Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunanin barinsa ya samesa har gida ya sakashi sharewa, juya kan motar yay zuwa station zuciyarsa fal tunane-tunane, ga aiki jibge a gabansa da baisan iyakaba, ga kuma matsaloli kala-kala da yarasa makamar dazai kama domin fara warwaresu. Saƙon ɗan fi'auna ne yazo masa arai, har ya shiga office ɗinsa yana juya zancen a ransa, ‘Mi ɗan fir'aunan ya sani a kansa da haryake iƙirarin ya basa har naira miliyan hamsin domin ya sanar masa? Shin waishi yaron nanma wanene shi? Kuma a ina su Momy suka samosa?’. Wannan tunanin da yazo masa a raine ya sakashi dakatawa daga ƙoƙarin kunna Computer gabansa da ya kai hannu zaiyi, komawa yay jikin kujera ya kwanta yana lumshe idanunsa.
       A haka Aliyu ya shigo ya samesa, sai da yay masa sallama har biyu sannan ya farga da shi, ya buɗe idanunsa da tashi zaune sosai, tie ɗin wuyansa ya sassauto ƙasa yana kallon Aliyu daya zauna. “Boss lafiya dai?”. Aliyu ya faɗa idonsa akan Jawaad, sassanyan numfashi jay ya sauke da cewa, “Lafiya lau Aliy”. Badan Aliyu ya yardaba ya ƙyalesa, saima takardun hanunsa ya miƙa masa yana masa bayani. Jawaad ya amsa ya duba ya sake miƙama Aliyun, magana suka ɗanyi Aliyu ya tashi ya fita.
        Koda Aliyu ya fita Jay kasa haƙuri yay ya ɗauka waya ya shiga neman ɗan-Fir'auna, tana gab da katsewa aka ɗaga, daga can wanda ya ɗaga ɗin ko sallama baiyiba balle batun gaisuwa yace, “Mai wayar yayi Accident yana asibiti”. “...Accident?” jay ya maimaita da maɗaukakin mamaki tare da sake kiran wayar dan har an katse.............✍

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.

SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
        ƊAURIN ƁOYE
      ALƘAWARIN ALLAH.

HAFSAT RANO tazo muku da;
         SAUYIN ƘADDARA
        ƊAURIN GORO

MAMU GEE tazo muku da;
           BURI ƊAYA
         ƘAUNAR MU.

MISS XOXO tazo muku da;
           KAIMIN HALACCI
           IGIYAR ZATO.

BILYN ABDULL tazo muku da;
          WUTSIYAR RAƘUMI...
         GUDU DA WAIWAYE....

abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai

Billy Abdul, [12/15/20, 12:50 PM]
iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.

Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899

sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.

Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻[12/16/2020, 2:27 PM] HASNA✍🏻: Bilyn Abdull 📚:
Page 29

...............Yanzunma dai saida taje gab da yankewar aka sake ɗagawa, sai dai yanzu ba'ace komaiba, cikin ɗan zafi-zafi Jay yace, “A wane asibiti ne?”. Ɗan jimm wancan yay, sai kuma cayay General”. Yanke wayar kawai Jay yayi batare da shima yace komaiba, maida akalar kiran yay ga Jabeer, bigu biyu ya ɗauka, bayan sun gaisa Jay yace ya fiyo zasu fita. Iyakar abinda yace kenan ya katse kiran ya miƙe, rigar suit ɗinsa daya cire tun shigowarsa yay hanging a bayan kujerar zamansa ya ɗauka, tare da ƙaramar bindiga ya tura a gefen ƙugunsa ya fice.
       Tare suka fita shi da Hafiz da Jabeer, dan Aliyu akwai aikin da yakeyi. Koda suka isa General hospital emergency suka nufa kai tsaye, tunda ance Accident can tunaninsu ya fara basu su duba farko. Hafiz ne yay tambaya duk da basu da tabbas ɗin cikakken sunan ɗan-Fir'auna bayan Habib, sudai ma'aikatan asibitin dake Emergency ɗin basu ganeba, amma alamun da suka gani na cewar su hafiz jami'an tsarone yasa doctor zagayawa dasu kaf gadajen dake cikin Emergency room ɗin suna dubawa, babu ɗan-fir'auna anan ɗin. Doctor yace, “To akwai dai wani da aka kawo tunda safe yayi accident, mun bashi ɗaki awa ɗaya data wuce, al'amarinsa akwai ruɗarwa, daga baya ƴan uwansa sukazo suka ɗaukesa duk da yana cikin mawuyacin hali”. Jabeer ne yace, “Suka ɗaukesa kamar ya? Baiji ciwo bane?”. “Yaji ciwo sosai yallaɓai, dan ko farfaɗowa ma bai gamayiba mundai dubasa babu karaya sai raunika?”. Kafin Jabeer ya sake magana Jay dake gefe yana latsa waya tamkar ba saurarensu yakeba yace, “Miye sunansa?”. Yay maganarne ba tare da ya ɗagoba, dan yasan idan har Dr Tayyeb ya gansa tsorata zai yaƙi faɗar komai.
      Dr Tayyeb dai yasha jinin jikinsa akan Jay, sai dai da yake bai ganin fuskarsa da ƙyau sai ya daure yace, “Kamar dai Habibu ƙaura suka bada a jikin katin”. Jay baice komaiba dan ya fahimci dai ɗan fir'auna ne, sai kawai ya nufi hanyar fita. Ganin haka yasa su Jabeer yima Doctor sallama suka biyoshi. Acikin mota suka iskoshi, sai da suka shiga suma Hafiz yace, “Boss yanzu a ina zamu ganosa kenan?”. Jawaad da har yanzu hankalinsa naga waya batare daya ɗagoba yace, “Anguwar kuke”. Tada motar Jabeer yay sukabar asibitin batare da sun sake cewa komaiba, dan sun lura akwai abinda yakeyi mai muhimmanci a wayar.
      Sun shiga Anguwar Kuke, inda Jay ya sanar musu dai-dai inda zasu tsaya, a tare suka fita a motar, Jawaad yay gaba suka bisa a baya har zuwa jikin jan gate, gidan bawani gidane mai ƙyauba, dan irin ginin da ɗin nanne, sai dai a da ɗin maishi ya kasance mai arziƙi, a rufe ƙofar take, hakan yasa Hafiz ƙwanƙwasawa. Kusan mintina biyar suna tsaye kafin a buɗe a fusace, kodamar tambayarsu suwanene su? wanda ya buɗe ɗin baisamuba Jay ya turashi gefe ya shige su Jabeer na biye dashi. Duk tsagerancin tsagera idan yay gamo da wanda ya fisa tsageranci nutsuwa ya keyi, hakan yasa saurayin bai iya cewa komaiba ya maida ƙofar ya rufe shima yabi bayansu dan ya gane Jawaad.
       Ɗunbin mamaki da al'ajab ne ya sakasu tsayawa cak a ƙofar falon, dan kuwa gungun samarine da adadainsu zai iya kaiwa goma  tsai-tsaye da candles kunne a hannu sun zagaye katifar da Ɗan-Fir'auna ke kwance a tsakkiyar falon, dukansu idanunsu a rufe suke babu mai magana bare motsi. Jabeer da Hafiz ne kawai sukai magana tare da jan birki, Jawaad kam uffan baiceba sai kafawa matasan idanu da yay a ransa yana nazarinsu. Hannu yasa da ƙarfi ya bugi ƙofar falon, a take duk suka dawo hayyacinsu, suka juyo suduka suna kallonsa. Su Jabeer dai abin ya firgitasu, amma a mamakinsu sai sukaga Jawaad ya danna kai cikin falon kamar baiga abinda yake faruwaba. A baɗini shima kuma lamarin ya firgitashi, sai dai ya danne saboda shi mutumne mai kasadar tunkarar abu kai tsaye, ko aiki suka fita duk haɗarin waje baya shakkar shigewa gaba.
          Cike da takun nutsuwa Jay ya ratsa ta tsakkiyarsu yana addu'a a ƙasan ransa har zuwa gaban katifar da ɗan-fir'auna ke kwance samɓal jikinsa duk raunika wasu ansa bandage, yay wani irin kukkumburewa a fuska saboda buguwar da yayi. Sai da yay masa kallon mintuna uku kafin ya ɗago ya kalli samarin da suma

suka kafeshi da kallo tamkar zasu cinyesa ɗanye. Yi yay tamkar bai fahimci kallon da suke masaba, cikin Kakkausan lafazi yace, “Dami yay Accident ɗin?”. Wanda yake gaba gab da katifar sosai ne ya fara hure candle ɗinsa, sannan ya juya ga sauran yay musu nuni dasu zauna. Babu musu duk suka zauna ƙasa suka tanƙwashe ƙafafunsu hannayensu riƙe da candles ɗinsu har yanzu kuma a kunne. Sake maida dubansa yay ga Jawaad yace, “Yakamata mu fara sanin baƙonmu ai”. Sake ɗaure fuska Jay yayi, kamar bazai tankaba sai kuma ya gyara tsaiwa da faɗin “Nine na kira waya ɗazun”. Karon farko saurayin da babu alamar mutunci tattare dashi yay murmushi da cema Jawaad, “Hutawarka lafiya babba, haɗari yay da mashin yau da asuba, sai dai abin ya haɗa da mabiya sahu”. Jawaad tsaf ya fahimci ma'anar kalamsa, amma sai yay kamar bai ganeba yace, “Amma miyasa kuka ɗakkosa daga asibiti? Suwaye ke bibiyar sawun nasa?”. Gayen yace, “Babba! wannan wasane tsakanin rindunar mafarauta guda biyu, suntaɓo inda za'a maida gayya da gayyane, dolene tsakaninmu  a fidda wanene sarki wanene bawa, zasu biya diyyar jini da jini karka damu, koma gefe kawai kasha kallo dan muna respecting ɗinka Babba, aishi sheri ɗan aikene maishi yake komawa, balle idan ka haɗu da waɗanda suka fika iya sherin, zamu zuba dasu muga wazai kwashe, idan har sukaci nasara a kanmu na rantse da jinin babata saina yanke kaina da hannuna da takobin da aikinta kawai shine shan jini”. Kafin Jay ya ƙara magana Ɗan-fir'auna yay wata irin mimmiƙewa da saki razananniyar ƙara data firgita su Hafiz dake a farkon shihowa Falon basu ƙaraso ba, shi kansa Jawaad sai da ya toshe kunensa. Abin mamaki sukam abokan ɗan-fir'auna ko gezau, saima sake miƙewa da sukai da candles ɗinsu a hannu suka kuma zagayeshi.
       Bayan wasu mintuna ɗan-Fir'auna yay shiru sai numfashi yake da sauri-sauri, kafin kuma a hankali ya nutsu waje guda numfashin na komawa normal. Sake komawa sauran sukai suka zauna, na ɗazun nan dai me ya sake magana, “Babba karka damufa, nasan akwai harƙalla tsakaninka dashi, zai miƙe nanda kwanaki kaɗan tunda gashi ya farfaɗo, alfarmar da muke nema gurinka kawai likitan dazai dinga zuwa gida kullum yana duba masa waɗanan raunikan”. Cikin haushi Hafiz yace, “Kai kushiga hankalinku, kufaɗa mana abinda ke faruwa?”. Kafin wancan yace wani abu Jay yay wani munafukin murmushi da yima Hafiz magana da ido ya ɗauke kansa tare da nufar hanyar fita. Hafiz ya sake kallon Ɗan-Fir'auna yana mai girgiza kansa, “Shikenan za'a kawo muku likita”. Shima yana gama faɗa yabi bayan Jay ransa a ɓace. Jabeer da baice komaiba sai nazarin kayan dake cikin falon shima yabi bayansu..
     Kusan a tare suka fito, suna shiga mota Jabeer yace, “Boss miyasa za'a kawo musu likitan da suka buƙata? Bayan dukkan alamun mutanen banza ya bayyana a garesu”. Numfashi jawaad ya sauke a hankali yana kallonsu, “Wato Jabeer kowane aiki akwai salon da yake zuwa da shi, waɗannan yaran da kake ganinsu duk a tafin hannuna suke, dan duk wani binciken daya dace na kammala yinsa a kansu, mubisu a sannu domin samun abinda muke buƙata yanda ya kamata”. Kai duk suka jinjina masa cike da gamsuwa, dan sunsan bazai jefasu a hanyar da bazasu ɓille ba.
      Sunbar anguwar Hafiz da Jabeer nata tattauna al'amarin, Jay kam dai yayi shiru, dan kuwa shi kaɗai yasan mi yake tattaunawa da zuciyarsa. Jabeer yace, “Wannan duniya nada abin mamaki da al'ajabi da bantsoro, rayuwar waɗannan mutane ta ƙanƙanin lokaci kawai ka gani ta isa saka zuciyarka tsorata da sake tsarkake girman ALLAH”. Cike da damuwa Hafiz yace, “Yaran nanfa kamar ba ainahin musulmai baneba ma, sannan dagani kaga ƴan Cultism”. Jay dai duk dai yana saurarensu, har suka iso station, office ya wuce ya cigaba da aiki biyu, na office dana zuciyarsa. Kalaman abokin ɗan fir'auna yaketa harhaɗawa waje guda da nazarinsu.
        Misalin biyar da wasu mintuna na yamma yaɗan fita wani waje, yanason zuwa ainahin inda suka taɓa haɗuwa da ɗan-fir'auna a ranada Gimba ya kawo masa zancen abinda ya gani. sai dai kuma hakan bata samuba saboda yana hanya kira ya shigo wayarsa daga balarabe, a amsa kuwwa ya saka

wayar ya amsa masa sallama da gaisuwar da yake masa. “Ka isa garin nasu ne?” yay tambayar wa balarabe. Daga can muryar balarabe cike da damuwa yace, “Ganima harna dawo Alhaji, tun inacan naketa kiranka baka ɗagaba. sai dai baizo gidanba ma ashe, kuma mamansa tace har waya sunyi lokacin dazai taso”. Babu shiri Jawaad ya taka burki, yace, “Kana nufin canba gidaba tun ran juma'ar?”. “Eh wlhy Alhaji hakane”. Mutuwar zaune Jawaad yay a cikin motar, gabansa sai wata irin mahaukacin faɗuwa yake, cikin rawar jiki ya ɗauka wayar ya katse kiran balarabe ya fara laluben Jabeer. Yana ɗagawa ko sallama bai masaba yace, “Jabeer maza dubamin daga ina Gimba yake a halin yanzun?”. Daga can Jabeer yace, “Ƙila matarsa ta riƙesa bata gaji da ganin kayantaba”. A tsawace Jawaad yace, “Jabeer kabar wasa mana!!, ka nemomin yaron mutane Jabeer Please”. Ya ƙare maganar a hankali tamakar zai fashe da kuka. Hankalin Jabeer ne yay matuƙar tashi, baƙaramin girgiza zuciyarsa tayiba da jin yanda Jawaad yay magana da tsawa da sanyin murya kuma a ƙarshe. Jabeer yace “Yi haƙuri, yanzu kana Office ne?”. “Gani nan zuwa” kawai ya iya cemasa ya yanke wayar. Reverse yay tare ya figi motar da shegen gudu ya koma station.
            A office ɗinsa ya iske Jabeer na jiransa, har wani jiri-jiri yakeji saboda tashin hankali, sai da ya zauna sannan Jabeer yace, “Mike faruwa da gimban?”.
      “Jabeer nima ban saniba, ranar juma'a ya tafi weekend amma bai dawoba, shinefa nasa a bisa aga ko yana lafiya, amma sai aka tararma baijeba”.
      Cikin ɗaurewar kai Jabeer yace, “Ya salam to ina yaje shiko? Yanzu abinda zamuyi bara mu bibiyi layin sa, ina fata kunyi waya dashi bayan tafiyar tasa?”. Kai kawai Jawaad ya girgizama Jabeer, yana faɗin, “Na kirashi jiya amma bai ɗagaba”. Jabeer yace, “Tunda dai kiran ya shiga zai taimaka mana”. Wayar kawai Jay ya miƙama Jabeer baice komaiba. Gaba ɗaya Jay ya kasa zaune ya kasa tsaye, sai faman zagaye office ɗin yakeyi, Jabeer kuma nata ƙoƙarin ganin ya samo inda gimban yake, a haka Aliyu da Hafiz suka shigo suka samesa harma da Rose da dawowarta kenan daga tafiya. Haka suka duƙufa su huɗu suna taimakawa Jabeer. Inda alama ke nuna musu wayar gimba na nan ɗinne ya tada musu hankali har suka kasa aminta suketa sake ninƙayar bincike. Cikin girgiza kai Jabeer yace, “Kai abinnan akwai rikitarwa, mizai kaisa wannan dajin mai haɗari? Inaga bara nai magana da kamfanin layinan dan muna buƙatar bayanan da yafi haka”. Hafiz yace, “Hakan shine zai taimaka mana Jabeer, danni kainama ya kulle gaba ɗaya”.
       Jawaad dai yama kasa cewa komai, zaune yake kawai tamkar butunbutumi. Aliyu ne yay kiran wanda yake musu aiki a kamfanin layin da gimba ke aiki dashi, bayan sunyi magana ya ajiye wayar Jabeer ya tura musu Number gimba.
      Ganin magriba tayi Aliyu yace, “;
Boss ka kwantar da hankalinka, ni ina ganin ko wasune suka Kidnapping ɗinsa bazasu kaisa wannan jajejinba, kawai sunyi hakane domin rikita mana tunani, idan muka kwantar da hankalinmu zamu fahimci komai cikin sauƙi, yanzu dai Ma'aruff ɗin yace daganan zuwa safiya zai turo mana komai, inaga muje muyi salla da addu'ar ALLAH ya kuɓutar dashi a duk inda yake, a kuma hannun duk wanda yake”.
      A tare suka amsa da amin har Jawaad.
          Koda suka fito daga salla Jawaad ya tafi gidane kawai cike da matsananciyar damuwa, bai shiga gidaba sai da yay sallar isha'i.

           A wannan dare idan har akace Jawaad yay barci to ɓarawone, kwana yay miƙama UBANGIJI kukansa akan gimba da murɗaɗɗun al'amuran dake faruwa a tsakaninan, roƙon ALLAH yake ya bashi ƙarfin zuciya dana jajircewa, ya kuma haskaka masa abinda yake a duhu daya gaza fahimta. Mutuwar ɗan-fir'auna, ɓatan gimba, mafarkinsa, dalilin aure da akaso yi tsakanin bilkisu da wanda ba mutumin kirkiba, damuwar da yaga Alhaji babba jiya a ciki. Duk wanda ya roƙa UBANGIJI yana mai ƙasƙantar da kai da fatan samu bai yanke ƙauna daga rahamarsaba ALLAH sai ya amince masa, ya kuma dafama al'amarinsa ta inda bai zato ko tsammani ba.
      Jawaad ya tashine da wata irin dakiyar zuciya, duk wani ɗigon tsoro da fargaba daya haifarmasa da ruɗa

ni da kasala a daren jiya sai yaji sun gudu, ya tashi cike da yaƙinin son tunkarar abinda ke tunkarosa. Dolene koda zai halaka da izinin ALLAH sai ya gano suwaye suka kashe ɗan fir'auna, miyasa suka kasheshi?, minene a binne da rayuwarsa da ɗan-fir'auna yaso sanar masa, yanaji a jikinsa kisan ɗan fir'auna nada nasaba da abinda ya shafesa, minene shi? Wannan ne bai saniba.
      Ƙarfe bakwai na safe ya gama shirinsa yabar gidan, yau ko gadonsa bai gyaraba, saƙo ya gani daga gimbiya Munaya akan zatasa akai Bilkisu wajen aiki basaima ya wahal da kansaba, idan sun tashi sai ya dinga maidota da kansa.
      Yaji daɗin hakan, dan dama yanata juya yanda zai dinga yawonan batare da wataran yay lattiba shiɗinan gwani ayyuka da yawa. Station ya nufa cike da zumuɗin son zuwa yaji ya ake ciki akan gimba.

________________________________

             Tunda muka shiga cikin masarauta notin kaina ya nema kwancewa, karon farko a tarihim rayuwata dana fara shigarta, ƴan uwa bansan yanda zan musalta muku abinda na ganiba, abinda kawai zan iya ce muku masarautar gagara badau wani katafaren garine kawai mai zaman kansa dake ɗauke da ɗumbin al'umma kala-kala masu abubuwan kallo. Kaina bai sake kuncewa ba sai da muka shiga sashen da naji ance na sarauniyane mahaifiyar su Amaturrahman, wato garin daɗi na nesa, angulu data leƙa masai. Nidai bana cewa uffan, binsu kawai nake tamkar raƙumi da akala. Mun yada zango a katafaren ɗakin Amaturrahman da Meenal sai Amatullah idan tazo daga Niger. Amaturrahman ce ta tsaya kaina da hidima har saida nai wanka na canja kaya aka kawo abinci ta takurani naci sannan ta barni na huta, muna zaune tana ɗan jana da hira saƙon gimbiya ya iso garemu daga amintacciyar baiwarta akan tace na kwanta na huta, kuma a bani dukkan kulawar data dace.
     To lallai naga hidima mai ban mamaki da al'ajabi wadda har kuka sai da nayi, ashe nima mutumce mai daraja irin haka? Ɗawainiyar da akeyi dani ta zabtare kaso mafi yawa na damuwar da nake ciki akan abubuwa kashi-kashi da basu ƙirguwa, tunda Safah kuma taji labarin nazo tadawo ɗakin su Amaturrahman ta tare tanata min hira. Banga gimbiya ba har dare yay muka kwanta, da safe kuma na tashi da shirin fita aiki kamar yanda boss ya tabbatarmin zasu zo ɗaukata, sunata barcinsu nai shirina tsaf, na cika wayata da caji dan haka nai tunin tanan zai kirani, sai dai kusan 7: 00am saiga ɗaya daga cikin bayin gidan tazo isarmin saƙon kira, bin bayanta nai muka fita, mun isa wajen Amintacciyar baiwar gambiya dake falon farko tana jiranmu, na gaisheta da girmamawa saboda babbar mace ce, itama cike da fara'a ta amsa min tana faɗin, “Sarauniyar gagara badau na gaisheki baƙuwar alkairi, baki samu ganinta bane tunda kika iso saboda takawa yana mura, tana sashenshi tun jiya tana bashi kulawa, akwai driver dake tsumayenki a waje ta bada umarnin a kaiki garesa”. Fuskata ɗauke daɗan murmushi nace, “Nagode mama, ALLAH ya bama maimartaba lafiya mai amfani da nisan kwana”. “Amin ya rabbi” ta amsamin damin nuni Abinci da aka ɗora akan babban yire wai na breakfast ɗina, badan nasoba ta tsareni naci sannan tayomin rakkiya waje.
     Duk azatona gimba zan tarar, sai dai na iske saɓaninsa, da alama madai wannan acikin masarautar yake shima, dalleliyar mota baƙa wulik yaymin nuni dana shiga bayan mun gaisa, tamkar kazar da ƙwai ya fashema a ciki haka na shiga zuciyata najin tarin ƙaunar waɗanan adalan mutane, ada nazata idan na rasa mafakar gidan Dad bazan sake samun watantaba, sai gashi alkairai nata niye da rayuwata. Tafiya muke ina tunani kala-kala a cikin raina ciki harda fargabar haɗuwata da mutum biyu, wato Boss da Yah Qaseem, tayaya zanyi aiki cikin nutsuwa a tsakkiyar waɗanan zakunan?.

       ★★★★★

    Jay da isowarsa kenan babu daɗewa yana zaune a kujerarsa ta office yana ɗan taɓa aiki da tsumayen su Jabeer, baifi mintuna gomaba suka shigo a jere su huɗu har Rose data dawo jiya, gaisuwa sukai cikin musabaha Rose kuma ta gaishesa kafin duk su zauna, binsu kawai da kallo Jawaad yake. Jabeer ya nuna masa takardar dake hanunsa yana faɗin, “Wannan sune bayanan da Ma'aruff ya kawo yanzun nan”. Jay

ya ɗago idonsa daga rubutun da yake yayma Jabeer kallo ɗaya ya ɗauke, “Ka buɗe mugani” ya faɗa hankalinsa akan Computer ɗin gabansa, sai dai sam bama ya fahimtar aikin da yakeyi ɗin.
        Buɗe  takardar Jabeer yayi, cikin nutsuwa yake bin komai da kallo daki-daki, a firgice ya kalli Jay cikin rawar harshe yace, “Ka duba wayarka, alama ta nuna kaine wanda ya turama saƙo na ƙarshe ta manhajar WhatsApp a ranar asabar da ƙarfe shida da mintuna talatin da huɗu (6:34pm), sai kiran wayoyi barkatai da akai masa amma babu wanda ya ɗaga a ciki, kuma wayardai tana a cikin jejin nan da muka gani jiya, abin farin cikin kuma har yanzu layin yana kan waya yana aiki alamar wayar tana a kunne”. Duk saurarensa suke, yayinda Jay keta ƙoƙarin duba saƙon Gimba, tabbas kuwa ya tura masan, amma sam hankalinsa bai kaiba saboda hidimarsa bata barima ya leƙa wata kafar yanar gizo ba a gaba ɗaya satinnan daya gabata. Babu wanda hankalinsa bai tashiba a cikinsu da wannan voice note na gimba, tuni jijiyoyin kan Jawaad duk sun miƙe ruɗu-ruɗu, muryarsa cike da damuwa yace, “Hafiz kaima Sir Ahmad magana ina buƙatar helicopter”. Cikin matsanancin tsoro suke kallonsa su duka, Aliyu yace, “Boss wannanfa dajine mai haɗarin gaske da ko soji suna masa shiri na musamman kafin su shigesa, idanma sun shigan ƙalilanne a cikinsu ke dawowa da ransu, baka tunanin ma wayar aka kai can dan a kauda mana hankali”. Cikin rufewar ido Jawaad ya bugi tebir ɗin gabansa, “Aliy!! ya kakeso nayi ne shin? Nabar yaron mutane mai mata da ƴaƴa har uku da uwa da ƙannen da suka dogara dashi a hannun waɗanda suke azzalumai?. Aliy ta dalilinafa suka kamashi, wlhy kaji na rantse maka sai ƙafata ta taka wannan jejin koda kuwa Gimba bayacan kokuwa nima ajalina nacan!”.
      Babu wanda bai firgita da alwashinsaba a cikinsu, sunaji suna gani ya fice daga office ɗin, basu da zaɓin daya wuce goya masa baya dan wannan shine alƙawarin da suka ɗaukama kawunansu duk rintsin da ɗayansu zai shiga suna tare dashi ɗari bisa ɗari. Cikin mintuna ashirin suka samu amsar helicopter daga hukumar sojoji tare da soji biyu da zasuyi musu rakkiya bisa tsayawar Sir Ahmad.
      Office ɗin Jay ɗin dai suka koma suna tsare-tsaren yanda zasu tunkari Jejin.

         A dai-dai wannan lokacin motar masarauta ta kawo bilkisu, godiya naima drivern da ko sunansa ban saniba na fice, shi kuma ya juya inda ya fito.
         Kaina tsaye office ɗinmu na nufa, a raina sai jina nake wani iri idan na tuna waifa akwai aure a kaina yanzun, aurenma na Boss. kowa yazo sunata aiki, shigowata yasa sukaimin caa da ido har gabana na faɗuwa da tunanin shikenan na mutu kowa yasan komai. Ummie ta taso da gudu ta ɗaleni tana murna, “Babie ALLAH banyi zaton ganinki ba yau a office”. Murmushi nai mata ina amsa gaisuwar sauran daketa min yaya jiki, sai naji daɗi da Ummie bata sanar dasu komaiba sai rashin lafiya.
         Na zauna a mazaunina idona akan Ummie da itama ta jawo kujerarta jikin table ɗina ta zauna. “Yanzu angonki yazo ya gama haukatamu da masifa anan”. Ta ƙare maganar da dariya. ɗan hararta nai na ɗauke kai bance komaiba, danni kam dama ta ambatosa jinai gabana ya faɗi. na shiga duba aikin dana bari,  Ummie kuwa na cigaba da tsokanata dan na tanka amma na shareta kamar banajinta.
     Dawood daya shigo yanzun ya ƙaraso gabana yana faɗin, “Bily Boss na kira”. Babu shiri na ɗago ina kallonsa, shiko yay ƴar dariya yana zama a kujerarsa dake kusa da tawa, “Kitafi da addu'a a baki dan wlhy yau a sama yake, yanzu naje office ɗinsa jinai kamar nai fitsari a tsaye da yanda yaketa masifa”. Ban iya cewa komaiba, Banida ikon kuma cewa bazanjeba, dan haka na miƙe cike da haushi na fita har Ummie namin dariyar ALLAH yasa aiki za'a bani dan taga kwana biyunnan hutawa kawai nake tunda bana zuwa office, ban kulataba na fice abina.
         Ina fitowa na hangesu sun fito tamkar zakuna, kowa fuskarsa a ɗaure musamman ma boss, gabana

1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

11 months ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment