Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

komawa kan karatun rayuwa.
Dan kuwa ƙawayena sun sake buɗe mun wasu shafukan koyan salo-salo dake maida mace mai aji da tsaftatacciyar wayewa, niko na nutsu wajen bin komai daki-daki ina haddacewa......


_________________________
BILKEESU
_________________________

Sai da su Shahudah suka cika sati uku cif sannan Jawaad yay ra'ayinma su kansu su ganshi, dan tunda ya saka aka kaisu aka ɓoye bai sake waiwayensu ba, harkokin gabansu kawai yakeyi.
Yau ɗinma dai tun safe yana office, yayi busy matuƙa saboda ayyukan dake kansa jibge.
Knocking akai dan haka ya bada izinin shigowa.
Bai ɗago ya kalli wanda ya shigo ɗinba, amma ya amsa masa gaisuwar da yake masa ta hanyar ɗaga hannu.
Ya jeho masa tambayar, “Lafiya kuwa?”.
“Lafiya lau Boss baƙine dakai”.
Jawaad dake rubutu ya dakata tare da ɗago manyan idanunsa ya zubasu a kansa, “Baƙi kuma? Maza ko mata?”.
“Boss namiji ɗaya ne dattijo sosai, sai kuma mata biyu da kamar dai budurwa”.
Shiru Jawaad bai amsaba, yadai kafeshi da idanu yana jujjuya pen ɗin hannunsa, yaɗan kaɗa hannunsa yana cigaba da rubutunsa yace, “Shigo dasu”.
Da to ya amsa masa ya juya ya fita.
Jay yaɗan tsaya da rubutu yana tunanin su wanene to? Bakinsa yaɗan motsa kaɗan kawai ya cigaba da abinda yakeyi, sai dai muryar da yaji tayi sallama ne ya sakashi ɗagowa babu shiri.
Kakansa ne da ƙannen mahaifiyarsa, ya ajiye biron da yake rubutun fuskarsa ɗauke da mamaki yace, “Baba kune anan?”.
Baba ya zauna da ƙyar yana ma Jawaad daƙƙuwa, “Kaci mai garin garinku, tunda gudunmu kake aini na biyoka har wajen ɓuyar taka ɗan jakar uba”.
Murmushi kawai Jawaad yayi ya koma ya zauna a kujerarsa yanama su Umman Batool sannu da zuwa, ya maida kallonsa ga Nabeelah datai musu rakkiya, “K miƙoma Umma ƙarama waccan kujerar ta zauna”.
Nabeelah ta amsa masa da to tana nufar kujerar dake gaban Computers ɗin office ɗin ta ɗakkoma Umma ƙarama.
Sanin halinsa da tayi ya sakata fita ta basu waje ita bata zauna ba, da kansa ya miƙe ya buɗe firijin dake office ɗin ya ɗakko musu ruwa da lemo ya ajiye yana sake musu barka da zuwa.
Su dai binsa kawai suke da kallo, dan damuwar da sukayi tunanin yana ciki sam basu ganta a tattare dashiba, sai ma ƙiba ƙamar ya ƙara da ƙyau.
Baba ne ya katse musu tunani da faɗin, “Ja'irin kaya, to yau ta gudu ta ƙare gani ga ka”.
Jawaad dake zama yace, “Haba mai ran ƙarfe ka iya rigima kaima, ni damafa ba gudu nakeba, kawai dai aikine yaymin yawa, iyayena kunajin mai ran ƙarfe fa ya sakani gaba”.
Umma babbace tace, “Ai gaskiya ya faɗa Jawaad, ka aikata laifi kuma ka koma guje-guje”.
“To Umma kema harda k? To duk laifin da ake tunanin nayi amin afuwa Please”.
“Ai ko munso yin fushin da kai bama iyawa Jawaad, amma hukuncin daka yanke akan matarka yayi tsauri da yawa duk da bata ƙyautaba” Umma ƙaramace mai maganar.
Jawaad da yay ƙasa da kai yana murmushi yace, “Baiyi tsauriba Ummana, hakan shine ya dace da Hudah tunda ita bata da hankali, lokuta da dama takan nunamin ita mai taurin kai ce, batasan nawa zafin kan ya zarce nataba, ina ɗaga ƙafane kawai bisa wasu dalilaina, bama ga itaba, su kansu waɗanda suka bata taimakon aikatawar zasuji shakkar aikata kwatan kwacin haka anan gaba”.
Baba yace, “Hakane Jawaad, dama wannan shi nake hango maka tun farko, dan Alhaji Ali yayi matuƙar sakaci da jagorancin tarbiyyar iyalansa, iyaye maza da yawa mukanyi irin wannan sakacin, ba komaine yake kawo hakanba sai ɗaukar kasuwancinmu da girma fiye da tarbiyyar yaranmu, mukan sakarma mata, bayan munsan hannu ɗaya baya ɗaukar jinka, bai zama lallai Uwar ƴaƴanka ta kasance yanda ya kamata uwa ta zamaba, saboda yanzu sam bama duba mai addini mu aura, ƙyale-ƙyalen duniya da adon jikin mace da zuri'ar data fito kawai mukafi kallo, sai kaga idan da raunin tarbiyya akan wannan zuri'ar kaima gidanka zai rayune a raunane, idanma ka samu mai addinin ka aura duk ƙoƙarinta sai kaga nauyin ya mata yawa sosai ta kasa kulawa da yaran yanda ya kamata, musamman ma da yanzu abubuwa ke ƙara taɓarɓarewa, dole tana buƙatar taimakonka, kama gina yaran bisa ƙyaƙyƙyawan tsari yaka ƙare balle ka rainesu bisa al'adun yahudu da nasara, ilimin boko ba haramun bane, ka saka ɗiyarka mace ko namiji suyi zurfi a cikinsa ba ɓarna bace, matsalar kawai ya kasance babu ilimin addini a cikinsa, to lallai kaima ka tabbatar da ɓarna a gidanka bama sai an faɗa makaba. Irin wannan sakacin shine Alhaji Ali yayi tun farko, mutane nawane ke rayuwa a wajen ƙasar nan kaga yaransu kuma a nutse cikin ƙyaƙyƙyawar tarbiyya, amma shi sai yay kuskuren rashin nuna musu hanyar ALLAH da dokokin saninsa, abinda ya sani kawai ya nema musu suci, ya basu ilimin boko saboda shine mutunci a yanzu. Wannan sam ba haka bane, maiyin wannan tunaninma sam bashi da tunani shi kansa. Nasan an cuta maka ƙwarai da gaske Jawaad, amma haƙuri shine magani, sannan banso kayi gaggawar yin sakinba shi kansa, dan hakan baida amfani sam, daka ƙara haƙuri munbi wasu matakai ko zata gyara”.
Jawaad yace, “Humm, baba ban katseka ba, amma ni nasan irinsu Hudah da wahala su zam cikin Masu gyaran, dan sufa gani suke sunfi kowa sanin abinda ya dace, sunema sukeyin mai ƙyau kowa wawane kidahumi a idanunsu, abinda ya bani matuƙar takaici shine wani kafirin banzane fa ya ɗorata bisa layi bayan ta haƙura zata haifi cikin, wanda ni a ganina maybe bayan hauhuwar tata ta ɗan canja wasu abubuwan, amma yazo ya sake rikita komai”.
Umma tace, “To inma banda jahilci tanada aure miye na wani riƙe ƙaton gardi wai abokinta, ba al'adarku ɗaya ba, ba addininku ɗaya ba, ba jinsinku ɗaya ba, sukuma su Hajiya Humairan suka zuba mata idanu tsabar rashin hankali”.
“Wannan ai shine illar sakacin da baba ya faɗa Yaya, dan inba sakaci ba da girmama al'adun yahudu wlhy hakan sam bazai faruba, yanzu dai komai dai ya rigada ya faru, haƙuri shine yafi cancanta ayi, sai kuma a tari gaba, Yarona ALLAH ya azurtaka da mace ta gari darajar haƙurin da kayi”.
Dukansu da amin suka amsa banda Jawaad da ya amsa nashi a zuciya.
Baba yace, “Yanzu dai Jawaad inason kayi haƙuri ka janye maganar zuwa kotun nan, sannan ka fiddosu daga inda ka ɓoye, nasan kai mai nutsuwane bazaka kaisu station ba dama, akwai dai inda ka kaisu”.
Jawaad ya ɗanyi jimm sai kuma yay guntun murmushi yana haɗiye abinda ya tokare masa maƙoshi, “Shikenan baba zanyi yanda kakeso, dan babu wani sharaɗi da zaku gindayamin na tsallakesa, dama suna gidan Qaseem ne”.
A tare sukace “Gidan Qaseem kuma?”.
Murmushi Jawaad yay yana faɗin, “Eh suna can, nasan halinsa baida hankali, tunaninsa kuma bazai taɓa bashi can na kai suba tunda yasan banma san gidanba, shi kansa bama ko yaushe yake zuwaba, idanma yaje ba ko'ina yake shigaba tunda babu kowa a gidan”.
Dukansu babu wanda mamaki da al'ajab bai fito a fuskarsa ba, yanzu nan duk wannan fafutukar da akeyi akan su Shahudah ashe gidan ɗan uwansu yaje ya ajiyesu, lamarin Jawaad sai shi.
Albarka sosai baba dasu Umma suka saka masa, shiko yana amsawa cikin jin daɗi.
Baba yace, “To maganar dawo da ita ɗakinta fa, shima kayi haƙuri kaji Abdull-Jawaad”.
“Ihm-ihm mai ran ƙarfe karka sake rikitomin sabon aiki, ayi haƙuri nayi kenan, nima inason naɗanyi ƙiba kamar kai ko a fuskane”.
Dariya suka ƙyalƙyale da ita, baba ya kamo hannun Jawaad yana faɗin, “Ja'iri yaji wuju-wuju, bazamu maka tilasba, ƙila nangaba idan ka huce ka maido kayarka koda bamu saniba”.
“Ai bama za'ayi hakanba” cewar Jawaad yana dariya su Umma na tayashi.

Har mota ya rakosu baba nata masa tsiyar wai yanzu sun koma ɗaya duk gwaurayene, wannan azumin zaiba yara su kaɗama Jawaad kiɗan gwauro inhar baiyi sauri yayi aureba..
Shi dai Jawaad nasa murmushi ne, dan yasan dai duk wayo akemasa danya tashi yay aure da wuri, shiko a yanzu dai kam yanda yasha wahala wajen Shahudah tamkar kurar wasa bai yi zaton sake kallon wata ɗiya mace da sunan wani abu so ba balle akai ga aure a yanzun, Kai shi a yanzuma haushi mata yakeji.


“Munga idi Shahudah ta ja mana tsiya a wajen Jay”.🤣🤣😂⛹‍♀


★★★★★★★

Bayan tafiyarsu Jay Office ya koma ya cigaba da aikin gabansa, dan gaskiya badan su bane bama zai iya sauraren kowa a irin lokacin nanba ma, gashi yanason fita wani waje kuma.
Ya sauke numfashi a hankali yana komawa bayan kujerar ya lafe, idanunsa ya lumshe yana maijin kewar mahaifiyarsa, sosai yake buƙatar ganinta a kusa dashi, badan ya rasa kulawa bane, shi dai yana so yaga ɗa a kusa da uwa, shiyyasa idan Qaseem na wani shirman yakan ga gatane kawai yay masa yawa.
Waya ya ɗauka yay kiran Hafiz akan yazo ya sameshi a office.

Babu jimawa kuwa saiga Hafiz ya shigo, zama yay bayan sunyi musabaha yana faɗin, “Boss ta samu ne?”.
Jawaad yace, “Kanka aka samu ko?”.
Dariya Hafiz yayi sosai, “Ba komai 1-0 kenan, nima lokacina na zuwa”.
“Zaka daɗe baka isoba kuwa, kasan miya farune?”.
“A'a” cewar Hafiz yana nutsuwa.
Jawaad yay guntun tsaki yana gyara zamansa, inason muje wajen yarannan, shima mai jan kunnen can dake a cell ku fiddoshi harma da likitan, sai dai shi likitan zamu dawo dashi dan wannan asibitin nasa sai mun masa bincike”.
“Ok Boss, yanzu naje mu shirya kenan?”.
“Ai da kai kaɗaima zamuje sai rose, tunda ga Securitys ɗinnan da aka mannamin dole”.
Dariya Hafiz yayi sosai, cikin dariyar yake faɗin, “Ni bansan miyasa bakason Securitys ɗinnanba, wlhy kuma suna ƙara maka ƙyau sosai, dan idan suka dafo maka bayannan dolene maƙiyi yaji tsoro, bakaga kwana biyu Qaseem ma ya shafa maka lafiyaba”.
Baki Jawaad ya ɗan taɓe, “Ai shi wannan bashi da cikakken man kai ne kawai”.


★★★★★★

Jack da Doctor suna nan tare da Jawaad a hukumarsu ashe, su Shahudah ne kawai a gidan Qaseem, kallo ɗaya naima su Jack tausayinsu ya kamani shida Doctor, dan daka gansu kasan ba ƙaramin jigatuwa sukaiba.
An fito dasu daga cikin wani cell aka jefasu a moto.
Dai-dai lokacin da Jawaad ke fitowa daga cikin Office nashi, yau ma dai yana cikin baƙaƙen Suit da suka zauna masa a jiki tamkar danshi akayisu, duk da dai rigar saman riƙe take a hannunsa bai sakaba, yakai hannu yana gyara tie ɗin wuyansa yana taku cikin ƙasaita da jin shifa ya kai, fuskarnan sam babu walwala a cikinta, kallo ɗaya yayma su Jack ya ɗauke idonsa.
Motar da aka buɗe masa ya shiga ya zauna suka fice.

Sun isa gidan Qaseem dake a wata anguwa da ban, gidan yayi ƙyau sosai matar aure kawai yake jira tunda maishi ya tsaya ruwan ido.
Jawaad bai shigaba, baima fita a motaba Hafiz ne kawai ya shiga shi da rose, babu jimawa sai gasu sun fito da su Shahudah.
Ba ƙaramin zare idanuba nayi akansu, Shahudah ƴar gayu ƴar ƙwalisa sati Huɗu babu wanka yay kuke tsammanin ganinta🥴? Ga tashin hankalin basusan inda sukeba, ga abubuwan da Jawaad ya shirya musu a gidan na ban tsoro babu duka babu zagi, kullum basa iya barcin kirki saboda tsoro🤣, ba kowane mai wannan aikinba kuma sai securitys nashi, su ya saka kullum dare suzo suyita abubuwan dake matuƙar firgita su Shahudah, wataran tsabar tashin hankali har fitsari sukeyi a wandunansu, ɓangaren abinci kuwa babu zancen mai daɗi, tsabar yasan Shahudah ma ta tsani tuwon dawa miyar kuka shi yake sakawa kullum batool tayo masa kuma bamai daɗiba a kawo musu, safe da rana da dare, daga ruwan Alwala kuma sai nasha kawai ake ajiye musu, hakan yasa babu damar wanka, to dama a tsare suke, duk bayan wasu awoyi kuma Rose na zuwa ta dubasu.
Tun Shahudah tana yunƙurin amai idan taga tuwon dawa har wahala ta sakata rinkaci tana toshe hanci, to taji zata mace a banza da yunwa, mutuniyarku tayi baƙi sosai kamar wadda ta taso a dokar daji, dama wajen kwanciya tabarma ne kawai aka basu, so babu dai marabar gidanma da prison, ƙilama gara jail ɗin, kowa kuma da ɗakinsa babu mai samun abokin hira ko yaji motsin dazai samu nutsuwa, dama can Rose haushin Shahudah takeji, dan a ganinta saboda Shahudah Jawaad yaƙi sonta😆, shiyyasa tafi takura mata sosai.
Har aka sakasu a mota suma baiko kalli sashen da sukeba, tun daga wajen ya sallami Rose da Hafiz akan su koma Office, shi kuma da securitys ɗinsa da motar dasu Shahudah ke a ciki suka nufi family house ɗinsu.

Da yake yammace sun sami Uncle's ɗin Jawaad ɗin duk sun dawo gida, shigowar motocin Jawaad ɗin ne ya saka mutanen gidan maida hankalinsu a kansu, ballema ya daɗe baizo gidanba.
Bai fitoba a mota ba har aka kammala fiddo su Shahudah kowanne hannusa da ankwa da yasa aka saka musu saboda son ya sake tada hankalin ƴan gidansu, su ɗauka daga wata uwa duniya aka ɗakko su Shahudah.
Aiko dabararsa yayi tasiri, dan ba ƙaramin tashin hankali kowa ya shigaba da ganin su Aamilah a wannan halin, gashi idanunsu duk a rufe.
Bai shiga sashen kowaba, koda ya fito a harabar gidan ya tsaya aka kawo masa kujera ya zauna ƙafa ɗaya kan ɗaya su Jack durƙushe a gabansa sai kace zamanin sayen bayi😂.
Duk wanda ya fito daga sashensa ya gansu haka sai zuciyarsa ta hautsina da tsoro da mamakin tsageranci irin na Jawaad, aiko harda masu koke-koke, shiko ko a kwalar rigarsa.
Mama Atika ta nuna Jawaad tana faɗin, “Kai dai ba yaron arziƙi bane, yanzu akan zubar da ciki kawai ka wajiga rayuwar waɗannan yaran haka?”
Ko kallon inda take baiyiba, ya bama gimba Umarnin ya buɗe musu fuska.
Uncle's nashi babu wanda ya iya cewa komai saboda tsabar mamakinsa.
Mummy kam zaman dirshan kawai tayi dan tama kasa cewa uffan, ta zubama su Aamilah idanu da Jawaad ɗin tamkar ta samu majigi.

Jawaad ya katsema kowa tunani, idanusa ya kafe Doctor dasu tamkar zai cinyesa.
Kasa jurewa Doctor yayi yay ƙasa da nasa cike da ƙara jin tsoron Jawaad ɗin har cikin ransa.
Murya a kausashe Jawaad yace, “Likita bokan turai ko? To nikuma Jay bokan likita, miyasa ka zubarmin da ciki?”.
Kai likita ya shiga girgizawa, cikin muryar jigatuwa yace, “Wlhy ban zubar maka da ciki ba, hasalima bansan wanene zaiyi amfani da allurarba, ni dai Zitun ce ta kirani ta haɗani dasu, wannan da waccan sukazo na basu allura suka tafi, amma bansan wa akaimawaba a cikinsu”.
“Uhyihmgg yayi ƙyau” cewar Jawaad yana maida hankalinsa ga Zaitun.
“To ke kuma mai nuna likitan dake zubda ciki fa? Kin taɓa zubarwa ne kema kenan? Shiyyasa har kika sanshi kika kai nawa cikin aka salwantar?”.
“Wlhy yaya, wlhy kaji na rantse ban taɓa aikatawaba, sannan bansan Shahudah ce zata zubar da cikiba, nidai kawai Aamilah ce ta kirani tace na faɗa mata inda zasu sayi maganin zubar da ciki, shine na sanar mata sunan Dr Jeo”.
“Kika sanar mata sunan Dr Jeo, to ke ina kika sanshi idan har baki da alaƙa da yin ɓarnar kema?”.
Hawaye na zirara a kumatun Zaitun tace, “Yah Jawaad ku gafarceni, wlhy sanadin ƙawata na sanshi, dan ita na taɓa rakawa aka zubarma ciki, shinema har na bama Aamilah labari, ni nama manta mun taɓa maganar, ashe ita bata mantaba shine a ranar ta kirani na haɗasu”.
Jawaad yaɗan matse idonsa cikin baƙin ciki, ya maida ga Aamilah, “To ke shugabar tawaga mi cikina ya tsare miki dan uwarki?” Yay maganar da ɗauketa da marin daya gigitata matuƙa ta nema jinta da ganinta ta rasa a lokaci ɗaya.
Babu wanda bai kauda fuskarsaba a wajen, Mummy ta fashe da kuka da tasowa zata riƙe Jawaad securitys nashi suka tareta, dan dama sune suka hana kowa ƙarasowa inda Jawaad din yake balle su Aamilah.
Sai da Aamilah taja kusan mintuna uku kafin hankalinta ya dawo jikinta, sai rawar jiki take tana hawaye.
“Ba magana nake dakeba!!!”.
Jawaad yay maganar cikin matuƙar tsawa.
“Brother zan faɗa maka gaskiya wlhy”.
Jawaad ya watsa mata harara yana huci, yace, “Karma ki faɗa, ki bari nakai ƙarshe wlhy dukan mutuwa zan miki”.
Aamilah na kuka da rawar jiki ta zayyane ma Jawaad duk yanda komai ya faru, kansa kawai ya kwantar a jikin kujerar yay shiru yana kallon Shahudah da tai ƙasa da kai tana hawaye, dan harga ALLAH wani masifar son Jawaad take ƙaraji da cikin data salwantar a yanzu, dan sai yanzu ta fahimci muhimmancin zaman cikin a jikinta.
Duk jikin mutanen gidan ya ƙara sanyi, saboda inhar gaskiya za'a faɗa Jawaad ya fisu gaskiya, dama kuma da yawansu suma sunajin haushin Shahudah saboda lalata musu komai da tayi.
Uffan bai sake cewa da kowansu ba, Shahudah da jack kuwa babu wanda yacema komai sai da ya miƙe, takawa yay a hankali zuwa gaban jack, cikin harshen turanci murya a kausashe yace,
“Na baka nanda awa goma sha biyu kacal, kabar ƙasarnan, inba hakaba, saina kaika inda babu wanda zai sake jin labarinka, kuma daga yau karna sake ganin wannan fuskar taka a ƙasata, idan ra'ayin zama take da kai, sai ta bika ƙasarka can ku ƙarata”.
Yana gama faɗaya ya wuce ta gabansu yana bama securitys ɗinsa umarnin su saki su Aamilah shi kuma Doctor su maida masashi mota.
Yanda bai cema Shahudah komaiba haka bai tankama jama'ar gidansuba kaf ya koma mota suka fice a gida.

Wannan al'amari shine ya kuma jijjiga zukatan ahalin Jawaad, daga kuma wannan rana ya ɗauke kansa daga garesu kaf ɗinsu, yazo duk wani abunsa mai muhimmanci a gidan ya ɗauke ya koma gidansa da zama, yamafi zama a headquarters ɗinsu dan dama can yanada gida a wajen, kawai dai bai cika zaman baneba saboda baya ra'ayi.
Duk kuma wata kaddararsa da takardunsa dake hannun Uncle's nasa ya basu umarnin maido masa, hatta da gidajen gonar mahaifinsa guda biyu duk ya amshe, hakama gonakin dake ƙauyensu suma dukya amsa sun dawo hanunsa.
Wannan al'amari ya matuƙar tada musu hankaki, harma suka fara tunanin kodai yasan manufarsu dama sharesu yayi?..........✍🏻


To amsa dai naga Jawaad, dan yanzune za'a fara wasan tunda maƙiyan ɓoye zasu fito fili wajen farauta🤸🏻‍♀, ga Jay namu kuma da alama ya shirya musu, dan haka kumuje zuwa my Sweet fans dan muji yaya wasan zai ƙare💃🏻🤫


*_ZAFAFA SABON KAFCE SUN DAWO GAREKU_*


_KADA KU MANTA MARUBUTAN DAI SUNE WANDA SU KA RUBUTO MUKU ZAFAFAN LITTATTAFAN NA BAYA, A YANZU MA SUN SAKE YUNKUROWA DA WASU SABBIN MASU SABON SALO_

_*KAUNARMU:* 💋❤️NA MAMUH GEE_

_*DAURIN GORO:* 💋❤️NA HAFSAT RANO_

_*ALKAWARIN ALLAH::* 💋❤️SAFIYYA HUGUMA_

_*GUDU DA WAIWAYE:* 💋❤️NA BILLYN ABDUL_

_*IGIYAR ZATO:* ❤️💋NA MISS XOXO_

_CANCADI DOMIN DUKKANIN LITTAFAN NAN ZAKA/KI IYA MALLAKAR SU A NAIRA DARI BIYAR_

_GUDA DAYA DARI BIYU_

_GUDA BIYU DARI UKU_

_GUDA UKU DARI HUDU_

_GUDA HUDU DARI HUDU DA HAMSIN_


_DOMIN MALLAKAR SU SAI A TUNTUBE MU TA HANYAR_

*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*


2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*

*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇

*09032345899*


_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_


Mucigaba da shakatawa da wannan dan yanzune aka fara kafta WASAN😁👉🏻📻



_Sannan akwai tashoshinmu na Youtobe da zasu fara kawo muku daɗaɗan labarai bisa tsaftataccen karatu, kuyu azamar garzayawa tashar *ALƘALAMI TV & MANHA HAUSA NOVELS* domin samun wannan gara ɓasa, a danna mana subscribing domin nuna ƙauna ta musamman masoyan gaskiya.😃🥰🥰💃🏻👌🏻_.







*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻Typing📲*_Typing📲_*


https://youtu.be/HFjVgQVnmn0


https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo



*_🧺ƘWAI_* _cikin_ *_ƘAYA!!🧺_*


*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_Wattpad:-_* _BilynAbdull😉_



*_____________________________________*
*_BOOK ONE_*
_Shafi na ashirin da tara_
*_____________________________________*


............Ɓangaren su Shahudah ma komai ya caɓe, gashi ma tunda suka fito bata da wani isashshen lafiya, su Mummy kuma sun kasa sanar mata maganar sakin da Jay yay mata.
Jack kuwa washe gari jirgin farko dashi ya tashi.
Abu ya tsayama Dad sosai a zuciya, idan ya zauna

1 Comments On KWAI CIKIN KAYA
avatar
zainab-nasir

11 months ago

Reply

Muna jin ddin yanda kuke ilimantar damu

Please Login or Register in order to submit comment