Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zan iya zarga a halin yanzun, sai dai hakan bazai saka na kasa fidda ɗaya a cikin dubu ba”. “Nasani gwarzona”. Sir Ahmad ya faɗa yana ɗan bubbuga kafaɗar Jay ɗin cike dajin ƙarin alfahari da ƙwazon yaron.
          Jabeer ne ya ƙaraso wajen riƙe da tab.. A hannu, yay salute ɗin Sir Ahmad sannan ya kalli Jay dake kallonsa shima. “Boss ƴan iskan mutanen nan basu bar wani alama ko kaɗan da za'a iya bibiyarsu ba, bayanan dake hannunmu ma a yanzu haka ko motar da sukazo a cikinta babu Number ma, abinda bayanan mutanen anguwa suke faɗa mana kawai motar baƙa ce, suma mutanen kuma baƙaƙen kayane a jikinsu, fuskokinsu a rufe”. Shiru yay yana kallon Jabeer cike da nazarin maganganunsa, kafin kuma ya kallesa yana ɗan cije lip ɗinsa na ƙasa, “Dama bana tunanin zasu bar wata alama ta zahiri, sai dai dolene za'a samu ta baɗini Jabeer. Zamanmu anan gidan baida wani amfani, inaga mu wuce office kawai”.
      Jabeer yace,  “Okay nima nayi wannan tunanin, dama isowarka muke jira muji ta bakinka, dan yanzu haka dai Number shi Alhaji Babba muketa ƙoƙarin bibiya saboda Batool tace tana zaton da ita ya tafi a jikinsa batare da suma maharan sun sani ba. a yanzu haka dai wayar na nuna tana titin gambari gab da babban titin ƴan robobi na gabashiya. Jami'anmu suma suna gab da isa wajen harda Aliyu”. Amsar Tab ɗin Jay yayi daga hannun Jabeer da sauri....
       Hakan yay dai-dai da isowar Bilkisu da wani tunani yazo mata a zuciya inda suke. Sai da tai Salute ɗin Sir Ahmad itama sannan taɗan matsa kusa da Jay da hankalinsa kega Tab... ɗin da ya amsa a hannun Jabeer, amma yasan da zuwanta, dan ƙamshin turarenta ma ya ishesa shaidar tana wajen. “Sir anya kuwa wannan aiken ba daga gidancan bane?”. Da sauri Jay ya ɗago yana kallonta, “Wanne a ciki?” ya faɗa cike da ƙaguwa. “Inda na dawo daga farauta shekaran jiya”. Kafeta yay da ido dan maganarta na tafiya bisa ƙamshin gaskiya. Ta ƙara risinar da kanta cikin girmamawa a garesu, cigaba tai da faɗin, “Bazai yuwu ace dama ya barmu ba, dolene zai bibiyemu kodan maigadinsa, sai dai bamu da tabbas, hasashene kawai nayi Sir”. Jawaad yay wani ɗan murmushi yana maida duka hannayensa biyu ya goya a bayansa, taku ɗaya biyu yay sai kuma ya sake juyowa, hannunsa ɗaya ya sauke daga bayan ya tura cikin aljihu, ɗayan dake riƙe da tab... Kuma ya ɗagosa yana goga tab... Ɗin akan hancinsa. Daga Jabeer har Sir Ahmad da bilyn duk kallonsa sukeyi. Wani murmushin ya sakeyi da tsayawa cak, bily ya nuna da tab... ɗin hannunsa yana faɗin, “Maganarki akwai ƙamshin gaskiya, dolene a cikin biyu a samu ɗaya, idan kuma nai wani nazari zan iya ɗaurasu a mizani guda ya zama aikin haɗaka ne”. Ya ƙare maganar yana maida dubansa ga sir Ahmad da ke binsu da kallo kawai. Kafin yace wani abu Hafiz ma ya iso riƙe da waya alamar magana ya gamayi. “Mutanen nanfa inaga sun farga da

wayar jikin Alhaji babba, sam yanzu bama ganinsu alamar an kashe wayar”. Kallonsa duk sukayi, Sir Ahmad yace, “Dai-dai ina kuka daina samunsu?”. “Sir a Roundabout ɗin titin General hospital”. “General hospital?”. Jay ya faɗa cikin sigar tambaya. “Ƙwarai kuwa boss, ka duba ma zaka gani anan”. Tab... Ɗin Jay ya sake buɗewa, dai-dai inda Hafiz ya faɗa shima nan ya nuna masa, ya miƙama Jabeer tab... ɗin yana faɗin, “Yanzunan inason a bincikamin inda Alhaji Kokino yake, a kuma bincikamin inda Alhaji Ali da Qaseem suke, sai Mr Gebrail shima”. Yana maganarne yana daddana wayarsa daya ciro a aljihun wandonsa. Da mamaki na kallesa jin ya sako Dad da Yah Qaseem ciki, sai dai yanda yay kicin-kicin da fuska yasa na gaza cewa komai, sannan ma bani da wannan damar dan a fagen aiki muke matsayinsa na ogana ba miji ba. Da to muka amsa masa kawai, muna barin wajen.
       Sir Ahmad dake kallon Jay yace, “Miyasa ka lissafo waɗanan mutanen? Kana zarginsu da aikata hakanne?”. “Sosaima kuwa Sir”. Jay ya faɗa yana ɗaura wayar a kunnensa jin an ɗaga. “Munkaila kana ina?”. Bansan amsar da aka bashiba daga can, ya gyara tsaiwarsa idonsa a sashen da su Bilkisu ke magana ita dasu Jabeer yace, “Ka ajiye wannan aikin, yanzun nan kaje gidan Alhaji Ali a ɗakkomin maigadin gidansa da kuku”. Kansa ya gyaɗa da sauke wayar.
       “Jay ka sake sakani a duhu, wai ba kana magana bane akan Alhaji Ali dana sani baban Qaseem? Da shi Qassem ɗin kansa?”. Fuskar Jay cike da murmushin takaici ya jinjina ma Sir Ahmad kai, “Shi nake nufi Sir”. “To amma miya haɗashi da Alhaji kokino da har kake tunanin zasuyi aiki tare?”. “Hasashene kawai Sir”. Ya bama sir Ahmad ɗin amsa a taƙaice. Badan bai yarda da shi bane, yanason tabbatarwa kasafin ya buɗe aikin kowa ya sani........

__________________
      BABA ƘAURA
______________

             Tun a safiyar yau baba ƙaura ya sa ake nemar masa Number Jay sai dai ba'a samu ba, iya ƙoƙari sojan dake taimakama baba ƙaura idan zaiyi waya da Jay yayi amma wayoyin Jawaad ɗin duk sun ƙi shiga, sai kusan goma na safe da ƙyar ɗaya ta shiga, sai dai kuma anƙi ɗagawa kusan kira goma.
        Ganin lokaci na sake ƙwacewa baba ƙaura yace sojan idan yasan inda gidan Jay yake ya kwatanta masa. Sojan shima bai saniba, dan haka yacema baba ƙaura bara yaje ya bincika ko za'a dace. Tunda sojan ya fita baba ƙaura ya kasa zaune ya kasa tsaye, ba komai ya kawo hakanba sai abinda ya jiyo a daren jiya, ga lokaci yanata sake tafiya kuma.
       A jiya gaba ɗaya zaman ya gunduresa, jiyay yana sha'awar zagaya jeji, dan haka tun bayan sallar la'asar ya sulale yabar Barrack batare da sanin kowaba sai sojan nan da General ya ɗaura alhakin kula da shi akansa, yanda yaron ke masane ya sakashi ƙaunarsa harma yake masa wasu abubuwa na taimako, sannan baya ɓoye masa wasu abubuwan da suka shafesa, hakan yasa a fitarsa ta jiya ma ya sanar masa. Yayi ninƙaya cikin jejin sosai jiya bisa al'adarsa ta farauta da sanin sirrin jajejin da ALLAH ya bashi badan zaiyi farautar ba, dan ko karnuka babuma a tare da shi. Tun daga farkon dare har kusan ƙarshensa bai fitoba yana a dajin. sai da ya gama jin sirri mai girma daga shaiɗanun da suka maida wani yankin jejin nasu sannan ya fito, gab da asubahi ya shigo cikin gari, ana shiga salla masallaci yana isowa Barrack. A gaggauce yay alwala ya shiga masallacin shima. bayan an idar da salla ya saka sojan nan ya nemo masa Number Jawaad zaiyi magana da shi, sai dai sam an gaza samunsa, da aka samesan kuma ma sai bai ɗaukaba.....
     Dawowar sojan tasakashi tsayawa cak daga kai kawon da yake faman yi da tunanin daren jiya, cikin ɗoki ya sanar masa an gano family house ɗin su Jawaad ɗin, kuma yana ƙyautata zaton a ciki jay yake zaune da iyalinsa. Baba ƙaura yayi murna, sojan nan yay masa rakkiya har bakin hanya ya sakashi a napep da faɗama mai napep ɗin inda zai kai baba ƙaura. Kasancewar gidan su Jay sanan nan gidane sai akaci sa'a mai napep ya sani.
       Da ƙyar suka samu maigadin ya sauraresu, danshi tsoron baba ƙaura ne ya kamashi ganinsa sanye cikin fatun namin jeji, gashi babu hannu guda. Sai da baba ƙaura yayta m

asa magiya sannan ya sanar masa cewar Jawaad ba nan yake zauneba yanzu, yana gidansa da ke a A.Y street. Nanma sunsha daga kafin ya basu address ɗin, mai napep ɗin da yake yanada kirki shine ya sake ɗaukar baba ƙaura zuwa A.Y. sai dai suna shiga layin, motar Jay na fita. A gidan Jay ɗinma sunsha daga da maigadi kafin ya sanar musu Jawaad ɗin baya gida ya fita babu jimawa, suka roƙesa koya san inda ya nufa yace shi bai saniba. Sosai hankalin baba ƙaura ya sake tashi, burinsa kawai yaga Jawaad, harsun baro gidan ya roƙi mai napep ɗin suka sake komawa. Tambayar maigadi yayi ko ina drivern Jawaad ɗin?. Maigadi ya amsawa baba ƙaura a daƙile cewar yau Sadiq baizai zo aikiba yana gidansa. “Dan ALLAH ka faɗa mana inda gidan nashi yake zamuje mu samesa?”. baba ƙaura ya faɗa yana kallon mai gadin. A fusace mai gadi yace, “Kai malam kafa isheni, taya zan faɗa maka bayan bansan kaiɗin wanene ba? Nama sani ko cutar da waninsu zakayi, indai ma ogane yafi ƙarfinka dan shima wlhy aljanin kansane da kake ganinsa nan”. Murmushi baba ƙaura yayi, yace, “Yaro nafika sanin hakan ai, ka daure dai ka faɗa mana kokuma ka kira mana shi direban a waya idan ya gammu shi yasan manufarmu”. Kamar maigadi bazaiyi ba, sai kuma miya tuna oho masa ya ɗauka waya yay kiran Sadiq.
           Babu jimawa saiga Sadiq mai napep shima ya kasowa, yana ganin baba ƙaura ya rikice, dan baiyi zaton shiɗin bane da gaske. Haƙuri yayta bashi akan abinda maigadi yay masa, baba ƙaura yace babu damuwa, so yake yanzunan ya kaisa inda Jawaad yake shidai. Maigadi dai jikinsa yayi sanyi ganin yanda Sadiq ya bama baba ƙaura muhimmanci, a take ya shiga bashi haƙuri. Baba ƙaura yay murmushi kawai yace karya damu........

___________________________

                Anbar ƴan sanda zagaye da gidan Alhaji babba, su Jay kuma suka kwasa zuwa station dan aikin zaifi yuwuwa acan cikin sauri.
      Bilkisu dai duk ta kasa sukuni akan sako Qaseem da Dad da Jay yayi a waɗanda yake zargi, zuwa yanzun kam tafara yarda da saƙe-saƙen zuciyaryarta, anya kuwa babu wani abu a rufe da bata saniba? Haka kawai mijinta da Dad bazasu ringa takun saƙa na kamar wasu maƙiya ba, a dafa surukinsa ne, sannan mijin yayar mahaifinsa ne. Ta tuna kallon kallo da suka dinga yima juna jiya duk da shi Dad yanata nuna babu komai.....
     Da wannan tunanin a ranta suka isa station, babu mutane da yawa saboda weekend ne. Ni da su oga hafiz muka nufi office ɗin boss, shi kuma suka nufi na sir Ahmad..
          
             Bamufi mintuna goma ba shima sai gashi ya shigo office ɗin ɗauke da takardu a hannu.
      Kujerar zamansa ya nufa yana faɗin, “Miemaa taso kiyi wannan aikin”. Miƙewa nai daga inda nake zaune ni kaɗai na nufesa. Kujerar zamansa ya nunamin, babu musu na zauna shi kuma ya shiga ƙoƙarin dai-daita Computer ɗin.
      Oga Jabeer da Hafiz dake can gaban Computers ɗin dake gefe guda biyu suka juyo suna kallonmu, Hafiz ne yace, “Boss babu watafa alamar waya data shiga tsakanin Alhaji kokino da Dadyn su Shahudah gaskiya, amma Dad yayi waya da Qaseem awa ɗaya da mintuna hamsin da uku da suka wuce. Barin inda nake yay ya nufesu, “Zamu iya samun maganar da sukayi?”. Jabeer da hankalinsa ke ga Computer gaba ɗaya yace, “Bazai yuwuba gaskiya, dan inhar mukai hakan zai gane, kasan wayar Qaseem tana da tsaro kamar yanda namu suke”. Jay yayi ɗan jimm na tunani. Numfashi ya furzar mai zafi yana dafe kansa dake sara masa, sai kuma ya zabura kamar wanda ya tuno wani abu. “Jabeer ina zuwa, bara na turo muku Numbers ɗin nan, dukansu inason mu tabbatar idan suna aiki a halin yanzun”. Yay maganar yana sake nufo inda nake, drawer ɗin jikin table ɗin ya jawo, flash ne da yawa a ciki, ya shiga ɗakkosu ɗaya bayan ɗaya yana duba rubutun da yay a jiki, cikin sa'a ya samo wanda yake nema, miƙamin yay yana faɗin, “Saka shi”. Yanda yake min magana babu wasa tattare da shi yasaka jikina har tsuma yake, sai da na gama dai-daita komai abubuwan dake cikin flash ɗin suka bayyana sannan ya ranƙwafo kaina, hannunsa ya ɗora bisa nawa dake a dafe da mouse muka ringa control ɗin Computer tare.
        A haka Sir Ahmad da wasu jami'a

nmu manya biyu suka shigo suka samemu. Nan take aikin ya sake ɗaukar zafi, ni dai ta ɓangarena da taimakon boss nakeyi. Kusan minti goma sha biyar mun duƙufa, hankalin kowa nakan abinda ke gabansa akai knocking ƙofar office ɗin, batare da jiran izini ba oga Aliyu ya shigo da sallama. Inda muke ya nufo bayan yayi salute ɗin su Sir Ahmad. Bansan miya gwargwaɗa ma Boss a kunne ba, na gadai shima boss ɗin ya miƙe ya nufi Sir Ahmad cikin zafin nama. Sai kuma suka fice shi da Sir Ahmad ɗin daga office ɗin.........

_________________
      BABA ƘAURA
_______________

         Cikin mintuna ƙalilan suka iso station ɗin bisa taimakon Sadiq, sai dai kuma securitys sun hanasu shigowa musamman ganin yanayin baba ƙauran, sun musu roƙon duniya amma sun hanasu, Sadiq ya kira wayar Jay amma bai ɗagaba, hakan yasa suka koma gefe cike da damuwa, musamman ma baba ƙaura dake matuƙar matse da son ganin Jay.
      Suna a wajen tsaye su biyu Sadiq na cigaba da kiran Number Jay sai ga motar su Aliyu, harma an buɗe musu gate zasu shige Aliyun ya hango baba ƙaura ta mirror. Sauke gilashin motar yay ya saka ɗaya daga cikin securitys ɗin yay masa magana da baba ƙaura. Ganin shi ɗinne dai kamar yanda yay hasashe sai ya bada umarnin barinsu su shigo. Bayan ya shige da motar ya samu waje yay fakin ya fito shi da waɗanda sukabi masu ƙwamushe Alhaji babba, gaisuwa kawai yay da baba ƙauran ya shiga ya sanarma Jay.

          Duk da Aliyu ya sanar masa baba ƙaura ne hakan nbai hanashi yin mamakin ganinsa har station ɗinsu ba, ya ƙarasa fuskarsa babu walwala, dan duk yanda yaso aro fara'a ya azama fuskar tasa kamar yanda ya saba idan yaje wajen baba ƙaura hakan ya gagara. Cike da girmamawa suka gaishesa har Sir Ahmad.
          Kallonsu baba ƙaura yay ya ɗauke kansa yana faɗin, “Kagani har a wajen aikinka ko?”.
         Ɗan murmushi Jay yayi da cewa, “Babu komai baba, ai nasan zuwan naka mai muhimmanci ne”. “Hakane” baban ya faɗa yana sake maido hankalinsa garesu sosai. Yace, “Tun da safe na saka a nemomin kai amma hakan ya gagara, ba'a samunka da farko, daga baya kuma ta shiga ba'a ɗagawa”. Kai Jawaad ya dafe, “Dan ALLAH kayi haƙuri baba, wlhy na tsinci kainane a yanayin da komaima bazan iyaba”. “Gudun faruwar hakanne ya sakani yimaka neman gaggawa ai daman,  tun bayan wucewarka na tafi jeji ne, acan ma na kwana, dan sai gabannin asubahi na shigo gari, sanda na iso nan har an shiga salla. Na saka a nema min kaine domin isar maka da saƙon abinda idona ya ganomin jiya a cikin jajin nan. Muhammad Jawaad lallai akwai matsala babba dake tunkaroku, da idona na gani, na kumaji da kunnena, gashi rashin samunka akan lokaci ya nunamin alamomin fara faruwar matsalar dana guda ma a yanzun”.
         Hankalin Jawaad a tashe yace, “Baba hasashenka duk haka yake, yanzu haka zancen da nake maka anje har gida an ɗauke kakana, akan binciken inda zamu samesa muke”.
             “Wannan shine shirinsu na farko dama. Na zauna nayi ƙyaƙyƙyawan nazari mutanen nan ba haka nan suke bibiyarka ba, akwai wani abu aƙasa wanda akwai jininka a ciki, ina nufin cikin zuri'arku akwai wanda ke tare da mutanen nan.....” cike da mamaki Sir Ahmad da Jay suke kallon baba ƙaura. Ya jinjina kansa yana cigaba da faɗin, “Kar kuyi mamaki, neman duniya babu wanda baya ɓatarwa, lallai kamar yanda na faɗa akwai wani abu a ƙasa, dan babu rami miya kawo rami? Bayan abubuwan dana sani ke a hannunku akwai wani abu da kuka ɗakko a wani gida ne?”. Sir Ahmad ya kalli Jay, shima ya kalleshi, sai kuma ya maida dubansa ga baban yana jinjina masa kai. “Akwai wani tukunya baba, wanda.........” ya labartama baba ƙaura da Sir Ahmad komai.
        Baba ƙaura da keta faman jinjina kai cike da nazarin maganganun Jawaad ya sauke nannauyan numfashi. “UBANGIJI ya baku kariya sosai to akan wannan aikin, dan suna cikin ruɗani mai girma akan son gano wanda ya ɗauki tukunyarnan, amma sun gaza gano komai, inuwar wadda ta ɗauka ɗin kawai suke iya gani, sannan har yanzu tsafin nasu kuma bai iya nuna musu mahaifiyarka ta shigo ƙasarnan ba. Wannan hikima ce da rahama daga UBANGIJI, inaga iyakar suce tazo shiyyasa komai

ya keta ƙwace musu. A taron da sukai daren jiya sun tattauna abubuwa da dama wanda zarge-zarge da yawa sun sami rinjaye a kai kanka, sai dai a yanda na fahimta na yau sai sun fisu muhimmanci. Dan haka nakeso ku kasance a wajen kai da matarka idan zai yuwu, sannan lallai matsayinku na jami'an tsaro wannan shaiɗancin ya kamata ma ace ku kawo iyakarsa ma baki ɗaya. Dan tabbas kakanka yana tare da su, acanne kawai zaku iya samosa a halin yanzun dama wasu mutanen da aka kai a wajen bisa zalunci da son zuciya”.
        Boss ya cika bakinsa da iska ya furzar yana taunar lip ɗinsa na ƙasa da ƙarfi. Kallon Sir Ahmad dake fahimtar dukan maganganun nasu a baibai yayi. sai kuma ya maida ga baba ƙaura yana faɗin “Babu damuwa baba, amma kana ganin ita zuwa da ita bazai zama haɗari ba?”. Ƴar dariya baba ƙaura yay yana kallon Bilkisu data fito da waya a hannu ta doso su, “Babu wani haɗari insha ALLAHU, matar nan taka akwai sirrika tattare da ita waɗanda ALLAH kaɗai yasan tushensu, amma haka kawai nakeji a raina kamar sunada nasaba da taka ƙaddarar. Amma ita ɗin ba jami'ar tsaro bace?”. “Eh jami'ar tsaroce, irin aikinsu ɗaya”. Sir Ahmad ya bama Baba ƙaura amsarsa. Baba ƙaura ya sake faɗaɗa murmushinsa “Ka barta itama ta nuna bajintarta a aikinta da ƙwazon da ALLAH ya bata, ALLAH yana tare daku a dukkan al'amuranku insha ALLAHU. kudai kuci gaba da gayama ALLAH”. A tare suka jinjina masa kawunansu da faɗin insha ALLAHU baba. “Karkuji komai, wannan tafiyar tafi ta farko sauƙi insha ALLAHU, ta wani ɓangaren kuma tafi waccan haɗari, dan haka runduna zaku haɗa mata da tafi ta farko indai aikin zakuyi da gaske” ya ƙare maganar dai-dai da isowar Bilkisu wajen.
       Rissinawa nai na gaida baba ƙaura da banyi tunanin ganiba anan, ya amsamin cike da fara'a da kulawa. Cikin girmamawa na miƙama Sir Ahmad takardar hannuna da aka aikoni na kawo masa. Amsa yay yana dubawa, ni kuma na maida dubana ga boss da yanayinsa ya bani tsoro. Da ido nai masa alamar ‘Lafiya?’. Kansa yaɗan girgizamin kaɗan yana lumshe idanunsa dake jajur.......
     Sir Ahmad ne ya katse mu da faɗin, “Jay inaga yanzu haɗa rundunar da zamu tunkaru jejin ne ya dace, bara na nema mana jirage masu saukar angulu yanzun nan, sai ku haɗa kayan operation ko”. “Okay Sir” Jay ya faɗa cike da karsashi na jami'i mai cikakkiyar lafiya da zafin nama..
     Tare muka koma da baba ƙaura office ɗinsa inda su Jabeer keta aiki cike da zafin nama da ƙwarewa. Boss ya ɗan bigi tebir da zafi-zafi yana faɗin, “Ayi shirin fita operation mun gano inda suke insha ALLAHU”. Duk juyowa sukai suna kallonsa da mamaki, harni kaina kallon nasa nake, amma sai ya ɗauke kai yana nufar telephone ɗin dake saman table ɗinsa yana jero sunayen waɗanda za'a kira yanzun nan”.
        Cike da bin umarni Aliyu ya fice zuwa office ɗinsa domin aiwatar da komai, shima bayan yayi waya da wani da bansan ko wanene ba ya ajiye yana kallona da nufar ƙofa yace na biyosa ni da Dawood da suka dawo da Oga Aliyu yanzun.
        Store ɗin station ɗin muka nufa, inda acan muka iske Sir Ahmad da wani ogan mu shima suna haɗa bindugu. Muma aikin haɗa wasu makaman aka sakamuyi. Mamaki ya kuma cika zuciyata, duk yanda nake hasashen al'amarin da alama ya wuce nan, nasan Boss mutum ne mai muhimmanci a hukumarnan tamu, ya cancanci a nuna masa kowanne irin halacci akan taɓa ahalinsa, amma yanda ake shirin fita operation ɗin sai nakeji a raina kamar ya zarce na maido kakansa kawai. Cikin mintunan da bazasu gaza talatin ba duk wani shiri an kammalashi, duk jami'in da aka buƙaci gani ya amsa kira, a mamakina harda su Ummie su dukansu, Rose harma dasu Ada, sai sauran jami'ai na departments ɗin da ba namuba ma. Dukanmu mun kasance cikin Uniform ɗin aiki, dan boss ma da yake sanye da kayan gida a da sai gashi ya fito cikin Uniform harsu oga Jabeer da Sir Ahmad ɗin kansa. An bamu bullet proof jacket duk mun sassaka, kafin oga Hafiz ya rarraba mana bindugu harda kibiya ga waɗanda suka samu horo na musamman a kanta, wasu kuma wuƙaƙe naga an basu manyan takubba, sosai mamaki abin yayta bamu mu baƙin shigowa hukumar, dan zan iya cewa wannan shine operation na

farko gagarumi da za'a fita damu..............✍

Da ace zan iya sai nabi wasunku da bulala goma-goma a ɗuwawu aradu🙄, wlhy nafiku son naga na kammala buk ɗin nan🤦🏻. Uzirin daya riskeni ya wuce dukan tunanin mai hasashe, yanzunma dauriyace kawai dason ganin na faranta muku, saɓanin wasunku da bakunansu ke furta abinda bai daceba a gareni😢🚶🏻.

ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻😭
[2/12, 7:51 PM] Wasila: *_ƘWAI CIKIN ƘAYA!!_*


*_Bilyn Abdull ce🤗_*


_ASSALAMU ALAIKUM MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR... 🙋🏿‍♀️🙋🏿‍♀️INA KUKE NE? 🔊🔊KU MARMATSO, DOMIN ZAMAN JIRA YA KARE, HAZIKAN MARUBUTAN NAN DA SUKA HADA HAZAKA DA KAIFIN TUNANI SUN SAKE ZAGE DAMTSE SUN ZO MU DA WASU SABBIN SALON RUBUTUN SU, WADANDA ZASUWA’AZANTAR, SU NISHADANTAR, KANA SY DILMIYA KU A KOGIN KAUNA, BASU TSAYA ANAN BA SALON RUBUTUN SU YA SAKE ZUWA DA SABBIN TSARE TSARE NA DARUSSA DABAN DABAN, DA KUMA HANYOYIN GYARIN JIKI DA WAJE._

_KADA KU MANTA MARUBUTAN ZAFAFAN DAI SUNE WADANDA SUKA YO MUKU HAR KASHI BIYU A SHEKARAR 2020 DATA GABATA,: WUTSIYAR RAKUMI DA GUDU DA WAIWAYE NA BILYN ABDULL. 2-DAURIN BOYE DA ALKAWARIN ALLAH NA SAFIYYAH HUGUMA.3-BURI DAYA DA QAUNAR MU NA MAMUH GEE-4- SAUYIN KADDARA DA DAURIN GORO NA HAFSAT RANO. SAI 5-KAI MIN HALACCI DA IGIYAR ZATO NA MISS XOXO.._

_A WANNAN SABUWAR SHEKARAR TA 2021 MA HAZIKAN MARUBUTAN SUN SAKE DAWOWA DA WASU SABBIN DA’DADAN LITTATTAFAN NASU:_

_1_

_* SAFIYYAH HUGUMA* MARUBUCIYAR KUNDIN KADDARA DA ABADAN TAZO MUKU DA SABON LITTAFIN TA MAI SUNA: *(SIRADIN RAYUWA)💜*_

_2_

_*HAFSAT RANO* MARUBUCIYAR GUGUWAR SO DA RUHI DAYA, TA ZO DA SALON NATA LITTAFIN MAI SUNA: *(ABINDA KE CIKIN ZUCIYA..*)💘_

_3_

_* MAMUH GEE* MARUBUCIYAR TARAYYAH DA EZNAH, TAZO DA SABON ZUWA MAI SUNA: *(MIN QALB)❤️.*_

_4_

_*MISS XOXO* MARUBUCIYAR NAUFAL DA SAIFUL-ISLAM, TA YUNKURO DA WANI MAI SUNA: *(KIBIYAR AJALI)*💜_

_5_

_SAI MARUBUCIYA *BILLYN ABDUL* WADDA TAYO MUKU KWAI CIKIN KAYA, DA CIKI DA GASKIYA TA YINKURO DA WANI MAI TAKEN: *(YANKAN BAYA)*💝_

_RIGIJI GABJI DUKKAN WADANNAN LAGWADAR DADADAN LITTAFAN BIYAR ZASU ZO MUKU NE INSHA ALLAHU AKAN FARASHI MAI RAHUSA KAMAR HAKA;_

Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,

Guda hudu 4 Kuma 500,

Guda uku 3 Kuma 450,

Guda biyu 2 Kuma 400,

Guda daya akan 300.

Ma'ana
Each one is 300
2 is 400
3 is 450
4 is 500
5 is 700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO- *0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS

1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

1 year ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment