gayyar Uncle's ɗinsa ya iske a falon mama Atika, harma dasu Mummy, murmushi yayi wanda ya bayyana loɓar kumatunsa duka biyu, wato taron dangi aka shirya masa kenan?.
“Duk zan iya daku ai” ya faɗa a fili murya ƙasa-ƙasa yana kaiwa zaune a kujerar da yake ƙyautata zaton dama shi aka barwa.
Wata ƴar ƙaramar dariyar muguntar daya tanadar musu yayi a zuciya.
Suko maɗaukakin mamaki duk ya bayyana a fuskokinsu, musamman yanda sukaga shi tashi fuskar babu alamun damuwa, saima wani kwarjini da cikar haiba shinfiɗe a kanta.
Ya zauna yana ajiye wayoyinsa a ƙaramin tebirin dake gefen kujerar da yake zaune.
“ALLAH dai yasa lafiya? Na ganku haka, Barkanku da safiya?”.
Yay maganar cikin nuna halin ko in kula da kallon ƙurillar da suke binsa dashi su duka.
Sosai tambayar rainin hankalinsa ta bugi ƙirazansu, Uncle Nasir yay masa daƙƙuwa yana faɗin, “Kaci gidanku Jawaad, ya kakema nuna kamar bakasan mika aikataba?”.
Wani murmushi Jawaad ya saki yana harɗe ƙafafu ɗaya bisa ɗaya, da kwantar da bayansa a kujerar, “Uncle minayi nikam?”.
Dukansu baki suka saki suna kallonsa.
A harzuƙe Mummy tace, “Kai mara mutunci, bama kasan mi kayiba? Kaje har gida ka kama matarka ta sunna da ƴan uwanka amma kake mana wannan rainin hankalin naka?”.
Jawaad yay wani luuu da idanu da sauke numfashi, ya taɓe baki kaɗan yana ɗaukar wayarsa ɗaya ya shiga latsawa, “Mummy kenan, na dai kama waɗanda suka bada gudun mawar zubarmin ciki da wadda ta aikata zubarwar, ai matar ƙwarai ta sunna data wadatu da tarbiyya koɗan shegene bata zubar dashi balle ɗan halak na sunna. ku sanarmin kawai yanzu ku miya taraku anan?”.
Mummy data nema zaucewa da kalamun Jawaad zatai magana Uncle Nasir ya katse ta.
“Kai Jawaad ka dawo hankalinka kaji, kasan da suwa kake magana bamason takadaranci, kai yanzu kanaga ya dace ace matar aurenkace ta kwana a rufe? koda abinda kake zargi ya faru ai wannan maganace ta cikin gida, miyasa mu bazakazo ka sanar manaba muyima tufƙar hanci?”.
Shiru kamar Jawaad bazai amsaba, sai kuma ya ajiye wayar da yake dannawar ya maida hankalinsa ga Uncle Nasir yana ƙoƙarin ɗaukar takardar daya ajiye tare da wayoyinsa.
“Uncle wannan ba maganar gida bace, yanzu haka badan yinta yasa nazo nanba, dan Office zanje ana jirana, inhar akan maganar yaran canne kuka taru anan to bazaku ji komai daga gareniba, kudai nema lauya kawai, dan sai an biyani cikina, ita kuma da kuke tunanin zan raga mata saboda igiyar auren da bata amfanamin komaiba tunda aka ƙullata to ga shi nan na tsinkata, kucirema zukatanku mutuncina ne zan taɓa saboda ta kwana hannun jami'an tsaro”.
Babu wanda bai zaro ido waje ba saboda mamakin furucinsa babu ko kunyar ambaton cikinsa da yake.
Jikin Uncle Ayuba har ɓari yake wajen ɗaukar takardar da Jawaad ya ajiye ya duba.
Cikin tsagwaron tsoro da firgici yace, “Wlhy yayi sakin”.
Kusan duk a tare suka ce saki kuma?!!!.
Jawaad ya tattare wayoyinsa zai miƙe yana katse musu tunani da fadin,
“Ku gafarceni zan wuce ana jirana, kuna tunanin zan cigaba da zama da jahilar da sam bata da tarbiyyar addinin islama ne?”.
“Jawaad yaushe ka zama haka?”.
Cewar Uncle Sadiqu baki a hangame.
Babu ko gezau kuwa Jay ya bashi amsa da, “Uncle ai indai nine na wuce hakan, dama can ƙaramin sani kukaimin shiyyasa”.
Hannu mama atika da Inno suka saka aka suka fasa kuka, wai Jawaad na musu rashin kunya, ko ubansa Abdul-aziz bazai musu wannan abunba.
Haƙuri sukaita basu, Jawaad kam yay shiru uffan bai ceba.
Sai da falon ya lafane Uncle Nasir ya kalli Jawaad ɗin ransa a ɓace yace, “Wai shin ko ka fara shaye-shayene bamu saniba? Yanzu kai Jawaad duk yabon hakurinka da ake a gidannan ashe hasashen banza mukeyi?”.
Jawaad dake ta ƙoƙarin danne fushinsa yay guntun murmushi yana shafa fuskarsa, “Uncle duk yanda zan maka bayani bazaka fahimceni ba, bansan wane irin haƙuri kukeso nayi akan jahilci da rashin tarbiyyar hudah ba, ankai maƙurar da bazan iya ɗaga ƙafaba kona yafe gaskiya, karku saka kanku a wannan rigimar domin tsakanin ni da itane kawai a cikinta”.
Da yawansu maganganunsa sun shigesu, dan kuwa dai kowa yasan Shahudah kam bata da tarbiyya.
Gwaggo Nafisa mahaifiyar Zaitun tace, “To anji rigimarka ce tsakaninka da Shahudah, ita kuma Zaitun da su Aamilah miya kawosu ciki?”.
Idonsa ya lumshe nanma yana rumtse hannunsa da ƙarfi, ya buɗesu akanta sun kaɗa sunyi jazur, kamar zaiyi magana sai kuma baice komaiba ya miƙe yana kwasar wayoyinsa, dan idan har ya cigaba da zama tabbas zaiyi abinda ba tarbiyyarsa ba.
Kamar ruwa ya cinyesu haka falon yay tsitt suka bishi da kallo kawai harya fice.
Uwargidan Uncle Nasir ce ta miƙe tana faɗin, “Inhar gaskiya kuke bukata a wannan zancen to yaron nan yafiku gaskiya, mai makon wannan titsiyen da lallaɓashi kukayi yafi, tunda da dai dukanku kunsan gargaɗin da yayma Shahudah tun yunƙurin zubar da cikin nan da tayi na farko, yanzu kuma ta aikata aiko dole ku shirya karɓar abinda yamafi haka daga gareshi”.
Tana gama faɗa tabar musu falon, bata saurari yanda suka kacame da maida mata murtani ba, duk da sunsan gaskiya ta faɗa a maganarta.

Koda Jawaad suka isa Office hidimar gabansa ya cigaba dayi baiko bi takan su Shahudah ba, waɗanda shi kaɗai yasan inda yasa aka kaisu saiko su Hafiz da suka kaisun.
Yayi hakane kuma saboda Qaseem, ilai kuwa ranar Qaseem ɗin yini yay fafutukar bincike nason gano inda Jay yakai su Shahudah ɗin, sai dai ko wata alamar da zai iya samu Jawaad bai bariba.
Daga ƙarshe Office ɗin Jawaad ɗin yaje yana masa magana a gadarance.
Jawaad yay masa banza kamar baisan kurar daya kwaso Qaseem ba, sai da ya gaji da hayaniyarsa ne ya miƙe yana kallonsa a wulaƙance, “Ni bani da lokacin yin magana da kowa akan wannan batun, kuje ku nema lauya zuwa gobe zamu shiga kotu”.
Aiko jin haka Qaseem ya kuma haukacewa da surutai, sai Jawaad ɗinne ya bar masa Office ɗin.

Duk yanda sukaso zama da Jawaad akan a sasanta sam yaƙi basu hadin kai, ranarma bai kwana a gidanba, a gidansa yaje ya kwana, da yake yanzu su Aliyu kowa ya koma gidansa wajen iyalinsa.
Su kansu su Hafiz ɗin yaki sanar musu abinda ke faruwa, duk tambayar da suke masa akan kama su Shahudah sai dai yace suyi hakuri subar maganar.
Daga ƙarshe dole suka ƙyalesa saboda basa bukatar shiga haƙƙinsa.
Dai dai da kakansa yaki yarda su haɗu, hakama su Umma sunbi duk hanyar da zasu gansa akan maganar ya tosheta, yaƙi sauraren kowa, yakumaki faɗama kowa ina su Shahudah suke.

Wannan abu ba ƙaramin tada hankalin Mummy yayiba, ga Abba bai dawoba dukda shima acan hankalin nasa a tashe yake, ya gwada kiran Jawaad ɗin amma saiya iske ya sakashi a black list shima.
Kamar wasa saiga su Shahudah na neman rufa sati guda ba'asan inda sukeba, Jawaad yakumayi finfiris yanata aikin gabansa hankali kwance, dan yama cirema kansa damuwar cikin acewarsa ALLAH yasa haka shine yafi alkairi.

Lokacin da ake wannan dambarwar kam Bilkisu na makaranta abinta hankali kwance suna shirye-shiryen fara zana jarabawa.


_________________________
BILKEESU
_________________________

Komai na fara zana jarabawarmu ya kammala, dan haka muka ajiye duk wani shiririta muka sake maida hankalinmu a wajen karatu.
Musamman ma ni danafi kowa buƙatar ƙarin haske akan komai, sai dai yanda su Zuhrah ke ƙaramin ƙwarin gwiwa yasa bana tare da wani tsoro ko fargaba, da ai banyi tunanin zuwa wannan matsayinba, ALLAH ya kawoni kuma ai bai kamata na sakama kaina tunanin rashin nasara ba.
A wannan yanayin muka fara zana jarabawar mu...........✍🏻



*_BAYAN SATI UKU😒_*



*_ZAFAFA SABON KAFCE SUN DAWO GAREKU_*


_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_


_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻



_Sannan akwai tashoshinmu na Youtobe da zasu fara kawo muku daɗaɗan labarai bisa tsaftataccen karatu, kuyu azamar garzayawa tashar *ALƘALAMI TV & MANHA HAUSA NOVELS* domin samun wannan gara ɓasa, a danna mana subscribing domin nuna ƙauna ta musamman masoyan gaskiya.😃🥰🥰💃🏻👌🏻_.



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻https://youtu.be/HFjVgQVnmn0

*_MANHA HAUSA NOVEL'S_*👆🏻


https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo

*_✍🏻ALƘALAMI TV_*👆🏻


*_Please and Please my dear fans, wannan sune chennals namu a taimaka dan ALLAH aje ai mana subscribing, zasu dinga kawo muku daɗaɗan novels namu babu ko sisinku, ga abubuwan gyaran jiki da ƙaruwa ta fannoni da dama, dan ALLAH a daure a nuna hallaci, hakan zai sake ƙaramin ƙwarin gwiwar baku ƙwai cikin ƙaya a kullum, dan zai tabbatar min kuna biye dani, kuma kuna sona har yanzu, dan ALLAH kar ayi sanya, a danna mana subscribe Please & Please😢🙏🏻🥰🥰💃🏻_*


*_Typing📲_*



*_🧺ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!🧺_*


*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_Wattpad:-_* _BilynAbdull😉_



*_____________________________________*
*_BOOK ONE_*
_Shafi na ashirin takwas_
*_____________________________________*


*_BAYAN SATI UKU_*
_BILKEESU_


............Babu abinda zancema Ubangijina sai godiya, domin kuwa jarabawa na tafiya yanda ya kamata, sai dai ƴan ƙalubale da ba'a rasaba, a yanzu haka abinda ya rage mana bai wuce sati ɗaya ba kacal mu kammala, muɗanyi hutun sati biyu daga nan muyi neco.
Gaba ɗayanmu mun maida hankali, sannan muna taimakon juna, musamman ma ni da suke taimakawa ta kowanne fani.
Yau ma mun fito a gajiye, kowa sai yaƙe yake saboda yunwar dake cin hanjin cikinmu, hostel muka nufa kamar waɗanda aka zanema ƙafafu.
Ummie tace, “Ni yanzuma bama kaje ɗakinba, ka rasa abinda zakaci shine matsalar”.
Rebecca tai dariya da faɗin, “Kina nufin yau ma bazakici abincin da akai ba?”.
“Wlhy bazan ciba, nifa badan kun hananiba da tuni na daɗe da kai report ɗin abinda na gani jiyan nan, ai insha ALLAHU daga jiya harna bar skull ɗinnan bazan sake cin abincin da akai a kitchen ba”.
Dariya duk muka saka mata.
Nace, “Haba ta wajena ki ɗan sassuta, daga jiya kin gani sai kuma akace shikenan kullum za'a cigaba da gani, wannan ɗinma nasan by mistake ya shiga ALLAH”.
Nazifa dake gefena tai saurin faɗin, “Barta Bily, kartaci, wlhy yunwar cikintama ta isheta, ita ɗinnan mayyar son cin doya, duk randa akayi zamuga bazataje ta amso ba da gaske?”.
Ummie ta harari Nazifa tana faɗin, “To ƴar sa ido, duk bin ƙwaƙwƙwafinki ƙyayi ki barni, dan zan tabbatar muku da maganata”.
“ALLAH ya bada iko” cewar Zuhrah.
Duk muka amsa da amin muna dariya, da haka muka ƙarasa hostel.
Sheƙawa da gudu Zuhrah tayi ta fara shiga ɗakinmu tana faɗin, “Nizan fara wanka ehe”.
Ƙarasa shiga muma mukai, Nace, “Kai Zuhraty kin sanfa yanda nake, Please ki barni na fara”.
Shigewarta tai da sauri tana min gwalo, “Ai dama saboda ke ne zanyi fes ɗin, karda ki gogamin nima na ɓule yau”.
“Zaki sani ai, insha ALLAHU gobe sai muna tsaka da jarabawa kiji ya zubo....”
“Wlhy ke muguwace Bily” cewar Rebecca dake cire kayanta, Nazifa da Ummie kuma suka saka dariya.

Haka muke a koda yaushe cikin nishaɗi da kulawa, nakanji tamkar na ɗauki wasu shekaru masu yawa tare dasu ne, dan wanda bai saniba ya gammu zaiyi tunanin tun yarinta muke a haka, ba ƙaramin sakin jiki nayi dasuba suma kuma hakan, idan kaga faɗa a tsakaninmu sai dai rashin fahimta, mukan zauna kuma mu warware da wuri kafin abun yay mana tsamari, Nazifa ma tuni ta fara sakin jiki dani, duk da dai ba kamar su Ummie ba hakan bai dameni ba.
Sai da duk mukai wankan sannan mukaje muka amso abinci, amma banda Ummie datai alƙawarin tabarci har ta wuce.
Irin wannan farin cikin dana samu daga garesune ya sake kawoma rayuwata canji da farin ciki, jikina ya murje tamkar ba'a makaranta nakeba, duk da babu wanda ya taɓa busting ɗina hakan baisa naji ɓacin raiba, amma dai ina kewarsu su duka.
A kwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI sai gashi mun kammala waec, a ɗan hutun da muka samu kafin fara neco ne ya sakamu sake

1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

11 months ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment